Showing 96001 words to 99000 words out of 238465 words

Chapter 33 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

nace

"Baza muje mu gaida su Baffa bane naga mun wuce gidan?"

Be tareda ya waiwayo ya kalleni ba yace "Ai ni munje dasu Aliyu ranar nan mun
gaishe su, ke kuma ba yanzu ba. Se kinyi wata sannan zamuje" ya maida kai suka ci
gaba da maganar su da Aliyu. Tsabar takaici bansan sanda kuka yazo mun ba. Muzo har
unguwar ina kallon kofar gidan na mu yace wani bazan shiga ba se nayi wata amma ai
shi munje nasu gidan idan Adalci ne me yasa be bari duk maje lokaci daya ba.

Sakin kuka na nayi ya fito fili, Yah Aliyu ya shiga bani haquri yana cewa Bashir
"muje mana ko a tsaitsayene ta gansu" amma mutumin nan mirsisi yaqi magana har muka
isa gida Aliyu ya ajiye mu na shige na barsu a waje yana wa Bashir din mitar be
kyauta ba.

Ranar haka na share shi, bayan mun kwanta ina jinsa yana wani shafani nai masa
banza qarshe yaja tsaki ya juya ya kwanta nima na gyara kwanciyata a raina nace
"kaima kaji yanda naji idan da dadi ai".

Haka na tashi washe gari babu walwala, nayi duk abinda na saba na koma daki na
kwanta, ina kallonsa se zarya yakeyi yana kallona amma dan baqin hali ya gagara
bude baki yayi mun magana haka muka wani har dare dadai yaga abin nawa bana qare
bane se jinsa nayi a cunkushe yana cewa

"Dan bamu shiga gida jiya bane wai kike ta wannan Fushin to shikenan wani satin se
kije" nayi masa banza kuwa tunda shi baze iya bani haquri ya rarrashe ni ba ai
shikenan. Dakyar ya samu na sakko shima seda ya yarda randa na cika sati biyu ze
kai ni nan da kwana uku kenan sannan na haqura, washe garin ranar da yamma yace na
shirya zamu je gidan Addah ashe ma unguwar mu daya suna ta bayan layin mu ne.

Sam Addah ta kasa zaune ta kasa tsaye sanda mukaje, haka ta ringa kawo mun Abubuwa
se sannu da zuwa take mun kamar wadda tazo daga China ina kallon Bashir se hada
fuska yake da gani abin be masa ba yaran Abokanan zamanta da yaransu suka ringa
shigowa muna gaisawa da yake akwai yammata da yawa Sa'annina a cikinsu dama wadanda
suka girme ni nan da nan muka saba.

A nan Bashir ya tafi ya barni yace ze dawo da magriba, Amirah na naniqe dani
qaramar Ummi ce me dan qyuya bata sakewa da mutane Addah kuwa ta ringa bani
labarai kala kala anan nake jin ashe su kadai ita da Dada iyayensu suka haifa
anyiwa Addah aure ba dadewa suka rasu dan haka Nafi(Dada ta koma gurinta har tayi
mata aure).

Na zata tana da wasu yayan bayan su Amirah a cikin hirar da muke naji su kadai ne
yayanta tace dai ta haihu duk basu tsaya ba dan Babban Danta ma ya girmi Amina
yayar Bashir.

Da zamu tafi haka ta hada mun kayan yaji su citta da kanumfari da daddawa dasu kuka
harda Barkono se kuma tace bari abarshi a daka se a kawo mun daga baya, Amirah
harda kukanta da zan tafi wai seta bimu seda Bashir yayi mata jan ido sannan ta
koma muka rabu da alqawarin zasu zo daman sun barmu mu dan huta ne tukunna.
Kwana biyu naje gidan mu, wannan tun safe na tafi ai kuwa nasha Fada gurin Goggo
kamar tayi me wai tunda nake wa na taba gani tazo gida sati biyu da aure sena
tattara na tafi bazan zauna ba aikuwa na ringa kuka dakyar Baffa ya bata baki ta
haqura na kuwa bar mata dakin ta na koma gurin Hajia Babba har dare seda zan tafi
naje mukayi sallama tana sake buga mun warning din karta sake ganin qafata idan ba
wani abu ake a gidan ba, a hanya Bashir yayi ta tsokana ta wai gashinan, da yace
bazan zo ba ai harda daukar fushi dashi yanzu gashi naje din an koroni.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa. Su Addah da kishiyoyinta uku masu kirki suma
duk sunzo haka yaran gidan suna zuwar mun musamman da yanzu Bashir ya koma aiki in
ya fita se gidan duk kadaici ya isheni in suka zo musha hirar mu kafin ya dawo sun
tafi.

Tunda Amirah taga hanya kullum seta zo, abinda na lura shekara shida amma ba'a
sakata a makaranta ba kuma duk sauran sa'anninta na gidansu suna zuwa. Dana tambayi
Addah dalili tana dariya take cemun

"An kaita fa in gaya miki se tayi ta kuka wai bata son makaranta, ni kuma nace ina
dalili tunda bata so yanzu a barta, in ta qara wayo dakanta ma zata ce a sakata".

Mamaki ya kashe ni, wai shekara shida se wani lokaci zatayi wayo ta zauna a
makaranta? Abinda na lura dashi daman sam Addah ta sangarta yarinyar nan yanda
kasan goyon gwarawa babu kwaba gata da shegiyar rashin kunya ga barna duk abinda ta
gani seta lalata abinda yake hadani da ita kenan ma na fara gajiya da zuwan naya
dan kullum tazo seta bata mun wani abun.

Akwai randa tazo inada wata yar Aku ta roba me magana, ina son Akun nan tun banfi
shekara goma Hajjin su Anty Suhaima ta siyomun ita. A lokacin tace a kantin ita
kadai ce tayi saura har Goggo tace baza'a siya ba dan rigima kawai zata zo ta hada
a gida idan sauran suka gani amma Baffa yace se an siyowa Mamansa suka kuma yita
nema ba'a samu wasu ba.

Tun sannan nake ta boyonta ko wasa bana fitowa da ita ayi kai in kana so kayi wasa
da ita sedai mu shiga daki kuma ka biya ni kudi shekararta Tara yanzu na qudure har
Yayana se sunyi wasa da ita.

Da yake babu wuta lokacin ni kuma ina Kitchen ina girki sena dakko mata na saka
mata batir wai ta samu abin wasa.

Ina Kitchen ina jinta tana magana Akun na maimaitawa, se ji nayi tana qundumawa
Akun zagi ita kuwa Aku ta maimaita.

"Yada wasan zagi Amirah ki dena babu kyau" na fada daga cikin Kitchen, se tace
"Anty ita ce komai na fada se ita ma ta fadi irinsa" tana gamawa Akuma Ta maimaita.

"Bazaki dena kwaikwayata ba ko" Amiran ta fada caraf Aku ta sake fada itama, se
abin ma ya bani dariya, ina shirin in leqo na gaya mata rikodin Akun takeyi duk
abinda mutum ya fada itama seta maimaita se ji nayi Amiran nacewa

"Shegiya mahaukaciya wallahi kika sake kwaikwayona sena cire miki kai" ba kuwa ta
rufe baki ba Aku ta dauka sena leqo ina cewa

"Ke Amirah bana hana ki zagi ba in banda shirmenki batiri ne da ita tana
rikodin...." maganata ta maqale daidai sanda tayi wurgi da Akun nan da qarfin gaske
ta daki bango take ta tarwatse komai ya kama gabansa.

Tsabar takaici kasa ko motsi nayi, yanzu Akun da har nagama tawa yarinyar ko
kwarzane be sameta ba shine yanzu zata rada mun ita da qasa? A fusace na qarasa
inda take na miqar da ita tsaye ina zare mata ido nace
"Amirah bakida hankali me yasa zaki fasa?"
Se kuwa ta wani murguda baki cike da fitsara tace "Na fasa din, ai seda na gaya
mata ta dena kwaikwayona harda fa zagina take yi yanzu dana fasa se naga yanda
zatayi".

Saboda haushi ban san sanda na kai mata ranqwashi ba, kamar zanyi haqaye nace "kin
san shekarun Akun nan kuwa ta ma girmeki amma saboda shegen rashin jinki shine zaki
fasa mun ai kuwa sena zane ki yau a gidan gobe ma ki sake yimun barna".
Fincikewa tayi ta nufi gurin Akun, injinta da shima ya cire ta hau tattakewa tana
cewa "kika ranqwashe ni toh na fasa na fasa din ayi koma menene".

Lallai rashin kunyar yarinyar nan ta isa dole na koya mata tarbiyya tunda bata da
ita ai kuwa na jata Kitchen na zari tsintiya na shiga tsula mata a jiki daman rigar
ta me kamar Bea ce bata da hannu ai kuwa dukan ya shigeta tana tsalle tana ihu ina
tsula mata ina cewa

"Gobe ki sake yiwa wani rashin kunya tunda ke fitsararriya ce". Seda na mata lilis
kafin na saketa, ta kwasa da gudu tana kuka ko ta kan Takalminta da Hijab bata bi
ba ta bar gidan ni kuwa ko a jikina na tattare fasashshiyar Akuna idona ya ciko da
kwallar takaici ganin babu ta yanda za'ayi ta hadu, a kan Centre table na ajiye jin
abincina na kamawa a Kitchen.

Ina kwashe abincin Bashir ya dawo, yasan yanda nake son Akun nan da mamaki ya kalli
pisis din da suke ajiye ya kwalo mun kira na fito ina masa sannu da zuwa.

"Meya samu Akun taki? waya fasa ta haka?" ya tambayeni yana kallona, se ji nayi
hawaye ya silalomin na bude baki da niyyar magana hargagin Addah ya katse ni.

A sukwane ta fado dakin tareda Amirah a bayanta da har sannan bata dena kuka ba
tayi tumu tumu da ita qasa har cikin gashinta da naci wuya jiya na gyara mata shi
tsaf da niyyar yau zamuyi kitso da gani birgima tayi a qasa.
Ke Asma'u me Amirah tayi miki zaki kama ta kiyi mata wannan dukan kamar kin samu
jaka" Ta fada tana hura hanci.

"Ni ba abinda nayi mata Addah kawai dan na fasa waccen shegiyar Akun shine ta kama
ta dokeni da zabori" Amirah ta fada cikin kuka kafin Addah tayi wani abu se ji
mukayi
"Fuu" Bashir daya fi kusa da Amiran ya dauketa da mari ta kuwa kwala ihu dan marin
ya shigeta da gaske.

"Zaki wuce daga nan ko sena tattakaki fitsararriyar banza da wofi, wato ke kika
fasa har kina sake fada kuma an hukuntaki shine zakije ki kai qara toh zuwa kukayi
a rama miki ko me" ya hayayyaqo mata kamar ze sake rufe ta da duka tayi bayan Addah
tana hadiyar zuciya dan tuni kukan nata ya tsaya.

"Idan ita ba'a rama bata ba ai kai seka zo ka dakeni dan ubanka se insan ka isa ka
tarewa matar ka fada" Addah ta fada kafin ta juyo kaina tace

"Ke kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake dukar mun Yarinyar idan ma ba cin
zali ba akan ta fasa abin wasa kawai ki hau dukan ta to wallahi karki sake" ta juya
fuu suka fice ni kuwa na rakata da ido.

"Maganin ki kenan ai da kike jawo yarinyar kece baki san halin ta ba amma Yanzu
gashi ta fara nuna miki, mtsw" ya ja tsaki ya shige dakinsa ya barni a tsaye.

Daga wannan abu naja baya gaba daya da Addah dan ba'a fi kwana uku ba se gata da
Amiran ta kawo su harda Ummi wai zataje unguwa akayi sa'a Bashir yana nan yace mata
muma fita zamuyi ta ringa mita kuwa nidai suna fita na sakawa qofa muqulli to ina
dalili yaro yayi maka ba daidai ba in ka hukuntashi a zo har gida a gabansa a ci
maka mutunchi to ni banga ana haka a gidan mu ba.

Bata haqura ba dan ba'a rufa sati ba ta kuma zuwa wai tazo duba mu kamar ma ba'ayi
komai ba, ranar nayi Farfesun kaji akan da daddare se na soya mana doya muci dashi.
Bayan na kawo mata ruwa da lemo na koma Kitchen din, har ga Allah banyi niyyar zuba
mata ba dan kadan nayi. Ina da dambun nama harda kilishi su nayi niyyar na kawo
musu se ji nayi tana cewa

"Asma'u zubo mana farfesun mana idan da biredi ki hado mun".

Se nayi tsam a Kitchen, a raina nace "ikon Allah" na dai samu dan bowl na saka mata
cinya daya da rabin qirji dan fa be kai gudar kaza bama wanda nayi nasan Bashir
kadai se ya tashi dashi ma.

Ina ajiye mata ta kalli kwanon, se cewa tayi "meye wannan kika zubo haka, a gidan
dan nawa a kawo mun wani abu kamar na roqa, matsa nan ki gani" ta miqe se gani nayi
ta shige Kitchen abinta, ina tsaye ta dawo da kular naman dukka da biredin dana
manta ban dakko mata ba ta zauna ta hau ci ta nayi mun hira.

Abinda yafi qarfin ka aka ce seka mayar dashi wasa, haka na zauna ina kallon ikon
Allah ta cinye tas har tana cewa wai tayar mata da kwadayi kawai yayi. Da zata tafi
babu kunya tace idan muna da danyan nama na bata, na shiga Kitchen zan debo mata se
gata ta biyo bayana, ta debi kwai, taga kayan miya suma ta diba nidai na saka mata
kaza daya a leda daga yanda ta karba nagane kamar ta raina ne nayi saurin tare ta
da cewa

"Daga gidan gonar Baffan mu aka kawo mun, kinsan idan ya fitar da kaji yana rarraba
mana da kwai" se tayi wata yar dariya tace

"Au uhm kunji dadin ku kuwa" mukayi sallama ta tafi. Ina sane na mata haka dan
karma tayi zaton dan nata da take iqirari ne yake siyowa bare har tayi iko dasu,
daga gidan mu aka akawomun dan har yau kayan miya kadai Bashir yake siyowa sedai
idan munyi sha'awar jan nama ya siyo danye ko gasashshe saboda tunda muna da komai
na cefane kamar ma bama taba kayan garar nan, sannan kaji basa yanke mun da kwai.

Idan na aika a siyomun a gidan gona Baba Idi Manager kyauta yake bani ko a bani
ninkin na kudin dana bayar.

Da naci da komai Amirah ta dawo zuwa tun Bashir yana fada shima har ya haqura
sauqin ta daya mun koma makaranta dan haka bana zama Asabar da lahadi ne kawai take
zuwa shima daga baya na takurawa Bashir akan yaje ya samu babanta yayi masa magana
akaita makaranta haka akayi kuwa aka sakata har Islamiyya ma shikenan muka samu
sauqin abun.

Watan mu shida da aure ranar da safe ina zaune Yah Bilki ta kirani take cemun wai
Goggo ta haihu, a kwance nake amma seda na miqe zaune nace "kinsan me kike fada
kuwa haihuwa fa kika ce wace irin haihuwa ana zaune lafiya yaushe ma ta samu ciki?"

"Wallahi dagaske, ni kaina bakiji yanda nayi mamaki ba amma kuka fa nayi zargin
haka dan zuwan da nayi na qarshe nidai naga cikin amma se nayi zaton ido nane
wallahi yanzu Su Bilal suka zo suke gaya mun munyi Auta"

"Ikon Allah amma yanzu dan Allah wace irin haihuwa ce haka yaya nayi suma suyi
gaskiya daga wannan an gama" na fada se Yah Bilki tasa dariya tace

"Se ki gayawa Baffan ki ai bani ba, nidai gobe zanje naga Baby kefa?"

"Nima in na taso makaranta inaga in biya goben yanzu dai ai bazata kori mutane ba
ko daman abinda bata so a gani kenan yasa take kora ta in naje" na fada ina dariya,
se tayi dariya itama tace

"Yo ai sanin hali, yanzu da kin sani har na America tuni da labari ya tarar dasu,
shikenan se mun hadu goben" mukayi sallama.

Bashir na dawowa na gaya masa ina ta mita dan me Goggo zata haihu shida cikanki be
qara ce mun ba tunda yace Allah ya raya.

Washe gari kuwa daga makaranta gida na wuce, abin Allah ina ganin yarinyar naji ta
shiga raina, haka na tasa Goggo a gaba kamar wata kakata da zolaya data gaji ma
daki ta shige ta barmu Baffa kuwa se nan nan yake da Yar Babyn me kyau da akayiwa
Huduba da Aminatu muka yi mata laqabi da Amna.

Ranar a gidan muka wuni da yawa munje ga matan yayyen mu maza da muka tashi tafiya
kowa ta kama hanyarta a motarta muka fito tareda Yaya Fati ina cewa "Bari na biki
ki sauke ni a gida toh tunda kece yar hanyar mu" daidai mun qaraso inda Yayan mu na
biyu a gidan Alhaji Yasir yake tsaye yana waya.
Muka gaishe shi har mun gota ya tsayar dani sena dawo.

Seda ya gama wayar ya kalleni yace "ke dawa zaki tafi"

"Yah Fati ce zata sauke ni a gida" na fada ina dan wasa da hannuna dan yafi Alhaji
Qarami zafi daukar sa muke kamar shine babban Yayan,

"Ta tafi, kije Bello ya kaiki gida, ga wannan" ya fada yana miqo mun kudi da ban
san ko nawa bane, sena karba nayi masa godiya na juya inda Yah Fati take jirana
nace mata

"Ki tafi Kawai, Baban Sharifa yace naje Bello direbansa ya kaini, kinga har kudi
nasa mu ma se jibin zaku zo dai ko?"

"wallahi kina sharafin ki yarinyar nan komai aka tashi ace ke wani tausayin ki ake
ji a gidan nan bayan babu abinda kika rasa ta wani fannin ma kin fimu jin dadi dan
dai ana ganin mu a qaton gida ne kawai, shikenan bari naje dare yana qarayi" muka
yi sallama muka rabu.

Kwana biyu dayin haka da daddare muna zaune aka buga get, Bashir ne ya fita ya bude
se gashi ya dawo wai gurina aka zo sena zura hijabi nabi bayansa.

Ina zuwa na ga Bello ne direban Alhaji Yasir daya dawo dani ranar nan da wata
dalleliyar mota Toyota qirar shekarar baqa dukda dareni amma kana ganin yanda take
qyalli.

Gaisawa mukayi nace da Bashir "Bello ne direban Alhaji Yasir fa" se yace "oh ai ban
san shi ba.

Key da takaddu Bellon ya miqo mun yana cewa "Gashi Alhaji yace a kawo miki, tun
jiya ma naso kawowa wallahi takaddun ne basu kammala ba se dazu, mota fa tayi kyau
Hajia Allah ya sanya Alkahiri ya tsare ki da sharrin qarfe".

Tsabar murna bansan sanda na dane Bashir ina dariya ba nace "wayyo dadi munyi mota
muma munyi mota"

shima dariyar yake ya riqeni ganin muna neman faduwa Bello ya juya ze tafi irin
yaji kunyar nan na tsayar dashi na shiga gida da gudu cikin kudin da Alhaji Yasir
din ya bani ranar nan na qirgo dubu biyar na bashi ya ringa kuwa zuba mun godiya ya
tafi.
A daren na kira Alhaji Yasir nayi masa godiya "Ba komai, ki tabbatar idan kina
buqatar wani abu ki ringa gaya mana" ya fada kawai ya kashe wayar.

Na kira Baffa na gaya masa shima yace "Inye yar gatan Yayanta kice se munzo dani"
nayi dariya. Haka na ringa kiran yan gidan mu ina fada musu abin arziqi kowa ya
taya ni murna, badan dare yayi ba ma ba abinda ze hana ni ta fiya gida yanzu na
nuna musu, haka nayi bacci da ido daya, bini bini na daga labule na leqa motar nan
Bashir se dariya yake mun.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 35

ASMA’U
Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka
akayi rabon gado yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa ma’aikata
barin aikinsu.

Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu
wani aiki daya samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin
yazo mana da sauqi saboda Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan
abinda ba’a rasa ba muke siya irin su kayan miya ko ganye da dai sauran masarrafi
dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da suke hannuna na siyo
mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun.

Duk sati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login