Showing 63001 words to 66000 words out of 238465 words

Chapter 22 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

ya
mayar mun na ajiye kwanon na jawo Babban Mug na tsiyaya masa kunun na saka Sugar
yace na saka masa Madara a raina nace “sarkin son dadi” na gama na tura masa komai
gabansa harna zauna na tuna da kunun Anty sena miqe ina cewa
“Bari na kaiwa Anty kunun nan”.

A bakin qofa na miqa mata na juyo duk yanda ta keta magiyar na shiga amma naqi dan
nasan in muka zauna qilan se Bashir ya biyo baya. Bayan na koma zama nayi nima na
zuba kunun ina juyawa na kalle shi nace “Wai yau hutu ka samu ne bazaka office ba?”

Seda ya cinye qosan bakinsa kafin yace “Eh zamuje fieldwork ne Delta so an banu
kwana biyu mu shirya”
“Toh Allah ya taimaka” na fada naja kununa da qosai na fara ci. Ya rigani tashi
daga wurin nima ina qarasawa na kwashe komai naje Kitchen na ajiye dan na gaji
gaskiya tun asuba idan na huta anjima na wanke su.

Kan Three sitter na kwanta ina cewa “wash na gaji wallahi anya bazan nemi me aiki
ba”
Hankalin sa nakan Tv ya ce mun “idan da takura se ki nema din ai amma bame kwana
ba”

“Nima ai bana son me kwanan, abinda yasa ma ban damu dame aikin ba kaga ba wuni
muke a gidan ba zaman gaba daya weekend ai” na fada ina gyara kwanciya ta yanda zan
kalli TV dakyau.

“Hakane” ya fada, se ya juyo yana kallona kuma yace “me kika yanke akan maganar
mu?”

Kallon rashin fahimta na masa, ya gane hakan se yace “maganar da mukayi jiya da
daddare nake nufi kin gama shawara?”

Na gano me yake nufi se nayi murmushi nace “Wai maganar Iman? To tunanin me zanyi
ai tun jiya na gaya maka amsata ko” na fada ina kafe shi da ido kamar yanda yake
kallo na shima, se ya sauke numfashi ya dan zamo gaba yana hade hannyensa guri daya
yace

“look Ma’u Alfarma zakiyi mun ki karbi yarinyar nan, kinsan uwarta sarai ba wai
nutsuwa ce da ita ba bare har ta iya kulawa da wani halayenta duk se a hankali.
Yarinyar nan mace ce karta tashi taga abinda takeyi ta dauka daidai ne, bana so ta
tashi daban da yan uwanta ina so ta samu kula da tarbiyya irin daya....”

“Anzo dai dai gurin” na raya a raina ina sheqa murmushi, tashi nayi dakyau na zauna
kafin nace
“Wai tsaya Baban Ali, da baka yarda da tarbiyyar ta ba ka aureta har ka hada zuri’a
da ita”, se ya watsa hannu ya koma cikin kujerar sosai kafin ya juyar da kai gefe
daya yace “ba haka nake nufi ba, beside Amirah ai tarbiyyar kice itama kawai.....”

“To ai ka gama magana, tarbiyya tace kaga zata koyar da ita harda qari ma ko,
sannan idan ma wani hali ne da ita na daban da baka so yarinyar ka ta dauka ai
aikin gama ya gama tunda har ta dauki cikinta jininsu ya gauraya ta haifeta sannan
tasha Nononta duk wani halayya kuma ai ta gama diba sedai ai fatan na kirkin su
rinjayi na banza ko?”

Zancen gaskiya ka bar mata yarta, nasan ma duk wannan maganar da kake bata sani ba
dan bazata yarda ba itama. Babu uwar da tana ji tana gani za’a rabata da yarta
hakanan ba wata gagarumar jinya ba ko mutuwa kai ko mahaukata se anyi da gaske ake
iya raba su da Yayan su bare ita yar tilo haihuwar farko ko nicefa bazan baka ba.

Idan Dan rashin lafiyar ta ne Allah ya hore maka ai ka barta a Asibiti suyi ta kula
da ita har zuwa sanda suke ganin tayi kwarin da zata juri ko wanne kalar yana yi
amma ba maganar ka bani ita, nawa ma idan za’a ragi wasu aciki bayarwa zanyi”.

Shiru yai yana kallona harna dasa aya ina sake turo dankwalina gaban goshi, ajiyar
zuciya yayi kafin yace “yanzu dai bazaki karba ba kenan?”

“Allah me iko, da Hausa fa nayi maka jawabi dalla dallah amma kake sake tambaya ta
kuma?”

“Eh saboda kinsan ni bana son dogon surutu, amsa daya nake buqata Eh ko Aa kawai”
ya fada a dan hasale alamar ya fara barin cool site dinsa ze koma Bashir dinsa na
gaskiya, se kuwa na tura baki gaba nace “Toh a taqaice dai bazan karba ba”.

“Shikenan, amma ina da ikon da zan kawota cikin gidan nan ko tunda gida nane” ya
fada yana miqewa, nima sena miqe tsaye jin wani qundumemen rainin wayo,

“Tabbas gidanka ne ka isa ka dakko kowa nene ka kawo shi ciki, zaka iya kawo ta
tunda itama gidan ubanta ne ai se ka hado dame kular maka da ita, ko kuma kai zaka
aje aikin ka ka zauna rainon duk ba matsala ta bace ni” na fada ina dauke kai gefe,
ina jin yanda yake qare mun kallo kafin yaja tsaki tareda sakin kwafa ya shige daki
na rakashi da harara ina cewa a fili

“Wallahi ba tsaki ba kome zakayi sedai kayi, bazan karbi raino ba, rainon ma yar
Amirah yarinyar da duk zamana da ita idan dana ze tsaga guri saboda kuka bazata
dauke shi ba balle aje ga tsarkin kashi ko wanka shine ni ga jaka yanzu ta haifa
za’a dakko a kawo mun in riqe mata toh ko daga turu aka kuntota qarewar rashin
nutsuwa sedai duk handa za’ayi ayi”. Tsaf nasan yaji ni dan da qarfi nayi saboda
yajin, na koma kan kujera na zauna, se kuma na miqe na dakko wayata na dokawa Dadar
su kira dan fa karma inji wata magana daga baya.

Ringing biyu ta dauki wayar, a taqaice na gaisheta ta amsa kafin na shiga koro mata
jawabin yanda mukayi da Bashir, na rufe da cewa “Iya gaskiya ta na fada ko bana
aiki bazan riqe mata ya ba kowa ya kula da nasa Allah ya taya masa, idan kuma Ya
dage akan hakan to sedai na bar masa nawa nima ya nemo wadda zata riqe masa su ni
intafi”. Shiru Dada tayi har na kai qarshe sannan ta numfasa tace

“Ya kirani ya gayamun kuma na gaya masa wannan ba me yuwa bane, todai yanzu duk se
hankalin ku ya kwanta tunda Allah ma ya raba muku gardamar ya karbi abarsa, se kowa
yayi haquri ya maida wuqar” Dadan ta fada cikin sanyin murya,

“Hasbunallahu wani’imal wakeel, ta rasu jikin ne ya sake tashi?” Na tambayeta a
rude dan maganar ta dake ni dagaske, “ta rasu yanzu Likitan ya kira Naziru yake
gaya masa lafiya lau dan yau sukayi niyyar sallamarta ma har an yi mata wanka ma
sun bata madara tayi bacci to daga baccin ne kuma bata farka ba”.

“Allah yasa me ceto ce, ya musanya mana da wadda tafi ta Alkahiri” Na fada a
sanyaya tareda sauke wayar daga kunne na, ina dagowa muka hada ido da Bashir daya
fito kamar wanda aka koro.

“Se ki zuba ruwa a qasa kisha, da baki karbeta ba ta mutu” ya fada yana jifana da
wani irin kallo kamar ni na kashe masa ita. Sena miqe na nufe shi ina cewa
“karbarta ko akasin haka be isa ya chanza hukuncin Allah akanta ba tunda babu dayan
mu daya halicceta ko kuma ranta yake hannunsa dan haka ko tana gidan nan tunda
wa’adinta yayi dole ta mutu, in zuba ruwa a qasa nasha kuma bani zaka gayawa ba
Uwarta da tai sanadinta can zakaje ka gayawa dan ita ta nuna a fili bata damu da
ita ba” na wuce shi na shige dakina tareda banko qofa, in banda ma rainin hankali
ji abinda fa yake cewa fa.

Ina ciki naji tashin motarsa alamar fita yayi a raina nace a sauka Lafiya Allah ya
gani qilan zamanta ze iya zama fitina shiyasa Allah ya karbi abarsa, Har qarfe
biyar ina dakin fito ba, gaba daya zuciyata a jagule take ga alhinin rasuwar Iman
ga soki burutsun Bashir na sake kiran Dada nayi musu ta’aziyya ta cikin wayar ina
iya jiyo kururuwar Amirah da muryoyin mutane wasu na tausarta wasu kuma suna mata
fada akan kukan da takeyi.

Na tausaya mata harga Allah Kuka kam dole tayi shi wannan duka wani kan wani amma
yata iya haka Allah ya tsara abinsa masu samari da yammata ma ake dauka bare ita
jaririyar da ba dadewa tayi ba.

Har na miqe da niyyar zuwana dora abinci wani tunani yazo mun, ta yuwu fa Bashir ya
tafi Gombe be gayamun ba ga yara a makaranta lokacin tashin su tuni ya wuce, Hijabi
na na dauka da wayata na fita, bari naje na ari motar Anty na dakko su dan tawa
tana gurin Service ba’a dawo da ita ba, ina kulle qofar gidan motar sa na tsayawa
da yaran ya dakko su se na bude na koma ciki ina jiransu.

“Mami ina zakije” Abdallah ya fada bayan daya rungume ni, “Da zuwa zanyi na dakko
ku na zata Abbi ya tafi Gombe” na fada ina kallon Bashir daya shigo a sanyaye kaman
wanda aka sheqawa ruwan sanyi.

“Abbi yace Baby Iman ta rasu wai Mami” Farida ta fada fuskarta kaman zatayi kuka,
sena riqo hannunta ina cewa “ta rasu Farida” kaman tana jira kuwa ta saka kuka
tanacewa “kenan banida sister mace yanzu har fa na fadawa friends dina yau a school
step mum din mu ta haifo mun baby sis”

“Dallah malama yi mana shiru, kina kallon yarinya kamar mage dama ai kinsan mutuwa
zatayi kuma ai ma...”

“Shut up You are very stupid Aliyu” Bashir da yake shan ruwa a dispenser ya katse
Aliyu cikin tsawar da harni seda na tsorata amma ko gezau yaron nan beyi ba sema
ido daya zubawa uban suna kallon kallo kamar wasu zakaru.

“Zaka wuce daga nan ko sena zo na same ka wawan yaro har fada kake daman mutuwa
zatayi kenan so kake ta mutu koh” Bashir din ya sake fada cikin bacin rai, se na
saki hannun Farida da Abdallah na miqe da niyyar yin magana Aliyu ya rigani yana
cewa

“Toh ni Abbi me nace kawai dan na fadi gaskiya wayace su jagwalgwalata sannan su
sakata a sanyi ai dole ta mutu....” be rufe bakinsa ba Bashir ya dauke shi da mari
da har seda gefen bakin sa ya fashe kafin ya fizgo shi ya hau dukansa.

Kuka yaran suka saka gaba daya ganin abinda be taba faruwa ba a gidan yau Bashir ne
yake dukan Aliyu kamar wanda ya samu jaki, tsakiyar su na shiga ina qoqarin kwatar
Aliyu da ko gezau sema cewa da yake yi

“Ai daman seda nace miki ki koreta daga gidan mu muguwa ce kika qi seda ta aure
shi, gashi nan yanzu yafi son su akan mu tunda ta haifi yarinyar nan kina kallo
yanda hankalinsa ya koma kanta komai ita har comapany da ze bude da sunan Farida ma
ya chanza na gani sunanta ya saka, shi yasa kullum nayi sallah sena yi Addu’a Allah
yasa ta mutu dan akan Abbi ze iya yin komai gashinan kuma kina gani”.

Bige bakinsa nayi ina fashewa da kukan nima dan na kasa tare dukan da Bashir yake
masa shi kuma yaqiyin shiru nasan kalaman sa ne suke qara tunzurashi seda ya gaji
dan kansa kafin ya kyale shi ya shige dakinsa ya banko qofar ya barmu muna rusa
kuka kamar nan ne gidan mutuwar.
Wannan wane irin bala’ine, ni na kashe yarinyar ko Yara na da ze huce akan mu? Ai
kuwa wallahi da sake zan dauki komai amma banda irin wannan dukan da kalaman da
basu dace ba akan yarana.



🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 25

Ina kuka ina gasawa Aliyu fuskarsa da ta kumbura sosai saboda marin daya sha a
hannun Bashir, tausayin sa ya cikani tabbas be kyauta ba amma ai dukan yayi yawa,
Yanda ya zage ya ringa dukansa kamar wanda yake dambe da sa’ansa.

Gaba daya yaran suna tsaye sunyi cirko cirko kowa fuska da hawaye kana kallonsu
kasan a tsorace suke, bude qofar da Bashir yayi da qarfi yasa suka zabura kafin
kace meye wannan sun maqalqaleni wani kan wani Jafar yana cewa “kice masa yayi
haquri Mami dan Allah karya doke mu”.

Tausayinsu da matuqar takaicin Bashir ya sake qume ni, na daga idanuwana da har sun
qanqance saboda kuka na kalleshi yana tsaye shima mu yake kallo, fuskarsa a daure
tam haka idanunsa sun kada sunyi jajir har wata jiniyace ta fito a goshinsa. Daga
tsayen yace mun “Ina kika saka mun folder dana ajiye akan Gado”.

Ayanda nake jina Banyi niyyar tanka masa ba amma saboda yaran da suke gurin bana so
na bada qofar da zamu ringa raba hali a gabansu dan hakan ze shafi tarbiyyar su,
“Ina zuwa” nace masa kafin na miqe na kama Aliyun da zuwa sannan jikinsa ya rufe da
zazzabi me zafi amma saboda dakiya da taurin kai har sannan ko digon kwalla babu a
idonsa.

Dakinsu na rakashi, ina tsaye ya shiga ya watsa ruwa a jikinsa ya fito dakyar ya
kwanta akan gadonsa. A cikin first Aid box dinsu na ciro masa Paracetamol na bashi
yasha, ina zaune a gefen kansa nace

“Aliyu kana babba kai kake so ka raba kan qannenka ko, irin abinda na koya muku
kenan ka tsaya mahaifinka yana fada kana fada Aliyu?”

Se a lokacin ya saka kuka yana cewa “Mami Abbi ya canza wallahi ya dena son mu, da
bakwayin fada amma yanzu kullum se sukunyi kuma duk akan Anty Amirah ne. Mami yanzu
fa da muna tahowa yana waya da Abokinsa Uncle Bala yana ce masa daman bakya son
yarinyar yace ze kawo miki ita kinqi yanzu gashi ta mutu hankalinki seya kwanta
ai”.

Shiru nayi ina shafa kansa, wato a gabansu ma ya fadi haka kenan, tabbas shi ya
bada qofar da yaran zasu ga baqin sa ko bayan haka yana sane Aliyu ai photocopy
dinsa ne daman, duk wani hali daya ke taqama dashi Aliyun ya kwasa harda qari dan
badan ma Irinta Allah ya bawa Aliyun a matsayin uwa ba da ba qaramin wuyarsa za’a
sha ba.

Numfashi naja kafin nace “koma menene karna sake gani, Abbinku yana sonku ka sani
irin son da yakeyiwa Iman, ba fata ba yau ko daya daga cikin mu ya rasa irin
damuwar da ze shiga kenan kasan halinsa kuma idan yana cikin damuwa Fada yakeyi da
kowa. Dan haka ka kiyaye Aliyu karna sake jin wata magana irin haka kaine babba
komai kayi qannenka suna koyi da kai ko so kake Allah yayi fushi daku kuna sabawa
mahaifinku?”

Girgiza kai yayi a sanyaye, na ci gaba da cewa “yawwa Haidar dina kar a sake, gobe
kuma ka same ahi ka bashi haquri kaji ko dan yanzu dai be huce ba”

“Insha Allah Mami bazan sake ba” ya fada.

“Yauwa Allah yayi muku albarka ya kulamun da rayuwarku”
“Amin Mami, I kove you”
“I love you more” na fada tareda kissing goshinsa kafin na ja masa bargo na fita.

Seda na lallaba sauran suka cire uniform na dora farar shinkafa dan ina da miya na
barwa Amna ta duba sannan na tafi dakin nasa.

Ina tura qofar yana sako kai ze fito, ya watsamun kallon banza na mayar masa da
martani na shige se ya biyo ni yana cewa “Wato daman abinda kike gayawa yaran nan
kenan kina koya musu mugun hali har Aliyu yana fadar na fi son Amirah akan su ko?”

Banza na bawa ajiyarsa, na jawo drawer dana saka folder na dire masa akan gadon
kafin na miqe na nufi qofa.

“Ma’u” ya kira suna na kafin yaci gaba da cewa

“Wato Ma’u kin rainani, saboda wulaqanci da rashin mutunchi ina miki magana shine
kika sa kai zaki tafi bayan tara yayana da kike yi kina cusa musu tsana ta a
zuciyar su ko?”

Tsabar mamaki daskarewa nayi a guri daya na kasa gaba na kasa baya, wace kalar
kwaya Bashir yasha ne? Ko kuma rasa Ÿa hauka ne ko a kansa aka fara, kai da alama
dai kawai Bashir ya shirya ci mun mutunchi ne idan ba haka ba ya gama jibgar mun Da
sannan ya kalleni yace wai ina masa wulaqanci da rashin mutunchi, waiwayawa nayi na
gyara tsayuwata sosai ina kallonsa

“Wulaqanci ko rashin mutunchi ba tarbiyyata bane dan da ace na iya da bamu kai
shekara goma sha shida tare da kai ba, batun in tara yaran ka kuma in cusa musu
tsanarka..” na dan dakata tareda qara taku biyu na dawo gabansa sosai, murmushi
nayi me kama da yaqe kafin na ci gaba da cewa

“Base na zugasu akan ka ba, yanda kyakykyawar mu’amalarka gare su ta sa suke sonka
haka sababbin halayen daka tsiro dasu zasu bi su goge duk wannan so da shaquwar da
kake gani a tsakanin ku, sannan kayi a hankali duk abinda yaro ya gani a gurin
iyayensa tarbiyyar da ze tashi da ita kenan musamman kai me Ÿaya maza zasu tashi su
zata abin kirki kake aikatawa kaga haka zasu tafi da matan da.....”

“Ya isheki Asma’u” Bashir ya katse ni cikin hargagi tareda daga hannunsa ya nufoni
da niyyar mari, sedai ko me ya tuna ya janye tareda kaiwa Bangon dayake bayan mu
naushi sannan ya juya ya dafe kansa yana huci kamar wanda ya hadiyi kunama.

Tabbas na tsorata, na kuma saddaqar sheya shararamun mari a yanda ya nufo ni amma
taurin zuciya da dakiyar dana dorawa zuciya ta bata sa baki na ya mutu ba,
kallonsa nayi da kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba, na tsana ne ko na
takaici da baqin cikin abinda Bashir yakeyi mun nace

“Nima dukana zakayi kamar yanda ka kusa illata danka gashi can kwance, to ka
tabbata hakan shine abu na qarshe da kwakwalwarka zata raya maka akaina dan wallahi
Bashir sekayi dana sanin dora hannunka a jikina da sunan duka, har Mahaifina ya
koma ga Allah ban taba ganin ya dagawa daya daga cikin matansa murya ba ballantana
har ya dake su se kai kake tunanin zaka daki yar sa? Toh bismillah” na fada ina
zare masa ido kamar wani dana.

Naga alamar se nayi masa haukan gaske sanann ze shiga hankalin sa, wata irin tsanar
Amirah ce tayi mun dirar mikiya dan itace sila, ita ta janyo komai da yake faruwa
da be aure ta ba da haryanzu muna cikin zaman lafiyar mu da qaunar juna amma tunda
ta shigo rayuwar mu abubuwa suke rinchabe mana bamu taba rufa sati ba tareda munyi
tashin hankali da Bashir ba.

Shiru mukayi gaba daya, ni ina jiran ya sake wata magana ko yunqurin marin nawa dan
wallahi sena gwada masa nima yar buyagi ce yau amma se yai shiru, kiran Sallar
Magriba ya sakashi shigewa Toilet ya bugu qofar da qarfin gaske se na bishi da
harara kafin na ja dogon tsaki na fice daga dakin.

Seda na tashi Aliyu na sake bashi awa paracetamol bayan yaci abinci yayi sallah
kafin bacci ya sake dauke shi, gaba dayan su basu da walwala haka na daure na ringa
tausarsu har sukaci abinci sunayin sallar isha kuwa kowa ya nemi makwanci sa har
yan biyu da suke qanana sun shiga nutsuwarsu dan Muhammad dayaga Bashir ya fito
daga dakinsa ze shiga Kitchen ma kuka ya saka ya rirriqe Jafar.

Ina kallon yanda yai turus

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login