Showing 213001 words to 216000 words out of 295847 words
ta sake ganin rigimar Mami da kannenta.
Kallo na bakinciki da hassada Salame take wurga mata. Mairama dai atampa ta saka
super itama amma duka wurin babu wanda ya kama kamar kyaun da suka yi ita da
Radhiya. Fatar jiki ta nuna hutu da jindadi gami da kwanciyar hankali.
Radhiya ta tashi ta fadi sunanta itama sannan tace akwai kaninta yana makaranta bai
sami zuwa ba. A sanyaye take magana saboda hawayen da take gani Rahima na zubarwa a
boye. Komawa tayi ta zauna ta kama hannun Rahiman guda daya ta rike amma bata ce
mata komai ba sai ma matsawa da tayi jikinta ta saka daya hannunta ta dan rungumota
a jiki. Sai da tayi mai isarta a hankali nutsuwa ta rinka zuwar mata ta dago
jajayen idanu ta kalli Radhiya.
"Abu ne ya fada min a ido fa kada ki zata kuka nayi"
"Mai karya" Radhiya tace tana kada kai.
"Ai dai baki ji na rantse ba"
Murmushi suka yi wa juna Radhiya taji kanwarta ta ta shiga ranta yayin da take
tunanin hanyar da zata bi ta kartawa Gwaggo Salame rashin m ko dan kadan ne taji
idan da dadi gwasale mutum a bainar jama'a.
💕 [11/2, 7:24 AM]🏽: 52..💕
Sai da kowa ya gabatar da kansa aka kare akan jarirai Hassana da Usaina. Malamijo
ya gyara babbar rigarsa yana kallonsu wai gabadaya tsatsonsa ne wannan. Bai taba
tsayawa ya duba wannan babbar baiwa da Allah Yayi masa ta 'ya'ya ba. Kafin yanzu
kallon nauyi da matsala kawai yake yi musu yana ganin matan da yake aura basa
kyauta masa kowacce tana zuwa sai ciki. Babu wanda bai tara ba cikinsu da nagari da
shakiyai. Akwai nutsatstsu ga kuma fitinannu. Biyu ma dai cikinsu kauraye ne 'yan
chau-chau. Malamijo ya kusa shekara bai sasu a idanunsa ba kuma bai damu ba saboda
sunfi zama a gidan kakaninsu na wurin uwa tunda babarsu daya. A can suka koma
kaurayen saboda 'yan uwan babar tasu irin mafarautan nan ne masu yawo da karnuka.
Ba'a tsaya nan ba duka dai cikin yaran nasa akwai rikakken dan jagaliyar siyasa
wanda yayi suna akan rashin mutumci indai aka taba 'yan jama'iyyarsu. Ga dreban
adaidaita sahu da karamin dan sanda mai mukamin kofur. Ga Mal Ayuba mafi rikon
addinin cikinsu. Akwai mai sayar da kayan fruits a wheelbaro a cikin Kano. Bature
shi da yake yayi NCE koyarwa yake yi, Habu kuma yana sayar da kayan masarufi.
'Ya'yan dai sai son barka kowa da inda yafi kauri.
A bangaren matan ma dai babu wata mai ilimin da ya wuce secondary sai Mairama da ta
koma lokaci daya da 'ya'yanta. Da yawansu basu gama makaranta ba. Na gidan mijin
kalilan ne ga zaurawa biyu. Akwai uku marasa jin magana daya saurayinta dan daba,
biyun kuwa samari ke daukar nauyinsu. Ba dai yawon ta zubar suke yi ba amma ana
kanwar ta zubar din kai na hayaki suna jinsu daidai da kowa.
Abinda Mal Ali Gidado Malamijon Sumaila bai saba ba kuma bai taba tunanin zaiyi ba
ne yayi masa bazata. Hawaye ne masu zafi yake fitarwa saboda tun bayan wata nasiha
mai nauyi da Ayuba ya cire kunyar mahaifinsa yayi masa jikinsa ya mutu murus. Duk
wata guntuwar hayaniya sai ta dauke wurin yayi shiru. Mairama da bata hada son
Malamijo da komai duk halinsa kuwa sai kuka.
Salame ta kalleta shekeke ta tabe baki "sabon salo"
Gyaran murya Malamijo yayi ya gama karya zukatan matansa musamman masoyiya Hajjo da
Nene wadda yace dole tazo 'ya'ya nata ne itama "abinda zan fada muku ba yawa ne
dashi ba, don Allah ku yafewa min"
Yaran nasa ma sai gashi daidai da daidai matan nan suna yarfe kwalla da wannan
kalami nasa.
"Babu wani abu da nayi muku wanda zan bugi kirji dashi a gaban Allah game da rike
amanarku. Haka Ayuba yace min jiya ko ba haka ba...Aradun Allah kasa bacci nayi duk
ya tsoratani"
Wasu na dariya wasu na murmushi saboda yadda yake maganar bai dauketa da wasa ba.
"Nayi alkawari zan gyara sha Allahu kafin na mutu zanyi kokarin gyara laifina."
Radhiya don ta rage musu nauyin da ya saka musu a zuci ta dauko zancen da tasan
baya so "dama ana cewa siituna aw saba'una tafiya tayi nisa"
"Don kaniyarki shekarata hamsin da bakwai watan azumin tsofaffi zanyi da takwas"
yace fuska a tamke don yaki jinin zancen mutuwa.
Gabadaya wurin ya kaure da dariya da mugun tsakin da Salame take saki. Sarai
Malamijo yaji kuma ya kudiri niyar saitawa 'yar tasa zama. Nasihar hadin kai ya
dora musu da ita sai gashi sannu a hankali wadanda basu magana a da ko dai don
rashin jituwa ko don rashin sabo da juna hira ta fara barkewa a tsakaninsu. Abinda
Malamijo bai sani ba shine gabadaya 'ya'yan nasa ba kin junansu suke yi ba rashin
tsayuwar uba a rayuwarsu ita ce babbar nakasun da suke fama da ita. Yau gashi zaune
dasu babu hantara babu zagi kowa ransa wasai. Yadikko ganin haka tace me zai hana
suna cin abinci yaran na zuwa gareshi yaji me kowa yake yi kuma ya bincike
matsalolinsu. Abin yayi masa dadi matan cikinsu masu kuruciya suka tashi aka zubo
abinci ga nama shar dasu. Hayaniya kuwa sai da Radhiya ta kira Emzee tace tana ta
tausayinsa saboda yayi missing. Sun dan taba hira ta ajiye wayar.
Rahima ta kalleta a kunyace saboda ganin kanta take wata muguwar local akan
Radhiyan tace "shine kanin naki da kika ce yana makaranta?"
"Eh bari ki ga hotonsa saboda kada ku hadu baku san juna ba" tace tana binciko mata
hotonsa a wayarta. Wanda yake sanye da khakinsa yayi wani kyau ta nuna mata.
Shiru Rahima tayi tana kare masa kallo lokaci guda taji wata irin kunya saboda wani
kallon kasa-kasa da Radhiya take yi mata "kema sojoji suna burgeki ko?"
"Uhm ni dai tsoronsu nake ji"
"Kice dai irin halin Fulanin zaki yi na tsoron duk mai uniform"
Dariya suka yi tare wata yarinya da bata fi shekara goma ba ta kawo musu tray
shakare da shinkafa dafaduka taji kayan lambu tayi kyau. Karamar uwa ce dai tunda
'yar Malamijo ce suka karba su hudu da wasu matan kusan sa'annin Rahima duka
'ya'yan gidan suka fara ci. Radhiya duka burgesu take yi kana ganinta kaga
wayayyiyar 'yar boko ga gayu amma da ta shiga cikinsu ajiye komai take yi ta koma
daidai dasu kamar yadda Umminta take yi.
Abinci suka fara ci sauran matan suna yiwa Rahima korafin tana cikin garin amma
bata son zuwa gidan duk ba'a saba da ita ba.
Murmushi tayi kanta a kasa ita kowa ma kunyarsa take ji "Zan rinka zuwa yanzu sai
kun koreni"
Daga sama suka ji muryar Salame babu wanda ya kula da zuwanta sai hannunta da ta
kama kunnen Rahima dashi da karfi "gani nazo tunda ke baki da hankalin idan kin
shigo ki zo ki nemi uwarki ki gaisheta"
Kunnen zugi yake kamar zai tsinke ta soma hawaye idanu sun fara dawowa kansu anata
bata hakuri ta wani hade rai ita me 'ya.
"Umma kiyi hakuri a makare nazo kuma bana son tsallake mutane na ga kinyi nisa"
"Tunda an samo abinda babu a gidan tsoho ai dole kice nayi nisa. Maza kici ki tashi
ki koma"
"Umma!" Halifa yace a zafafe yana tahowa wurin ransa yayi mugun baci.
Kafin ya iso Mairama ta fizgo hannun Salame wadda bata sassauta rikon kunnen
Rahiman ba sai da ta saki wata wahalalliyar kara.
"Ke wuce da ita dakin Yadikko ina zuwa" ta umarci Radhiya kafin ta finciki hannun
Salame zuwa bangaren samarin gidan daga can gefe.
Kwace hannunta Salame tayi tana furzar da yawu da hura hanci. Maganar da zata yi ce
ta makale saboda ido da suka hada da Mairama.
Borin kunya duk ya kama ta tace "ni kike yiwa wannan kallon Mairama?"
"Nayi miki Adda ko zaki dauki mataki ne?".
Bata ce komai ba ran Mairama a sama don zuciyarta wani irin tafasar bacin rai take
yi saboda abinda Salame take yi. Ta gama kunyata kanta cikin kannenta sannan tazo
ta matsantawa yarinya.
"Hantara ko kadan bata da dadi ya kamata ace ke da kika girma a gidan nan ki fi
kowa dorarwa amma shine tun dazu kin saka yarinya a gaba kuma a cikin mutane. Ko me
tayi miki ki bari ku kebe mana. Su wadanda kike fifitawar ai ba finta suka yi ba
tunda yadda kika haifesu itama haihuwarta kika yi"
Cinya Salame ta buga "dadin abin dai baki isa ki fada min dadin haihuwarta ta ba
bare kice ina cusgunawa 'yar wani. Ban shiga sabgar iyalinki ba kema ki tsame
hannunki akan nawa. Halifa ma da kike wani jansa a jiki wallahi na hana daga yau a
kyale min kayana"
"Nan kuma baki isa ba. Idan kinsa karfi kin shiga tsakanin zumuncinmu bazan yarda
da na 'ya'ya ba."
"Mairama" tace da sigar warning tana kada yatsa "kada ki kaini bango"
"Allah Ya ganar dake don ban ga amfanin magana dake ba" Mairama tace tana juyawa.
Yadikko suka gani a gefensu "ke da nake yiwa kallon mai hankalin kuma ashe biye
mata kika yi zakuyi rigima Mairama? Wai me ya sameku ne ku da kowa yasan kanku a
hade yake kamar tagwaye"
Tsaki Salame ta buga tayi gaba tana harare harare. Yadikko da take matsayin uwa a
garesu a gidan abin yayi mata zafi sai Mairama ke bata hakuri.
A can dakin da Radhiya ta kai Rahima kuwa yarinyar kuka take yi sosai abin tausayi.
Radhiya taji wani irin haushin Gwaggon tasu ya dada shigarta. Maganar da Rahima
tayi mata ne ya sake karyar mata da zuciya ita da Halifa da ya biyo su dakin.
"Me na yiwa Umma ta tsaneni? Don Allah ku tayani bata hakuri"
Kwalla ce ta taru a idanun Halifa ya fice daga dakin don babu yadda za'ayi ya fada
mata abinda ya fahimta wato talaucin mahaifinta yasa take kinta. Dreban da ya kawo
shi ya kira dama ya zaga cikin gari ne yace yazo su tafi an gama taron. Babu wanda
ya yiwa sallama yayi tafiyarsa yana ji inama inama....don dai kawai uwa uwace babu
yadda mutum zaiyi da ita.
Radhiya rarrashin Rahima tayi ta yi tace mata idan babanta zai yarda tazo su koma
Abuja tare.
"Baffa baya son kwadayi Adda Radhiya" tace tana dan murmushi.
"Zuwa gidana sunansa zumunci ba kwadayi ba kinji ko." Ummi tace tana shiga dakin da
murmushi saboda yadda take jin son Rahima a zuciyarta. Hannunta ta kama ta mikar da
ita "Tashi in hadaku da Habu ya biki gidan ya tambayeshi idan yaso kya dawo bayan
bikin Addar taku"
Baki ta bude da murmushi "Adda aure zakiyi?"
Ganin idon Ummi yasa Radhiya jin kunya ta fita daga dakin. Ita kuwa zaunar da
Rahima ta sake yi tana mata nasiha akan hakuri da mahaifiyarta.
"Gwaggo na ga ku ma duk kun tsaneta kuma a gidan nata ma Alhajin kullum idan yana
nan naje fada suke yi. Bata son kowa sai su Ya Halifa kuma itama ba'a sonta"
Wani iri Ummi taji zuciyarta tayi nauyi. Wane da ne zai so ya ga kamar ba'a son
iyayensa? To Salame haka kawai hassada da kyashi yasa ta bata da kowa nata kuma
rainin da tayiwa baban Rahima yasa bata son 'yarsa bayan saboda soyayya ko auren
fari baiyi ba ya aureta tana bazawara.
"Ba tsanarta muka yi ba...kinga ki cire komai a ranki zamu daidaita kanmu babu
ruwanku. Ke da 'yan uwanki zumuncinku nake so yayi karfi"
Idan ba kakarta ba zata rantse bata taba doguwar magana da wata mace mai matsayin
uwa ba a gareta sai yau. Ashe salihancin nan duka rashin samun wuri ne don samun
fuska da ta gani wurin kanwar mahaifiyarta yasa ta saki jiki ta rinka fada mata
matsalolinta da tambayoyi kala kala sai ga Ummi tana dariya sosai saboda sosai take
ganin zallar kuruciya tare da Rahima. Irin abinnan ne dai wai ita kada a raina
talaucinsu shine sai tayi ta daure fuska.
Salame a zatonta ta tafi sai ganinta tayi da Mairama sunyi wajen inda mazan suke
tana magana da Habu. To su din ma kowa yaji takaicin yadda ta rinka yiwa Rahiman
shiyasa ba musu shi da Bature suka tasata a gaba har gidansu suka roki arzikin a
barta tabi kanwar mahaifiyarta saboda suna son a farfado da zumumcin da aka saki a
baya. Kakarta Iya abin yayi mata dadi don tasan Rahiman tana bukatar dangin uwa.
Babanta kuwa da farko ki yayi sai daga baya ya rinka kashedin don Allah a cewa
Mairama amana kada su wulakanta masa 'ya kuma a dawo da ita kwana uku bayan an gama
bikin zaiyi daidai da kwana biyu kafin a koma 3rd term lokacin da zata koma
makaranta suyi jarabawar fita. Da zasu tafi kowanne ya samo dan canjinsa ya bata ta
shige da murna Iya tace maza ta debo kayanta masu kyan ta wanke.
Duk bidirin nan Salame bata sani ba. Kuma tafiyar tasu washegari ne don da dreba
aka hadosu. Tafiyarsu Rugar Barkindo ma Zayyan ya nace suyi kwana biyu kacal har
Radhiyan su dawo saboda gaskiya shi an cuce shi ace sai ana baifi kwana biyu daurin
aure ba Alheran dinsa zata dawo gida. Har yaushe suka gama hirar yaushe gamo. Sosai
ya rufe idanunsa yace idan Mairama bazata iya fadawa Innawuro ba shi zai fada ai ba
rashin kunya yayi ba kawai yana bukatar lokaci ne da 'yarsa kafin ta koma karkashin
wani.
"Son 'ya'yanka yayi yawa Sojana" Ummi tace tana dariya.
"Kada ki ga laifina kinfi kowa sanin ni dasu muna bukatar juna"
"Ni kuma ba'a bukata ta ko?"
"Ke kuma matsayinki ai ba irin nasu bane. Idan kin dawo sai in kara jaddada miki
cewa Tureta na Fillo ne ita daya"
Hirarsu suke yi gwanin sha'awa bayan sun gama ta koma wurin Malamijo suna zancen
bikin Radhiya da ya gabato. Don Zayyan ya fada mata washegari Rayyan da Badaru zasu
je Abuja saboda zuwan iyayen Awwab wadanda Daddy Haroun zai yiwa jagora neman auren
Alheran Radhiya.
***********
Karfe goma na dare bayan Radhiya ta gama shirin bacci ta dauko wayarta ta ga missed
calls din Awwab rututu. Turo baki tayi ta kira shi ya soma mita kuwa saboda rashin
daukar wayarsa da ta tsiri yi.
Ya damu sosai ya kwantar da murya a hankali yace "Me yake faruwa ne Schatzi? Nayi
laifi?"
"Hammana yaushe zaka dawo ne" yaji tace kamar za ta yi masa kuka. Yadda yake
missing dinta ma baya jin ta kama kafarsa amma da yake ita ce mai bakin rigimar sam
ta hana shi sakat.
"I am trying to finish up da wuri na taho."
"To" kawai tace ya dafe kai don ya sani ranta a bace yake da dadewarsa.
Komai na Alheran burgeshi yake yi zuciyarsa tana kara aminta da soyayyar dake
tsakaninsu cikin wani yanayi yana jan kowace kalma yace "Do you love me that much?"
Kunya taji ta kalli gefenta da Rahima take kwance da sauran 'yan matan babu mai
bacci sai kawai ta suri hijan ta fice. Shiru yaji bata yi magana ba sai da taje
wurin dan tudun nan na soron gidan ta zauna.
"Kasan ina nake yanzu?"
Yadda ta iya yi masa shagwaba haka ya koyi yi mata shima "Baki bani amsata ba ni"
"I do"
Shiru suka yi kowannensu na begen dan uwansa. Shi yayi ta maza ya tambayeta ina
take din.
"A soron gidan Malamijo"
Ai kuwa duk abinda yayi a soron nan ya tuna. Zamansu na cin abinci da suka rinka
kama-kama da cokali daya sai kuma ranar da ya fara bata ragowar alawar bakinsa ta
shanye sauran kadan din ya karba ya karasa. Kewarta sosai ta kama shi ya riga ya
sabar mata da yasha ko yaci abu ya rage mata. Sau tari yanzu yana kai abu bakinsa
ita ce take fado masa ya rinka tunani kenan.
"Kin tuna min da memories masu dadi a wurin na kara missing dinki fiye da yadda
nayi few seconds back. Bari na fada miki su daya bayan daya"
Ita kadai take ta sakin murmushi yana fada mata din. Sai kuma ya koma rigimar wai
ta kalli tsabar idonsa tace bata son aure. Wannan rigima taki wucewa a wurin Awwab
sai dai idan bai tuna ba. Zancen gidan da zasu zauna ya yi mata idan bata da
matsala dashi dazu iyayen nasu maza sun fada masa za'ayi musu gyara a bamgaren Ummi
na da kenan zasu zauna kusa da Mami da Mama. Idan ta gama makaranta gabadaya sai ya
nemi wani saboda bashi da ra'ayin zamansu a Germany duk da can yake aiki. Tunda
aikin ba na zama bane babu amfanin ya ajiyeta can. Duk lokacin da yake off duty zai
dawo Nigeria. Yana so ta cigaba da Military Voice ne amma babu inda zai fiye masa
sama da ace tana yiwa kasar haihuwarta wannan aikin. Kare hirar tasu yayi da cewa
ta turo masa sizes na duk abinda tasan cewa da size ake saya.
"Kamar me da me?"
"Seriously Schatzi? Nayi zaton zaki gane ba sai munzo muna jin kunya ni dake ba. Ai
dai kinsan nasan size din takalminki"
"Kunya kuma? Banda takalmin akwai wani abu ne da za'aji kunyarsa?" Tace batare da
ta kawo komai a ranta ba.
"Eh to kamar b...."
Ihu ta saka masa ta ma manta dare ne da kuma inda take "zan yi maka text sai
anjima"
"Silly girl....call me kafin ku tafi goben kuma ina jiran size din b..."
Kit yaji ta kashe wayar yana imagining din yadda take yi da fuska saboda kunya.
Washegari suka wuce Rugar Barkindo harda Rahima. Tunda take bata taba fita daga
Sumaila ba shiyasa ta kasa boye farincikinta. Ko me ta tambaya Ummi da Radhiya basa
gajiyawa wurin bata amsa. Nan da nan ta zama lively kamar ba yarinyar nan mai boye
kunci a zuciyarta ba. A irin shekarunta na tashen 'yan matanci babu abinda take
bukata kamar uwa da zata sakata a hanya ko da ba ita ta tsuguna ta haifeta ba. Jin
kanta take yi wata daban itama kamar kowa. Ummi har wani dokin isarsu Abuja take yi
domin ta hadata da Zayyana kawance.
Sakon Zayyan na a koma masa da 'yarsa ya riski Innawuro a take Ardo yace baiga
laifinsa ba domin da ya girma dasu bazai fadi haka ba. Amma tabbas bayan aikin da
ta tafi tana yawon garuruwa kuma ta dawo ana shirin aure ta sake nisa dashi bai
kamata ba. Innawuro bata ji haushi ba sai ma dadin cewa mijin Mairama tabbas dan
halak ne ya dawo da dakon son 'yarta kuma yana kokarin samun kyakkyawar fahimta da
'ya'yansa. Sai dai bata so yadda bata samu ta gyara 'yarta Mairama ba a lokacin
nata auren jikar ma ta rasa. Su ma suna da hanyoyinsu na gyara amarya na gargajiya
wanda bata so Radhiyanta ta rasa. Da suka yi kwana biyunsu suka zaga 'yan uwa ta
hada kayanta ta bisu tunda su Ardo zasu je wannan babban taro na dawowarsa ga
daurin aure sa dawo tare.
Kafin su isa Ummi tayi waya a kai mata Zayyana gida ta taho mata da kanwa. Mami sai
ta nemi Ibrahim tunda bai koma ba sai farkon February. Kadaici ne ya dame shi
saboda rashin Emzee kullum baya gida kamar yaci kafar kare.
A hanya suna tafiya tayi shiru kamar ba ita ba. Tun ranar nan da yayi mata magana
akan dena kula shi da tayi bata yarda su hadu su kadai sai ta gudu. Kunyarsa take
ji sosai kamar wani surukinta. Gidan Mama ma ta dena sakewa saboda tsoron kada ya
rutsata. Gefen titi ya samu kusa da