Showing 75001 words to 78000 words out of 238465 words

Chapter 26 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

kuwa ji yanda kake cin abinci?”

“Bazaka gane ba, rabo na da abinci tun shekaran jiya”.

Dakyar ya iya kaiwa qarshen meeting din, suna gamawa suka fita sallar Juma’a. Bayan
sun dawo Office din sa ya koma ya kwanta ya ringa bacci ba shi ya farka ba se qarfe
bakwai shima Security da suke bi office office ne bayan an tashi suka ga fitilar sa
a kunne dan haka sukaje su duba ko lafiya tunda be saba kaiwa dare a gurin ba.
Haka ya tattara a gida ya wuce gida, da murnar sa ya shiga dan tun daga waje ya
jiyo qanshin tuwo da miyar kuka harda man shanu abinka da me jin yunwa.

Ya bude qofar ya shiga, fuska a sake Ma’u tayi masa sannu da zuwa harda tambayar ya
akayi yau ya dade yace bacci ne ya kwashe shi.

Da zumudinsa yai sallar magriba da Isha ya sako jallabiyya ya dawo palour aka kame
akan kujera yana jira ayi masa tayij abinci ya kwashi gara amma har kusan minti
goma da zaman sa yaji shiru sema harkar gaban su kawai suke.

Gyaran murya yayi yana kallon Ma’u dake dannan waya yace “Akwai abinci ne yunwa
nake ji”

Seta dakata ta dago ta kalleshi da murmushi tace “ai kuwa babu dan ban san zaka
dawo ba”.

“Kamar ya baki san zan dawo ba ce miki nayi zan tafi wani gurin ko yaya, sannan
nida gida na ayi abinci ace baza’a a jiye mun ba saboda me? Haka fa dazu da safe
kika ce mun akwai abinci na duba ko ruwan zafi baku ajiye ba” ya fada a hasale, dan
ya rigada ya gama saka rai da Tuwon.

“Ko ajikina na sake gyara zama nace “Aa abin bana zafi bane bafa Baban Ali, gani
nayi yanzu ai Idan zakayi tafiya baka fada seka isa inda zakaje toh gudun kar mu
ringa asarar abincin yasa mukeyi dai dai cikin mu, idan kace zaka ci se a dafa
dakai”.



Abubuwa sun sha kaina, idan na samu sarari zaku jini gobe idan kuma ban samu dama
ba se Monday In Sha Allah 🙏🙏🙏

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 28


Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na
safe. Ko yaya Bashir ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya
fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a
dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta.

Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga
dakin nake jiyo kaya kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude
qofata Yan biyu na suka taso da gudu suka riqe ni.
“Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne” na fada ina kama hannayensu, se
Ahmad yace “Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya
masa Irish”.

Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara
kamar idonsa ze fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na
wayance ina nufar inda yake nace “Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka
tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu qoshi ba se a qaro wani”
nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna.

Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar
sake qular dashi nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa
nace

“Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?”
Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace “Banci abinci da daddare ba
jiya da yunwa na tashi”.

Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar
dan kwallo, cikin jimamai nace “Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko
Spaghetti ce ta dafa maka ai”.

Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani
gamawa, seya miqe ya shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan
na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa ya dauka, be mun magana ba ya fice yara
suna masa a dawo lafiya.

Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa “zan
fita amma ba jimawa zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch”.

“Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma
yanzu tunda munsan kana nan ai zamu girka da kai” na fada ina dan murmushi. A raina
nace “da bakayi magana ba wallahi yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin
yunwa.

Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya
cin Tarwada shi se gasashshiya.

Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace “Mami idan mun gama muje gidan Baba?”

“Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa”.

Bashir ne yace “Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza
mu fita ba sedai ko gobe”.

Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu
Ahmad, Aliyu da sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya
rage daga ni se Bashir.

Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin
da yayi bani da niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a
Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk yanda naso nayi tawaye a dole fushi
nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima nayi kewar sa nan da
nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir.

Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana
waya, ta cikin mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya
sakar mun kafin ya qaraso ta bayana yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be
jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya karbi Dryer yana cewa “Dama baki
wahalar da kanki ba dan ba’a gama ba”

“Wasa kenan” na fada ina zaro ido, saman da yai dani yasa sauran maganar suka
maqale ban samu kaina a hannun sa ba seda aka kira Magriba.

Ranar haka mukayi kwanan farin ciki duk fushin nan seda Bashir ya bi ya kore mun
shi. Se wani nan nan yake dani ranar ba’ayi wata doguwar hira ba kowa ya tafi ya
kwanta. Muna kwance a dakin sa nayi pillow da dantsen hannunsa yace

“Dan Allah Ma’u karki sake horani da yunwa kinji”
Dariya na sheqe kafin nace “wannan din ma bada gayya nayi ba, aka si kawai aka
samu”.

Lafiya qalau muka cinye Weekend din mu ranar Monday Amnah suka fara WAEC, da yake
practical suka farayi sha biyu zasu fito dan haka nace mata ta taho gida kawai idan
ta gama sauran idan sun tashi Zan dakko su yanda muka saba.

Dawowar da Amnah takeyi da wuri ya sake ragemun abubuwa da yawa dan kafin mu dawo
ta ci qarfin girki wani lokacin ma zata dafa musu nasu idan nazo sedai nayi wa
Bashir kawai. ne da wuri.

Har aka ci sati uku banji Bashir yayi zancen zuwa Gombe ba kuma da alama ko waya
basayi da Amirah ban dai sani ba ko a cikin gidan ne bayayi se ya fita waje yake
kiranta.

Ranar wata Alhamis daya kama Sati hudu da dawowarsa da daddare muna kwance Text ya
shigo wayarsa, Number Amirah ce dan da sunanta yayi saving, na fishi kusa da ita
dan haka na miqa masa yana daga kwance se naga ya tashi zaune.

Kamar wani mara gaskiya ya kalli wayar ya kalleni muka hada ido sena basar na gyara
kwanciyata daidai sanda wayar ta shiga qara alamar kira se ya tashi daga kan Gadon
ya fita waje.

Tashi nayi nima na zauna, Kusan Awa daya yana wayar sa har sannan kuma bacci yaqi
daukata, bawai na damu bane da kiran Aa harga Allah ina tsoron abinda ze iya zuwa
ne kuma dan a duk sanda muke zaman lafiya kamar tauraruwa me wutsiya yarinyar nan
seta wargazashi.

yana bude qofa nayi luf kamar me bacci, ina jinsa ya tsaya akaina yana haskani da
wayar dan fitilar dakin a kashe take kafin ya zagaya ya kwanta shima.

Da Asuba yake ce mun daga Office Gombe ze wuce.
“Ai ka kwana biyu daman baka je ba, ka gaishe mana su idan zaka dawo Dan Allah zata
taho mun da saqo a gurin Maman Ayman (Bilkisu) saura kace ka manta” na fada ba
tareda damuwar komai ba.

Ni na hada masa dan abinda ze tafi dashi dan baya daukar kaya muka rabu salin Alin
kowa ya tafi aikinsa, sanda jirginsu ze tashi ma seda ya kirani ya gayamun yanzu
zasu tafi nayi masa fatan sauka lafiya mukayi sallama.

Gombe
A ranar da Bashir ya tafi itama ta koma gidan Addah cikin dacin rai. Naziru ne ya
kaita bisa umarnin Dada, suna zuwa suka ci karo da Addah a qofar gida da alama fita
zatayi.

“Yawwa shiga da kayan ki fito muje” Addah ta fada tana kallon Amirah, seta wuce
ciki ta ajiye jakarta ta fito, Nazirun ne ya rage musu hanya har zuwa gidan wata
tsohuwar qawar Addan da tace wai mijin matar ne ya rasu zata je mata gaisuwa.
Suna shiga basu zauna ba dan a shirye suka sameta itama tace su tafi. Amirah dai
ranta fal mamaki toh ina zasuje haka dai ta bisu su ka hau Napep ya kaisu Tasha
suka hau motar Dukku.

Bayan sun isa can ma ashe ba iya tafiyar kenan ba, Babura suka hau daga tasha suka
dauki hanyar wani surququn Jeji kafin su isa kuwa jikin su ya gaya musu da iska
gashi lokacin sanyi da Hazo musamman Amira dan daman doguwar rigar Abaya ce a
jikinta tayi rolling da mayafin rigar har wani kadawa taji haqoranta nayi tsabar
sanyi.

A wani dan qauye suka sauka da gaba daya bukkokin garin basufi shida ba, Masu
Baburan suka tsayar kafin Hajia Maliya tayi musu jagora zuwa bukkar data fi kowacce
girma. Sanda suka shiga ciki seda Amirah ta dawo da baya da son tabbatar da daidai
take gani ko kuwa gizo idonta yake yi mata.

Wato daga waje bukkace ta kara irin ta fulani amma abin mamaki idan ka shiga tamkar
ka shiga dakin wani hanshaqin me kudi. Ciki da palour ce, palour Gaba daya a malale
yake da Carfet Ja me shegen laushi har wani lumewa qafarsu take a ciki ga kujeru
royal an zagaye gurin dasu, yanda gurin yai dumi ya tabbatar mata harda Room heater
aka kunna.

Zama sukayi ita da Addah se qarewa gurin kallo suke, Hajia Maliya kuwa da alama ta
saba zuwa babu mamaki a fuskarta. Zubgurar ta Addah tayi tana cewa “Maliya ina kika
kawo mu karfa muje gurin yankan kai ne”.

Dariya Hajia Maliya tayi tace “ke fa Fatu shegen tsoro ne dake” daidai nan wani dan
fari dogo siririn Bafulatani ya bude qofar uwar dakin ya fito.

“Aa Hajia kune ashe tun dazu nake tsammanin zuwanku naji shiru saura kadan ma muyi
sabani” ya fada yana zama a qasa inda aka qara shimfida wata darduma ga tarkacen
kayan aikinsa akai.

“Mune fa Malam kasan tafiyar mutane da yawa basu shiryo da wuri bane” Hajia Maliya
ta fada. Gaisawa sukayi yana tambayar ta bayan rabuwa nan suka dan taba hirar aikin
da yayi mata da irin yanda taji dadinsa su Addah dai anyi tsuru.

“Wannan itace Fatu yar uwata da nayi maka baya ni wannan kuma Yarinyar tace Amirah”
Hajia Maliya ta gabatar masa dasu Addah, seya gyara zama yana cewa toh toh
bismillan a gurguje dan sauri nakeyi zan shiga garin ne nima zanje gidan Gomna.

Matsawa Addah tayi gabansa tace “Allah gafarta yanzu dai matsalar wannan yarinyar
itace a gabana dan tawa me sauqi ce”

“Ki fadi taki kawai Hajia itama ai tana da baki zata fadi tata ko” malamin ya
katseta. Se Addah ta gyara zama tace

“Malam abubuwan da yawa gaskiya amma kadan daga ciki dai kaga Kishiyoyina uku nice
ta fari. Da gaba daya gidan a hannuna yake daga Alhajin har su matan ni nake juya
su ko kara na ajiye wa mutumin nan be isa ya tsallake ba amma yanzu Malam karka so
kaga yanda yake mun wulaqanci a gaban kowa ci mun mutunchi yakeyi yanzu duk
kishiyoyi sun rainani,

gashi yayan su duk sunyi aure sun samu gidan hutu ni kuma biyu ne dani fa kacal na
samu daya ta daga to gidan me mata ta fada dayar kuma yanda kasan wadda aka watsawa
jinin baqar jaka ko tsayayyen an gagara samu se tarin matsiyata dake sintirin zuwa
gurinta”.

“Ya sunan me gidan naki da kishiyoyin?” ya tambayeta se tayi sauri tace
“Alhaji Murtala, su kuma matsiyatan akwai Binta da Nasiba se Memuna”.
Shiru malam yayi yana ta jan carbinsa daya shafe da turare Addah se zura ido take
yana kallon bakinsa da yake motsi kamar tasan abinda yakeyi, minti biyu ya dago
yana kallonta yace

“Se haquri dai Hajia banajin wani aikin ki ze sake tasiri akan Mijin nan naki dan
yanzu ya farka shima a tsaye yake da Addu’a da neman tsari, kishiyoyi kuma ai ke
kike shiga harkar su kuma ni cikinsu banga wata da take jifanki ko wani abu ba”.

Raurau tayi kamar yarinya tace “yanzu malam babu yanda za’ayi wallahi yanzu ko dan
abinda nake samu a hannun Alhaji ya dena, kwanan nan da rigima ta hadani da wata
mata akan kudi, gida na da na saka yan haya ya siye ya biyata kudin ni da so nake
inda yanda za’ayi ma a dawo mun da gidan”.

Dariya malam yayi yace “Hajia sama da shekara Arba’in fa kina yanda kika ga dama da
bawan Allahn nan yanzu kuma Allah ya taimake shi ya kwace shi daga hannunki ki
qyale shi mana.

Ki godewa Allah ma daya ci gaba da zama dake dan yana sonki idan da zaki ajiye
komai ki bishi zakiji dadin zama dashi sosai Allah na tuba kwana nawa ya rage muku
gaba daya ma da kike tashin hankalinki? Gida kuma inda rabonki idan ya mutu se ki
samu wanda ya fishi. Bismillah matso ke” ya qarasa maganar yana nuna Amirah.

Addah zata sake magana Hajia Maliya ta riqe mata hannu tana girgiza mata kai, se
tayi shiru kawai ranta gaba daya a dagule. Wannan wane irin abu ne? Yanda Maliyan
ta zuzuta mata shi ta zata da tazo buqatarta ta gama biya amma tazo se wasu
maganganu marasa kai aka gaya mata.

Jiki a sanyaye Amirah ta matsa gabansa, ya dago ya kalleta yana murmushi yace Hajia
ya akayi?”

“Ni malam bani da wata matsala kawai so nake ya ringa so na yanda yake son matar
sa”
“Kunji Asararriya ba” Addah ta katseta kamar zata kai mata duka kafin taci gaba da
cewa
“Shiyasa nace ka barni nayi maka bayani malam dan wannan sallamammiya ce bata san
ciwon kanta ba”.

Seda Malam yayi dariya sannan yace “toh Hajia ina jinki”. Gyara zama Addah tayi ta
shiga koro bayani

“Kanaji malam, shi mijin nata Bashir Dan yar uwata ne. Da dabara muka samu har ya
fara sonta ya aure ta. Toh munyi haka dan zumunchi sannan kuma ko ba komai dan na
samu me taimakamun tunda ni kaga bani da Da namiji toh Amma yana da Mata.

Ita Matar Asma’u sunanta ta riga tasha kansa gaba daya abinda ya mallaka akanta
yake qararwa daga ita se yayanta, shekara biyu da auran nan amma ba uwar daya
tsinana mana se rashin mutunchi salo salo daga wannan se wannan kuma ita matar tasa
na can kusa dashi a Lagos ita kuma wannan ya barmun ita anan se sanda yaga dama
yake leqo ta nayi nayi ya maida ita can amma abin yaci tura”.

“Toh ita matar shekarar su nawa a tare kuma yayan su nawa” Malam ya tambayi Addah
yana murmushi dan matar dariya ma take Bashi, se Addah ta karkace tace

“Inaga ta sha bakwai suke yanzu, haihuwar ta biyar harda tagwaye da anyi magana se
ace ai ita tare suka sha talauci”. Seda Malam yayi dariyar qarfin halin Addah kafin
yaja qasarsa ya baza yana cewa

“Toh yanzu Hajia in banda qin Allah irin naki ta yaya kike so ya fifita matar daya
aura shekara biyu akan wadda suka shafe shekara goma sha bakwai tare Ai koda
Arziqinsa ya aure su dukka su biyun bazaki taba hada shaquwar shekaru goma sha data
kwananna ba sannan ga zuri’a har shida a tsakani”.

“Toh nidai malam ko ma menene dai ina so Amirah ta zama mowa a gidan sannan ya
ringa sakar mata hannu yana mana bushasha idan so samu ne ma ni banqi Ma’u tabar
gidan ba dan indai tana nan be zama kallai mu samu yanda muke so ba”. Addah ta fada
tana hura hanci, se Malam ya dago ya kalle ta yace

“Hajia ribar musulmi ya mutu ya shiga Aljanna ni bana kashe aure sedai na qulla
qilan Hajia bata gaya miki ba kinganni nan bana aiki in cutar da wani sedai nayi
maka kai ka samu mafita sauran zunubai na ma sun ishe ni bazanyi dakon haqqi ba”.

Seda ya gama irga carbinsa kafin ya mayar da hankalin sa kan Amirah yace

“Ita uwar gidan naki ma tana dab da fita, sannan mijinki duk kalar asirin da zakiyi
masa tasirinsa qalilan ne akan sa baze dade ba ze karye. Ko ita da kuke ganin ta
mallakeshi bada Asiri bane kawai ta iya zama dashi ne amma bawai dan tana jin dadi
yanda kuke zato ba.

Shawarar da zan baki itace kije ki gyara kanki ki gyara zaman ki kawai shi me son
kyalekyale ne tun farko abinda ya ribace shi harya aure ki kenan kuma itama matar
sa da abinda take galaba akan sa kenan amma batun ya so ki sama da ita babu shi,
dan ko mutuwa tayi ba na jin akwai wadda zata iya maye masa gurbin son da yake yi
mata”.

“Toh malam na gode, se kuma matsalata malam haihuwa biyu kenan nayi ta farkon bezo
da raina ba ta biyun kuma sati uku da haihuwar ta koma daman bakwaini ce” Amirah ta
fada a sanyaye,

“Wannan Kuma daga Allah ne itama mahaifiyarki ai haka tayi ko, randa yaso se ya
baki rayayyen” ya fada yana miqewa.

Kamar anyiwa Addah Bushara da aljanna baki har kunne tace “Malam kace zata fita
yaushe kenan amma bazata dawo ba ko?”

Banza yayi mata ya shiga dakin daya fito minti kadan ya dawo da daurin wata saiwa
da kuma garin magani a leda ya miqawa Amirah yace “ki tafasa ki ringa sha ze gyara
miki jiki wannan kumburin ya sabe tunda bakiyi wanka ba wannan kuma kisha da madara
ko Kunu Allah ya qara rufa asiri amma a shawarce dai da kin nutsu dan kalar mijinki
ko kinyi asiri idan baki san yanda zaki tafiyar dashi ba wahalar banza zakiyi”.

Godiya tayi masa ta miqe, Addah ta kalleta tace ina zaki je kuma?”

“Shikenan ai ko Hajia na sallame ku koda wata magana” ya fada yana kallon Hajia
Maliya se Addah tayi caraftace “malam baka ce komai akan daya yar uwar tata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login