Showing 33001 words to 36000 words out of 238465 words

Chapter 12 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima
yayarta ta fada, seda ta cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya
sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya da daddare an ciro mata baby girl”

“Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar
yayansu Sunusi suka amsa da Amin gaba daya.

“Kinje kenan?”
“Naje mana daga can nake ma yanzu”

“Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na
rantse da Allah in nice kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi
wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi kwatakwata baki san abinda ta mana ba
ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan Amirah da suke uba daya) wai
saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan Bashir ne ai
dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita
Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka
ranar amma da se mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka
gane zallar takaicin Amirah da take ji.

Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema
zakije dan ciwo na gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku”

“Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan
dama indai aka fara wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin
Amiran harma dana Bashir din dan ita fa tunda yai auran nan ta dena gaishe shi.
Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji kunyar dauke kai
idan ta ganshi ba taqi gaishe shi.
Asma’u ta kance wai
“Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace
“Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan
bazan koma ba”.

Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara
watsewa bayan tayi musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda
zata kwana biyu a garin.

Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman
idan suka zo indai ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu
baya taba bari suje ko nan da can su kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana
cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa gidan ba.

Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka
barshi sukayi gida yace se ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan
taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita da Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata
hannun Naziru, ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki
daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da
mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane biyun qannenta yan biyu Bilal
da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure tuni yana
zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa
transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan
Nan da kwana 7 zasu tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da
kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta bari se anyi radin sunan yar Amirah
idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu in ta tafi ze iya
zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana
zaune ta jiyo hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take
kallon su Addah dake fitowa daga mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar
ba tana asibitin ita har yanzu.

Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan
dai yau za’a sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton
nan zata dawo ba kodan yanayin jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da
dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da kulolin da ta zuba tuwo da
miyar kukar da ta saka Amna tayi.

Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani
tsilli tsilli alamar basu da gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan
sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata zauna ba tayi musu sallama ta
koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan
Addah Fatu, Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu
ringa kiranta, setayi Murmushi kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka
mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan Dada ze saka ba ce mata yayi shi
bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne badan Aliyu
Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby
Iman ragunanta biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai
qudurce a ransu fa se sunyi daga baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta
kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u dan Amirah tace shagali zatayi
na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin
barin garin tayi ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya
tafi tun safe kuma har nasa rabon suka cinye.

Toh maji ma gani dai.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 15

YOLA
Su Asma’u sun isa yola lafiya sun kuma samu tarba me kyau daga mamansu da suke kira
da Goggo da bakinta yaqi rufuwa ganin yayan nata da kuma jikokinta a gabanta ba
qaramin faranta mata yayi ba. Se sannu da zuwa take musu tama rasa wanne zata kama
ciki idan ta janyo wannan yaron se saki ta kamo wancan su Asma’u har seda sukayi
kwallar kewar Mahaifiyar tasu.

Seda suka nutsu sukayi sallolinsu sukaci abincin da Abokiyar zaman Goggon Innawuro
ta kawo musu ga fura me sanyi da gardi sannan Goggo tayi musu jagora zuwa bangaren
megidan su gaishe shi.

Fari kyakykyawan bafulatanin me kamilalliyar fuska dake cike da haiba da hasken
salati yana nan a yanda Asma’u ta sanshi tunda tayi wayo sedai a kwantar a tayar
tun zamanin da suke zuwa Tareda Baffan su dubashi wanda kuma tun kafin a haife ta
yake wannan ciwon kimanin shekarun sa Arba’in kenan a kwance yana wannan jinyar da
har yau Allah ne yanke masa ba sedai fatan ta zamo masa kankarar zunubi.

Seda sukayi dagaske gurin danne kukan tausayin bawan Allahn dake musu maraba daga
kwancen ya miqa hannu ya kamo Abdallah yana cewa “Zo nan Abdullahi bawan Allah
madallah da Amini na kwarai, Rahmar ubangiji ta dawwa ma tare da takwaranka a
makwancinsa”.

Akan shimfidar sa da take a gyare ya zaunar da Abdallah sannan ya janyo Arif din
Yaya Bilki yana cewa “wannan kuma me idon yan Chinese dinfa wanene” seda sukayi
dariya gaba daya Innawuro tace “Toh takwaranka ne Isma’il dan wajen Bilkisu”

“Toh toh yi haquri ta kwara gajiyar hanya ce ta rufe idon ko nasan anjima zasu bude
irin nawa”.
Cikin mutuntaka suka gaisa ya tambayesu sauran Yan uwansu da kowa da kowa duk suka
amsa lafiya daga nan ya shiga saka musu Albarkar da bakinsa baya gajiya da ita a
kullum suka hadu ko suka gaisa a waya. Sun dan zauna kafin yace suje su huta haka
suda suka sha hanya, a nan suka bar yaran suka koma Dakin Goggo jikinsu dukka a
sanyaye.

“Allah sarki Baffan Yola wannan jinya dai taqi ci taqi cinyewa Allah yasa kankarar
zunubi ce” Asma’u ta fada tana kwanciya akan gado Goggo da Bilkisu suka Amsa da
“Amin”. Basu ja wata hira ba suka kwanta aka barwa gobe dan sun gaji gaskiya.

Washe gari bayan sun je sun gaisa da Innawuro da Baffa suna zaune a palour Goggo
suna cin Wainar Gero da Kunu me kyau da Innawuron tayi musu dan tasan suna son sa
sosai. Goggo dake zaune daga gefe ta kalli Asma’u tace “Ma’u ya Abokiyar zaman ki
kuwa kuna dai zaune lafiya koh”

Seda ta tsame hannunta kafin tace “Muna lafiya Goggo to ina muke ganin juna bare
wani abu ya hada mu ina Lagos tana Gombe”

“Haka ake so ai dama wani sa’in raba gidan yana da amfani idan har akwai wasu
matsaloli amma dai ko zuwa gaba idan ta fara tara iyali itama dole ya hade ku
saboda a samu daidaiton kawuna tsakanin su dan dai nasan baki tashi kinga ana yan
ubanci a gidan ku ba kuma zaki kaishi gidan wani ba”.
“Haka ne Goggo ai tama haihu fa shekaran jiya akayi suna” Yaya Bilkisu ta fada jin
Asma’u tayi shiru bata ce komai ba.

“Kai Masha Allah me aka samu? Kuma cikin satin da aka fita fa Bashir din ya kirani
Allah yasa kuwa beji babu dadi ba banyi masa barka ba ban sani ba ai da har ita
Dadan tasu da Fatu na kira na musu barka, miqo min wayata nan Bilki ki gani karma
na sha’afa da batun”.

Wayar Yaya Bilkisu ta bata ta kuwa shiga kiran Bashir sedai be Amsa ba saboda
lokacin aiki ne seta maida kiran kan Dada ita ma seda ta kusa katsewa sannan ta
daga. Cikin mutuntaka suka gaisa Dada ta tambayeta ya me jiki tace jiki gashinan se
fatan Afuwa.

“Ashe kuma an samu qaruwa wallahi ban sani ba se yanzu muke zancen dasu Asma’u nake
ji”

“Asma’u? Sunzo yola ne?” Dada ta tambaya dan bata sani ba Bashir din be gaya mata
ba daman kuma tasan Ma’u ba Sallama zata mata ba yanzu.

“Eh wallahi sunzo tun jiya ita da Bilki, Allah ya raya yayi Albarka, haduwa tayi
wuya amma Insha Allahu ina sa ran zuwa Bikin Hashim (Qanin su Ma’u da suke uba
daya) anyi abubuwa da yawa Gombe ban samu leqowa ba”Goggo ta fada, da haka sukayi
sallama ta kashe wayar bata ajiye ba ta dannawa Addah Fatu kira.

Itama lafiya lau suka gaisa tayi mata barka harta bawa Amirah waya suka gaisa da
Goggo tayi mata sannu sannan ta kashe wayar ta maida hankalin ta kan Asma’u da tayi
kinini da fuska dan tasan seta mata maganar qin gayawa Dada tafiyarta.

“Wato Ma’u bazaki chanza ashe, wai ni shin Nafi ce tayi miki kishiya ko Bashir da
zaki bi ki qullaci baiwar Allah ki ringa gaba da ita. Sehi wanda ya miki laifi kina
zaune qalau dashi amma kina raina uwarsa”

“Ni wallahi Goggo ban rainata ba me nake mata? Duk wani girma da ya kamata in bata
ai ina bata to me ake so kuma nayi”

“Oh kina ma da bakin mayar min kenan, yanzu ina bata masan kin taho nan ba kin
kwaso mata jikoki har shida kin biyo wannan hanyar bata sani ba, ba fata ba idan
wani mugun abu ya faru kuma fa sedai kawai suji sama”.

“Toh ni yanzu Goggo ai ba haqqi na bane na gaya mata Danta ne ya kamata ya sanar da
ita tunda ai ya sani da izininsa muka taho ai”

“Haka ma zakice, to maza ki kirata yanzu a waya ki bata haquri kuma kodan gaba ki
kiyaye kar irin haka ta sake faruwa” Goggon ta fada.

“Dan Allah Goggo karki tilastani yin wani abun kuma dan kinsan bazan bijirewa
umarninki ba, wane kalar haquri ne banayi, tunda Bashir yai aure sau daya na taba
daga waya na kawo miki qarar sa akan yayi mun wani abu ai badan baya yimun din bane
dan kince mun naje na shanye komai nayi haquri ne.
Bazan iya ci gaba da alaqa dasu ba abinda ya zama dole zanyi amma wallahi na yanke
duk wata alaqa ta baya da kika sani tsanina dasu ga yar uwarsu nan se tayi musu
abinda suke ganin ni bazan iya ba”. Ta qarasa maganar hawaye na sakko mata

Ta rasa me Goggo take so ta zama, a zatonta kowa irinta ne me tsananin hakuri,
yakana da dauke kai akan komai? Ko kuwa duka maza kalar Mazajen data zauna dasu ne
masu Adalci da sani ya kamata? Sannan kowane yayi dacen kishiyoyi na qwarai da
dangin miji na gari. Sun fa qare tuni irinsu amma ita Goggo bazata gane wannan
baudadden zamanin da muke ciki da ko cikin yayan da mutum ya haifa yake nuna
banbanci dan daya yafi daya wadata, Namiji yake fifita buqatar wata mace akan wata
saboda alaqar jini, sannan surukai suke zabar jinsu akan sauran surukai da suke
baren su.

Ita Dadan ai da bakinta tace mata Dama sun dade suna son dorar da zumunchinsu kuma
ta hanyar hada auratayya ne kadai haka ze yiwu ko to gashinan sun hada ta kuma
janye ta basu guri suyi yanda suke so se kuma ace seta cusa kanta cikinsu ina sam
fa bame yuwuwa bane.

“Toh yanzu menene na hawaye kuma daga magana” Goggo da jikinta yayi sanyi ta fada
ai kamar Asma’u na jira kuwa ta fashe da kukan gaske harda sheshsheqa. Haka sukayi
zukudi duk suna kallonta ranau babu dadi musamman Goggo, seta janyo Asma’un jikinta
tana cewa

“Kiyi Haquri nasani ba’a kyauta miki ba, ba’a miki daidai ba kuma badan nafi son su
nake cewa kiyi haqurin ba Aa sedai ina so ki rabauta da ladan da Allah ya tanadarwa
masu yinsa. Idan kika jure kikayi haqurin idan ma sun zalince ki ko anan ko acan se
Allah ya saka miki amma kiyi shiru ki dena kuka dan Allah”.

Dakyar ta tsagaita kukan tana ci gaba da share hawayen dai dai Innawuro ta shigo
dakin.
“Ashsha Maryam me yasa kike haka duk sanda yarinyar nan tazo se kin saka ta kuka
dan Allah menee haka” Innawuro ta fada tana janye Ma’un gareta kafin taci gaba da
cewa

“Nasan zancen daya ne akan mijinki da danginsa, Duk abinda suka miki na cutuwa kar
kiyi shiru Asma’u kiyi magana ki kwaci yan cinki, ki tsarkake zuciyarki kar ki nufi
kowa da sharri kar kumaki bari su raina ki da sunan wai kina da haquri ko ita da
take gaya miki hakan saboda Allah be jarabceta da irin wadannan fitintunun na
zamani bane shiyasa take ganin kamar kowa irin zaman ta yake yi.
Share hawayenki dan Allah karki ragawa duk wanda yace ze taka ki ki rama kinji
Ma’u”.

Dadi kalam Innawuro suka mata ai kuwa ta share hawayenta aka dauko wata hirar
daban. Suna zaune Sauda da Maimuna Yaran Innawuro sukayi sallama sunzo wa su Ma’u
sannu da zuwa nan suka shiga hirar yaushe gamo dan dama Saudah qawarta ce sosai.

Se yamma suka fita tare dasu Saudah sukaje gidan Hamma Isah Babban Dan Innawuro
matarsa ta haihu suna gidan a ka kira waya aka fada. Washe gari kuma suka fara zaga
dangin Goggonsu ta ko ina sune har Mambila daman haka sukeyi, basu fiya samun damar
zuwa ko yaushe ba amma duk sanda suka zo se sun zaga ko ina sun gaisa da dangi
tareda kai musu abun arziqi hakan kuwa ba qaramin dadi yake yiwa yan uwan Goggon
dadi dan ko basu kai musu komai ba zuwa a gaisa din kadai ya wadatar.

Mu dawo Gombe 😂😂
Amirah na ci gaba da jinyar jikinta da kuma shirye shiryen shagalin sunan data
rantse seta yi dukda haryanzu basuyi maganar da ogan ba amma jira takeyi da an
sallamo baby Iman, ita kanta Addah wannan karon tace mata ta haqura gaba inda rabo
se tayi kudin da ze bata se suyi wata hidimar dasu amma Amirah ta qeqashe qasa
Allan fir se tayi. A cewarta haka kawai duk qawayenta tana gani in sun haihu yanda
ake raqashewa kamar biki sannan ita ace kartayi wallahi ita ma se sunci uwar sabada
kowa yazo ayi bushasha asan itama fa me kudinnan take aure se kuma Addah tace haka
ne fa toh suyi kodan ma a maido musu da bikin gudummawar da sukayi.

Ranar Talata da daddare lokacin data tabbatar yana gida ta danna masa waya dan tana
so ya bata kudaden da zata siyi kaya ta bada dinki ga kuma shirye shiryen suna.
Bashir na zaune a palour yana shan Tea da cake gaba daya dauriya yakeyi amma zaman
kadaicin ya isheshi gidan ya masa wani wawakeke saboda babu Ma’u a ciki ji yakeyi
kamar ya kirata yace ta dawo.
Abinci kansa se kame kame yake in yunwa ta ci shine dole yake zuwa Restaurant yaci
gaba daya besan me yasa wannan karon dan girke girken data saba masa ta saka a
frizzer idan zatayi tafiya irin haka batayi ba, ya saba da sedai ya bude ya dauko
yayi microwaving yaci to yanzu ko miya ce kadai itama ta qare dan Ma yayi dabarar
sakawa a kunna wutar gidan bayan sun tafi wancan ranar daya tuna da abubuwan zasu
baci gidan yayi wari dan haka ya saka aka karbo spare key na gidan a Estate
Management Anty ta shiga ta qarasa kashe musu duk wani abu da ze iya kawo matsala
aka bar frizzer.

Yana cikin tura Cake din Wayar Amirah ta shigo ya harari wayar sannan ya daga a
dake dan ya san labarin gizo baya wuce na qoqi, indai Amirah ta kira shi to ko
tambayar kudi ko qorafi in yana son jin yanda suke sedai shi ya kirata.

Bayan sun gaisa se duk sukayi shiru, yanayin dataji miryarsa ba walwala tasan
dakyar in zata samu yanda take so amma haka ta daure taja numfashinta tace

“Abban Iman dama naji shiru ne baka ce komai ba akan siyayyar kayan Iman da nawa
kasan wancan da ka bani unisex muka siya na amfanin farko farko”.

Seda ya mula sannan cikin dakewa dan karta kawo masa wani wargi yace “ke yanzu
kayan me kuma kike magana kina fama da kanki?”

“Kayan barka mana” ta fada itama tana dakewa.

“Ni babu kudin wasu kayan barka da zan baki abinda nake dashi na bawa su Dada zasu
hada da na gurinsu a siya wannan kayan Al’adar data ce na zata ma sun kawo muku”

“Basu kawo ba inaga se gobe” ta fada a cukule dan ba haka taso ba yanzu ma sune
zasu siyo kayan aka san irin wanda take so? Sannan itama nata duk se sun gama gane
wa kenan kafin tayi kwalliyar gaskiya bazata yarda ba sedai ya bata ko kudin Lace
daya ne da zatayi kwalliyar Suna dashi dan haka ta gyara zama tace

“Toh shikenan amma dai se ka bani na siyi wanda zanyi fitar suna dashi danne kamata
kowa ya gani ba sena saka”.

“Suna wane sunan kuma” ya tambayeta da mamaki dan dai yasan ai shekaran jiya akayi
radin suna ko?

“Taron suna mana, idan an sallami Iman dole zamuyi tunda ai na farko ne kaga”.

“Karki kuskura wallahi idan bakiji tausayin kanki da jikinki ba to kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login