Showing 27001 words to 30000 words out of 238465 words
ta shiga toilet yin fitsari shi kuma Jafar ya zauna,
ba abinda yake son ya tambaye shi ta sani qulafucin uba ne da Jafar dan gani takeyi
yafi son Bashir akanta. Indai yana gida tofa yana nane dashi in ko tafiya yayi ya
ringa kiransa a wayarta kenan shi kuma haka yake.
A dakin ta barshi ta tafi nata tayi wanka, seda ta shirya sosai tabi dakunan yaran
ta tabbatar sun kwanta har Jafar din ya dawo sannan ta kashe Fitilun palour ta
tafi dakinsa.
Yana zaune da waya a hannunsa yana juyawa Asma’u ta shigo, tunani yake ya kira
Amirah ko yaya tunda ita Allah besa tayi hankalin jin ya ya sauka ba yauma. Yanayin
walwalar da ya gani a fuskar Asma’u yasa ya fasa sema ya kashe wayar gaba daya ya
ajiye kafin ya miqe ya fita.
Seda ya leqa ko ina ya tabbatar da komai lafiya ya tofe ko wacce kusurwa da falaqi
da nasi kafin ya koma Dakin har Ma’u ta kwanta taja bargo zuwa rabin jikinta.
Kwanciya yayi shima yana jawota jikinsa, hannunsa ya tura cikin gashin kanta ya
zame band din data daure shi dashi, Bashir nason Gashi sosai yana daga cikin
abubuwan da suka sake jan sa akan Amirah yanda take kwalliya da gashi.
“Madam ya akayi ne da alama ko missing dina bakiyi ba tunda na tafi bako waya”.
Gajeran murmushi tayi tace
“Qalau fa kawai dai mun barka ne ka huta sosai ka kula da Amarya, ya ka baro su
suna lafiya ko?”
“Lafiyar su qalau suna gaishe kuma”
“Muna amsawa” daganan taja bakinta tayi shiru, shima shirun yayi tana jin sa yana
jagwalgwala gashinta kafin bacci ya dauketa. Da Asuba ta rigashi farkawa, harta
dauro Alwala be tashi ba dan haka ta shafa fuskarsa da sauran lemar ruwan hannunta
jin ana qoqarin tada sallah. Kafin kuwa yayi Alwala an shiga, dole se a palour suka
hadu da yaran dukka ya jasu sallar.
Bayan sun idar ma bacci ya sake komawa tayi mamaki dan da wuya Bashir ya koma bacci
da Asuba kai ko ba zashi aiki ba ze zauna yayi ta lazumi har se rana ta daga yayi
walaha sannan yake komawa bacci. Tana wanka tana gulmarsa a ranta wato yaje ya gama
kashe Arnansa ze zo yana baccin gajiya a nan ko.
Tsaf suka shirya, tana jira taji shi ze tafi dasu ko kuwa ita zata ci gaba da
jigilar har suka fita yaran suka shige motarsa taga ya kunna beyi magana ba ,
Hamdala tayi a zuciyarta kafin ta kunna tata motar suka hau hanya seda suka je
junction din da suka saba rabuwa tayi musu horn ta shige kwanar office dinsu.
Bayan tayi parking tana qoqarin Daukar jakarta da system Ilhama Abokiyar aikin ta
ta qaraso gurin motar,
“Aa Maman Farida yau da wuri haka” Ilhama ta fada bayan sunyi musabaha.
“Wallahi fa Maman Khairi Allah ya ceto ni daga yawo kai yara makaranta” tare suka
jera suna yar hira har suka isa 3rd floor inda anan office din Asma’u yake ita kuma
Ilhama tana 4th floor ne.
Tana isa office dinta ta tarar da takaddun da zatayi aiki a kansu kamar koda
yaushe. Seda ta kintsa komai sannan ta fara duba su daya bayan daya kafin wani
lokaci ta gama har ta shiga replaying mails da suke jiranta.
Asma’u nada hazaqa sosai ta kuma qoqarin aiki gata Allah ya bata fasahar harshe,
duk baqin abu Idan Asma’u ta tsara ka tace Fari ne bazaka san sanda zaka yarda ba
dalilin da ya saka ta karantar Business Administration kenan dukda a farko taso ta
karanci Law ne yanzu haka tana aiki ne da wanni babban company hadahaar ma’adanun
qasa (Mineral resources) tana matsayin Sales Manager (manajan siye da siyarwa).
Yanda take qoqari gurin janyo musu customers yasa take samun cigaba da Alkahiri
sosai a kan aikin nata ga damammaki da suke shigo mata saboda yanayin aikin yana
bata damar hulda da manyan mutane sosai masu siya ko wadan da suke kawo hajar su
company ta siya.
Tana tsaka da aiki Kiran Fainusa ya shigo mata
“Tauraruwa me wutsiya” ta fada a fili dan ita dai duk kiran wayar Fainusa ba
Alkahiri bane a gurinta, seda ya katse ta sake kira sannan ta dan dakata ta daga.
Cikin sabuwar girmamawar da Fainusan takeyi mata tunda ta fara zaman gida suka
gaisa Fainusan ta ke tambayarta yara tace suna makaranta itama ta tambaye ta ya
Dada tace tana lafiya.
Shiru ne ya biyo baya tana jiran taji dame tazo yau kuma can kuwa ta nisa kafin
tace
“Anty jiya har dare mutuniyarki suna nan gidan da yaya”
“Uhm” kawai ta amsa mata, ita tarasa wannan abu kamar wadda take biya ta kawo mata
rahoto kuma duk sanda ta tashi kawowar ba masu dadi bane.
Fainusa kuwa bata damu ba taci gaba da cewa “wai fa in gaya miki ta samu Dada wai
tayiwa Yaya Magana ya tafi da ita Lagos, to wai ke take so ki dawo nan ko kuma
hadaku dukka ze yi anan?”
Shiru Asma’u tayi tana so tayi tana sauraronta, jin tayi shiru alamar ta gama kenan
yasa tace mata
“Toh Nagode ina office ne ki gaida su Dada” taa kashe wayar.
Duk yanda taso ta ci gaba da aikin seta kasa, ita sam ta manta da maganar da yai
mata ta komawa Gombe se yanzu wato Amiran ce take Son dawowa nan kenan shine ita
za’a tarkatata ta koma gida tunda tasan bazasu barshi ya debo su su dukka biyun ba
dole ya bar daya acan Gombe. Lallai ma tayi yaya da aikinta toh? Bama wannan ba
makarantar yaranta fa ko kuma yanzu Amiran ta shirya zama tayi mata rainon Yayan
kamar yanda suka ce a lokacin da ya nemi su ringa karba karba
A sannan Amiran ai cewa tayi kowa ta zauna a matsayin ta, dan baza tayi mata bautar
Yaya ba, daga baya ma tace ita gara ta zauna cikin yan uwanta kuma ya yarda da
hakan shine yanzu data juyo mata zata ce tana so ta dawo nan still kuma ya sake
yarda wato ita ga sauna tana zaune se dai su juyata yanda suka so ko? To maji ma
gani.
Aikin ta taci gaba dayi a ranta tana shirya irin dibar Albarkar da zata masa duk
ranar da ya sake tado da zancen ma wallahi se ta masa tatas, qaton sa dashi yazo
yai tayi mata muzuran qarya se yaje yarinya qarama ta ringa controlling dinsa
kawai.
Data tashi kaitsaye ta biya ta dakko yara, sun dan bata lokaci a hanya dan ta
tsaaya yin cefanen abubuwan da suka qare musu sam ta manta cikin weekend bata damu
tayi ba dan haka kusan tare suka isa gidan dashi.
Jakarta kadai ta ajiye ta shiga kitchen sauqinta daya tana da miya a Frizzer dan
haka ta cirota ta dumama bayan ta dora white rice ta zuba kwan da zata hada salad
dashi su dafu tare. Bata bar kitchen din ba seda ta kammala komai ta jere a Dining
yana zaune a palour da yara suna kallo bayan sun dawo daga masallaci.
Sannu suka yi mata yaran banda Oga daya bita da ido kawai Amna da Aliyu suka shiga
kitchen din dan su jera kayan da suka siyo aikin su ne wannan. Seda tayi wanka da
ruwa me zafin gaske tayi sallah sannan taji dan dama dama. Kai gaskiya mata na
qoqari, kayi hidimar gida da yara kayi ta miji sannan in kana aiki ko Kasuwanci duk
ka hada wallahi bataga laifin Cina zaune ba indai za’a basu komai na buqata dan
aiki wahala ne amma dai ko yaya dai gara ka nemi na kanka kodan bacin rana.
Kishingida tayi a gurin da tayi sallah kafin kace me baccin gajiya ya kwasheta se
farkawa tayi taga Bashir a tsaye a kanta da alama tashinta yayi. Agogo ta kalla
goma harta wuce, cikin dan baccin da be gama sakin ta ba tace
“waifa na idar da sallah ina zaune ashe bacci nayi, wallahi yau din nan na gaji da
yawa kullum work load dina qaruwa yakeyi maimakon ya ragu”.
“Sannu, ki tashi kiyi sallar isha kici abinci ina jiranki” yasa kai ya fice daga
dakin
“Aifa Allah ya kawo mu” ta fada tana miqewa ta shiga toilet. Seda tayi sallar
sannan ta fita neman abinda zata ci, kadan ta dibi abinci ta dora da fruit salad
kafin ta tattare sauran ta gyara komai.
Dakinta ta kima tayi brush ta chanza kayan ta sannan taja qofar ta tafi gurin
Bashir. Yana kwance a kan gado ya zubawa pop dakin ido ta shigo, be motsa ba harta
ajiye kayan da ta dakko su zata saka da safe tana zama akan gadon wayar sa dake kan
mirror ta hau ringing.
Bata motsa ba dan tasan me kiran shima kuma bece ta dakko masa ba dan haushin
Amiran yake ji wato se yanzu ta raya mata ta kirashi kenan, jin kiran na yankewa
wani na shigowa ya sakashi sakin tsaki ya tashi zaune tare da dakko wayar a fusa ce
ya daga da niyyar balbaleta da fada amma kukan ta da kururuwar ta shiga uku da
takeyi ya dakatar dashi.
“Ki nutsu malama kimun magana meya faru” ya fada cike da gundura da kukan nata,
Amira kuwa dakyar taja fasali ta tsagaita kukaj kafin ta shiga kora masa bayani
tana cewa
“Daman Addah ce tun da safe ta tafi gidan Umma Balaraba toh bata dawo ba se dazu
bayan La’asar aka kira mu wai tana FMC wasu sun tsinceta a hanya a sume shine suka
kaita can” Sabon kuka ta rushe dashi bayan data gama kora masa jawabin kafin qit ta
kashe wayar kuma.
Dafe kai yayi yana maimaita Innalillahi, a garin yaya toh meya sameta kuma?
Asma’u data ga yanayin da ya shiga ce cikin damuwa ta shiga tambayarsa meya faru ya
gaya mata ita hankalinta ya tashi sosai. Tasan baze wuce a garin shegen yawon
qauyukan da take zuwa gurin malamai bane Allah dai yasa ba wani mugun abun ta hadu
dashi ba.
Haka suka hadu sukayita jimami bayan Bashir ya kira Naziru shima dai yace masa
besan meya faru ba yana zaune Dada tace suje ya kaita Asibitin, kuma dai har yanzu
suna zaune Addah bata farfado ba dukda Dr yace babu wata matsala sun dan mata
allurar bacci ne ta huta kamar wani abu ne ya firgitata ta shiga tashin hankali.
Sudai sunfi tunanin ko yan kwace ta hadu dasu suka zare mata wuqa tunda ba’a sameta
da komai nata ba wayarta ma da aka kira aka fadi tana Asibitin ba’a san waye ya
kira ba an kuma bi kiran wayar a kashe.
Haka dai suka kwanta kowa rai babu dadi.
Da safe ma tunda suka tashi yake bige bigen wayar jin yayi jikin nata, ance ta
farka tun cikin dare se ihu take tana Allah ya isan kudinta abunda ya qara tabbatar
musu da zargin kwace aka mata kenan todai seda aka sakeyi mata Allurar bacci kafin
aka samu sa’ida.
Be kira Amira ba seda ya isa office ya dan babbata baki kafin ya sukayi sallama
yace ze turawa Naziru kudi koda zasu buqaci wani abun.
Asma’u ma ta kira Dada tayi mata yame jiki ta kuma kira Ummi, shawarar ta kira
Amirah ta shigayi da zuciyar ta ko karta kira dan ita ta manta rabon ma da suyi
waya tana ga tun lokacin da Amiran kwanta a Asibiti bayan haihuwarta ta farko
lokacin tana Adamawa taje gurin Goggonsu se a waya tayi mata sannu dan tacan ta
wuto Lagos. Dama ta dade da blocking dinta a whatsapp saboda irin abubuwan rashin
mutunchin da take dorawa a status dan Asma’u ta gani, yanke shawarar kiran tayi ko
ba komai Ai rashin lafiya na gaba da komai.
Seda wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga murya a dashe tace “Hello” tayi shiru,
Ma’u tayi qarfin halin cewa
“Amirah ina kwana yame jiki kuma?” Jin bata da niyyar magana.
Seda na mula sannan kamar wadda akayiwa dole tace “Lafiya da sauqi kuma zata
warware insha Allahu se an kammala abinda aka fara idan ma turen wani mugun abun
akai mata sedai ya komawa mutum kansa ehe” ta ja tsaki tareda murguda baki kamar
tana gaban Asma’un kafin ta kashe waya.
Mamaki ne ya nemi kashe Asma’u a zaune, ita sam bata ma gane kan zancen da takeyi
ba illah zallar rashin kunya da taji a muryar Amiran ga kuma kashe mata waya da
tayi, daga abin arziqi shine zata mata wannan diban Albarkar?
Koda yake ita ta kai kanta ai da bata kirata ba ai bazata mata ba gobe ma ta sake.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 13
Addah, abinda ya faru waccen ranar.
Kuka riris Addah ta shigayi bayan data tabbatar da cewa Malamin nan dan damfarane,
qarin tabbacin data samu tana tsaye wata da ta yankawa kanta kazar wahala ita ma ta
zo neman malam Wizy anan suka samu daya daga cikin Almajiran ya fede musu abinda
yake faruwa.
Wato dama shi ance aikinsa kenan kuma takamaimai basu san dan wacce unguwa bane.
Haka yakeyi duk sanda suka tashi zasu je inda ba’a sansu ba su kama guri idan sun
gama cin kasuwarsu ta watse ba zaka san ina sukayi ba.
Haka suka dauki hanya da me Adaidaita tana faman rusa masa kuka batayi aune ba taga
yayi kwana da ita wata hanya daban, da taso tayi masa ihu ya zare mata wuqar dake
boye a qugunsa dole Addah tayi shiru se yan idanu tana hawaye haka tana ji tana
gani seda sukaje inda babu mutane ya kwace jakarta data zubo kudin raguna biyu ga
kuma wadanda Hajia Balaraba ta bata na nata aikin duk ya kwamushe harda wayar ta
sannan ya buga mata abu akai ta suma kafin ya kwasota ya kawota Asibiti ya tsere
abinsa.
Seda ta kwana 4 a Asibitin sannan aka samu kanta ta dena iface ifacen kudinta da
takeyi shima se bayan da Alhaji Murtala yayi mata horror sannan ta dauki dangana a
fili a zuciya kuwa baqin ciki kamar zeyi ajalinta. Abu goma da ashirin gashi babu
damar ta raba baqin cikin da wani ayi mata Allah shi qara dan ko Amirah bata jin
zata gayawa bare tsautsayi yasa wani yaji zancen.
Amma fa wallahi an cuceta, Dubunta fa har dari da sittin dan iskan yaron nan ya
lashe ga Hamsin din Balaraba. Wai ma wace toshewar basira ce ta same su kai wannan
ibtila’i da yawa yake, amma bazata haqura ba wallahi insha Allahu seta nemo wanda
ze mata aikin da Wizy ze kawo kansa da kansa ya biyata kudin ta (baki daddara ba
ashe 😂😂).
Haka dai tace a sallame ta ta warke suka koma gida taci gaba da jinyar zuciyarta.
Dama damanta ma yanda Bashir yake ta rawar jiki akan ciwon nata, kamar yanda yace
ya turowa da Naziru dubu dari yace ayi hidimar Asibiti dan ko babu auran Amirah ai
Addah uwa take a gurinsa ze kula da ita kamar yanda zeyiwa Dadansa dan ma dai Addar
se a hankali dai, already kuma Alhajin ya biya komai dan haka Nazirun ya danqawa
Amirah kudin yace ko zasu buqaci wani abu inji Bashir. Wadan nan kudi ta qudure a
ranta da taji dama dama zata kaisu a shaqo mata wuyan wizy kuma (Ai me rabon shan
duka baya jin bari dama 😂).
Ganin yanda Bashir din yake ta tasu dan kullum sau biyun nan Safe da Dare se ya
kira yaji ya jikinta yasa taga dama ta samu na yadda zata tura Amirah gurinsa, (wai
nikam dole ne 😂😂 Allah sa dai ba rabon wahala ke kiran Amirah ba itama). Tunda sun
gwada wacceb hanyar bata yuwu ba dan haka suka sake wata.
Sun san yanda Bashir yake da son yara ya kuka kwallafa rai akan cikin jikinta dan
haka yanzu shine target dinsu, Addah batayi sanya ba ta karanta mata duk yanda
zatayi, da Bashir din ya kira waya zata langwabe yau tace kanta anjima cikin ta, Aa
jiri ne yake damu ta shidai se yace mata taje Asibiti ta kuma rage yawan zurga
zurga saboda halin da take ciki. Ganin an kwashe sati biyu ana haka be ce ze zo ba
ko ita ta tafin yasa suka shirya sabon plan.
Ranar Juma’a data kama Sati biyu kenan rabonsa da Gombe da daddare suna cikin waya
tace bari tayi fitsari, bata kashe wayar ba ta ajiyeta akan sink ta dauki hand
shower tana tsiyayar da ruwa kaman me fitsari se kawai ta fasa ihu.
Bashir da acan bangare yana riqe da waya yana jiran ta gama ya miqe a sukwane jin
ihunta har yana tunkude cup din da Asma’u ta cika masa da Kunun Aya ya tuntsure a
qasa take kuwa ya fashe.
“Lafiya meya sameki” ya tambayeta a kidime, seta fashe masa da kukan qarya tana
cewa “Jini, jini ne yake zubomun” ta ci gaba da kukan.
Sosai hankalin Bashir ya tashi, idan be manta ba wancan karan da haka ta fara zubar
da jini kafin Wani lokaci jaririn ya mutu a cikinta se inducing dinta sukayi ta
haihu dan haka yake taka tsan tsan da abinda ze sake janyo faruwar hakan.
“Subhanallahi a garin yaya toh ko kinyi wani abun ne daya fi qarfin jikinki?” Ya
tambaye ta
“Nima ban sani ba kuma ni banyi komai ba, dama ba tun yau ba ya fara kawai gaya
maka ne banyi ba bana so hankalin ka ya tashi” Amirah ta fada tana sheshshekar
kuka, a ranta Addu’a takeyi Allah yasa yace zezo dan wallahi qafarsa qafarta itama
se taje an ci uwar da ake ci acan tare da ita.
“Kin gane ki gyara bari na kira Naziru yazo ya kaiki Asibiti yanzu” maganar sa ta
katse mata tunani, se ta dan diririce dan bata zaci zece aje Asibitin ba amma kuma
idan taqi tasan wata matsalar zata kwantowa kanta in kuma sukaje akaga ba haka ba
nan ma ba tsira zatayi ba, daurewa tayi tace masa
“Aa karbar shi dare yayi yanzu kuma bada yawa bane ai da nayi tsarki ma ya dena
zuwa, sannan Anty Ramle tana gida (Amaryar babansu Nurse ce) koda wani abu ya taso
zata iya taimaka min kafin muje Asibiti”.
Sallama sukayi ya kashe wayar Badan ya gamsu da maganarta ba dai ya qyaleta tunda
yasan Anty Ramle tasan aikinta sosai zata kula da ita amma koma menene zuwa safiya
dole taje Asibiti dan baze dauki ganganci ba, kai qila gobe ya tafi ma dakansa ya
kaita gara in ma wani abune a shawo kan matsalar da wuri.
Tsakin daya sakeyi a karo na ba adadi ya saka Ma’u daga kai ta kalleshi, tunda ya
barar da kunun Ayan ta kwashe kwalaben tareda goge Gurin kawai ba tareda ta
tankashi ba dan taji duk maganar da sukeyi. A ranta tadan tausayawa Amiran in da
gaske takeyi dan dai duk mace tasan wahalar ciki da haihuwa dole in kaga wani dashi
ka tausaya masa.
Bata tambaye shi abinda ya faru ba shima kuma be gaya mata ba har sukaje kwanciya,
juyi daya biyu ya saki tsaki kai har abin ya fara bawa Asma’u haushi amma ta jure
bata tanka masa ba sema danna kanta da tayi cikin pillow ta tilastawa kanta yin
bacci. Wai kuma ashe shirun data yi laifine se jinsa tayi yana cewa
“Wai dan wulaqanci kina jina amma bazaki iya tambayata meya faru ba ko?”
“Ikon Allah” ta fada a ranta, a fili kuwa daga kai tayi ta kalleshi