Showing 156001 words to 159000 words out of 238465 words

Chapter 53 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

da hankali dan
haka ya yanke shawarar ya nemi guri ya tsaya daga farkon Layin ta yanda zega duk
motar da zata shigo ciki dan idan ya koma qofar gidan sa waccen jarababbiyar
yarinyar seta dagula masa lissafi har Ma'un ma ta wuce be sani ba.

Yana zaune a gurin kusan Awa guda motar Yusuf ta danno kai, plate number motar da
aka saka WUNTI 2 yabi da kallo ya tabbatar bata cikin Estate dinsu bace sedai idan
wasu ne sukayi baqi, seda suka matso kusa dashi ya hango Ma'u zaune a gaban motar
yanda suka saje ita da Yusuf din seka rantse da Allah wasu Mata da Miji ne sabon
aure sukayi anko zasu je unguwa ga wani kallo me nuna so da yaga Yusuf din yana
yiwa Ma'u ita kuma ta sunkuyar dakai tana murmushi.

Wani Yum yum yaji akansa lokaci daya kamar an tsikara masa abu a qirjinsa har seda
ya dafe saitin zuciyarsa yana sakin numfashi ajere a jere, ya tabbatar idan ya miqe
a sannan to kuwa seya fadi idan beyi wasa ba ya hadu da paralyze abinda ya dakatar
dashi kenan ya zauna yana kokawa da nutsuwarsa, gashi ya kasa dena kallon motar har
ta tsaya mutanen ciki suka fito dukka banda Ma'u abinda ya qara masa hauhawar jini
kenan haka ya dafa motar ya sauko yana jin jiri na kwasar sa amma ya daure.

Seda ya kwashi kusan minti biyar a tsaya kafin ya iya daga qafarsa ya fara tafiya
yana rangaji, duk takun da yake kusanta shi da motar ji yakeyi kamar anan suka masa
wuqa a maqoshi idan ya tuna Ma'u ce a ciki tareda wani qato da besan me yake gaya
mata ba.

Ji ya ringayi kamar ya debi duwatsu tundaga nesan ya yita rotsawa gilasan motar har
se sun rugurguje amma baze yuwu ba dan yasan irin su ba qaramin duka zasuji ba ace
sun balle haka ya qarasa Gurin zuciyarsa kamar zata fashe ya kai hannu ze kwankwasa
Ma'u ta bude qofar gabansa ya yanke ya fadi ganin irin yanayin data fito, yanayine
irin wanda take shiga lokacin da take cikin maye da shauqin soyayya.

Bude baki yayi ze mata magana ta rabe shi ta wuce gaba daya se hankalin sa ya kasu
biyu, ita ze bi ko kuma tsayawa zeyi ya fara cin uban wannan me bibiyar masa matar
tukunna?
Maganar da Yusuf yayi ce tasa ya wai waya ya kalle shi

"Yallabai barka da rana ashe gaba kayi dazu bamu samu mun gaisa ba ya aiki ya su
Madam?? Yusuf ya fada yana miqo masa hannu fuskar dauke da wani shegen murmushi.

Kallon hannun da yake bashi yayi ya sake kallon fuskarsa, 'qut' ya hadiye yawu
kafin ya bude baki dakyar yana nuna Yusuf yace

"Ka fita daga sabgar matata, idan ba haka ba sena koya maka hankali ta yanda ko
kallon matar wani bazaka sakeyi ba bare har magana ta hada ka da ita".

Ko a jikin Yusuf se ya janye hannunsa da Bashir yaqi karba yana murmushi yace
"Yallabai ni kuma meya hadani da matarka nida ban ma san tare kuke ba seda zaku
tafi na hango ku zaku shiga mota, ai ni ko kalar fuskar ta bansani ba bare wata
mu'amula ta hadani da ita".

Wani banzan kallo Bashir ya watsa masa kafin a harzuqe yace
"Karka raina mun hankali, ni kake cewa baka san matata ba, to bari kaji wallahi ko
a hanya na sake ganin ka kalli Ma'u se nayi qararka na bata maka career badai
taqamarka siyasa ba?
To sena gayawa duniya cewa kai Manemin matan aure ne idan yaso se naga ta yanda
zaka tsira da mutunchinka".

Dariya sosai Yusuf yayi harda dukan sutiyari kafin ya kalli Bashir daya shaqa iya
wuce ya nuna shi yace
"Oh wai akan Asmy kake magana daman ai cemin zakayi tsohuwar matarka se nafi
ganewa.

Toh tunda anyi haka yanzu bari nayi amfani da wannan damar nayi maka jajen wautar
daka tafka ka rabu da Mace kamar Asmy bayan ka manta akwai irin mu a waje da duk
sallah biyar ta duniya da zamuyi a rana se mun roqi Allah ya bamu mace kamarta.

Nagode maka kwarai daka sako min ita a daidai lokacin da nake tsananin buqatar ta,
na kuma yi maka alqawarin zan riqe Asma'u na bata kulawa da soyayyar daka gaza
bata, kai amma ka tafka Asara yallabai se in ce maka Allah ya mayar da Alkahiri ko
da yake naga ka samo wata me fada akan Abinci a gurin taro ko?

Irin matan nan in gaya maka ba'a zuwa gurin kunya dasu dan se sun zubar maka da
mutunchi a ringa kallonka kamar baka yi musu komai Alhalin tsabar rashin godiyar
Allah ne kawai. Kayi haquri fa amma dai dole in gaya maka kayi wauta Allah dai ya
mayar da Alkahiri" yana gama fada ya dage gilashin motarsa yayi gaba yana cigaba da
yiwa Bashir dariya.

Bashir kuwa tsabar yanda ya tafi wata duniya na wucin gadi besan sanda Yusuf ya bar
gurin ba se qugin motarsa yaji. Ya juya ya kalli motar ya waiwaya ya kalli Gidan
Ma'u wai ma takamaimai laifin wa ze gani anan.

Yanzu har Ma'u ta bawa wani dama ya maye gurbinsa a rayuwarta Innalillahi wa'inna
ilaihi raji'un.

YUSUF
Wato rai fes sunan wata Atamfa haka ya ringa tuqinsa yana murmushi shi kadai idan
ya tuna yana yin fuskar Bashir sanda yake gaya masa magana.

Tun ranar daya hadu da Ma'u da daddare yana sauketa ya kira Alhaji Tukur ya gaya
masa yau ya hadu da Ma'u babu bata lokaci kuma ya sanar masa da zancen mutuwar
Wanda yayi bala'in yi masa dadi ya kuma jin jinawa wauta da hauka irin na Bashir
amma daya tuna cewa Allah shi yake qulla aure ya kuma rabashi a sanda yaso se ya
gode masa ya kuma tabbatar da Allah ne yake son sa shiyasa be sake hadasu shi da
ita ba se a yanzu da take babu igiyar kowa akanta.

Yana sane yake nuna mata kamar besan komai ba dan yafi so ita da kanta ta gaya masa
bata da aure a sannan ne ze dakko tsohon littafin soyayyarta ya karkade shi ya fara
biya mata shafi shafi dan yayi alqawarin a wannan karon babu gudu babu ja da baya
se inda qarfin sa ya qare amma se ya mallaki Asma'u kuma in sha Allahu rabonsa ce.



M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.


ASMA'U
Kai tsaye dakina na wuce sanda na shiga gidan ban ko tsaya jin Anty data tareni da
tsokana ba na wuce. Seda na cire kayan jikina da naji kamar harda su gurin tare mun
numfashi kafin na watsa ruwa na saka doguwar riga mara nauyi na fito har sannan
tunanin Yusuf da kalamansa suna mun yawo a qwaqwalwa.

Anya kuwa Yusuf be san aurena ya mutu ba amma idan ya sani me yasa ze tsaya beyi
mun maganar ba? Da wannan tunanin na dawo palour na tarar da Anty Hadiza ita kadai
tace mun Anty taje gida ta dawo.

Hira muka shigayi da Anty Hadiza, itama ba baya bace wurin zance nan da nan ta
shiga kwashewa Bashir Albarka.

"Ni wallahi naga qarfin halinsa irin yanda ya iya tsayawa a gaban mu bayan duk
rashin mutunchin daya tatawa mutane, kinsan da Alhaji ya kirashi akan maganar ya
bar miki yara me yace masa? Cewa fa yayi shi baze bar Yaransa a hannun Mace ba yana
buqatar ya basu tarbiyya kiji dan abu ta kazan uba ko ina tarbiyyar take a gurinsu
da yake iqirarin baiwa wasu oho.

Allah ne yaso ki ya rabaki da Shi tun yanzu dan wannan mutumin tantirin mara
mutunchi ne wallahi qila da se kin kai shekarun da baki da yanda zakiyi ko yaka ki
zeyi dole ki haqura ki zauna sannan zece ze sakeki.

Ni wallahi ma sena raina ajinsa dana ga ita matar so din, me mace kamar ki, da se
ya bari idan ya auro wadda ta fiki sannan se yayi duk kadifirin rashin mutunchinsa
amma yanzu ai baya yaci wallahi ba kuma ze taba maida kamar ki ba In Allah ya
yarda"

Nidai "hmmmm" kawai nake ce mata dan har a sannan tunanina yana kan Yusuf ne, so
nake na tambayeta ko sunyiwa Yusuf zancen amma sena dake, kai dole ma yasan da
maganar nan qilan wani dalilin ya sakashi qin yi mun zancen dan haka zan saurara na
gani zuwa wani lokaci.

Se qarfe bakwai na Magriba Anty Hadiza suka tafi bayan Alhaji qarami sun dawo gidan
ya sakeyi mun nasiha tareda jan kunnen na kula da kaina na kuma kare mutunchi na a
duk abinda zanyi.

Yusuf be zo ba be kuma kirani a waya ba, nima sena rabu dashi nasan dai baze wuce
qila zuwa gobe yazo daukar Ma'u ba tunda litinin akwai makaranta dukda bansan a ina
take karatun ba.

A bakin Farida da taje gidan su dakko abu naji Bashir bashida lafiya, ko me ya same
shi oho nidai haka na kwanta ba tareda na sake bi takan maganar ba a dalilin haka
ma ranar har yan biyu a nan gidan suka kwana.

BASHIR
BASHIR
Yana kallon motar Yusuf har ta bace masa kafin ya dafe kansa daya sara da hannu
daya ya daga qafafunsa da sukayi sanyi ya wuce gida, a tsaye ya tarar da Amirah ta
riqe qugu tana zazzagawq Su Aliyu da suka hada PS anan palour suna game su kuwa
babu wanda ya ko daga kai ya kalleta abinda yake gabansu kawai sukeyi tana jin
shigowar Bashir din ta juya cike da masifa tace masa

"Gara daka zo kai tunda Ubansu ne zasuji maganar ka. Idan banda iskanci da
wulaqanci gardawa dasu zasu zo su zauna mun a palour harda wani qarin dorin dosano
da suka samo sannan ina musu magana sun mayar dani kamar wata mahaukaciya sunqi
kulani ai idan uwarsu ce bazasuyi mata haka ba".

"Amirah ki na gaya miki ki dena zagar musu uwa koh? Amma idan baki bari ba in sun
rama karki kuskura kice zaki kawo mun qara, ki barsu suyi sabgarsu.

A sati sau nawa suke zama a gidan da har ze zama abin magana dan yau daya sun zauna
a palour zaki zo kinawa mutane tashin hankali, dan Allah ki kyakeni na huta" Bashir
ya fada kafin ya rabeta ya wuce, dakinsa ya shiga ya bude first aid box dinsa yana
neman paracetamol dan sosai kansa yake masa ciwo amma be samu ba.

Palour ya sake komawa ya kwalawa Aliyu kira, Aliyun ya ajiye pad din game din ya
tashi yaje ya same shi a zaune bakin gado ya dage kai da hannaye biyu.

"Aliyu idan kuna da paracetamol a dakin ku kawo mun idan kuma babu ga kudi nan ka
dauka mota kaje pharmacy din tsallake ka siyo mun maganin ciwon kai" Bashir ya fada
dakyar dan idan yayi magana ji yake kamar ana sara masa abu akansa.
Abin Da da uba duk yanda Aliyu yake jin zafinsa ganin yana yin da yake ciki seda ya
sanyaya masa jiki, cikeda tausayi ya dauki muqullin motar Bashir din dan basu da
paracetamol din suma, be dauki kudin daya nuna masa ba ya juya ya fita.

Baffan Abuja yacewa yazo ya rakashi nan da nan suka tafi, hana da kudi cikin wanda
Bashir din yake basu ko Ma'u wani lokacin a ciki ya hado masa magungunan ya tsaya a
wani gurin siyar da Abinci ya siyo masa sakwara da miyar Egusi da wani gashin nama
da akeyi a kusa da gurin dan ya lura be ci wani abun kirki dazu ba kuma Antyn su
batayi girki ba suka hado komai kafin suka dawo gida.

Sosai Bashir yaji dadin Abincin, yana ci yana sakawa Aliyu da yayi tsaye a gurin
Albarka. Seda yayi nak yasha maganin ya kwanta kafin Aliyu ya barshi ya fita, yana
bude qofa suka ci karo da Amirah zata shiga se yayi saurin tareta da cewa

"Bashi da lafiya ki barshi ya huta"

"Idan naqi fa ubana se ayi yaya?"

"Nidai na gaya miki ki barshi ya huta idan ba haka ba ai baki manta gamon mu sau
biyu ba idan aka sake na uku se kin gane kurenki, sena cire miki haqori in yaso
naga da bakin da zaki ringa yiwa mutane hayaniya a gida, tunda kika zo kin mayar
mana da gida kamar kasuwa mu bamu saba ba" Aliyun ya fada yana sake daure fuska
sosai.

Seta ganshi kamar Bashir dan kwabo da kwabo haka yake da Bashir har kuwa halin be
baro ba sedai abinda ba'a rasa ba da kuma banbancin kwaba daga gurin uwa da suka
samu, kwafa tayi dan tana tsoron Allah tana tsoron yaron nan bashida mutunci, na
farko ya fasa mata goshi na biyu kunne tasan idan ta matsa dagasken yana iya sauke
mata haqora kuma yaci bulus tunda ubansa babu matakin da ze dauka
Seta juya dakinta tana ci gaba da zage zage shima ya wuce gurin game dinsu ba
tareda ya kulata ba.

Maganin nan da Bashir yasha ya sakashi bacci sosai dan se ana daf da magriba ya
farka ko La'asar beyi ba. Seda ya watsa ruwa saboda yanda jikinsa ya yi masa ba
dadi amma yaji sauqin ciwon kan dukda yana farkawa hoton Ma'u da Yusuf ne ya fara
gilma masa a ido yayi saurin rufewa jin yanda zuciyarsa ta buga da qarfi, a
dakinsa yayi sallolinsa be ko fita palour ba yana jiyo hayaniyar Amirah da be san
ko da wa takeyi ba se ma ya sakawa qofarsa muqulli.

Naman dazu yaci da lemo dukda yayi sanyi amma bayaso ya fita ma balle ya hadu da
Amirah ta qara masa ciwon kai, yana yin isha ya sake kora magungunan saboda yanda
yaji tunanin dazu na neman tado masa da Sabon ciwon daya fi na dazu, dole ya dauki
mataki baze zuba ido ba yana ji yana gani wasu wawaye su ringa kula masa mata har
suna gaya masa magana.

Dole ya nemi Ma'u su daidaita dan yasan itama bazata taba bawa wanin sa dama ba
koshi wannan shishshige mata yakeyi bawai dan tana so ba (A naka tunanin kenan
malam Bashari 😂).
WASHE GARI
WAI YA LABARIN MUTANEN GOMBE KUWA???
GIDAN DADA
Tun ranar da labarin sakin Ma'u ya sameta tabi duk ta tsangwami kanta, ko kadan
abun beyi mata dadi ba kuma da ace Bashir yayi shawara da ita bazata taba bashi
goyon bayan aikata hakan ba to a wanne dalili ma ze saki Ma'u??

Babban tashin hankalin ta irin yanda Alhaji Amadu yayi mirsisi kamar besan abinda
ya faru ba bayan lokacin da Naziru yaje yana mata buyagi akan abinda Yayan nasu ya
aikata ya tabbatar mata da Alhajin ya kira Bashir din sunyi magana amma ita bece
mata komai ba har yanzu da aka kusa dosar wata da maganar.

Tasan Alhaji ta kuma san shirun sa ba Alkahiri bane bata san ta inda ze kamota ba,
tsoronta Allah kar wannan abin itama ya zama sanadiyyar igiyar auranta kamar yanda
ya taba ambata mata a baya da in har bata zare hannu daga sabgar gidan Bashir ba
tabbas ze iya yanke igiyoyin da suke kanta idan yaso se taji dadin yin abinda take
so tunda ne isa da ita ba to yanzu ma irin yanda ya dauke mata wuta baya shiga
sabgarta sam dan ko abu yake so sedai ya kira Fainusa tayi masa abin yana mugun
damunta har ta fara tunanin ko da gaske itama an sake ta ne kawai gaya mata ne beyi
ba kuma tana tsoron ta tunkare shi da maganar tajiyo hakan ne dan bata san ina zata
dosa ba, aure shekara Hamsin ba kadan a saketa ta kama ina toh??

Da hantsin ranar Tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi abinda duniya ya taru
yayi mata yawa, tun shekaran jiya da Addah ta sanar mata da Sabon bala'in da Ummi
ta janyo musu ta sake rasa sukuni. Dan shege a zuri'ar su wannan wane kalar tashin
hankali Ummi take neman jefa rayuwarsu a ciki? Idan aure take so me yasa tun farko
bata fada ba in ma bata da me sonta ne ai ko a tsakanin Naziru da Sa'ad ita me iya
tursasa daya ya aureta ne a taru dai a rufawa juna Asiri amma yanzu wannan abu data
jawo musu ina zasu saka kansu a garin nan??

Shigowar Fainusa da kukan data fasa ne ya dawo da ita daga tunanin data tafi, a
gigice ta ke tambayarta meya faru? fainusan na kuka take cewa

"Dada Umar ne, na gaya miki nafi sati ina kiran wayar sa kota shiga baya dauka
shine yanzu ya daga yake cemin wai nayi haquri ya fasa aurena. Ya rasa ta yanda ze
gaya mun ne shiyasa idan na kirashi baya dauka na kuma tambaye shi dalili yace mun
ba komai, ni yanzu yaya zanyi Dada? Shekara Shida kenan fa ina zaman jira yanzu
dakyar Allah ya kawo mun mijin kuma shima ya gudu yanzu ya ake so nayi da
rayuwata?"

Kuka sosai takeyi, Dada tayi tsam ta kasa cewa komai. Tunda auranta ya mutu da uban
da ta shekara shida kenan an tafi ta bakwai kamar wadda aka watsa wa jinin baqar
jaka babu wanda ya sake zuwa yace yana sonta, da kyar da Addu'a Allah ya fitowa
Fainusa da Umar din nan har ya turo manyansa anyi magana sukace sati biyu zasu dawo
da komai da komai a tsaida ranar daurin aure yanzu kusan wata daya kenan babu su ba
labarinsu shine ze bullo da wannan maganar kuma kai su dai suna ganin hawa hawan
tashin hankali.

"Kiyi haquri, ni tsoro nakeji nayiwa Alhaji magana yanzu kinga tunda Yayanku ya
saki Matarsa Ahaji be ce mun komai ba ina tsoron na jangwalo shi dan kinsan gani
yakeyi kamar da saka hannuna a faruwar
abun nan.

Ki bari a qara kwana biyu idan yaso ko Amiru ne se na saka ya kira Umar din shi
yaji menene matsalar se a magance ta" Dada ta fada da son kwantar mata da hankali,
se Fainusa ta fizge daga riqon datayi mata tana cewa

"Nidai kije kiyi masa magana dan idan na rasa Umar mutuwa kawai zanyi duk duniya
bayan da Iro ya sako ni babu wanda ya qara ko kallona da sunan so se shi sannan
yanzu yace ya fasa wallahi gara kawai na mutu na huta da wannan baqin cikin da nake
gani. Duk sakayyar abinda kukeyiwa wasu akaina take qarewa, nayi aure naje Miji da
kishiya sun wahalar dani sannan yanzu bayan na gama cin benci na samu wani dakyar
shima ya gudu to gara na bar gidan nan na koma wani gurin ko Allah ze dubeni ya
cireni daga bala'in da kuka jefa rayuwata a ciki".

Sosai hankalin Dada ya tashi, tasan Fainusa ba hankali ta cika ba itama tsaf tana
iya yin abintzata illata kan nata kamar yanda ta fada kota gudu daga gidan dan haka
jiki a sanyaye ta miqe zuciyarta na bugawa kamar zata fi to ta nufi dakin Alhaji
Amadu.

Yana zaune yana sauraren radio ta shiga ya daga kai ya kalleta sau daya ya mayar da
kansa a ransa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login