Showing 114001 words to 117000 words out of 238465 words

Chapter 39 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

bari na
kiraka naji ko kunyi magana yau shikenan se an jima" na kashe wayar. Daga yanayin
sa sam banji cewa wani abu ya faru ba to me yasa Rahma zata kira ta daga mun
hankali??

Qoqari nayi na yakice tunanin daga zuciyata muka shirya muka tafi masallaci, ina
cikin yin shafa'i da wutri wayata da sam na manta ban saka ta a Silet ba ta dauki
qara lokaci daya gaba ya yanke ya fadi da har seda na dafe qirji na shiga nanata
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuciyata.

Ina sallamewa na jawo wayar na duba, Alawiyya ce ta kirani, sena miqe kawai ina
shirin bin bayanta wani kiran ya shigo sena yi saurin daga wa na saka wayar a
kunnena.
"Ma'u bansan daga ke har mijinki yan kutumar uba bane se yau, anya ba asirce ki
yayi ba kike zaune dashi ya kulle miki baki? yanzu ace za'ayi miki kishiya duk
duniya ki kasa gayawa kowa sema ki tsallake kibar qasar wai kin tafi Umara sedai
kawai muji a gari, shikenan ai Bashir ko gaki gashi nan tun ba'aje ko ina ba kin
fara karbar saka makon ki a hannunsa".

A duk maganganun Alawiyya babu abinda na tsinta banda kalmar kishiya data fada,
seda na da dage piller masallaci jin jiri yana neman kadani.

"Lallai wato ga mahaukaciya tana magana kin yi mun shiru ko Ma'u, shikenan amma ki
tabbata kin nemi wata yar uwar da zaki raba baqin cikin Bashir da ita dan wallahi
bazaki dora mun hawan jini da takaicin mijinki ba, mtsw" taja tsaki.

Seda nayi da gaske na iya bude baki nace
"Alawa ni duk ban gane abinda kike nifi bane waya gaya miki Bashir yayi aure?"

"Kina nufin baki sani ba to maza shiga whatsapp yanzu na tura miki hotuna kigani
se ki tabbatar wa idon ki" tafada kafin ta kashe wayar.

Wata wawuyar Ajiyar zuciya na sauke lokacin da naga hotunan da Alawiyya ta tura
mun. Hotunan Bashir ne da Amirah tareda sauran yan uwan su wanda na tabbatar na
daurin auran Amiran ne amma ai na zata se gobe Asabar aka saka a katin data tura
mun kuwa.

Da daddaya na ringa binsu da kallo Bashir yaci uwar Babbar riga fara gasu Addah nan
baki ya gonar Auduga an washe shi ina shirin bude na qarshe da naga kamar kati ne
kiranta ya sake shigowa.

"Yanzu kin yarda ko kuwa dai kina tantama" ta fada".

"Haba Alawa haka kawai kin saka hawan jinin dare daya ya nemi kamani a marrar nan
kike mun zancen kishiya. Amirah cefa kin manta da bikinta akeyi hotunan daurin
auren nefa duk kika bi kika kidima kanki".

"Allah ya yafe miki Asma'u ya nuna miki hanyar daidai, shikenan tunda ni na kidima
kaina ba lefi idan kika dawo hayyacin ki se muyi magana dan naga alamar
kwakwalwarki ta juye Ma'u kina buqatar saiti amma ki nutsu ki sake kallon hotunan
dakyau ga wasu can ma na qara tura miki" Alawiyya ta fada sannan ta yanke waya.

Hotunan na sake bi da sababbin Videos din data turo mun na Amirah data sha kwalliya
tayi kyau suna ta shaqiyanci, akan katin dazu na sake tsayawa na bude shi na fara
karanta abinda aka rubuta.

"DAURIN AURAN ENGINEER BASHIR AHMAD DA AMIRAH MURTALA" Abinda na gani an rubuta
kenan, daga Bashir din har Amirah ko daga bacci na farka naga sunansu na san sune
ballantana wannan ga gurin daura auran nan masallacin dake layin gidan Addah ne
hakan ya sake tabbatar mun da gaske dai Nawa Bashir din ake nufi bawai wani na
daban ba.

Wayar hannuna ce ta dauki qara, ban san ya akayi na daga kiran ba nidai naji muryar
Anty Halima tana cewa

"Asma'u dagaske ne ko wasa yanzu a duniya Bashir ya rasa irin cin Amanar da ze yi
miki se ya tura ki wata qasa sannan ya daura da yarinyar da kika riqe?"

Iya abinda naji kenan lokaci daya tsikar jina suka zuba kaina yayi mun dum kamar
wadda aka kwadawa guduma daga nan ban sake sanin inda nake ba se farkawa nayi na
ganni a gadon Asibiti.
Waya ta da nagani a gefena na jawo na sake budo hutunan dazu dan in tabbatar
gaskiya ne ko qarya. Ina kunna Data kuwa kamar ana jira messages rututu suka fara
shigo mun alamar dai magana ta baza gari ga status din yan gidan su Se a sannan
ma naga status din Jama'a ashe an yi posting hotunan sosai hankali na nae bekai kai
ba.

Tun yaushe aka shirya hakan? Daman Bahsir da Amirah suna soyayya ina zaune dasu ban
taba ganin wata alama ba?

Wai ma me nayi wa Bashir a rayuwa dana cancanci irin wannan sakayyar bayan tarin
dumbin sadaukarwa da Alkhairan da ni da yan uwana muka yi masa.

Wane irin mugun hali ne dani da har ya kasa gayamun zeyi aure sedai naji a duniya
bayan daya rigada ya daura me nayi masa dan Allah?

Sannan Ace duk matan duniya manya da yara farare da baqar fata Bashir ya rasa wadda
ze aura se Amirah yarinyar dana gama bautawa tun tana qanqanuwarta har girma yanzu
ace da ita zanyi zaman kishi yarinyar data san sirrina, na bude mata duk wasu
sirrika da nake taqama dasu saboda yanda na dauketa tamkar qanwata na gyarata
saboda ta samu daraja a gurin mijin da zata aura yanzu ashe duk mijina nayiwa
wannan tanadin? Ni za'a yaqa dasu?

"Yah ubangiji kaika halicceni, kai ka tsara mun rayuwata tun kafin wanzuwa ta a
doron duniya Allah kasan zan iya shi yasa ka dora mun na roqeka nayi tawassali da
sunayen ka tsarkaka nayi tawassali da Annabin ka Muhammad SAW Allah in har sunyi
dan su cutar dani na roqeka karka basu ikon ganin gazawa ta, ka sanya min juriya da
dakiyar tun karar duk wani qalubale da zan fuskanta a rayuwa. Ubangiji ka sauqaqa
mun dau wani ka bani zuciyar da zan iya dauka" na fada a fili ina fashewa da wani
irin kukan baqin ciki.

Wallahi ko kadan banji haushin auran da Bashir yayi ba, da ace wata ce daban zan
shanye na danne bazan taba nuna masa komai ba har in ga iya gudun ruwan sa amma
Amirah fa Amiran Addah me yasa se Ita? Da ace Ummi qanwarta ya aura nasan bazan ji
baqin ciki irin wanda nake ji yanzu akan auran Amirah da yayi ba.

"Amirah zata dawo gidan nan kuma a sannan baki isa ki koreta ba" kalaman Addah suka
dawo mun a kwakwalwa ranar da na kori Amirah daga gidana a Gombe. Ashe abinda suka
shirya yi mun kenan daga ita har Dadan suka dakko kishiyata suka kawo mun da nufin
na gyarata su kuwa wasu irin mutane masu saka Alkahiri da sharri ta ina na kuskure
musu a rayuwa da suka zabi hukunta ni ta irin wannan hanyar?

Kuka na ringayi wanda tun likitocin da suka dubani suna bani haquri har suka haqura
sukayi shiru, bana buqatar sauran bata lokaci a qasar tunda daman ba dan Allah ya
turani ba dan ya aiwatar da nufin sa ne to yaci galaba amma nima dole na koma
Nigeria muyi wacce zamuyi da Bashir dan bazan taba hada miji da Amirah ba.

Yana da damar ya auro mun mata uku mu zauna amma ba Amirah yarinyar da nakewa
Kallon Yata ita ce ze hadani kishi da ita baze sabu ba.

Sanda na koma Hotel din da muke na tarar da yara zuru zuru dan da aka kaini Asibiti
can suka koma saboda a qa'idar su ba'a barin dan jinya.

"Ku hada kayan ku yau zamu tafi" na fada ina hargitso duk abinda hannuna ya kai
kansa ina sakawa a jaka. Seda na gama sannan na tuna da ai Passport dinmu ma baya
hannunmu yana gurin Agent din da Bashir ya hadamu dashi, wayata na dauka na shiga
kiran nayi sa'a tana shiga ya daga.

"Malam Isah kayi mana booking jirgi idan da akwai Yau ka, ka fada mun kudin ko
nawane zan biya wani abu ya taso mun bazan iya jira har se gobe ba" na fada ba
tareda na amsa gaisuwar daya fara mun ba.

"Amma Hajia me ya faru haka, bayan haka kuma ai Ticket din ku bana komawa Nigeria
bane Dubai zaku wuce daga nan na zata ai Engineer ya gaya miki ma"

"Isah dakai da Dubai din da Engineer kunci abu ta kazan ubanku" na lailayo wata
Ashar me maiqo da ni kaina bansan na iya ta ba na kora masa kafin na ci gaba da
cewa

"Ka kawo mun passport din mu nan da Awa daya idan ba haka ba wallahi se nayi qarar
ka nace safarar mu kayi, kasan ina da duk wasu bayanai naka da zan bayar ka kuskure
lokacin baka zoba ka gani".

"Kiyi haquri hajia ku shirya yanzu zan turo mota da zata kaiku Jiddah ni ina can
yanzu haka akwai jirgin da ze tashi yau da daddare bari na bincika idan da akwai
guri se a siya" Isah ya fada jin abin yafi qarfinsa.

A dakin muka bar kusan rabin kayan mu dan bana buqatar abinda ze bata mun lokaci
bate har aje ana maganar wani awon kaya ko wani abu muka hau mota se Jiddah gaba
daya ma gani nayi motar bata sauri, ina ma ace zan iya rufe ido na ganni a Nigeria,
ina buqatar naje naga da wadanne idanu Bashir da danginsa zasu kalleni.

Mun samu jirgi amma se munyi jiran Awa goma sha biyu kafin tashinsa, haka Isah ya
nema mana hotel gaba daya ya rasa meya faru haka gashi kiran duniya Bashir yaqi
dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar gaba daya Asma'u kuwa bega fuskar da ze mata
tambayar abinda yake faruwa ba ma dan haka yaja Aliyu yana tambayarsa ko mutuwa
akayi

"Nima ban sani ba, kawai daga Masallaci aka kaita Asibiti kuma data dawo mun kasa
tambayarta abinda ya faru idan mukaje gida koma menene se mu gani" Aliyun ya bashi
amsa.

Haka muka hawo jirgi se Nigeria ya sauke mu a Kano,Asuba ranar lahadi muka sauka
tun a AirPort na samu shatar mota ta kwashe mu kafin Goman safe mun sauka a Gombe
muka ci burki a qofar gidan su Bashir cikin Sa'a nayi kyakykyawan gamo da Ango
Bashir da tun daren Alhamis rabon da ya sake daga wayata.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 39

A qofar gidan motar mu ta tsaya, idona akan Bashir da suke tsaye tareda wasu mutum
biyu da ban gabe su waye ba.

“Ku jirani karku fito” na fadawa yaran, seda na yi kokawa da duk wani rauni da
karayar zuciyar daya taso mun kafin na bude motar na fito ina gyara mayafin kaina
gaba daya mutanen gurin suka bini da kallo banda Bashir da tunda muka hada ido ya
maida kansa qasa kaman wanda aka kama yayi qarya.

Kai tsaye cikin gidan na shiga, nayi sallama ina jiyo hayaniyar su daga cikin dakin
Dada amma ba’a Amsa ba dan haka na nufi can din, har na kai bakin qofar naji an
kira sunana, sena waiwaya.

Alhajin su Bashir ne yana tsaye daga qofar dakinsa ya yafito ni da hannu sena juya
na koma gurinsa.

Ina durqushe a gabansa kusan minti biyu kafin yaja numfashi yace dani

“Asma’u kiyi haquri nasan an cutar dake amma zan roqeki Arziqi kar kice musu komai
yanzu, ki barsu akwai ranar da su da kansu zasu maidawa junan su martanin abinda
sukayi miki.

Na sani Qarin aure ba haramun bane amma ta yanda aka shirya naki sam be kamata ba.
Ya zama zamba cikin aminci. Ki sani Ita Amana daya ce kuma wanda yacita baya taba
zama lafiya, idan har Bashir da uwarsa sun qulla wannan aure dan su ci mutunchin ki
Asma’u in Allah ya yarda muna raye ko mun mutu se sunga sakayyar cin Amanar da
sukayi miki.

Ina qara roqonki da kiyi haquri, ki qara akan wanda kike yi in sha Allahu bazaki
tabe ba, duk me neman gazawarki akan idonsa zakiyita ci gaba da yardar Allah”.

Kuka nakeyi dagaske a raina ina hasaso irin tarin qaunar da na nunawa Bashir da
Ahalinsa, a tsahon zamana dashi kusan shekara goma sha uku yanzu bazan iya cewa
taka maimai ga wani abun laifi daya taba hadani da wata daga cikin su ba, a kullum
cikin kyautata musu nake iya qarfina kuma duk albarkacin so da qaunar da nakeyi wa
Bashir din ce ta shafi su amma ace a gurinsu basu da abokin hamayya seni.

Sosai nasha kuka na ba tareda Baba ya hanani ba in banda “kiyi haquri Asma’u” babu
abinda yake cewa.

“Naji zan haqura Baba bazan tanka musu ba amma kayi haquri bana jin zan iya ci gaba
da zama da Bashir. Bazan iya ci gaba da zama cikin Ahalin da basa qaunata ba Baba.
Sannan Baba Amirah fa, yarinyar dana raina da hannuna ita zan hada miji da ita
wallahi bazan iya ba.

“Zan bi umarnin ka a yanzu zan koma ba tareda na cewa kowa cikin su komai ba amma
Baba karka roqeni ci gaba da zama da Bashir saboda ina girmamaka bazan iya tsallake
unarninka ba amma tabbas zan cutu. Zuciyata zata iya bugawa a dalilin haka muddin
zan zauna inuwa daya da Amirah a matsayin kishiyata” na fada cikin sheshsheqa me
qarfi.

Se Baba yayi murmushi wanda da ganinsa na takaici ne kafij yace
“Asma’u ke Yarinyar kirki ce sannan abar Alfaharin duk Miji me hankali da yayi
katarin samun irin ki sannan ko wanne uba zeyi alfaharin zamtowarki Suruka a gare
shi.

Bazan so na rasa nagartacciyar suruka irin ki a cikin zuria’ata ba domin ke din
mayafi ce da kika lullube Bashir duk kuma ranar da wannan mayafin ya yaye ba baki
nayiwa Bashir ba tabbas se rayuwar sa ta shiga cikin gararin rayuwa.

Idan har ki ka ce bazaki ci gaba da zama da Bashir ba ni me tsaya miki ne in tayaki
kwatar yancin kanki amma yanzu kije ki samu nutsuwar zuciya, karki yanke hukunci
cikin fushi idan kika nutsu duk abinda kika yankewa zuciyarki ki dawo ni ki gaya
mun in Allah ya yarda zan baki goyon baya dari bisa dari ki share hawayenki yanzu”.
“Baba bana tunanin ina da buqatar yin wani dogon nazari ka taimakeni kawai kasa
Bashir ya sawwaqe mun dan ina da yaqinin ko ba yanzu ba watarana se sunyi nasarar
fiddani daga dakina” na fada cikin kuka, se ya tare ni da cewa

“Haba Asma’u ke da na sanki jaruma ya zaki karaya tun yanzu ki bada qofar da za’a
ci galaba akanki? Maganar su fitar dake daga dakinki kuka babu wanda ya isa yayi
Abinda Allah beyi ba, kije gida ki huta ki bawa zuciyarki haquri idan kuma kinga
bazaki iya karbar Al’amarin ba ki dawo zan tsaya miki”.

“Shikenan Nagode Baba Allah ya qara girma”
“Nima na gode Asma’u Allah yayi miki albarka keda zuri’arki gaba daya”. Haka mukayi
sallama da Baba seda yasakani na share hawayena tas yace naje na dauraye fuskata a
bayin da yake cikin palour sa kafin na fito.

Ina fitowa naci karo da Dada da yayanta sun fito daga dakinta, Yanda kasan anyi
ruwan sama an dauke haka sukayi shiru gaba daya suka zubo mun idanu kamar wanda
sukaga wata sabuwar Halitta nayi musu kudin goro gaba dayabna watsar na nufi qofar
fita.

Sanda Na fita ban tarar da Bashir a waje ba se Naziru suna tsaye a jikin motar da
muka zo tareda yara. Kallo daya nayi masa na kama murfin motar na bude se ya riqe
yana cewa

“Wallahi Anty babu sa hannuna basu gayamun ba se ana gobe za’a daura, da nace zan
gaya miki Dada tace duk wanda ya kuskura ya sanar dake wallahi se tayi masa baki
shiyasa ko Yaya Amiru da kika kira jiya ya kasa gaya miki komai” ban bi takansa ba
na cewa me motar muje na nuna masa hanya ya qara sa damu gidan mu gidan Baffana. A
waje na barsu ana sauke kayan mu bayan na sallame shi na wuce ciki.

A yanzu babu abinda nake buqata sama da na kebe ni kadai a inda zan sha kukana kar
wani ya rarraahe ni. Dakin Hajia Babba nayi masauki na haye can qarshen gadonta na
saka kaina a cinya na ringa rirgar kukan da wadda akayi wa irin abinda akayi mun ce
kawai zata fahimce ni, tambayar kaina nakeyi me nayiwa Bashir a rayuwa daya
qullaceni yaga ta haka kadai ya kamata ya rama.

Ina jin matan gidan mu suka ringa shigowa suna bani baki amma na toshe kunnena,
nasha kukana seda naji Numfashi shina yana barazanar daukewa kafin na bawa kaina
haquri na koma sauke ajiyar zuciya kawai ga wani masufaffen ciwon kai daya dirar
mun maqogarona kuwa kamar ze tsage saboda bushewa dan in ban manta ba rabonda ko
ruwa ya wuce ta cikinsa tun kafin na samu wannan baqin labarin.

Har dare ina cikin dakin sallah kadai na tashi nayi na koma na kwanta ba tareda na
ko kalli kayan abincin da Hajiyar ta kawo mun ba. Haka ta zauna akaina tana ta
faman yi mun nasiha dana gaji da jinta sena sa mata kuka dole ta tashi ta bani
guri, qarin abinda yake damuna ganin har zuwa sannan banji komai daga Bashir ba, be
zo ba be kuma kirani a waya ba haka na kwana kafin safiya jikina ya rijice dole se
da aka danganani da Asibiti.

Gwajij farko likita ya tabbar mun da jini na ne ya hau sosai abinda ya saukar mun
da mugun ciwon kai kenan ga kuma zazzabi me zafi, shawara ya bani da koma menen
yake damuna nayi haquri na kuma fawwalawa Allah domin lafiyata tana gaba da komai,
duk wani al’amari na rayuwa baze tafiyar mun daidai ba idan babu lafiya daga nan
yayi mun Allurai da zasu taimaka mun zafin jikin ya ragu da ciwon kan ya bani
magunguna muka tafi gida.

Seda akayi mun wuqa wuqa sannan naci abinci nasha maganin ban dade ba bacci ya
dauke ni seda na shafe awanni ina yi kafin na tashi.
A yammacin ranar Alhaji Qarami yazo, bashi kadai ba kusan yayyena dukka seda suka
zo gida aka taru masu tsinewa Bashir nayi masu bani baki sunayi. A bakin su nakeji
wai ashe jiya da daddare ma yazo gidan ma, nidai ina kwance ina jinyar zuciyata.

Seda muka kwana biyu da dawowa a daren ranar da daddare ina kwance a daki da carbi
a hannuna ina ja Jafar ya shigo yace wai naje inji Dadyn Abuja. Da dogon Hijabi na
har qasa nayi sallama a Palour Hajia Babba kaina a qasa seda na kai tsakiya sannan
ido na ya sauka akan Bashir da Bala se Abdulkarim Dan Qanin Baban su ne, ba tareda
na qara ko taku daya ba na juya da niyyar fita Alhaji Qarami ya dakatar dani dole
na koma na samu can gefe kusada qofa na zauna ina jin zuciyata kamar an watsa fetur
an cinna mata wuta.

“Asma’u mijinki ne yazo bada haquri shine nace a kiraki tunda ke akayiwa laifi ke
ya cancanci abawa haquri ko” Alhajin ya fada yana kallona, kafin ya miqe yana sake
cewa”ki matsa ciki kin zauna a bakin qofa ga dare idan kun gama ki same ni gurin
Hajia Umma ina son ganinki”.
naji shi sarai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login