Showing 54001 words to 57000 words out of 238465 words

Chapter 19 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

wuce su tayi ta nufi kitchen tana
kaiwa daidai qofar Bashir ya shigo da sallama ciki ciki ai se kawai ta qame a gurin
ta kasa gaba ta kasa baya, bata so su hadu ba, a yanda ta tsara in ta shige daki
bazata sake fitowa ba abincinma idan an gaji a ringa binta dashi har seya bar garin
gashi yanzu tun ba’aje ko ina ba sunyi kicibus.

Shi kuwa Bashir bema lura da ita ba ya nemi guri kusada Asma’u ya zauna, Dada ce ta
shigo itama daga Gurin Alhaji tan cewa Naziru yaje Alhajin na kiransa. Kallon
Amirah dake tsaye kamar an dasa ta tayi tace

“Ke kuma lafiya kike tsaye kin qi gaba kinqi baya” kidan duma zuciyar Amirah ta
shigayi daidai sanda ta waiwayo idanunta suka hadu dana Bashir, wani mugun kallo
ya aika mata dashi daya saka hanyar cikin ta kadawa bashiri ta shige kitchen din ta
fara matsar kwalla.

“Me yarinyar nan takeyi a gidan Dada oh danace ta tafi shine ta taho gidanmu saboda
raini ko tam” ya fada yana sakin qwafa dagani yama rasa me zeyi kawai. Seda Dadan
ta zauna tana kallonsa tace

“Dalilin kiran dana maka kenan ai nima ina zaune sukazo ita da Addah sunce kace ta
tafi gida”

“Eh nace ta tafi gida Dada wannan yarinyar bata da mutunchi ta raina ni ban isa na
bata umarni tabi ba se abinda ta rayawa kanta, seda na gargadeta nace baza’ayi
taron sunan nan ba amma saboda ta nuna mun ban isa ba taje tayi”

Bakiga dakina irin barnar da akayimun ba iya abinda na gani kenan ma Allah kadai
yasan me aka dauka a ciki tunda ban duba ba, shikansa gidan karkiso kiga yanda suka
maidashi. Ga Iman can a Asibiti babu tabbacin ta tashi sannan saboda ma sun raina
mun hankali na dawo na tarar da wata mata ta biyo karbar bashinta wai ni suke cewa
na roqar musu ita tayi haquri. Wallahi Dada Idan yarinyar bata kama gabanta ba ta
bari hannuna ya sauka akanta sena mata dukan mutuwa wallahi....”

“Babu inda zataje kar kuma ka fasa mata dukan mutuwar” Alhaji Amadu da Naziru ya
turo akekensa ya katse wa Bashir Hanzari, se suka juya gaba daya suna kallonsa
bayan da Nazirun ya kawo shi tsakiyar Palour.

Kallon Bashir da yake ta qoqarin hadiye malolon daya tokare masa wuya Alhajin yayi
ya girgiza kai kafin ya Kalli Dada yace “Ina Amiran take kirawo ta nan” Miqewa
Dadan tayi ta shiga kitchen suka fito tareda Amirah dake risgar kuka kamar an ce
mata Addah ta mutu ta nemi can gefe ta zube tana ci gaba da kukanta.

Kallonsu Alhaji Amadu yayi daya bayan daya ya tsaida idonsa akan Asma’u da tunda ya
shigo ta tsame hannunta daga cikin tuwon ta gyara lullubinta, se ya saki wani
murmushi da bazaka tantance na mene ne ba ya kalli Bashir yace

“A lokacin da zaka auri Amirah me nace maka”
Sunkuyar da kai Bashir yayi yana cigaba da komawa da abinda yake taso masa idanunsa
sun kada sunyi jajir,

“Ba magana nake da kai ba” Alhaji Amadu ya katse shi cikin daka tsawa se Bashir din
ya dago da sauri yana kallon mahaifin nasa, kalaman sa suna dawo masa daya da daya
a kwakwalwa ranar dayazo yace masa ze qara aure ze auri Amirah diyar Addah tamkar a
yanzu yake fada masa su.

“Sharadi zan kafa maka Bashir, yanda ka dakko auran nan to ka tabbata Babu Yaji har
qarshen rayuwarku. Ina raye ko bana raye idan ka rabu da yarinyar nan ban yafe maka
Ba Bashir kaje ku zauna duk wuya duk dadin da zata zo maka dashi”

“Kace babu Yaji babu saki” Bashir ya fada da kyar kamar me ciwon haqori.

“Madallah, ka tashi ka dauki iyalan ka ku tafi aje ayita haquri, daman shi wanda ya
siyi rariya ai yasan zata zubda ruwa”.

“Asma’u ya gidan ya Mutane nawa dazu sun shigo Ina bacci kafin na yunqura kuma suka
fice” Alhajin ya fada yana maida hankalinsa kan Asma’u. Seta sunkuyar da kanta tana
dan murmushi tace “ lafiya lau Baba suna Babban gida ai yanzu zaka gansu ma tunda
na fada musu ina nan”.

“To masha Allah, yaushe zaku koma hutu ya qare ko?”

“Eh Baba daman litinin muka shirya dazu kuma yace wai gobe zamu tafi amma a mota
gashi bamu qarasa shirye shiryen mu ba” Asma’u ta fada tana janye fuskarta gefe dan
karma su hada ido da Bashir.

“Wane irin tafiyar mota kuma ana zaune lafiya, ko a zamanin da da muke tafiye
tafiyen ai munji jiki bare ku yanzu da baku saba ba ga yara kuma, kudai jira
litinin din dai kubi jirgin safe kamar yanda kuka saba, Allah yayi muku Albarka
yaci gaba da ruqo da hannunku” Baban ya fada suka amsa gaba daya da Amin.

Naziru na zaune kamar ya buga tsalle tsabar yanda da Al’amuran suka masa dadi,
yanda aka tilasta Yayan nasa maida Amirah gida ya mugun masa dadi aransa fadi yake
“Allah ya qara ai kadan ma ka gani in bakayi da gaske ba wataran se sun saka a
kulleka kana zamanka da matar rufin asiri ka kwasowa kanka kaska.

Baban ne ya katse shi yana cewa “zo Naziru ka maidani na kwanta kaji Dare ya
farayi” yayi musu sallama Naziru ya maidashi.

Kamar kurame haka sukayi jugum jugum a gurin, Amirah dai a tsorace take da hukuncin
na Baba dan data bi shi su koma gara ta zauna agidan kai gara ko can gidan su ne
ace ta tafi ita kuwa Ma’u ba abinda ya shalleta masifa ce dai tasan zeyi ya gama
tunda dai an rushe zancen mota ai shikenan, shikuwa oga Bashir har wata zufa yake
kamar wanda ya hadiyi kunama.

Makwallaton wuyansa se sama yake yana qasa ya kasa furta komai se “hmmm” kawai.
Miqewa yayi dakyar ya iya ce musu su tashi su tafi ya fice ko sallama be yiwa Dada
ba, Asma’u ce ta fara miqewa tayiwa Dada seda safe tabi bayansa Amirah dai ko motsi
ta kasayi.

Kallonta Dada tayi tace “ki tashi ko so kike ki qara wani laifin a gurinsa” ai
kamar tana jira ta sake fashewa Dadan da kuka tana cewa “Dan girman Allah Dada ki
roqi Baba Ya barbi yau na kwana a gidan nan idan sun koma Lagos sena tafi wallahi
idan na bishi yau kashe ni ne kawai Yaya bazeyi ba Dada dan baki san irin abubuwan
da nayi masa bane” ta qarasa tana sake rushewa da kuka.

Miqewa Dada tayi tana cewa “koma mene ai ke kika ja gara ki tashi ku tafi dan nima
bazaki ja mun wani fadan a gun Alhaji ba kije kawai ba bu abinda zeyi miki” tayi
shigewarta daki ta barta.

Amirah tana kuka tana komai ta hado jakar Naziru ya daukar mata suka fita yana mata
dariyar mugunta, dakyar ta bude bayan motar ta shiga dan tuni Asma’u ta kame a gaba
abunta cikin ranta qal da wannan abubuwa da suke faruwa.


Afuwan 🙏🙏🙏🙏qundumemen uzuri ne ya riqeni kwana biyu amma komai ya dawo daidai zaku
ci gaba da jina insha Allah

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

*INA MANYAN MATA NE*
*INA MASUSON FARA SANA'A*
*HANNUR COLLECTION tazo maku da alkairi domin qarin bayani kobiyo💥🔥💥*Munada amarya
da uwargida package wannan package ya* *qunshi,abubuwa guda goma*
*maganin sanyi da basur*
*Nasha da madara*
*Nasha da lipton*
*Na dahuwar kaza*
*Na tsarki*
*Nasha da kankana*
*Garin tsumi*
*Hadadden tsumi*
*Na matsi*
*Nahadawa da zaitun*
*Muna saida tahnia me gyaran aure*
*Akwai kayan ORIFLAME*
*Akwai kayan GHT*
*Akwai kayan faforlife*
*Akwai chocolate da coffee na mata*
*Akwai turaruka,sabulai mayuka da duk wani kayan gyaran jiki da aure*
*Munada dogayen riguna sari,yadin hijab materials,atamfofi,shadda,laces dss*
*Albishirunku ina registration din ORIFLAME, GHT, FAFORLIFE ,Duk kayanmu farashin
sarine,kuma muna aikawa kowanne gari cikin aminci*
https://wa.me/message/3BCXWNGTI7ILC1



Page 22


Gudu ya ringa fellawa dasu kamar masu barin gari sanda ya tsayar da motar a bakin
Get kuwa har qauri takeyi, a Get din ya watsar dasu yai gaba dan Amirah bata ko
samu damar daukar Akwatinta ba Asma’u ta saka key din hannunta ta bude musu Get
suka shiga.

Yanda taga Amiran tana tafe tana layi se ta bata tausayi dan haka ta qarasa ta riqo
kafadarta ai kamar me jiran majingini kawai ta fashe mata da kuka tana cewa”Dan
Allah Anty ki bashi haquri, wallahi ba laifina bane Addah ce kema kin santa ita
tace se anyi”.

Asma’u bata tanka ta ba har suka shiga dakin Amiran ta zaunar da ita akan Kujera
tana qarewa palour kallo baki bude saboda mamaki. Duk wani abu daya danganci glass
an fasa harda Tv ba’a barta ba daidai da labulaye duk duk an sauke su qarafunan sun
karyo.

Ajiyar zuciya tayi kafin ta Kalli Amirah da har sannan kukan take tace “Kiyi shiru
komai zai daidaita Insha Allah, ina zuwa”.

Part dinta ta koma, Farfesun Tsokar rago ta ciro a freezer ta dumama kafin ta hada
Shayi a qaton Mug ta dora su a kan Try hade da Bread ta dauka ta koma part din
Amiran. Bayan ta ajiye su ta sake komawa ta debo mata tuwon semo da miyar danyar
kubewa da tayiwa Bashir bema ci ba ta sake komawa part din Amiran.

Tana zaune a qasa ta zamo daga kan kujerar riqe da cikinta tana murqususu, da sauri
Asma’u ta ajiye try din ta nufeta tana “lafiya Amirah meya same ki?” Ita dai se
juyi take tana malele
kuwa akan Tiles saboda bala’in qullewar da cikin yayi mata.

Dakyar ta nutsu ta kamata ta koma kan kujerar, Shayin ta fara bata a baki tana
karba, kurba uku tayi Amai ya taso mata ko kafin ta miqe tayi shi a Gurin Asma’u na
tsaye se sannu take mata. Bowl babba ta dakko ta debo ruwa a babban kofi da dawo
gurin Amiran, ta zuba mata ta kurkure baki da dauraye fuskarta Ta koma yaraf ta
kwanta tana sauke Numfashi.

Abincin ta ajiye mata nan ta shiga ci kuwa dan Aman ya taimaka ya bude mata ciki
ita kuma ta dauke robar ta tafi dakko mopper da packer, Duk Kyankyami irin na
Asma’u haka ta daure ta kwashe aman tsaf ta zuba ruwan omo ta goge Gurin kafin ta
sake saka ruwa ta goge tas ta nemi freshener amma bata samu ba sanda ta gama itama
ma Amirah ta cinye farfesun tsaf ta shanye shayin se ajiyar numfashi takeyi.

“Nagode Anty Allah ya biyaki” ta fada tana sunkuyar da kai, se Asma’u tayi murmushi
kawai tace “bakomai, ki samu kisha magungunan ki se ki kwanta ki huta. Ga ragowar
abincin nan koda zaki buqata anjima Allah ya qara kiyayewa” ta fada tana nufar
qofa.

Tashi tayi ta rakata tana sakeyi mata godiya ta kulle qofarta gam ta ciki karma ya
dawo kenan ya shigo bata kwashe kwanukan ba ta haye kan kujera se baccin wuya ya
kwashe ta.

Asma’u ma tana komawa part dinta kulle qofar tayi idan Bashir ya dawo da akwai key
a hannunsa dan sunyi waya yaran sunce a can zasu kwana ma bazasu dawo ba. Sama ta
wuce ta shiga wanka, seda ta gyara jikinta tsaf lokacin har sha daya tayi ganin
Bashir be shigo ba yasa tayi kwanciyarta kawai dan daman dai yau koya dawo tasan
bazasu kwashe qalau ba.

Bashir
Yana sauke su kai tsaye tsohuwar unguwar da suka taso ya wuce gurin Bala, Abokinsa
ne tun na yarinta tare suka tashi a unguwarsu su Hudu Bashir, Marigayi Aliyu, Bala
da Sadiq yayan Asma’u su hudun Abokaine na rai da rai tun daga Primary ajinsu daya
har jami’a sannan suka rabu kowa ya karanci course dinsa daban.

A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe
motar yayi tareda jan kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar ,
zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata
a mangyada.

Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara
biyu an tafi ta uku da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba
wai dama haka qarin auran yake ko kuma shine beyi dace ba.

“Me yasa baka nemi wata ba me yasa se Amirah zaka aura Bashir? Yau da ace wata
daban ka aura wallahi ko mata uku ka auro lokaci daya bazan damu kamar wannan auran
da kayi ba amma shikenan haquri ko nayi haquri. Idan dan Allah kayi Bashir Allah ya
bamu zaman lafiya ya bani ikon cinye jarabawar da yayi mun, idan kuma kayi ne dan
kaci mutuncina to Allah baze bari na tozarta ba ba kuma zaka samu nutsuwar da kake
iqirarin samu ba” kalaman Ma’u na qarshe wanda daga su bata sake tayar masa da
hankali ko wata magana ba sanda ya auri Amirah.

To wai alhakin nasa ne ko nawa shidai Allah ya sani beyi auran nan da wata manufa
ba yayi ne kawai dan yana ra’ayi bakuma dan ya tozarta Matarsa ba kamar yanda take
tunani amma gashi nan shi yake karbar sakamakon sa da Hannun hagu wai ta ina toh ya
kuskure?”

Glass din window da aka kwankwasa ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago
yana gyara zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen
qafafunsa yana sake kokawa da dacin ransa kafin ya fito gaba daya.

“Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran
fitowar Bashir din ya zo ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai
yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse maganar tasa.

“Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da
ya aure shi ya bude murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin
zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu
son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai nasa.

Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda
Bashir din “Engineer wai yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane”

Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda
banyi da quruciyata ba shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida
hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan wata kwaya kai dai da ka riga ka illata
rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne kodan su ya kamata ka dena
abinda kake yi”.

Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna
secondary Bala ya fara bin wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar
shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan ya dena amma ina qarshe har yaso
koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya bari amma shi
Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa
dan shi kadai ne danta Namiji.

Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura
mata Da ba’a qaunar sa seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da
idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai kayan maye har a cikin gida sha yake babu
abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har kuwa ta mutu da wannan
baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa ko
yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su
Bashir dan dai babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir
da Yake ganin Balan na bashi shawarwari daidai da ra’ayinsa.

Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan
so samune Sadiq ya kamata ya gayawa dan yafi Bala hankali amma tun auransa da
Amirah alaqarsu taja baya dan a lokacin gani yake Sadiq din ya goyi bayan qanwarsa
dan haka ya zage ya masa rashin kyautawa shi kuma da zuciya ya fita sabgarsa sam
yanzu babu wata kwakwkwarar mu’amala tsakanin su daman ga banbancin gari yanzu ga
aiki yasha kan kowa.

Labarin duk abinda ya faru da hukuncin daya dauka da wanda Baba ya dauka shima ya
bawa Balan, Bala dayai zuku di kamar gaske yana sauraronsa ya jinjiga kai yana cewa
“kai Engineer kafa debo da zafi wallahi, nifa daman wannan Addan taku kasan yar
bala’i ce tun duniya na kwance bazan manta sanda muke zuwa gidanta ba lokacin tana
kiwon kajin nan in muka kwamusu daya haka zata biyo mu har layi tana sababi, amma
ai ita Amiran tayi fa. Ka jure kawai tunda ka samu yarinya me kyau duk abinda ze zo
ai daga baya ne”.

Baki bude Bashir yake kallonsa, wai ma wannan ya gane kan matsalar sa kuwa yake
masa wannan soki burutsun koda yake shima da laifin sa wani sa’ilin ina shi ina
shawara da dan wiwi? Tsaki ya buga kawai tareda yaiwa motar key yace masa “Malam
sauka seda safe”

Bala ya kwashe da dariya yana cewa “ah da wuri haka kodayake gara kaje ka lallashi
yar Babynka wallahi baka san wahala suke yanzu ba ko kodan kai Allah ya baka zuqa
zuqa har biyu ka ajiye a gida baka san yanda kan gayu yake gwaruwa yanzu kafin su
samu wadannan kalolin ba”

“Bala sauka ko na tafi da kai” ya sake fada a fusace, se Bala ya balle murfin motar
ya fita yana ci gaba da yi masa dariyar qeta yace “Haba Engineer ai daman ba’a
samun abu biyu ka hada kyau da zaman lafiya ai baze yuwu ba mu dai da muka auri
munanan ba gashi muna qalau ba wayake jin kanmu...” fizgar motar Bashir yayi Allah
yasashi ya matsa gefe ya koma majalisarsu yana ci gaba da dariya a ransa yana cewa
“Ai baka ga komai ba wallahi, yanda ban samu abinda nake so ba kai ka samu, a baya
dai kaji dadi amma bazaka sake samun kwanciyar hankali ba”.

Bayan Barin Bashir gurin yawo ya ci gaba dayi a mota dan baya so ya koma gida ko
waccensu haushinta yake ji, seda sha biyu ta buga sannan ya kama hanyar gida bada
ban ba ma Hotel zeje ya kama amma yanda duniyar nan take yanzu abu qalilan seya
jefaka a masifa wani ya ganshi be san meya kaishi ba a canza masa manufa, gidan ya
dawo masu gadin layinsu na zazzaune suna hira mutum biyu suka taso suka bude masa
get bayan ya aje motar ya koma yayi musu dan ihi sani ya koma ciki.

A tsakiyar part biyun ya tsaya ya riqe qugu yana balla musu harara kamar masu dakin
ne a gabansa, fitilun palour Amirah a kunne suke, daga inda yake yana hango cikin
palour tarwai ta window saboda babu labule kamar ya share sedai tunawa da Maganar
chanza key da Asma’u tayi masa ya saka shi dosar gurin dan be san ko an sace din ba
da gaske.

Da key din hannunsa yayi amfani ya bude qofar tana kwance akan kujera ta duqubqune
ya isa kanta ya tsaya ya, ganin yanda ta bar kwanuka ya sa ya fara kiran sunanta.
Amirah kuwa Kamar a mafarki taji muryar Bashir yana kiranta, tana bude ido kuwa ta
ganshi akanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login