Showing 75001 words to 78000 words out of 295847 words

Chapter 26 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

Bakin mota suka firfito
Mami da Ummi zasu bi karamar motar sauran kowa yace bus din da Awwab zai tuka zasu
shiga. Radhiya da jikinta yayi sanyi tana jin babu dadi akan maganar da tayi tace
ita ma motarsu zata shiga sai ta zauna a gaba.


"Koma cikin 'yan uwanki Radhiya" Zainab tace tana turata bakin daya motar.


Awwab ta kalla ko zaiyi magana sai ta kula hirarsa kawai yake yi da Ghazalatu.
Juyowa yayi ya kalli Radhiya duk ta zama wata salihar karfi da yaji "ina zuwa" ya
cewa Ghazalatu ya taho inda take tsaye a jikin motar.


"Zo in nuna miki wani abu"


"Wai ba fushi kayi da abinda nace ba kake yi min magana"


Murmushi yayi "Silly girl, kawai sai nayi fushi bayan nasan ta kusa kare miki
kwanannan...auren dreba ba fashi"


"Shine ka barni inata damuwa, kuma a gaba zan zauna inyi ta ganinka tunda yau zaku
dawo"


Wurin wata katuwar fulawa inda Ghazalatu ke tsaye suka nufa. Suna jiran iyayensu su
gama maganar da suke yi su dau hanya ne shiyasa basu tafi ba.


"Dama babu mai zama wurinki ne nima inyi ta kallonki"


Dariya tayi fuskar Ghazalatu ta hade tsaf da kishi. Awwab yasan me yake bata mata
rai don yanzu ta gama fada masa ita bata son yadda yake yiwa Alheran dinnan bayan
ba karamar yarinya bace. Domin ya kwantar mata da hankali yaje ya kira ta.


"My G, ga Alheran kanwata. Alheran ga Ghazalatu kanwata kuma matar da zan aura"


Sai yanzu hankalin Ghazalatu ya kwanta sosai. Ta kurawa Radhiya ido sai ta ga
yarinyar ko a jikinta sai ma dariyar ta take yi fuskarta ta tana wani annuri.


Dage girrarta duka biyun ta rinka yi yadda ta saba idan zata yi tsokana

" Eyye eyye Hamma shine kace zanyi aiki a gidanka? Naji zan rinka tayata indai
itace matar"


"Bana bukatar house girl so kiyi zamanki" Ghazalatu tace tana shan kamshi.


Fuskar Awwab kadai zaka kalla kasan kalaman basuyi masa ba.


"House girl?" Yace yana kankance idanu.


Ta fuskanci ransa ne ya baci sai ta wayance "naji kace za tayi min aiki ne dazu"


"Lallai wannan 'yar wulakanci ce" Radhiya tace a ranta. Ita bata san maganar wasa
bane da zata yi tunanin da gaske aiki zata je yi mata. Hamma Awwab yafi karfin
komai a wurinta tunda yake son Umminta da babanta da ita kanta. Kuma ba wani abu
bane a wurinta ta taya matarsa aiki amma wallahi ba dai taje a house girl ba. Idan
bata gwaba mata magana ko yaya bane tasan bazata ji dadi ba shiyasa ta ajiye katon
murmushi a fuskarta tace "ko babu albashi zanyi miki aikin ma, kinsan mu 'yan kauye
bamu san komai ba sai bautawa 'yan birni"


"No ki barshi fa bana bukata, idan ina so Yayana zai nemo min"


" Yes dai inzo inyi ko babu komai zan hutar da Hammana barnar kudi"


Hannuwansa ya zuba a aljihu yana kallon ikon Allah. Rigima ke neman tashi
tsakaninsu daga su gaisa.


Daure fuska yayi yace "ku wuce ku shiga mu tafi"


Suna zuwa bakin motar Ibrahim zai bude gaba ya shiga saboda yana son Awwab ya koya
masa tuki Ghazalatu ta riga shi budewa itama tana son zama kusa da masoyinta.
Radhiya da ta fisu iyawa tayi sauri ta shige ta kofar bayan ta haura gaba. Awwab
kansa sai ganinta yayi ta kusa fado masa garin sauri. Gyara zamanta tayi ta ballawa
Ghazalatu da Ibrahim harara suna tsaye suna kallon abinda tayi.


"Ni dama ga wurina can kusa da Zeezee" Ibrahim yace yana shiga bayan inda Emzee ke
yi masa dariya.


Ghazalatu ta kalli Awwab tana jira yayi magana "kace ta koma baya ina son muyi
magana"


"Idan muna dawowa sai ki zauna a nan din kinji."


Tsabar bakinciki ji tayi kamar tasa ihu. Mami daga cikin tasu motar tace ta shiga
su tafi rana tana kara yi. Hararar Radhiya tayi ita kuma tayi mata gwalo.


"Bansan mutum nayi ba sai naji a jikina"


"Alheran" taji yace muryarsa a dake sannan ya kalli Ghazalatu da take ta cika tana
batsewa "ki shiga ki zauna mu tafi"


Daurewar da yayi yasa ta shige ba don ta hakura ba. Radhiya da take kusa dashi kuwa
ji tayi kamar ta koma baya ita ma. Tukinsa kawai yake yi wanda baya masa dadi
saboda bin bayan Abdallah da dole sai yayi tunda bai san hanya ba.


Motar duk sai tayi musu shiru mai bakin tsoro ya hanata magana Zayyana har ta soma
gyangyadi a jikin Zahra. Su basu ma san me yake faruwa ba sai Ibrahim da yake
tunanin saboda zaman gaba ne kawai.


Can dai taji shirun ya isheta ta dago a hankali ta saci kallonsa. Titi dai yake
kallo har yanzu babu wannan sakin fuskar.
"Hamma" Radhiya ta kira sunansa a tausashe.


"Kar ki dameni please"


Shiru tayi ran sojoji ya baci. Ita kadai zaiyi fushi da ita bai ji masoyiyar tasa
tana kiranta housegirl ba. Tura baki tayi ta juya duk jikinta tana kallon waje.
Shima satar kallonta yayi yayi gajeren murmushi. Da gaske dai Alheran dinsa bata
chanja ba sai ma abinda yayi gaba. Su mata abin rigima baya yi musu kadan ya kula.
Su biyun kowa matsayinta daban to me ya kawo rigimar. Ko don Ghazalatu tace mata
house girl? Shima kalmar bata yi masa dadi ba. Duka su biyun sai yayi aikin basu
hakuri kenan. Haka kawai zasu tayar masa da hankali kamar wasu kishiyoyi. Ta mudubi
ya hango Ghazalatu ita ma fuska babu wakwala kamar ma kuka take shirin yi. A take
ya jinjinawa masu mata biyu.
[02/11 7:31 AM] My 2nd Mtn: 27. Sun isa Sumaila karfe biyu na rana a gajiye saboda
tashin wuri da suka yi. Emzee ne ya koma jagora da suka shigo garin shiyasa tasu
motar take gaba. Awwab ba tsayawa Emzee din ya fita da sauri saboda magana da yake
son yi wa Ummin tasu. Gefe ya ja ta ana kokarin fitowa da kayan da ita kanta bata
san da zamansu ba a boot.


"Ummi wai kuwa sun san zamu zo da baki?" Yace yana rage murya.


"Na fadawa Innawuro da ta kira nace ta sanar dasu tunda kaga ba waya gareni ba.
Menene?"


Da damuwa a fuskarsa yace "kada muje a rasa abinda za'a basu nasan bazaki ji dadi
ba"


Murmushi Mairama tayi. Zayyan dinta akwai hankali da nutsuwa ga zurfin tunani.
Rashin abin tarbar baki tabbas zai iya faruwa don tasan halin gidan nasu "to yanzu
me ya kamata ayi?"


"Idan kina da kudi kawo naje na siyo gurasa da tsire kawai"


Karamar jakarta ta mika masa. Dubu uku ya cire cikin kudin da Ardo ya bata ne da
zasu taho. Ya tafi tana ta masa addu'a a zuciyarta.


Radhiya kuma ta kama kofa za ta bude Awwab ya danna central lock. A zuciye ta juyo
"bude min"


"Ko nima balotellin zaki yi min ne? Zai fi miki sauki akan wannan juya idanun"
bayansa ya juya "Ghazalatu zauna magana zamuyi"


Murtuke fuska tayi itama ya kallesu ya tabe baki. Mata, mata halinku sai ku.


Su Zayyana duk sun fita sun bi bayan iyayensu cikin gidan. Basu san me yasa ya
tsayar da su Radhiya ba amma ko ma meye tabbas basu ga alamun wasa a tare da yayan
nasu ba.


"Kun gama fushin ko har yanzu da saura?"


Ghazalatu dama jira take yi "don na biyoka shine zaka wulakantani akan wannan
yarinyar kamar wata kishiyata? Tunda muka zo sai kayi mata magana sau uku baka yi
min daya ba. Sannan nazo shiga gaba ta shige duka ka kyaleta. Idan wani abu ne
tsakaninku gara ka fada min da wuri na san matsayina. Amma bazai yiwu ta rinka jin
kanta kamar wata a wurinka ba tana neman shiga tsakaninmu"


"Kin gama? To bari kiji in fada miki. Alheran wata ce a wurina Ghazalatu kuma bazan
yarda kici mata mutumci ba. She is my sister kamar yadda na dauki su Zahra haka ita
ma na dauketa. Idan ma kishi zakiyi ba da ita zakiyi ba. Ki bari sai kin hadu da
wadda take da matsayi irin naki a wurina"


Dazu gani take wannan Ghazalatun take ko wa tayi mata rashin mutumci amma maganar
Awwab ta yanzu tafi kona mata rai akan komai duk da cewa gaskiya ce ya fada. Ita
din kanwa take a wurinsa amma meyasa kalaman nasa suka yi mata zafi haka.

Daga haduwa dashi kwana daya kawai take neman matsayi fiye da abinda zai iya bata.
To me ma take nema ta tambayi zuciyarta. Ranta taji ya cunkushe gabadaya taji ta
tsani zaman da take yi tare dasu a motar. Dago kai tayi kamar ba ita bace zuciyarta
take kai kawo a abinda ta kasa gane zahirinsa ta kalli Ghazalatu.


"Matar Hamma kiyi hakuri don Allah. Haushi naji da kika kirani house girl. Ke da
kishiya sai dai mota in sha Allahu"


Awwab kallonta yayi yadda ta nutsu tana magana kamar ba ita ba. Suka hada ido tayi
masa wani murmushi da ya tsaya masa a rai yaji kamar ya dora hannunsa a kumatunta
da ya lotsa.


"Kaima kayi hakuri bazan kara ba"


Tana kaiwa nan ta kama kofar zata bude sai ya cire lock din ta fita tare da duka
tunaninsa kamar ta zare masa duk wani kuzari da yake jikinsa. A katon soron gidan
ta ya da zango jikin wani dan tudun siminti da akayi domin zama. Abinda ya bata
mamaki bai wuce kukan da ta fashe dashi sosai ba. Ji take idan bata yi ba ma
zuciyarta zata iya bugawa. Kukan na meye? Oho, itama bata sani ba. Abu daya ne
kawai ya tsaya mata a rai kalmomin Hammanta na karshe wai Ghazalatu ta jira sai ta
hadu da mai matsayi irin nata a wurinsa sannan tayi kishi. Tsaki taja tana jan
hanci "Mtswwww in kun ga dama ku cinye juna karewarta, aikin banza. Dadinta dai
nima Kawu Zakari ina komawa zai ce yana sona. Mu za'a yiwa burga da wata soyayya?
Maza na fita filin yaki ko su je ceton rai a asibiti kai ka makale a jirgin sama
kamar tsuntsu wa zai so ka idan ba wannan mai kwalakwalan idanun ba dama"


Hannu tasa ta share hawayenta bayan ta gama rarrashin kanta ta shiga gidan da
sallama. A can mota kuwa Awwab da Ghazalatu an bude sabon shafi sai dai a wurinsa
babu wannan dokin jikinsa kamar wanda aka yiwa duka haka yake ji. Su ma tana shiga
suna shigowa.
Tabarmi ne aka shimfida daga can gefe inda inuwa take don dakunan gidan babu mai
girman da zasu zauna a wadace da su da kuma tawagar Malamijo da suka zo kallon 'yan
gayu. Akan abin sallah yake zaune ya mike kafafu dawowarsu kenan daga asibiti an
zuke fitsarin an hadosu da tulin magunguna. Sallamar baki yasa aka kawo masa babbar
riga ya saka ya rufe kasusuwan kirjinsa.


Radhiya ya hango zai fara tsokanarta sai da ta matso ya kula idanunta sunyi ja
sosai.


"Kukan me kika yi ke kuma?"


Kamshin turaren Awwab kawai ta ji a bayanta ta gane ya shigo shima. Gashi ana ta
kallonta idanunta sunyi ja haka saman hancinta.


"Ji nayi kamar ana kuka ance ka tafi shine na fara nawa nima. Ashe ashe kana nan."


"Kaniyarki" Malamijo yace ya yi mata dakuwa "Mairama ki rasa da wa zaki zo gidan
nan sai da wannan aljanar 'yar taki, ko wancan hutun da kika turo su ni banji dadin
zama da ita ba. Sau biyu tana yi min barna a gona"


Awwab sam hankalinsa kasa kwanciya yayi da aka ce tayi kuka. Bayan ya gaisa da
mutanen gidan da suke wurin fuskarta ya rinka lalube yana son hada ido da ita amma
fafur taki. Baya so ya zama sanadin kukanta ko kadan. Muryarta ya tsinkaya tana
cewa "wai me ya sameka ne Malamijo, ciwon me kake?"


Hajjo ta soma dariya za ta tona masa asiri a gaban 'yan gayu yayi saurin cewa
"zazzabi ne mai zafi ya damkeni kamar bazan kai labari ba. Ai naci wahala ba kadan
ba. Yanzu ma daga asibiti nake"


Sannu da adduar samun sauki suka yi masa. Yadikko ta soma cigiyar Emzee shine
Mairama tace ya tafi sayen gurasa da tsire wai yana sha'awa. Hakanan Malamijo ya
tsargu ya daure ya cije yace a kira guda cikin samarin gidan ya yanka kaji uku ayi
musu farfesu.


Mami ce tace " Kada ka damu Baba muna sallah zamu juya akwai tafiya a gabanmu.
Ibrahim idan Karami ya dawo ku shigo da kayan nan ciki"


Nan fa hankalinsa ya tattara yayi waje. Ba dadewa Emzee ya dawo da ledoji a hannu.
Ya sayo gurasar da nama a wadace harda lemuka irin su cway, lacasera da maltina
masu sanyi. Ashe 'yan matan yunwa suke ji. Kafin Hajjo ta gama dafa shinkafar da
Malamijo ya aunar mata bayan ya koma daki daga buhu daya cikin wanda su Mami suka
kawo don kwarewa a tsiya har sun koshi.


Sallah kasaru suka gabatar azahar da la'asar sannan suka ce zasu koma. Idan sun isa
da wuri ma Katsina zasu wuce kawai saboda kada su yiwa Zainab yawa a gida.
Da sauri Radhiya ta dago kai rike da gurasa a hannu sai lokacin take ci ta kalli
Awwab. Hada ido su ka yi shima tun dazu ita yake kallo. Kin kula shi da take yi
shine yake damunsa. Kwana biyar Mairama tace zasuyi a nan sannan su wuce Rugar
Barkindo. Sai bikin su Zahra ya rage sati daya zasu koma Katsina.


"Wannan dan samarin baici komai ba zaku tafi. Radhiya ko saurayinki ne kika kawo
baki gabatar min dashi ba?"

Malamijo yace yana kallon Awwab. Yaron da gani akwai maiko maiko zai so ya auri
jikar tasa.


Murguda baki tayi da ta ga Ghazalatu ta sha kunu "idan ma kishi kake yi to ka dena
Malamijo, ka jira sai na sami mai matsayi daidai da naka amma ba wannan ba."


Yanzu ya gano bakin zaren. Da gaske maganarsa ce ta bata mata rai harda kuka don
sai da ya gano ja da kankancewar da idanun nata suka yi. Da ya juya kalaman a
bakinsu sai ya ga rashin dacewarsu a dazun.


Mami haka nan ta fara zargin ko Awwab din ya yiwa Radhiya wani abin ne ya bata mata
rai. Bazasu so ayi aure basa son juna ba. 'Yar dabarar manya ta kirkiro wadda bata
baude da yanayin Awwab din ba a yadda ta san shi "haka yake baya son cin abinci, ga
tuki a gabansa mai nisa"


"Ke zuba masa abinci ki kai masa wajen soro tunda babu kowa a wurin. Kila kunya
yake ji ko dan Ummi" Mairama tace tana murmushi.


Hakan yayi masa daidai har ransa. Abincin da Hajjo ta dafa da wanda Emzee ya siyo
ta zuba masa a plates biyu ta dora akan tray tayi gaba batare da tayi masa magana
ba. Ghazalatu kamar ta bisu sai ta tuna bayan fitarta dazu daga motar yadda ya
jaddada mata son da yake mata. Tayi ta gama iyayinta ta koma kauyensu kowa ma ya
huta.


Wurin yana da fadi daga kan tudun dazu ta ajiye abincin ta koma daukar tabarma suka
yi kicibus. Wai sai tayi masa murmushi a zuwan komai lafiya shima ya maida mata. Da
ta kawo tabarmar yana zaune a gefen abincin ta shimfida ta sauke masa a kasa.


"Hamma sauko kaci kada kuyi dare"


Kura mata idanu yayi sai da taji kallon ya hanata motsi sannan ya sauko ya zauna a
kan tabarmar ya tankwashe kafafunsa.


"Zauna mu ci"


"Na koshi"


"Ban isa da ke ba ko?" Taji yace a hankali yana daukar cokali.
Bata so yana magana irin haka sai ta taji zuciyarta tayi wani iri. Zama tayi a daya
bangaren tray din ta tankwashe kafa yadda yayi. Cokali daya ne a ciki ya debi
abincin yaci ya mika mata. Satar kallonsa tayi ya dage mata gira da ido yayi mata
nuni da taci. Sai da ta sauke numfashi tana kunyar wannan abu ta rufe ido taci da
cokalin da ya fito daga bakin Hamma Awwab.


Karba yayi ya sake ci ya kuma mika mata. Za tayi magana yasa hannunsa a kan lebensa
sai ta hakura. Duk loma daya sai ya mika mata har suka cinye abincin gabadaya.


"Wannan gurasar dai bani da inda zan cusa ta ki mayar ciki"


Dama ta kagu ta tashi ta kinkimi tray din za ta gudu ya danne gefensa.


"Ban gama magana ba"


Komawa tayi ta zauna ba don taso ba taji yace "I am sorry Alheran. Nazo ina ta yi
miki laifi ba da niyya ba"


Sake karyar mata da zuciya maganarsa tayi. Shi kam bashi da girman kai. Wai ita
dinnan kanwar bayansa 'yar kauye yake bawa hakuri.


"An daure harshen ne? Talk"


Rufe ido tayi sai hawaye sharrr kamar famfo. Ta rasa gane irin emotions din da suke
yawo a zuciyarta yau dinnan.


Hankali a tashe yace "Ya Allah, me nayi miki kuma?"


"Nima ban sani ba Hamma" tace tana kara fashewa da wani kukan. Me ya sami zuciyarta
ne a cikin kankanin lokaci? Rabonta da kuka tun farkon zuwan su Mami rugarsu da ana
bada labarin abinda kawunsu Maikudi yayi.


Kuka tayi harda shessheka Awwab bai hanata ba har ta gama don kanta ya bata tissue
irin ya ledar nan karama ta goge idanunta.


"Feeling better?"


Ta gyada kai tana kallon kwanukan gabanta.


"Good, yanzu ki fada min tsakani da Allah me ya same ki? Nine ko?"


Rasa me za ta ce masa tayi ta kare da cewa "ba kaine kake murna zaka tafi ba"
"Ke kuma ba kya so na tafi?"


Kada fa ya fassarata ta soma tunani "dena fada kada budurwarka taji. Duk baka
tambayeni labarin komai nawa ba zaka koma kila bazan kuma ganinka ba sai an dade.
Shine naji raina ya baci"


"Sai nake ji kamar dai maganata ta dazu ce ta baki haushi. Amma nima bana son
tafiyar ko sabawa bamu gama yi ba ko" yayi yar dariya.


"Eh, ko askina ban fada maka me yasa akayi min ba"


Sai da yayi dariya sosai yace "an gaya miki ni bana tsoron kiyi min balotellin ne?
Ina sane naki tambaya kada na janyowa kaina"


"Ashe kai matsoraci ne" ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.


Sweet ya dauko daga aljihunsa irin mai mint dinnan ya bare ya jefa a baki yana
dariyar matsoracin da ta kira shi.


"Dazu ka raba abin leda baka bani ba yanzu ma a gabana ka shanye alawar? Kuma nice
karama ni ya kamata ka bawa"


"Sorry gashi in kina so" ya cirota daga bakinsa dama niyyarsa kenan.


Wata zuciyar tana kwabarta wata tana ingizata har ta mika hannu tayi saurin janyewa
"wayo zaka yi min, na tuna me kace dazu"


"Ke dai kina kyankyamin abin bakina kawai"


"Haba dai..." bata rufe bakin ba ya saka mata sauran da ya rage har hannunsa yana
taba lebenta. Saurin tashi tsaye yayi ita kuwa ta rasa me zata yi ma.


"Ki rage min kinga kadan na sha"


Lumshe ido tayi tana tsotsar alawar yana kallon yadda bakinta yake motsawa yana jin
kamar ya taya shi. Girgiza kai yayi da sauri. Lafiyata kalau kuwa ya tambayi kansa.


"Ahhhh" Radhiya tace ta bude bakin ta mike tsaye yadda zai gano cikin bakin nata
sosai. Ta shanye alawar saura yar kadan.


"Cewa nayi ki rage min fa"
"Nima bata isheni ba. Babu kari?"


"Zan gamu dake ne, muje ciki su fito bana jin zamu iya wucewa a yau sai dai mu
kwana a Kano" tafiya ciki ya soma yi.


"Hamma gashi" ya juyo ta miko masa yar karamar sweet din ya karba yana kallon cikin
kwayar idonunta ya saka a bakinsa. Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login