Showing 195001 words to 198000 words out of 238465 words

Chapter 66 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

kayi haquri, kasan fa daman ina ta so na baka sautu kuma ina
tsoron kar kace na mai dakai dan aike shi yasa nayi shiru amma a siyo mun mana ayi
mun afuwa” na fada cikin shagwabar da ban san nima inayi ba.

“Dagaske hukuncin bata mun ran da kikayi kenan, badai wannan karon ba ko zan siyo
miki sedai wani lokaci” ya bani amsa

“Shikenan toh Allah ya kaimu wani lokacin”

“Fushi kikayi?” Ya tambaye ni, se na yi murmushi nace

“Aa ba fushi nayi ba”.

“Karki damu zanyo miki tsaraba saura itama idan na kawo kice bakyaso, ki turamun da
size na takalmin ki”.
Hira kadan muka sakeyi kafin mukayi sallama na kwanta dan ina so na tashi da wuri.


Wai dan Allah ni kadai nake fama da matsalar network if yes to to ya kamata a san
yanda za’ayi dani 😭😭

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 58

BASHIR

Beyi niyyar zuwa sallah Gombe ba amma saboda karya shiga haqqin Amirah yasa ya
tuntubeta ko zasuje. Suna zaune ita da Addah a palour ya fito daga dakinsa da ya
mayar dimun da iman yana ciki indai yana gidan.

Ledar kayan sallar ta daya karbo dazu ya dauka ya fito palour,
Suna zaune Tayi daddaya a qasa taba cin Gyada dafaffiya ga cikinta nan daya fara
girma a waje saboda Half vest ce a jikinta kawai ta daura zani kanta babu dankwali
wai zafi take ji dukda akwai wuta sun kunna Ac suna hira da Addah da tayi shar
abinta duk rama da baqin da tazo dasu babu to aci me kyau a kwana a Ac meya dameta.

Zama yayi ya gaida Addah ta amsa tana hararar sa dan haushin sa take ji, bama ya
zama bare suyi magana da ita tun ranar nan da tayi masa zancen kayan sallah be
kulata ba gashi har yanzu ana jibi sallah koda uwarsa yake so taje idi oho.

"Ya jikin naki? Me yasa kika zauna haka a cikin sanyi gashi kanki ko rufeshi bakiyi
ga dare ba bakya son kula da lafiyar kwata kwata" ya fada bayan daya amsa gaisuwar
da Amirah tayi masa.

"Kai in ka gaya mata qila taji ai mata da ciki ki zauna duk kiyita budewa Aljanu da
ifiritai jiki suna kallo ai se kiyi tayi se wani abu ya same ki kuma azo ana yaya
za'ayi" Addah ta fada tana gyara zama.

"Babu abinda ze sameta In sha Allah kawai dai ta ringa kula kuma meye ma amfanin
zamanki idan bazaki ringa nuna mata abinda ya kamata tayi ba"

"Bazan nuna ba ubana nace bazan nuna ba, kaifa daman ba mutunchi ne dakai ba to ni
banzo dan in kula da ko wacce qatuwa ba zuwa nayi nima a kula dani na hutawa
rayuwata a toh" ta hayayyaqo masa.

Be kulata ba ya turawa Amirah ledar daya fito da ita Addah tayi zaraf ta dauke ta
zazzage kayan ciki a qasa.

Kayane kala hudu, Atamfa biyu se Lace daya da Brocade material shima daya duk an yi
musu dinkuna masu kyau. Seda ta ware ko wanne dukda a goge suke tas ta hargitsa
kafin ta watsar qasa tana cewa

"Ina nawa naga duk wasu riguna fici fici babu wadda zatamun a ciki"

"To daman an ce miki da naki a ciki ne kayan Matata ne kema ki siya da kudinki mana
ai kina dasu ko ni aka ce na miki kayan sallah?" Ya fada kansa tsaye.

Amirah kanta da take murna tana daddaga kayan dan babu wanda beyi kyai ba kana
kallo kuma kasan masu tsada ne seta tsaya tana kallonsa jin abinda ya fada tace

"Yaya Addah ce fa kake gaya mata haka"
Harara ya maka mata yana cewa
"Gobe Solomon zezo ya kaiki ki siya takalmi da mayafi zan tura miki kudin sannan na
manta ban tambayeki ba ko zakije sallah Gombe ne dan ni bazan je ba"

"Uwarka Nafi ita kake wulaqantawa Bashir bani ba shege wanda be gaji Arziqi ba. Ni
zaka kalla kayiwa gori to wallahi bazanyi da kai ba da uwarka zanyi dan ita ce
daidai dani se inji idan ma ita ta baka damar ka ringa wulaqanta ni. Idan ma banda
lalacewa Bashir in haifar maka matar ka aura amma baka da wadda ka raina a duniya
sama dani ko? Nagode.

Ke kuma kina zaune yana qarewa uwarki tana di ai Shikenan gaki gashi nan kuci
kanku" Addah ta fada tana miqewa, har tayi gaba kuma ta dawo tana cewa

"Babu Gomben da zamuje uwar me muka manto acan da zamu koma dakkowa?"

Shidai be kulata ba ya kalli Amirah yana jiran tata amsar itama a sanyaye tace
"Anan zamuyi sallah"
"Shikenan, goben da wuri zezo daganan se ku biya kuyi cefanen abincin sallah"

Ya dauki wayarsa yayi danne danne kafin ya miqe ya shige daki yana cewa "gashi nan
idan kunje ze kaiki inda ake siyar da Ready made ki dauki 50k ki siya mata kala
biyu ai zasu isa".

Wayarta da take gefen ta ce tayi qara alamar shigowar saqo ta janyo ta duba, dubu
dari da Hamsin ya tura mata tayi ihun murna daidai sanda Addah ta fito daga dakin
da take da waya a kunne tana cewa

"To qarya zan miki Nafi? Zagina yayi ta uwa ta uba ko ince zagin mu nida ke tunda
iyayen mu daya har yana cewa idan na isa na danne shi ma kwata mana" se tayi shitu
ta zauna a kujera kafin tace gaba da cewa

"Oho dai Idan ma ke kike karanta masa cewar ya wulaqanta ni to dani dake dukka ya
wulaqanta aikin banza mana, daman nasan ai ba son zuwana nan kike ba kina baqin
ciki nazo naci arziqi ke kina can to wallahi naga guri idan ma zaki barshi ya sake
hannu ya ringa yin wadaqar da yakeyi da a gidan sa gara ki bati dan ba dawowa zanyi
ba nida Gombe seda ziyara muzo a jirgi mu dawo abin mu".

"Haba Addah, a yaushe ya zageki dan Allah yanzu kin hadashi da Dada so kike ta kira
tayi masa fada bayan ga kudi fa ya turamun yace na siya miki kayan"

"To qarya nayi kenan dan ubanki nawa ya turo?" Addah ta zaburo mata, seda ta kalli
qofar dakin kafin tayi qasa da murya tace

"Dubu hamsin ce yace na dauki talatin kudin mayafi da takalmi naki Ashirin".

"Hamsin din banza da wofi uwar me za'a siya da dubu hamsin a zamanin nan, su desina
takalmi da mayafin da mata suke sawa duk a ciki zaki siya" Addah ta fada cikin daga
murya.

Alamar tayi shiru karya jiyo Amirah take mata amma ina qara daga muryarta take yi
abinta se Amirah ta narke fuska kamar zatayi kuka tace

"To ke Addah Ina ruwan ki ni hakan daya bani ma na gode dan ba abinda zan suya duk
ina da mayafai kalar da zata shiga da kayan gobense muje a siyo miki naki in be isa
bama sena cika miki a nawa" ta fada qasa qasa danbata so Bashir ya jiyo su
ballantana asirin cuwa cuwar da take shirin yi ya to nu.

Bashir kuwa yana shiga bandaki ya shiga yayi uzurin sa da shirin kwanciya bacci
yana fitowa ya tarar da Missed calls din Dada biyu dan haka ya dauki wayar yabi
bayan kiran.

"Bashir me yasa akullum baka da aiki sena son tayar mun da hankali ne ace kullum ta
Allah seka takali Addah se kace wata sa'arka bayan kasan qarshe duk akaina abin ze
qare" Dada ta fada bayan daya gaishe ta. Dafa kansa yayi ya zauna akan gado yace

"To yanzu kuma me tace na mata? Maganar kayan sallah cefa mukayi kuma ni tsokanarta
nayi da nace bazan mata ba amma gashi can ai na bada kudin a siya mata"

"Saboda tsarar wasanka ce dole ka ringa tsokanarta ai, kuma zanin sallah ai ba yau
ka fara mata ba balle kace mantawa kayi karkuma ka manta yanzu fa matsayi biyu take
dashi a gurinka ko baka mata a komai ba ka mata na surukuta ai sannan saboda
wulaqanci se ana jini sallah zaka bada kudin a siya waye ze dinka mata toh?"

"Nifa Dada ba dan tana sirikata nake mata dinki ba kawai ra'ayi nayi dan in haka ne
Goggon Ma'u ko qualle ban taba siya na kai mata ba kuma baki taba cemun nayi mata
dan tana sirikata ba, nidai na bada kudin duk ma yanda zasuyi suyi ni ba damuwata
bace tun farko ma waya gayyato ta tazo duk gashi nan ita ba taimakon mutane take da
komai ba se qara hura musu matsaloli"
"Allah ya rufa asiri toh, nidai dan Allah ka dena biye mata kuna sa'insa kodan
darajar yarta in ma baka dubi ni yayata bace, naji ku shiru da alama dai bana
bazaku zo ba kenan?"

"Eh se zuwa bayan sallah in sha Allah ni zanzo, yaran dai zasu taho tareda Mamansu
nasan zasu zo muku nan da sallah" ya bata amsa,

"Uhm, ni wai ya kuke ciki ne haryanzu Bashir ba'a samu daidaito bane? Ni wallahi
gaba daya ma nauyi yasa na kasa tunkarar kowa nayi maganar nan dashi. Jiya mun hadu
da Hajiya Anjin a gidan wata mutuwa haka ta ringa sakar mun habaici mutane na
tayata nidai qarshe kasa zama nayi na taho wallahi gaba daya gari kowa laifin mu
ake gani wai mun aura maka yar uwarmu mun saka ka saki uwar Yayanka haka kawai
bayan ni baka yi shawara dani sanda ka aikata abinka ba.

Dan Allah Bashir ka maida yarinyar nan dakinta dandai kasan bazaka taba maida
kamarta ba, idan ma wani surkullen aka muku na saka anata yi maka sauka da addu'oi
Allah ya karya shi ya daidaita tsakanin ku" Dadata fada cikin jimami.

"Toh Amin ina ta qoqarin haka amma Ma'un yanzu ba irin wadda kika sani ada bace,
gaba daya ta canza kamar wadda aka zuga akaina. Na ina ta addu'a Allah ya shawo mun
kanta"

"Toh Allah ya amince, ai ka gani bana ka ja mana, zanin sallar da ake mana bamu
samu ba Allah dai ya rufa asiri"

Tsabar takaici sallama kawai ya mata ya kashe wayar, ba Addah ce kadai me matsala
ba ita kanta Dadan se a hankali kawai na Addah ne ya fito fili idan ba haka ba ana
maganaryanda za'ayi a daidaita ita damuwarta ma ta zanin sallah da bata samu bane
Toh Allah ya rufa asiri.

Shi duk meyasa da be gane Baba kadai yake son sa da Alkahiri ba shi kadai yake
hango masa illar da rashin Ma'u a tareda shi zata haifar masa duk sauran abin da
suke samu ta dalilin ta kawai shine a gabansu ai shikenan yanzu da ta barsu kowa
seya ji a jikinsa ai daga shi har su kowa ze gane amfaninta da rashin amfanin ta.

Washe gari tun goma yayi wanka ya shirya dukda jirgin qarfe daya zasu bi, sha daya
da rabi ya fito daga dakinsa, gidan shiru dan Amirah sun tafi kasuwaga ko ina kaca
kaca yanda yake tun jiya ko arziqin shara be samu ba daidai da bawon gyadar da taci
jiya yana gurin basu kwashe ba.

Tsaki yaja ya leqa dakin yaran sun tattare komai hatta Bedsheets dinsu da pillow
case sun cire se tsurar katifu akan gadajen na su ya janyo qofar ya fito, bashi a
tabbacin ta fita da muqulli dan haka daya kulle gidan ya nemi wani dan guri ya
ajiye muqullin ya zaro wayarsa ya shiga kiran wayar Amiraj dan ya gaya mata daidai
sanda wata shegiyar Sienna ta shigo layin kai tsaya ta wuce qofar gidan Ma'u ta
faka.

Irin masu baqin kayan nan da yake gani da wannan mutumin ne daya ya fito yaje ya
kwankwasa qofar gidan, yana tsayen dai se gani yayi suna fito da akwatunan su ana
sakawa a mota, a fusace ya qarasa qofar gidan.

Yana zuwa Suna fitowa dan an gama zuba kaya, yaran suka gaishe shi gaba daya be
amsa ba ya matsa kusa da qofa inda yake jiyo sallamar Ma'u da Baba Harira alamar
suna fitowa seya matsa yana sake hade fuska tareda ayyano abinda ze gaya mata idan
ta fito din.

ASMA'U

Da wuri muka gama shiryawa dan kafin goma mun hade komai munyi wanka se dan abinda
baza'a rasa ba. Tun sassafe daman mukayi magana da Yusuf ya gaya mun zuwa sha daya
ze turo wanda ze kai mu Airport dan haka shadaya da mintina ina jin an buga qofa
nasan ya iso, a shirye muke dan haka nace su fara fita da kayan na qarasa sallamar
Baba Harira sannan na kira mata Taxi da zata kaita gida dan Anty bata nan itama
bana a Zamfara tayi Azumi.

Muna fitowa na kalli yaran da sukayi cirko cirko a tsaye bayan gashi nan an bude
musu qofar motar nace

"Me kuke jira kuka tsaya kamar wasu sojojine ku shiga mota in ba so kuke mu makara
ba" fada ina kallon su se a sannan na lura da Bashir daya hade girar sama data
qasa yana gadin qofa, da yar fara'a na kalle shinace

"Aa Baban Ali ina kwana? Ai da baka wahalar da kanka ka fito ba nasan dai kunyi
sallama ai kafin su fito ko??"

"Motar waye wannan zaku shiga" ya fada cikin dakiya kamar me magana da wata yar sa,
ko a jikina, jakata na miqawa Amnah ina Cewa

"Mun tafi se Allah ya dawo damu" na kama qofa zan shige ina sake cewa
"Kwa taho mudai munyi gaba" dan har sannan Aliyu da Abdallah suna qasa su basu
shiga motar ba.

"Magana fa nake miki Ma'u zaki shige mota ki barni, kai dallah ku fito waje"

"Aa to meye matsalarka da sanin motar waye kuma? Ku kuma malamai idan bazaku jeba
ku cire kayan ku tsabar iskanci ana muku magana kun tsaya kuna kallon mutane"

"Yayana bazasu shiga motar ko wanne dan iska ba ku sakko" ya fada a harzuqe yana
janyo Farida datafi kusa dashi.

"Bana son abinda kake mun ka ringa takalata a gaban yara muna abinda be kamata ba,
ka rabu dasu mu tafi koda yake shikenan" na juya ina kallonsu nace

"Ku sauka, malam bude boot za'a cire kaya" na fada cikin hade rai. Baba Harira da
har me Taci dinta ya iso ta saka kayanta ta dawo da sauri tana cewa

"Aa mene haka kuma, Alhaji Bashir ba girman ka bane. Kayi haquri kaga motar ka
qarama ce idanma kace zaka kaisu bazata kwashe ku ba a takure zaku tafi wannan kuma
tana da yalwa sosai ai. Be kamata ku ringa irin wannan abun a gaban yara ba dan
Allah ga mutane duk ana kallon ku"

"Shikenan kinci darajar ta wallahi kuje amma wannan ya zama na qarshe da zaki sake
daukar mun yara a motar wani banza" yaja kwafa ya juya. Ko kallon iskar daya kwashe
shi ban sakeyi ba wayata ma na ciro ina danne danne na.

Ina jin Baba Harira na magana itama naqi kulata suna gama shiga Driver yaja mukayi
gaba abin mu, ta gefen ido na hango yanda yake zabga wa motar harara se nayi tsaki
a fili nace

"Iska na wahalar da me kayan kara".

Mun sauka Gombe lafiya lau, daga gidan mu aka zo daukar mu. A cikin dakunan mu na
yammatanci da yanzu babu kowa guda dayane Yaya Suwaiba da Mijinta ya mutu ta dawo
gida take ciki nan aka gyaramun daya nima na shiga na zauna.

Wani iri na ringaji a zuciyata, ada kai tsaye gidan mijina nake sauka idan munzo se
munkwana mun huta kafin nake zuwa gida mu gaisa amma yanzu wai har daki na samu na
zawarci Allah kenan.
Saboda rashin ganin wata a daren ranar dole washe gari aka tashi da cikon Azumi na
talatin kenan. Har gida aka samo mana me lalle da kitso tazo akayi mana ga yan
sannu da zuwa qannena da yayyena suna ta zuwa abin dariya wai duk wadda tazo barka
take mun na barin gidan Bashir kamar wadda aka sako daga kurkuku a maimakon su
tayani jimami Yah Fati ce kadai ta nuna Alhini da rashin jin dadinta.

Nidai nasan banyi rayuwar qunci a gidan Bashir da har za'a ringa murna haka da
rabuwar mu ba.
A daren aka kawo kayan su Jafar na gurin Yusuf, shadda ce yar ubansu kala biyu daya
doguwa daya me babbar riga ko wanne da hula da takalmi qafa daya harda Agogo se
dogayen riguna Abaya masu kyau na Amnah da Farida.

A daren na kira wayarsa amma a kashe, se na tura masa da saqo kawai nasan in yagani
ko zuwa safiya ze kirani.

Washe gari aka sallace, munje sallar Idi mun dawo gurin qarfe sha biyu na saka
Aliyu ya hada kan qannensa suka tafi gidan su Bashir suka gaishe su, se bayan
Azahar suka dawo tareda Naziru da Yaran Amiru dukkansu da yake suka sunzo sallah
harda Dan gidan Fainusa da alama shima bana an kawo mata shi kenan.

Har cikin gida Naziru ya shigo muka gaisa ina tayi masa tsiyar ko a waya ya dena
nemana yanzu laifin me mukayi masa.

"Wallahi Anty bansan me zan ce Idan na kiraki ba, Yaya Bashir ya bata komai gaba
daya ya saka kunyarki mukeji ko yanzu abinda Yaya Amiru ya gama fada kenan yake
Lagos kwanaki amma ya kasa zuwa ku gaisa dan besan da wanne ido ze kalle ki ba"

"Haba Naziru, dan Bashir ya hada mu se kum ace dalilinsa zamu rabu, ni ban qullaci
kowa a cikin ku ba wallahi in ma banda abinka shi daya aikata muka ci gaba da
gaisawa muna zaune guri daya se ku da bakusan sanda akayi bane zaku ringa ji masa
nauyi ai ba'a haka sedai idan kuma daman neman hanya kuke kaga ae ku yanke alaqa
dani bawai dan abinda ya faru tsakanina da Bashir ba"

"Haba dai Anty alaqa kuma ai yanzu ma muka qullata kin taba ganin da ya sake uwa ai
baze yuwuba, ni yanzu tsoron da nake ma kar ace za'a hanani Yayana ya jawo mun dan
dai nasan baki manta alqawarin mu ba" ya fada yana sosa kai.

Dariya nayi sosai ina cewa
"Oh ni Baba Naziru wai kai dagaske kakeyi me zakayi da wannan kwailar ga manyan
yammata nan a gari? Nida har ina maka kamun wata ma ashe kai kana nan dagaske kake
ashe"

Kallon Amnah data tura baki gaba yayi yace
"Haba Anty wane irin wasa wallahi dagaske nake ni sedai idan kuma baza'abani ba in
cire rai amma duk wani lissafina ai kena kinsani Anty tsokana ta kawai kikeyi"

"Babu wanda ze hanaka Naziru indai yarinya ta amince mu kam yan shan biki ne ko
Amnah" Zainab data shigo ta tsokaneta ai kuwa ta kwasa da sauri ta bar gurin tana
boye fuska.

"Yawwa Anty Zainab inaga qafarki zan kama ki tayani campain tunda naga Anty wasa ta
dauki abun, nida ina can na saki baki wai ina da uwa a bakin murhu ashe ita
sagegeduwa zatayi mun gara da Allah yasa na sani da wuri" Dariya mukayi gaba daya
muka ci gaba da hira shidai jaddadamun yake fa wallahi Yana son Amnah kuma tun tana
yarinya damanya gayamun bashida mata se ita nace toh Allahya tabbatar mana da
Alkahiri.

Seda aka kira La'asar yayi mana sallama bayan ya rabawa yaran barka da sallah dubu
daddaya ina ta masa maganar yayi yawa yayi gana yana cewa

"Bamu samu zama bafa Anty akwai labarai inaga da daddare zan dawo tuna dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login