Showing 234001 words to 237000 words out of 295847 words

Chapter 79 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

wai yanzu damarsa ce sun gama nasu bai ce komai ba. Zama Radhiya
tayi ya gyara mata rigarta ya rufe kofar sannan ya ja suka tafi kana leka motar
taurarin soyayya sun mata kawanya.


Wani katafaren events hall suka nufa inda suke iya ganin taron motoci sun cike
wurin parking din ciki an fara layi a gefen titi. Suna shiga Emzee yana fita bayan
ya karbi mukullin motarsu daga hannun Ibrahim da su suka ajiye su Laila da Zayyana.


"Ina kuma zaka je kasan yanzu su Daada zasu iso a fara"


"Yanzu zan dawo Rahima zan dauko please kace bazan dade ba idan an nemeni"


"Emzee kodai-kodai?" Ibrahim yace yana daga gira.
Cike da shauki Emzee yace "fadi ka kara bros yarinyar nan ta cuceni...ko shiryawa
banyi ba kawai na nemi zuciyata na rasa ashe ita ta dauka. Da tayi warning dina
kasan kai zan fara sanarwa"


Duka Ibrahim ya kai masa a baya yana kyakyata dariya "shege malamin soyayya ya fada
ruwa....tabdi amma har ta bani tausayi ta kwaso Emzee chewing gum"


"Me ka mayar dani?"


"Irin mazan da idan suna son mace zasu iya sadaukar da komai nasu domin kyautata
mata mana"


"To kai din ba shi bane?"


Bangaren da Zayyana take Ibrahim ya kallo "I can die for her man"


"I feel you bros nima haka nake ji. Ina bukatar time da ita ne domin in san ko
wacece. Na dai fi tunanin tana da alaka da gidansu Halifa maybe cousin dinsu ce
tunda ina ganinta da Hibbah."


Gaban Ibrahim ne ya fadi ya soma tunanin yaya akayi Emzee bai san wace Rahima ba.
Tunawa yayi da yadda ya tsani Gwaggo Salame yaji jikinsa yayi sanyi. Bai taba ganin
Emzee so cheerful ba irin yanzu, gaskiya bazai iya rushe masa wannan sabon
farincikin ba. Zai bari ya gano da kansa kila sanadiyar shiryawar iyayensu kenan.


"Na tafi" yaji Emzee yace.


A gurguje ya tada motar ya koma gida. Minti goma ya kaishi saboda babu nisa da
gidansu. Sai yanzu ya tuna bashi da nambar wayarta to ta yaya zai kirata. Idan kuma
ta tafi wurin bata jira shi ba fa. Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan sai ga
mai aikinsu 'yar budurwar ta fito itama a shirye fes da ita.


"Yauwa don Allah kirawo min Rahima a dakin Adda Radhiya."


"Kowa ya tafi fa muma Ummi tace yanzu dreba zai dawo daukarmu shine na fito dubawa
da ka shigo"


Gwiwarsa ce tayi sanyi ya koma motar sai ya sake dawowa zuciyarsa na fada masa
Rahima na jiransa "daure ki duba min nasan tana nan"


Ba musu ta shiga gidan. Dakin kasa da suke ta shiga tayi sa'ar ganin Rahima a
shirye cikin nata kayan kamar kowa Ummi ta dinka mata sai dai ita dasu Zahra
dankwalin kayan suka saka. Arifah da Radhiya ne kawai masu ashoke manyan amare.
Mayafinta daidai da ita har ka ta lulluba shi yadda ta saba tayi kyau sosai.
"Karami ke kiranki a waje"


Da faduwar gaba ta tashi tana tunanin karfin halinta na zama don yace ta zauna. Sai
dai bata jin akwai ranar da za ta yi fatan yi masa musu saboda babban matsayin da
ya kwata ta karfin tsiya a zuciyarta don itama bata shirya ba.


Kayansa hatta hula sak na mahaifinsa yana tsaye a bakin kofa ta fito. Ido suka hada
ya sakar mata murmushi ta janyo mayafin ta rufe rabin fuskarta.


"Hey kada ki cuceni ki hanani ganin fuskarki yau ba kawance"


Langabe kai tayi suna tafiya wurin motar "sai me?"


"Muhammad da Rahima"


Sake rufe fuska tayi komai nata yana burge shi matuka ya dora hannunsa a saitin
zuciyarsa "my God, she is so adorable"


Sun kusa kaiwa motar yaji an kwala masa kira daga cikin gidan "kai Karami ku jirani
wannan dreban da za'a turo ban ga ranar zuwansa ba"


Ba kowa bace illa Salame ta taho buguzum cikin wata kodaddiyar shadda wadda take
yiwa kallon mai kyau har yanzu tana goye da Khadi kamar wata jaririya.


Gaban Rahima ya fadi zuciyar Emzee kuma tamkar ta fito ta baki saboda bacin rai har
ta iso bakin motar ta bude gaba ta shige kwam abinta.

💕[11/2, 7:46 AM]: 56. 💕

Dan duka kanta tayi tana lekensa ta sake daga murya "kai shigo mu tafi mana" ta
kuma lekawa ta daya bangaren "kema shiga kin yiwa mutane wani kikam"


Emzee alama ya yiwa Rahima da ta tsaya don bai ga dalilin daukarta da makiyar Ummi
a mota daya ba. Sannan abu na biyu baya son a matsayinta na yayar Ummi tayi abin
zubar da mutumci a gaban Rahimansa.


Khadi da ke kan cinyar Salame kuma duk maganar da take kusan akan fuskarta tayi sai
sa hannu tayi ta toshe hanci babu kunya tana yiwa babarta wani irin kallon haushi
"hmmm Umma hmmm wali-wali a bacinci"


Da sauri Emzee ya fitar da kansa kafin ya shaka yayin da Salame ta dage ta zabgawa
Khadi duka a gadon baya ta fashe da kuka. Rahima ta tafi da sauri ta bude kofar ta
daukota Emzee ya yiwa Salame wani disgusting look. Gaban motar ya riga ya fara wani
abu sama-sama mara dadin ji ga hakoranta masu kore daga samansu. Sannan abin
haushi dubi yadda ta daki karamar yarinya haka. Kayan jikinta kuwa ya rasa abib
fada. Shi dai ya tabbatar Ummi ta sasu sayen kaya ready made na mutan Sumaila shi
da Ibrahim da Laila suka je. Haushin abinda Ummin ta yi mata dazu shine yasa taki
saka kayan wai tafi karfinsu.


Khadi 'yar banza ta tasha hannu ba musu ta gudu wurin yayarta ta lafe tana kuka.
Jikin Rahima na rawa dreban ya dawo. Ajiyar zuciya Emzee yayi yana kallota ta saman
motar.


A hankali yayi mata magana yana kallon yadda ta rikice sosai "ki bisu zan taho
yanzu okay"


Kai ta gyada da sauri ta tafi daya motar tana tsoron kada Salame tayi mata wata
maganar ko tace su koma gida. Ita kuma zuciya a baka saboda bacin rai yau rashin m
din na Khadi akanta ya kare a gaban wannan yaron na Mairama. Muryarsa taji ya gama
goga hannuwansa da juna.


"Lets get going Gwaggo"


Dauke kai tayi yana ganin dreban yayi waje kawai ya cire hularsa da riga daga shi
sai wando da vest. Bayan motar ya ajiye rigarsa da kyau ya dora hular a kanta don
kada ta fado ya shiga ya zauna ya daura belt. Salame ta kalle shi tana tunanin
dalilinsa na tube riga bata gama sannin me ake ciki ba ya fizgi motar a guje ya
fita da ribas sai da cikinta ya kada. Wata irin cin taya yayi da burki yayi kwana
tamkar mai shirin zuwa Sumaila a awa guda daga Abuja ya kwashi motar ya hau titi.
Gudu yake na karshen rashin hankali sai dai kaji qeeeyyyyy quuuuu....yaci taya ko
ya taka burki sai motar tayi kamar za ta hantsila. Salame tana kallon yadda ya
murtuke fuska kuma jikinsa baya motsawa amma ita sai dai tayi gaba yif ta dawo baya
yif jikinta yana ta mazari.


"Kai dan ubanka tafi a hankali ko ka saukeni"


Idan motar za ta amsa to Emzee ya amsa. Salame sai da ta kai ta daga hannu za ta
doke shi yayi mata wani razanannen kallo tare da taka burkin gaggawa sai ga kanta
ya tafi saura kiris ta doki glass. Hannunsa yasa ya tareta don ba jini yake son
fitar mata ba. Burinsa ko ta halin kaka ya fanshi wani abu na makantar Ummi na
shakara goma. Tsanar Salame ke kara ruri a zuciyarsa zai bincika ya tabbatar da sa
hannunta. Idan akwai ko su Ummi basu sani ba da shi da Addarsa sai sun yi mata
abinda zata ji rayuwarta tayi kunci. Yanzu haka ranar zuwa Sakkwato biki suke jira
shi da Radhiya su barwa Maikudi abinda bazai manta ba. Ba wani abu bane kuma yafi
taba zukatansu sai wulakancin da ya yiwa Umminsu ga wahalar haihuwa ga radadin
mutuwar miji da taji.


Kowa ya sani a Nigeria biyu ga watan junairu ana tsaka da sanyi ne amma banda
Salame matar Haji Indararo. Gumi take kashirban tana yiwa Emzee tofin Allah tsine.
Lokacin da suka isa wurin yayi sa'ar ganin wata motar na fita yasan zai sami wurin
parking. Katinsa ya nuna aka wangale gate ya shiga Salame tana ta numfarfashi. Yana
tsayawa ta kama kofa zata fita taji a datse.


Ashe harda hawayen wahala tayi bata sani ba cikin fada tace "shegen yaro mai kama
da ifiritu bude min"
Emzee a soja yake baka ganin wani abu wai shi sani ko sabo a tattare dashi sai
murmushin mugunta "kinfi kowa sanin cewar ina da uba mijin kanwarki....ko ince
mutumin da kike so?" Ya yi mata wani kallon gefe.


Jikin Salame ya bugu saboda tukin da ya yi amma abinda yafi daga mata hankali bai
wuce maganar da yayi ba. A ina yaji? Mairama ce ta fada masa ko waye? Karfin hali
tayi ta daure fuska.


"Rashin kunyar taka har ta kai haka Karami? Irin tarbiyar da Mairama take baku
kenan ashe, kun tashi ba ku ganin girman kowa"


Juyowa Emzee yayi ya mata wani kallo mai firgitarwa kamaninsa sun sauya
gabadaya...soja mazan fama.


"Kada ki kuma ambaton sunan Ummina domin tunda take bata taba nakasa dabba ba bare
mutum"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Salame ta fada a tsorace jikinta yana tsuma
baki na rawa "me...me kake nufi? Sharri za ka yi min kace ni na makanta ta?"


Sai da kansa ya sara a lokacin domin dama bugun cikinta yayi ya bata tsoro domin
jin gaskiyar lamari kuma yaji abinda yake so kafin ma ya tambaya. Duk da yana
zargin tabbas ita ce amma yanzu da ya tabbatar sai da abin ya girgiza shi matuka.
Ba ya kaunar Salame ko na digon sakan saboda bata cancanci a sota ba. Umminsa tana
makance tsayin shekaru Salame tana gidan miji tana ciki da haihuwa taci me kyau
tasha me kyau lokacin gwamnatinta na ci a zuciyar Alh Indararo.


"Kuruciya tasa ban fahimci me kika yi ba shiyasa ban tona miki asiri ba tun lokacin
da kika saka mata...." yace don ya kara tunzurata yana bude dash board.


Sabon gumi na yake tsattsafo mata jin sirrin boye da ko da kanta bata zancen a zuci
yau Emzee ya bankado shi. Harda sanyi ta rinka ji yana ratsata ya cigaba da
lalubensa kamar ba ta cikin motar.


Hakoranta sai sarkewa suke yi don tsoro tace "to yanzu kuma uban me kake lalube
bayan ka gama yi min sharrin"


"Bindiga"


Idanunta kamar zasu fado karshen tsoro ta kai sannan ga uwa uba wani mahaukacin
zawo da ya matsota saboda tsoro.


"An...an. fada. Maka idan...idan ka kasheni. Mairama zata yi murna ne?"
Bude pin din motar yayi "kin zata harbinki zanyi? Allah Ya kiyaye ba'ayi min wannan
tarbiyar ba"


Budewa tayi da sauri ya leka da kansa ta inda ta tashi "uhmm nace ba....nagode da
kika tabbatar min da zargina akan waye ya makanta min uwa"


Salame sai bude baki tayi tana masa kallon tsananin mamaki shi kuwa ya zura hannu
ya janyo kofar ya rufe ta bangaren da take sannan ya kifa kai akan sitiyari yana
kokarin mayarda hawayen bakincikin da suke neman zuwar masa. Dago kai yayi ya nemi
wayarsa sai ya ga har lokacin tana tsaye. Da kallo daya ya karasa razana ta ta wuce
ciki wurin da ake ta karbar baki za'a fara abinda ya tara jama'a.


Yau ranar farinciki ce dole ya saita kansa. Ibrahim ya kira bugu daya ya dauka.


"Bro turo min Rahima" yace da wata iron murya can kasa.


"Bangane ba. Ba tare kuke ba?" Zai sake magana ya hangota tare da Zayyana zasu
zauna "kana ina ne na ganta"


Kwatanta masa inda yayi parking Emzee yayi Ibrahim yaje inda suke ya fadawa Zayyana
ita kuma ta fada mata. Tana tashi bayan ta ajiye Khadi akan kujerarta ta hango
Salame amma da ta ga hankalinta baya gareta sai ta wuce ta tafi.


Ya gama saka rigarsa kenan yana gyara zaman hular a kansa ta bullo. Shagala Emzee
yayi da yadda Rahima take tafiya cikin nutsuwa. Yanayin da ya shiga mai wuyar
fassara soyayyarta ta mamaye masa kowane lungu da sako na zuciyarsa. Duk kunya ta
isheta saboda yadda ya kafeta da ido har ta karaso.


"Mu zauna a nan ko mu shiga ciki?" Yace yana fatan ta amince su zauna.


"Za'a nemeka ai"


"Okay muje" sun fara tafiya ya ga dacewar ya bata hakuri akan abinda yayar
mahaifiyarsa tayi musu "Rahima kiyi hakuri akan abinda ya faru dazu. Na saka ki
zaman jirana kuma bani na kawoki ba"


Ita da tasan mahaifiyarta ce tayi sai tayi saurin cewa "ni ya kamata na baka
hakuri"


"Akan me? For being a good girl me jin maganarrr.....maganar wa dinki kika ji?" Ya
zuba mata idanu.


Murmushi tayi kanta a kasa "Ya Emzee?"


"Nope" tsayuwa yayi ya hanata tafiya "Rahima wane matsayi kika bani?"
Kasa magana tayi tambayar tayi mata nauyi duk da amsarta tana jin tamkar ta amayo
masa ita ne ko za ta sami saukin wannan soyayya da tayi mata mugun kamu.


Kamar yayi mata kuka saboda taki magana "gobe zan koma Kaduna da sassafe. Please
Rahima ki fada min ni waye a gareki kafin na tafi....idan ba haka ba retire zanyi
tun kafin na fara aikin na dawo ga filin yaki nan in your beautiful eyes muyi ta
fafatawa."


Zuwa yanzu ko fuskarta baya iya gani ta shige cikin mayafin ta rufe kanta gabadaya
sai murmushi kawai take yi. Da kyar ta iya cewa "ni wa dinka ce to?"


"My heart..." yace da sauri "ke fa?"


Babu wanda zai wuce ya gansu baiyi musu kallo na biyu ba. Kana ganinsu ka ga
masoyan da suka mutu akan juna kuma suka dace sosai da juna. Emzee fari ne kamar
yayarsa ga kyau ga jikin matashin soja. Rahima kuwa baka ce fatarta tafi kama da
wankan tawarda don da kadan Zayyana ta fita haske. Kyakkyawa ce sosai tafi Halifa
da sauran 'ya'yan Salame nesa ba kusa ba sai dai su nuna mata haske. Round shaped
eyes dinta sunfi komai daukar hankali akan fuskarta. Kamaninta sosai da kakarta Iya
shiyasa take ji da ita.


"Kinyi shiru Rahiman Muhammad"


Sautin loudspeaker suka ji za'a bude taron da addu'a Rahima ta daure tace "to me
kake so nace Muhammadun Rahima?"


Murmushinsa dariyar farinciki ya koma yana kallonta da adoration "kince
komai....realy? Kin yarda Muhammadun Rahima ne ni? Daga ni fa babu kari"


Dariya tayi ta cikin mayafin tana gyada kai. Zuciyar Emzee ta cika da soyayyar
kanwarsa da bai san suna da alaka ba ko kadan. Da sauri sauri suka karasa hall din
za ta wuce bangaren mata ya bi bayanta da sauri yana maida numfashi tamkar wanda
yayi tsere taji yace "Ina sonki Rahiman Muhammad"


Juyowa tayi suka hada ido kowa da kayataccen murmushi a saman fuskarsa sannan suka
nemi wurin zama.


**********

Taro ya soma kankama bayan addu'o'i da mika godiya ga Allah mai gabatarwa Ibrahim
Hadir ya gabatar da manyan baki na musamman. Ba kowa bane illa manyan aminai 'yan
uwa ga Zayyan kowa da matarsa. Excellency baban Arifah, Major Daddy, Baba Hadir sai
kuma Tante da mijinta mahaifin Yousuf. Wadannan mutane kowannensu ya taka
muhimmiyar rawa a rayuwar iyalin Zayyan shiyasa idan suna ganin ya kyautata musu
wurin ceton rayuwarsu ya kan ce babu kyautatawa mafi tsada da daraja sai wadda za
kayi a bayan idon mutum idan ya mutu. Wannan kyautatawar kayi ta ne ba don ganin
ido ba bare kasa ran a saka maka. A gefe guda ga duka 'yan uwan Zayyan mata uku da
maza biyu domin Maikudi bazai taba iya zuwa ba duk da Zayyan ya bukaci hakan. To da
wane ido zai kalli su Mairama, Daddy da har yau bai manta kalar bacin ran da ya
gani a idanunsa ba, da uban gayya Zayyan wanda ya mare shi. Ya kure Zayyan iyakar
kurewa kuma ya tabbatar abinda yayi musu bazai taba gogewa a zukatansu ba. Son
zuciya da kwadayi ya mayar dashi mujiya a cikin ahalinsa. Yana ji yana gani sai dai
yayi ta dari dari dasu domin tsanarsa da yake gani a idanunsu.


Captain Onomza shima yazo ga jama'ar Rugar Barkindo, na gidan Malamijo da abokan
arziki. Sannan mutumin da Zayyan ya dauka da matukar mahimmanci a rayuwarsa wato
Chibuzor da matarsa da 'yarsu su ma kayan jikinsu irin na wadanda su ka yi ankon
fari da green din. Sai kuma Maman Dolapo da Christie ma sun zo kafin shigowar Emzee
suka share hawayensu dasu Mama. Ga Alh Salisu da nasa iyalin abin sai son barka.


Ibrahim ne yake magana da turanci da hausa domin kowa ya fahimta ya sanar da cewa
akwai gajeren wasa da abokan Emzee zasu gabatar mai taken A Soldier's Dream (Burin
Soja).


Drama ce mai kayatarwa wadda ta janyo wurin yayi shiru aka zuba musu idanu daga kan
stage. Sojoji ne rataye da bindiga da 'yan jakunkunansu sunyi shirin tafiya filin
daga. Gefe guda matansu da iyayensu suna ta kuka da yara. Idan ka ga yadda suke
gabatar da dramar da matukar ban tausayi. Sun rabu da iyali suna ta kuka sannan
sunje yakin an kashe da yawansu. Nan ma wurin dawowarsu mata da yawa suka rinka
suma duk wadda ta ga babu mijinta. Mutane kuwa sai share hawaye domin an shigar
dasu cikin rayuwar da basu santa ba kuma a da babu wanda yake damuwa da sanin nata.


Da dramar ta kare Radhiya ma duk yadda ta ga abubuwa a Military Voice lokacin da
suke dauka sai da tayi wani kukan. Bayan an gama tafa musu Ibrahim ya bukaci
wadanda ake taro dominsu su hadu wuri daya.


Zayyana dauke da DK wanda kayansa harda hula babu bambanci da na Daada da Emzee
anyi masa komai dan karami daidai da jikinsa suka je wurin Daada. Wani envelop da
Ummi tayi wrapping mai dan tudu Zayyan ya daga hannun DK da yake jikin Zayyan ya
dora masa a kirjinsa.


"This is for you my son"


Su Daddy suna kallo babu wanda yasan menene a ciki. Wani ya sake daukowa ya fi
wancan girma da dan nauyi ya mikawa Zayyana.


"Kallabi tsakanin rawuna Zayyanatun Zayyan ga naki"


Sai da ta rissina tace "Allah Ya kara budi Daada Ya saka da alkhairi"


"Amin" su Excellency suka ce suna murmushi.


Wani dan karami sosai Zayyan ya mikawa Emzee "Soja dan sojoji kaima ga naka"
Godiya yayi sosai shima aka fara daukarsu a hotuna sannan kamar hadin baki aka
shiga miko musu gifts kowa da abinda yake badawa. Family picture aka tashi dauka
aka hada iyalan Zayyan, Daddy, Baba Hadir, Excellency duka wasu a tsaye wasu a
durkushe. Zayyan ya dan gama waigensa ya hango Chibuzor ya kira shi da hannu shi da
matarsa.


"Sir this is a family picture" yace yana sake ja da baya.


"You are my family Chibuzor" Zayyan yace yana yi masa murmushi tare da nuna masa
inda zasu tsaya kusa da sauran yaran nasu. Chibuzor bai taba tunanin karamcin
Zayyan ya kai haka ba. Yana da masaniyar yadda addini da yare ke kawo tawayar
kyakkyawar alaka a tsakanin 'yan Nigeria amma ga wani babban soja masoyi ga mutane
da dama ya rungumi kowa hannu bibbiyu.


An gama hotuna aka fara cin abinci wanda yake serve yourself anyi shi a wadace kowa
yaci ya koshi. Duk wannan abu da akeyi Salame tana rakube ko motsin kirki bata son
yi saboda ko yaya ta ga giftawar Emzee sai cikinta ya duri ruwa. Yanzu idan ya bude
baki a wurin nan ko kafin ta koma Sumaila ta kade har ganyenta don bata san me zasu
yi mata ba. Ana yiwa Zayyan kallon mai kirki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login