Showing 87001 words to 90000 words out of 238465 words
inda duk ihun ka bazaka iya
fitowa ba” yana gama fada masa haka ya shige motarsa ya bar Bashir da cizon yatsa.
BASHIR
Ko kusa beyi nadamar abinda ya aikata ba dan a ganinsa yayi irin abin nan na ya
tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro. A tunaninsa dole Asma’u zata bishi ta roqe shi ya
maida ita dakinta, shi kuma ya qudurce se ya gama wanata son ransa tukunna ta gane
muhimmancin sa sannan se ya mayar da ita. A lokacin yasan ta biyu ta yanda ko kara
ya ajiye mata bazata tsallake ba.
Be damu da kwashe kayan ma da tayi ba, sema guri daya samu a palour ya dora kafa
daya kan daya, a cikin kudin da yayi niyyar biya musu umara shida itan ya yi order
sabon gadon da za’a saka a dakin da ta cire nata da kuma labulaye kai kujerun ma
chanza su ze kawai idan yaso kayan Kitchen in Amirah tazo se ta siyo da kanta tunda
shi be san abinda ake buqata ba.
Koda ya shiga dakinsa ma yaga kaya a watse be wani damu ba yasan duk cikin haushin
sakin ne yasa tayi haka, se kawai ya tattare ya watsa su kan gado yayi shigewarsa
Toilet yayi wanka kafin yayi shirin bacci ya zauna akan kujera da wayarsa a hannu.
Cikin sa da yayi qara ne ya tuna masa da yau fa be ci komai ba, se ya miqe ya fito
palour kai tsaye ya wuce gurin Dining sedai kafin ma ya qarasa ya hango shi wayam
daga teburi se kujeru, yar Show gilas din kwanukan da ta qawata gurin ma an dauke
bare yasa ran samun wani guntun abinci.
Dolensa ya sake fita ya siyo abincin a waje a ransa yana cewa “Dole yarinyar nan ta
dawo a satin nan dan bazan iya sintirin zuwa siyen abinci ba, yana gama ci ya ahige
daki yayi kwanciyarsa abinsa.
ASMA’U
Qarfe 11 na dare ina zaune akan abin sallah tun bayan da nayi sallar Isha ban tashi
ba, gaba daya hankali na yayi nisa da inda nake na yi nutso a cikin kogin tunanin
abubuwan da suka faru dani tun daga haduwata da Bashir har zuwa yau daya yanke
alaqar da take tsakanin mu.
Tiryen tiryen komai ya ringa dawo mun lokutan da suka kasan ce masu dadi a cikin
rayuwar mu da wadanda suke aka sin haka, haduwar mu ta farko da Bashir wadda har
muka qulla soyayya a tsakanin mu nake tunawa.
ASMA’U ABDULLAHI TUKUR shine cikakken sunana. Baffan mu Alhaji Abdullahi haifaffen
Kumo ne ta Jahar Gombe.
Yana da matan aure guda hudu Hajia Babba da Hajia Umma rana daya aka saka musu
lalle se Hajia Anjim kafin ya auro Goggon mu Maryam daga qarshe.
Ita Goggon mu yar Asalin Numan ce kuma Babanta shine limamin garin a lokacin. A
yanda aka gaya mana asali ba Baffan mu Goggon zata aura ba, Baffa Sama’ila Amininsa
ne saurayinta wanda har an saka musu rana cikin tsautsayi a ranar da za’a daura
auran ya gamu da mummunan hatsari akan hanyar su ta zuwa Numan daga Yola wanda yayi
sanadiyyar tabuwar lakar bayansa dalilin da yake kwance kenan har yau yana jinya.
A lokacin su Baffan mu sun riga su isa garin, bayan da aka samu wannan mummunan
labari hankalin kowa ya tashi har aka watse daga taron daurin aure seda Baffa
Sama’ila ya bar wasiyyar akan Baffan mu ya auri Maryam dan beyi zaton ze tashi ba,
haka kuwa akayi se kawai gani sauran matansa sukayi yazo da Maryam da suka je bikin
Amininsa a matsayin kishiyarsu babu kuma wata jayayya ko tashin hankali suka
karbeta tamkar yar uwa.
Zaman gidan mu zama ne me tsafta tsakanin matan guda hudu wanda suke kishi gurin
kyautatawa mijinsu da qoqarin ganin ko wacce ta zama ta gaban go shi bata hanyar
cutar da yar uwarta ko tashin hankali ba.
Allah ya azurta Alhaji Abdullahi ta kowanne bangare domin ya masa arziqin Dukiya,
mata da kuma Yaya saboda seda ya haifi Yara 42 inda biyu suka mutu tun kafin a
haife ni yanzu haka mu 40 cif muna raye Maza 24 mata 16.
Mu 8 ne a dakin mu, maza uku mata biyar.
Zan iya cewa kusan nice mafi soyuwar ya a gurin mahaifina kodan ina da sunan
mahaifiyar sane amma dai kowa ya shaida nidin yar gata ce ta gaske, Baffan mu yayi
matuqar qoqari gurin bamu tarbiyya tareda hada kanmu dan bamu san wani abu wai shi
yan ubanci a gidan mu ba mun tashi tamkar tsintsiya baka taba banbance yan wannan
daki dan kowa inda yake so yake warkajamin sa.
Dukda kasancewar Baffa beyi boko ba amma yayansa ya bamu damar yin ilimi iya yanda
kaso kuma mata da mazan mu, baya tsawwalawa, dukda anayiwa mata auran wuri a
lokacin sam shi babu ruwansa idan yayyen mu mata sun gama secondary school yana
basu zabin aure ko makaranta wanda kika dauka shi zakiyi dan tun duniya na kwance
Baffa yake fitar da yayansa mata qasashen waje suyi karatu, idan ma kuma kina
karatun kika fitar da miji dukka ze miki auranki.
Nice ya ta Ashirin da bakwai a gidan mu, Ma’u kwalisa shine laqabin da akeyi mun a
makaranta saboda yanda Allah yayi ni dason gayu abin ya hade mun da irin qirar
halittar da nake da ita dan haka nake bawa gayu haqqinsa yanda ya kamata.
Tun muna SS1 na qudurce a raina nifa dana gama secondary aure zanyi duk kuwa da
yanda nake da qoqari sosai a makaranta nidai kawai aure nake so abinda ze baku
dariya shine ko saurayin bani dashi dan bana kulasu, ni a lokacin ma duk wanda yace
yana sona tofa ya zama abokin gaba ta har tsokanata yan gidan mu sukeyi indai kana
so muyi rigima dakai to ka nuna wani kace saurayi nane.
Ranar da muka fara haduwa da Bashir wata rana ce mun taso daga islamiyya da yamma,
muna hanya wani da Ake kira Ibbah saurayine dan layin mu daya nace shi ala dole
sona yake yi mun taho a hanya kawai ya tare mu.
Ibbah girman Ingila ne acan aka haife su dan basufi shekara biyar da dawowa Nigeria
ba dan haka gaba daya dabi’unsa na turawa ne abinda yasa nake qara tsanarsa kenan
muna tafe muna hirar mu se ganin sa kawai mukayi a gaban mu ya kalleni yana
murmushi yace “Hey pretty yau na kamaki bazaki gudu ba, tsaki nayi masa na murguda
baki kafin na kauce ina cewa
“Aikin banza mutum kamar maye yayi ta bin mutane, se kayi tayi ai dan wahala” nayi
gaba abina se ji nayi caraf ya riqomun hannu banyi wata wata ba kuwa na kwashe shi
da mari kafin na hau zazzaga masa tsiwa ina zaginsa.
Tahowar da Yaya Abubakar din gidan mu da Abokanan sa uku yasa na dakata ina hararar
Ibbah dayayi mutuwar tsaye yana kallona, Yayan ne ya tambayi meya faru Alawiyya
tayi caraf tace masa “Ma’uce ta Mari Ibbah saurayinta” tun kafin ta gama na juya
kanta da masifa ina cewa
“Ta ina ya zama saurayina wallahi karki sake hadani dashi niba saurayina bane”
kawai na saka kuka kawai se suka samun dariya dan yanda nayi abun seka rantse wani
mugun abu aka jinginani dashi.
Daya daga cikin Abokan Yaya Abubakar wanda ban sanshi ba, cikin taushin murya yace
mun “waya gaya miki mekyau tana yin kuka rabu dasu ba saurayin ki bane ki share
hawayenki”.
Haka kawai naji ya burgeni, na saka hannuna na goge fuskata tsaf kuwa fuu nayi gaba
na barsu suna ci gaba da yi mun dariyar ina jin Yaya Abubakar na bawa Ibban haquri
kafin ya taso su Alawiyya a gaba suka biyo bayana.
“Ma’u danja Ma’u rigima daga ance mutum saurayinki kawai ki kama kuka ke wai baki
san kin girma ba” Bala daya daga cikin Abokan nasu ya shiga taokana tun kafin ma na
bude baki Yaya Aliyu da duk yafi sauran abokan su kirki ya tareshi da cewa
“Zaka fara ko Bala, Ma’u kyaleshi yi shigewar ki gida” seda n harari Bala na
murguda masa baki kafin na shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba
nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa su Yaya suke kula shi ba.
Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin
abun da ya faru
“Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma
sukeyi mun” na fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar
wata yar jaririya zuba tabara nake son raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make
ni.
“Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki
kiyaye kar a sake kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri
kinji ko” Baffan ya fada. Sena marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba.
Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har
gidan su Ibbah na bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma
Maman sa se nan nan take dani wai yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana
kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole turawa.
Muna zuwa qofar gidan mu muka ci karo dasu Yaya Abubakar yau ma su na zaune, gaishe
mukayi ina ta satar kallon na jiyan nan daya maida hankali yana danna waya so nake
naga ko zeyi mun magana amma har muka shige gida be ko dago ya kalle mu ba.
Baki na tunzura nayi wucewata dakinmu, inajin su Alawa suna cewa nazo mu raba kayan
da Maman au Ibbah ta bamu nace bana ci nayi kwanciyata ina jin haushin da ban san
koma mene ne ba.
Da daddare Yaya Abu yace na dafa musu Indomie, ina gamawa na juye a flask na bawa
Khadija ta kai musu ina zaune a palour Hajia Umma se gata wai naje inji Yayan yana
kirana.
Suna zaune a tsakar gida daga gefen inda akayi kujeru na sumunti da tebura, su
hudun dai kamar kullum ga kular Indomin a tsakiya an cinye tas Yaya Aliyu ya
kalleni yana cewa “wai Bashir ne yace ne yadda ke kikayi girkin nan ba shine muka
kiraki ki gaya masa da kanki”
“Wai daman Yaya Bashir kaine” na fada da mamaki ina kallon wanda aka kira da Bashir
din. Se yanzu kuma nagane fuskarsa Bashir din gidan Baba me Mota ne, rabon dana
ganshi har na manta tunda su ka fara zuwa Jami’a shi aka ce A Zaria ban sake
ganinsa ba kusan shekara shida yanzu.
“Daman Fainusa tace Yayansu ya zama dan gayu ashe dagaske take “na fada ina zama a
gefen Yaya Abubakar, se Bashir ya dago ya kalle ni yana murmushi yace “dagaske? Har
nakai ki gayu?”
Rufe fuska nayi da mayafina irin naji kunyar nan, sosai na ringayi masa tambayoyi
meyasa na dena ganinsa yace makaranta ce tasa saboda nisa baya zuwa gida se qarshen
shekara, duk sanda yake zuwa mu kuma bama nan munyi tafiya. Haka na shantake seda
Goggo ta aiko kirana sannan na tafi.
Tundaga wannan ranar kullum da daddare idan na dafa musu indomi zanje na zauna ina
taya su hira kuma duk saboda Bashir dan haka kawai nake jin ina son yin magana
dashi, haka ko a cikin gida banida labari se na Bashir yayi Bashir yace kaza ana
haka muka fara shirin qualifying exam daga ita zamu shiga SS3.
Bashir ne yake tayani karatu yana ganar dani inda ya shige mun duhu, wannan
kusancin da muka qara samu ya saka Shaquwa sosai ta shiga tsakaninmu dan idan na
wuni ban ganshi ha har ji nakeyi kamar bani da lafiya gashi lokacin sun fara
Service dan ma anan Gombe yakeyin nasa.
Banfarga cewa nayi nisa a soyayyar Bashir ba saboda ban ma san menene so ba, abu
daya dana yarda Ya zama wani bangare na jikina haka ina bala’in jin haushin na
ganshi yana magana da wata mace ranar haka zan wuni ina qunci.
Yaya Bilkisu ce ta fara haska mun cewa son Bashir nakeyi, nayi futu futu nace
qaryane ni ba wani so kawai dai Allah ne ya hada jinin mu amma a qasan raina ina
jin dama hakan ta kasance yace yana sona dana ji dadina kuwa.
Mun shiga SS3 kamar anyiwa Samari bushara da zuwa gurina sukayi mun caaa saboda
yanda kyau da surata suka sake bayyana sosai, ban kuma canza hali ba ina nan ina
tatawa duk wanda yace yana sona rashin mutunchi a qasan raina kuma ina cike da
damuwa da takaicin me yasa shi Yaya Bashir baze ce yana sona ba se wannan banzan
Balan ne ranar ya wani ce wai yana so na se kace nayi masa kalar budurwar yan shaye
shaye.
Muna second term aka fara Registration na Jamb, duk su Alawiyya sunyi ni kuwa ranar
da za’a kaisu siyi qin zuwa nayi nace banida lafiya, washe gari da yamma Su Yaya
sun shigo gida ake hirar, Ina ji Bashir na tambayar kowa course din daya cike nayi
banza dasu sanda yazo kaina har seda Junaidiyya ta tabo ni sena tura baki nace
“Ni ba zanyi ba”.
Kafe ni yayi da idanunsa masu sakani a wani irin yanayi da bansan na menene ba yace
“Me yasa bazakiyi ba?”
“Haka kawai” na fada ba tareda na kalleshi ba, se ya miqe yace na biyo shi muka
fita can tsakar gida inda muke zama muna hira.
Idonsa akaina na sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna yace mun “me yasa
bazakiyi Jamb ba”
“Ni babu komai kawai bana so nayi” na fada ba tareda na kalle shi ba.
“Toh aure kike so kenan?”
Sena dago da sauri na kalleshi, ganin ni yake kallo se na sauke idona ina tura baki
nace
“Ni ban ce haka ba”.
“Toh idan ba aure kike so ba me yasa bazaki ci gaba da karatu ba bayan ma ko
saurayin baki dashi wa zaki aura ma”.
Harara qasan ido nayi masa kafin nace “Allah ze kawo ne Idan lokacin yayi”
“Idan kuma yanzu ya kawo fa” ya fada cikin qasa da murya, se na daga kai na
kalleshi.
“Allah kasa yace yana sona” na fada a raina tamkar kuwa Bashir yaji ni se ji nayi
yace
“Idan kuma ni ne mijin naki fa Ma’una zaki aure ni?”
Abunku da ba kwaila tsabar murna se kawai na tashi nabar gurin da gudu ina dariya
ina jinsa shima yana mun dariya abinda ba kasafai ya fiya yi ba.
Kan gado na na hau na ringa tsalle ina ihun murna, Yaya Fati Dake kwance akan Nata
gadon ban sani ba ta tashi ta rufeni da fadan wane irin shirme ne zanzo ina wa
mutane tsalle a gado kamar wata yarinya. Sena fada kanta ina cewa
“Tsallen murna ne Yah Fati ki barni nayi”.
“Murnar me kikeyi” ta tambayeni bayan data daga ni daga jikinta.
“Bazaki gane ba Yah Fati kawai kedai se lokaci yayi” tashi nayi na shige Toilet
nayo alwala, inajinta tana cewa Allah ya shirye ni nidai na tayar na ringa jero
sallolin godiya ga Allah daya sa Bashir yace yana sona.
Washe gari dakansa ya tasani a gaba mukaje nayi register Jamb, Law na ciki muka
gama komai muka koma gida.
A hankali soyayyar mu ta bayyan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina da Bashir.
Da yawa gani sukeyi kawai shirme nane haka shima a bangaren Bashir lokacin daya
gayawa Aliyu halin da muke ciki se yace masa
“Anya Bashir kana ganin abin nan me yuwuwane?”
“Me yasa kace haka Aliyu” Bashir din ya tambaye shi, se ya ci gaba da cewa
“Kawai gani nayi kamar akwai tazara me yawa tsakanin mu dasu, ka ture abotar mu da
Abubakar wannan ba wani abu bane amma ka fahimceni da wuya kaga mace ta fito daga
gidan Attajiri ta auri na qasa da ita sedai shi namiji me kudi ya auri diyar
talaka, sannan idan ka dubi irin mazajen da yaran gidan su suke auri babu qaramin
mutum a ciki ita kanta Ma’u a kalar da Allah yayi mata Bashir ko a gidan talauci ta
fito ba matar qaramin mutum me fafutukar neman abinda ze rufawa kansa asiri irin mu
bace ba”.
Shiru Bashir yayi dan tabbas Aliyun yayi gaskiya. Shidin ba dan kowa bane Babansa
me rufin asiri ne kawai Ma’aikacin gwamnati me da yake dab dayin ritaya kuma ba
wani babbaba kusan yanzu shi ake saka ran ya zama jigo a cikin gidan su tunda shine
Namiji Babba yayar sa daya da qanne biyar,
a yanzu ne ma ya gama makaranta yake bautar qasa kafin ya fara fafutukar neman
aikin yi kuma.
Amma tabbas yana son Asma’u kuma itama ya yarda tana sonsa ba kuma ya fatan ace ya
rasa ta.
“Haka ne Aliyu, ka taya ni da Addu’a Allah ya zaba mana abinda yafi Alkahiri toh”
“In sha Allahu, Allah ya sadamu da akhairan mu” Aliyun ya fada.
Wannan maganar da sukayi da Aliyu seta sa ya dan fara ja baya da Ma’u musamman
yanda a yanzu kullum yaje gidan ze tarar da zaratan samari yayan masu qunbar susa a
manyan motoci sunzo gurin Ma’un duk da bata fitowa amma hakan se yake ganin kamar
wata rana zata iya chanza ra’ayi ta zabi wani daya fishi dan haka se yayi baya da
zuwa gidan.
Da yake itama suna shirin fara SSCE se bata damu ba dukda indai sun hadu se tayi
masa qorafin me yasa yanzu baya zuwa gidan sosai se yace mata aiki ne ya masa yawa
dan yanzu ya samu temporary aiki a wani company yana zuwa.
Cikin dan lokaci su Ma’u suka gama Jarabawar su, kamar kuma yanda Alhaji ya saba a
shekarar ya kaisu gaba daya suka sauke Farali tafiyar da sukayi kusan rabi da
kwatan tsarabar da tayiwo ta Bashir ce harda yan gidansu. Randa suka dawo bata jira
yazo ba ta hada akwati guda ta kai masa har gida tayi sa’a ta same su gaba daya yan
gidan suna nan harda Alhajinsu dan haka bata zauna ba suna gaisawa ta tafi.
Bayan tafiyarta Su Fainusa suka bude akwatin suna zaro kayan ciki, sosai mamaki ya
kama su ganin uban tsarabar se Dada ta kasa haquri tana kallonsa tace “Bashir ni
meke tsakanin ka da yarinyar nan haka irin wannan uwar tsaraba data kawo mana?”
Fainusa ce tayi caraf tace “Dada soyayya sukeyi, ina jin a Islamiyya ma Ma’un
Bashir ake ce mata”. Se Bashir ya harareta yace “ke waya tambaye ki? Tashi a nan
kona mammake ki”.
“Ikon Allah, Anya bata fi qarfinka ba Bashir kaida zaka dauko daidai”
“Daman mace tana fin qarfin namiji ne Nafi?” Alhaji Amadu ya katseta, seta girgiza
kai tace
“Gani nayi Alhaji idan ka kallemu ka duba gidan data fito kar ace son zuciya ne
yasa ya nemi auranta”.
“To ai Annabi ma yace ana auran mace dan Asali da kuma dukiyarta kinga in hakan
yayi ma ba laifi bane ballantana nasan ma ba hakan bane, idan matarsa cea se kiga
Allah ya qulla abun, kiyi masa fatan Alkahiri kawai” cewar Alhaji Amadu.
“Hakane Allah ya tabbatar da Alkahiri toh ai Asma’u yarinyar kirki ce”. Daga haka
suka ci gana da hirarrakin su.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 33
ASMA’U
Mun rubuta jarabawar Jamb cikin Nasara kuma ko wannen mu ya samu isashshen makin da
ze samar masa gurbin karatu a fannin daya zaba