Showing 177001 words to 180000 words out of 238465 words
na shiga hidimomi ne 🙏🙏
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 54
Washe garin ranar tun goman safe Bala ya sake zuwa, yau ma wuni sukayi dai suna ta
tattaunawa duk dai akan Asma'un ne har kuma yamma Bala beyi shirin tafi ba seda
Bashir da kansa ya tambayeshi wai ba yace aiki ne ya kawo shi ba yaushe ze fara.
Cikin kame kame Balan yake ce masa
"Eh daman aikin na kwana daya ne mun gama kawai dai ina so na huta ne. Ni na gaji
da zaman gida ma mu fita waje mu sha iska kuma ita wannan matar daman haka take
bata dafa abinci ne?"
Shiru Bashir yayi masa harya qaraci surutunda yayi shiru, be haqura ba bayan wani
lokaci ya sake ce masa su fita waje dole ya takurawa Bashir din seda suka fita
wajen suka saka kujeru suka zauna.
Basu jima a gurin ba motar makaranta ta sauke yara, gaba daya suka gaishe su, Bala
ya kamo hannun Abdallah yana cewa
"Abdallahn Mami an dawo kenan. Ya naganku a school Bus ina Mamin taku?"
"Daman a school bus muke dawowa" Abdallah ya fada yana shigewa cikin gida yabi
bayan yan uwansa.
"Wai mutumin ta dena dakko yara daga makarantar kenan?" Bala ya fada yana yar
dariyar nan irin ta wanda yaso munafunci akayi sa'a ko kallonsa Bashir beyi ba
hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa.
Kusan minti talatin wata hadaddiyar mota Toyota latest model Baqa ta kunno kai
cikin layin, daga Bashir har Balan da ido suka bita harta tsaya a daidai qofar
gidan Ma'u, seda aka kwashi yan mintina kafin qofar ta bude ta zuro fararen
qafafunta da suka sha Jan lalle sukayi shar dasu ga wasu hadaddun takalma na yan
gayu masu tsinin dunduniya data saka.
Lokaci daya ta fito gaba dayanta, tana sanye da straight gown ta Ash din Leshi tayi
daurin nan nata na tsokano sharia kunnenta saqale da AirPod tana murmushi da alama
waya takeyi ba tareda ta kalli ko ina ba ta qarasa bakin qofa ta kwankwaso Amnah
tazo ta bude tareda karbar jakar hannunta suka maida qofa suka rufe.
A tare Bashir da Bala suka sauke wata Ajiyar zuciya. Shi Bashir tashi ta ganin
Asma'u ce ita kadai ta fito daga motar saboda yanzu har fargaba yake yaga sabuwar
mota me kyau a layin tunda Asma'u ta fara kule kulen nan idan yaga mota ta shigo
zuciyarsa ta ringa lugude kenan harse yaga wanda yake cikinta sannan hankalinsa
yake kwnaciya.
Bala kuwa tsabar yanda Haduwar Ma'u ta tafi dashi ne se bude baki yake amma ya kasa
cewa komai harta shige gidan se ya sauke ajiyar zuciya ya waiwaya yana kallon
Bashir yace
"Kaga wata Arniyar mota Alaji ga kuma hadaddiyar mata ta fito daga ciki kai ina ma
ace na samu irinta ai wallahi komai ma zan iya bayarwa indai zan mallaki wannan".
"Asma'u ce fa" Bashir ya fada yana jifansa da wani kallo, Bala kuwa ko a jikinsa
sema tabe baki da yayi yace
"Ita dinfa, Allahna tuba ni ko Asma'u na samu ai da mugun gudu zan karbeta dan ni
nasan darajar irinta. Ai wallahi ban taba sanin kai lusari bane se randa kace mun
ka saki Ma'u, yo Allah na tuba ko yankar naman jikina zata ringayi ai zan jure kai
in fita ma a kalleni ace ga irin matar da nake aure ma ai martaba ce".
Sakin baki kawai Bashir yayi yana kallon Bala daya dage yana rattabo magana, Lusari
daya kira shi ma be dame shi ba kamar jingina kansa da Ma'u da yayi. A mugun fusace
ya shaqo wuyansa jin yana ci gaba da maganarsa yace
"Idan ka sake hada kanka da Matata sena yanke maka harshe..."
"Malam tsohuwar matarka dai ko ka manta ka sake ta ne, kuma wallahi dan dai bazata
saurareni bane amma duk da haka ma bari kaji sena gwada sa'a ta waya sani ko rabo
na ne ya rantse Allah ya matse ka ka saketa" Bala ya fada yana banbare hannun
Bashir daga wuyansa.
Tsabar mamaki Bashir daskarewa yayi a gurin be dawo hayyacinsa ba seda Bala ya kusa
barin layin ko kafin ya yunqura ma ya bace masa.
Naushi ya kaiwa Iska cikin azababben kishi da fushin da suka turnuqeshi.
Kenan angiza me kantu Bala ya ringa yi masa yana nuna masa aibun ta yana qara
kambama masa laifuffukanta har seda ya rabu da Ma'u shine yanzu ze zo yana cewa
idan ya sameta shi baze rabu da ita ba. Wai ma ina hankalinsa yake da duk be taba
lura da hakan ba se yanzu?
"Kaico na dana zama me daukar zugar was akan iyalina, kaicona ni Bashir da na
fifita lalataccen Aboki akan masu gaya mun gaskiya" ya fada yana dafe kansa.
Cikin gidansa ya koma suka hadu da yan biyu zasu fita da gudu ya kauce musu yana
binsu da kallo cike da tausayin kansa.
Haka kawai ya raba musu kai ya saka suna rayuwa tsakanin gidaje guda biyu. Shidai
ya yarda da qaddara ce ta gifta data tilasta rabuwarsa da Ma'u kuma Allah kadai
yasan hikimar sa tayin haka. Baze sare ba yanzu nema ze daura dambar gyaran
kuskurensa ya kuma maido da Asma'u cikin rayuwarsa kota halin qaqa.
Dakinsa ya shiga ya tarar da Amirah tayi daidai akan gado tana sauke numfashi,
fuskarta ya kalla kafin ya kalli qasan Tiles yaga amai ne a Gurin. A mugun fusace
yace mata
"Ki tabbata kafin na shiga na fito kin gyara gurin nan yanda kika tarar dashi idan
ba haka ba na lahira se ya fiki jin dadi yau a gidan nan" yana gama fada yayi gaba
ze shige bandaki ya jiyota cikin kuka tana cewa
"Nifa bani da lafiya, zuwa ma nayi na gaya maka shine amai ya kamani gaskiya bazan
iya tashi bama bare na gyara guri".
"Ko mutuwa kike kina tashi se kin gyara gurin nan, duk gidan nan nan gurin ne yayi
miki kama da kizo ki zuba qazantarki? Amma karki kwashe ki jira na fito na tarar
dashi a nan" ya shige Bandakin ya barta a gurin.
Yanayinsa da ta gani tasan tabbas ba tausaya mata zeyi ba idan ya fito din, haka ta
tashi ta dakko tsintsiya da abin kwashe shara ta debe kafin ta debo ruwa da mopper
ta gyara gurin se haki takeyi tana gamawa ta wuce dakinta ta ta fada kan gado kawai
ta fashe da kuka.
Wannan masifa har ina? Ace kana da ciki amma banda hantara da kyara ba abinda yake
shiga tsakaninka da uban cikin se baqin rai to ko ana so ko ba'a so seta haife
cikin nan sedai baqin ciki ya kashe mutum.
Bashir kuwa yana shiga ruwa ya sakarwa kansa ba tareda ya cire kayan jikinsa ba.
Kalaman Ba ne suke masa yawo a kwakwalwa suna barazanar fasa masa ita.
Shi Bala zece yana son matarsa? A yanda ya dauki Bala ya zata ko mutuwa yayi se
inda qarfinsa ya qare gurin kare masa martabar gonarsa amma se gashi da ransa
rabuwa kawai sukayi yana iqirarin idan zata so shi ze aure ta gaskiya dole ya
koyawa Bala hankali ta yanda ba matarsa ba ko wata can a gari aka saka baze sake
sha'awar cewa ze aureta ba.
Tsabar yanda kansa ya dauki zafi haka ya fito jikinsa na digar da ruwa ya manta da
kaya a jikinsa seda ya kai tsakiyar dakin kafin ya ja tsaki ya koma ciki, wanka ya
sakeyi ya fito.
A gurguje ya shirya, gidan Musa yake so yaje yanzu yana buqatar wanda ze fadawa
abinda yake ransa ko zeji dadi.
Sanda ya fito bebi takan Amirah ba, a bakij qofa ya hadu da Jafar ya taho da paper
bag a hannunsa suna zuwa kusa yaji qanshin Snack be bata lokaci ba ya miqawa Jafar
din hannu ya kuwa bashi ya tsaya kawai yana kallonsa.
Meatpie ne guda uku manya a ciki, se ya zaro daya ya miqawa Jafar din Murya a
cunkushe yace masa
"Dakko mun Exotic ne sanyi" Jafar ya kwasa da sauri ya wuce Kitchen kafin ya dawo
har Bashir ya kunna mota yana bashi kuwa ya qara gaba.
Yana tafe yana cin Meat pie yana kora lemonsa can qasan zuciyarsa kuwa yama rasa
wanne tunani ze kama yayi a haka ya qarasa gidan Musa ya tarar be taso daga aiki ba
se ya kirashi a waya yace masa yana hanya ya kusa qarasowa dan haka ya jira shi.
Seda sukayi sallar Magriba sannan suka shiga gidan. Musa na tattare kayan da suke
kan kujera yace
"Se haquri Engineer kasan gidan Gwauro ko ina ma zubarda kaya muke tunda bamu da
masu tattare mana"
Bashir dai yaqe yayi har Musa ya gama ya dakko musu ruwa da Lemo da Abincin daya
taho dashi ya zauna se ya kalli Bashir da yayi shiru ya zubawa guri daya ido yace
"Yadai Bash naga kayi shiru ko dai jikin ne har yanzu?"
Numfashi Bashir ya sauke yana gyara zama yace
"Musa akwai matsala ina jin kamar kaina ze fashe wallahi damuwa tayi mun yawa".
Musa daya debi abinci ya kai baki yayi saurin hadiyewa yana kallon Bashir ya gyara
zama yace
"Wace irin Matsala kuma Bashir meya faru?"
Ba bata lokaci Bashir ya shiga lissafa masa abinda ya faru tun daga kan dalilin
sakin Ma'u har zuwa yanayin da ake ciki a yanzu haka da maganar da Bala ya fada
masa. Musa da tuni ya sume a zaune yana kallon Bashir seda ya kai aya kafin yaja
numfashi ya dire yace
"Gaskiya Bashir ka tafka wauta qundumemiya ma kuwa kai wa yace maka ana rabuwa da
matar fari, matar dakuka sha wahalar ku tare sannan yanzu ka saketa akan wata can
da ka ganta rana tsaka Bashir ka rabu da matar ka uwar yayanka gaskiya ka bani
kunya ka kuma bani mamaki tsahon lokacin nan ace baka tare da Asma'u amma baka gaya
mun ba.
To ni yanzu me zanyi maka ma ai ka riga kwabarka tayi ruwa sedai na baka haquri
kawai Allah ya kawo maka dangana amma duk macen dakayiwa haka ka sake ta akan yar
uwarta mace gaskiya da wuya tayi haquri ta sake dawo maka dan ka rigada ka nuna
mata iyakarka ka nuna mata cewar waccen ta fita martaba da mutunchi a gurinka to
zaman me zata sakeyi da kai?"
"Haba Musa kaida nazo neman mafita a gurin ka ya zaka ringa magana haka?
Dan Allah ka taimakamun ka bani magita ina son matata bana so na rasata" Bashir ya
fada kamar me shirin saka kuka.
Musa kuwa Ido ya saka masa yayi tagumi yana kallonsa har yayi ya gama sannan yace
"Kanaji ko shawarar da zan baka kawai ita ce ka tafi malam ka gwada sa'arka, wani
girman kai duk ba naka bane yanzu dan ka rigada ka kwafsa yawwa kaje ka sauke kai
qasa ko roqeta in Allah ya soka ta haqura ta dawo maka shikenan amma dai Asara kam
ka tafka wallahi".
Haka suka rabu da Musa ya koma gida yana sake tunanin abinda ya gaya masa kuma ya
tabbatar hakan shine mafita dole ya nemi yardar Asma'u dan baze tsaya yayiwa kansa
salalan tsiya ba.
Ya tarar da Amirah na fama da kanta tayi amai ta galabaita kamar bazata kai ba,
dole ya dauketa suka tafi Asibiti saboda yanayin jikin dole se gado aka bata. Seda
ya biya duk abinda ya kamata kafin ya barta ya tafi gida da yaje be tarar da Yaran
ba Aliyu ne kadai yace sauran suna gidan Mami. Be damu ba yayi kwanciyarsa, dan
yanzu yafi samun kwanciyar hankali ma idan suna can saboda anan sun ringa tsokanar
Amirah ita kuma tayi ta sababi tanazage zage.
Washe gari ya kamata ya koma aiki haka ya tattara ya fita seda ma ya kusa isa ya
tuna da Amirah dake Asibiti be biya ya dubata ba bare ya kai mata abinda zata ci
duk da dai Asibitin suna bada Abinci.
A waya yayi order abinci ya basu Adireshin Asibitin dan baze iya komawa ba, haka ya
wuni sukuku a gurin aiki se sannu ake masa dan duk a zatonsu jikin nasa ne har
sannan be gama warwarewa ba haka ya tashi kai tsaye ya wuce Asibitin dan duba halin
da Amiran take ciki.
Da kuka haiqan ta tareshi tana masa qorafin baya sonta be damu da ita ba tunda ya
banzatar da ita a Asibiti be sake bi ta kanta ba. Ganin mitar bame qarewa bace ya
tafi ya barta dan abinda yake kansa ma a yanzu ya isheshi bayay buqatar qarin wani
abun kuma.
Ya isa gida ya kasa tsaye ya kasa zaune. Tunanin yanda ze tunkari Ma'u yakeyi, meze
ce mata? Ta yaya ze tunkareta?
Wayarsa data dauki qara ce ta katse masa tunani, shnan Dada da ya gani ya sakashi
dagawa da sauri.
Bayan sun gaisa take ce masa
"Bashir Ashe Amirah bataji dadi ba har tana Asibiti?"
"Eh wallahi Dada jiya da daddare ne zuwa yau amma gobe ma zasu sallameta ai" Ya
fada yana mamakin waya kirasu ya gaya musu bata da lafiya.
"Toh ai shikenan Allah ya bada lafiya amma ya kamata ta samu wani babba a kusa da
ze ringa kula da ita saboda yanayin jikin kaga tana da zafin laulayi dole seta samu
mataimaki"
"To ai anan din ma ba abinda takeyi tun tana da lafiyar ma se shirme kawai ta iya"
ya fada a hasale
"Haka za'ayita haquri dai, seka turo da kudin jirgi na wanda ze zo ya tayata zaman
dai, ya bangaren su Asma'u kuwa in ce dai abubuwa sun dai daita ko?"
"Hmmmm" kawai Bashir ya fada daga nan sukayi sallama dan besan me ze ce mata ba ma,
qarin haushin sa ma wani da tace za'a turo ya taya Amirah zama in dan ta shine a
barta ta gane kurenta wallahi haka ba yadda ya iya ya turawa da Naziru kudin dan
yana tunanin Fainusa za'a turo ko banza gidan ya samu kulawa ai.
Shiru ya sakeyi yana tunani, kiranta zeyi ko kuwa kawai zuwa zeyi suyi magana fuska
da fuska?
Yanke shawarar ya fara kiranta yayi a waya nan da nan yayi Na'am da wannan shawara
ya shiga loda lambar wayar Ma'u da ya dade da haddacewa ya dannan mata kira.
Seda tayi ringin harta katse bata dauka ba, be haqura ba ya sake kira nan ma bata
daga ba seda yayi mata kira uku ana hudu ta daga cikin muryar nan tata me sanyi
tayi masa sallama.
Shiru yayi, ta sake maimaita sallamar se kawai ta kashe bayan data ja qaramin
tsaki. Be sare ba ya sake doka mata kira, cikin dan fada fada ta daga wannan karon
tace
"Waye wai? An kira ni kuma anqi ayi magana" jin ya sakeyin shiru ta sake kashe
wayarta shi kuwa tsabar mamakine ya daskarar dashi wannan karon, kenan ta goge
lambarsa ma kai ko ta goge ai bazata ce bata gane lambar akai ba shi Ma'u zata ce
waye sannan ta kashe masa waya???
ASMA'U
Wato wata irin sabo da shaquwa da ban taba tsammani ba ya ringa shiga tsakanin na
da Yusuf. Zuwa yanzu idan muka wuni bamuyi magana ba ji na nakeyi kamar bani da
lafiya.
Dukda ba wata doguwar magana mukeyi ba amma duk sanda ya kirani seya gaya mun
maganar da zatayi Rugurugu da zuciyata ta tsaya mun a zuciya har zuwa sanda zamu
sake magana.
Aikina kawai nasa a gaba gefe ina kurbar madarar soyayya a ruwan sanyi wadda har
yanzu ni ban yarda wai ina son sa bane,kawai ina jin dadin magana dashi na kuma
dauke shi kamar wani Aboki ne domin dai so dayane kuma Bashir nayi wa shi.
Daren yau ina zaune nayi daidai a qasa ina duba wasu takaddu dana taho dasu daga
office, gaba daya na gaji, Allah Allah nake na gama na kwanta na huta ga yara da
suka isheni da hayaniya na korasu daki dan gaba daya yanzu kusan rayuwarsu a nan
gidan sukeyinta tunda Bashir ya kwanta rashin lafiya suka dawo kwana anan gidan
Aliyu ne kadai yake komawa se fa Jafar wata rana idan yaga dama ya bishi su tafi
gida.
Wayata da na saka a chaji ce ta dauki qiwar in tashi na dakko tasaka na barta tayi
tayi harta katse dan kanta idan na gama na kira dan nasan baze wuce Yusuf ba ko
sabon Mayen daya maqalemun Hayatuddeen.
Jin ana ta kira ba qaqqautawa ya sakani jan tsaki na miqe na jawota, lambar Bashir
ce, na tsurawa wayar ido ina so na gano dalilin da ze saka Bashir kirana a waya
yanzu to qila yace Yayansa su tafi gida ko amma me yasa baze kira Aliyu ba tunda
yana da waya ko Amna se ni ze kira?
Ina wannan tunanin har kiran ya sake katsewa wani ya shigo sena daga na saka a
kunnena tareda yin sallama. Shiru naji anyi, na cireta na duba dan na tabbatar ko
kiran katsewa yayi amma naga sakannin suna tafiya na sake maimaita sallama naji
ba'a amsa ba se kawai naja tsaki na kashe.
Ta yuwu ma bani ze kira ba ko kuma besan kiran ya taho bama gaba daya ina qoqarin
ajiyewa se ji nayi ta sake daukar qara alamar shigowar wani kiran hakan ya tabbatar
mun da yana sane kenan wulaqancin nasa ne ya motsa dan haka na gyara zama tare da
dagawa nace
"Wai waye ne yake kira ana magana kuma anyi shiru? Idan baka da abin fada ni ina da
aikin yi" na sake kashe wayar.
To haka kawai ze ringa kirana yamun shiru me zan masa, ni kadai nayita mita ina ci
gaba da duba takadduna can jimawa se shigowar saqo naji nayi banza da wayar ban
tashi dubawa ba seda na gama abinda nakeyi kaf na je kwanciya dan har na manta ma
seda na janyo ta zan saita Alam kafin naga saqon akan wayar se na bude na fara
karantawa kamar haka.
"Zuwa ga Ma'una. Nasan ni mai laifi ne a gareki kuma na karbi kuskurena da hannu
biyu sannan a shirye nake da karbar ko wanne irin hukunci daga gareki in har hakan
ze saka ki huce daga abinda ya faru.
Kiyi haquri mu komawa kyakykyawar rayuwar da muka faro ko dan saboda so da qaunar
da yake tsakanin mu.
Bashir".
Dogon tsaki naja bayan dana gama karanta saqon nasa nan take na goge. Ashe ma nayi
haquri ne mu komawa rayuwar mu, juyawa nayi na kwanta ina rufe idona na tashi na
zauna ina sake tuna dalilin daya saka Bashir yimun sakin wulaqanci.
Akan Mace fa, me daura zani da dan kwali Macen ma yarinyar dana raina da hannuna
harta zama abin sha'awar daya gani ya aura ya hadamu zaman kishi da ita a saboda
ita ya kassaramun rayuwa ya hadani da zawarci shine yanzu saboda tsabar rashin
kunya ze turo mun wannan saqon yana tunanin wannan ya isa ya wanke tarin laifin sa
a gurina kenan? Lallai ba shakka ya dauke ni sakarya.
Baccina na kwanta, washe gari da wuri muka fita tun a hanya kuwa na kaftawa yaran
warning akan kan kar wanda ya sake zuwa ya kwanar mun a gida kowa ya zauna a gidan
ubansa. Idan taqamarsa su to yanzu na rigada na saki zuciyata ko da su ko babu su a
tare dani babu abinda ze chanza daga walwalata. Na barsu a hannun ubangiji nasan ze
kulamun dasu.
Sau kusan hudu ina ganin missed calls dinsa a office dinma amma naqi dagawa to me
ze gayamun wai? Ko