Showing 222001 words to 225000 words out of 295847 words

Chapter 75 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

minti goma MC KDM sunan mai gabatar da taron wanda baya
zuwa kowane irin taro dama sai na manya yace kowa ya tashi shugaban kasa zai shigo
da first lady. Wurin zamansu daban aka zauna bayan national anthem da akayi. Ummi
duk ta damu ina Karami sai da Zayyan yace ta kwantar da hankalinta dan nata yana
nan za ta ganshi. An shiga taro ka in da na in hankula suka karkata suka koma ga MC
da abubuwan da ake gabatarwa. Salame kallo daya ta yiwa Zayyan bata kara ba domin
zuciyarta sai da tayi barazanar ballo mata kirji kuma abin takaici ga Alh Salisu a
gefe sai taji duk ta muzanta a cikin mutane saboda kayan da ta saka na taron gidan
Malamijo ne ganin kanta tayi wata koma baya a cikinsu.


Duhu hall din yayi a take hasken screen da za'a gabatar da tarihin Zayyan ya mamaye
wurin. An fara da nuna hotunansa yana matakin farko a soja sai dariyar manyan baki
kake ji kadan kadan saboda daga hoton kadai zaka iya gane cewa Zayyan Tureta ba
karamin fitinanne bane. A hankali aka zo kan aurensa duka ana nunawa ne KDM yana
bayani. An tsayar da hoton akan shi da Daddy da Baba Hadir ranar tafiyarsu Liberia.
Daga nan ya cigaba da narrating rayuwar da Zayyan yayi sai da gwamnoni biyu suka
zubar da hawaye musamman da aka zo video din fitowarsa daga motar da ta kaishi
Nigerian Embassy lokacin da ya hadu da Excellency da Awwab. Su Ummi sai hawaye yasa
hannu ya rike nata a hankali tace "I love you Sojana"
"I love you too Fillo" ya maida mata iya jin kunnenta.


An kare video din da wani hotonsa ne shi da Ummi, Radhiya da Emzee a falon gidansa
bayan sun koma. Fitilu aka kunna mutane sai sharbar hawayen jin labarin al'ajabi na
wannan soja.


MC yace kowa ya shirya domin ganin wasan da sojoji suka shirya domin murnar dawowar
jan gwarzo jarumin jarumai.


Wata murya suka ji inda mai ita yake commanding Cadets 'yan uwansa da kowa ya shiga
layi. Tsit hall din yayi kamar ruwa ya cinyesu lokacin da aka saka wani kida irin
na band din sojoji sai gasu nan sun fito mutum arba'in cikon na arba'in da dayan
shine commander din wannan parade din wato Cadet Muhammad Zayyan Tureta.


Sun sha training ba na wasa ba daga shi har sauran shiyasa babu kuskure ko na motsi
daga garesu. Bindiga ce a hannunsu duk da ba harbi zasu yi ba suka yi wani wasa da
ita da ya burge kowa a wurin. Komai nasu tare kidan yana chanjawa da umarnin Emzee.
Karshe mutane suka ga wadanda suka gama parade din sun matsa Emzee ya sake bada
umarni sai ga wasu suna fitowa cikin tsari suka shiga sahu suka yi wani layi layi
sai da suka durkusa kowa ya gane sun rubuta Nigeria ne ai kuwa mutane a tare suka
karanta

"NIGERIA"


Wasu suka fito a bayansu suma suka dunkule a kasa aka sake karantawa.


"WELCOMES"


Sai na karshen suma cikin gwaninta suka yi nasu layin tare da durkusawa.


"ZAYYAN"


Habawa sai wuri ya kaure da tafi da murna KDM yace

"Da wannan nake gabatar muku da tauraron wannan rana Major General Zayyan Muhammad
Tureta"


Chanja kida akayi yazo ya haye stage din bayan ya yiwa dansa abim sonsa Emzee kallo
daya tak yana tsaye ya kame sauran suna nan inda suke.


KDM yace ko yana da abin fada ga dimbin 'yan Nigeria da suke wurin da masu kallo
live a gida.


"Thank you Nigeria you have given me 22years worth of love in a single night. Long
live Nigeria, God bless my country"
Wani hawayen Mairaman Zayyan ta fitar batare da ta sani ba. A nan tsaye aka barshi
shugaban kasa ya taso zai bashi award. Hularsa ya cire ya mika masa hannu sai da Mr
President ya bawa kowa mamaki domin bai karbi hannun ba sai rungumar Zayyan da yayi
sannan ya karbi award din daga hannun Chief of Army Staff ya mika masa.


Rahima babu inda take kallo sai Emzee da yake tsaye har lokacin a kame babu
gajiyawa taji wata irin azababbiyar soyayyarsa tayi mata kamun in ba kai babu
rayuwa. It was a moment da bazata taba mantawa ba a rayuwarta har abada.


Bayan Zayyan ya zauna ne su Emzee sun koma mazauninsu Chief of army staff din da
kansa ya gabatar da shirin Military Voice yace suna alfahari da wannan yunkuri na
sanar da duniya sadaukarwar da sojoji da iyalansu suke yi. Sannan gashi sun sake
ganin inda yake bukatar a duba domin tallafi ga wadanda suke cikin mawuyacin hali.


Sake yin duhu wurin yayi sai ga Radhiya tana gabatar da shirin sannan aka nuna
bangarori daban daban a ciki wanda ya janyo zubar hawayen mutane da dama a wurin.
Iyayenta da mijinta were so proud haka ma 'yan uwa.


MC KDM sai cewa yayi Radhiya ta fito tace wani abu game da shirin nan Ita da Arifah
suma nasu shirin suka fara inda da sahalewar angwayen nasu suka amince a hada
dinner a Abuja bayan kowacce anyi mata nata bikin na gida. Arifah a Jos za'ayi wasu
events din bikin 'yar gwamna guda daya tilo ita kuma Radhiya sai da aka yi ta
tunanin inda yafi dacewa karshe Mama tace ayi a Abuja amma yini a Sakkwato za'ayi
kamar yadda za'ayiwa Arifah a Jos. Ranar kai amarya kowacce a daukota daga garin
mahaifinta washegari suyi dinner dinsu. Daga nan kuma tsugunne bata kare ba domin
Tante tana can Nijar da sauran 'yan uwa ana shirin bikin 'ya'yanta Yousuf da
Radhiya saboda haka ana wannan dinner din can zasu wuce ayi sabon biki sannan
amaren su tare. Dama kuma Tante din ta riga ta sanar dasu Ummi kada a dauko wata
mai gyaran jiki zata taho da kawarta tun suna 'yan mata idan sun zo taron Zayyan
zata barta a nan. Arifah daga Nijar zasu wuce France shi kuma Awwab ya riga yasa an
fara nemawa Radhiya visar Germany can zai tafi da ita suyi sati biyu su dawo
Nigeria.


Tun yanzu kowa jiki ya fara fada masa saboda shirye shirye. Ana ta kai dinkunan
biki na amarya , 'yan uwanta da iyaye. Zahra da Raji sun dawo daga Katsina sai hutu
ya kara daga wurin aiki amma fa idan ya koma shekarar kaf bashi da hutu. Fauziyya
itama sauki ya samu sun koma Katsina sai daurin auren Bilal zai taho da ita.


SANNU SANNU BATA HANA ZUWA


Saura kwana uku daurin auren Arifah hakan na nufi kwanaki hudu ya rage na Radhiya
amma har yanzu Awwab bai dawo ba sai bata hakuri yake yi al'amura sun zo ba yadda
yayi zato ba. Radhiya tun tana daurewa sai da tayi masa kuka da daddare akan bata
fatan a daura auren baya nan. Hakuri ya bata domin wani training aka saka yake
jagoranta. Ainihi bashi bane da tuni ma ya dawo gida sai matar wanda zaiyi ta haihu
sati biyar kafin ainihin lokacin haihuwarta. Abu yazo da tangarda dole ya dauki
hutu. Gashi daga shi sai Awwab ne suka yi wannan course din a Ukraine. Tunda sunsan
aure zaiyi shine aka daga masa kafa zai taho ana gobe daurin auren Yousuf.


Ga abu ya dame shi ga fushin Alheran dinsa sannan Mami da Daddy sun kira shi a
lokuta mabambanta kowanne baisan dayan ya kira ba suna jaddada masa idan ya bari
aka daura aure babu shi zai ga fushinsu.


Ya gama shirinsa tsaf ranar da zai taho ana gobe daurin auren su Arifah yayi ta
kiran Radhiya taki dauka tana ta kunkuni. Text yayi mata mai dauke da dadadan
kalamai ya sanar da ita yana hanya zai sauka shadayan dare. Bata yi masa reply ba
sai sai kowa ya ga sauyi da walwalarta da ta karu. Tante ta fadawa ya taho tace to
maza ta tanadar masa abinci a kai gidan Mami. Yousuf da suka zo da sauran mutanen
Nijar shi acan yayi masauki dakin Awwab tare da Raji. Gidan Major General Zayyan
kuwa babu masaka tsinke saboda 'yan uwansa na Nijar iyaye su Alh Sidi da Alh
Ghoumar. Alh Mousa dai da mijin Mammee da sauran tawagarsu hotel aka kama musu.
'Yan uwa ne aka taru ko ta ina. Emzee ma ya da safe ya iso sai dai gidan Mama ya
wuce kai tsaye ga mamakinsa Halifa ma ya riga shi zuwa suna tare da Ibrahim. Sakin
fuska yayi kamar babu komai a ransa ya rungumi dan uwansa sai dai har ransa yana
jin babu dadi da kuma hangen me zai faru idan gaskiya tayi halinta.


Sai bayan magariba Radhiya ta dora girkin da Tante tace tayiwa Awwab Emzee da
Ibrahim suka zo dauka. Farar shinkafa ta dafa masa tayi shar da ita sai dai baifi
minti biyu ya rage ta kwashe ba ta juye mata alayyahu madaidaici a ciki. Gyareshi
tayi amma bata yayyanka ba a haka tayi amfani dashi bayan ta cire shi. Ba kuma
tsigar nan ta ganye kawai ba, ta hada ne harda itacen inda yayi karfi da yawa kadai
take yankewa. Yau dai tayi kamar na mutum biyar ne tunda tasan su Yousuf na gidan.
Miyar kuwa farfesun kaza ne da ta barshi ya danyi kauri an yanka dankali amma da
girmansa a ciki da caras shima da dan girma sai koren wake. Rahima, Zayyana da
Hibbah suna makale wurin koyon girki tayi ta gama. Sai da ta dibar musu suka sama
mata lafiya. Ibrahim ne ya fara zuwa kitchen din yace Zayyana tazo ta bashi labarin
Khaleel.


Radhiya da bata gano komai ba tace "ashe dai zatona ya zama gaske da nake tunanin
ko saurayinta ne kusan kullum sai ya kirata sai ta gudu don kada muji me ake cewa"


Kashewa Zayyana ido yayi da take ta jin kunya Hibbah da Rahima sun san komai shiru
kawai suke yi "zan binciko mana shi Adda Amarya muna zuwa"


Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa Radhiya
tambayoyi suna tsaye ita da Hibbah ita kuma tana wanke kwanukan da ta bata Emzee ya
shigo. Bata ganshi ba sai alama ya yiwa Rahima da suyi shiru. Ido ya rufe mata ta
baya sai dai jini baya buya tuni ta gano rabin jikinta ne Zayyan dan Zayyan.
Rungume juna suka yi tana ihun murna don har ta fitar da ran zai zo saboda tasan
tsananin makarantarsu.


Ya wani kara budewa ya kereta tsaho sosai yana mata dariya ya dan duku kansa "ashe
nayi missing dinki Addata yau gaskiya kwanan hira zamuyi kafin Hamma ya daukeki, na
fasa bin Ibrahim ma"


"Ka manta ko an daura ina gida har sati biyu?"


"Eh to idan ya bani damar hirar kenan. Muje dakina kiga wani abu"


Suna juyawa Hibba tace "Ya Emzee ina wuni"
"Lafiya kalau mai tale baki number two"


Dariya tayi za ta fita taji Rahima tayi mata wani irin riko tabi bayanta da sauri.
Radhiya tayi saurin cewa Emzee ga Rahima tana dakatar da ita su gaisa.


Haba Rahima idanu tuni sun raina fata ashe tunda ya shigo ta tabbatar shine sojan
taji cikinta ya kulle saboda girmansa da ta gani. Sai yanzu ya kula da ita a
zatonsa 'yar uwar Hibbah ce ko wata dai cikin bakin biki ya saki fuska zai amsa
gaisuwar da tayi masa a tsorace suka hada ido. Wani irin yanayi ne da bai taba zato
ko tsammani ba ya fizge shi a take a lokacin ya fadada murmushinsa gareta yanayin
idanunta tamkar wani maganadisu ya zame masa.


"Kinyi kama da matsorata, yaya sunanki?" Ya tambayeta a kasalance.


Yawu ta hadiya tace "Rahima"


"Rahima zaki zama kawar soja?" ya sami kansa da cewa babu wani tunani.


Duka Radhiya ta kai masa a baya ganin idanun Rahiman sun kara girma duk ta firgice
"kada ka tsorata min kanwa dama har yanzu bata sakewa idan Daada ya shigo."


Tana ganin Radhiya ta dauke masa hankali ta fita da sauri ta riga Hibbah zuwa daki.
Sai da ta rufe kofa ta soma sauke numfashi da sauri da sauri. Tunda take bata taba
ji ko ganin wani abu da ya kwashe mata nutsuwa kamar wannan bawan Allah ba.
Danganta abin tayi da tsoron sojoji da take yi ta kai hannunta kirji tana jin yadda
zuciyarta ke bugawa.


A kasa kuwa kafin su bar kitchen din Ibrahim ya shigo yana kiran Emzee dreban da
zai dauko Awwab motar ta lalace a hanya Raji kuma da yake gida bai san gari ba
shine Ummi tace suje su dauko shi. Shi dai Emzee so yayi ya zauna a kira masa
yarinyar nan mai idanu bai gaji da kallonta ba.


Da abincin da Radhiya tayi a motar suka je dauko shi. Ibrahim kasa hakuri yayi sai
da yace masa yayi jiki saboda aikin nasa yafi yawa a zaune gashi babu inda yake
zuwa daga gidan da ake basu kamar hostel idan baka da ra'ayin kama wani ko kana da
naka sai office din nasu. Murmushi kawai yake yi yana jin kewar Radhiya amma dare
yayi ana neman shabiyu gashi jirgin safe zasu bi zuwa Jos saboda karfe biyu ne
auren kuma suna tare da ango. Wanka kawai yayi da sallah yaci abincin nan sosai
tare dasu Raji suka kwanta a gajiye bayan ya tura mata text din godiya tunda taki
daukar wayar tasa. Ya dena damuwa don ya ma fi son haduwarsu ta gaba da amsa sunan
matar Awwab.


Da safe kuwa ba a nutse suke ba anata shiri. Duka kayan da zasu saka na daurin
auren a jaka suka saka su. Suka wuce airport mota mota sai Jos. Karfe biyu da 'yan
mintuna bayan sallar azahar Major General Zayyan Tureta ya karbi sadakin Arifah
daga hannun kanin Alh Mousa naira dubu dari da dalleliyar mota. Nan da nan jama'a
suka shaida auren Yousuf da Arifa abinda wata uku da suka wuce ko sanin juna basuyi
ba bare suyi tunanin wannan rana. His Excellency the Executive Governor of Plateau
state Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ya tara jama'a sosai 'yan siyasa manya a wannan
taro mai dumbin tarihi. Ansha hotuna a ranar biyar na yamma suka sake dagewa sai
Birnin Shehu. Ga gajiya an dauko ga wata za'a sake dauka gobe.


Hotel da wani guest inn Zayyan yasa yayunsa kama dakuna da dama saboda yayi mamakin
jama'ar da suka zo wannan aure. Da wuri ya biya kudin masaukin saboda haka basu
sami wata matsala ba. Mutanen Katsina gayya guda sai kayi mamaki kamar ba su bane
masu cewa dole Awwab ya auri 'yar uwarsa don duka kakanin Awwab sunzo su ukun.
Malamijo da 'ya'yansa maza kananun ne kadai babu amma ya dauko kowa ga kannensa
suma motoci suka ciko da mijin Nene. Ga jama'a guda daga Nijar wadanda suka halarci
auren Yousuf jiya. Daga Rugar Barkindo Ardo, Baffa Gide, Baffa Habubakari da su
Zakari kusan kowa yazo shaida auren 'yar soja. Mutanen Tureta da su Alh Salisu da
duk wanda ya kamata sun zo. Chibuzor dashi aka daura na Arifah kuma yau ma yana
tare da babansa Zayyan shima zai shaida. Karfe goma na safe aka saka saboda masu
komawa a ranar su iya tafiya. Kusan ma dai kowa juyawa zaiyi suna sa ran da an
daura anci abinci a fara tafiya.


Zuwa lokacin Zayyan ya ciko sosai don Mairamansa ba da wasa ta tasarma fito da
mijin nata ba. A babban masallacin juma'ar unguwarsu da yake bakin titi za'a daura
auren. Wata hadaddiyar mota ce ta tsaya a harabar masallacin sojoji suka yi dafifin
kare shugabansu. Mutum uku ne suka fito daga motar wata shadda suka saka iri daya
ruwan zuma mai dan karen tsada. Dinkinsu da komai hatta hula da takalmi basu
bambanta ba. Suna fitowa aka fara daukarsu a hotuna tun kafin su karasa ciki. Uban
gayya ne Major General Zayyanun dan mutan Sakkwato yana ta murmushi kamar shine
angon. Har yau da yake shirin aurar da 'ya bai dena tafiya da hankulan mata ba.
Daga gabansa rike da wata sanda mai kyau domin samun balance din jiki Daddy Rtd
Major Mustapha ne mutumin Katsinan Dikko kunya gareku ba tsoro ba. Kamilin mutum
msi tafiyar da komai cikin tsari da haiba. A bangaren damansa kuwa aminin kwarai ne
wanda abotarsu ta zame musu 'yan uwantaka Rtd Lt Hadir gaisuwarsa daban take
jinjina ga dan mutan Kanon Dabo mai dutsen Dala da Gwauron dutse, Kano ko da me
kazo an fika. Hadir Murtala abokin da Zayyan Tureta wadanda sukayi zamani a
matsayin zaratan jaruman samari kyawawa. Su ukun nan tarihin rayuwarsu abin duba ne
domin kada duniya ta manta da soyayyarsu da sadaukarwa domin kasarsu domin
abotarsu. Taku suke maza 'yan uwansu na waigensu domin sun isa a dube su din. Cikin
masallacin suka shige ana ta gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.


Daga waje mintuna kadan bayan shigewarsu wata motar ta iso Awwab ya fito rike da
waya a hannunsa yana sanye da shadda fara kal wadda aka yiwa aiki da zare ruwan
toka msi duhu. Hula da takalminsa kalarsu daya da zaren sai agogo da links din
hannun rigar duka silver masu kyau. Saboda kurewar lokaci ranar da zai taho yayi
aski saisaye aka yi masa wani irin gyaran fuska da ya fito da gajeren kwata miliyon
dinsa. Matashi ne ajin farko mai tattare da nutsuwa da kamala. Kallo daya za ka yi
masa kasan cewa yau din ta dabance a wurinsa ranar aurensa da Alheran dinsa. A
gefensa angon jiya ne Yousuf bayansu kuma Emzee da Ibrahim sanye da wani ubansun
yadi da Mama ta dinka musu. Su dinma kamar iyayensu daga sama wato hula har takalmi
babu ta inda su ka bambanta komai. A tare dasu Halifa ne shima ya fito fiye da
zato.


A cikin masallacin kuwa wakilan ango da amarya aka nema Hadir da Zayyan su ka matso
gaban limanin suka zauna a kusa dashi. Yadda yake a tsarin musulunci haka aka
gabatar da komai inda Hadir waliyin amarya ya karbi sadakinta naira dubu dari daga
hannun Zayyan waliyin ango. Addu'a aka yi aka shafa Captain Muhammad Awwab Mustapha
ya zama mijin Alheran Radhiya Zayyan Tureta.
Hamdala ya rinka yi babu tsayawa a lokacin da yaji kammaluwar komai Schatzi dinsa
ta zama tasa halak malak. Hotuna ake ta yi da gaishe gaishe na 'yan uwa da abokan
iyayensu. Malamijo da tawagarsa kadai sun isa gayya. Gidansu Zayyan aka wuce ya
sakarwa 'yan uwansa da matansu Badaru ragamar girkin da za'a ciyar da mutane kafin
su tafi. Da farko Mairama yaso su zo su kwana a garin domin yin abincin ita kuma
tace dama ce ta nuna musu yana kaunarsu kuma ya yarda dasu. Ai kuwa basu bashi
kunya ba domin kowa yaci ya sha anyi abu cikin girma. Kuma sai da Baban Arifah ya
samu yazo shima duk da mutanen da ya baro a gida. Maikudi ne dai idan akwai namijin
mujiya to shi ne a wannan taron. Yana ta rakubewa a gefe Zayyan sai ya dauke kansa
kawai. Daga baya ya ga bai da amfani nunawa duniya akwai baraka tsakaninsu shiyasa
ya koma sako shi cikin al'amuran. Da yace Maikudi kuwa sai ka ganshi da mugun sauri
ya taho.


Ba su suka sami saukin kebewa daga mutane ba sai lokacin da ya idar da sallar
la'asar. Yana zaune da 'yar cikinsa ya ajiye babbar rigar da hula can gefe. Bayan
doguwar addu'a ya dauko wayarsa ya turawa Radhiya text din da yake ta son yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login