Showing 66001 words to 69000 words out of 238465 words
yana kallon yaron, duk da fuskarsa bata nuna ba amma
jikinsa yayi la’asar daga gani cike yake da nadamar abinda ya aikata amma izza irin
tasa bazata barshi aga gazawarsa ba.
Palour na dawo na zauna bayan duk sun shiga daki ina jiran kota kwana, jira nake
naji ko Bashir zece na bashi abinci ko ya sake gayamun wata maganar banza a daren
nannayi masa wankin babban bargo amma shiru har sha daya ina zaune ban sake jin
motsinsa ba.
Dakina na shige nayi wanka, Idona sun soye bana jin bacci dan haka nayi Alwala
nayita jera salloli ina kaiwa Allah kukana har seda gabbaina suka gaji kafin na
kwanta ina ci gaba da jan carbi.
Nayi niyyar washe garin na kira Amirah da Addah nayi musu gaisuwa amma wallahi na
fasa, na kuma shirya duk wanda ya sake bude baki ya gayamun zancen banza a gidan
nan bazan daga qafa ba sena gaya masa na wofi.
Da safe ban jira shi ba na shirya yara na kaisu Makaranta a motarsa daya bar Key
akan Dining be dauke ba. Tare muka fita da Aliyu bayan na bada excuse din bashida
lafiya na wuce dashi Asibiti aka sake duba shi suka rubuta masa magani muka dawo
gida.
Ina Kitchen ina dama masa wa Aliyu custard naji fitowar Bashir daga daki, sena dawo
bakin qofar na leqa tareda kasa kunne ina jin Aliyun yana gaishe shi, se ya amsa
harda tambayarsa yaya jikinsa yace da sauqi.
“Abbi kayi haquri bazan sake ba” naji Aliyun yana fada, se Bashir yace
“Ya wuce Aliyu kaima kayi haquri ina cikin fushi ne na dake ka gashi har naja maka
ciwo, kaci abinci muje na kaika Asibiti a duba ka” Bashir ya fada, se Aliyun ya
nuna masa ledar magungunan da muka siyo yace
“Mami ta kaini yanzu ga magani ma an bani”
“Ok Allah ya qara sauqi, ka huta sosai kaji bari naje office nakai papers din nan.
“Yawwa yaron kirki ga shi tashi kasha” na fada ina ajiye masa.
Nida Aliyu muka wuni a gidan ya warware har yana tayani aiki munata hirar mu, qarfe
hudu har na kira Uber zan tafi dakko yara se gasu sun shigo wai Driver Office dinsu
Abbi ne ya dakko su.
Bashir ne dawo gidan ba se 9 na dare, muna zaune muna kallo ya shigo da sallama
hannunsa dukka biyu da ledoji, Kallon cikin ido mukayiwa juna kafin na janye nawa
ina tabe baki yara suka tashi suna masa sannu da zuwa ya amsa ya basu ledojin
hannunsa manya guda biyu ya wuce da qaramar dakinsa.
Be dade da shiga ba ya kwalawa Aliyu kira ya tashi ya tafi sauran suka bude
ledojin, tarkace ne kowa Abinda yafi so ya siyo masa, indai yaudara ce ya kware
daman, ya zuga rashin mutunchi sannan ya siye ka da abinda yasan kana so. Ina jinsu
suna tsallen murna banbi takansu ba.
Aliyu ne ya fito ya debi abinci a plate ya hada da ruwa da cup akan Try yaje ya kai
masa ina kallonsa ban ce masa komai ba ya sake dawowa ya debi zobon dana hada ya
kai masa.
Da gudu ya fito daga dakin yana tsalle da ihun murna na waiwaya ina cewa “kai meye
haka zaka zo kana mana ihu akai”
“Kukalla ku kalla” ya fada yana daga kwalin wayoyi iphone X guda biyu, Amna ya
jefawa daya kafin ya zauna cikin zumudi ya shiga bude ta hannunsa.
“Yaya waya aka siya muku” Jafar ya fada yana komawa kusa dashi,
“Wallahi Mamai waya ce, yeee munzama yan gayu muma Faree mun samu tayim snap” Amna
ta fada tana daga wayar tata Fara ta Aliyu Baqa. Duk su biyun suka dawo kusa dani
suna nuna mun, na karba ina cewa “iye yan gatan Abbi gaskiya kun gode Allah ya
sanya Alkahiri ya sa lafiya ta kashe”.
Gaba daya sun cika gurin da ihun murna, sun dade suna nacin a siya musu waya amma
yaqi yace se sun gama secondary school idan zasu kira abokansu sedai su karbi tawa
ko tasa kowannensu dai yana da Laptop itama dan dokar makarantar suce amma yanzu da
yake neman shiri yake da yaran shine ya siyo musu da kansa, Bashir kenan.
Ana tsaka da murnar ya fito da plate din abincin, Jafar ya tashi da gudu ya karbo
yana cewa “Abbi mufa, se yaushe za’a siya mana?”
“Ba yanzu ba Sheik baku isa riqe waya ba amma zan chanza muku PS 5 gobe kuma za’a
kawo muku” ya fada yana zama akan kujerar da take kallon wadda nake kai. Sabon ihu
suka dauka harda yan biyu dan suma sun koya musu Game, ba damar a samu zama a gida
anyita buga PS sena gaji wani lokacin na dauke.
Ina kallon yanda yake ta wani murmushi yana jin dadi ganin yaran na murna an shirya
kenan, yana kallona na sake hade girar sama data qasa, sen miqe ma ina cewa Farida
idan sun gama tura hotunan da sukeyi daga wayata ta miqomun na shige dakina a
jikana ina jin yanda ya bini da kallo amma ban waiwaya ba.
A dakin ma ban zauna ba, wanka na shiga nayi shirin bacci, sena dakko Backpack din
da nake zuwa office da ita na fito da kayan ciki ina dubawa dan nima ranar Monday
zan koma aiki in Allah ya kaimu, gajiya da jiran Farida nayi sena leqa dan ina so
na kwanta har sannan suna zaune Bashir na nuna musu ko menene oho a wayarsa.
“Farida bani wayata, bazaku tashi kuje ku kwanta ba ko gobe akwai school fa” na
fada daga bakin qofa. Seta taso da gudu ta bani ta sake komawa,
“Oh ina magana duk kunyi mun shiru ko” na sake fada, se Bashir ya dago yace
“Babu aiki gobe Workers day”
“Au toh, seda safen ku” na fada ina juyawa ciki.
Harna kwanta naji message ya shigo wayata, kamar bazan duba ba sedai na janyota,
Bashir ne
“Ina son magana dake” ya rubuta. Guntun tsaki nayi na maida wayar na ajiye naja
bargo na,
Befi minti uku ba tsakani kira ya shigo, sauri nayi na sakata a silent, ina kallo
seda yai kira uku nai likimo abuna dan bazan dauka ba, wato nice baze lallaba ba
tunda ya shirya da yayansa shikenan ba ina cikin wannan tunanin naji an turo qofa.
Luqus nayi harda wurga qafa gefe dan fitila a kashe take ni a dole bacci nakeyi,
ina jinsa ya kunna hasken ya tsaya akaina yana kallona.
“Ma’u Ma’u” ya fada yana bubbuga pillow da nake kai, senayi miqa tareda qantsarewa
ina salati irin an tashen nin nan nayi mici mici da ido ina kallonsa nace “Lafiya
zaka zo kana tashina a bacci”.
Seda ya zauna gefen qafafuna ya wani kumbura baki yace “baki ga message dina ba da
calls dina ba?”
“A mafarki ka turomun halan” na fada ina tura baki gaba. Se da yayi kwafa sannan
yace “saboda abinda ya faru yasa kika dauki fushi dani, naga wanda na doka din ma
mun shirya se kece zaki ci gaba da gaba dani”
“Ni kuma inyi fushi dakai ana me Baban Ali space dai na baka ka gama zaman makokin
idan ka dangana kayi tawakkali se mu ci gaba da magana” na katse shi ina gyara
kwanciya, gajeran tsaki yaja kafin yace
“Oh banida tawakkali kenan”
“Ni awa ince baka da tawakkali, hausa nayi maka bawai abinda nake nufi kenan ba” na
fada ina danne dariyar dake neman kufce mun ganin yanda yai kinini da fuska yana
jan iska.
“Gobe da asuba zamu tafi Delta inaga zamuyi kwana biyar ko sati saboda tafiyar nema
yasa ban tafi Gombe ba”
“Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya” na fada a qagare dan na fara jin baccin
gaske, se ya miqe yana cewa “ta so muje can, ban hada kaya ba kuma ina so nayi
bacci kinga fitar Asuba zamuyi”.
“Yi gaba gani nan” na fada ina miqewa kamar zan shiga bandaki, yana fita na rufe
qofar na murza key, a fili nace “Dan rainin wayo sedai ka tafi babu kayan kuwa” nai
hayewata Gado na kwanta ina jinsa yana kiran suna na yana kwankwasa qofar a hankali
nayi biris dashi harya gaji ya tafi, duk randa ya koyi karbar laifinsa, ya iaya
bada haquri ma shirya.
Da Asuba da muka hadu kamar kububuwa ya wuceni ya shiga kitchen, ya gama diri
dirinsa ya fito daman nasan ba abinda ze iya tsinanawa mutumin da inaga ruwan zafi
kadai yasan yanda ake dafawa. Amna ya kwalawa kira ta fito daga dakinsu yace maza
ta soya masa kwai.
Ina kallonsa ya shiga dakin ya fito yana doka uban tsaki ya kalli inda nake ya sake
komawa seda ya shiga sau biyu ana ukun ne yace “Dan Allah Ma’u kizo ki hadamun kaya
su Musa har sun kusa qarasowa”
“Au wai baka hada kayan ba me kake jira toh” na fada ina tashi zaune akan kujera.
“Kin sani ban iya ba ke kike hadamun, please Ma’u”.
“Badan halinka ba muje” na fada ina miqewa. Kusan rabin wardrobe din ya watso su
qasa, cikeda takaici na shiga hada masa kayan a qaramar akwati na gama ina zugewa
ya shigo da kofin shayi a hannunsa ya ajiye akan mudubi yana cewa “har kin gama”
Ban amsa ba na shiga kwashe na qasan ina mayarwa, horn da muka jiyo daga waje yasa
na dakata na daukar masa Laptop bag dinsa shi kuma yaja akwatin muka fito, Jafar na
tsaye a kofar dakin su ya gaishe shi yace “Abbi a kawo fa”
“Za’a kawo Sheik ina sauran yan uwanka”
“Sun koma bacci Abbi”
“Ok idan sun tashi ka gaya musu na tafi Delta zamuyi waya idan na sauka” ya fada
yana tafiya.
“Allah ya tsare Abbi” Amna da Jafar suka fada. Daga bakin qofa na tsaya ya miqawa
Driver Akwatin ya karbi jakar hannuna bayan na masa Adawo lafiya naja kofar na koma
ciki. Seda na kwashe kayan da ya zubar tsaf ina mita “Abinda ko Su Muhammmad baza
suyi mun ba shi yake yi, da yake buqatar kansa ce ai ya iya roqa a masa mtsw” naja
tsaki.
A dakin na kwanta na qarasa baccina.
GOMBE
Acan Gombe kuwa ranar talatar da safe Bashir sukayi waya da Naziru ya gaya masa
yaje Asibiti ya karbi Iman daga nan ya wuce da ita gurin Dada kafin ya gama yanke
abinda za’ayi.
“Ni se nake ganin yaya da kayi haquri, be kamata ace ka raba Uwa da yarta ba idan
kayi haka kamar ai bakayiwa Amirah da ita kanta Babyn Adalci ba. A yanayinta tana
buqatar dumin uwa da kuma Nono ko dan ingancin lafiyarta” Naziru ya fada bayan da
ya gama jin umarnin yayan nasa.
Shiru Bashir yayi, Tabbas gaskiya Nazirun ya fada amma toh amma meye amfani mayar
mata da ita ma yanzu bayan ta riga ta yaye ta kusan sati bata sha Nonon ba se
madara ai dakyar ma idan zata karba yasan, kuma fa shi ya gama yanke hukuncin sa ta
hakane kadai ze hukunta Amirah taji a jikinta yanda gobe bazata sake gwada yin
abinda tayi ba.
“Kaje kawai ayi yanda nace, na rigada munyi magana da Dadan, zuwa Next week idan na
samu dama zanzo nan Lagos zan dawo da gurin Ma’u”
“Anty kuma? Ita tace zata riqeta?” Naziru ya tambaya cikin mamaki. Se Bashir din
yace
“No, bata rigada ta amsa ba amma ai gida nane ina da ikon sawa da hanawa ko”
“Hakane” Naziru ya fada sukayi sallama, a ransa yana mamakin wannan zallar rashin
Adalci irin na dan uwan nasa. Tayaya zaka taba jaririya da uwarta ka dauka ka kaiwa
wata wadda ita kanta tana da buqatar me taimaka mata. Ÿaÿa Bakwai nefa a gaban ta
take kula dasu ga shi sannan kullum seta fita aiki ai wallahi ko ita kanta yanzu
kamata yayi yace ta dakata da haihuwa ta ji da abinda yake a gabanta balle har ya
dauki raino ana zaune lafiya ya kai mata.
Daman lokacin daga wanka ya fito dan haka ya zura rigarsa ya cewa Dada bari yaje
Asibitin ya karbo yarinyar “Amma fa Dada kiyi masa magana idan ba haka ba wallahi
ze janyo abinda za’a zo ana samun sabani daga qarshe kuma ace za’a ga laifin Anty
Ma’u” ya fada yana tsaye daga bakin qofa.
“Ka rabu dashi Naziru, gurin uwarta za’a maida ta, shi a ina ma ya taba ganin anyi
haka? Idan so yake ya kaita cikin yan uwanta se ya bari idan Allah ya rayata ta isa
sakawa a makaranta a sannan yana da hujjar da ze iya dauketa ya maida ita can ko
dan ta samu ilimi irin na sauran amma ba yanzu ba. Ni wallahi na rasa me yake damun
Bashir, mutum tamkar wanda yake da wani motsi a kansa”.
“Ba wani motsi wallahi Dada tsabar samun gurine tunda yaga duk sharar daya debo
kina goya masa baya shiyasa”.
“Yanzu dai jeka, idan ka dawo se muje tare can gidan nasa, dukda ya kamata na
kirashi ma yabar yarinyar nan ta koma gida tayi jego ko ta dawo nan dole se an
taimaka mata kafin ta saba ai” Dada ta fada, Naziru yayi mata sallama ya tafi
Asibiti.
Yana zuwa ya tarar da wannan tashin hankalin, bashida karfin guiwar kiran Bashir
dan haka likitan ne ya kirashi shi kuma ya kirawo Dada ya gaya mata.
Bayan an gama cike ciken takardu ya saka hannu aka bashi gawar, be iya tafiya ba
seda Ya kira Sa’ad Yayansa da yake bi yazo suka tafi tare suna kaita gida Dada tace
suje su dakko Amiran sannan ta kira Ummi a waya tace suzo ita da Addah yanzu.
Fadar tashin hankalin da Amirah ta shiga bata baki ne dan sumanta uku ta ringa
kururuwa tana ihu kamar wadda ta hau bori, se da Goggo Ladi qanwar Alhajin su
Bashir tayi mata tatas sannan aka samu ta lafa da ihun amma fa bata dena kukan ba.
Addah kanta tasha kuka fadi take daman yan baqin ciki basu so aka haifeta ba gashi
yanzu anyi manaqisar da seda aka rabata da duniya su dai Allah ya isan su bazasu
yafe ba.
Babu wanda ya ko bi ta kanta, da dare yayi zata tafi da Amirah Alhajin su Bashir ya
hana yace ta barta acan dan yasan idan sun tafi ma a maimakon ta taishe ta Allah
kadai yasan abinda zata je ta kitsa mata kuma.
A wayar Ummi Bashir sukayi magana da Amirah, yanda ta ringa ya bala’in daga masa
hankali gaba daya tausayinta ya rufe shi. Allah ya sani yana son yara kuma wannan
yarinyar haka kawai yaji duk cikin Ÿaÿan sa tafi shiga ransa kamar sanda aka haifi
Farida sedai har nata ya zarce Faridan.
Badan Assignment din da yake gabansa ba da a ranar yaso yaje amma ya mata Alqawari
daya gama zezo Gombe, ya ringa rarrashinta yana gaya mata kalamai masu kwantar da
hankali tareda Alqawarin kwanan nan zasu samu wata qilan ma yan biyu, da haka ya
samu tayi shiru har tayi bacci sannan ya kashe wayar.
Kunsan December watan hidima ne 😁😁 weddings everywhere
To all the December brides Allah bada zaman lafiya 🙌🏼🙌🏼
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 26
Har Bashir ya gama kwanakin sa a Delta ba wani magana mukeyi ba, a ranar da ya tafi
dai bayan sun sauka ya kirani haka washe gari da safe kafin su fita field munyi
waya bayan nan kuwa har suka kwana hudu be sake kirana ba nima kuma ban kirashi ba.
A tunani na ko aiki ne yayi masa yawa, dan daman yawan ci idan yana field bamu cika
yin waya ba shine dai idan ya samu lokaci ze kira to wannan karon ma na dauka a
hakan ne.
Ranar Lahadin da suka kwana hudu da daddare muna zaune wayar Aliyu dake kusa da ni
tayi qara,
"Aliyu wato har ka rarrabawa Jama'a Number ka ni bani da ita koh, waye yake kiranka
da daren nan?" Na daga wayar ina dubawa.
"Super hero" naga an saka, na gane Number Bashir ce sena miqa masa ina cewa "uhm
uhm su Bat Man ne ko Spider man naga an sa super hero".
Gaba daya suka saka dariya, Aliyu ya daga wayar suka gaisa, ban san meya gaya masa
ba nadai ji yace "toh ga Mamin ma ko na bata ka gaya mata?"
"Tam Abbi bye" ya sake fada kafin ya kashe wayar yana kallona.
"Mami, Abbi yace Mr Kunle ze zo yanzu ya kawo saqo, akwai kudi a bedside drawer
dinsa ki bashi 20k".
Kamar wata sokuwa haka nake kallon Aliyun harya gama. Abubuwan mamakin da yawa,
ashe Bashir yana da lokacin kiran waya nice baze kira ba.
Sannan yaushe muka fara haka da ze fadi abu ni baze kirani da kansa ya gaya mun ba
sedai ya kira Aliyu?
Wayata dake kan centre table na janyo na danna power button dan na tabbatar ko a
kashe take be sameni ba ya kira Aliyun naga a kunne take. Ga network dina full to
meye dalili?
"Hmmmm" na fada a fili kawai na ci gaba da kallon da muke, ba'a jima ba kuwa aka
danna Door Bell Jafar yaje ya bude se gashi da Babban Package da alama PS din da
aka ishe ni da naci kamar nina ce zan siya aka kawo.
"Mami yana jiran saqon wai" ya fada bayan ya zauna ya fara budewa Abdallah na taya
shi.
Se na waiwaya na kalli Aliyu nace
"Kaje ka dakko masa baya gaya maka inda suke ba?"
Seda yai dan jim kafin ya miqe ya shiga dakin nasa, be jima ba ya fito da kudin a
hannunsa ya miqo mun yana cewa "Gashi na dakko".
A hasale nace masa "zaka tashin mun akai ne ko yaya, ina kai ya gayawa saqon kuma
kazo kana nunamun me zanyi dasu".
Zugui zugui ya fice ya kaiwa Kunle kudin ya dawo. Ina kallon yanda yake satar
kallona ganin na dora qafa daya kan daya ina girgizawa duk sanda suka ga ina haka
to sun san zuciyata a kusa take, ina iya make su idan suka matsamun.
Hayaniyar da Jafar da Aliyu suka fara suna qoqarin jona PS din da Tv tasa na daka
mutsu tsawa ina cewa "ku bace mun a nan, ba gobe Monday ba shine a wannan lokacin
kuke shirin dasa wata Game, ku tattara ko yanzu na fasata wallahi".
Kama kansu sukayi sum sum gaba daya suka watse, ina zaune ina sakin tsaki, son na
tabbatar da zargina sena janyo wayata na dokawa Bashir kira na kuwa taki sa'a akace
call waiting.
A da, indai na kira Bashir ko da wa yake waya se ya dakata ya amsa kirana, ba
qaramar waya me muhimmanci bace zan kirashi ya kasa katseta amma yau har ta gama
ringing ta yanke be daga ba.
Na sake kira nan ma be daga ba, seda na jera masa kira hudu amma bawan Allahn nan
ko a jikinsa kuma har sannan call waiting.
Agogo na kalla, tara harda rabi tayi, nasan babu wani official call da ze ce yana
yi yanzu, kuma na tabbata bada Dada yake waya ba dan sanin da na mata da Tayi Isha
take kwanciya to da uwar wa yake waya da baze amsa tawa ba?
"Amirah" zuciya ta ta raya mun, se ta yuwu kuwa din. A jiye wayar nayi ina jiran ya
biyo baya amma har goma da rabi shiru ba kiran Bashir babu labarinsa, sena miqe
jiki a sanyaye na shiga dakina.
Tunani na shigayi ko na