Showing 27001 words to 30000 words out of 295847 words

Chapter 10 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

gantali ni dai na gaji. Kiyi fatan daga islamiyya ya biyo sai ya kaiki
wurin Mami"


Tana jin sunan Mami kuma kukan ya karkata tana kiranta. Tana ta bata baki yarinya
taki shiru. Ba yadda ta iya dole ta kaita gidan. Mami tana cewa ta zauna tace gida
zata tafi jikinta babu dadi. Radhiya harda yi mata bye bye tace idan Awwab ya dawo
yazo ya karbar mata kaya don tasan yau ma ita kadai zata kwana Mami bazata bari a
dawo da Radhiya ba.


Cikin dare bacci ya gagareta kamar yadda take ta fama 'yan kwanakin nan. Kullum
cikin mafarkin Zayyan take, watarana ta tashi da kuka wani lokacin kuma idan
mafarkin yayi dadi ta tashi da farinciki. Sai dai a can kasan zuciyarta tana fama
da wani irin firgici wanda ta kasa gane dalilinsa.


Envelop din da ya bar mata ranar tafiyarsa ta dauko ta shafa amma har yau taki
budewa. Tsoron me ya rubuta take yi, karshe ma dai ta fadawa kanta idan ya dawo ya
karanta mata da kansa.


Haka ta cinye daren a tunani baccin da kyar ya dauketa. Bayan tayi asuba ma komawa
tayi abinta ta kwanta. Wurin tara na safe ta ji bugu kamar za'a balle mata kofa.
Haka ta taso da hijab a baibai saboda sauri ta bude tayi karo da Christie. Itama
makociyarsu ce tare da mijinta akayi tafiyar.


"Mama Radhiya e bi like say your sister don die ooo. She just knack her head for
ground after one officer wey I no know come give her letter"


Cikinta ne ya murde da tsoro ta bi bayan Christie da gidanta yake kallon na Zainab.
Mata ta ga sun zagaye Zainab ga Ibrahim yana ta tsala ihu. Ashe a kansa ma ta fada
bayan ta karanta takardar Allah Yasa akwai mata a wajen suka dauke shi.


Da kyar Mairama ta durkusa a gabanta tana rike mata hannu "Zainab menene?"


Takardar ta iya mika mata kawai. Mairama tana karantawa itan ma sai kuka da
tausayin Hadir. Christie ta cewa ta shiga da Zainab gida tana zuwa. Hankali a tashe
tana baza sauri ta tafi gidan Mami don ta fada mata. A can ta tarar da wani
mummunan tashin hankalin.


Mami ke kuka sosai tana ta hada kaya ta jibge akwatuna biyu a falon tana ta watsa
kayanta da na su Fauziyya a ciki.


Gabadaya yaran suna gefe kowa yayi tsit harda Radhiya da ta ga babu mai kula ta.
Awwab bai san me ya faru ba amma ganin mahaifiyarsa na hawaye shima yake tayata.


Mami na ganin Mairama taje ta rungumeta ta sake fashewa da kuka "Ummin Awwab na
shiga uku, ina zan sanya kaina"


Duk ta gama tsorata ta daure tace "addu'a zakiyi Mami ba kuka ba, komai yayi zafi
maganinsa Allah. Me ya faru?"


"Daddy ne..." sai ta mika mata takardar ta karanta da kanta.


Hawaye ne ya cigaba da zuba a fuskokinsu Mami tace "Katsina zan tafi yanzu. Sai
naje na ajiye yaran in sanar dasu sai mu wuce Legas din"


Suna haka Zainab ta shigo ta goya Ibrahim da har yanzu yake kukan faduwarsu ta dazu
tana jijjiga goyon tana kuka. Mairama ce tayi mata bayanin me ya sami Major kuma.
Su uku suka hada kai suna ta kuka abin tausayi.


Kusan a tare Mami da Zainab su ka fuskanci Mairama "Zayyan fa?"


Dammm taji gabanta ya yanke ya fadi ta juya a guje ga nauyin ciki ga kafarta da
take yawan rikewa ta nufi gidanta. Tsoronta daya kada itama anzo sanar da ita halin
da Zayyan yake ciki ba'a sameta ba. Bata tarar da kowa ba ta tsaya tana ta haki
tana jin kamar za ta amayar da abinda yake cikinta a lokacin. Da jan kafa ta koma
gidan Mami sun gama shiri ita da yaran.


"Zainab, Mairama...Allah kadai yasan ranar sake haduwarmu. Komai nawa ya danganta
da samun saukin Daddy"


"Babu komai, Allah Ya basu lafiya baki daya."
"Amin" suka amsa sannan Zainab ta kara da cewa itama zata je ta sanar da nata
iyayen ne domin a aika Kano gidansu Hadir. Sannan a san yadda za'ayi a dawo dashi
gida.


Ji suke kamar daga ranar sun rabu kenan suka yi ta kuka sosai. Radhiya da kyar aka
rabata da Awwab ta makale masa wuya tana ta ihun Amma.


***********


Gidan iyayenta Zainab ta wuce cikin kasa da awa guda ta isa. Bayan ta yiwa
mahafinta bayani a take ya taso babban wan ta ya bashi kudin mota yace ya wuce Kano
gidansu Hadir ya sanar dasu.


Zainab na kuka tace masa su yaushe zasu tafi Lagos din.


"Zainab kinfi kowa sanin halin da nake ciki. Kudin da na bawa yayanki wallahi harda
na cefanmu na yau da gobe ne. Kasuwar babu kudi yanzu sai nayi huluna biyar ba'a
sayi ko daya ba"


Shiru tayi wani hawayen yana sauko mata. Ita ta sani kuma bata boyewa iyayenta
talakawa ne fitik. A Kano ma iyayen Hadir ba wasu masu karfi bane. Sai dai sun fi
nata sosai. Albashin Hadir shine yake turawa gida kuma a haka yake yiwa iyayenta
ihsani lokaci zuwa lokaci. Zuciyarta ta gama tsinkewa da wannan bakon lamari a gefe
guda kukan Ibrahim yaki tsagaitawa.


Mahaifiyarta ta karbe shi tana ta juya shi da shafa jikinsa ashe ya sami gocewar
kashi ne a hannu sakamakon faduwar da Zainab tayi a kansa. Babanta ya karbe shi ya
tabbatar hakan ne yace ta tashi su tafi gidan dori.


"Wayyo Allahna Baba. Da me zanji?" Ta kara rushewa da kuka.


"Zainab kamar baki da ilimin Tauhidi? Ki fawwalawa Allah ki yawaita addu'a. Daga
gidan dorin zan wuce wurin kawunki ko Allah zai sa yana da abinda zai ranta min ko
ni kadai ne sai na wuce Ikkon. Kinsan babu yadda za'ayi na barki kije ke kadai baki
san ko ina ba ga yaro babu lafiya"


Kai ta gyada kawai suka tafi gidan dorin aka gyara masa hannun. Ibrahim ya zama
abin tausayi don ya jigata ba kadan ba. Suna dawowa sai zazzabi da amai ya sarke
shi ko hannu baya iya motsawa da kyau. Zainab tayi kuka har taji babu dadi.A rana
daya rayuwar wannan baiwar Allah ta juye gabadaya. Miji yana asibiti a wata uwa
duniya, amma babu kudin zuwa gareshi. Babanta yace su jira yayanta da yaje Kano ya
dawo. Idan iyayensa sun dauko shi sai ta tafi can ko da yaya zai samu ya biya mata
kudin mota. Yini kuka, kwana kuka haka ranar ta kasance mata.


***********
Gidansu Mami unguwa daya ne da na su Major Mustapha. Iyayensu maza su biyar ne a
gidansu. Baban Major ne na biyu nata kuma auta. Da suka tashi aure sai suka zauna a
gidajen da katanga kadai ke raba su.


Daga tasha bus ta hau zuwa unguwar tasu. Tana shiga layin ta hango babban wan
iyayen nasu da suke kira Alh Baba. Yayi shigar mutumci da babbar riga da farin
rawaninsa irin na malamai. Motarsa kirar Pigeout (pijo) zai shiga daya daga cikin
yaransa zai kaishi unguwa ya hangota. Dakatawa yayi don ya tabbatar da wace ce
saboda ita da Usainarta sai kayi musu farin sani kake iya tantance su.


Tana matsowa ya saki murmushi saboda daga yaranta ya ganeta masu kama da mahaifinsu
"Mutanen Shehu saukar kenan?"


Daga ita har yaran sun durkusa da niyar gaishe shi kawai ta fashe da kuka. Yaran ya
kalla yasan duk yadda akayi wani abu ya faru "Kai Muhammadu wuce ciki da kannenka"
ya fadawa Awwab.

"Ke kuma muje" ya nuna mata hanyar gidansu Major.


Awwab kamar ya bita ganin tun a gida suke ta kuka amma tarbiyarsu tasa ya bi
umarnin kakan nasu. Ciki suka shiga matan gidan suna ta murna ana tambayarsu
mamansu suka ce tana wurin Alh Baba.


Basu sami baban Major ba sai Iya mahaifiyarsa. Alh Baba ya tura aka kira ragowar
kannensa sannan suka bukaci jin dalilin zuwanta tana kuka. Duk sun sani cewa ya
tafi Liberia tunda yazo yayi musu sallama. Tana kuka ta sanar dasu abinda takardar
da aka bata ta kunsa. Gidan sai kuka tamkar ance ya riga ya rasu.


Bayan dawowar mahaifin Major iyayen su kayi zaman shawara. An daidaita magana akan
cewa Alh Karami baban Mami da kuma yayan Major Mustapha da suke uwa daya uwa daya
su ne zasu tafi.


Mami ta kasa daurewa tana kuka, Alh Baba ya dubeta "kiyi hakuri Hassana. Su dinmu
dauko shi zasuyi a dawo dashi gida yayi jinyar a kusa. Legas tayi mana nisa. Idan
munje da yawa bamu san ina zamu kwana ba"


Ba haka taso ba ko kadan amma bata da yadda zata yi. Tana ji tana gani asubar fari
suka kama hanya a motar Alh Baba.


**********


Kwanaki biyar kenan da samun sakon da ya tada hankula a Giginya army barrack.
Mairama ta rame sosai a 'yan kwanakin. Radhiya ma bata samun kulawa yadda ya kamata
saboda tun ranar da suka tafi fargaba tasa ta fara nakuda a tsattsaye tana daurewa.


Rayuwa take yi mara dadi. Babu miji kuma babu wadanda suka zame mata tamkar 'yan
uwa na jini. Tarin fargaba ne ya cika zuciyarta da kokonto. Ta damu tasan halin da
su Hadir suke ciki ga kuma rashin sanin komai game da Zayyan ya sanya take jin
kamar zata yi hauka.


A kwana na shida ciwo yaci karfinta ta daure taje ta buga kofar gidan Christie. Ita
dinma duk zulumi da fargaba sun cinyeta tana ta ramewa. Tana ganin Mairama a haka
tasan nakuda ce. Gida ta koma ta dauko zani ta saba Radhiya a baya sannan ta
taimaka mata suka tafi asibitin sojojin inda take awo.


Ta kwashe kusan awa shida tana fama banda wanda tayi a cikin gidanta kafin Allah
Yasa ta sauka lafiya ta haifi danta tamkar Zayyan yayi khaki don yafi Radhiya kama
dashi sosai.


Likitocin sun bata kulawa yadda ya dace sannan aka kaita dakin da zata huta saboda
wahalar da tasha. Christie tace mata zata je gida tayi girki ta kawo mata don taji
kwari. Matar akwai kirki sosai ita ma. Radhiya ta sake dauka dama da tana ciki
wurin haihuwa ta siyo mata fanke a 'yar kasuwar gefen asibitin taci ta koshi ta
debo ruwa a famfon waje ta bata.


Suna fita ta sake daukan jaririn sai kawai tasa kuka. Yaron da tayi fatan zuwansa
duniya mahaifinsa ya karbeshi yayi masa addu'a. Sai gashi ta haihu din a lokacin da
bata da masaniyar halin da yake ciki. Karin kukanta yau ta haihu babu kowa nata sai
Christie da ta tsaya mata tamkar 'yar uwa. Mami da Zainab suna can lalurar
mazajensu ta saka su a gaba. Yanzu ita wa take dashi da zata tura a sanar da
gidansu da gidan iyayen Zayyan. Tun tafiyarsa babu wanda ya tako ganinta cikin 'yan
uwansa ko da wasa. Me ya ja mata nesanta da 'yan uwanta da na mijinta da rashin
zama cikin mutanen da tasan sunyi tarayya a yare, addini da al'ada? Auren Soja ta
bawa kanta amsa. Sojan ma Zayyan wanda idan za'a sake bata zabi tayi rantsuwa har
ranta shi din a sojansa zata sake aure. Tana sonsa kuma tana alfahari da aikinsa
kamar yadda yake yi shima.


Tunani ta zurfafa tana yi akan rashin sanin yaya zata yi labarin haihuwarta ya iske
danginsu. Lokacin Radhiya shi yayi komai abinsa. Yanzu kuwa komai ya dawo gareta.


Kan jaririn ta shafa tana hawaye "Daadaa yaci burin ganin zuwanka duniya ko suna
bai yarda mun zaba ba saboda yace yana son yayi yiwa jaririnsa huduba da kansa"


Yaro yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ta kwantar dashi a gefenta daga jikin
bango tana shafa shi a hankali.


"Sojana ka bar min amana mai nauyi. Baka fada min yaya zanyi ba idan baka dawo da
wuri ba"


Kuka ta shiga rerawa a hankali tana jin wani matsanancin ciwon kai. Kwanciya ta
gyara a gefen dan ta lumshe idanunta ta baiwa kofa baya.


Tana ji likitoci biyu suka shigo dukkansu sojoji da nos guda daya. Wanda ya karbi
haihuwarta ya yiwa dayan bayanin cewa ta zubar da jini kuma jininta ya hau kada a
sallameta sai gobe.
"Na fahimta Dr. Ina file din nata?" Ya tambayi Nos ta mika masa.


Zaro idanu yayi ya dago yana kallon wancan likitan.


"Matar Lt. Zayyan Tureta ce? Sune last week akace gabadaya unit dinsu...."


Wanda ya karbi haihuwar yayi saurin sa hannu akan lebensa yana magana a hankali
harda juya harshe zuwa turanci a zatonsu bacci take, kuma kana yi mata kallo daya
ka ga bafillatana wadda ake musu kallon basu da wani ilimin boko sai kiwon shanu.


"Shhh I don't think they know what has happened"


Mairama taji gabanta ya fadi wani abu yana mata yawo a jiki tun daga kai har tafin
kafa, sai ta daure ko motsi bata yi ba. Nos din ta kalli bayanta da tausayawa a
hankali tace.


"I pity their wives"


Basu san daga ina ba sai ganin Mairama suka yi rike da kafadun Nos din idanunta a
rufe cikin karaji take tambayarta "what happened to my husband?"


Kallon kallo suke yi sai taji gabadaya duniyar tana son kife mata. Durkushewa tayi
gwiwoyi a kasa tana kallonsu tamkar wadda ta sami tabin kwakwalwa.


"Don Allah don Annabi ku fada min gaskiya"


Tashinta yazo musu a bazata haka fahimtar turancinta shiyasa suka kasa bata amsa
kai tsaye. Shirunsu kadai ya isheta amsar da take nema da yanayin da taga sun shiga
na tausayinta da tsoron fada mata gaskiya.


"Kinga ki kwantar da hankalinki idan kinji sauki za'a fada miki komai"


Murmushi tayi mai sauti tana ja da baya da baya har ta kai jikin bango ga hawaye
tana zubarwa kamar ruwan famfo "da hankalina fa, nasan abinda nake tunani hakane.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah....ahhhh. ....kirjina..wayyo Allah..
Ka jikanka Sojana"


Likitan da yazo zai canji wancan aiki ya dan matso kadan "kizo ki zauna...uhmm"


Nos tace "Mairama"


"Ok Mairama ki zauna muyi magana kinji"
Jaririnta kawai ta dauka ta saka shi a kafada tana cigaba da kukanta tana cewa "tun
yaushe ya rasu?"


Basu iya cewa komai ba tayi hanyar kofa suna kiranta taki tsayawa. Sai dai kafin ta
fita jikinta ya soma rawa likitan da yafi kusa da ita yayi saurin karbe jaririn ta
fara neman faduwa tana wata irin jijjiga ga jini ya balle mata.


Nos da daya likitan ne suka kamata aka dora akan gado suna neman ceto rayuwarta.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 14. Kwana biyu da rabin wuni Mairama tayi kafin ta gane
inda take da babbar jarabawar da ta tunkaro rayuwarta. Ta farfado da misalin uku na
rana washegarin ranar da ta haihu. Idanunta a rufe suke amma tana iya jiyo
maganganu kamar ana fada. A hankali ta fara fuskantar me ake cewa wanda yayi
sanadin fitowar hawaye daga idanunta, kuma har lokacin a rufe suke.


"Ni dai na fada miki gobe zan tura Rayyanu yaje garinsu ya sanar da iyayenta su zo
su dauketa don bazan iya jigila ba."


"Haba Maikudi kai kuwa baka ganin ga danyen jego ga rashin lafiya. A barta ta huta
mana"


Gwaggo Ladi da tayi maganar ya kalla darajar mijinta Mal Aminu ya kasa bata amsar
da yayi niyya. Wani dan tunani yayi ya kara tabbatarwa gara yabi komai a hankali
don samun biyan bukata.


"To naji sai ta zauna har sai ta gama takaba an raba gado. Ince ko hakan yayi" ya
mayar da kallonsa ga Mal.Aminu da ya dauke kansa saboda takaicin halin Maikudi.
Yaron ya fita zakka tamkar ba jinin Mal Muhammadu ba.


Mal Aminu da ya gama tofe jariri da addu'a ya dago kansa "bana son hauka Maikudi.
Takaba dai tana haihuwa ta fita. Sannan tun muna shaida juna kada inji kada in
gani, kaf abinda Zayyanu ya bari na matarsa ne da 'ya'yansa tunda yana da da
namiji."


A fusace ya juyo "inji uban wa?"


"Inji ubanka"


Mamaki kamar ya kashe shi saboda Jume ce ta bashi wannan amsar. Akan tabarma take
tana bawa Radhiya abinci. Daga jiya zuwa yau tayi wuri-wuri da ita. Rasuwar Zayyan
ta tabata fiye da zato da tsammaninta. Duk wata mugunta da ta taba yiwa
mahaifiyarsa dashi kansa sune suka yi mata dabaibayi. Cikinsu babu wanda ya taba
nufinta da sharri gashi sun bar mata duniyar tayi yadda take so. Nadama ce ta gaske
take nukurkusar zuciyarta. Ga Maikudu don abin kunya daga jiya zuwa yau banda
rashin mutumci babu abinda yake zubawa a dakin. Daure fuska ta sake yi


"Saboda baka san me kake yi ba ace kaninka ya rasu amma ko a jikinka?"
"Kina ji fa aka ce yayi wata guda harda dorin kwanaki, duk dacin mutuwa ai yaci ace
tayi sauki an fara fuskantar gaba"


Mairamu ta kasa boye kukan zucin ta koma yi a fili. Ashe har yafi wata da rasuwa
bata da masaniya. Shine take ci tasha har tayi wasa da dariya? Ashe Sojanta ya koma
ga Allah take ta tunanin dawowarsa. Yanzu shikenan nata mijin saboda soja ne ko
kabarinsa babu wani danginsa da zai sani? Anyi masa wankan gawa? An sallace shi?
Wace irin mutuwa yayi duk basu sani ba.


Kukanta ya tsananta Gwaggo Ladi ta tashi ta matsa kusa da ita ta tsaya a gefen
gadon.


"Mairama hakuri zakiyi da yawaita yi masa addu'a"


Rarrashinta suke ta yi ita da Jume sannan Mal Aminu ya fita saboda ance ta shayar
da jaririn.


Maikudi yayi qiqam kamar sanda sai da Jume tace ya fita, yayi waje yana surutai.


Yaron ta karba wanda rabonta dashi tun jiya. Yaji yunwa kuwa sai ruwa aka rinka
bashi da tana kwance.


Gwaggo Ladi tace Malam yayi masa huduba da Muhammad Zayyan. Ina fata hakan yayi
miki"


Hawayen Mairama har fuskar jaririn tayi murmushi "Sojana Allah Ya raya min kai."


**********


"Wai Zayyanu dai Zayyanu soja mijin 'yata Mairama kake nufi?" Malamijo yayi maganar
kamar zaiyi kuka.


"Shi nake nufi. Allah Yayi masa rasuwa a kasar da suka je" Rayyanu ya bashi amsa.
Shi da Badaru da 'yan uwansu mata kaf mutuwar Zayyan ta shigesu sosai. Mutum mai
barkwanci da saurin manta bacin rai. Duk yadda su ke bata masa bai hana shi
kyakyawan zumunci dasu ba ko da su bazasu yi masa kallon arziki ba.


Malamijo ya daga hannu ya dora a ka "Laaaaahhhh ha'ila ha ilallahu, kaico Mairama,
'yar marainiyata ta rasa miji kuma"


Lokaci kankani a tsakani zance ya bazu ko ina mijin Mairama ya rasu a filin daga.
Mutane suka fara zuwa yiwa Malamiji ta'aziyya yana cewa nan da kwana biyu zai wuce
Sakkwato.


A cikin gidan ma jikinsu duk yayi sanyi. Ba wani haduwa suke yi sosai ba saboda
nisan garuruwansu amma duk da haka a iya lokutan da su ka ganshi anyi masa shaidar
arziki. Malamijo yasa a dafa abincin sadaka ya saki bakin aljihu abinda basu saba
gani ba. Cikin yaransa maza ya tura babban mai bin Mairama a shekaru yaje Balan ya
sanar da Nene Marka. Idan zata bisu ta'aziyya ta taho washegari su wuce jibi.
Sannan ya tura mai bi masa Kano gidan Salame.


Suna zaune shi da 'yan gaisuwa wani yake tambayar yaya Zayyan din ya rasu don shi
ma akwai dan uwansa soja a kudu, yana tsoron a tura shi yaki. Malamijo bai tashi
bada amsa ba sai da yaga Rayyanu ya tashi zai zaga ya soma jawabi.


"Hmm ai ba'a cewa komai Haladu. Yaron nan harbi, harbi dai da kake ji da gani a
finafinan su Amita Bachan sai da aka sakar masa harsashi kusan goma amma a haka ya
rinka kutsa kai cikin abokan gaba yana gamawa dasu. Bawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login