Showing 276001 words to 279000 words out of 295847 words

Chapter 93 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

Labulayen dakin kansu abin kallo
ne. Toilet din a cikin daki yake an chanza tiles, tray din wanda, toilet seat da
sink gabadaya an zuba sababbi. Kayan cikinsa ma sun hadu kamar ba toilet ba anyi
masa kyale kyalen zamani.


Falon bai kai girman dakin ba shi kuma royal chairs ne aka saka 3 sitter da one
sitter guda biyu saboda wurin kada ya cushe. Ga katuwar wall tv da duk aka hada
kayan kallo akan wani kayataccen tv stand. Centre table dinta da kananunsa na gefen
kujeru duka masu kyau sai wani chest of drawer a karshen falon an jera plates da
tarkacen kayan kitchen. Ana shigowa falon kofar dakin ce a farko daga dama sai
kofar kitchen tana kallonsa daga hagu. Idan ka shiga kamar kada ka fita, gashi dai
karami amma komai cikin girma da wadata akayi shi.


Zaman aikin karasa duk wani gyara da yayi saura su kayi. Emzee da Ibrahim ne a
kitchen suka hada gas cooker da su fridge. Kafin isha bangaren amarya ya fito fes
sai wani uban kamshi har bangaren Mami ana ji. Su Hajjo sunyi mamaki sosai ganin
Mairama bata yi musu zancen akwai wani gidan a Katsina ba. Ba tayi kasa a gwiwa ba
wurin nemanta inda ta ce musu bata da labari ko kadan itama. Zayyan ta fadawa yace
shima bai sani ba. Sun tabbatar aikin su Mama ne wannan ta kirata kuwa ta ma kasa
godiyar sai kuka tana cewa "Zainab Allah kada Ya taba bawa shaidan dama a kanmu.
Kada Allah Ya bani ikon zama butulu a tsakaninki da Mami"


"Amin amma ki bar magana irin haka kada kisani kuka zan kira anjima" katse wayar
tayi ta share kwalla. Me zasu cewa iyalin Zayyan. Gidansa da ya gida da guminsa da
gadon mahaifiyarsa dungurugum ya baiwa DK kuma ya sayawa Ibrahim mota. Da shi da
Daddy basu taba nuna wata alama da Hadir zai ji cewa bai kaisu arziki ba. Sun dauki
kawunansu abu guda basa hangen komai sai soyayyar da suke yiwa juna.


Bayan sun koma ciki ne take fadawa Mami gobe ana gama budar kan bayan magariba sai
a kai Radhiya.


Mami ta girgiza kai "a'a fa Zainab abinda biki bai kare ba, ko me za'ayi sai mun
gama da Nijar dinnan kowa ya huta lokaci guda"


Mama ta kankance ido don bata da niyar chanza shawara "Mami kuji tsoron Allah, aure
kwana nawa ana jawa yarona rai. Yo banda ma dai shi Awwab din anyi mai hakuri da
tuni ba sai dai labari ya sha bamban ba. Kullum saka ido nake in ga tafiyar Radhiya
ta sauya....."


Da sauri Mami ta mike "ba dai tariya kike so gobe ba? To a kaita dakinta gobe ba
sai kin fara barambarama ba"


Shu'umar dariya Mama tayi "haka kawai don dai daga shi har ita ba wayis bane ta
wannan fanin ga gabontar 'ya'yan fari da duk mun kwashi kunyarmu a hannu tun a
Abuja"


Yousuf tun daga wurin dinner ya zarce da Arifah Nicon ya karbe wayarta sai gobe
zasu tafi Nijar. Mom dinta tayi ta korafi Excellency kuwa yace yaro yayi masa
daidai. Su basu yi lissafin halin da yaran zasu shiga ba kawai sunyi tsari yadda
yayi musu.


Gidan tun safe aka tashi da aikace aikace saboda walima ce babba Mami ta shirya a
farfajiyar gidan. 'Yan uwa na nesa da kusa sun taru. Daga shabiyu zuwa la'asar anyi
kade-kade da raye-raye Rahima tun tana jin kunya da komawa baya har ta ware saboda
Zayyana bata san bakunta ba. Duka kayan da Radhiya ke sakawa Mami ce ta tanada.
Bayan la'asar atampa aka bata ta saka super exclusive dinkin sosai yayi mata kyau
aka dora mata wata bakar alkyabba tasha ado sai sheki da daukar ido. Wurin zamanta
daban an kawata shi ga kujeru a jere aka kira wata babbar malama tazo yin bayanai
da nasiha game da zaman aure da hanyoyin samun kyakkyawan zama da miji. Radhiya
jikin gabadaya yayi sanyi hawaye kawai take zubarwa don kalaman matar akwai shiga
rai da tsoratarwa. Sai da magariba ta gabato sannan taron ya watse bayan addu'o'i
daga bakin malamar.


Ciki aka koma ana alwala da sallah. Radhiya ta fito daga toilet kenan Mama ta shiga
dakin ta kirata. Dakin Mami ta kaita babu kowa a ciki ta bata wani abu a cikin kofi
mai zaki da wani dandano da bata gane ba.


"Maza shanye kuma kada a sake baki wani abu ki sha kada kizo cikinki yayi ciwo sun
isa haka. Sannan ki zama cikin shiri idan anyi sallah zamu kaiki kyayi wanka a can
don nan ko ina a cike yake"


"Ina?" Tace a firgice murya na rawa.


"Bangarenku mana"


Wani abu taji ya tsirga mata a ciki ta daure tace "Mama wane bangaren kuma?"


Daure fuska tayi ganin Radhiya ta firgice lokaci guda kafin ta tara mata mutane
"ina kinsan cewa akwai dakin Awwab a gidannan"


Idanu cike taf da hawaye tace "eh"


"To nan aka gyara miki idan kunzo kinga babu ruwanku da takurawa Mami kuna da komai
a can" cewar Mama tausayin Radhiyan ya soma kama ta.


"Amma ba. Ance. Ance sai mun dawo daga Nijar ko Mama?" Tace da sigar roko.


Kafadarta Mama ta dafa tace "Radhiya, aure kika yi ba kwana kika zo yi gidan Mami
ba kema yanzu nan gidanki ne. Ina so ki cire tsoro kamar yadda kika ji nasihar
malamar nan dazu kada ki bani kunya kinji ko 'yar albarka. Jeki kiyi sallar zan zo
mu tafi, kuma banda kuka ki tabbatar kin daure takalminki da kyau dai.." ta kare da
zolayarta.


Kasa daurewa tayi tana sallah tana hawaye. Yanzu shikenan sai kowa ya kwana a cikin
gidan ita kuma a kaita dakin Hamma Awwab? Da an fada mata da wuri da ta shirya
zuciyarta amma wannan bazatan ya shammaceta da yawa.


Sukuku haka tayi sallah ta idar harda su sharar hawaye. Kukanta yasa Rahima rasa
walwala tazo ta rungumeta itama tana yi batare da taji dalilinsa ba. Zahra da
Fauziyya ne suka shigo Zayyana ta kira su akan kukan su Radhiyan.


Zahra tace "amaryar Hamma me ya faru?"


Kara sautin kukan tayi "wai kaini za'ayi"


Da ido Fauziyya ta yiwa Zayyana da Rahima alamun su fita sannan ta kwashe da dariya
"wai, wai, wai....kice yau za'a kwana ana goge janbaki. Gara kisa 24hours shine
baya fita da wuri"


Zahra ma dai dariyar tayi Radhiya na kuka tace "sai na fadawa Hamma"


"Tuba nake anti amarya. Tashi muje in baki karatu kinji kanwata yayata"


A dakin Mami kuma Mama ta kira Awwab tace masa shima ya taho da shiri yanzu za'a
kai amarya jiya sha'afa tayi bata fada masa ba.


"Ina za'a kuma kaita Mama?"


"Bangarenku mana mun karasa jeren tun jiya"


Wata irin murna ta kama shi yace "Allah Mama?"


Sai da tayi dariya tace "idan ma kayi nisa ni dai yanzu zan rakata kasanta da son
shiga jama'a kada taji ka shiru ta dawo cikinmu"


Takalmansa yake sakawa lokacin a gefen gidan Baban Biyu inda sukayi sallar magariba
yace mata "gani nan Mama....Mama nagode sosai" ya cigaba da zuba mata godiya sannan
ya ajiye wayar ya taso Bilal ya fada masa a ina zai siyo abubuwan da ango ke shiga
gida dasu.

**********


Tsokanar Radhiya Fauziyya take tun tana kuka ta dena wani abun ma sai sunyi dariya
ita da Zahra. Sallamar Mama taji wadda ta tsinke mata zuciya ta tashi da sauri.


"Taso mu tafi"


"Wayyo Mama banyi sallama dasu Adda Zahra ba" tace a rikice.


Mami taji wani irin tausayinta domin tana kusa da Maman. Duk bakin Radhiya da
dakewar zuciya yau babu.
Mama ta rungume hannu a kirgi "to ina nan yi musu sallamar"


Rungumesu ta shiga yi sai ta basu tausayi bare ma Fauziyya kukan take tayata.


Hannunta Mama ta janyo "muje kinji gobe da safe zan turo miki su ayi ta rungume-
rungumen"


Mayafi kawai ta yafa ta saka wasu flat shoes masu dan uban kyau suka fito. Wata
kanwar Ummi ce ta dauko akwatinta wanda bata san da zamansa ba duk cikin aikin Mami
ne wannan kayan da ta dinka mata kala goma. Kayan kwalliya da underware daga cikin
wanda ta taho dasu ne aka dibar mata aka zuba.


Suna fitowa bakin kofa Emzee na danno kai zai shigo. Ai yana ganin tana kuka ya
fara tambaya hankali a tashe. Kanwarsu ta bangaren Badaru ce ta fada masa kaita
za'ayi. Ya bata rai kuwa.


"Yanzu Mama ana kai kowa a mota amma Adda a kafa"


Hajjo ta kamo kunnensa "To sannu me taya bera bari ina zamu kaita da mota"


"Ni gaskiya ban yarda ba Mama don Allah bari na kaita a mota" yace yana turo musu
baki.


Rahima murmushi kawai tayi ganin halayen Emzee mabambanta. Ta dai tabbatar baya
hada kowa da yayarsa kuma baya boyewa ma.


Iyaye na masa fada ya kama hannunta ya rike "da so nayi na zagaye gidannan sai
biyar dake a mota sannan a kaiki amma tunda sun ki muje na rakaki Addata"


Dariya ya basu ya fuske abinsa wai ai bata da kawaye shine dai babban abokin. Haka
ya shige cikin mata abinsa har falonta aka wuce dakin da ita ana musu fatan
alkhairi. Ko minti shabiyar basuyi ba suka tafi Mama tace mata tayi wanka akwai
kaya a ciki ta nemi wanda bazai takurata ba ta saka.

**********


Tana jiyo hayaniyar mutane sama-sama daga main house din tayi kuri tana tunani wai
yau ita ce a gidan nan a matsayin matar aure-matar Awwab. Ita ma bata da masaniya
akan za'a ware musu wuri a gidan nan shiyasa take ta mamaki. Kanta ta bude ta
karewa dakin kallo a take ya shiga ranta komai ya burgeta matuka. Ta tashi a
hankali ta leka toilet, falo da kitchen zuciyarta fes.


Tunowa tayi da gargadin Mama akan tayi wanka ga turaruka da ta nuna mata na humra a
showglass da kuma wasu a cikin akwatin da aka zuba mata kaya. Mikewa tayi ta cire
kaya tayi sa'a akwai tawul biyu a bandakin kuma akwai heater ta bango a kunne.
Wanka tayi kafin ta gama taji ana kiran isha ta dauro alwala ta fito.
Jakar kayan kwalliyarta ta dauko ta jeresu akan dressing mirror sannan ta shafa
mai. Gaban showglass din taje ta bude ta shafa humrar masu daddadan kamshi tazo ta
shiga fesa body spray. Gashi dama jikinta yasha dukhani dama cikin kamshin take.
Tana durkushe gaban akwatin neman kayan sawa daga ita sai tawul taji an murda kofar
dakin za'a shigo. Gabanta ya fadi da sauri taje ta danne kofar tana cewa waye cikin
rawar murya.


Murmushi Awwab yayi saboda a haka ma ya iya gano hakikanin firgici da tsoro a
muryarta.


"Schatzi masallaci zanje, na ajiye aby a falo ne kada ki gani ya baki tsoro baki
san wanda ya kawo ba"


"To"


"Ba zaki bude naga fuskarki ba kafin na tafi?"


Shiru tayi tana kallon kanta yaushe ma zata yarda ta bude.


"Sai na dawo matsoraciya"


A hankali yaji tace "adawo lafiya"


Kasa kunne tayo taji karar rufe kofar gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya. A
gurguje ta janyo wasu riga da skirt na wani yadi mai laushi ta gyara fuskarta da
kwalliya madaidaiciya ta kuma fesa turare sannan ta saka wani zumbulelen hijab mai
hannu har kasa shima ta bishi da turaren. Sallar isha tayi ta hada da shafa'i da
wutiri. Bayan ta idar ta zauna addu'a akan sabuwar rayuwarta kafin ta shafa ta ake
jin alamun an shigo sai dai yanzu kai tsaye ya bude kofar dakin ya tsaya yana
kallonta a zaune kan abin sallah.


Shafawa tayi ba don ta gama ba sai dai kawai kallon da yake mata yayi yawa kuma
yaki magana. Yana ganin tayi yunkurin tashi yace ta zauna. Abin sallah ya dauko a
inda ta dauki wanda take kai ya shimfida a gabanta. Ta san sallar me zasuyi bata
bukatar karin bayani ya ja su suka yi nafilar godiya ga Allah. Addu'a sosai yayi
musu tana cewa amin a hankali ta kasa daga ido ta kalle shi.


Mikewarsa ne ya sanar da ita ya gama zai nade abin sallar ta karba da sauri amma
har yanzu bata kallonsa. Shi burge shi take yi komai nata. Ta bayanta taji ya tsaya
ya zuro hannayensa ya tayata ninke abin sallar. Faduwar gabanta ya sake tsananta
lokacin da ya rungumeta a haka ya dora kansa a kadafarta yana mata magana a kunne.


"Dama kin ajiye wannan shirun bani da niyar chanja abinda nayi niyya yau ko da zip
zaki saka a bakin"


"Hammana me kayi niyya?" tace jiki a mace.
"Good ashe da bakinki...idan na fito daga wanka zan fada miki, abinda na sani dai
shine...." ya juyo da ita suna fuskantar juna tayi saurin runtse idanu. Matso da
fuskarsa yayi saitin ta sosai "muna da alkawarin massage idan kin manta zan tuna
miki"
[11/2, 8:28 AM] 👸🏽MAMIN SADIQ 👸🏽: Bai jira cewarta ba ya saketa ya kama rigarsa zai
cire. Da sauri ta bar dakin ta rufe masa kofa tana haki ita dai yau ta shiga dari.
Awwab kuwa dariya yayi ya wuce yayi wanka shima yayi duk wani abu da ya saba na
shiri bacci.

Tana zaune tsuru kamar wadda ta yiwa sarki karya ya bude kofar dakin ta dago kai da
sauri suka hada ido. Kayan bacci ne a jikinsa na cotton riga mai gajeren hannu da
dogon wando. Wannan kamshin da yake janta gareshi ta soma shaka ta lumshe ido a
hankali. Kusa da ita ya zauna ya bude ledar kazar da take da zafi har yanzu sai
kuma ya mike ya dauko robar maltina daya a fridge ya dawo.

"Cire hijabin kici abinci"

"Ni dashi zan ci"

"To babu laifi shi ma bazai hana ango abinda yayi niyya ba" yace yana kashe mata
ido.

Turo baki tayi cikin shagwaba "ni wallahi tsoro kake bani Hammana. Me kayi niyya"

Mischieviously yayi murmushi "nothing...ahhh bude baki" ya mika mata naman.

Kasa karba tayi ta sunkuyar da kai. Ya kula dai yau da rigima a tare da ita sai ya
dauko remote ya danna tunda an jona komai na tv din ya shiga neman channel din da
zai bari a nilesat. MBC 2 ya kai ana wani film ya tambayeta ko tana son gani tace
eh da sauri.

"Zan barki ki gani amma da sharadin zaki cire wannan hijab din muci naman nan if
not yanzu zamu shige daki..."

Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji numfashinsa ya
tsaya na yan dakiku saboda kyaun da tayi masa. Gashin ta ta kama ya zare ribon din
ya zuba a bayanta da kafadu. Wannan lallen da tayi yasa kan yayi kyau sosai inda
kalar ta fito ya zura yatsunsa a ciki yana rufe idanu.

"I love this Alheran" ya janyota kusa dashi sosai yana yamutsa mata gashin.

A gefen jikinsa ya rabata ya shiga bata naman yana ci shima. A haka suka koshi yace
tayi zamanta ya kwashe komai zuwa kitchen. Sauran ya saka fridge ya wanko hannunsa
ya dawo. Miko mata hannu yayi yana son ya taso ta kyabe fuska "ai ba'a gama film
din ba"

"Brush kawai zamuyi mu dawo"

"To kaje ka fara yi kaine babba"

Dariya ta bashi wai nan wayo zata yi masa ya wuce dakin yayi ya dawo "saura ke"

"Kada ka kashe tv din Hammana yanzu film din ya fara kyau" tace tana tashi bayan
bata fuskantar komai a ciki. Ko wuka za'a saka mata bata san me akeyi ba.

"Zama zanyi na gane miki inda kika tashi" ya zauna ta tafi.
Tana rufe kofa ya kashe tv din da fitila sannan ya shiga daki ya rufe kofa.

Ai tana jin motsin shigowarsa jiki ya soma rawa ta gama brush din ta kasa fitowa.
Sai da tayi minti biyar ta yanke shawarar ce masa ita fa kallo zata yi kawai. Da
kwarin gwiwa ta fito yana waya cikin harshen jamus yaki kallonta. Zaune yake akan
gado ya mike kafafunsa ya jingina da pillow. Kofar dakin taje ta murda taji a rufe.
Ta sami wuri ta tsaya tana jiran ya gama.

Sallamar mutumin yayi ya taso yana tahowa gabanta na kara faduwa. A tsakiyar dakin
ya tsaya ya ware mata hannuwansa yana murmushi tare da yi mata nuni da ka. Babu
yadda ta iya ta saki hannun kofar ta taka da sauri ta fada kan kirjinsa. Sun dauki
kusan minti biyu a haka kowa da nasa tunanin da yake tattare da soyayyar dayan.

Da yatsunsa ya dago kyakyawar fuskarta a tausashe yace "Babyna guduna kike yi
kuma?"

"Film din...." sai kuma tayi murmushi ta kasa karasawa.

"Kema kin san baki da gaskiya gashi kinyi shiru. Muje ni inyi miki tausar tunda kin
kasa cika alkawari"

"Zanyi maka"

"Fara saka kayan bacci"

Akwatin nata ya bude babu ko daya na lefenta kuma suna Sakkwato za'a wuce dasu
Abuja. Wardrobe ya bude inda ya zuba nasa kayan ya dauko mata t-shirt dinsa tana ta
kamshi.

"In saka miki?" Yace yana dariya don yasan bazata yarda ba.

Harararsa tayi "da kayana zan kwanta"

"Schatzi" yace hannuwansa na jindadin yamutsa mata gashi ya rasa dalili ita kuwa da
kyar take iya bude idanu saboda yadda take ji.

"Naam" ta amsa a raunane.

"Saka riga ko Ango yayi abinda yayi niyya"

Sakinta yayi ba don yaso ba tana ture turen baki ya fita daga dakin don ta shirya a
tsanake. Cikin sauri take komai tana yi tana kallon kofa gashi key din ta waje
yake. Rigar ko cinyarta bata gama rufewa ba. Tana fesa turare ya turo kofar jikinta
ya soma rawa shi kuwa Awwab rufe kofar yayi ya jingina da bayanta tare da harde
hannuwansa a kirji yana kallon Alheran a matsayin matarsa abar so da kaunarsa.

Turaren da ta dauka ta ajiye jikinta yayi matukar sanyi tana kallon gadon tana son
zuwa ta kwanta ta rufe jikinta amma bata son yin kwakkwaran motsi a gabansa. Tahowa
yayi gabanta yasa hannu a waist dinta ya matso da ita jikinsa da dayan hannun kuma
turaren da ta ajiye ya dauka ya feshe mata jiki dashi sannan ya saka hannuwansa
duka ta bayanta ya dagota jikinsa ya soma juyi da ita a dakin tuni ta kankame shi
tana dariya.

"Please, please, pleeeeaaass ka ajiyeni" tace tana zagaye hannuwanta a wuyansa.

"Sai na cire miki wannan tsoron da yake hanaki sakewa"

"Zan sake....Chéri na sake ma.....Hammanaa"
Ajiyeta yayi a hankali tana jin kamar har yanzu juyin suke yi ta kankameshi tana
sauke numfashi. Hannuwansa ta sake ji ta bayanta ya tura yatsunsa cikin gashinta da
ya mayar abin wasa yana magana can kasan makoshi "na yafe miki tausar nan fa"

Zare jikinta take neman yi ta kasa saboda rikon da yayi mata a hankali tace
"nagode"

Dago kanta yayi yana bin bakinta da kallo idanu a lumshe "gani nayi ko da tausa ko
babu bazai hanani abinda nayi niyya ba"

Tsoron ya soma dawowa tace "Wai me kayi niyya ne?"

Wani irin kallo mai kashe jiki yake binta dashi yace "Spending the whole night
loving you my baby. Ki taimaka ki bani dama saboda ko kinki bazai hana Awwab abinda
yayi niyya ba, bani da hakuri indai akan sonki ne Alheran" kasa yayi da kansa ya
soma kissing dinta tamkar ranar ya fara samun wannan damar. Radhiya bata iya sake
komai ba sai abinda Awwab ya koya mata. Kamar yadda yace ya nuna mata soyayyar da
bazata taba hadata da komai ba a rayuwarta. Bacci kuwa sai can cikin dare ya
rungumeta tsam a jikinsa ta soma yinsa a wahale tana ajiyar zuciya hawaye har cikin
bacci yana jin digarsu a kirjinsa.

"I am sorry my love" yace yana kara karfin rikon da yayi mata.
"I love

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login