Showing 12001 words to 15000 words out of 238465 words
randa kika gaji kya barni na Auri Auwalu da nake so yake so
na”.
Mafice Adda ta cilla mata tana auna mata Ashar
“Shegiya da bata gaji arziqi ba da dai wallahi ki auri wannan faqirin gara kiyi ta
zama ina kallonki ba auran, duk yayan gidan nan wa kikaga ta auri ko Malamin Jami’a
bare malamin makarantar primary”
“Wato Fatu bazaki dena yin munanan kalamai akan Yaran nan ba ko? Amma ki ci gaba ai
kina gani Idan Alkahiri kike shukawa kanki koma akasin haka” Alhaji Murtala da
basuji shigowarsa ba ya fada, be ko qaraso ba ya juya kawai dan yasan wani qarin
bacin ran ze jawa kansa. Tun kafin ya fito da safe ta bar gidan haka duk a kunnensa
Indo Tazo tayi tijarar ta dakyar Yaran gidan Maza suka lallaba ta ta tafi dan shi
qin fitowa yayi. Ya gaji da halin masufar da Fatu take jefashi a kullum shi be san
Adadin bashin daya biya mata, idan baazo yau ba gobe se anzo to ya gaji.
Yanzu ma maganar ya shigo ya mata akan ta nemi kudin matar ta bata idan ba haka ba
tace gobe idan ta dawo da police zata zo to wallahi sedai su kulleta dan shi sisi
baze sake biya mata ba ai badan ita kadai yake nema a rayuwarsa ba.
Adda kuwa ko a jikinta ta cigaba da gayawa Amirah yanda sukayi da malami da kuma
tabbacin da ya bata da an gama ai Bashir ze dawo hannunsu.
“Amma fa Adda ni bana yarda idan akace wai Anty tana wa Yaya Bashir Asiri ke kanki
Adda kin san ba haka bane”
Hararar ta Adda tayi kafin tace “Ji banza, idan tanayi se tace miki zata fito fili
a sani ne? Ko kuma ace da batayi to daman me zatawa Asirin bayan kusan ita ce Mijin
shi Matar yanzu kuwa daya bunqasa ai bazatayi sanya wata tazo ta taya ta ci ba. Ni
in zaki karbi abu kiyi kawai kiyi kafin ki fara saka wasiqasi ki bata mana aiki
dama ni ina zargin bakyayin yanda akace shiyasa komai baya tafiyar mana daidai to
ke kika sani wallahi kina ji kina gaji zata kado ki waje ki dawo mujere ana mana
Dariya” da haka ta shige dakinta dan yin Sallar Azahar da La’asar da suka sameta a
tafe ga Magriba an fara kira.
Amirah ma jiki a sanyaye taja jug ta fara bankawa cikinta ruwan magani dukda qasan
ranta bata jin Bashir zezo wannan satin amma dai gara tasha saboda tsaro se sannan
ta tuna bata gayawa Adda yanda a ka qare da Indo me kaya ba, ta cicciba zuwa dakin
Addan ta tarar tana sallah se itama ta wuce nasu dakin dan yin Sallar.
WASHE GARI
Qarfe bakwai a qofar gidan tayiwa Indo ta shiga biga gate baji ba gani dan ta
rantse wallahi yau ko ita ko Fatu a garin nan ita zata rainawa hankali lallai bata
san wacece Indo ba. Alhaji Murtala da fitowarsa kenan ze tafi wata Jana’iza ya
qarasa ya cire sakata ta hankado qofar saura qiris ta bige shi tayi ciki abunta se
kawai ya girgiza kai tareda juyawa ya kunna motarsa, Aminu daya daga yaran gidan ya
qarasa bude masa gate yai ficewarsa dan bama ze tsaya yaga yanda zata kaya ba.
Adda Fatu da tunda tajiyo bugun ta janyo abinda Malam Wizy ya bata ta bantara se
taga kaman Namijin Goro amma kai bashi bane qila kama ce ita dai ta afa baki ta hau
tauna harda guara zama akan kujera tana jiran shigowar Indo se kuwa gata kaman an
jefota ta fado.
“Fatu bani kudina kafin na yaga miki rigar rashin mutunchi a unguwar nan” ta fada
tana huci, se Adda ta miqe tana qara bantarar magani ta tauni ta nufo Indo tana
cewa
“Ke Indo fita ki tafi karki sake dawo wa gidan nan ki manta da zancen bashi a
tsakanin mu har abada idan ma da wasu kudin a jakarki yanzu cirosu ki bani”
“Fatu hauka ne ya sameki ko to bari kuwa yanzu zan sauke miki shi wallahi ina batun
ki bani kudina kina min wata maganar banza harda in qara miki wasu to bari kiga”
Indo ta fada tana ja baya ganin Adda ta nufo ta tana sake maimaita kalamanta se
zare ido takeyi ai bata yi aune ba se Ji tayi Indo ta dauke ta da wani gigitaccen
mari daya sakata furzo da goron ba shiri ta kife gurin tana kururuwa dan ji tayi
kunnenta, indo bata haqura ba ta sake kai mata Mahangurba a hanci aikuwa take ya
fashe ya fara bulbulo da jini sannan ta bita ta turmushe ta hau duka, Adda ba hakin
kwace wa se ihu take tana neman dauki.
Kishiyoyinta uku duk suna tsaye a bakin kofa da yayan su mata ransu qal akan wannan
abu se Ummi da Amira a gefe suna taya ta ihun ba damar kai mata dauki 😂. Se da tayi
mata lilis sannan Samarin gidan suka kawo taimako dakyar aka kwaceta Indo na
jaddada mata wallahi ko kudinta ko kuwa kullum seta zo ta nada mata na jaki dan ta
bar maganar police ma da kanta zata kwaci kudinta sannan ta fice daga gidan.
Adda fuska tayi luhu luhu se hawaye da ajiyar rai take ga hanci ya fashe a ranta
Allah ya isa take jerawa Malam Wizy akan wannan abu daya bata gashi nan ba biyan
buqata se bugu data sha a banza, bari Suga na Bashir idan taga ba nasara dole ta
koma ya biyata kudinta dan bazata dauki asara biyu ba. Ita se yanzu ma taji wani
tsautsayi ya kaisu yarda da Dan Napep din nan? Anya ma ba hadin baki bane shida
Hajia Balaraba suka kaita a cinye mata kudi amma ai itama Balarabar ta bayar. Bari
tayi ta kanta yanzu zata kirata taji yanda akayi. Ummi ce ta kamata ta kaita daki
ta hada mata ruwan Me zafi a toilet ta shiga dan gasa jikinta, dakyar ta iya
watsawa ta samu dai Habon ya tsaya ta dauro towel ta fito ta haye gado kan kace
meye wannan zazzabi ya rafke ta se rawar sanyi take.
(To Adda Allah ya qara lafiya ya kiyaye na gaba 😂😂😂😂).
Kafin yamma dai jiki ya qi dadi dole suka kaita asibiti tasha Allurai suka dawo da
magunguna gashi har sannan babu Bashir babu labarin sa kuma ta kira Dada ma wayarta
a kashe, kukan baqin ciki ta fashe dashi da tsoron haduwarsu da Indo gobe.
Mu koma Lagos
Qiri qiri Asma’u ta qi bari a sallameta acewarta se tayi sati, Dr beqi ba tunda
sabga ce ta kudi qaruwar su ce dan haka yace wa Bashir dole ta zauna suyi
monitoring Bp nata na wani lokacin kafin a sallame ta. A kwana biyun nan idan kaga
Bashir se ya baka tausayi yanda yayi wurjanjan dashi har a office an gane bashi da
nutsuwa dole suka bashi leave na 1 week saboda ya samu ya kula da yaran kafin a
sallami Asma’u, sauqin sa daya yaran sun rage kokekoken tunda kullum yanzu da safe
ze kai su da daddare ma su koma.
Shi ya ma manta da wata Amirah sam bare zancen zuwa Gombe yau ranar Sunday kaman
yanda ya saba bayan ya kawo yaran, suna gurinta Abokinsa Abdurrahman da Matarsa
suka zo dubata, su suka tafi da yaran gidan su akan da dare idan ya gama se yaje ya
dauke su su tafi gida ya dan rage zirga zirga.
Suna zaune kamar kurame bame cewa komai, ita tana chatting a wayarta shi kuma ya
tasa ta a gaba yana kallo ganin yanda ta sake wani mugun fresh tayi kyau alamar ta
samu hutu ba abinda yake damunta shi kuwa banda uwar rama da baqi da yayi to ga
Damuwa ga babu abinci me kyau daya saba kwasa dan yanzu suma yaran mata yassara
kawai suke ci dama Mami ce take tsayawa ayi abinci me kyau to bata nan dan haka
baya iya ci ko sun dafa in yunwa ta dameshi ne ma zeci Indomie yasa tea in ba haka
ba Snacks da lemo ne rabin abincin nasa.
Dagowar da Asma’u tayi tana dan murmushi tareda tsare shi da ido tace “wannan week
din bazakaje Gombe bane”
Se a sannan manAmirah ta fado masa ya tuna rabonda suyi waya tun ran Laraba be
kiratan ba yasan kuma itama bazatayi gigin kiransa ba tunda ya mata warning.
Numfashi yaja kafin yace “Wallahi na ma manta shaf kuma ko waya banyi nace bazan
shigo ba gashi har yau Sunday, ya kamata kam na kirata”.
Kishi ne ya dan tsikareta ta wani fannin kuma tana yabawa Bashir dan ba laifi yana
kaman ta Adalci wani Sa’ilin. A farko farko se sati biyu yake zuwarwa Amiran ze
tafi Friday ya dawo Monday da safe to da aka samu qarin kudin jirgi dole ya chanza
tsarin zuwa Qarshen wata, daga bayannan kuma bata san dalili ba wani Sa’in se ya
jera sati uku hudu ma duk weekend se yaje duk kuwa da ayanzu kudin jirgin ma yafi
da ita dai bata taba tambayarsa dalili ba haka nan ko tare sukaje Gombe ko kwana na
wa zasuyi bata da Kwana a yanda suka tsarawa kansu shida Amaryar sa kuma da
taimakon Adda to ita hakan be dame ta ba tunda daman idan taje ba zama take ba a
lokacin take samun ziyartar yan uwa da sauran abubuwan da akayi bata nan.
Tana kallonsa ya zaro waya ya shiga kiran Amiran ringing biyu kuwa ta daga tana
fashe masa da Kuka, kallon Ma’u data juya baya ta kwanta yayi ya tabbatar ta jiyo
kukan Amiran se ya miqe ya nufi qofa yana ce mata “kukan kuma Na mene kinsan bana
so”
Wani qululu ya tsayawa Asma’u, wato itace banza a wajensa da in zata mutu tana kuka
baze ce ta bari ba kenan ashe ita ta zata so ne yasa yake barinta ta fitar da
damuwarta ashe tsabar be damu bane kai Anya kuwa Bashir ya taba sonta a ransa??
Abubuwa da yawa da ada take daukar haka yaje se a yanzu take ganin banbance
banbance ko kuma dama Haka Mazan suke ko wacce Mace da yanda halayyarsu taje a
wajen ta? In kuwa haka ne Sun Amsa sunansu na Hawainiya.
AMIRAH
Sanda Bashir ya kirata suna zaune da Addah da har yau fuska bata daidaita ba ko
jiya Indo ta dawo Allah ya taimaketa Alhaji na Nan, shi ya kashe rigimar cikin
Kudinta da yake hannunsa yake juya musu da a qalla sun kai 2 Million yau ta kirbi
dari gobe Hamsin a wayonta kudinsa take ci da yaga fa da gaske Fatu ba hankali ne
da ita ba dole ya saka akayi rubutu kowacce cikin Matan da kudinta dake hannunsa ya
kuma gaya musu duk wadda ta nemi kudi indai ba abinda ya zama dolensa ba to a cikin
kudinsu suka ce sun yarda kowa ta saka hannu to ita Adda a nata baqin wayon da
ganin tasha kansa bata dena ba ta ci gaba dacin kudinta hankali kwance ba tareda ta
sani ba shi kuwa yana lissafe da komai ga kuma takaddu saboda Adar rai. To tun jiya
daya fita ya yanke shawarar cikin 500 din data rage mata ze biya mata bashin nan
dan ba ita kadai ba harda shi take zubarwa mutunci maqota kullum na jiyo an zo
karbar bashi gidansa bayan Allah ya rufa masa asiri.
Jiyan Indo na zuwa ya fito a gaban Fatu ya zaro kudi ya bata ta qirga su cif sun
cika tace mata “Allah ya taimakeki wallahi da dukan yau se yafi na jiya kuma
wallahi ko da wasa karki kuskura naga qafarki kinzo neman abu gida na dan ance ba
kunya ce da ke ba se ki dawo” ita dai tayi muqus harda yiwa Alhaji godiya yace mata
“Godiyar me zakimun a cikin kudinki na biya miki ai ba nawa ba tunda haka kika zaba
se kiyi tayi wata ran idan ba kiyi hankali ba suturar da zaki daura se ta gagare ki
indai baki dena cin bashi ba.
Yana fita wayar Bashir na shigo wa Adda ta zabga Hamdala tace kin gani ko a sannu a
sannu komai ze daidaita maza ki daga ki rushe da kuka duk kibi ki hargitsa shi ki
samu yazo ko ya turo mana wani abun, haka akayi tana dagawa ta saka kukan.
Seda ta tsagaita ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta jikinta tace da sauqi.
“I’m sorry Amirah ranar nayi miki ihu raina ne a bace Wlh ga Ma’una bata da lafiya
a lokacin ke kuma kin dame ni da kira”
“Ba komai Yayana ya wuce yanzu ya jikin Antyn? Ban sani ba ai dana kira na mata
sannu dukda idan na kirata ma bata amsawa kaga yanzu kosu Aliyu ta hanani magana
dasu”
“Qorafi dai qorafi halin daya tsana da Amirah kenan a rayuwarsa” ya ayya a ransa a
fili kuwa se yace
“Ta samu sauqi, se zuwa Next week zan shigo insha Allah akwai abinda kike da bugata
ne?”
Se Adda ta zungureta tana rada mata tace kudi se tace
“Uhm uhm Ba komai maganar siyayya ne kawai daman se kuma ni Yayana ina so in dawo
kusa da kai gaskiya saboda....”
“Amirah I’m looking forward to that ok maganar kudi kuma idan mun gama zan saka
miki wani abun kafin End of the month saboda nayi hidimar Asibiti duk na kashe
kudaden hannuna yanzu”
“To shikenan amma dai gaskiya Yaya nidai ko wani gidan ne se ka samar min da zan
zauna amma irin Na Anty nake so me kyau sannan fa yaya karka manta da zancen canjin
kujerun irin natan” ta sake fada dan harga ranta fa ita tunda ta tashi burinta
kawai shine ta kamo Asma’u ta ko ina.
“Naji ki gaida su Adda” ya fada yana qoqarin kashe wayar jin tana so ta bata masa
rai,
“Bama ta da lafiya bari na bata kayi mata sannu” ta fada kafin ta miqa mata kuwa
qit ya kashe wayarsa dan itama Addan haushin ta yake ji dan abu da yawa ita take
dora Amiran akai, idan banda bata da tunani kwana nawa basuyi waya ba amma da
abinda ya kamata ta tare shi kenan? Bayan haka yanzu fa yake gaya mata bashida kudi
amma ita wannan baya gabanta buqatarta ce kawai a gaba. besan dalilin ta na gasa da
Ma’u ba komai ta gani a gurinta yunqurinta se itama ta samu, tana mance cewa Asma’u
na aiki tana da abin kanta abu dayawa ko beyi mata ba zatawa kanta.
Gudun karta ishe shi ya saka shi yi mata transfer 100k saura 200k kenan kudin
siyayyar kayan haihuwa dana fitar suna da tace ya bata, yace sun yi yawa ta ringa
masa mita da qorafin bala’i dole ya yarda ze batan kota qyale shi.
shi tunda Asma’u take haihuwa baya tunanin ya taba bata dunqulalliyar dubu Hamsin
wai da sunan tayi siyayya shi bata ma taba tambayarsa ba, duk abinda ya dakko ya
bata idan yana dashi karba take idan ma bashi dashi haqura take yan uwanta su mata
harma ya samu Arziqin shaddar fitar suna shima.
Baze taba manta Haihuwar Abdallah ba da tace ya saka mata sunan Babanta yace mata
sedai ta se masa rago hakan kuwa akayi ta siyo raguna har biyu ta kuma cewa Yan
uwanta da Nasa shi ya siya har yu har gobe ya kalli yaron se yaji wata kunya da
Nauyin sa dana Uwarsa ya kamashi, shi wallahi a duniya in yai wani abun se yaga
kamar dai shafar Aljanu yake samu su saka shi yayi abu daga baya yazo yana dana
sani (Shafar Aljanu ko iskanci ba 😂😂)
Dakin ya koma Ma’u najinsa tayi shiru kamar me bacci ya gaji da tsayuwa ya qaraso
ya mata peck a goshi ya fita yanaso yaje gida ya dan yi bacci tunda yaran basa nan
yau shima ya dan huta kafin gobe Monday.
Su Addah kam Kudi na shigowa suka hau Murna “Ke yar nan kinga abu kaman wasa aikin
malam ya fara kama Bashir to wannan aka gama aiki kuma ai ban san yanda zamu taka
shi ba yanda muke so. Ita waccan shegiyar dama itama ba a zaune take ba dole nata
yaqi tasiri amma tunda mun rabu lafiya shikenan, yanzu bari an jima zan kira Malam
se ya nada account mu sake tura masa ko kudin biyu ne tunda na bada na biyu ayi a
gama aikin nan mu fara shan romon damokaradiyya”
“To Adda amma da mun bari dai akwana biyu a sake samun wani abun wannan mudan rage
siyayyar mana” cewar Amira.
“Ke dallacan ba gara a gama ba nasan ko million goma kika ce ya baki kawo wa zeyi”
“Kuma fa haka ne, to ki kira se a tura masa din”
“Allah dai ya kauda bacin rana” Ummi ta fada tana miqewa kafin ta karbi duka ko
Ashar daga gurin Adda ai kuwa ta shiga aika mata dasu tana ce mata yar baqin ciki
haka zata qare tana gani suna abin arziqi banda ita.
Wai ya Hajia Balaraba ta qare da maganin Malam Wizy ne?? 😂😂😂
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 7
A bangaren Hajia Balaraba kuwa cike da farin ciki ta bude gida ta shiga ganin har
sannan Kishiyarta bata dawo daga gurin aiki ba, cikin sauri ta fito da rubutu ta
huda leda tareda guntsa ta feshe kofar dakin Amarya tana cewa “Shegiya maza ki dawo
ki taka ni Alhaji yaiyo waya daga kasuwar ma yace ya sake ki base ya jira ya dawo
ba” ta qulle ragowar gudun kar ya zube ta qarasa qofar ta.
Mayafinta kadai ta ajiye ta shiga kitchen ta hau kicikicin dora girki qarin farin
cikinta ita ce da girki dama kai yau koda ba itace da girki ba ai dole tasan yanda
za’ayi ta aiwatar da aikin nan tanayi tana tuna irin cin mitunchin da Alhaji yai
mata dazu da safe kafin ya fita kuma ta tabbata duk Amarya ce ta zugoshi har yana
iqirarin tabar ganin sun tara yaya da jikoki tsaf seya yanka mata tikitin zawarci.
Itadai tunda Malam na kan Tudu ya kwanta dama kamar ya tafi da duk ayyukan da Tayi
akan Alhaji ne komai ya karye shekara da shekaru tana cin duniyarta da tsinke se
yanzu da tsufa ya kusa cin mata ne zata fara karbar taskun namiji ina bazeyuwu ba
ai.
Tsaf ta gama hada lafiyayyar Miyar taushenta kafin ta dakko qaramar tukunya ta sare
wata wadda zata ci, nan da nan dakko ragowar rubutun Malam Wizy ta kurbe tas ta
kuskuro dattin bakinta da komai ta watsa musu a miya ta sake kurbe ragowar ta zuba
ta juyata dakyau ta rage wuta ranta fes dan gani take kamar ma aikin gama ya gama.
Tana cikin malmala tuwan autarta me suna Ruqayya ta shigo ta dawo daga makaranta
dan tana shekarar ta ta qarshe ne a GSU da mamaki ta kalli maman tata kafin tace
“Hajia kece dakanki yau a kitchen ina Baba Zulai din”
Bata ko dago ta kalleta ba tace “Taje gida Sa’adenta batada lafiya ina ga se gobe
zata dawo”
“Kai dukda haka da mamaki ace Hajia kina girki lallai yau zamu kwashi dabge bari
nayi sauri nayi wanka nayi Sallah muzo mu kwashi ganima”
“Zaki kwashi ganima dan uwarki duk zan kulle bakinku ai na