Showing 39001 words to 42000 words out of 238465 words
zece daman kinga ai ta ta uwar tafi tawa a gunsa shiyasa ya saka mata
sunanta”.
“To da be saka ba dama Addini ne yace dole ayi ko kuwa da ze zama laifi” cewar
Goggo da shigowarta kenan. Muqus Asma’u tayi, dan tasan idan ta tofa wata fada ne
zata sha ita kam se taga kamar Goggo tafi son Bashir a kanta ma wani lokacin, bargo
taja ta rufe har kanta hankali tacewa Yaya Bilki “idan ta fita ki gaya mun” jin
Goggo ta ci gaba da magana.
Seda Goggon ta fita kuwa ta bude tana cewa “Ita Goggo bata san takaicin da ake
qullawa mutum ba tayi ta rufeshi da fada, wai fa kinji ma cewa yake idan mun koma
se mu bishi mu tafi ni nama fasa tafiya Sunday din sena tabbatar ya koma tukunna.
Sati uku mukayi dashi munci biyu se na qarasa sati na wallahi dan har Bauchi nake
so Naje wa Alawa sannan naje Jos ma”.
“Ai kuwa da ba kwana zakiyi a Bauchin ba nima da naje Alawiyya har tayi mitar ta
gaji ban taba zuwa ba” inji Yaya Bilkisu
“Kai haba dai amma baki kyauta ba wallahi ina Gombe ina Bauch” cewar Asma’u
“Ba haka bane kinsan yawan ci abin zuwan haihuwa ce to kusan tare muke haihuwa kota
rigani kona rigata amma daya baya Arba’in to sedai mu hadu a gida”.
“Eh to hakane”. Hira suka ci gaba dayi kafin sukayi bacci.
A Gombe kuwa washe gari Bashir ga haushin cinye masa nama gana tambayar kudi da
Amirah tazo ta fara masa da sassafe, buyagin gaske yai mata ya faffada mata
maganganu son ransa qarshe ta fita tana kuka da dana sanin zuwan daman Qawarta
Husna ce ta tsara mata yanda zataje ta same shi gashi babu biyan buqata se baqin
ciki ta kwaso tana shiga dakin ta kuma ta tarar da Addah ta cika baho da ruwan zafi
ta tube Iman tana shirin tsumbulata tai mata wanka.
Da mugun gudu Amirah ta tare ta hannun ta ya shiga cikin ruwan da sauri ta cire jin
zafin ruwan ta yayimi towel ta nade Iman tana kallon Addah data saki baki da Hanci
tana kallonta itama.
“Dan ubanki saboda zan mata wanka shine kika buga wannan tsallen kamar wata yar
ball kika kwace ta? So kike a bar ya mace ba wanka kusan sati biyu da haihuwa tayi
warin qashi To wallahi ba da ni ba dole a wanke mata dattin mahaifa”.
Ita dai Amira bata kula ta ba, se jijjiga Iman da ke dan kukan da ko muryar ba’aji
dakyau take dan ta firgita, jin Addah bazatayi shiri ba yasa tace “wai Addah baki
ji me likita yace bane gaskiya idan ba zaki mata irin yanda yace ayi ba ki bar
wankan kawai zan nunawa Inna Gaji ta ringa mata. Haka kawai idan wani abun ya
sameta ai nice da Asara kuma ji ruwan da kika saka kamar wanda zaki fige kaza”.
Salati Addah ta debo ta dire kafin ta shiga auno mata ashar tana cewa “kiji mun yar
banza ni kike shatawa layi akan wannan magen dan bazance mutum ba to kinyi da yar
halak in na sake taba ta kice shegiya nake” ta mike tana gyara zani tana ci gaba da
banbaminta.
Inna Gaji da shigowarta kenan ta tambayi ba’asi Amiran ta mayar mata seta dubi
Addah tace
“Wallahi Fatu kin fiya tada zaune tsaye in ba haka tunda ga abinda likita yace se
kibi na dan lokaci ne ko cewa akayi zata dawwama ba wankan ne se ki mata yanda suka
ce.
Yanzu kizo ki zunduma musu ya a ruwa bayan naji ance tana da munoniya wani abu ya
faru kinsan dai wannan sirikin naki manta komai zeyi wallahi har ni nan da babu
ruwa na qila se yayi qarar mu ai wannan ruwan yayi yawa...kaii” maganar ta katse
bayan data tsumbula hannu a ruwan, seta kalli Addah ido waje tace
Fatu kice kisan kai kika shirya wannan ruwan ko uwarta bata wanka da me zafinsa
shine zaki jefa wannan tatsitsiyar yar a ciki? To nidai inaga watan tafiyata gida
ya kama dan bazan iya zuwa polisteshan bada sutotimen ba”.
Addah da tayi tsilli tsilli dakyar tace “nifa ji nayi jikin ba kwari shine nake so
na gasata jikinta ya hade amma tunda banyi abin kirki ba shikenan kuda kuka iya se
ku mata” fuu tayi waje.
Wunin ranar haka ta yini mita duk wanda yazo seta gaya masa abinda Amirah tayi mata
kuma dai kowa ita yake bawa laifi.
Ganin dai dagaske Bashir baze bada kudin taro ba Addah ta shiga ta fita da abinda
Baban Amirah da yan uwanta suka hada da bashin Jama’a duk ta ganganda za’ayi bikin
suna. Kayan abinci dama ba matsala bane sunyi akan na Store dinta za’a diba ayi
komai.
Kaji kawai zasu siya se ruwa da lemo da kayan snacks se kuma kayan rabo da Amirah
ta nace se tayi dan har ta kira me
hoto yazo ya dauki Baby wanda za’a saka ajikin Jaka da Memo. Duk shirin nan basu
gayawa Dada ba tunda tace bada yawunta ba balle Bashir da ya rantse ya kuma
rantsewa baza’ayi ba shiyasa ma suka tsaida ranar Laraba bayan ya tafi litinan
sannan zasuyi sunan.
Allah kaimu ranar suna lafiya 😂😂😂
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 17
Ranar Litinin Bashir ya tafi a ranar kuma Asma’u ta dawo dan ta tabbatar daman
kafin su iso ya tafi. Da wuri suka taso dan haka sun sauka da wuri.
Gaba daya ranar baccin gajiya sukayi har zuwa washe gari talata sannan suka
wartsake. Da yamma ta shirya dan tana so ta fita harta kunna motar ta amma taqi
tashi tayi duk abinda zata iya amma taqiyi dole ta haqura ta kira Naziru ya zo da
bakanike suka dubata yace dole seya tafi da ita gareji haka suka lallaba suka tafi
se fasa fitar tayi.
Seda aka yi Sallar Isha tayi order Bolt, itada yaran suka fita, Shagonta na siyar
da kayan yara sukaje dan tana so ta siyowa Baby Iman riguna, basu bata lokaci ba ta
zabi masu kyau yan turkey guda uku se Shawl shima me kyau daya sannan tacewa yaran
kowa ya dauki abu daya da ze kaiwa Baby Iman.
A leda aka zuba musu kowa aka bashi nasa suka juyo zuwa gida, seda ta dakko Atamfar
data ajiye da zata hada musu da ita ta saka da qaramar Barimar Gold da tun cikin su
Ahmad ta siyeta da aka ce mata mace ce qarshe se gashi ta haifi yan Biyu duk Maza
tama manta da ita se zuwan nan ta ganta shine ta dakko ta hada musu da ita.
Yan uwan Amiran Suna zaune a palour sun baje kayan rabo ana zuzzubawa ita kuma tana
daga gefe tana duba dinkunan ta ga gadon Iman a kusa da ita Asma’u sukayi sallama
ita da yaran gaba daya.
A sake suka amsa musu, Amirah ta ajiye Kayan hannunta tana kallonsu, hada ido
sukayi da Ma’u, seda ta murguda baki ta juya ido sannan ta gaisheta ita ko Ma’u
data na ankare da duk abinda takeyi murmushi tayi kawai ta amsa mata a ranta tace
“zaki gane kurenki yarinya Allah sa kiyi kuskuren zagina wata rana”.
Addah da tajiyo muryar Asma’u tai wuf ta fito daga daki, bakin kaman ze tsage
saboda fara’a suka gaisa tana satar kallon Ledojin da suka shigo dasu.
“Miqo musu Yar mana Amirah kina zaune” Addah ta fada tana yiwa Amiran signa da ido,
se Amiran ta daga ido ta kalleta fuskarta na nuna alamun “kin san me kike cewa
kuwa” Ma’u da duk tana kallonsu tayi saurin cewa”Aa barta ma kawai bari mu qaraso
mu ganta kar a jagwalgwalata”.
“Wane irin magana ne haka ke gafara da Allah ki gani se ayita wani saka ya a ke ji
kamar kaza tunda tazo duniya ai dole a dauketa a haka zata saba” ta kwashe Net ta
ciro Iman ta miqawa Ma’u.
Bakinta dauke da Bismillah ta karbeta cike da taka tsan tsan, masha Allah kuwa ga
kamannin Farida nan a Fuskarta koda yake ai duk yaran da Bashir suke kama saboda
ita macece shiyasa kamar ta da Farida tafi fitowa. Tana hannunta duk yaran suka
leqata har Ahmad yana kama dan hannunta ya riqe.
“Mami muna son ta mu tafi da ita Lagos” ya fada yana wasa da hannun yarinyar, se
Ma’u tayi murmushi kafin ta amsa shi Addah tayi caraf tace “Da ita zaku tafi ai
Malam Amadu ko kuma in kunyi gaba zata biyo daga baya”.
Sunyi kaman minti Goma Ma’u ta miqe ta kwantar musu da ita kafin ta turawa Amirah
ledar kayan tace gasu nan babu yawa a sakawa Baby nan suma yaran kowa ya dire tasa
duk kowa da abinda ya tsinto mata banda Aliyu da daman shi a qofar palour ya coge
bema shiga ba.
“An gode madallah” Addah da sauran Yan gurin suka fada, sukayi musu sallama ta
tattara yaranta sukayi waje kamar suna jira suka shiga zazzage kayan a qasa.
“Ke Amirah kinga rigar da nake gaya miki wallahi yar dubu Ashirin da biyar dinnan
kin gani ga kudinta nan ma a jiki” Nusaiba Diyar Inna Gaji ta fada dan zancen rigar
da za’a sakawa babyn lokacin Shagalin suka gama take gaya mata akwai wadda tagani
ta fita kunya a gurin wata qawarta har sun fara shawarwarin yanda za’a samu kudi
aje a siyo se gashi Allah ya kawo mata daga sama.
Atamfar ta sake dagawa ta riqe baki tace “Amirah Embellished ce fa, bari dai muga
ko qaramar ce” ta hau duba lambar Atamfa da fentin jiki seta dau sowa tana cewa
“Wallahi babbar ce, ke harda dan kunnen Gwal kai lalai matar nan dagaske take Dama
Allah ya bani kishiya irin haka ai na huce takaicina se in ta haihuwa duk shekara
tana kawomun kayan arziqi” Nusaiban ta fada tana ta faman daga kayan.
“Ke na taba ki da Arziqi, wannan uban kayan da kudinta ko na mijin aka siya?” Asiya
yayar Amirah ta fada se Ummi da bata sa musu baki ba tayi caraf tace
“Ce miki akayi itama cima zaune ce irinku kuna zaune kuna jira se abinda miji ya
dakko ya baku, toh nema takeyi tana aiki tana kasuwanci ta kayan nan ma da kika
gani a shagon ta take siyarwa ga ledar nan kina gani”.
Ledar suka duba gashi nan kuwa “Asma’u Kiddies shop” a rubuce, se Nusaiba ta riqe
baki tace
“Lallai kice ta kama qasa irin wannan kaya yan order kodai ma shagon ne naji ana
zancen sa an ce duk Gombe Albarka ko da yake wannan iwar dukiya da aka mutu aka bar
musu dole suyi ta bude gurare, jifa Salon din Yayar ta Bilkisun nan ba abinda
ba’ayi na gyaran mace a gurin” Inji Asiyar,
daga nan kace nace ya kaure aka shiga fadar irin abubuwan da yan gidan su Ma’un
suka kafa, kowa fadi yake suna birge shi yanda kansu yake a hade bazaka taba ganin
wani abu wai shi yan ubanci a cikinsu ba.
Ran Amirah in yayi duba ya baci jin yabon da suke wa Ma’un, ta rasa a duniya
dalilin da yasa Asma’u keda farin jinin mutane, duk wanda ya budi baki sedai ya
fadi Alkhairinta badai sharri ba.
“Ke kanki shaida ce akan kyawawan halin Asma’u ai da mu’amarata me kyau” zuciyar ta
ta raya mata. Seta ja tsaki tabbas ita sheda ce akan karamcin Anty Asma’u, tana da
kyakykywar zuciya tabbas da mu’amala me kyau. Sannan sam abun hannunta be rufe mata
ido ba gata da sauke kanta matuqa bazaka taba cewa ta fito daga gidan arziqi ba
sedai idan ka dubi halayyarta kasan tabbas daga babban gida ta fito da suka tashi
cikin Arziqi suka jiqu dashi dan haka basu dauke shi a matsayin wani abun dagawa ko
da zesa suyi girman kai ba.
Tsaki ta kuma ja ganin itama ta bige da yabon Ma’un a zuciyarta, tabbas tana kishi
da Asma’u da duk wata halayya ta ta. Ta kan ji dama ita ce Asma’un, bata kasance
yar Babban Attajiri kamar Baban Asma’u ba kuma wannan ne kadai tasan bazata samu ba
amma baya ga haka tayi Alqawarin duk abinda Ma’u ta mallaka seta seta same shi.
Tayi zurfi cikin tunaninta har bata san sun gama zuba kayan ba kowa ya fara neman
makwancinsa se itama ta miqe ta dauki Iman suka shige daki suka kwanta saboda su
samu tashi da wuri.
A bangaren Ma’u ma suna komawa kowa ya nemi makwanci da wuri nan da nan bacci ya
dauketa dan bata ma ji jerin missed calls din da Malam Bash ya ringa jera mata ba
har bakwai seda Asuba data farka. Seda tayi sallah ta kirashi, qorafi ya hauyi mata
akan rashin Amsa wayar ta samu ta bashi haquri akan bacci ne ya dauketa, basu jima
ba sukayi sallama kafin ta sake komawa bacci.
Qarfe goma na safe sautin kidan kwaryar da ake a filin gidan ya tasheta, da farko
ta zata ko kunnenta ne beji daidai ba, seda ta kasa kunne sosai sannan ta tabbatar
dagaske fa a cikin gidan ne dan ga hayaniyar Mata nan tana jiyowa.
Miqewa tayi zuwa jikin window dan tana dakin ta na saman Bashir ne, labulen ta
janye ta leqa da mamaki take kallon Mata masu kidan kwaryar da kuma wadanda suke
juyi a fili suna watsa musu kudi.
“Ikon Allah to me akeyi a gidan?”Ta fada a fili, ganin babu me bata amsa yasa ta
saki labulen, gadon ta fara gyarawa kafin ta shige toilet tana ci gaba da mamakin
abun. Wanka tayo ta shirya cikin wani danyen Lace Baqi da akayiwa kwalliya da Jan
Zare ya karbi farar fatarta sosai da sosai ta kashe dauri tareda baza turarenta
kafin ta dauki wayarta ta fito daga dakin takalmin qafarta na kwas kwas.
Palour kasan qal dashi Aliyu da Amna na zaune akan Dining suna karyawa duk sunyi
wankan su. Gaba daya suka gaisheta tana shirin tambayarsu sauran Ahmad ya bude qofa
ya kwaso da gudu Muhammad na bayansa har yana neman faduwa ta tare shi
“Ya haka bana hanaku guje gujen nan ba se kunji ma kanku ciwo ko” ta fada bayan ta
tsaida Ahmad din.
“Mami biki akeyi a waje zo ki gani harda masuyin kida da calabash irin na gidan
Baba Sarki” Ahmad din ya fada.
“Nima naji kidan tun ina sama ai me yake faruwa a gidan ne?” Tayi tambayar tana
kallon Amna da Aliyu dan sune manya.
“Wai suna waccen matar sukeyi” Aliyu ya fada ba tareda ya dago ya kalleta ba.
“Wace matar“ ta tambaya tana tsare shi da ido dukda ta gabe wa yake nufi amma se
yaqi ya dago bare ya kalleta kuma yaqi magana se ma kaida kansa gefe da yayi.
“Yayi kyau matar Baban naka ce waccen matar ko Aliyu idan na sake ji se ranka ya
baci tabbas” ta fada tana jan kujera ta zauna. Tea ta hada ta debi dankalin da suka
soya dan da zafinsa ta hada ta fara ci a ranta tana ayyana kenan bikin suna sukeyi
yau, sekace dole su kuwa ai da sun haqura sa hadu a wani karon amma to ita ina
ruwanta ma.
Tsaf suka gama cin abincin ta koma cikin palour ta zauna, wayarta ce ta shiga qara
Amna dake kusa da ita ta miqa mata. Zahra ce take kiranta Qawarta ce tun ta yarinta
tare suka tashi daman sunyi da ita yau din zata zo bayan sun gaisa kuwa take shaida
mata tana nan tafe fa gurin qarfe biyu na rana sukayi sallama ta kashe wayar.
A hankali hayaniya ta kaure gidan mata kuwa se shigowa suke kamar ana tunkudo su
lokacin har sha biyu tayi ta dena jiyo kidan kwaryar da alama sun tashi ne sedai
hayaniyar mata kawai.
Saboda zuwan Zahra yasa ta shiga kitchen, fried rice ta dora ta window kitchen din
da yake kallon tsakar gidan take kallon ikon Allah yanda Jama’a ke tururuwa a gidan
nasu wasu na shiga wasu na fita. Bata tsinke da lamarinba seda ta ga an wangale get
ana shigo da kujeru harda Wata rumfa da kayan decoration ba bata lokaci suka shiga
har hadawa kuwa
“Shagali kace abin nayi ne to Allah yasa a tashi lafiya” ta fada a fili tana hada
salad dinta, kafin ta gama kuwa har sun gama sauke kaya sun hau shiryawa ga kayan
DJ an ajiye daga gefe suma.
Harabar gidan nasu nada dan girma ba laifi dan a qalla zataci mota biyar zuwa shida
saboda filin gefen su da Bashir ya shigo dashi yayi ginin Bangaren Amirah ya ragu
sosai shi ya qarawa gurin girma. Tsaf suka gyare ko ina aka jera kujeru can daga
gefe ga High-table an shirya se zama kawai ya rage.
Tsaf ta gama girkinta suka jere kayan akan Dining tana shirin shiga daki tayi
sallah dan har biyu ta kusa a ka kwankwasa qofa, jafar tacewa yaje ya bude ta dan
daka dan taga wanene.
Sadiya da Afiya ne qannen Bashir se Suwaiba diyar qanwar Baban su suka shigo ko
wacce da shirgin Jakar kaya a hannunta ga yara na biye dasu. Kada ran kada han take
kallonsu har suka qaraso tsakiyar palour suka zube akan kujeru suna wash Allah jij
sanyin Ac da qanshin turare na ratsa su.
A kusan tare suka gaisheta, Asma’u da bata dara daga inda take ba ta amsa tana
kallonsu da jiran ji da wacce suka zo kuma.
“Ku tashi mu shirya lokaci ya na tafiya dan nasan yanzu zakuga shagali ya kankama
fa kuma ni ko wanka ma banyi ba na fito daga gida” inji Sadiya
“Ai bake kadai ba nima banyi wankan ba haka na fito” Suwaiba ta mara wa Sadiyan
Baya suka miqe kowacce ta sabi jakarta suka doshi corridor da dakunan suke inda
anan Ma’u ta coge. Seta qara gyara tsayuwarta ta yanda ta raba hanyar biyu ba ta
yanda wani ze wuce fuskarta na nan a yanayin da bazaka iya fasaltawa ba.
“Bari mu wuce Anty” Sadiyan ta fada
“Zuwa ina?” Asma’u ta tambayeta, se suka kalleta duk su biyun da mamaki, Suwaiba ce
tayi qarfin halin cewa
“Wanka zamuyi”.
“To yaushe gidan nan ya zama gidan wanka kuma bani da labari?” Ta fada tana gyara
tsayuwarta da jinjinawa rainin hankalin wadannan yaran ta kuwa shirya nuna musu
iyakarsu yau dan yanzu ba da bace.
Kallon kallo aka shigayi tsakanin Suwaiba da Sadiya, still Sadiyar ce ta sake
magana dan tafi sauran baki tace “ban gane ba Anty wanka fa mukace miki zamuyi anan
kine zancen wani gidan wanka kuma ko bamu da damar da zamuyi wanka a gidan dan uwan
mu ne?”
“Allah sarki masu Dan uwa dama kuma babu ita kuna iya juyawa kuje wani Gurin tunda
bani kadai bace a gidan ko? Ina ga ai kamar a kwai yar uwarku ma kuna iya zuwa
gurinta”.
Ba qaramin mamaki ne ya kama su ba da jin kalaman ta, Antyn da ada a dakinta suke
duk wata dabdalarsu qarewar wanka har kayan sawa ta kama basu take idan ana wani
taro ka zo da kayan da basu kamata ba seta dakko na fita taro ta baka ko yanzu ita
Sadiya bata zo da mayafin da zata hada kayan da zata saka ba dan a safiyar nan suka
samu labarin taron