Showing 48001 words to 51000 words out of 238465 words

Chapter 17 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

kwamushe musu waya wadanda suka tsira kuwa sunyiwa tasu boyo me
kyau kafin a sane ta.

“Addah lafiya, meya faru? A ina kuma? Dada ta tambayeta cikin damuwa da jin kukan
nata tasan ba lafiya ba amma Number Asma’u data gani yasa hankali be tashi da yawa
ba tasan koma mene ne da sauqi.

Addah kukan ta taci gaba dayi, ganin da Asma’u tayi bata da niyyar ansawa Dada ya
sakata karbar wayar ta danyi mata bayanin iya abinda ta fuskanta da lamarin.

“Ashsha abu beyi kyau ba, yanzu waye ya kulle gidan? Shi Bashir din ya sani?” Dada
ta tambaya se Asma’u tace mata
“Muma bamu sani ba Ai, Baban Ali kuma ban sani ba gaskiya ko yasan maganar dan
wayarsa a kashe take tundazu dana kira”.

“Shikenan bari nayiwa Amiru magana gashi can yana cin abinci daman nan gidan naku
ze taho ya dauki Rahma in yaso se suzo da Naziru yanzu Allah ya kiyaye gaba” Dadan
ta fada zuciyarta sam babu dadi, yanzu wannan wane irin abune ai yanzu Allah kadai
yasan inda maganar sunan nan zata tsaya sun jawo musu abun fada a gari. Fitowa tayi
daga dakin ta ta tarar da Amirun a tsaye yana niyyar fita dan sunyi sallama ta
shiga ciki.

“Amiru ka nemi Naziru ku tafi tare gidan Yayan naku ba lafiya ba”.

Da”Allah ya kyauta” ya amsa mata ya fita yana dannan kiran wayar Naziru dan shi duk
a zatonsa be wuce a ce rigima ce tsakanin Ma’u da Amirah ba, a hanya ya dauki
Naziru daya maze kamar besan me yake faruwa ba, gama wayarsu da Bashir kenan ya
kirashi da wani layi yace masa duk me za’ayi karya kuskura ya bude gidan nan qasa
da qarfe goma na dare yanzu kuwa har tara ta gota dan haka ya qara musu awa daya se
sha biyu ze bude su kuwa.

Kamar wata boarding school ranar hutu haka suka tarar da qofar gidan cike da
motoci, yawanci mazajen wadanda Allah ya taimakesu suka tambaya kafin suka fito ne
an kuma san inda suka tafi da sukaji shiru suka biyi sahunsu se wadanda yan uwansu
suka kira su dauke su.

“Kai lafiya kuwa gidan meyake faruwa haka” Amiru ya fada se Naziru ya marairaice
kamar na Allah yace
“Yanda ka gansu yaya nima haka na gani, mu qarasa mugani Allah yasa dai lafiya.
Bakin get suka qarasa inda wasu suke qoqarin yanke kwado amma kamar na tsafi yaqi
yankuwa wasu daga gefe kuma suna musu magana akan su bari, ta yaya zasu budewa
mutum gida bada izininsa ba duk abinda yake ya dawo su tabbata yana kansu.

“Wai meyake faruwa haka ne” Amiru ya tambayi masu yanke kwado dan shi tunaninsa ya
tafi kodai gobara ko wani babban Al’amari ne kuma yake faruwa amma kuma hmga kwado
ta waje ga kuma kururuwar mata suna jiyowa daga ciki suna ihun a taimaka musu.

“Kagane Alhaji nima bansan me yake faruwa ba gaskiya Beb dita ce ta kirani tace
nazo na dauketa a gidan nan tazo suna daman ni na kawota dazu se kuma tace na taho
da me yankan kwado idan zan zo kaji iya abinda na sani nidai” shugaban masu
kiciniya da kwado ya fada.
Se Amiru ya kalle shi cikin masifa ce“wannan wane irin rashin hankali ne, meye a
cikin gidan da har zaku zo ku budewa mutum ba tareda izininsa kona wanin sa ba idan
wani abun nema ai se ku fara neman izinin me gidan tukunna”.

“Megida ka ganmu nan dukka jiran a bude gidannan muke takamaimai babu wanda zeje
maka yasan me yake faruwa dayawan mu munji shiru ne matan mu basu dawo ba muka biyo
sawu wasu kuma kiransu sukayi a waya suzo su dauke su kaji yanda abin yake” wani
mutum ya sake fada, se Amirun ya zaro wayarsa bayan yacewa Me Yankan ya tsaya ya
dannawa Bashir kira cikin Sa’a kuwa ta shiga.
Basu ko gaisa ba Bashir da yasan kiran ko na menene yace masa

“Ni na saka Naziru ya kulle gidan kuma wallahi duk wanda ya budemun gida kafin sha
biyu na dare se nayi sharia dashi” qit ya kashe wayarsa. Se Amirun ya juya yana
kallon Naziru daya sha kunu

“Bani key din Idan yaso se yayi shari’ar dani” ya fada fuska babu wasa.

“Amma yaya kasan dai ni laifina ze gani ai kuma...”

“Zaka bani ko bazaka bani ba, daman kasanabinda yake faruwa muka taho amma baka
gayamun ba kayita biye masa kunawa mutane shirme. In ba haka ba matan auran zaku
kulle har se sha biyun dare saboda shirme” fada sosai Amiru ya rufe Naziru dashi,
wayarsa da ta shiga qara ce ta katse shi ya daga Ummi ce cikin kuka take gaya masa
halin da ake ciki dan a zatonta yana Katsina shiyasa tun tuni bata kirashi ba.

“Tundazu ina bakin Get din na rasa ta inda zan fita na kai yarinyar Asibiti Yaya
tsoro nakeji karta mutu a hannuna” ta fada cikin kuka. Nan da nan hankali sa ya
qara tashi, Naziru da yake kusa dashi duk yaji me take fada tun kafin ma ya masa
magana ya zaro key ya bude gidan ba tareda ya saurari Mazan da sukayo masa caaa
akan daman shi ya kulle amma ya barsu suna shan sanyi a tsaye.

Yana bude qofar da Ummi yaci karo da azama ya karbi Babyn suka juya shida Amirun
tabi bayansu suka shiga mota kafin Mata suka fara tseren fitowa kamar an sako kaji
daga keji wata dankwali a hannu wata da takalmi qafa daya babu dai me cikakkiyar
nutsuwa a cikinsu kowa tayi ta kanta. Suna dai kam da yawa sunce ko su suka haihu
sun yafe bare a sake gayyatarsu suje.

Cikin qasa da minti Goma sha biyar gida ya rage Me jego da Addah da Inna Gaji se
wasu dangin su Addah da basu fi biyar ba ga Hajia Mariya data sha goyo Aljanar ta
tafi har sannan shame shame bata farfado daga Iskokan data hau ba.

Inna Gaji da ta rakube a lungu ce ta fito tana cewa “Allah na tuna Allah karka kuma
hukuntani da irin wannan bala’i na tuba wallahi bazan sake zuwa taron suna ba” babu
wanda ya kukata se ajiyar zuciya suke saukewa, dakyar Hajia Hassana ta numfasa tace

“To Fatu se a san yanda zaayi da Mariya a kaita gida dan kinsan duk sanda tayi irin
haka seta kwashi kwana biyu ko uku bata farfado ta dawo daidai ba nidai wannan suna
naku ya shiga tarihi wallahi kar Allah ya sake maimaita mana...”

Jiniyar Yan Sandan data karade gidan ta sakata yin shiru, toh fa wane bala’in ne
kuma ya tunkaro???
Kuyi haquri qarfin hali kawai nakeyi abubuwa sun sha kaina 🙏🙏🙏🙏

A karanta da haquri banyi editing ba

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 20

A kofar gida Alhaji Kabiru Dangaske ya faka motarsa data yan sandan dake tare
dashi. Kofar gidan wayam kamar anyi ruwa an dauke kai bazakace gidan Engineer
Bashir ne daka kwashi uwar Sabada dazu ba dan tuni ko wacce ta kama gabanta dan
dare ya farayi musamman gashi garin sanyi daman. Mata biyu yan sanda doguwa da
gajeriya da suka zo dasu ne suka shiga gidan dan qofar a bude take.

Mamaki ne ya kamasu tsakar gidan ga kujeru Birjik wasu ma sun karye kamar wanda
akayi wasan dambe a gurin ko ina dai kacakaca daidai da kayan DJ fa nan sukabarsu
tunda suka samu hanya suka fece to ana ta kai wayake ta wasu Kayan kida 😂😂.

“Naga part biyu ne ina zamu shiga” gajeriyar ciki tayi tambayar
“Nima haka na gani mu koma gurinsu muji ina tracker ta tsaya” dayar ta bata amsa
suka juya inda ragowar tawagarsu suke.

“Oga mun shiga amma gidan part biyu ne wanne guri matar take?” Yar doguwar ta fada.

“Inaga ku shiga tare kawai bana son bata lokaci nifa” Wani Dan baqi tsamurmurin
mutum dayasa uwar babbar rigar shadda Getzner se maiqo take daga gani shine Alhaji
Kabiru Dangaske ya fada.

“Ai baze yuwu ba mu shiga gidan matan aure ba Alhaji sedai su matan da dai zamu
samu ayi mana sallama da me gidan ne idan ya bada izini se mu shiga kuma kaga layin
babu kowa, ku je na daga hannun hagu dai direction din yake nunawa”.

Komawa sukayi kai tsaye kuwa suka nufi part din Amirah dan shine a hannun hagu din
suka tsaya abakin qofa sukayi knocking.

Bugun da suka jiyo anayi ya qara hargitsa musu ciki dan daman tunda suka jiyo
jiniya kowa tasha jinin jikinta, Inna Gaji kuwa daman kuka ta saka tana tambayar
wai wane tsautsayi nema ya tsayar dasu ne a gidan bayan wannan uban bala’in da aka
sha yanzu idan wani abun nefa yazo ya sake rutsa dasu ta tafi ta kulle qofa ilai
kuwa gashi ana bugu.

Hajia Hassana ce tayi qarfin halin tambayar waye jin muryar mata ta dan sauqaqa
musu tsoron har taje ta bude qofar sedai ganin mata da uniform yasakata ja da baya
tana karanto wa’innahu sulaimanu dan itafa duk tashin hankali ayi shi amma aduniya
tana tsoron Allah tana tsoron hukuma.

Tsakiyar palour suka tsaya suna qarewa palour da akayi wa wada wada kallo,
“Amm muna neman Hajia Mariya ne” yar gajerar ta fada tana qara tsuke fuska ganin
yanda duk suka zuba musu ido ai kuwa a tare suka nuna musu Mariya dake kwance shame
shame tana bacci”.

“Meye haka ku tashe ta mana tana kwance cikin wannan tarkacen wai meya faru haka a
gidan ne?” Doguwar ta fada kafin ma su amsata Gajetiyar ta katseta da cewa “Ba
wannan ya kawo mu ba muyi aikin mu kawai” ta qarasa inda Hajia Mariya take kwance
ta shiga tashinta amma shiru bata motsa ba.

Dagowa tayi ta kalli su Addah da sukayi tsilli tsilli a gurin tace “Nauyin baccine
da ita haka?”
“Ranki ya dade yanzu ta sauka daga iskokai ne wani lefin tayi ake neman ta
station?” Hajia Hassana ta tambaya. Ba tareda officer ta amsa mata ba ta juya tana
cewa dayar “ina zuwa” ta fita.

A qofar gidan tayi musu bayanin abinda aka fada musu, Alhaji Dangaske ya hau kumfar
baki shifa a shiga a dakkota kawai haka takeyi duk sanda ta aikata wani abu seta
hau iskokai To wallahi wannan karon ko bulukiya t hau se dai a kulle su ita da
Aljanun nata.

Inspecta da suke tarene yace taje tayi musu sallama da me gidan ta koma minti kadan
ta dawo tace baya nan.

“Wato ni za’ayiwa wasan kwaikwayo kuna tsaye kuma Naga alamar bazakuyi abinda ya
dace ba ni bari na shiga dakaina na fito da ita dan wallahi wannan karon Mariya
bata isa ba, ta saba salwantar mun da qananan abubuwa ko nata tace an sace to
wannan karon bazan dauka ba ina gani ta sabautamun miliyan Ashirin a sama ba taci
bulus seta biyani ko mota ta ko kudina fita kuma ba izinina da takeyi taje ita da
Allah dan na gaji”. Ya tattare riga ya doshi Gate inspecta na tsayar dashi amma
yaqi.

Yana zura qafarsa Amiru na faka mota Suka fito da sauri ganin yan sanda, da sauri
Naziru ya qaraso yana tambayarsu lafiya se Alhaji Kabiru ya dakata ya yo baya yana
cewa
“Yawwa Samari gidan kune ko? To shiga ka fitomun da Mariya qawar Fatu data zo suna
gidannan ka gayamata wallahi idan bata fito ba tunda wadannan dana zo dasu basu da
amfani mopol zanje na dakko ai tasan halina”.

Amiru ne ya qaraso gurin shima Ummi daman wucewarta tayi bata ko kallesu ba tayi
cikin gida. A taqaice Naziru yayiwa Amiru bayanin abinda ya fahimta cikeda takaici
Amirun yacewa Alhaji Kabiru da Inpectta su biyo shi dan abin nasu Addah ya kaishi
maqura.

Yanzu haka Iman nacan a NICU sun barota wanda dakyar likitan ya karbeta yace tunda
uwarta bata san ciwon kanta ba subarta kawai su koma gida idan ta mutu Allah yasa
qarshen wahalar da zata sha kenan dan shidai be taba haduwa da Uwa da Ya marasa
tunani irin Addah da Amirah ba, dakyar suka roqeshi suka karbeta yanzu dai sun baro
an jona mata oxygen da sauran tarkacen wayoyi sedai su bita da Addu’ar samun lafiya
dan su da kansu sun cire rai da yarinyar.

Dirar mikiya sukayiwa Palour Amirah, Hajia Mariya da farfadowarta kenan tayi
arangama da Alhaji Kabiru ai take qirjinta ya bada daram dam.

“Gasunan ku duba wadda kuke nema ku tafi dare yayi ya kamata a rufe gida” Amiru ya
fada yana qara hade rai. Ba bata lokaci Matan yan sanda sukayi ram da Mariya suka
tisa qeyarta akayi waje Alhaji Kabiru na zuba tijara se muce Allah ya bada yanda
za’ayi a biya Kabiru kudin motarsa 😂😂😂

suma basu tsaya ba suka fita, a qofar Asma’u ya tsaya ya kira Rahma da harta fara
bacci ta fito suka tafi lokacin sha biyu harta gota, a gidan suka bar Naziru ya
kwana saboda gudun abunda ka iya faruwa kuma, seda ya duba ko ina kafin ya kulle
gidan ya kwanta a dakin Aliyu.

Su Hajia Addah dai kamar masu kwanan keso haka suga safiya ido biyu kowa da abinda
ya dameta Asubar fari kuwa wadanda suka kwana suka dade akabar Addah da Amirah se
Ummi da itama tace gida zata tafi anjima bazata iya wannan masifa ba kafin takwas
na safe kuwa se su biyu kawai ga uban barnar da akayi a dakin sun ma rasa ta ina
zasu fara.

Dakin Bashir Amirah ta nufa da niyyar tayi wanka saboda bala’in tsamin da jikinta
yai mata kafin su san abinyi sedai ta tarar da qofar a rufe se a sannan ta tuna da
Anty Aisha ta bawa key jiya kuma ita bata ma sake ganinta ba gashi babu waya bare
ta kirata dole haka ta shiga dakinta ta binciko inda ta boye key din toilet data
rufe dan kar a bata cikin Sa’a sega na Dakin Bashir a gurin da alama anan ta boye
mata.

Da murnarta ta dauki key din ta fita, Addah na zaune akan kujera ta rafka uban
tagumi abin duniya ya taru ya mata yawa dare daya harta zabge tsabar Tashin Hankali
yanzun ma tayi zurfi a tunanin yanda zasuyi su gyara gurin kafin azo tunanin neman
kudin da za’a biya bashin da suka karbo bata maji fitowar Amirah ba se ihun
salatinta data jiyo a dakin Bashir ba shiri ta miqe ta bita.

“Na shiga uku Addah shikenan sun kashe ni wallahi Yaya Inaga yanka ni ne kuma kawai
bazeyi ba” Amirah ta fada hannu aka tuni idonta ya fara tsiyayar da hawaye lokacin
data ci karo da murfin Wardrobe din Bashir da aka fashe ga kan Mirrow dinsa wayam
babu ko kwalli suma an kwashe wai iya abunda idonta ya gani kenan Allah kadai yasan
dame dame aka dauka kuma.

Ita kanta Addah seda hankali ta ya qara tashi dan duk a zatonsu tunda qofar na
kulle bala’in be taba can ba basusan ta nan Al’amuran suka fara sauka bama 😂

“Dallah can ki mana shiru aikin gama dai ya riga ya gama duk ma abinda za’ayi daga
baya ne me afkuwa ta afku ni dai yanzu ciro sarqar nan ki gani mu Adana su kafin
suma bala’in ya dirar musu nidai wannan Ya dakika haifa kamar yar Allah bani ta
jefa mu a masifa (babu ruwan Iman ku dai kuka jefa kanku uku ah to 😚😚).

Wata sabuwa inji yan caca ai seda Amirah ta shafa wuyanta taji wayam sannan ta
ankare babu wannan sarqa dama babu batun awarwaro tun tuni su ta ankare da sun zube
amma a sannan bata su takeyi ba, yanda take rarraba ido ne yasa Addah a fusace cewa
“bazaki ciro bane kike tsareni da ido ko kuma daman ta kice” ta wara idonta akan
Amiran.

“Shikenan ashe ba Mariya kadai ce take da rabon zuwa Birsin ba harda ni wayyo Allah
na na shiga uku na lalace wannan wane irin bala’i ne suke bibiyata sahu sahu ni
fatu?” Kuka riris Addah takeyi, sarqar da hayota tayi dakyar Hajiya Inna Qawarta
tayi mata hanyarta a gurin wata qawarta.

Seda ta bada dubu dari kudin Haya sannan ta bata takaddun gidanta dashi kadaine
kadarar datayi mata saura a yanzu akan idan wani abu ya samu sarqarta sedai a siyar
ta cire kudinta ta bata chanji to a qalla da sarqar da abin hannu sun kai na kusan
miliyan biyu gashi babu ko daya se warin dan kunne daya ne a kunnen Amiran to ita
kuwa yau ta shiga ina taga haske wannan Asara kan asara babu biyan buqata?

Rasa me bawa wani haquri akayi cikinsu ita Amirah tana kukan haduwarsu da Bashir
ita Addah tana na sarqa seda suka gaji dan kansu sannan sukayi shiru kowa tayi
wanka suka shiga gyaran guri kafin kuma su san abinyi a gaba. Tsakar gida suka
watso sharar Addah ta fita ta samo yara suka shiga sharar tsakar gida aka tattare
kujeru masu lafiya aka ware karyayyu gefe suma kafin masu su suzo ayi lissafi haka
suka tattaro kwanuka da kulolin abinci suka bayar yaran suka wanke komai bayan
yaran sun gama ta biyasu suka koma ciki sukayi zugun zugun.
Babu wanda yayi tunanin zuwa duba halin da Iman take ciki a cikinsu tunda dai Ummi
ta gaya musu tana Asibiti shikenan daman ko wancan kwanciyar da tayi bayan an
sallamota ba kullum take zuwa ba, da aka fara bata abincine taje zuwa tayi pumping
Nonon da za’a bata daga baya ma a gida takeyi ta zuba a Container da suke bata akai
shikenan. Seda sukaji Yunwa na neman hallaka su suka nemi abinci suka ci suka ci
gaba da zaman jiran tsammani kuma.


A bangaren Bashir kuwa Tun a daren Dr Ishaq ya kira yana zuba masa ruwan masifa
kamar shine Amiran, bayan sun gama ya kira Naziru ya gaya masa yanda akayi harda
qarin maggi da gishiri abinda ya qara tunzura zuciyar Bashir din kenan ya shiga
kiran wayar Amirah amma Allah ya taimaketa wandaya sace ya kashe dan kuwa daya
sameta a waya Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a daren, Ganin be sameta seya
maida akalar kiran kan Asma’u.

Tana nade akan gadonta bayan ta gama shirin bacci har sannan Bata bar mamakin
abubuwan da suka faru ba yau a gidan nasu kiransa ya shigo. Daga yanda ya amsa
sallamarta tasan ba qalau ba se tayi shiru tana jin yanda yake magana ta inda yake
shiga bata nan yake fita ba masifa yake mata akan me yasa tun farko bata gaya masa
zasuyi taron sunan ba.

Galala ta saki baki tana sauraronsa ganin fa ba shiru zeyi ba yasa ta katse shi da
cewa “Dakata Malam wai ko baka san wa kakira bane To Asma’u ce ba Amirah ba”.

Cike da masifa yace “oh maganar banza zaki gayamun kenan ce miki nayi bansan wanda
na kira ba ai koma mene laifinki ne tunda kina gaba da ita ya kamata ki nuna mata
abinda yake daidai da ba daidai ba data tace zatayi taron seki hanata tunda kinsan
bana so”.

“Ashema ni ce gaba da ita, meye darin gami na da ita da zatayi abu na hanata ko an
saka ni a ciki ballantana kuma nima gani nayi anayi. Kuma da kake maganar daidai ko
rashin sa qarewarta naga da sa hannun yan uwanku tayi komai danginku kaf babu wanda
bezo gurin ba su a cikinsu babu wanda yasan daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login