Showing 24001 words to 27000 words out of 238465 words

Chapter 9 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

ta leqa ta tabbatar babu kowa sannan ta dannawa Addah kira dan
kwatakwata bata samu sun tattauna komai ba dan Bashir na gida kusan ko yaushe in ya
fita kafin tayi ayyukan ta gudun bala’insa kan ta gama ya dawo ita kuma Addah ba
karatu ta iya ba bare suyi chatting Ummi ba shiri suke ba bare ta karantawa Dadan.
Seda ta jera mata kira biyar sannan ta daga dan so take suyi shawarar abinda za’ayi
kafin subar wurin Dada tunda itace makamin yaqin nasu.

Addahn na dagawa babu gaisuwa ba komai tace“Addah gamu a gidan Dada fa kuma da safe
ze tafi haryanzu beyi maganar tafiyar tawa ba”

“Au nida naji ki muqus ai nazata komai ya kammala dama yanzu nake so nakira ki wato
tunda kura tayi lafiya har kin manta dani”.

“To dai ba lefi Addah, yanzu dai ya za’ayi kinga da safe fa ze tafi”.
Motsin da ta jiyo ya saka ta saurin cewa Addah “nidai kishiga whatsapp dinki
kiyimun voice na abinda zance mata dan wallahi muka bar nan kinsan dai ba iya
magana zan masa ba” tayi maza ta kashe wayar.

Fainusan ce ta dawo, gaisawa kawai sukayi ta shiga hidimominta batareda ta sake
koda kallon Amira ba dan basa shiri. Ta girmewa Amiran amma tunda ta Auri Bashir ya
zamana dan girman da take basu ma ta dena a cewarta yanzu matsayin Yaya take a
gurinsu tunda tana auran Wan su dukda dama dai tun usuli ba Kunya ce da ita ba.

Tana zaune tana duba waya kusan minti goma sega voice din Addah tayi maza ta kunna
tareda saka wayar a kunne

“Kinajina bude baki zakiyi ki mata magana kice befa ce miki ki shirya ba dan haka
tayi masa magana dan gaskiya fa ke kina cutuwa bazaki zauna ba” qasa rayi da murya
sosai kafin tayi mata reply tace

“Addah anya kuwa Dada fa yanzu surukata ce nifa wallahi kunya nake ji”

“To dan ubanki se ki zauna ai, kina dai jin abinda Jummai yar Bori ta fada tace
indai ba kusa dashi kika koma ba babu aikin mu da zeyi tasiri to tun wuri kafin
wannan din da muka dan samu yayi ya sake shi kiyi ta kanki” Addah ta fada cikin
masifa.

Shiru Amira tayi tana jimamin abun a ranta anya kuwa zata iya dosar Dadan dan duk
wannan abun Addah ce takeyi mata yaqin amma fa yanzun ne kadai damar ta. Bata da
burin daya wuce ta Mallaki Bashir ta same shi sama da yanda Anty Asma’u ta same
shi.
Ita ma yaringa yawo da ita a gaban mota duk inda ze shiga ya nuna ta a matsayin
matarsa ya kuma ringa nuna yana sonta a gaban kowa.

Tana zaune tana wasiqar jaki Dada ta leqo dakin, “Amirah kina zaune shiru ki fito
palour kici abinci” Dadan ta fada

Da “toh” ta amsa kafin ta yunqura tabi bayan Dadan Fainusa ta rakata da harara
tareda tabe baki dan taji maganar Amiran batasan dai Me Addah ta fada ba ko akan me
suke maganar.

A palour kuwa Bayan Amira ta zubo abinci ta zauna tana tsakura Dada kuwa Ta maida
hankalin ta kan Tv dan dama ita bame sakewa da mutane bace. Amirah ta dago yafi sau
goma da niyyar yi mata magana seta kasa daga qarshe dai tayi qundumbala kamar an
fuzgo maganar tace

“Dada kiyiwa Yaya Bashir magana gashi har gobe ze koma beyi zancen tafiya ta ba
kuma” ta qarasa tana sunkuyar dakai ganin yanda Dadan take kallonta. Shiru Dada
tayi kamar bazata tanka ba se kuma ta sauke numfashi tace

“Munyi magana da Addah na gaya mata ki zauna anan tunda tun farko da ya baku zabin
jeka ka dawo ke kika qi kafin ma Asma’u ta fara aiki lokacin dan haka yanzu bana
son wata fitina ta sake tasowa ki yi haquri ki zauna a inda ya ajiye ki ko dan
lafiyar jikin ki ma yanzu kama ta yayi ki hada hankalin ki guri guda kiyi fatan
Allah ya sauke ki lafiya”.

Seda Amirah ta harari Dada qasa qasa wanda sarai tana ankare da ita kafin tace “Toh
ai Dada lokacin ma shi yace nace na fi son zama anan din Anty ze bari acan kuma
yanzu ma bani nake son komawa ba ai saboda Dan sa ne nake son zama a kusa dashi”.
Ido bude Dada take kallonta har ta qarasa, bata iya ce mata komai ba illah
“Allah ya rufa asiri” ta maida kai ga kallon da takeyi dan abin yafi qarfinta kuma.

Amirah jin tayi shiru ta tabbatar da bazata sake cewa wani abu ba, se sannan ta
gano wautar da tayi cikin salon son kare kai ta fara cewa “Dada ba abinda kike
tunani bane wallahi ni kawai...”

“Idan kin qoshi ki kai abincin kitchen zan koma gurin Alhaji in Bashir sun dawo ina
can” Dada ta fada tana miqe wa jin da gaske so take ta baro wata maganar in ba haka
ba menene kuma nayin bayani gaskiyar magana Addah ba tayiwa yarinyar nan goyon
kirki ba ace yarinya bakinki babu control a gaban kowa ki fadi duk abinda yayi
miki, Allah ya sawwaqa toh.

Tana fita Amirah ta shiga kiran Addah a waya tana dagawa ta sakat mata kuka tana
cewa “Addah kin gani ko nace miki bazan iya ba kince sena mata magana gashi yanzu
na bata komai”

“Dan ubanki me kika ce mata a garin yaya? Rashin hankalin naki kikayi ko ni wallahi
na rasa wace Asararriyar yarinya ceke da komai baki iya siyaya da kissa ba se wauta
da rashin hankali kika saka a gaba yanzu me kika ce da ita?”

Tsaf ta gaya mata yanda sukayi da Dadan, Ajiyar zuciya Addah ta sauke kafin tace
“Ni na zata ma wani babban abu ne rabu da ita na lura Nafi so take ta kware mana
baya amma bata isa ba wallahi yanda ta saba tursasashi yayi abu yanzun ma haka
za’ayi. Ki kwantar da hankalin ki ki rabu dasu muna zaune se ya dawo ya dauke ki
wallahi in sun san wata basu san wata ba kedai yi qoqari ki amshi wani abu a
hannunsa a turawa Malam a qarasa aikin nan Idan muka samu yanda muke so ko ita
Nafin se mun so zata ganshi” fanfo ta cigaba dayi mata da bata dabarun yanda zata
wanki Bashir din kafin sukayi Sallama.

Gajia tayi da zamanta zame takwanta akan kujera bacci ya kwasheta, Bashir kuwa se
qarfe goma ya dawo gidan, seda yaje sukayi sallama da iyayensa kafin ya shiga
palour ya ganta harta fara bacci. Tashinta yayi suka tafi basu koyi sallama da Dada
ba. Da suka isa gida ma kwanciya tayi dan baccin yaci qarfinta.

Washe gari tun Kafin a kira Assalatu ya tashi Amirah, tana qunquni tana komai seda
yasa ta gyara ko ina dukda beyi datti ba tunda kwana biyun tana kula da komai.
Qarfe 6 suka sauketa a qofar gidan Addah, be shiga ba dan haushin Addan yakeji
haryanzu dama basu sake haduwa ba tun waccen ranar dukda har kasuwa yaje ya gaida
Baban Amiran kamar yanda yakeyi duk sanda ya shigo gari, duk yanda Amiran taso ya
shiga wi yayi yace ta gaisheta kawai sauri yake qarfe 7 jirginsu ze tashi sannan
ya kawo 50k ya bata sukayi sallama Naziru ya kaishi Airport ya juyo da motar.

Murna gurin Addaha kaman wanda ya basu 50M. Shi dama bame kyautar kudi bane idan ze
tafi dai komai ze ajiye mata na amfani sanda tana zama a gidanta Ummi taje ta
tayata zama. Da ta koma tafiya gida ma be fasa ba duk qarshen wata ze sa akai Buhun
shinkafa carton din taliya, macaroni da Indomie harda Mai da Maggi ga Kayan Tea
sannan in ze tafi ya bata 10k kuma duk sati yana saka musu Katin waya na 1k ita da
Asma’u Idan kuma zataje Asibiti Nazir ne ya ke kaita ya dawo da ita.

“Yanzu cire Goma ki riqe a hannunki bari na kirawo Malam ya turo a karba in kuma A
Akawun za’a saka masa toh. Nidai Alkahiri ya hada mu da Me Keken nan shekara da
shekaru muna yawon rabar da kudin mu a banza babu biyan buqata kinga rana daya mun
tsinci dami a akala” Addah ta fada tana qoqarin kiran wayar Malam Wizy, kira Daya
biyu ana ce mata Switch off amma bata lura bama se sake kira takeyi, wayar ta
miqawa Amirah tana cewa

“Ke jimin me matar nan take cewa be wayar taqi shiga”

“A kashe take Addah” Amirah ta fada bayan ta sake kira.

“To bari mu saurara zuwa anjima na sake kira dan bazanyi wasa ba gara ayi wuta wuta
a gama aikin nan bari ma Babanku ya fito inaga yau ze bamu ribar mu duk na hada a
tura masa kawai a qarasa”.
Ita dai Amirah neman guri tayi ta kwanta dan bacci ne fal idonta.

Har kusan Magriba Addah na gwada layin wizy baya shiga, seta kalli Amirah dake cin
Abinci a gefenta tace “Bari kiga na kira Hajia Balaraba itama tunda muka dawo ba
waya da alama ta samu kan gidan se muji idan ta kama gobe mu koma kawai ko da
abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai nan ta maida akalar kiran kan
Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari akan Gobe
idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da
suke uba daya ta haihu).

Gidan Hajia Balaraba

Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin
me zatayi, wai itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune
tana tunanin me zatayi, wannan hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa
ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman taimako ba? Dole da sake idan dama
taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi a zuciyarta har
zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta
miqe tana cewa

“Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo
mana ba kuma iya dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama
da sace sace shi....” kallon da yake binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar
ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin zuba tuwo abinta dan tana
wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba.
“Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan
dukda be gani ba ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan
ba yau ta saba ba ita idan ta tashi abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha
kowa da kowa take hadawa na gidan.

Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya
kwarara miyar a sink din ya bi da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa
ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo ya bude, murmushin takaici yayi
zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be bata lokaci
ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining.

Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya
bar Balaraba a tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta
taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma
ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau amma bata da rabo sena baqin
ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya.

Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje
da kanta ba se tayi aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta
ba gara ta samu wanda ze yi mata komai da kansa bate ma har ta kuskure asake
kamata.

Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin
kiran Addah ta gaya mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa
mata ta bashi wayar cikin mamaki ta miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu
yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace
“Wallahi ko da wayar wani kika karba kikayi amfani da ita ki kira wani Boka Ban
yafe ba” ya sa kai ya fice ya barta da baki a bude.

Matakan tsaro na gaske ya saka mata ba waya ba fita ita ma kuma ya hana kowa zuwa
gurinta har kuwa da Yayanta da suke gidan aure. Ruqayya kanta cewa yayi ta tattara
ta koma Hostel haka me aikinta yace karta dawo ta zauna ta qara hutawa na wani
lokaci duniya fa tayiwa Hajia Balaraba zafi Raba zafi inuwa quna gashi babu abokin
shawara ita da Alhaji kuwa sedai tajiyo qarar bide qofarsa ko rufewa.

Seda Addah ta jera kwana biyu tana kiran Hajia Balaraba da Wizy dukka bata samu ba,
ranar Talata ta yanke shawarar zuwa gidan nata ta gano ko lafiya.

Dakyar da sidin goshi Me gadi ya barta ta shiga shima seda tayi masa qaryar Ita Yar
uwar Hajia Balaraba ce suna ta kiran wayarta ba’a samu shine tazo taji ko lafiya,
be barta ba seda ya kira Alhaji ya shaida masa sannan yace ya qyaleta ta shiga.

Halin da taga Aminiyar tata ya girgiza ta nan ta shiga tambayar ta meya faru, Hajia
Balaraban na kuka ta shaidawa Addah komai harda sharadin da Alhaji ya gindaya mata.

Addah tayi buqwi tana sauraronta kafin tace “Ikon Allah kinga dama akace magani
dace ne to ni kuma kinga dai mun dace wallahi dan yanzu lafiya lau abubuwa suke
tafiyar mana. Kema din nasan akasi aka samu wannan shegiyar ta ganki amma da
abubuwan sun kammalu na tabbatar yanzu wani zancen ake ba wannan ba Allah dai
yajiqan Malam na kan tufu shine Maganin Fitinannen Alhajin nan naki mtsw” taja
tsaki kafin ta dora da cewa

“Yanzu dai ai cewa yayi idan kika qara zuwa ko a sharadij nasa shikenan kiyi
zamanki ni zan koma insha Allahu za’a gyaro komai base kinje ko kunyi waya ba”

Cikin jin dama dama Hajia Balaraba tace “Yawwa Aminiyata shiyasa nake qaunar ki
wallahi yanzu to zaki gane gurin? Dan Allah idan kinje ki gaya masa so nake ayi mun
maganin Alhaji yafi da kamuwa yanda ko kara na ajiye ba ze tsallake ba ke ko magana
in banace ya bude baki ba karya yi”.
Da haka sukayi Sallama Addah ta kama hanyar zuwa Gurin Malam Wizy.

Tiryan tiryan ta nunawa Me Adaidaita hanya har qofar gidan Malam dan Addah akwai
gane hanya, da dan mamaki ta kalli shagon na Malam Wizy da ta gani cike da kayan
provision ana siyar wa. Gaba tacewa Me Adaidaita ya qara ko basu zo gidan ba sedai
har suka kai qarshen layin suka jiyo babu wani gida me kama dashi ma.

Fitowa tayi ta tsaya dason tabbatar da nan din ne gama dakalin da suka ga yaran nan
a zaune ranar, qarasawa tayi gurin me shagon suka gaisa kafin tace

“Dan Allah tambaya nakeyi me shagon nan”
“To hajia ai gani”
“Aa ba kai ba Malam nake nufi” ta bashi amsa.
“Malam kuma Malam wa?”
Wata sabuwa inji yan caca ita ai se yanzu ta tuna da ko sunan sa bata sani ba,
cikin ta ne ya bada qululu ta daure tareda korar abinda zuciyar ta take hasaso mata
tace

“Malam dai wanda yake zama a shagon nan Mijin Maimuna me wannan gidan” ta fada
bayan ta tuno da sunan matar malam din.

“Toh gaskiya hajia ban san wanda kike nema ba, hasalima nan shagona ne nafi shekaru
goma ina saida kaya a ciki gida kuma da kike magana ba gida bane kangone da
Almajiran waccen makarantar suke kwana zaki iya leqawa ki gani” me shago ya fada
yana nuno mata makarantar daga nesa.

Addah bata qi ta tashi ba ta leqa gidan, kamar yanda ya fada kuwa incomplete ne ta
cikin ga kayan Almajirai nan tsubi tsubi, wata hajijiyace ta kwasheta jin zancen da
wani saurayi da yazo siyya shagon yakeyi

“Tab Malam Musa Allah dai yasa ba itama tafada komar Wizy bane dan a satin nan mata
sunfi Goma da suka zo neman Malam” yana kaiwa nan ya karbi kayansa yayi gaba yana
wa Addah dariya.

Allah sarki Addan mu Allah maida Asara 😂😂😂
https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 12

Lagos

Asma’u bata tsammaci dawowar Bashir a yau litinin ba ganin tun ranar Asabar din be
ko sake bi ta kansu ba dan haka koda ta tashi aiki ta biya ta dakko yaranta suka
wuto gida.

Bayan Sallar Isha suna baje a palour, Dan wake sukayi abinsu sunaci suna kallo
sukaji tsayuwar mota. Basu kawo shi bane dan baya haura 6pm a waje tsananin hold up
ne ze riqeshi zuwa Magriba yanzu kuwa har 8 ta gota shiyasa ma suka fidda ran
dawowar sa a yau dukda dai tasan akwai aiki to qila excuse ya dauka.

Bude kofar da akayi ya saka su juyawa gaba daya , Bashir din ne hannunsa dauke da
rigar coat din sa se waya a kunnensa. Da gudu yaran suka nufe shi suna murna, taso
ta basar amma wata zuciyar tace “ki tura masa aniyar sa” se itama ta miqe tana
gyara zaman hular kanta ta nufeshi.

Side Hug ya mata tareda pecking goshinta bayan yaran dukka sun ruga mota debo kayan
daya bari dan sun saba in dai ze dawo se yayiwo musu tsara ba ita kuma ta karbi
rigar hannunsa tayi gaba ya rakata da ido bayan ya zauna a daya daga cikin kujerun
palour ya ci gaba da amsa wayarsa.

Ruwan wanka ta hada masa kafin ta fito masa da duk abinda ta san ze buqata. Sanda
ta fito ya gama wayar yana tsakiyar yaran da suke zuba masa surutu se murmushi
yakeyi Muhammad na kan cinyar sa yana cin Pizza.

“Oh bama za’a jira ni ba kenan ko” ta fada tana daga Muhammmad din kafin ta ci gaba
da cewa
“Oya kowa ya kwashe nasa duk kunyi scattering palour,ga plates din nan ma ba’a
kwashe ba”.

ledojin suka shiga tattarewa kowa ya dauke tasa suka shige kitchen su ajiye seta
juya ta kalleshi shima ita yake kallo. Murmushi me kyau tayi masa tace “Yallabai ai
mun zata se gobe, ga ruwan wanka can na hada maka”

“Jazakhillah” ya fada yana miqewa dan a gajiye yake sosai, tunda ya diro be huta ba
aiki sosai yau yasha a office din ba. Sanda ya fito daga wanka tana zaune akan
kujerar dake dakin sa. Ita ta taimaka masa ya shirya kafin ya tada Sallar isha ita
kuma ta fita hado masa Tea da yace ta kawo masa.

A babban Mug ta hada ta saka masa madara da Ovaltine sosai banda sugar se Cake din
da tayi musu na makaranta ta zuba masa a bowl ta hado akan dan Try ta fito. Sun
gama ciye ciyen an tafi yin Brush se Jafar kadai dake tsaye yana jiranta.

“Ya akayi” ta tambayeshi
“Gurin Abbi zani na tambaye shi abu”
“Muje toh” ta fada tayi gaba yana binta a baya.

Suna shiga dakin ta ajiye masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login