Showing 285001 words to 288000 words out of 295847 words
laifin Rahima a tunaninsa yaudararsa tayi taki fada
masa wace mamanta"
Jinjina kai ya rinka yi "indai zaki yiwa Emzee wannan kukan ni kuma me zaki yi min
idan na kamu da son wata aka rabamu?"
"Kace me?" Ta jefa masa tambayar idanunta sun wani kankance tana huci.
Dariya ya soma yi mata "cewa nayi fa...ke dai banyi magana ba"
"Ya dai fiye maka idan ba haka ba kuma yau babu bacci a dakin nan" ta juya masa
keya.
Kwanto ta yayi jikinsa "wasa nake yi miki Schatzi don ki saki ranki. Ina jindadi
idan naga 'yan uwa suna son juna domin Allah. Keep it up my baby amma fa kada kowa
ya kamo matsayina"
Sunkuyar da kai tayi tana jin kunya "kowa matsayinsa daban...KAIMA.KA.SANI"
"Wanne ne matsayin Awwab?"
"The only man in my life"
Rungume ta yayi suna shakar kamshin juna daga baya ya tasheta daga kan gadon "muyi
wanka idan nayi sallar magrib zan koma wurinsa muyi magana man-to-man. Amma ki sani
tun wuri sai na rankwashe shi. Haka kawai ya janyo min dan janbakin da naci burin
gogewa idan mun dawo ya bi hawaye ya gudu"
Da sauri ta tashi ba shiri ta koma ta zauna. Abu goma da ashirin ke damunta, dama
jikin lallaba shi take ga kuma hawa rakumi da tayi dazu ta rinka jin kanta kamar
akan kaya. Runtse idanu kawai take yi Awwab dama ya san matsalar yana mata sannu
suka yi wanka ta gasa jiki sosai. Ana kiran magrib yace mata za'a kawo abinci
takwas da rabi idan ta ci ta yi isha ta kwanta kafin ya dawo. Da kyar ta tsakuri
abincin tana idar da sallah bacci mai nauyi ya kwasheta saboda irin gajiya da ciwon
jikin da yayi mata rubdugu lokaci guda.
Tare da su Daada Awwab yayi sallah ya nemi Ibrahim ya kira masa Emzee. Dawowa yayi
yace yana kwance kamar bashi da lafiya kuma yaki bari ya fada a cikin gidan.
"Kyale shi muje dakin"
Ibrahim sauri yake yaje wurin Zayyana bai shiga dakin ba. Awwab na shiga ya same
shi ya hada kai da gwiwa zaune a kasa. Kusa dashi yaje ya zauna yayi irin zaman da
yayi suna zaune kusan minti biyar sannan Emzee yace "yaya zanyi Hamma?"
Ya tabbatar dole zai ji daga bakin Radhiya kuma abinda ya kawo shi kenan.
"Rahima tana sonka?"
"A da ba! Ni yanzu ban ma san me ta daukeni ba" ya amsa cikin kunar rai.
"Bana jin wannan yarinyar mai nutsuwa da hankali ga karancin shekaru za ta iya
amince maka saboda wani mugun nufi. Emzee open your heart and listen to its voice.
Me kake so?"
Baiyi wani tunani ba yace "Rahima"
"Shekarun baya dangina sun rabani da Radhiya a tunaninsu sunyi domin karfafa
zumunci sai gashi ya lalace fiye da zato da tsammanin kowa. Idan kana tunanin za ka
gujewa Rahima saboda zumunci ne you are making a grave mistake. Emzee aurenka da
ita shine abinda zai fi komai saurin gyara abinda yake tsakanin Ummi da yayarta."
Da sauri ya dago kai "Allah Hamma?"
"Talking from experience" yace da murmushi "da ace tun wancan lokacin na auri
Ghazalatu da Radhiya zumuncin iyayenmu da yafi karfi iyaka mata suyi kishi a
junansu. Amma da hakan bata samu ba sai da akayi shekara uku su ukun suna jin
haushin juna ana rigima mara tushe. Babu wanda nake fadawa amma I hate myself da na
zama dalilin faruwar hakan so if you can avoid it please do so"
A raunane Emzee yace "ina jin ni fa yanzu ta dena sona ta sami wani"
Awwab ya ce "So da wahala yake komawa ki. Kai dai kada kayi wasa da damarka at the
same time ka tuna cewa kaima yaro ne ko karatu baka karasa ba. Zanfi so ka gama
karatun ka fito da karfinka ka yaki zuciyar Rahima har sai ta amince maka."
"To yanzu dai in kyaleta?"
"Da zancen soyayya kam ka rabu da ita ka gama karatu itama ta gama secondary. Amma
try your best ka tabbatar ka mamaye rayuwarta..."
Chuckling Emzee yayi yau fa yana daukar darasi sosai "how?"
"Kada ka bari wasu mazan su sami dama. Keep her close, babu zancen soyayya amma ka
bata kulawar da ko wani yazo a bayan idonka zata rufe ido ta kore shi batare da ka
sani ba ma"
Haba Emzee ya rike "Allah Sarki Addata, Hamma ka rinka yi mata a hankali kada son
ka yayi mata yawa"
Keyarsa Awwab ya talle yana dariya "kai kace ita, iya tace kai ni mai bada shawarar
kuma baku damu dani ba"
"Daga fadan gaskiya" ya turo baki.
"Ladan kukan da ka saka min mata ne...bari na koma na barta ita kadai karshenta ta
kasa....."
Kofa Emzee ya bude masa da sauri "Allah Ya bamu alkhairi ba sai kace komai ba" ya
kara da toshe kunnensa kada ya jiyowa kansa.
Awwab ya fita yana dariya sosai ya ce masa "ni dai ka daure ko P.O.P ne kayi sai mu
aurar da kai....ga Rahima 'yar karama da ita har ta bani tausayi"
Kamar zaiyi kuka ya ce "wayyo Hamma ya na neman fassara ni"
"Me kaji nace? Daga cewa 'yar karama to ba karamar bace?" Ya kuma yin dariya.
"Wallahi zama da Adda ya fara nunawa a jikinka ni dai sai da safe" Emzee ya bata
rai ya rakoshi waje.
Tare da su Yousuf suka tafi. Yana zuwa shima kwanciya yayi yana rungume da
Radhiyansa. Washegari akayi gagarumar dinner da daddare inda ma'auratan suka yi
shigar buzaye su da iyayensu. Da safe kuwa kowa ya kama gabansa. Yousuf da Arifah
Hawaii suka wuce honeymoon daga can kuma zasu tafi France inda gidansa yake kusa da
na iyayensa.
Su Awwab ma a ranar da suka koma washegari bakwai na safe suka tashi zuwa Athens
babban birnin Greece zasuyi kwana goma kafin ya koma aiki.
Duk wannan abu da akeyi babu wata alama ko kadan da Rahima ke nunawa ta damuwa sai
dare yayi ta kwana tana kuka. Sabanin Halifa da yake namiji ita abin ya tsaya mata
a rai fiye da kima. Da ciwo matuka ace mahaifiyarka ta cutar da wani, wanin ma
kanwarta ta hanyar asiri har tayi shekaru goma babu ido. Ita nata daya ne yanzu
baya bambance mata abubuwa amma yaya take ji bare wanda zai ga tsananin duhu na
tsayin lokaci. Abu na biyu bai wuce mahaukacin so da tausayin Emzee da take yi ba.
Ko kadan bata ganin laifinsa don ya kyamaceta. Uwa tafi karfin wasa. Ita ma bata
guji Salame ba duk munin halinta ta yaya shi ba zai tsayawa tasa mahaifiyar
ba..mace kamar Ummi mai kyauta da kyautatawa. Bayan dogon tunani da koke koke a
boye ta yankewa kanta shawarar hakura dashi har abada. Emzee ba sa'an aurenta bane
da kunya ta iya hada ido dashi bayan abinda Ummanta tayi musu. Sai yanzu ma take
dada godiya ga Allah da ita ta samu a ido da wayar ba Radhiya ba. Da zasu barta ta
koma Sumaila da tafi jindadi ma. A zahirin mu'amalarta da mutanen gidan duk
karancin shekarunta ta iya daurewa ta nunawa Ummi bata da matsala. Har daki Ummin
ta kirata akan maganar Emzee ta ce mata ko yana sonta bai taba fada ba. Shi kuma
yana makaranta bare ya karyata.
Satinsu guda da gama biki har an kai Rahima sabuwar makarantarsu anyi sa'a sun
barta a SS3 amma Daada yasa an dauko mata lesson teacher wuni suke suna karatu
saboda ta ci WAEC tunda bata yi rejistar NECO ba kuma an riga an makara. Ummi ma ta
soma zuwa Baze tana kuma samun kulawa sosai daga maigida ran gida Zayyan Tureta.
Cikinta mai laulayi ne shiyasa daga makaranta sai daki saboda rashin son kamshin
gidan.
A yau ana sauran kwanaki hudu su Radhiya su dawo Emzee yayi magana da Awwab wanda
yace kada ya manta shawarar da ya bashi game da Rahima. Bayan sun gama hirarsu ne
ya tura mata text.
Zaune take tana kokarin solving din wani aiki da lesson teacher din ya bata a
physics text din ya shigo. Duk a zatonta irin na layin wayan nan ne shiyasa
zuciyarta tayi wani irin bugu da ta ga sunan Emzee. Jikinta wata irin rawa ya kama
yi ta bude da sauri.
(Kanwata kwana biyu boko ya boyeki. Ina fata babu wata matsala a sch din taku. All
the best Rahima, Allah Ya bada sa'a. Yayanki)
Ta karanta wannan gajeren text yafi sau shurin masaki. Dama malamin nata ya tafi
aikin ta zauna yi sai kuma ta kasa fahimtar komai dole ta tashi ta shiga ciki.
Wayarta a hannu lokaci lokaci sai ta duba ta kuma karantawa duk da tana kwabar
zuciyarta da take jinya har yanzu.
Da safe ma tana shirin tafiya makaranta wani text din ya kuma shigowa shima dai
addu'a ce yake yi mata da fatan alkhairi. Baiwar Allah sai ta koma ruwa tsundum dan
karfin halin nata ya guje mata. Haka dai akayi karatun ta dawo gida. Daga bakin
kofa take jin muryar Salame tana cewa maiaikin nan gidan kanwarta ne ita bazata ci
dan wake ba a dafa mata sabon abinci.
"Banda ta raina ni ai tasan yau zan taho amma shine da zata tafi makarantar bata
bar muku sallahun dafa min komai ba sai danwake? Ko ki dauke shi ko na yanko masa
tsinuwa dashi da hannun da ya tsumbula shi a ruwan zafi"
A kidime yarinyar tace "Ta fada mana zaki zo amma kinfi son danwake"
"Da kenan! Amma Yasin bazan zo Abuja inci danwake ba kamar wadda iyaye suka cewa
jeki kya gani"
"Harda farfesun da salad din ma na kwashe?" Mai aikin ta tambaya a tsorace.
Salame ba kunya ta karbe tray din "kece bakiyi bayani ba, cha nake mai da yaji zaku
bani."
Da gudu-gudu Rahima ta shigo ga takaici ga dariya ta fada jikinta.
"Umma?"
Salame ta washere baki kamar gonar auduga ta rungumota "Rahimata...."
Allah Sarki zuciya na wuya sai kawai ta soma kuka tana kankame a jikin mahaifiya
mai dadi ko da kuwa ta buzuzu ce. Da kyar Salame ta samu Alh Indararo ya barta ta
taho sai da tayi karyar zuwa zata yi suyi magana akan yaran da za ta basu. Malamijo
kuwa cewa yayi indai tasan rigima ce za ta kawota Abuja bai yafe mata ba idan ta
je. Damuwa ce fal a zuciyarta akan Rahima. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da
yarinyar sosai. Daga baya ta fahimci dama can tana son abarta wasu abubuwan ta saka
a gaba kawai.
Wannan kuka na Rahima ya tada mata hankali fiye da tunani ta kama hannunta zuwa
dakin baki da yake kasa.
"Rahima wani abin kika sake ji nayi?" Ta tambayeta a tsorace tana fata yanzu kuma
ba labarin ta taba son Zayyan Tureta bane ya fito.
Girgiza kai tayi hawayenta yana karuwa cikin rawar murya ta ce "Umma nace ki rinka
yi min addu'a Allah Ya cire min Ya Emzee daga raina Umma ba kya yi...Umma ko sau
daya kiyi min addu'a a rayuwata" ta durkushe a kasa tana matsanancin kuka.
"Ina miki addu'a duk sallah Rahimata, idan ban miki ba wa zanyiwa bayan duk abinda
naja miki" Salame ji tayi ta tsani kanta tana Allah wadai da son zuciya. Ita bata
girbe da hannunta ba 'yar da take jin kunya ita ce take mata dakon wahala.
A wannan lokacin Mairama ta nufo dakin saboda an sanar da ita zuwan Salame. Nan ta
jiyo kukan Rahima ta bude kofar da sauri sai ta ga sabanin abinda ta zata wato tana
dukanta rungumeta tayi.
"To me yasa bana jin komai, kirjina kullum ciwo yake. Ki koma gida dani ina kunyar
Ummi, ina kunyar Daada dasu Adda Radhiya"
Fuska sharbe da hawaye Salame take shafa bayan Rahima "kiyi hakuri zan roki Mairama
na santa da hakuri za ta duba lamarinki tunda tana sonki"
Rahima sai girgiza kai take yi "a'a Umma bazan taba auren Ya Emzee ba ko...."
"Ya isa haka Rahima zo ki fita" Mairama ta yi mata tsawa cikin bacin rai "ina zaune
da ke ina bibiyar me ya sameki ni kin kasa fada min saboda ni baki daukeni uwa ba?"
"Ba haka bane Ummi kiyi hakuri" tace tana dawowa kusa da ita tana wani irin kuka.
Rungumeta Mairama tayi sannan ta ce "Karami ya taba cewa yana sonki?"
Kai ta daga kawai jiki na rawa. Wannan wane irin so ne mai cin ruhi da ba za ta iya
hakura kamar yadda take son yi ba.
Cikin kulawa ta sassauta muryarta "indai ni na haifi Zayyan in sha Allahu sai kin
amsa sunan matarsa tunda shi ya fara nemanki"
"Ummi a'a" tace saboda sanin da tayi cewa yanzu baya sonta.
Salame ta galla mata harara ga hawaye har yanzu "ke kaniyarki, ku ji min yarinya
ana baki kina kin karba"
Mairama murmushi tayi sannan ta ce "Kina so muyi fada ne?"
"A'a"
"To kada na sake jin zancen me ya hadani da Addata a bakinki ko na 'yan uwanki sai
na saba muku. Babu ruwanku tare kuka ganmu. Karami kuma ki tattara shi ki zuba a
kwandon shara ki fuskanci karatunki sai ya nemeki da kansa. Akwai wani namiji da ya
isa ya ja wa RAHIMATA aji ne" ta kalli Salame da jin baki taji me zata ce.
"Na fada miki Mairama ba dai hakuri ba ke dai barta da zuciya kamar kuturwa" cewar
Salame tana fyace hanci da mayafinta.
Rahima tayi murmushi ta ce "kai Umma"
Mairama tayi 'yar dariya ta ce "Kin dai ga yadda nake hakuri da ita ku ma sai kuyi
ta yi. Kiyi wanka ki ci abinci. Yau ranar zuwan malamin islamiyyar ne ko na
lesson?"
"Lesson ne"
"Kici ki kwanta zan kira shi nace ya bari sai gobe....idan na sake ganin hawayenki
akan wata damuwar da ba taki ba ni da ke ne"
Fita Mairama tayi Salame ta bi bayanta da sassarfa. Kamar ba ta ji ta ba sai da ta
shiga dakinta itama ta shigo kawai ta durkusa a gabanta tana kuka. Itama Mairaman
kuka ta saka tana tsaye Salame na durkushe tana yinsa mai cin rai da zuciya abin
tausayi.
Lallai duniya mai yayi duniya juyi juyi yau ita Salame Ali ita ce durkushe a gaban
Mairama Ali tana kuka irin wannan "Ki gafarceni Mairama wallahi ban kyauta ba,
soyayya ba hauka bace ni ban san me yake damuna ba ko tunanin me nake har na rinka
yi miki irin wannan diban albarka. Da gaskiyar mijinki hassada na dorawa zuciyata
gashi ina nan jiya e-yau. Don Allah ko bayan raina Mairama ki aurawa Karama Rahima
ko ta sami saukin cutarwar da nayi mata. Kinga ni ce da laifin amma ita ke da
wahala banda haka ina ita ina wata soyayya mai zafi haka..."
"Adda ki tashi ki zauna muyi magana"
"Idan kinga na zauna to yafe min kika yi"
"Ke fa kika ce mun wuce wannan matakin tun a Nijar" inji Mairama
"Lokacin ma wasa ne nake yi mutum baya wasa da rokon gafara." Salame ta sake
kwantar da kai.
"Komai ya wuce a wurina, dama can ke kika jawo muna zaman zamanmu kika canja hali.
Allah Ya kara mana hadin kai"
Wani kallo mai cike da girmamawa da mutuntawa take yiwa kanwarta. Idan tana da
sauran shakku na cewa Mairama tayi mata fintinkau a komai ya kau a yanzu. Za ta iya
rantsewa cewa idan ita ce Mairama sai ta baro mata rashin mutumci kwando kwando
kafin ta hakura. Halinsu ba daya ba haka nan zuciyarsu da bambanci. Kila shiyasa
ita ta kare a kasa marainiyar wayonta ta haye ta barta.
"Nagode, nagode, nagode...amma nace ba, maganar Karami da Rahimata za ki sanar da
maigidan naki da wuri ko"
Dariya ta baiwa Mairama "Adda Salame kenan maganar aure ai babu ita?"
"Cewa zakiyi baki yafe min ba!" Salame ta saka sabon kuka.
Zaunar da ita Mairama tayi don ta gaji da tsayuwar ta soma magana a nutse "Adda
daga Karami har Rahima yara ne masu karancin shekaru. Shi yanzu yana ashirin da
biyu da watanni ita ko sha bakwai bata rufa ba haka ne?"
"Eh to amma auren wuri ba yafi ba ko don fitintinun zamani"
"Nima zanfi son haka amma shi da yake namiji bai gama karatu ba. Ita ma bana so a
yanke mata ba hanzari muke yi ba. Wannan soyayyar da suke yiwa juna wuta-wuta kamar
yaki harda kuruciyar da take cinsu su duka da kuma isharar Allah akanmu ni da ke.
Mu barsu su kammala, su kara nutsuwa su sake hankali sai mu ga abinda Allah zaiyi.
Kada kiyi min mummunar fassara duk duniya babu matan da Karami zai kawo min a
matsayin suruka nayi farinciki sama da Rahima ko Zayyana saboda su ne 'ya'yana. To
Alhamdulillahi ba tare da wata dabara daga garemu ba sun daidaita kansu. Mu kara
hakuri kadan wannan hayakin ya sauka hankali ya game jikinsu musamman shi namiji da
ragamar gida za ta hau kansa"
Kallonta Salame take cike da sha'awa tana murmushi "lallai boko ya ratsaki Mairama
ji yadda kike fito da bayani mai ma'ana da kuma hangen nesa. Hakan yayi min wallahi
dama burina ni dai in hada zuri'a dake duk tsiya ko albarkacin jikoki sai kin yafe
min" ta kare da murmushi.
Sai da Mairama ta dara don tasan tsokanarta take yi "zan yiwa Rahiman bayani da
kaina ba rabasu zanyi ba amma a maida kai wurin karatu. Babban tashin hankalinta
kuma kinsan akan yadda kike yi ma ta ne ina rokon arziki ki gyara ko zamu ji dadi"
Dofana mazaunanta tayi a kusa da kanwarta sai ta ga bata kyareta ba sannan ta saki
jiki "Mun riga mun shirya da ita fa...zancen gaskiya ma ina ganin laifinku a yadda
na canza ke da Malamijo"
"Da muka yi me?"
"Tunda abin nan yake ta faruwa da kun sani kun karbo min taimako ko da na ruqiya ne
don jikina yana bani me yiwuwa shafar jinnu ke damuna"
Mairama ta kwashe da dariya "idan jinnu basu shafeki ba ai wannan annakiyar
kazantar za ta shafeki. Adda ji hakoranki don Allah koraye babu kyaun gani. Na san
da wuya idan Alh Indararo yana iya kusantar wannan bakin naki"
Salame ta rike haba "su Mairama babu ranar girma, kada dai kice min kuna nan kun
daddangwalar bakunan juna ke da mijinki"
Dariyar da Mairama tayi ta jima rabonta da irinta "wai dangwalar baki...to naji ko
ma me kike kiranshi ku ba kwa yi ne?"
"Allah Ya agajeni ni ko magana yake min kaina baya matsowa kusa da bakinsa mai dan
uban wari"
"Wai Kura ce za ta ce da Kare maye, ke ma me zai kawo shi gaban naki. Ina ku ka
baro brush da makilin?"
"Tabbb..mu sami na kai wa bakin salati dai shine magana." Tashi tayi tana murza
hannuwa "yanzu dai tunda hankalinki ya kwanata Salame ta dawo gareki a taimaka a
bani abinci"
"Au ni kadai ce hankalina ya kwanta? Shikenan jeki abinki kowa yayi ta kansa"
"Daga wasa sai ki hade rai kamar zawo" Salame ta ce tana murmushi. Babu abinda zai
faranta mata yanzu kuma sama da ganin ko yaya ita da Mairama sun fahimci juna.
Wata dariyar Mairama tayi kawai tana cewa ta kula kazanta ta sami mazauni a tattare
da yayarta.
Abinci Salame taje taci ita kuma Mairama tayi wanka ta sauko kasan. Salame dai kasa
sakin jiki tayi duk yadda ta so saboda wani girma da kwarjini da Mairama ta kara a
idonta. Masu aiki take gani su na rawar jikin cika umarninta kuma ba wai don ita
din ta kasance mai tsanantawa ba. Ko kadan, tsabar iya mu'amala da nuna musu cewa
su