Showing 9001 words to 12000 words out of 238465 words
bako” Adda Fatu ta fada cike da jin haushin
Dada, se Dadar ta gyara zama tareda cewa
“Ni ba haka nake nufi ba amma gani nayi ai tun farko tare suke a can, yanzu ko cewa
akayi suringa yi idan wannan ta je ta kwana biyu se wannan taje kinga bame yiwuwa
bane tunda Asma’u tana aiki a garin bakuma ze yuwu muce tabar aikin ta ba tunda
idan Amira ce a matsayinta muma bazamu bari a mata ba ko?
Ni dai a nawa ganin Adda ayi haqurin shi yafi a zauna lafiya tunda har komai ya
daidaita tsakaninsu bana son wata rigima ta sake tasowa kindai san sharadin da
Malam ya kafa mun dan Allah bana so ya sake ganin laifina akan lamarin gidan
Bashir”.
Se Adda Fatu ta miqe nan da nan ta fara sababi da fadan maganganu ta inda take
shiga bata nan take fita ba, ga baqin cikin rashin samun biyan buqata a gurin
Bashir gashi da Alamu wannan Karon Nafi na nema ta bata matsala amma ina bazata
sabu ba wallahi dole tasan abinyi. Miqewa tayi still tana masifar ta nifi qofa,
“Wato Nafi kina ganin yanzu kinkai matsayin da zaki qalubalance ni ko? Kin manta
duk halaccin da nayi miki a rayuwa saboda qasa ta dade da cinye Naman Baffa da Inna
dole ki watsar da maganar su tunda kina ganin yanzu kema Kin kawo qarfi. Na gode
zan kuma tafi amma daga yau kisa a ranki baki da sauran wata yar uwa data rage miki
a duniya tunda kin zabi Matar danki akaina da Yata shikenan Nafi na yafewa Duniya
ke” ta qarasa tana rushewa Kukan munafunci wanda dashi take cin galaba akan Nafin.
Ta kuwa samu yanda take so dan nan da nan hankalin Dada ya tashi ta shiga son nuna
mata ita fa ba abinda take nufi ba kenan,
“Idan har da gaske kike kuma kina so na haqura nida kawai kiyi yanda zakiyi Bashir
ya dauki Amira ta koma kusa dashi, kuma baze yuwu yace Ze kwashe su su dukka ya kai
can ba se dai ki saka shi ya dawo da daya ya dauki daya idan kikayi haka shine
kadai Ze sa na haqura in ba haka ba wallahi ki saka a ranki baki da wata Yar uwa
Fatu a raye”
Ita dai Dada son su rabu lafiya ya saka ta amince mata, dole ta hado yan kudaden
hannunta dubu 30 ta bata tace gashi nan ta kaiwa Amirar ta riqe kafin Bashir din
yazo se a san yanda zaayi haka ta rakata har get Addan na sake jadda da mata fa
akan tana nan tana jiran saka mako da haka suka rabu.
Numfashi ta sauke bayan ta dawo cikin palour ta tazauna, gaba daya ta tasa ina zata
kama akan wannan al’amarin. Har ga Allah bata so ta sake yin wani kuskuren akan na
baya amma ya zatayi da Adda Fatu yar uwarta tilo a kaf fadin duniyar nan bata da
kamarta. Addan tayi mata komai a rayuwa ya kamata ace ita ma ta saka mata da abinda
ta mata. A zatonta Auran Bashir da Amira ya isa ga tukuicin kyautatawar amma se
yanzu take dana sanin ma aikata hakan domin kamar ta bude wata qofa ce da Addan ta
mayar da ita tamkar birin wasanta.
Ko da yaushe cikin daga mata hankali take tunda akayi wannan auran da ita dai bata
ga amfaninsa ba in banda bacin rayuka da ya janyo da yawa, shigowar Nazir Autan ta
ya sakata dagowa ta kalle shi
“Yanzu na hadu da fitinanniyar yayar ki a hanya seda tayi mun fashin 10k wallahi,
gaskiya Dada ki ringa yiwa Adda fada abubuwan da takeyi basa dacewa. A yanzun fa ga
kudi a hannunta amma ta tsaya suna fada da Dan Napep dan yace a 200 ze kaita gida”
“Hmm Allah ya rufa asiri kawai Naziru amma ni lamarin Adda ya fara bani tsoro,
yanzu ma fa kaji abinda ya kawo ta” tiryan tiryan ta labarta masa yanda sukayi.
“Wallahi Dada ki kiyayi matar nan, ni dai ina ga Asiri take yi miki ma kike wasu
abubuwan idan ba haka ba dan ta riqe ki ai ba baiwarta bace ke da kuma zata ringa
juya ki yanda taso. Tun farko abinda muka guda a hadin wannan auran kenan amma kika
rufe ido kika ce se anyi zumunchin ku ya qara qarfi ko ai gashi tun ba’aje ko ina
ba kinzo kina dana sani. Shima Yayan banga qaddarar daya gani a jikin wannan mara
mutunchin yarinyar ba daya yarda ya aure ta”
“To Naziru yaya zanyi Adda yar uwata ce da bani da kamar ta ka sani kuma farincikin
Yayanta shine nata idan banyi mata ba a rayuwa ta wa zan yiwa?”
“Ai kuwa gashi nan, kafin da ki sake yanke wani hukuncin se ki tuna cewa Auranki
kema yanzu lilo yake yi a garin faranta mata kuma baza muso ace Uwar mu ta shiga
zawarci a wadan nan shekarun ba” ya fada ya miqewa dan ya fita dan dagaske Bala’in
haushin Adda yake ji har ma da Dadan da yake ganin tana biye mata ne.
“Allah ma baze sa ba Naziru zan lallabata insha Allahu babu abinda ze faru ma” Dada
ta fada itama tana miqewa dan neman abinda zata ci, ko karyawa batayi ba Adda ta
doko mata sammako.
ADDA FATU
Bayan barinta gidan Dada gaba ta qara dan kuwa bazata koma gida yanzu ba dan tuni
Amira ta gaya mata matar tazo karbar kudinta gata nan a tsakar gida tana ta zuba
Rashin mutunchi akan Adda ta fito ta bata kudin ta sunce mata bata nan amma taqi
yarda, gara ta qara gaba ko Allah ze sa ta dace ta samo wani abun koda taimakon da
zesa Bashir ya turo musu kudin ne. Gidan Aminiyarta Haj Balaraba ta wuce, ta sami
Balaraban a qofar gida an kira mata me Napep zata fita unguwa.
“Fatu daga ina da safiyar nan haka” ta fada tana qoqarin rufe gida.
“Ke zan tambaya Balaraba keda nasan se ki kai 12 ma baki tashi ba”
“Hmmm ta ina Kishiya na neman sabautani ina naga ta bacci, kinga yanzu ya akayi dan
ni a tafe nake neman taimako zan tafi” Balaraba ta fada tana jefa muqulli a cikin
jaka.
“Ai kawai muje dan nima matsalar ce ta kawo ni ma tattauna a hanya” nan suka fada
Napep Balaraba ta fada masa inda ze kaisu. Suna tafiya Adda Fatu na jerowa Hajia
Balaraba matsalinta.
“Ni na rasa wane irin shegen yaro ne Bashir wallahi naje gun malaman naje gun Yan
Bori amma an kasa cin galaba akansa, ke har fa nafi ganin aikin kissa idan tayi
masa akan na asirin nan wallahi dama Da Nafi nake samun yanda nake so a gurinsa to
itama naga alamar tana so tayimun Bore. Ga shegiyar me kayan can da kika hadani da
ita bashi kamar na masifa na kasa biyanta”.
“Tab ai seda na gaya miki daman ita fa Indo in kaci bashin ta wallahi toshe maka
hanyoyin samu yake kika ce bakomai shiyasa kika ni kudi hannu muke sabga da ita
gata bata san sabo ba akan dubu daya seta keta miki rigar mutunchi”
“Ai na gani kuwa yanzu haka fa tana can gidan tana ta tijara nidai na ce su Ummi su
kulle qofa kar su bari ta shiga bare ta daukar kun wani abun, kudinta Dubu dari
biyu yai saura da Mun samu kan Bashir zan tattara na biyata mun rabu kenan”.
“To ai shi wannan yaron fa se kin dage masa gaskiya amma bari muje nan gurin, Maman
lurwanu ta kwatantamun tace aikinsa sha yanzu ne dan shi yai mata aiki akan Isah ya
saki Kishiyoyinta dukka biyun rana daya yanzu bakiga yanda take shanawa a cikin
gidan nan ba ita kadai” cewar Balaraba
“Kice Allah, ashe gara da nayo nan Allah yasa qarshen wahalata kenan (ko kuma
farkon wahalar ki ba) in samu ina kafa Amira da kyau sannan in waiwayo kan nawa
qananan kwarin ko da yake ni da zaman su da babu duk daya ai kin sani” haka suka ci
gaba da tattauna wa har suka isa unguwar da aka mata kwatancen sedai ta kasa
ganewa, sunyi tambaya kowa yace be san mutumin da suke nema ba kuma ta kira Number
Maman Lurwanu a kashe.
Kamar Adda zatayi kuka ta kalleta tace “yanzu Balaraba ya zamuyi dan Allah wallahi
na gama saka ran waraka ta zo” kafin ta bata amsa Me Napep da tunda ya dakko su
bece komai ba, tsaf ya gama nade hirar su ta hanyar voice note daya kunna tareda
fahimtar matsalar ko waccen su se ya kashe mashin din yace musu bari ya kama ruwa
kafin su gama yanke shawara.
Can Nesa dasu yaje ya zaro wayarsa ya shiga kiran abokinsa aransa yana ayyana Banza
ta fadi daga can bangaren aka daga wayar ana cewa “ungulu baka jewar banza da alama
ta samu”
Dariya yayi kafin yace “yi maza ka shirya area, ka duba whatsapp na tura maka saqo
nan da minti Ashirin zan qaraso idan ta saitu”
Dayan ya bushe da dariya yace”an gama kwaro kamar kasan wallahi dama ina ta
lissafin ta inda zam samu kudin yiwa Latifa Anko gashi ta matsamin kwana biyu babu
kasuwa, Allah dai yasa ta waru, se kun qara so toh” sukayi sallama.
Gurinsu ya dawo harda karbar pure water a wani shago ya fasa ya zubda rabi ya taho
yana wanke hannunsa,
“To hajia ina muka nufa yanzu” ya tambaye su bayan ya kunna Mashin.
“Maidamu inda ka dakko mu kawai” Balaraba da abun duniya ya ishe ta ta fada, se ya
cilla suka dau hanya yana jin yanda suke ta jimami. Daidai wani gidan mai ya tsaya
ya sha, seda ya dan bata lokaci sannan suka ci gaba ya gama shirya abinda ze gaya
musu se yayi gyaran murya.
“Am nace Hajia kuyi haquri fa dukda ban gane kan damuwar taku ba amma idan kuna so
akwai wani guri da wancan satin nakai wasu passengers, can na jirasu suka gama
gaskiya daga yanda naji sun fito nasan sun samu biyan buqatar data kai su, kun gama
saqon daya daga cikin su daga Kano tazo ashe suka karbi Number dazu naje na karbo
zan saka mata ta tasha akai mata” ya fada yana bude dan gurin da suke zuba kudi ya
zaro baqar leda, basu san mene ne a ciki ba gadai shi harda suna da Number waya an
rubuta ta wanda zaa turawa saqon. To wanda kwakwalwar sa ta toshe ai se a hankali
ba tareda tunanin komai ba suka ce ya kai su, a ransa ya ayyana “Madallah” ya cilla
kan mashin suka dau hanya dan yasan zuwa yanzu an kimtsa komai dukda haka seda ya
sake yi masa text ya tabbatar masa komai is ready su taho.
Tafiyar yan mintina takai su layin gidan har qofar gidan me dauke da shago se kuma
soro na shiga cikin gidan. Wasu yan samari biyu ya gani daga gefe kan dakali yai
musu sallama tareda tambayar su ko Malam yana nan
“Ai kuwa ya fita amma nasan ba dadewa zeyi ba qilan ma yana hanya.. au ka ganshi ma
muna maganar” daya daga ciki ya bashi amsa. Se ya nufi gurin Wizy abokinsa daya sha
uwar babbar riga harda wani rawanin iskanci shi a dole ga malami ya miqa masa hannu
suka kashe amma se ka zata musa baha sukayi. Cikin daga murya Yanda su Adda zasu
jiyo su Wizy yace “Mal Kamar kaine ka karbi saqon hajia Larai dazu ko lafiya dai ko
mantuwa kayi”
“Eh wallahi Malam nine ba mantuwa nayi ba wasu iyayen daki na na rako ne”
“Ah to to bismillah ku shigo ka barsu anan kuma kai Iliya me yasa baku bude musu
shago sun shiga ba ko ka kaisu cikin gida gurin Maimuna kan nazo” ya fada yana
hararar samarin da suke zaune. Seda Iliya yayi dagaske gurin riqe dariyar sa kafin
yace “Malam ai ta fita gidan suna itama kuma ka tafi da muqullin shagon ai”
“Anyi haka ya fada yana bude musu kofar suka shiga gaba daya, bayan sun zauna Me
Napep yace bari yaje daga waje idan sun gama shima se yazo a bashi taimakon kasuwa.
Malam ya jawo faranti me dauke da yashi ga kuma carbi me dubu ya hau ja yana muimui
da baki nan kuma yana faman zane zane sannan ya dago ya kalle su “toh hajia dawa
Zamu fara?” Ya tambaye su.
Hajia Balaraba ce ta fara matsawa tace “Malam ni matsalar kaina ce a fara dani
dama..” se ya dakatar da ita, “ki bari mu duba abunda bamu fahimtaba se kiyi mana
bayani da kuma matakin da kike so a dauka.
Tiryan tiryan ya ringa jera mata zance kamar me gani a film kai har abinda basu
fada Me Napep yaji ba seda Wizy ya canka ya fada se kuwa tace kai Malam aikuwa
hakane wallahi, yana ta tiqar dariya a qasan ransa to ai labarin duk daya ne dukma
wadda tazo indai akan kishiya ne banbancin basu da yawa. Seda ya gama ratta ba mata
zance Adda da me gefe ta gama yin Ammana sun zo inda zaa magance musu matsalar su
harta gama Ayyano Yanda zasu juya Bashir kaman Tanda a waina.
Tsaf Hajia Balaraba ta gama gaya masa yanda take so ayi nan kuwa ya yanka mata 50k
babu neman ragi ba komai ta cake masa su to taji sauqi akan ubannin kudin data ke
kashewa babu biyan buqata. Allonsa ya jawo da tawada ya hau rubuta abunda in zaka
kashe shi be san menene ba ya gama ya miqa mata da kwano da ruwa yace ta wanke idan
taje gida ta guntsi rabi ta fesa a kofar dakin kishiyar ko inda tasan zata taka
rabin kuma ta kuskure baki ta zuba a miya kowa na gidan yaci to daga nan babu me
jin maganar wani se tata.
Wasu qullin Jan Maganin da kore ya sake dakkowa ya bata su kuma yace ta ringa
jiqawa kwana 7 tana sha sannan ya qara mata da wani kuma a jarkoki guda biyu yace
ta juye a bokiti ta qara musu ruwa ta ringa sha shima mijin ta san yanda zaayi
yasha koda tea ne ta dafa masa dashi sauran aiki kuma karta damu zeyi daga nan
shidai idan buqata ta biya kar a manta dashi (kuji dan banza 😂😂Koren Magani na
sabara da Jan magani yake ba wa duk wadda tazo se na cikin jarka kuma maganin Basir
ne ko banza ai ya temake so ko 😂😂😂😂😂😂).
Adda ce ta matso aka buga mata nata duban se ya kalleta “Wace Mace ce haka gata nan
dai Fara kyakykyawa kamar ma bata da lafiya tana gadon Asibiti”
Ai caraf ta amshe “Asma’u ce ita ce kishiyar yar tawa” gyara zama yayi yana ayyano
yanda ze tatsi matan nan yace
“Kamar a kudu take fa wannan kai” se yai shiru kafin ya ci gaba
“Tab di hajia akwai babban aiki a gabanki fa dan koma wacece wannan tasha kan shi
wannan mutumin sosai dan kuwa Arnan kan dutse ne suke mata aiki an hada shi da
gungun Aljanu suna gadinsa gaskiya wannan aiki yafi qarfina”
“Ai Adda kamar zata rushe da kuka tace “haba Malam ba abinda ya fi karfinka ai
(haba Adda Allah ne kadai keda maganin komai) ka duba ka taimakamun nidai a
tarkato mana hankalinsa ai ko baya auran yata ni me tsayawa na nema masa taimako ce
tunda dana ne ai dan yar uwata”.
Zama ya gyara yace “abinda kamar wuya gaskiya kin san aiki da kafiran Aljanu akwai
wahala amma in zaki saki kudi ayi musu yanka kinsan su jini suke so to wala Allah a
dace”
“Malam indai zaa samu biyan buqata ba matsaka yanzu kamar me zaa yanka?”
“Gaskiya hajia a qalla za’a yanka musu raguna 20” seta dafe qirji tace Malam ina
zan samu kudin nan yanzu fa nake maka bayanin na biyan bashi ma nake nema ni a fara
rufemun bakin matar nan ma tukunna ta manta da zancen kudin”.
“Wannan duk ba matsala bane kuma zaki iya ringa bayarwa a hankali ai in kin so ma
kiringa yankan da kanki amma akwai kalar dabbobin da ake so da kuma abinda ake fada
in za’ayi yankan in kina da wanda ze miki duk sena gaya miki ai”
“Aa malam zaa mata komai anan” Hajia Balaraba ta fada
“To ba matsala”
“Kamar nawa kenan Malam” ta tambaya
“To akwai qauyen dana ke siyo dabbobi ana samun qosashshen rago dai daga dubu
Arba’in kinga a qalla guda koma dubu Dari hudu kenan amma zaki iya ringayi a sannu
in so samu ne dai cikin wata biyu a kammala aikin”.
Nan dai Adda ta zazzage masa dubu tamanin kudin data harhada zata rage biyan bashi
tace in an kwana biyu zata kawo abinda ya samu, ita be bata komai ba se wani abu
kamar goro yace idan matar tazo ta saka a bakinta ta ringa taunaqmwa tana mata
magana kamar remote haka zata controlling nata aikin Bashir kuma Wannan Ze duqufa
yai tayi itama Amira jin tana da ciki ya nemo wani garin Maganin zaqi dana sanyi da
aka aike shi ya kaiwa Yayar sa da take da ciki ya bata yace ta kai mata tayi tasha
zuwa sanda Bashir zezo daya kwanta da ita anci rabin aiki.
Kamar wanda yai musu kyauta suka ringa zabga godiya ya basu Number wayar sa suka
fito Me Napep har ya gaji bacci ya dauke shi fitowarsu ta farkar dashi,
“Gaskiya kun dade hajia yau balance kawai zaku bani na maida Machine din nan na
huta dan har na gama gajia” ya kunna suna shirin tafiya har sun ja Iliya ya
tsaidasu akan Malam yace ya manta da taimakon kasuwar ne, se suka koma ya barsu a
cikin mashin ya shiga.
Be zauna ba 40% 60% suke raba duk abinda suka samu Wizy se dauki 50% ragowar 10 ya
bawa su iliya da sauran masu yi musu cover a harkar, cas ya cake masa kudin sa
tareda bashi wata qatuwar takadda da aka nade kamar laya yace zasuyi waya ya fito,
ransa fes suka kama hanya bayan ya saqala Takaddar a gaban mashin wai ta kiran
customers 😂😂 ikon Allah kuwa duk inda suka gifta se an tsaidashi yace drop ne har
ya ajiye Hajia Balaraba ya wuce Da Adda Fatu dan tace gara taje ta kai mata ta fara
sha tunda yau Alhamis a qa’ida gobe Juma’a ze zo
To se muce Allah kauda tsautsayi da Asara 😂😂😂😂
https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 6
Da Isar Adda gida bata ko zauna ba ta jiqawa Amirah maganin da aka bata tace gashi
nan tayi tasha Zuwa goben sega yanda za’ayi.
“Adda kin ganin ze zo ne ko kin manta yanda mukayi dashi jiya da daddare” Amirah ta
fada cikin sanyin jiki.
“Ke dallacan barshi ai idan be zo bama baze samu nutsuwa ba saboda sabon malamin
nan da muka samu da zafin sa in gaya miki kedai kakarmu ta kusa yanke saqa, ai da
lamarin ki sun gama daidaita zan juya kan wannan me baqin jinin itama ai taimaka a
samo mata wani zaman ya isa haka” ta fada tana Kallon Ummi. Se Ummi tai zarab ta
miqe tana cewa
“Wa ni wallahi na yafe dadai irin Auran Amira kullum kina tafe ba biyan buqata gara
in zauna banyi ba duk