Showing 150001 words to 153000 words out of 238465 words

Chapter 51 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

motar suka shiga, haka ya kaisu
makaranta ya ajiye su sannan ya tafi ya siyo musu breakfast a wani gidan abinci
kusa da gurin ya sake kai musu kafin ya wuce office dinsu zuciyarsa kamar zatayi
bindiga saboda takaici.

AMIRAH
Suna fita ta tashi dakyar ta dakko wayar ta ta dannawa Addah kira, a speaker ta
saka dan da gaske fa kunnenta yaji duka tana dagawa ta saka mata kuka tana cewa

"Wallahi Addah na gaji bazan iya ba, haka kawai na zama kamar jaka shi ya dakeni
sannan yanzu takai yayansa su dake ni nidai na gaji tahowa kawai zanyi"

"Ki taho ina? Ni Fattu kashe ni kuke so kuyi ne ko me, nan ga wannan shegiyar ta
dibgo mun abun kunya ke kuma kina shirin kaso auranki ki dawo to bazaku kasheni ba
koma menene yanzu ki dakata mun na kashe wanann wutar kafin ta fasu idan yaso se na
dawo kanki" Addah ta fad cikin tashin hankalin da muryarta ta kasa boyewa.

Cikin rashin fahimtar maganar Addahn Amirah tace
"Addah meya faru? Wane irin abun kunya kuma aka dakko miki badai bashi kika sake
ciwo aka zo ana miki cin mutunchi ba?"

"Yo ba gara in ci bashi ba ko birsin ne a kaini da abinda wannan yar iskar yarinyar
tajawo mun, ciki fa cikina haihuwa Ummi tayo har wata uku yanzu ina zaune ban sani
ba.
To wallahi na gaya mata zubar dashi zamu tafi yanzu ayi dan bazata ja mun abinda
za'a ringa zundena a garin Idan na wuce ba shi kuma shegen matsiyacin da yayi mata
daga baya inyi qararaa tunda ai na raba shi da yata yaqi barinta seda ya dibga mata
ciki tukunna" Addah ta fada cikin masifa se haki takeyi,

Amirah na jiyo kukan Ummi daga gefe tana cewa "ni wallahi baza'a cire ba, haka
kawai ance mutuwa akeyi. Ki kyaleni ai Jawad din ya yarda idan na haihu zamuyi
aure"

"Sedai ki auri ubanki, na gaya miki indai ina raye bazaki auri wannan matsiyacin ba
wallahi" Addah ta zabura tayi kanta, can ta wullar da wayar ma da alama ta manta da
cewa waya takeyi.

Zugudi Amirah tayi da waya a hannu cikin tashin hankali, ciki dai cikin shege Ummi
ta yi to yaushe hakan ta faru? Zama tayi akan gado ta rafka tagumi radadin da
takeji a kunnen ma ya tafi saboda jin sabon tashin hankali yanzu me Alhajin su zece
idan yaji wannan maganar ta tabbatar da sedai Allah ya tsare amma da wuya auran
Addah be mutu ba a dalilin wannan abun amma.

Ummi ta cuce su koda yake ba Ummi ba Addah zatace ta cuci Ummi tunda babu yanda
batayi akan ta barta ta auri wanda take so ba amma ta kafe cewar bazata aureshi ba
saboda bashida komai, shegun da take yawan ambatarsu dashi gashi yanzu ya tabbata
ai seta shirya goya shegen jika.

Wanann maganar ce ta kashe wutar abinda ya faru da safe, haka ta wuni jiki a sabule
batayi musu girki ba daman yaran suna dawowa gidan Ma'u suka wuce shima Bashir daya
dawo yaganta a yanda ya fita ya barta kwafa kawai yayi ya sake wanka ya fice be
kuma dawo gidan ba se bayan data kwanta.

ASMA'U
Da safe ganin harna shirya yara basu shigo yasa nayi tunanin sun koma cin abinci a
gidan su kenan, toh itama Amna ta huta, a tsatstsaye na karya dan ina sauri mukayi
sallama da Amnah ina fitowa na gansu cirko cirko a qofar gidansu fuskar Aliyu dana
kalla ta tabbatar mun wani abu ya faru.

A gabansu na tsaya da mota na sauke glass, dukkan su suka gaishe ni na tambaye su
lafiya Jafar na shirin magana Aliyu ya galla masa harara yace mun babu komai. Sena
tabe baki nace "toh yayi, ina Abbin naku kuke tsaye anan kun kusa makara fa" ina
rufe baki na hango an bude qofar, nasan Bashir ne dan haka nayi musu sallama kawai
na wuce haka nan bana son haduwa dashi kuma.

Gurin qarfe goma ina zaune a office wayata tayi qara, ta true caller naga sunan me
kiran YUSUF IBRAHIM WUNTI ina gani na gane Yusuf ne dan haka na daga wayar na kara
a kunnena tareda yin sallama.

"Barka da rana Hajia" Yusuf ya fada daga daya bangaren sena amsa da cewa

"Barka dai Excellency"
"Ashe baki manta sunan ba" ya fada yana dariya sena mayar masa da amsa da cewa
"Haba dai ya za'ayi na manta, waya sani ma ko sunan ya tabbata yanzu dan Majalissar
Jaha ne kai ko na taraiyya?"

"Haba Hajjaju ai tuni muka tsallake nan, sanata nake meci a yanzu kuma Gomna me
jiran gado in Allah ya yarda" Yusuf ya fada, sena bude ido da mamaki kamar yana
kallona nace

"Dagaske amma babu labari ko a gurin Alaqiyya ban taba jiba ita da take yar
garinku, toh Allah ya tabbatar da Alkahiri kace na kusa zama qanwar Gomna".

"Toh ai baki taba neman koda labari na kinga bazaki sani ba, duk kuma sanda zanje
gida se muyi sabani ace kinso kin tafi shiyasa amma yanzu da Allah yayi zamu sake
haduwa kinga a arha na ganki a hanya, ya gida ya yarana na shigo Lagos ya kamata
nazo na gansu ki sanarwa da Oga kar nazo yayi mun rotse"

Yanda ya fadi rotsen seda nayi dariya nace "ba abinda zeyi maka ai yasan kai Yayana
ne ko, ba damuwa toh yaushe zaka shigo?"

"Injiwa ta ya za'ayi ya yarda da wannan nima bazan fara shigar masa gida ba a waje
zan tsaya ki turo mun yarana na gansu kar naje mun sha haduwa ma ban san su bane ko
da yake bayanda za'ayi naga jininki na kasa ganewa, ina jin ko a taron Arfa naga
wanda ya shafeki sena gane shi wallahi

Zan zo gobe da yamma, idan babu damuwa zan sa a kawo takwarar ki anjima kafin nazo
kin san an kawota gurin Hajia to ban samu na shiga Bauchi ba ita kuma ta saka
rigima se an kawota gurina, inaga na saka a kawota nan din dan idan aka kaita Abuja
ma bani da lokaci acan saboda aiki"

"Ok ba damuwa a kawota, ba tare zasu zo da mamanta ba?" Na tambayeshi, a maimakon
ya amsa mun se yace

"Shikenan se goben In Allah ya kaimu kiyi saving Number ta nasan yanzu ma qila sa'a
naci kika daga tunda baki da ita"

"Ai naga sunan a true caller na gane kaine, Allah ya kaimu goben a gaida Madam"
daga haka mukayi sallama.

Dana tashi a hanya naga wani boutique da suke siyarda rigunan yara masu kyau, na
tuna gobe ne fa Graduation partyn su Amna jibi kuma suyi prom kuma Faridah bata da
kayan da zata saka goben dan haka na tsaya a gurin na siya mata riga me kyau, har
na gama na tuno da za'a kawo mun wata yarinyar dukda bani da tabbacin ze bar mana
ita ne ta kwana a nan nace bari na siya mata.

A hoto dana ganta dai nasan bazata wuce tsahon Abdallah ba amma dan na tabbatar
sena kira wayar Yusuf amma line busy
Text yayi mun cewar yana busy akwai wani abune?
Sena mayar masa da cewa menene tsahon Takwara da size din takalminta ba'a dauki
lokaci ba ya turomun kuwa na siya mata kalar ta Faridan da takalmi harda su Ribbon
dan naga tana da gashi kafin na wuce gida.

Ina zuwa na tarar dasu sunyi kaca kaca da gidan na kuwa hausu da Fada akan su gyara
na wuce dakina ina shiga Jafar ya biyo ni a baya tas ya kwashe abinda ya faru dazu
ya gaya mun.

Sosai raina ya baci akan abin, wane irin rashin hankali ne ze saka Aliyu ya daki
Matar Babansa da ko bata aure shi ba matsayin uwa take a gurinsa cikin bacin rai
nace ya kiramin shi na hadasu su biyun tunda sune manya nayi musu tatas nace kuma
idan ya koma ya bata haquri sannan na kira sauran na tara su gaba daya na sake ja
musu kunne akan duk wanda na sake jin ya mata ko kallon Banza ne se ransa yayi
bala'in baci, haka na wuce daki na barsu Aliyu ya cika kamar ze fashe har na tafi
na koma na sake masa warning akan karya kuskura ya taba Jafar dan nasan qarshe se
ya huce haushin gayamun da yayi akansa.

Ina Wanka najiyo wayata na qara, da yaje na kammala sena dauro towel na fito kafin
na daga ta katse sega wani kiran ya sake shigowa.

Yusuf ne, ina dagawa muka gaisa yace
"Gata can a waje sunzo amma taqi fitowa daga mota, dan Allah ko zakije ki lallaba
ta idan kuma taqi su wuto da ita kawai nan bansan ya zanyi da ita bane meeting
mukeyi nasan zan iya kai qarfe biyu ma kafin na gama".

"Zama ta yarda in sha Allah bari naje na gani" na fada kafin na kashe wayar. Dogon
Hijab har qasa na zura na saka takalmi na fito har sannan yaran suna zaune suna
kallo, Abdallah na ganin na fita ya biyoni, a qofar gida naga motoci guda biyu masu
numfashi da wasu qarti su biyu a gaban daya daga cikin motar.

Number Yusuf na sake dialing tana shiga ya katse se naga wayar daya daga cikin
qattin tayi qara ya daga da sauri kafin ya juyo inda muke se gashi da dan gudunsa
ya taho gurin.

Cikin girmamawa kamar ze durqusamun ya gaisheni cikin harshen turanci kafin ya
nunamun motar da take a rufe yace tana ciki.

Gaban motar na qarasa na kwankwasa super tint windown motar, kusan minti daya aka
sauke shi wani ni'imtaccen qamshin yan gayu ya daki hancina har seda na lumshe ido
kafin na bude fuskata dauke da murmushi na kalli cikin motar mukayi arba da wata
farar mata irin fara fat din nan dan duk farina se na ganni na zama wata kala a
gabanta siririya me dogon gashi da ta barshi a bude, a yanayinta ma zan iya kiranta
da bauturiya ko kuma dai ruwa biyu amma ba hausa ko Fulani bace wannan.

Qara fadada fara'ata nayi, dan naga yanayin yarinyar Yusuf a fuskar ta dan haka na
tsammaci itace matarsa, cikin harshen turanci na miqa mata gaisuwa dan bana tunanin
wanann zataji hausa, ta amsamun a wani yatsine har seda abin ya sosamun rai nan da
nan kuwa nima na datse fara'ar dan ban son wulaqanci a rayuwata.

Cikin yauqi da iyayi tace mun "kece Asma'u?"
Sena daga mata kai kawai ina kallonta ta waiwaya daya bangaren da bana hango wanda
yake zaune tace
"Sweetheart kije ga Namesake dinki nan zaki zauna a gurinta, ki zama yarinyar kirki
kinji"

Cikin muryar yara da kanaji kasan yaron ma sangartacce ne Yarinyar ta fara mana
tana cewa
"Ni bazan je ba gurin Dady na zanje"
"Dadynki bashi da lokacin ki na gaya miki kece kike ganin yana sonki amma baya
sonki sam, idan ba haka ba ya za'ayi ki taho tundaga United State amma ya kasa zuwa
ya tare ki sema yace a kaiki gurin wata stranger ki zauna hmm" Matar ta fadawa
yarinyar seka rantse da wata babba Sa'arta takeyi ni kuwa ina daga gefe ina kallon
ikon Allah.

Wannan wace irin uwa ce me qoqarin turawa yarta wata aqida da zata sa ta tsani
mahaifinta?
Ganin dramar bazat qare ba ya saka na zagaya daya barin da take, badan kar Yusuf
yaga rashin kirki na bama qyale ta zanyi su tafi amma bansan dalilin sa na cewa a
kawota ba tunda ga uwarta amma yanzun ma sau daya zan lallabata idan bata yarda ba
su sauka lafiya.

Qofar na bude da murmushi na na miqa mata hannu seta dakata daga bubbuga qafar da
takeyi ta zuba mun ido

"Muje ko kinga dare yayi Momy tana so ta tafi gobe da safe se na kaiki gurin Dady
da kaina" na fada cikin lallashi, seta kalleni ta kalli uwarta data wani tabe baki
ta dauke kai gefe, kai na gyada mata alamar tabbatar wa se kuwa gashi ta zuri
qafafunta sena dagata na fito da ita daga motar ashe ma afili batafi girman Yan
biyu ba.

Qato daya ne ya bude boot ya ciro mata akwatinta ta yangayu me shegen kyau ga wata
qatuwar Teddy da tayi girmanta ma ya wuce da kayan bakin qofa ya ajiye, a taqaice
nayiwa matar sallama na juya seta dakatar dani, ta bude jakarta ta zaro wata farar
takarda ta miqo mun, da rashin fahimta na kalleta se tace

"List na abubuwan da Sweetheart take ci ne"
"Ikon Allah" na fada a fili na sa hannu na karbi takardar na shige gida ina
jujjuyata a hannuna, muna shiga muka tarar suna kallon wani cartoon na Bluey ne
sunan sa kome ta kuwa dage ta kwala sunan a kunnenan babu shiri na ajiye ta ta wuce
da gudu cikin palour, ganin sun cikia ko ina kan kujerun bata tsaya ba ta dane
Cinyar Aliyu da yake kujerar data fi saiti da Tv tayi zamanta.

Se kawai muka tsaya muna kallonta, ita kuwa ba abinda ya shafeta dariyarta takeyi
da alamar tana son abinda take kallon.

"Mami wacece wanna" Aliyu ya fada yana sauke ta daga jikinsa amma taqi saukar, se
nayi murmushi nace "sabuwar qanwa kuka samu tazo mana weekend, gobe Babanta zezo
zaku ganshi" na wuce ciki na barsu.

Akan Mirror na ajiye takardar ina mamakin wannan wace irin mata Yusuf shi kuwa ya
aura ko a ina ya samota se Allah.

Seda na gama shiryawa tsaf na kalli agogo nasan lokacin sun fara shirin tafiya dan
haka na fito, ina sako qafata ido na ya sauka akan Yar Amana tana zaune tayi daidai
tana cin wainar fulawa da Manja da alama yanzu sukayita farar rigar jikinta tayi
kaca kaca ta canza kala.

"Na bani ni Asma'u me kuka bata haka" na fada ina qarasawa gurin da sauri, seta
dago tana yar dariyar yarinta cikin turancinta da kana ji kasan rainon America ce
tace

"Mami da dadi amma akwai yaji"
"Waya ce ku bata Amna me yasa baku tambayebi ba kafin ku bata" na fada ina janye
farantin se kawai naga yarinya ta fara birgima kamar me hawa bori, Amna na dariya
tace
"Wallahi Mami ban san ma sanda suka shirya ba Jafar ne yayi musu gashi can ma yana
soya sauran a Kitchen"
"Kun kyauta, idan cikin yar mutane ya baci se kusan yanda zakuyi da ita ai" na fada
ina akiye mata kwanon na koma na dauko wayata na shiga kiran Babanta.

To a takardar fa wasu lissafin abincinsu can na turawa yan gayu aka rubuta sunzo
sun hadata da fulawa da manja, saurin fa da nayi kenan na fita ko oat ne na saka su
hada mata tasha dan banida tarkacen dana ga an rubuta a takardar.

Nayi Sa'a kira daya ta shiga ya daga yana cewa
"Badai yar rigimar taqi zama ba"

"Wa ai gata can muan shigowa ma ta shiga sabgarta, Mamanta ce ta bani list na
abincin da take ci, todai in gaya maka ina daki kafin na fito su Jafar suka dura
mata wainar fulawa da yaji na dauke na hanata ci ta farayi mun bori shiyasa na
kiraka kar muje cikinta ya birkice ga dare yayi" na fada masa.

Dariya sosai yayi yana cewa "Ma'u kenan sarkin ci ai indai taga abinci setaci ko
wanne iri ne, ki manta da wata takadda na rasa me yake damun Intee Allah yasa dai
batayi miki halin nata na wulaqanci ba"

"Aa ba komai gaisawa kawai mukayi ta tafi, to shikenan ba matsala kenan mu bata duk
abinda muke ci" na sake tambayarsa

"Ki bata komai, dambu fura tuwan dawa ba abinda Hajia bata dura mata a Bauchi tun
bata kai haka ba me kuma ya sameta tsabar matsala irin ta uwarta ce kawai" ya sake
fada, se nace masa

"Allah ya rufa Asiri, goben da wuri zaka shigo dan zamu fita, zamuje Graduation din
su Amna qarfe goma"

"Kai masha Allah har Amna ta gama secondary school dagaske dai tsufa ya fara kama
mu, ba damuwa a wacce makaranta ne idan na samu dama sena shigo nima"

Sunan makarantar na gaya masa mukayi sallama, ina jiyo ihun Ma'u takwara na fita
naga meya faru na tarar wai su Faridah ne zasu tafi ta kama qafar Jafar ta riqe da
gani dai dashi aka qulla abota se tsalle take tana ihun bazasu tafi ko kuma seta
bisu, kamo ta nayi ina rarrashi amma ina qara zillewa take yi, qarshe dakyar na
samu ta haqura shima seda nace Faridah ta zauna ta kwana suka zille sauran suka
tafi na saka Amna tayi mata wanka suka kwanta a raina ina Addu'ar Allah sa kar
Bashir yace zeyi tashin hankali a daren nan cikin Sa'a kuwa har muka kwanta shiru.

WASHE GARI

M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 48



WASHE GARI


Washe garin ranar da wuri muka shirya saboda su basayin African time irin namu na
yan Arewa. Sosai nayi kwalliya da Doguwar rigar Lace baqi me Golden din zare na
yafa mayafina a kafada na saka coge nida kaina na yaba kwalliyata dan na fito cas
dani.

Da muka fito zamu tafi Anty se tsokanata take wai taga alamar fa Zawarcin nan me
lasisi nake zuba to dai nayi a hankali kar na sa maza suringa karo a hanya a garin
kallo na.

Bashir ne ya tafi da yara mazan a motar sa harda Amirah suka tafi, daman bamu hadu
ba a bakin Amnah naji cewar da Amiran aka tafi nayi murmushi kawai a raina ni kadai
nasan tsiyar da zan qulla mata tunda nidai ban gayyaceta ba ai, A motata muka tafi
tareda Anty da yammatan harda sabuwar yata da tasha kwalliya dan tun dare na gyara
musu gashin su ita da Farida sunyi kyau sosai cikin rigar jiya kamar wasu Yaya da
qanwa haka muka rankaya muka tafi.

Sanda muka isa lokacin an fara shiga dakin taron, sallama Amnah ta mana ta wuce
gurin Yan ajinsu ni kuma na tsaya dakko Get pass dan suna motata tun ranar da aka
kai mana ban cire su ba nasan su Bashir ma basu shiga tunda dole su jira pass din,
murmushi nayi sanda na fito dasu na qirga.

Guda goma ne cif, daman guda hudu suke bawa ko wanne dalibi idan kana son qari seka
siya dan haka na qara guda shida ya zama teburi daya muka kama kenan, nida yarana
banda Amnah mu bakwai se Anty ta takwas ga Bashir tara ragowar daya kuma daman na
siyane kawai dan teburin me Goma ne to yanzu ga sabuwar yar da nayi shi kenan mun
cike shi.

Haka kawai naji dariya ta kama ni sanda na hango Amirah yanda taci uwar kwalliya
kai ka rantse wata dinner auren qawarta zata tafi se wani karairaya take a gefen
Bashir hannunta cikin nasa, wani ikon Allah se banji komai a raina ba illah ma
dariya data bani kawai dan a yanda take abun kana gani kasan irin da gayyar nan
take dan ta bata mun bata san ko a kwalar rigata ba.
Mijin nata ma da da na dauka na dora akai yanzu na sauke nima na huta.

Seda na qara gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login