Showing 24001 words to 27000 words out of 295847 words
kowa allura sannan aka shiga bawa marasa lafiyan
taimakon da ya dace. Ta bayan wayar suke magana da Major yana tambayarsu halin da
suke ciki. Nuna masa suke yi babu wani abu lafiya kalau suke.
Ta'aziyar Papa Dolapo yayi musu wanda aka saka gawarsa a cikin motar da zasu koma
da ita nasu sansanin. Idan sunyi sa'a za'a bari gawar ta koma Nigeria. Idan basuyi
ba kuma to a nan za'a binne shi iyalinsa su dau hakuri.
"Shekaranjiya da aka toro wani troop din wannan wasikar tazo. Ta Lt Badmus ce"
Wasikar ya dago musu kowa jiki a sanyaye domin Papa Dolapo ne Lt Badmus.
Major Mustapha ya kara da cewa "duk da ban bude ba amma an fada min matarsa ce ta
haihu. Zayyan makotanku ne ko?"
Kai ya gyada ya kasa cewa komai ya juya ya bar wurin zuciya tayi nauyi.
"Follow him Lieutenant" ya umarci Hadir.
Sai da ya ga sun shiga cikin wurin da yake mazaunin dakinsu ya koma motar da ta
kawusu suka bar wurin.
**********
Rayuwar matan da mazajensu basa nan a barikin babu dadi. Ci da sha bai yanke ba
tunda ana basu albashinsu to amma fa kowacce kullum kwanan duniya da fargaba take
kwana matsawar ba mijinta ta gani ya dawo ba.
Mairama, Mami da Zainab dauriya suke yi kowacce tana son nuna ita ma jarumar kanta
ce mai hakuri da juriya. A gefe daya basu fasa yiwa mazajensu addu'a da fatan
alkhairi ba.
Awwab kusan ya dawo gidan Mairama da zama. A nan yake kwana idan ya dawo daga
makaranta ya lalace wurin wasa da Radhiya. Sunyi shakuwar da har Mairama tana
tabawa kyuya musamman idan zai fita. Kyalesu take yi tana fama da cikinta don ma
laulayin yayi sauki yanzu.
Awwab ya fita da Radhiya sun tafi wurin Mami sai Mairama ita kadai a cikin gida.
Hayaniya ta soma ji daga waje ta yafa mayafi ta leka. Can ta hango Zainab da wasu
matan da suke tare sun zagaye wata. Fitowa tayi cikin sauri jin kamar ana kuka.
"Innolillahi wa inno ilaihi raji'oon....Oko mi tikú" kuka Maman Dolapo take tana
tumani a kasa ga danyen jego.
Mairama ta tsorata da yanayin da ta ganta, ta taba wadda ta fi kusa da ita "what is
wrong with her"
"Ahhh Mama Radhiya...Papa Dolapo don die oooo"
Ita ce amsar da ta doki kunnenta taji gabanta ya yanke ya fadi. Zainab ta matso
kusa da ita tana fada mata wai yanzu aka sanar dasu rasuwar tasa. Cholera ce ta
kashe shi Zayyan ne ma ya sallace shi, sannan anyi masa sutura a can kasar.
Kuka su ka taya Mama Dolapo aka kaita cikin gidanta. Bayan kwana biyu sai ga 'yan
uwanta da yayan mijin suka zo daukansu ita da yaranta guda hudu zasu koma Akure.
Ranar ma wani sabon kukan ne ya barke a tsakaninsu domin da yawa sun sani da wahala
su sake sanya juna a ido har abada. Maman Dolapo ta tafi ta barsu da kewa da kuma
fargabar labarin wa zasu sake samu kuma.
**********
Jaruman kasarmu suna can suna aiki tukuru bisa umarnin da kasa ta basu na wanzar da
zaman lafiya a daya daga cikin kasashen gamayyar ECOWAS.
A yayin da magidanta suke tashi da safe su je ofishoshinsu yamma na yi su koma gida
ga iyalansu, su ci, su sha mai kyau, su kalli matansu da 'ya'yansu su ji dadi
wadannan sojoji suna cikin dokar daji suna fama da cizon sauro da wasu nau'in
kwarin, rashin abinci mai gina jiki, karancin tsaftataccen ruwa balle ayi maganar
wanka kullum da sauransu. Masu aure a cikinsu suna kewar matansu amma babu halin
kasancewa dasu.
Yau da gobe kunnuwa sun saba da jin harbi da karar tashin bomb. Da idanunsu suke
ganin 'yan uwansu, abokansu harsashi ya huda wani sassa na jikinsu sun mutu a take.
Ko kuma bomb ya tashi dasu kana kallon mutumin da kuke tafiya kuna hira dashi ya
tarwatse gabobin jikinsa sun watsu ko ta ina.
Jaruman nan sun yarda sun aminci su sadaukar da rayukansu a duk lokacin da kasa ta
bukata domin zaman lafiya da kwanciyar hankanlin al'ummar kasarsu. Babu ruwansu da
addini, kabila ko wata al'ada. Sun hadu akan abu daya ne wato TSARO na rayuka da
dukiya.
A yayin da wahala tayi wahala, anga jiya anga yau a fanin rashin makusanta ko a
kama mutum a sansanin abokan gaba a gana masa azaba domin ya fadi wani sirri da
za'a iya cutar da nasa 'yan uwan sai ka ga zukatansu sun bushe ana yi musu kallon
mutane marasa tausayi da imani. Sai dai abubuwan da idanunsu suka gani da wanda
kunne yaji wani fa har ya bar duniya bazai taba kusantar abu makamancin wannan ba.
Jarumanmu ababen alfaharinmu, sadaukanmu da babu albashin da kasa zata basu da zai
wanke ciwuka na zahiri da badini da suke dawowa dasu daga filin daga. Ga kuma
iyalansu a yashe madogaran nasu, bangon jinginar nasu basa nan.
Wata hudu da tafiyarsu Zayyan sun fara jiyo kamshin komawa gida wata rana da yamma
gari ya hade yayi bakikkirin ruwa zai iya saukowa a kowane lokaci wani mutum yazo
wurin gaje gaje dashi da shiga irin ta mutanen wani kauye a kusa dasu. Jikinsa duk
raunuka yace 'yan tawaye sun yiwa garinsu kawanya suna harbi kan mai uwa da wabi.
Sun riga sun san mutanen suna yin haka shiyasa su ka shiga motarsu ta yaki su ka
durfafi kauyen da hanzari. A bakin wurin da yake kamar gate dinsu ne su ka hadu da
motar su Major Mustapha. Ya fake da aiki ya taho ganin kannensa.
Duk da bambancin matsayi bai hana Zayyan zuwa ya rungume shi ba. Major yayi turus
yana cewa.
"Stand at attention Lady"
Zayyan ya dago yana gyara rigarsa ya dan basar "Sorry Sir"
Major Mustapha sai yayi murmushi yana mikawa Hadir hannu.
"My Ladies are all grown up, sun dena dariya"
Zayyan ya kara gyara fuska sai dai dole dariya ta kwace masa. Karar bomb suka ji
mutumin da ya kawo rahoton yace ‘yan tawayen sun kai mota shida. Su Major Mustapha
sai kawai su ka bisu.
Sai da suka yi rabin tafiya kawai babu zato babu tsammani sai tashin bomb suka ji a
gabansu ga ruwa ya fara sauka. Mutane ne suka fara bullowa ta tsakanin bishiyu da
yawa ba na wasa ba sun zagayesu. Babu wata mafita sai fitowa suka yi suna musayar
harsashi ga wuta motarsu ta kama saboda tankin mai da aka harba.
Bayan wani lokaci a cikin wannan yanayi ruwa mai karfi ya soma sauka kamar da bakin
kwarya a cikin jejin gari yayi duhu baka ganin komai sai tashin kura, hayaki da
wutar da ruwan bai gama kashewa ba. A gefe guda kuma Zayyan da Hadir ne suke gudun
ceton rayukansu sakamakon bomaboman da suka tashi a wurin har uku ga harbin bindiga
da bazasu iya tantance takamaimai daga ina yake fitowa ba.
A motocin yaki uku suka fito banda babbar range rover da suka ciko ta su Major
Mustapha. A lissafe sun kai mutum ashirin da takwas amma su biyun suka rage wanda
kusan da taimakon Zayyan ne Hadir bai mutu ba. Duk inda ka juya gawarwaki ne kwance
cikin ruwa da jini. Kallo daya zaka yiwa wurin zuciya ta tsinke kaji inama dai
mafarki ne. Duk mai imani bazai so koda makiyinsa ya tsinci kansa a wurin ba. Suna
cikin wannan jeji dumu-dumu a tsakanin abokan gaba. Hankulansu a tashe kunnuwansu
basa jin komai sun dode saboda karar bomb ya yi musu karfi.
Zayyan ne ya hango Major Mustapha wanda a bisa la'akari da matsayi shine shugabansu
a wannan fitar. Mutumin da yake tsananin mutuntawa kwance yana daga hannu. Baya
yayi da sauri Hadir yayi masa kallon mamaki don bai iya ganin komai shi saboda
karfin ruwan "kada kace min komawa zakayi? Kazo mu bar wurin nan don Allah"
Kallon Hadir yayi ya sake kallon Major din ya koma gareshi a guje. Dago shi yayi da
zafin nama sautin harsashi yasa shi komawa ya kifa a kansa suka fadi tare. Wata
siririyar kara Major Mustapha ya saki mai cike da tsananin azaba wadda ta saka shi
kai duba gareshi. Wani mummunan firgici ne ya saukar masa ganin kafar Major din ta
dama a gutsire bomb ya tarwatsata. Zuciyarsa ce tayi nauyi ya soma kokarin daga shi
domin su gudu.
Wata damka yaji ya kai masa ruwa yana wanke musu fuskoki "Lieutenant get out of
here"
Bai saurare shi ba ya ciccibe shi duk da cewa ya fishi girma sosai ya saba shi a
baya. Ture shi yaji yana yi yana dan dake muryarsa "this is my final command to you
Tureta. Go!"
Sojoji sun horo da tsananin biyayya ga na gaba amma wannan karon bazai bi ba. Gudu
ya soma yi dashi suka nufi inda Hadir yake tsaye hannunsa na zubar jini sakamakon
harbinsa da akayi suka soma yankar daji.
Cak ya tsaya ya dena tafiya har Hadir yana cewa "muje mana"
Gabansa ke lugude ya kalli kafarsa ya dago a razane "Karbe shi ku bar wurin nan"
Major ya dan leko da kansa ta saman kafadar Zayyan "Lieutenant?"
Wata ajiyar zuciya ya sauke kafin Hadir ya karbi goyon duk da shima yana da
raunuka. Matsawa yace suyi nesa dashi sannan ya dago idanunsa da suka jike da
hawaye sosai. Kamar mai rada yake musu bayani.
"Bomb ne"
Su biyun duka suka kalle shi a gigice. Bai nuna damuwa ba ya cigaba da magana
hawayensa suna tona asirin firgicinsa. Motsi kadan zaiyi bomb din wanda aka binne
cikin kasa ya tarwatsa shi. Daya bayan daya yake kallonsu
"My friend..." yace da Hadir
"....Major am afraid this is the end"
Abinda Major ya dade baiyi ba ya soma shima sai kuka duka su ukun babu mai
rarrashin dan uwansa.
Kafarsa ce ta danyi rawa cikin karaji yace su bar wurin. Ba yadda suka iya dole
suka bar wurin a guje zukatansu suna kuka idanu na hawaye. Basuyi nisa sosai ba
suka jiyo muryarsa mai dadin sauraro idan yana yi musu limanci.
"Mairama, Alheran waye zai dubi iyalina?"
Kuka ya fashe dashi sosai a hankali ya soma karanto kalmar shahada yana ji a ransa
wannan ma dama ce da Allah Ya bashi.
Sunyi gudun rabin kilometer suka ji wata gigitacciyar kara wadda tasa su biyun
faduwa su ka gangara kasan wani katon rami. Kafin su kai kasansa daga Major
Mustapha har Hadir tunaninsu yana ga Zayyan Muhammad Tureta. Zayyan sarkin
barkwanci, mutum mai tsananin so da kaunar iyalinsa da basu da wani wanda zasu
jingina dashi suji dadi idan ba shi ba ya mutu a bakin aiki bayan yayi matukar
kokari wurin tseratar da rayukansu.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 13. BAYAN AWA TALATIN DA BIYU
Mutumin da ya kai rahoton karya ga rundunar su Zayyan shine durkushe a babban
sansanin da su Major Mustapha suke. Kuka yake kamar karamin yaro ga sojoji sun
tsare shi babu wasa a idanunsu.
"Ka tabbatar ba yaudararmu kazo sake yi ba?" Cewar Captain Jonah.
Mutumin ya daga idanunsa jajir ya sake maimaita musu cewa yan tawaye ne suka
kamashi. Sunyi masa mugun duka sannan aka umarce shi da yaje ya san yadda yayi ya
kawo sojojin Nigeria wannan wurin. Idan baiyi ba garinsu gabadaya zasu tasa. Tsoro
ya sanya shi cika umarni. Amma suna zuwa da ya ga me ake yi ya gudu. Shine yazo
nema musu agaji duk da yasan da wahala a samu mai rai cikinsu.
Yana rufe baki wani zuciya ta debe shi ya buga masa kasan bindiga a keya ya fadi
sannan ya bishi ya rinka duka da kafcecen takalminsa. Da kyar aka rike shi kowa ya
sani akwai kaninsa uwa daya uba daya a cikin wannan sansanin.
Motocinsu suka cika da makamai suka tafi tare da wannan mutumin. Daga nesa suke
hango sauran hayaki ga kauri ya karade wurin. Dirgowa suka shiga yi daga motocin
suna gudu har suka je wurin. Su din sojoji ne fa jaruman maza amma hankulansu sunyi
mumminan tashi da ganin wannan kisan gilla da aka yiwa mutanensu. Binsu suka rinka
yi daya bayan daya wadanda jikinsu yayi alamun harbi ne kawai likitocin cikinsu
suna dubawa ko akwai masu rai. Basu yi dacen samun ko daya ba. Duk da haka shugaban
tawagar yace su bazu cikin dajin babu mai tafiya sai sun tabbatar ba'a bar kowa ba.
Mutum biyu ne suka bi hanyar da su Zayyan suka wuce cikin sa'a sai gasu a bakin
kwazazzabon da Major Mustapha da Lieutenant Hadir suka fada. Suna hangosu daya ya
dira ciki dayan kuma yana daga waje ya fara kiran ga wasu gawarwarkin a nan. Sai
dai me, yana juya Major Mustapha yaji yayi wani irin gurnani na azabar ciwo. Ya
zubar da jini ba kadan ba wurin da kafar ta cire ya kumbura suntum ta soma yin
kore. Ihu yasa yana kiran suyi sauri wannan yana da rai don bai ma gane shi ba.
Ya koma ya juya Hadir. Mamaki karo na biyu, shima da ransa saboda bugun zuciyarsa
da yake a raunane amma baya motsa komai na jikinsa. Sauran sun zo an taru an fitar
dasu cikin sauri suka isa sansanin inda aka wuce dasu bangaren kula da lafiya. Daki
ne madaidaici da 'yan kayayyakin taimakon gaggawa da abinda ba'a rasa ba.
Komai cikin sauri ake gabatar dashi domin alamu sun nuna su biyun sun galabaita
fiye da zato da tsammani. Anyi nasarar cirewa Hadir bullet a hannunsa sai dai
buguwar da yayi wanda suke tsammani a kansa ne har yanzu bai motsa ko da yatsa ba.
Babu kayan gwaje-gwaje sosai da zasu iya gano ainihin matsalarsa.
Major Mustapha shima an gyara wurin da kafarsa ta cire. Bayan allurai da ruwa da
ake kara masa babban likitan Major Dalhatu ya tafi ofishin ogansu gaba daya a
wurin. Izinin shiga ya nema ya tsaya a kame a gaban Colonel Fredrick Madueke.
"Sir they need medical attention more than we can provide"
Lt Col Madueke ya dago idanunsa sunyi ja kamar gauta. A yini daya sun rasa sojoji
da dama wanda duka a karkashinsa suke a wannan tafiyar.
"I am trying to reach the HQ at Monrovia Captain . We need to fly them back to
Lagos"
Captain Dalhatu ya juya ya fita bayan ya sara masa. Yasan Lt Col Madueke akwai
tsantseni. Bazaiyi saken da rayuwar wadanda suka tsira zata salwanta ba a nashi
bangaren.
Kwana daya, biyu, uku, hudu....shiru headquarter bata turo helicopter da suka roka
domin a kai su Major airport din Monrovia ba. Lt Col Madueke kullum yana magana da
headquarter sun ce suna jiran feedback daga Nigeria. Abu yaci tura suka debesu da
kansu a motoci ga gargada da komai zuwa Monrovia din. Nan ma a basu dama ko izinin
fitar dasu ya zama aiki. A haka sai da suka kwashe sati uku ana abu daya. Hadir
yana nan jiya-e-yau. Major Mustapha kuwa ya farka amma azabar ciwon kafarsa tasa ya
koma yana sumbatu. Dole yayi sambatu wurin ciwon nasa ya soma fitar da ruwa mai
wari saboda kwayoyin cuta da suka shiga ga rashin kayan aiki. Anyi rigima harda
nunawa juna bindiga tsakanin Capt Dalhatu da wani soja a headquarter din saboda
rashin daukar patients dinsa da akayi. A haka sai manya masu mukami ko wanda yasan
wani shine abin dubawa. Mu kasarmu har kullum wa ka sani wa ya sanka ce.
A rana ta ashirin da bakwai Allah Yayi aka dauki Major Mustapha da Lt Hadir zuwa
Lagos. Yanayin da suke ciki suna bukatar taimako na gaggawa sosai. Kai tsaye aka
wuce dasu 68 Nigerian Army Reference Hospital dake Yaba a Lagos.
An yiwa Hadir gwaje gwaje karshe dai likitoci sunce kawai a jira ko dai ya tashi ko
kuma rai yayi halinsa. Idan da hali ana bukatar 'yan uwansa domin jinya da kuma
fara biyan kudaden asibiti idan ana son su cigaba da aiki a kansa. Buguwar da yayi
a kansa sai ya farfado zasu san ainihin iya damejin da tayi masa.
Major Mustapha kuwa aiki gagarumi yake bukata a rubabbiyar kafarsa. Ciwo wata guda
ya ga izaya ra'ayil aini har yanzu bai san waye a kansa ba duk da ya farka.
Dungulmin kafar ke fitar da tsutsa saboda rashin gatance musu da kasa tayi a
lokacin da suke da bukata. Gasu da rauni ga rashin kayan aiki a inda suke. Anzo
kasar tasu kuma asibiti na bukatar makudan kudade domin su yi masa aiki a yanke
abinda yayi saura na kafar. Sojoji da basu kirguwa sun tafi da lafiya sun dawo
gidajensu da nakasa ta har abada. Shima dai an bukaci a nemo nasa iyalin domin
kulawa dashi da kuma kudin asibiti wanda gwamnati bazata iya daukar nauyi ba duk
kuwa da cewa a kokarin bin umarninta suka riski kawunansu a wannan hali.
BOYAYYUN JARUMAI (NA SARAWA MATAN SOJOJI)
Jiniya ce irin wadda aka kunna ranar tafiyarsu yau ma aka saki. Motoci manya na
sojoji suka rinka shigowa barrack din a guje zuwa bangaren ofisoshin manyansu. A
can aka bada cikakken rahoto game da mutuwar gabadaya sojoji da aka dauka a ranar
tafiyarsu Zayyan daga Giginya Barrack da kuma halin da Hadir da Major suke ciki.
Wuri ba sai ya kaure da hayaniya ba, manyan sojoji ana ta shige da fice suna samun
cikakkun bayanai. Tattaunawa ce tsakaninsu akan yadda ya kamata su bullowa lamarin.
Masu aure cikin wadanda suka tafin wurin tara ne sauran duk samari. Wasu ma basu
dade da zuwa barikin ba.
Matan wadanda suke asibiti dai babu yadda za'ayi a boye musu. Bisa wannan dalilin
aka buga takarda mai dauke da bayanin halin da kowanne yake ciki za'a bawa matarsa.
***********
Mairama tana gidan Zainab taje kitso suna zaune daga bayan gidan wanda katanga ta
karesu babu mai ganinsu. Sannan an dan zarta bangon gidajen ta barin hagu da dama
domin ya zama kariya tsakaninsu da gidajen kusa dasu. Sai dai ba'a hade ginin ba
zasu iya wucewa. Yawanci matan ke amfani da wannan wurin domin ayyukan da suka fi
karfin cikin gidan kamar suya da babbar sallah.
Zainab tana yi mata kitson gefe Radhiya ce da Ibrahim an baza musu tarkacen wasa
suna ta ihunsu irin na yara da duniya ta yiwa dadi.
"Ke yaushe zaki yi kitson ne?" Mairama ta tambayi Zainab
"Ai kallonki nake duk sati kitso, ni nan ina jiran muji kishin kishin din zasu dawo
ne naje ayi min famin (perming ko saka relaxer). Ya tafi ya barni da kitson ya dawo
ya tarar dashi. Hum'uhm"
Dariya Mairama tayi "nima da kika ga na nacewa kitson bana son haihuwa da kai a
tsefe ne. Lokacin wannan yarinyar kan na kusa cizgewa don azaba"
Tafawa suka yi suna kyakyata dariya kowacce tana tuna nakuda da haihuwarta.
"Kin gansu tafiya daga wata uku an shiga na biyar ga ki haihuwa ko yau ko gobe"
cewar Zainab da 'yar damuwa a fuskarta.
Wannan dadewar tasu ta dami matansu sosai. Kowacce dai tana kokarin daurewa ne don
kada su rinka tadawa juna hankali. Amma a zahiri babu wadda bata kukan dare idan
kewar mijinta da rashin sanin halin da suke ciki ya dameta.
Radhiya baki ya bude ba laifi don akwai surutu. Zaman da take yi dasu Zahra shi
yake kara bude bakin. Ta dai fi likewa Awwab saboda yawo. Sai ya dauketa suyi ta
karade barikin nan.
Yanzu ma 'yan takalmanta masu madauri aka sanya mata bayan an gama kitson tasa kuka
ganin sun doshi gida "Ummi, Amma wawo" nufinta a kaita wurin Hamma su tafi yawo.
"Hajiyar