Showing 165001 words to 168000 words out of 238465 words
cewa
“Dan Allah Baba kar ka bari ta kaini a cire mun mutuwa ake yi ni kuma bana son na
mutu”.
Riqeta yayi sosai a jikinsa zuciyarsa na tafa sa, tausayinta ya cika shi ya
tabbatar duk abinda ya sameta qaddara ce da kuma halin Fattu ya janyo.
Cikin bacin rai ya kallo yan sandan yace “ku rabu da ita tunda naga Yata kuje kawai
zan zo station din anjima na gode”
Sukayi masa sallama suna harar Addah sukaja mota dan sun so sun samu damar moreta.
A motar sa ya saka Ummi ya zagaya ze shiga Addah ta biyo shi ba ko dar tana cewa
“Bari nazo mu tafi Alhaji, Talatu se munyi waya ko zan kiraki idan naje gida”.
“Idan kinje wane gidan? Da alama baki ji saqona ba kenan” Alhaji Murtala ya fada
yana dakatawa daga shiga motar da zeyi, Addah ko qoqarin bude mota take tana cewa
“Saqon me kuma wa ka bawa ya bani? Ni ba’a ce mun komai ba”.
“To bari na gaya miki yanzu da kaina, na yanke igiyoyin aurena biyu da suke kanki,
ma’ana na sake ki Fattu saki biyu”
“Alhaji ka sake ni fa kace kuma har saki biyu? Uku fa kenan ko ka manta akwai daya
daman?” Addah ta fada cikin ihu tana ja da baya hannunta aka, seda ya shiga motar
ya danna lock kafin yace mata
“Ina sane Fattu na gaji da halinki na dade ina Addu’ar Allah ya yakice mun ke se
yanzu ya karbi Addu’ata, zan ma aiko miki dashi a rubu ce saboda shaida” yana gama
fada yaja motar sa Addah kuwa kamar sabon kamu ta bishi da gudu tana ihun ta shiga
uku ta lalace.
*SODA COMMUNICATION📱💻📱
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*💃🏽💃🏽 with the validity of 30days at affordable
price we are available 24/7 08137145294
*MTN DATA*
1GB@280✅
2GB@550✅
3GB@850✅
4GB@1150✅
5GB@ *1400* ✅
10GB@2800✅
*AIRTEL DATA*
1gb@320✅
2gb@640✅
3gb@950✅
5gb@1600✅
*Pay through👇🏽👇🏽*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*🥰🥰🥰we are always there at ur service. WhatsApp/Call📞08137145294
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 51
Seda motar Alhaji Murtala ta bacewa Addah kafin ta tsaya tana haki ta dora hannaye
biyu akai tana rusa ihun ta shiga uku ta lalace
“Ni Murtala ze saka? Shekara Hamsin da aure ace zanyi zawarci gidan ubanwa yake so
naje yanzu wallahi be isa ba, ban saku ba dole na koma” Addah ta ringa sambatu tana
rusa kuka.
Anty Talatu ce ta ruqota suka shige gida tana cewa
“Se kace kanki aka fara saki ji yanda kika bishi da gudu kamar wata karya. To Fattu
ai ya miki da kyau ma daya tsaya a iya sakin dan ni na dade ina hasaso miki haka a
irin tashin hankalin da kika dade kina kwasowa bawan Allahn nan. Ni da ban kaini
Jaye jaye bama aka sake ni bare ke? Kawai muje ki share guri ga daki nan na kusa da
nawa ki shiga ki zauna Allah ya kiyaye na gaba”.
Kuka sosai Addah ta ringa sharba se kace qaramar yarinya. Anty Talatu tun tana bata
haquri har abin ya bata haushi ta tashi qarshe ma ta fice gaba daya ta bar mata
gidan ta tafi karbo zubin Adashen mutane dan ita uwar Adashe ce.
Se bayan Magriba ta dawo gidan, lokacin Addah tayi kukan ta dangana, dukda ba
haqura tayi ba ta bari ne zuwa gobe da safe zata koma gidan ta idan Alhaji yaqi
kuma zata bi Aminansa da yan uwa a saka baki dan bazata iya barin gidan nan ba.
Toh ta kama ina dan zaman ta da Talatu tasan ma ba me yuwuwa bane kawai dai zata
zauna na dan lokaci kafin komai ya daidaita.
Tana kan sallaya bayan ta idar da sallar Isha Talatu ta shigo tana ta masifa akan
matan sunqi bada zubi. A qofar daki ta zaune kan taburma, Addah ta leqo kamar wata
me takaba murya duk ta dashe saboda kuka tace
“Talatu se yanzu? Tun dazu nake zuba ido na jiki shiru ga duhu seda wannan yarinyar
ta dawo ta kunna mun fitila”
“Ba dole ki ganni yanzu ba Fattu, Mata saboda bala’i sun qi bada zubin Adashi ai
basu isa ba, gobe dirar Asuba zan wa kowacce kafin mijintavya fita sedai ayi wacce
za’ayi”.
Guri Addah ta samu kusa da ita ta zauna ta rafka uban tagumi, ga damuwar saki ga
Yunwa tana sakadarta dan ita sam bata da jumurin Yunwa.
Shinkafa Talatu ta sake dora musu suka ci da miyar dazu kafin suka kwanta tana ta
jan Addah da hira dan ta saki jikinta amma ina tayi shiru idan ka ganta bazaka ce
wannan Addahr bace yar rigima.
Washe gari Asubanci tayi ta tafi gidansu Amirah, a qofar gida suka ci karo da
Alhaji Murtala yana tsaye kamar daman jiran zuwanta yake yi kanta a qasa ta shiga
gaishe shi ya dakatar da ita da cewa
“Lafiya Malama? Me kika zo yi mun a gida?”
Gaba daya yau se taga yayi mata wani kwarjini tsoronsa ma taji tanayi, murya a
rarrabe tace masa
“Dama, am dama Alhaji kayan sawa ta nazo dauka”.
“Ki jira a nan, bari a kawo miki” ya fada yana shigewa ciki, ta yunqura zata bishi
kafin ta shiga ya mayar da qofa tana ji ya kullo ta ciki se ta saki baki kawai tana
kallonsa.
Tana nan tsaye kusan minti goma se gashi da Akwatu na biyu babba da qarami ya tura
mata gabanta yana cewa
“Sauran idan kika samu gurin zama se ki sanar mun na saka a kwashe miki kayan
dakinki dukka dukda dai da kudina kikayi su amma zan baki” ya sake shigewa gida ya
bar Addah da ta qame saboda tsabar mamakinsa.
Murtala dai Murtalan da ko kara ta ajiye be isa ya tsakkake mata ba shine yayi mata
wannan korat karen yau??
Almajirai tasaka suka daukar mata akwatunan nata, har tayi gaba ta tsayar dasu
daidai gidan Sa’adah ta shiga buga mata qofa.
Sa’adah na tsaye da mijinta ta rakoshi ze fita sukaji ana buga get, shi yaje ya
bude, yana ganin Addah ya tsugunna har qasa ya shiga gaisheta ta amsa tana
tambayarsa Sa’adah na ciki ne a daidai lokacin da itama ta qaraso gurin, tana ganin
Addah ta wani hade fuska, murya a daure ta ce mata
“Gani ya akayi?”
“Wace irin magana ce haka Sa’adah Addan kike cewa gaki ya akayi haka qatsal?”
Mijinta ya fada yana kallon ta.
Seda ta harare su daga shi har Addan sannan tace
“To ba nemana take yi ba nace kuma gani ko da wani abu bayan wannan?”
Ze sake magana Addah tayi saurin dakatar dashi da cewa
“Aa babu komai, daman kudi nazo ki aramun zanyi tafiya idan yaso zan saka Amirah
seta tura miki ta banki”
“Bani da su” Sa’adah ta fa mata kai tsaye tana juya wa da niyyar barin gurin seta
dakata ganin Mijinta ya dage rigarsa yana lalubo kudi daga Aljihun wando.
“Kan bala’i, ba yanzu na tambayeka kudin kacemun baka dasu ba shine zaka dauka ka
bawa wannan matar yanzu? To duk munafunci da kitimurmurar da kuke qullawa kai dasu
na sani kuma wadda kake rawar qafar akanta cikin shege tayi se naga ta tsiya”
Sa’adah ta fada tana kama qugu.
Be saurareta ba ya qirga dubu Ashirin cif ya bawa Addah ta kuwa karba ta hau godiya
kamar zata durqusa masa, be saurari zage zageb da Sa’adah takeyi ba yaja motarsa ya
bar gidan.
Addah kuwa me Napep ta tare bata tsaya ko ina ba se Asibitin da sukaje jiya dan
tana so ta karbo dubu Talatin da biyar dinta data bada kafin Alqalami.
Tsayar da me Napep din tayi, da yake Nurse din ta gane ta tana shiga kai tsaye tace
ta ciki na fitowa ta shiga ofoshin likitan haka kuwa akayi tana shiga likita ya
dago da murmushi a fuskar sa yana mata sannu da zuwa.
Gaisawa sukayi, ta gyara zamanta tace
“Likita se kaji mu shiru jiya ko? Chanza shawara mukayi abinda ya kawo ni yanzu ma
kenan na karbi dubu talatin din dana baka ka riqe biyar din kan ma ladan ajiya”.
Tunda Addah ta fara magana litita ya gintse murmushin da yakeyi, se da ta kai aya
kafin ya kalleta yace
“Wane kudi kike magana Hajia? Yaushe kika zo nan kuma kudin ma kika bani” ya fada
fuskar sa hade kamar da gaske. Se Addah tayi yar dariya tace
“Lallai likita aiki ya sha maka kai, baka gane ni ba nice fa nazo da yarinyata jiya
za’a cire mata ciki kace na bada dubu dari biyu na bada talatin da biyar akan zan
taho da cikon idan zamu can inda kace mu same ka din”.
“Inaga dai kinyi makuwa Hajiya, sannan maganar zubar da ciki fa naji kinayi ni ba
aiki na bane dan haka ki tashi maza ki nemi wanda kika bawa kudinki tunda wuri ma
kafin lokaci ya qure miki”
Ganin fa dagaske yana neman raina mata hankali yasa Addah ta fara daga murya tana
bala’i, Nurse din da take bada kayi ce ta shigo da sauri tana tambayar ba’asi
likita ya rufeta da fadan akan me zasu ringa barin masu tabin kwakwalwa suna shigo
masa, haka ta iza qeyar Addah suka fito tana ji tana gani aka korata waje ta ringa
Allah ya isan kudinta har suka je gidan Dada inda tace me Napep ya kaita.
Dada na zaune a tsakar gida abin duniya ya taru ya mata karo, Gaba daya bata jin
dadin zaman gidan saboda yanda Alhaji ya dauke mata wuta. Naziru da Sa’adu daman
tuni sun dena wunin gidan bacci kadai yake dawo dasu ga Fainusan da suke dan
harkoki tare itama ciwo ya lafketa tun jiya da akayi maganar fasa auranta take kuka
seda zazzabi yayi mata ligib sannan ta haqura.
Zaman da tayi a tsakar gidan ma wayar Bashir da ta manta rabon da suyi magana take
ta kira amma baya dagawa. Sababin da Addah ta shigo tana yi ne ya sakata janye
tagumin tana kallon qofar shigowa.
A kurar kusada Dadan ta zauna tana tsinewa me Napep din daya dakkota akan wai ya
tsuga mata kudi ita bataga zaman jiran da yayi mata a Asibiti ba.
Kallonta kawai Dada takeyi da akwatunanta data ga dai mitar bazata qare ba taja
Numfashi tace mata
“Ina zaki haka da Akwati niqi niqi Addah?”
Kamar wadda aka tunawa se kuwa Addah ta fashe da kuka tana cewa
“Dole ki ganni da Akwatu Nafi, Murtala ya sake ni sannan ya koroni. Dakansa ya
shiga ya hadomun kayana Nafi saboda tsabar wulaqanci” se kuka.
Salati Dada ta ringayi tana tafa hannu tace
“Yanzu shi Babansu Amirah me yayi zafi haka? Akayi haqurin kusan shekaru hamsin ma
se na dan taqin da yayi saura kai amma wannan abu beyi dadi ba, Allah yasa hakan
shi yafi Alkahiri”
“Wane Alkahiri ne acikin saki Nafi? Nidai yanzu idan Amadu yana ciki ki masa magana
ya roqar mun arziqi Alhaji yayi haquri ya mayar dani dan gaskiya ba zan saku ba,
tsofai tsofai dani naje ina nace ansake ni? Da can banyi zawarci da jajayen sawu ba
se yanzu da girma ya cimmani bani da sauran mamora wallahi baze yuwu ba”.
Nan suka shiga Daki Dada ta hau hada mata abin kari kafin Alhaji Amadun ya dawo. Se
gurin sha biyu ya shigo daga dubiyar da be samu sunje jiya da Sa’ad dinba, tun daga
tsakar gida yake jiyo maganar Addah ya girgiza kai a ransa yace
“Tazo kenan, koda wace fitinar take tafe yau kuma se Allah” ya shige dakinsa ba
tareda ya keqa su ba. Ba jimawa Dada ta shiga, bayanin dalilin zuwan Addah tayi
masa, cike da jimamin abun yace ta kirawo Addan tana zuwa ta zube a gabansa ta
shiga rusa sabon kuka, abin nata kamar tashin iska, tun dazu take warkajamin ta ta
manta da an sake ta se yanzu da taga Alhajin ta tuna.
A wayarsa ya kira Alhaji Murtala suka gaisa a mutunce kafin yace masa
“Idan babu damuwa Alhaji akwai maganar da nake so mu tattauna ne ko zuwa dare zan
iya zuwa gida na same ka”.
“Indai maganar Fattu ce Alhaji muyita yanzu dan babu buqatar zuwan ka ka sameni”
Alhaji Murtaa ya fada.
Se Alhaji Amadu yace “toh idan kace hakan, zan roqar mata arziqi kayi haquri ka
mayar da ita dakinta, mata haquri akeyi dasu Alhaji sannan aka iya share shekarun
da suka wuce ana haquri se da aka zo gangara tukunna dan darajar Allah kayi haquri
taci arziqin zuri’ar da take tsakani”.
“Wato Alhaji bana buqatar na gaya masa wacece Fattu dan sharrin ta har cikin gidan
ka ya iso, tunda na aureta kamar qaddara ban taba kwanan farin ciki a rayuwata ba a
kullum daga wannan bala’i se wannan zata kwaso mun, yanzu kana gani kaf dangi da
zuri’ar mu babu wanda irin wannan qaddara ta taba fadawa se ni a sanadin Fattu kuma
to ni kuwa naci gaba da zama da Fattu saboda me indai ba kuma so nakeyi wata rana
ta janyo mun Ajalina har gida ba” Alhaji Murtala ya fada, daga muryarsa zaka
karanci irin dacin abinda da yake ji a zuciyarsa.
Alhaji Amadu yaja fasali cikin jimami shima yace
“Na sani Alhaji ni kaina shaida ne amma abinda ya faru kaida kanka yanzu ka kirashi
da qaddara, kaga kuwa kota sanadin Fattu ko bata sanadin ta ba abinda Allah ya
hukunta faruwarsa seya faru da haka ina dai sake roqar mata arziqi, kayi haquri ka
maidata dakinta Allah yasa hakanya zamar muku kaffara”.
“Daga yanda ka dage kana roqona na tabbatar bata gaya maka saki nawa nayi mata ba
ko? To saki biyu ne. Kasan dama akwai daya tun shekarar dana auro Binta shekaru
Ashirin da biyar kenan yanzu na cikashe mata biyu ya zama uku kenan babu kome, taje
Allah ya hadata da daidai ita a gaba ni kam Allah ya yaye mun” Cewar Alhaji
Murtala.
Se Alhaji Amadu ya juya ya kalli su Dada da suka zauna kamar masu daukar karatu har
sun fara jin dadi ko Allah ze sa a dace yace
“Kayi haquri Alhaji, wallahi ban sani ba badan haka ba me ze kaini neman sulhu?
Shikenan Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri” ya amsa masa da Amin tun be kashe
wayar ba ya fara sauke musu kwandon bala’i ita da Dadangaba daya a kan me zasu
mayar dashi mutumin banza bayan sun san saki uku ne.
Hawaye Dada ta fara yi tana rantse rantsen itama bata sani ba ya hadasu yayi musu
tatas suka fito daga dakin ko wacce fuska da Hawaye.
A wayar Dada ta sake kiran Alhaji Murtala ya daga cikin masifa yake ce mata
“Ina ganin mutunchinki Nafi karki sake kirana indai akan abinda ya shafi Fattu ne
wallahi idan ba haka ba zaku sha mamakina “
“Nice Baban Amirah dan girman Allah kayi haquri, ni ko bazaka mayar dani ba to ka
barni naje nayi zaman Yayana” Addah ta fada cikin kuka.
“Wadanne Yayan zakiyi zaman su? Amirah dake gidan mijinta ko kuma Ummi dana Tura
Katsina itama data haihu zan daura mata aure dashi uban cikin nata, tsakanina dake
Fattu Allah ya isa bazan taba yafe miki ba kin cuce ni ki bata mun zuri’a amma kije
dan kanki” yana gama fadar haka ya kashe wayarsa, tana sake kira aka saka mata line
busy alamar ya toshe layin ma gaba daya.
Kwananta biyu a gidan Dada sukayi uwar watse ta kama gabanta, Alhaji Amadu kuwa
daman ido ya saka musu koda Dadan ta roqeshi akan Addah zata zauna a gidan be hana
ba dan ko ba komai Fattu jininta ce babu yanda za’ayi ya raba su amma ya saka musu
ido yasan halin su ze raba gashi kuwa tun ba’aje ko ina ba gayyar ta watse.
Gidan Anty talatun dai ta sake komawa, nan din ma bata rufa sati ba sukayi fada
qarshe dai har kasuwa tabi Baban su Amirah tana kuka akan ya rufa mata Asiri ya
barta tayi zaman Yayanta baqin ciki da takaici kamar ya kashe shi saboda irin
wulaqanci da tayi masa har cikin kasuwa fa.
Wani daga cikin abokansa ne ya saka baki akan ya taimaka ya bata gurin zama, dakyar
da taimakon Allah ya bata daki daya da bandaki a wani gidan Hayarsa ya kuma ce ze
ci gaba da bata ribarta duk wata tunda kudinta ne, taje ta kwashe kayan dakinta tas
ta siyar katifa kadai ta bati da yan kayan amfani ta koma gidan.
Haka dai da dadi babu aka kafa zaman zaman take tana ciyar da kanta, ba ta dai
haqura ba, tana nan tana tanadi zata nemi duk yanda za’ayi a shawo mata kan Alhaji
Murtala ta koma dakinta dan bazata iya wannan zaman ba dan ci uku ba wasa ba.
BAYAN WATA UKU
LAGOS NIGERIA
A cikin watanni ukun nan abubuwa da yawa sun faru na dadi da na rashin sa. A
bangaren Ma’u dai Abin dadi ne ya sameta na qarin matsayi data samu a gurin aiki
domin yanzu itace babbar manaja gaba daya a sashim su na siye da siyarwa ga kyautar
danaareriyar mota da akayi mata da kuma kudin haya da kamfani ya dauke mata banda
sauran Alawus kala kala da take samu.
Zuwa yanzu ta rigada ta saduda da komai rayuwarta takeyi ta jin dadi idan ka ganta
bazaka iya mata kallo daya ka dauke ido ba saboda yanda hutu da jin dadi suka ratsa
ta ta sake zama wata hadaddiyar Mace me aji bazaka taba mata kallon wadda ta haihu
har biyar ba tafi kama da irin manyan Yammatan Abujan nan da suka kwana biyu basuyi
aure ba.
A yanzu bata da wata damuwa a gabanta idan ba aikinta ba. Tana da isashshan lokacin
kanta ta je duk inda take so a sanda taso dan wani lokacin Ranar Juma’a zatayi musu
booking jirgi ita da Amnah su tafi Abuja ko Gombe suyi weekend su dawo, tun yaranta
na damuwa har zuwa yanzu sun rigada sun saba da rayuwar gida biyu.
Idan tana nan zasuje mata idan bata nan kuwa basa damuwa zasu zauna a gidan su ne
kawai tareda Abbinsu daya dawo kamar wata matar kulle daga gida se Office, dan
yanzu se anyi dagaske ne zakaga Bashir a qofar gida ma bare ya tafi wani guri.
ASMA’U
Yau ta kama Lahadi na tashi da shirye shiryen tarbar Yusuf daya ce mun ze zo, zuwa
yanzu na saddaqar da Yusuf yasan aurena ya mutu dukda be fada mun ba amma yana yin
yanda yake kirana a waya dukda ba ko yaushe ba se muyi sati biyu uku kafin ya
kirani, amma a duk snada ya kira se ya gaya mun wasu kalamai da zasu saka na rasa
nutsuwata na tsahon lokacin da zamu dauka kafin mu sake yin waya.
Tun safe na tashi nake ta shirya abinci, nasan Yusuf a wancan lokacin shima irin
Bashir ne suna da son abinci dan haka na tsaya na shirya masa kafiyayyun abinci
dukda bansan meya fi so ba amma nasan dole zasu burge shi.
Ina jera abincin akan Dining Bashir ya fado mun a rai, se nayi murmushi kawai a
fili na furta
“Rayuwa kenan, sekaga abu ya faru ya wuce kamar ba’ayi ba”.
mamaki nakeyi yanda gaba daya Bashir ya fita daga zuciya kamar wanda aka wanke da
ruwa dan idan ba ganinsa nayi ba ko kuma yara sun ambaci sunan sa wallahi mantawa
nakeyi da shi a lissafin rayuwata gaba daya.
Ba kuma dan na dena sonsa ba, Aa wannan abune da Allah ya halicci zuciyata dashi
kuma na yarda Son Bashir shine Jarabtata amma nayi qoqari na saka