Showing 231001 words to 234000 words out of 238465 words

Chapter 78 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

gilashi se Yusuf kowannen su ya kama waya yana dannanwa Baba yana binsu da
kallo.

Da sallama na shiga suka dago a tare suka zuba mun ido, ina kallon yanda Yusuf ya
wani harare ni ban daga ba kuwa nima na maka masa tawa se yayi murmushi ya
sunkuyarda kai. Cikin girmamawa na gaida Baba nayi shiru, se kuma kamar an mun dole
na hadasu su biyun nace

“Ina wunin ku” babu wanda ya amsa mun a raina nace
“Maganina kenan ai”
“Asma’u se gashi mun hadu da Ango kuma muna zuwa muka tarar dashi shima daman kuma
zuwan nawa da niyyar ki kiramun shi a waya na roqi Alfarma se gashi kuma mun hadu”
Baba ya fada cikin sakin fuska yaci gaba da cewa

“Masha Allah, Allah ya sada ku da dukkan Alkahirin da yake tare da junanku ya tsare
ku da dukkan sharri. Ba tareda bata lokaci abinda ya kawo mu Bashir ne yace na
rakoshi yana so ya sake baki haquri akan duk abubuwan da suka faru a baya, sannan
mu nemi alfarma akan takunkumin da Me gida ya saka masa kodan Albarkacin yaya”

“Ni Baba babu abinda yayi mun ai kuma ko yayi na gaya masa ai na yafe masa tun
tuni, in dan wannan ne ma da be taso ka a daren nan ba ai” na fada kaina a qasa.

“Kina fada ne kawai Ma’u amma nasan nayi miki laifi kuma hankali na ne ya kasa
kwanciya ina so naji da kunnena kin furta kin yafe mun ko zan samu nutsuwar zuciya”
Bashir ya fad yana zamowa daga kujera kamar ze durqusa.

Seda na kalli Yusuf da fuskarsa ta gama bayyana kishin da yake cinsa kafin nace
“Na yafe maka Baban Ali Nima ka Yafe mun”
“Baki mun komai ba Ma’u” ya fada da sauri

“Shikenan Allah ya yafe mana gaba daya, sannan dan Allah ga amanar yarana nan, ka
kula dasu kasan bani da sama dasu a rayuwata” na fada kamar zanyi kuka, kafin yayi
magana Yusuf yayi saurin cewa

“Baba wace Alfarma kace zaka tambaye ni”
Baba yayi murmushi yace
“Yaro saboda Bashir ya gaya mun ka yanke duk wata alaqa da take tsakaninsa da
Asma’u koda gaisuwa baka yarda da ita ba, shine nace zan roqi alfarmar Yaran lokaci
zuwa lokaci zasu ringa zuwa gurin mahaifiyarsu idan ka amince”

Seda ya shafa kansa kafin yace
“Ai wannan Baba daman dole ne, ni idan ma ze yarda ya bamu yaran se mu riqe babu
komai ai Da na kowa ne”

“Bazan iya ba, na dai yarda duk hutu zasu ringa zuwa gurinta” Bashir ya fada yana
kallona.

“Wanan al’amari daya faru gaba dayan mu ya isa ya zamar mana izina mu kuma qara
tsorata da lamarin Allah, a duk sanda Allah ya azurtaka da samun abu kayi qoqari ka
riqe shi dakyau saboda ba lallai idan ya kufce maka ka sake mayar da irinsa ba. Ina
miki fatan Alkahiri Asma’u tabbas nayi baqin ciki rasa nagartacviyar suruka irinki
a cikin ahalina, ina fatan kuma hakan baze sa ki yanke zumunchi dani ba kodan
Arziqin abinda Allah ya rigada ya hada” Baba ya fada

Se naji Hawaye na neman zubo mun da maganar da yayi ta idan Allah ya baka abu dukda
nasan da Bashir yake amma se naji kamar ni yakewa gugar zana akan matsayin da nake
kai da Yusuf a yanzu. Dakyar na bude baki nace

“In sha Allahu Baba ai kai ubana ne babu yanda za’ayi nace na yanke alaqa dakai,
Nagode kwarai da irin qaunar daka nuna mun na gode”.

“Allah yayi muku Albarka gaba daya, yaro kai dai ina tayaka murna Allah kuma ya
baka ikon riqeta da Amana Amin” yana gama fadar haka ya shiga qoqarin tura kekensa,
se Bashir ya miqe ina kallonsa ya dauke kwalla daga idonsa kafin ya mayar da baqin
gilashin daya kwamo ya zura hannu a Aljihu ya zaro wata Envelope ya ajiye a gaba
yana cewa

“Ina miki fatan Alkahiri” ya tura Baban suka fice, miqewa nayi tsaye ban yi aune ba
se ji nayi anyi sama dani

“Ka sauke ni Yusuf”na fada a tsorace dan a bazata abin yazo mun
“Naqi na sauke ki se kin dena fushi dani” ya fada yana mun cakulkuli, duk yanda
naso na daure na kasa haka na shiga kyalkyaka dariya kamar wata sabon kamu na
tabbatar su Bashir sun jiyo ni dan basuyi nisa ba kuma darene ko ina yayi shiru.

“Wash Allah na matar nan fa nauyi ne dake” ya fada bayan daya direni akan qafafuna.
Baki na tura gaba ina harararsa ya miqo hannu kamar ze tsokane mun ido ina ja baya
ya biyo ni muka fada kan kujerar baya na ina qasa yana sama na se jinayi kawai ya
kama Bakina ya shiga bani wani irin kiss me goge hadda.

Dakyar na iya kwatar kaina na rarumi hijabina da tuni Yusuf yayi fatali dashi ban
jira komai ba na ranta a na kare dan naga alamar tabbas in na qara ko sakan daya
za’a tafka abin kunya a gidan Jama’a.

Yusuf kuwa dafe kansa yayi ya bini da hargitsatstsuj idanunsa da suka canza kala
har na fice daga dakij kafin ya janyo robar ruwan da aka kawo musu ya balle daya ya
kwankwade, beji dai dai ba ya sake daukar wani ya shanye yayi cilli da robar har
sannnan yana jin wani bala’in son kasancewa tareda Ita yana taso masa.

Wayarsa ya zaro daga aljihu ya shiga kiran layinta yaji qarar wayar nan qasa kusada
qafarsa se ya dakkota, Envelope din da Bashirya bani ya gani a gurin ya hada ya
dauka, seda ya samu ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kama hanya yana sunkuyar da kai
dan karma ya hada ido da kowa Allah ya taimake shi harya fice bega idon kunya ba
bayan ya bawa daya daga cikin masu gadi wayar da envelop din yace su kai mata.

Daren ranar da ciwon Mara na kwana saboda yanda Yusuf ya yamutsani ga kayan tsumin
da nake amfani dasu gaba daya suka rikitamun lissafi se gurin qarfe biyun dare na
samu bacci ya dauke ni ina kallon yana ta kirana bayan da aka kawo mun wayar amma
naqi daga wa qarshe qarin wata damuwar ce gara koma menene da safe ma hadu.

Washe gari tun Asuba natacciyar me Lallen da Alawiyya ta dakko tun daga Kano ta
saka ni a gaba da naci dole na zauna muka fara, ta zana mun hadadden Jan lallae na
qasa da qasa dan bana son na Salatif, tana gamawa kamar Aljana ta hau zana mun
kitso, ko wahalar kitse doguwar Jelar gashina bataji ta kuma debeshi yiri yiri ni
kaina da nake gani a mudubi seda ya burgeni.

Kusan awa biyu lallen yayi ya kama sosai kafin aka cire se mita nake dan gaba daya
duwawuna ya qage da zaman shiyasa nafi gane ayi mun baqin lallae idan ma jan ne
sedai da Sajam shi kuma se suce wai saurin fita yake amma ai yafi saurin kamawa.
Seda muka gama kitson tsaf mukayi sallar Azahar ta doramun da baqar fulawa sega
Ma’u ta fito kamar wata fure, gyaran da fata ta ta samu da hutu ga Kitso da kalle
suka sake fito da yarintata babu yanda za’ayi a nuna maka zaratan Yayana ka yarda
nina haife su, a qaryar me Lallen ma cewa tayi ta zata ban taba aure ba, ta ringa
rantsuwar qaryane da aka ce Jafar Dana ne wai dan ma bataga Aliyu da ya gama
zangamewa ba.

Kafin La’asar gidan mu ya dinke da Jama’ar da bansan sanda aka gayyato su ba,
dagaske dai yinin biki suka shirya harda masu kidan kwarya, haka nasha kwalliya da
wani Arnen leshi cikin dinkunan da nayi Aljanar me Lallen da komai ta iya tayi mun
make up, muka sha shagali abinka da hidimar mata zallah kowa tayi rawa ta gyagije
an zubda galan galan masu kidan kwarya kuwa sun kwashi kudi dan ganin dangin Yusuf
mukayi daga sama qannensa da yayyensa mata, matan yan uwansa harda matar Gwamnan
Bauchi data Gombe suka hado kusan mota Goma suka zo.

Aka hadu aka yi harkar Arziqi da zasu tafi bansan daga inda Alawa ta ringa fito da
kayayayki tana loda musu musu a mota ba, harka dai akayi ta ta girma da Arziqi se
godiya suke haka na rungume Alawiyya dan ta fitar dani kunya ta kuma siyamun qima a
idon dangin Miji, ni kuwa me zan saka wa wannan Yar uba tawa me tsananin qaunata?
Da ace ko wanne Yan uwa haka suke riqe zumunchi ba tareda saka banbanci uwa a
tsakani ba irin na gidan mu da duniya ta zauna lafiya.

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 65


Qarfe Hudun ranar Juma'a jerin gwanon motocin da suka dakko mu daga Gombe zuwa
Bauchi suka tsaya a qofar gidan Marigayi Malam Suleiman Wunti. Da Bismillah na fito
daga mota ina qara gyara zaman Lafayar da na nannade Jikina da ita.

"Yah ubangiji ka saka na shiga cikin su a sa'a, Allah ka wanzar da zaman lafiya da
kwanciyar hankali a gidan aure na. In sha Allahu yanda na saka qafata a cikin gidan
aure na babu abinda zan aiwatar se wanda ze saka Mijina farin ciki, na haqura na
sallama komai a yabzu bani da kowa bani da komai a Duniyata se Yusuf da yake
mijina" na fada a zuciyata ina bin bayan Hajiya Aisha da take riqe da da hannuna
Qanwar Baffan Mace tilo a cikin su.

Ina jin yanda mata suka dauki guda ana sanar da na ciki ga Amarya ta iso a haka aka
shigar dani inda nake tunanin Dakin Hajiyar su ne. Falo danqam da Mata manya masu
aji qamshi kala kala na tashi.

"Sannunku da zuwa maraba lale" wata me zaqin murya take fada har muka zauna a
tsakiyar falon kan wani lallausan Kilishi kaina nidai yana qasa ina ta maimaita
Hasbunallahu a zuciyata.
Gaisuwa aka shigayi kamar yanda ake tsakanin dangin ko wacce Amarya dana Ango, aka
gama bada Amana, ina ji aka kwalawa wata Hauwa kira akan tazo takai Amarya dakin da
zata huta kafin lokacin budar kai, Budar kai fa sekace wata budurwa dan Allah.
Nidai nabi su su biyu suka sakani a tsakiya har muka shiga wani daki se qamshin
turare yake.

"Nidai bari naga Fuskar Matar Yaya bazan iya jira se anje budar kai ba" Hauwan ta
fada tana qoqarin bude fuskata se dayar tayi saurin riqewa tana cewa
"Baki isa ba se kin biya"
"Ya haka ku meyasa bakwa girma ne se kun cire mata dankwali dallah ku matsa" wata
data shigo dakin ta fada taba matsowa kusa da mu sena dago kaina na kalle su ina
murmushi a tare suka hada baki suka ce

"Masha Allah wai zuqi, kai amma Yaya ya iya zabe" murmushi na sake yi musu ina
kallon mutum biyun da muka shigo tare dasu kamar su daya kana ganinsu kasan Yan
biyu ne irin masu tsananin kama da Juna ma.

"Sannunku" na fada ina kallonsu,
"Yawwa Amarya ke za'ayiwa sannu ai, karbi biyewa shirmen wadan nan yaran, kiyi
sallah yanzu lokaci ya rigada ya tafi kuma ba'aso akai magriba ba'a gama Budar kan
ba" Babbar cikin su da a qallah zamu iyayin sa'anni ta fada tana murmushi.

Ita ta nuna mun bandaki dan korar qannen nata tayi, na warware Laffayar jikina na
shiga, ko ina qal na kama ruwa na dauro alwala na fito a raina ina tunanin ina su
Alawa sukayi, jakata tana hannunta kuma zan dan buqaci Powder da lipstick.

Seda na idar da sallah ta sake dawowa dakin hannunta dauke da dan kit na kwalliya
se Madarar kwali me sanyi ta miqo mun tana cewa

"Kisha nasan be zama lallai hidima tabarki kinci abinci ba, ni sunana Nusaiba, ni
nake bin Yaya Yusuf"
"Nagode Anty Nusaiba" na fada bayan dana karba dan tunda ita take bin Yusuf ta
girme ni kenan jikin ne irin namu da baya nuna tsufa.

"Aa fa karki jawo a janye mun tallafi yaji kina kirana Anty, barni dai ni nace miki
Antyn, Idan kin gama ko zaki gyara fuskarki ga kayan kwalliya nan" ta fada tana
dariya.

Nima dariyar nayi nace "Tam Shikenan, dan Allah akwai wata da zakiga kusan kamar mu
daya ko zaki kiramun ita?"

"Ai duk wanda kuka zo kamarku daya kawai dai kin fisu kyau ne"
"Kai banda zolaya fa, toh kice Alawiyya tazo" na fada ina dariya

"Toh shikenan bari naje" ta fita bata dade ba sega Alawiyya da Zahra Aminiyata suka
shigo.

"Kai amma kinyi sa'ar dangin Miji Ma'u, suna da kirki kinga yanda ake ta nan nan
damu kamar wasu gwal? Allah dai yasa su dore a haka zakiji dadin su" Zahra ta fada
tana zama akan gadon da nake.

"Gaskiya dai basu da matsala dukda haka dai saura ki sake musu yanda kikayi da
wadancan matsiyatan banzan baya baya, babu shishshigi babu wulaqanci" Alawiyya ta
fada

Su suka tayani na qara gyara fuskata Zahra ta daura mun dankwali dan gwanace. Ina
cikin qara turaruka masu sanyin qamshin a jikina mukaji ana kwankwasa qofa, a
zatona Nusaiba ce dan haka muka ce a shigo se ganin Yusuf mukayi yaci wata shadda
yar ubansu anyi masa irin rawanin nan na malamai harda wani kwagiri ya riqe yana
dogarawa.

Rige rigen neman mayafi aka shiga yi tsakanin Alawa da Zahra abin harya bani dariya
ma. "Kuyi haquri ban san kuna ciki ba" ya fada yana dauke kai, yanda kasan wani
surukin su jiki na rawa suka fice suka barmu Alawa harda waiwayo wa tana qiftamun
ido na maka mata harara dan na gane me take nufi.

"Amaryar Yusuf" ya fada yana qarasowa inda nake tsaye ya kamo ni jikinsa se nayi
saurin cewa

"Jirana ake dan Allah karka bata mun kwalliya"
"Jiran mu ake dai, kuma kwalliyar daman wa kikayi wa ita idan ma na bata ai tawa
ce" ya fada yana shinshina fuskata. Kai wannan jaraba da yawa take, buga qofar da
akayi tareda turowa ta taimakamun na zille daga hannunsa wata Mata fara yar
gajeriya me jiki ta shigo tana cewa

"Yanzu Excellency ka iya tsallake matan da suke falo ka shigo nan gaskiya ban sanka
da rashin kunya ba, to kaje Hajiya tana kiran ka, Amarya taso muje kinji wannan
Angon naki rawar kansa tafi qarfinsa".

"Allah ya taimaki Woman Leader" ya fada yana dariya, dukda haka seda yayi mun peack
akan lips dina ko kunyar Woman leader data juyar da fuska tana murmushi beji ba
yayi waje.


Ita ta sake dawo dani falon dazu da duk mutanen ciki sun fita se yan biyun da alama
jiran mu suke, haka suka saka ni a tsakiya muka fita can wani qaton fili da yake
daga gefen gidan an gyara gurin da kwalliya irin ta Kamu ga rumfuna an saka da
kujeru da tebura ta ko ina yanda kasan za'ayi wani hamshaqin biki ne.

Seda suka kaini har kan wata kujera da aka tanada saboda Ni, kaina na qasa seda na
zauna naji mutum ya jani a firgice na dago ashe Yusuf ne shi harya nemi guri ya
zauna shi Budar kan tare za'ayi mana kenan.

Seda aka bude taro da Addu'a, manyan mata suka ringa zuwa suna mana ruwan Naira da
daloli Alawiyya da Zahra na durawa a jaka yanda kasan basu san darajar kudi ba da
wannan ta gama juye nata wata hajjajun zata sake zuwa ta watsa nata seda aka kwashi
kusan awa daya ana wasan kudi kafin MC ta kira Qannen Ango akan suzo su bude fuskar
Amarya.

"A dakata Yammata, Uwargida sarautar mata tace ita zata bude fuskar qanwarta" naji
MC ta sake fada danjar yan biyun nan sun taso suka koma. Ta qasan lafaya ta nake
kallon qafafunta da take hardewa tana irin tafiyar Models wato cat walk, straight
gown ce a jikinta data kamata ta wani arnan leshi yanda kasan zatayi nishi rigar ta
bude dan ma bata da qiba se irin mayafin Chantilly dinnan ta dora a kafada daya ta
ruqo jaka a daya hannun tana taunar cingan.

"Oh waifa yanzu gidan wata nazo da ina nawa gidan a matsayin uwargida yanzu wannan
figaggiyar za'a kira da uwargida na Allah kenan.

Tana isowa ta bude jakarta ta fara yi mana ruwan yan dala dari dari seda ta zazzage
mana rafa biyu dala dubu biyu kenan MC kuwa se kirari take mata yanda kasan tayi
tsalle ta kwashi kudin ita ko se wani yatsina take yanda kasan an mata dole.

Da hannu daya taja Lafayar dana rufe fuskata na dago na kalleta ido cikin ido a
raina ina karanta 'A'uzubikalimatillahi tammat minkulli shaudanin wa hammatin wa
min kullu aynin lammati' ta kalle ni na kalleta kafin ta wani tabe baki tace
"Kinyi kyau" da irin sautin da tayi magana nima na mayar mata nace
"Nagode" se jin Yusuf mukayi ya saki wata siririyar dariya muka kalleshi a tare
ashe Video yake mana.

A tsakiyar mu ta zauna aka mana hoto se waniliqe masa take shi kuma yana faman
rirriqeta na ja tsaki qasa qasa yo mani ina ruwana, qarewar ta ya haduye ta mana su
suka sani.

Haka aka ci gaba da gudanar da shagali nidai murmushi dole nakeyi dan idan na tuna
yanda Intee ta ringa wani kwanta masa ana hoto se naji raina ya bacihar seda Yusuf
ya gane ya matsa hannuna da yake cikin nasa yace

"Asmy kishi, ita bata ji haushin kin aure mata miji ba se kece kike kishi da ita"
ya fada qasa qasa daidai kunnena.

Harara na maka masa nace
"Saboda bata iya riqe mijin bane shiyasa har aka iya qwace mata shi din zata wani
zo tana kwanta maka a jiki se ta nunawa wanda be taba kwanciya a jikin ka ba"

"Wallai kuwa qarewarta ma yau a kan jikin zaki kwana ko?" Ya fada yana mun wannan
shegiyar dariyar tasa se nayi sauri sunkuyar da kai dan se yanzu na gane
baranbaramar da nayi ya ringa tsunkulina kuwa yana gaya mun maganganun da suka
girmi kaina nidai haka na kanne dan kar muzo muna raba hali a gaban Jama'a.

Seda mukayi sallar Isha a gidan su Yusuf kafin muka shiga motoci muka wuce gidana
duk a zatona ma anan cikin gidan nasu ne. Gida kam se dai ace Masha Allah dan fadar
haduwar sa ma bata baki ne wai a haka fadi suke sema kinga na Abuja ai nan a qauye
kike Aljannar duniya na Abuja.

Seda akai dagasken gaske kafin Yusuf ya haqura yabar yan uwana su kwana a gidan dan
har seda wata Antyn sa Anty Mami ta kirashi a waya tayi masa tatas lokacin muna
tsaye ya tsareni wai se naje nace su tafi su koma can gidan Hajiya su kwana ko subi
Alawiyya ai wasu da yawa sun tafi gidan ta me yasa sauran zasu ce se sun kwana.

Haka ya kwashi fushinsa ya tafi harda ce mun kuma gurin Inter ze tafi ya kwana nace
a tashi lafiya, to idan ba fitina ba kawai se nacewa mutane su tafi wani guri bayan
kuma duk wanda suka zauna din yawanci yan uwan mu na Kumo dana Yola ne yan gidan mu
wasu suna can gidan su Yusuf wasu sunbi Alawiyya, su cewa sukayi ma badan dare ba
da tuni sun jiya abin su su kuwa wadannan yanzu ince su tafi ai an samu na yawo
dani a dangi ko.

Washe gari kuwa kafin sha biyu kowa ya watse ya rage daga ni se halina a cikin
gidan. gurin qarfe biyu qannen Yusuf mata da maza suka zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login