Showing 36001 words to 39000 words out of 238465 words

Chapter 13 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

ke kadai
amma ko da wasa karki sako mun ya a ciki ke ko yan barka ki ka ringa bawa yata aka
jagwalgwalata se ranki yayi mummunan baci wallahi bare har ki tara mata hayani ya
akai. Ke yanzu ko lafiyarta qalau ma ai kya dagamun qafa kodan kashe kudin da nayi
a Asibiti kice ba se kinyi wani taro ba bare yarinyar har yanzu kina ganin yanda
take”.

Seda ta tunzura baki kamar yana gaban ta tace “ to kowa ya haihu ana suna se ni ace
baza’ayi nawa ba nidai se nayi gaskiya”

“Allah ya baki sa’a” ya fada tareda kashe wayar, ya fuskanci so take ta qure shi
seya saita mata kwakwalwar ta sannan zata dawo kan hanya. Allah ya bata ikon yin
taron sunan tabbas seta gane waye Bashir kuwa.

Amirah

Hararar wayar tayi harda murguda baki tace “Dan rainin hankali wallahi se nayi kuma
seka bada kudin, naga matar ka duk haihuwa ai setayi suna na Alfarma sanda ma baka
dashi bare ni yanzu dole ma ka nemo su ka bani. Labarta wa Addah komai tayi tace ta
rabu dashi ze bayar bari dai a sallamo yarinyar ai taji Likitan yace Alhamis ko
Juma’a zasu iya sallamar su ko, haka sukaci gabada tsare tsaren su.

Washe gari gurin goma na safe Suna zaune a palour tareda yan gidansu da suka sake
zuwa dubata harda kishiyoyin Addah dukka biyun da matan yayyenta kamar aike sega
Sallamr Dada ta shigo Naziru da Fainusa da Ihsan na biye da ita da akwatuna guda
biyu ga kuka saitin baho da Qaramin gado me net.

Nan suka shiga musu maraba suka zauna aka gaisa kafin Dada ta kalli Addah tana cewa
“Addah ga kayan barka nan nace dai ya kamata a kawo tunda al’adace gashi munyi sa’a
ma yan gidan nasu suna nan.

Addah baki har kunne nan aka shiga zuge jakun kuna ga kaya nan tabarakallah komai
yaji Babbar kayan jaririyane tsala tsalan riguna da sauran tarkacen kayan baby na
yan gayu seta tsakiya kuma kayan Amirah Atamfofi guda biyu Madam Getzner daya se
Laces masu kyau suma biyu kayan da gani kaf kasanba qanana bane harda mayafi kalar
lace daya da jaka da takalminsa.

Amirah na nade akan kujera Lace din da aka hadowa da takalmi da jaka ya tafi da ita
amma kuma batajin zata saka tunda mutane sun gani.

“Gasunan dana gurin Bashir da gudummawar yan uwansa dukka aka hada mukayo siyayyar”
cewar Dada.
“Kaya sunyi sosai Allah ya qara arziqi yasa lafiya ta kashe, Se ki fito da na gurin
ku kema su gani ko Fatu” Inna Gaji dake faman daga kaya ta fada.

“Fatu ai se ku fito dana ku ko tunda gasu su gani” ai Addah ji tayi kaman ta
kwadawa Inna Gaji mari wannan tonon silili da take neman yi mata a gaban kishiyoyi
sun kuwa zuba ido da kunnuwa suna jira suji me za’a ce dan Al’adar gidan su haka
akeyi da an kawo kayan gidan miji suma zasu fito da masu a hada amma ita ko pant
bata siya ba.

Rasa ta cewa tayi dan haka ta shiga kame kame tana yaqe Dada ta taimaka ta kwaceta
da cewa “kai se kace wani abun bare ai bamu raba daya biyu ba duk gasunan ai na
dangin uwa dana miji kune dai zaku fito da naku yanzu dangin uba” tayi maganar
cikin sigar wasa akabat Addah da sauke ajiyar zuciya da yaqen dole.

Dada bata jima ba tayi musu sallama ta fita Addah tabi bayanta.
“Kai Nafi kin ceceni wannan shegiyar Gajin dason qure mutum haihuwar data zo
lokacin ta beyi ba ina naga ta siyan wasu kaya ga wannan lalura”
“Hakane” Dada ta bata amsa.

“Yauwa dama yau nake so nazo muyi maganar taron suna da za’ayi idan an sallamo yar,
kin san yanzu se ya zama abin magana idanba’ayi ba fa”

“Wace irin magana kuma Addah bayan kowa yasan halin da uwar da yar suke ciki, dan
Allah kibar wannan magana Allah ya kaimu gaba ai ba gamawa tayi ba se ayi”. Cewar
Dada

“Kiji ki Nafi da wata magana to in kin manta bari na tuna miki Binta ba bakwainin
kika haifeta ba(Babbar yarta) kuma haka muka shirya taron suna akayi”.

“Amma Addah bazaki hada zamanin Binta dana wannan yarinyar ba, Binta a sannan ba ma
waye da zuwa Asibiti ba qarewarta a gida na haifeta yanzu kuwa abu ko da anyi shi
babu matsala tunda zamani yashiga cikin abubuwa koya kika kuskure se kiga an samu
akasi azo ana dana sani nidai a shawara ku haqura nasan kuma shina Bashir din baze
bari ayi ba”. Dada ta sake fada ranta fal takaicin Addah.
“Wallahi se Anyi jikar tawa ta fari kuma takwarata kice bazanyi suna ma baqin ciki
ma kikemun kenan ko”

“Wane irin baqin ciki kuma Addah nima ai jikata ce ko ban haifi Bashir ba”

“Toh in ma dai hada baki kukayi kedashi yace baza’ayi ba tun wuri ki gaya masa
wallahi suna ba fashi ya lalo kudade ya bata da zatayi hidima in ba haka ba rai ya
baci” tana gama fadar haka ta juya fuuu tayi ciki.

“Dan Allah Dada muje wallahi ko Yaya ya yarda bazasuyi sunan ba ai dai ni zece
nabada kudin ko zamu gani” Naziru ya fada yana huci, haka suka shiga motar suna
tafe shida Fainusa suna debewa Addah albarka Dada dai bata iya ce musu komai ba
gaba daya ta tafi tunanin meke damun Addah a rayuwa ne. Su yanzu inda hankali ko
cewa akayi suyi ai sace Aa amma har tana rantsuwar ae sunyi, to wannan karon zata
ja itama bazata takurawa Bashir ba kuma ko sunyi galaba akan sa ya yarda seta hana,
zata nuna mata bafa tsoro yasa take mata biyayya ba.

Allah dai ya mana maganin abinda yafi qarfin mu.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 16

Ranar Juma’a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa
ya dakkota bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se
yadawo saboda matsawar da Addah tai masa akan zancen shagalin suna.

Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa
yi mata tatas dan dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn
dan haka ya qara tabbatar mata da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba
idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar ba ta godewa Azabarsa. Ai
kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta kuma sake
tabbatar masa fa taron sun ba fashi.

Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na
munafukai basu barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa
bazata sabu ba shidai ya mata shiru harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa
rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be sake kiranta ba idan ma ta
kirashi baya dauka se yau Juma’a daya dawo garin suka hadu.

Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar
a karanta mata yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita
da Hajia Addah aka shige mota.

Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da
abin ya isheta tace “Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara
mara mutunchin kawai, kuma duk baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga
ka mutu”.

Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula
da Iman, Banda wanka a tsundumata a ruwa, suna tsaye ya saka Nurse ta kwatanta musu
yanda za’a ringa wanke mata jikin shima ba kullum ba musamman yanayin garin sanyi
ya kankama.

Sannan ya dora musu da bayanin in so samu ne mamanta kadai zata ringa daukarta kar
a jagwalgwalata su tabbatar kuma ko yaushe tana cikin dumi kar ake fitar da ita
cikin iska ko sanyi a kula da kayan da za’a ringa saka mata kuma.
Sallama sukayi suka tafi bayan ya basu ranar da zasu dawo ganin likita.

Bashir be yadda ma an dauke ta a hannu ba cikin Baby carrier daya siyo tundaga
lagos ya sakata ya dauka Addah ta hau salati da salallami wai ya saka ya a kwando
to duk bala’in sa dai ko mayu ne su se ya basu yar in sunje gida tunda ba da ita ze
ringa yawo ba,

shida be tankata ba. Seda ya ajiyeta dakyau ya maqala belt din ko ina sannan ya
shige ya tada mota har sukaje gida kuwa Addah bata saduda ba se sababi takeyi.

A gidan ma suna zuwa da kansa ya bata feeder ta fara sha dan bottle feeding suke yi
kafin ya bawa Amirah taci gaba da bata yana tsaye, seda ya tabbatar tasha yanda ya
kamata ya dagata kamar kwan da baya so ya fashe ya sakata a kafada tayi gyatsa
kafin ya kwantar da ita a dan gadonta. Seda ya dauketa hoto a wayar sa sannan ya
juya.

Kallo daya yayiwa Amirah dake doka uban Murmushi saboda ganin irin tattali da
kulawar da yake nunawa yarinyar, ta san yanzu ko Albarkacin Iman seta qara matsayi
a zuciyarsa shi kuwa gogan tsaki ya buga ya fice daga dakin dan haushinta yake ji.

Yana fita Addah da jama’arta suka duru daki ganin Baby, kamar me tattaro kaya ta
zura hannu zata cukumota Amirah kuwa tayi caraf ta riqe tana cewa “Haba Addah
bakiji me likita yace bane shine zaki kawo mata wannan cafkar ai seki ballata”.

Suka kwashi salati ita da jama’arta kafin ta fara masifa tana cewa “Eh lallai yanzu
na yarda ba iya Bashir ne tanbadaddenba harda ke, yo in banda tanbada ni uwarki
zaki hana na dauketa har ni zaki gayawa kar a karya miki ya, to da ban haihu ba yau
se nayi kuka kiji da jinki seda na haifi Goma na binne takwas gaku nan biyu a raye
harke ma kinyi yar kanki zaki nunamun sanabe da iyayi”.

Inna Gaji ce ta ceci Amirah tace “Ba haka bane Fattu yanzu dai barta mu kalla daga
haka dan Allah abunda in muna da tsahon rai watarana da qafarta zata taka ta hau
jikin duk wanda take so” haka aka lallaba Addah kowa ya leqa yarinya dake baccinta
masha Allah kyakykyawa da ita kowa se yace ta kwaso kaman nin yayan Ma’u.

Addah dai bata haqura ba seda ta daukota Amirah na kumbura baki tana komai,
“Oh ni Fatu wannan abu kamar yar kyanwa, kwanta karna manta Dan mutum ne nayi jifa
dashi” ta fada tana maida yar cikin Gadonta kafin ta harari Amirah data cika baki
da iska tayi qwafa ta fita daga dakin.

Bashir kuwa yana fita Part din Ma’u ya bude ya shiga, ya zuqi qamshin da a gurinta
kadai ya sanshi dan gidanta na nan dana Lagos qanshi su daya duk kuwa da bata ciki
ya rigada ya kama Gurin se a sannan ya tuna dakin masu jegon ma daya shiga kodan
Air freshener beji ba bare Turaren wuta.

Wanka ya farayi ya yi sallar Isha da shafa’i da wuturi sannan ya shiga kitchen ko
ze samu abinda ze ci tunda can basu bashi ba. ya yi sa’a kuwa cikin Freezer ya samu
farfesun kayan ciki dama mutuminsa ne nan da nan ya dumma ya dauki bread ya hada
tea ya fara ci. Seda ya kusa cinye wa naman suna ya fado masa a rai, kunsan
mutuminku ko kura Albarka nan da nan ya qarasa cinyewa ya dauki waya ya dannawa
Amirah kira dan baya so ya koma su hadu da Addah.
Amirah na cikin waya da Tailor data bawa dinki dan tuni ta kai musanyen lace din da
aka sako mata na barka ta karbo wani ta bada dinki da sauran kayan da zatayi amfani
dasu a lokacin ma tailor yana gaya mata ya gama ne gobe ze kawo ya karbi bakance
din kudinsa, ganin kiran Bashir yasa ta cewa Tailor tana zuwa ta amsa wayar da
fatan Allah sa Zancen sunan ze mata.

“Kizo ina son ganin ki, ki taho mun da nawa kason Naman” ya fada a taqaice. Seda
cikinta ya bada qulululu dan bata taba zaton ze tambaya ba. Tas suka rabe naman nan
ko gutsiren hanji beyi saura ba ita yanzu me zata ce masa?

Ai kuwa beci ta manta ba aduk sanda Anty Asma’u ta haihu kasawa yake ya tsare se an
cire masa nasa kason, tana kuma yawan jin Asma’un na qorafin daga baya se ya biyo
wanda aka aje mata ya cinye ta rasa wane irin so Bashir yakewa Nama a rayuwarsa
dukda gashi yanzu ita sun hada sun lamushe.

Haka ta zari mayafin ta ta fita tana taraddadin me zata ce masa, a qofa taci karo
da Addah ta dawo daga raka baqin ta.
“Ke kuma ina zaki fita a daren nan da danyen jego” ta fada tana kallon ta ganin ta
da mayafi.

“Yaya Bashir ne yake kirana”
“Oh to se kin dawo” Addah ta fada tana rabeta zata wuce se Amirah ta ruqota tana
rartaba ido.

“Ya akayi se wani qifta ido kike kamar an kama Kwarto?”

“Addah wai cewa yayi in taho masa da kason naman sa na suna” cewar Amirah.

“To se ki tafi ai” Addah ta fada tana son wucewa ciki.

“Kin manta Addah ya qare fa babu ko diddiga yanzu me zan ce masa”

“Ke dallah matsa ki ban guri se kice masa ya qare ko kice an hada an kaiwa Nafi
bashi kenan ba”.

“Addah wace Dadan kuma kin manta itama fa baki basu ba wanda aka ware musu bashi
kikace a bawa su Hajia Salamatu ba da suka Zo barka kika ce ta rabawa yan group
dinku?”.

Se Addah tayi kasaqe tace “haka ne kuma fa, tab di amma fa mu ma munyi gwari
wallahi to yanzu ya za’ayi?”

“Nima ban sani ba” Amirah ta fada tana marairaicewa. Ta tabbatar laifin cinye nasa
kadan ne akan idan yaji ko su Dada ba’a aikawa dashi ba.

“Kinga yanzu kije kawai in ya tambaya kice kin manta, idan ya biyo sahu ni kuma zan
ce masa Muzuru sun shigo sun cinye bamu sani ba se in nuna masa duddugar bashi
kenan ba, shima ai yasan dangin ku da yawa ya wani se miki rago biyu ai yayi kadan”
(😳) tana gama fada tayi ciki abinta, nama dai sun cinye ba kuma a isa ace su biya
ba.

Amirah kuwa jiki a mace ta shiga palour, ga abinda yake a gabanta amma ta bige da
kallon qurilla taga me aka chanza a ciki i lai kuwa taga sabuwar Kantamemiyar
Cinema Tv bango guda da Asma’un ta saka kana ganin muatanen ciki kamar zasu fito,
sannan ta chanza Dining dinta ba na da bane ga wasu hadaddun Kwanuka akai shikansa
Turkish Centre carpet din ba wancan bane kamar.

Kallonta Bashir yake ba laifi ta sace amma bata gama dawowa daidai ba ga cikinta
nan haryanzu da girman sa Allah dai yasa kar tayi tumbi dan a duniya ya tsani tumbi
a jikin mace kuma da Allah ya taimakeshi Ma’un sa haihuwa Biyar amma har yau bata
da tumbi ko dan tana kula da jikinta ne oho?

yanda yaga Amiarn tana kalle kalle yasa ya girgiza kai kawai kafin yace “Malama ko
zauna mana kin tsaya mun akai. Zama tayi kan Kujerun da suka dade da tsole mata ido
ta kuma quduri niyya itama fa se ya mata irin su yanzu ko ga qarin Dining ma da TV
duk irinsu take so itama a siya mata.

Sake gaishe shi tayi ya amsa hankalin sa akan Tv, jin shiru bata miqo masa komai ba
ya sakashi kallonta yace “Ina naman” dan fa shi har ya dakko a exotic drink coconut
and pineapple dinsa da ze hada ya kora nama seta hau kame kame tana sosa kai tace
“uhm uhm daman”

Idonsa akanta yace “malama daman me kin tsaya kina wani kwana kwana in ma wani abu
zaki tambayeni bani dashi ki bani namana ki tafi daman kiran da na miki kenan”.

“Ai naman ne ya qare” ta zabi da ta fada masa gaskiya kawai komai ta fan jama
fanjan.

“Ya qare?” Ya tambaye ta, se daga masa kai alamar Eh dan ta kasa kuma bude bakinta
saboda kallon da yake mata.

Daurewa yayi ya danne bacin ransa kafin yace “ toh kun kai gidan Dada kun bawa
Ma’una nata ko?”

“Ai se tafi da rikicewa, kai ta juya masa alamar Aa cikin tsawar da seda ta zabura
yace “Malama ki bude baki kiyi mun magana ko”

Jiki na rawa tace “Ni wallahi ban sani ba kasan bani da lafiya su Addah ne suka
raba ban san kota kai musu ba dan ni wallahi ko yanka daya banci naman ba”.

Ya tabbatar basu bawa ko daya daga ciki ba kenan, dan haka kawai yace ta tashi taje
kafin ya jawo wayarsa ya danna kiran Dada yana saita fushinsa. Bayan ta daga suka
gaisa, tambayarta yayi an kai musu naman suna kuwa tace Aa.

“Kar kace zakayi magana Bashir nama dai Allah na tuba kullum ai muna ci, ba wani
Abu kasan yan gidan su nada yawa kowa ze so a qulla masa” Dada ta fada da son
kwantar masa da hankali dan tasan Bashir da Nama.

Seda yayi kokawa da bacin ransa kafin yace “Amma Dada raguna har biyu manya ne fa
ba wai qanana ba su soya su cinye ko yanka daya su kasa kai wa uwata idan ni da na
siya banda mutunchin da zasu bani sannan ga Ma’u da yara gaba daya suna cikin gidan
a soya duk su kasa basu”.

“Kadaiyi haquri” Dadan ta sake fada kafin su kayi sallama. Ransa a bace ya shiga
dakinsa ya kwanta se kuma ya ja wayar ya kira Asma’u dan yau duk basuyi waya ba.

“Ran Alhaji Bashir Baban Ali ya dade” ta fada cike da nishadi dan hirar sa suke yi
da Yaya Bilki ya kira. Murmushin da beyi niyya bane ya kwace masa kamar wanda ake
watsawa ruwan sanyi yaji zuciyar sa na huce wa, muryarta kadai ta wanke masa bacin
ran Naman suna seya gyara kwanciya yana cewa

“Ba wani nan bayan kunyi tafiyar ku ma kin manta dani inaga sena biyo ku sannan
zaku dawo”

“Haba dai kwatakwata fa kwanan mu biyar yau cikin weekend muke saka ran dawowa ai”
Asma’u ta fada.

“Shikenan ma kinga da kun dawo se mu wuce kawai, na gaji da zaman gwauranta kan
nan”.

Dariya tayi kafin tace “oh kana Gombe kenan”

“Eh na shigo dazu, an sallamo Fatima yanzu tana gida”.
“Masha Allah Allah ya raya mata ya bata lafiya, ashe Addah aka saka”.
Da “Amin” ya amsa ya share tambayar ta ta. To me take so yace mata in dai ba son
tada zaune tsaye kuma ba.

Yaran ya tambayeta tace sunyi bacci suka dan taba hira kafin sukayi sallama bayan
sun gaisa da Yaya Bilkisu.

“Kinji mutuminki nace ashe Addah aka saka yayi kamar beji ba” Asma’u ta fada bayan
ta ajiye wayar.

“Kema da neman magana kike wallahi me kike so to yace miki?” Cewar Yaya Bilki
“Me kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login