Showing 123001 words to 126000 words out of 295847 words

Chapter 42 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

sun kare a universities
ki rasa abin zaba sai soja."


"To, to ni ba so nake na gaji su Daddy ba. Kuma Babana ma ai 'Yar soja yake ce min"


" 'Yar soja da Soja daya ne a garinku. Ki cire wannan tunanin a ranki da kaina zan
zabar miki course. Kin ci SSCE din dai ko"
Kumbura baki tayi cikin fushi "naci"


"Bayan bikina gida na zaki koma sai kiyi karatun a Abuja. Gara ku fara shiri da
Ghazalatu tun yanzu kada na fita watarana ku tayar min da gida"


"Ha'ann lallai ma Hamma ni bazan yi auren ba har sai kayi na dawo gidanka?" Ya ma
za'ayi yace haka. To zaman me zata yi musu idan ba housegirl din da Ghazalatu ta
kirata ba.


"Ashe aure kike so, gara da kika fada min"


Hannu tasa ta rufe fuska wai ita kunya "kai Hamma to ai kaine wai na koma gidanka
nayi karatu...shi kuma abin sai yaushe?"


"You must be kidding"


"Me kenan ka ke nufi?"


Dariyar da baiyi niya ba ce ta biyo bayan tambayar ta ta. Yarinya 'yar shekara goma
sha tara ke zancen aure. Karatu yake da burin tayi mai zurfi kafin maganar aure. Da
kyar ya daidaita kansa bayan ya hango irin kallon da Ghazalatu take jefo masa.


"Okay, seriously kina da wanda yake sonki ne?"


Sama ta kalla kamar me tunani "akwai Kawu Zakari sai na koma gida zai gabatar da
kansa sosai"


Ransa yaji ya soma baci to amma yanayin maganarta ke bashi dariya "zai gabatar da
kansa wurin su Ummi?"


Innocently tace "a wurina dai, ai bai riga yace min I love you din ba"


"Ya Allah" Awwab yace dariya na sake kama shi sosai.


"Don na fada da turanci kake dariya?" Ita bata ga me tayi ba daidai ba. Wato shi
yayi aure ita kuma ya hanata cikar burinta na zama soja sannan bazai barta tayi
auren ba ita ma sai kace wata alhudahuda zai rinka kira mata karatu.


Sai da yayi dariya mai isarsa ya fadi abinda yaje mata a bazata "Allah Ka bani
Alheran Radhiya" yana kallon kwayar idonta.


Wani irin abu ne ya fizgi zuciyarta zuwa gareshi a daidai lokacin taji farinciki ya
saukar mata irin wanda bata taba ji ba. A nasa bangaren sai da maganar ta fito ya
fahimci nauyinta. Maganar zuci ne ta fito fili. Sai dai kuma shi ya sani cewa
zuciyarsa bata raya masa karya ba haka nan bakinsa bai fadi karya ba. Haduwar kwana
daya jinta yake kamar basu taba rabuwa ba. Zuciyarsa ta ginu da son wannan yarinyar
tun tana cikin mahaifiyarta. Tsayin shekaru bai sa ya manta da ita ba. Ya cigaba da
rainonta a zuciyarsa har zuwa haduwarsu ta jiya a inda yadda ta koma ya sake
kayatar da ruhinsa zuwa gareta. Da kwalkwalin kan, shirme, shiririta da fada duk
yaji ya dauka yana son abarsa a haka.


Dena kallonsa tayi don duk abinta bata da rashin kunyar da zata iya jurewa kallon
da yake yi mata.


"Ehemmmm ga ruwa ga sabulu a ina zan ajiye?"


Aikin Emzee ne da tun kafin su karaso ya hangosu suna magana. Allah Yasa Ibrahim da
Zayyana sunyi wajen wata tinkiya da take haihuwa ya taho wurinsu shi kadai da ledar
purewater da sabulu.


Kumatun Radhiya har wani ja yayi don tsabar kunya ta tashi da saurinta zata gudu.


"Da fuskar taki mai warin maza zaki shiga cikin mutane? Dawo ki wanke"


Emzee bai yi wata wata ba ya arce daga wurin. Ya kamata su Ummi su farga da wuri
kafin a laluba a nemesu a rasa.


Sabulun ya bata ya farke ledar purewater din ya dauko daya "fara wanke wannan
hannun"


Durkusawa yayi a gabanta tana cuda hannuwan yana zuba mata ruwa har ta gama
wankewa.


"Saura fuska" yace mata. Sabulun ta sake sakawa ta dage hijab din ta soma cuda
fuskarta ya duku gab da ita "wai nan kunya na baki ne kika kasa magana? Kowa yasan
Alheran ta Awwab ce baki da wurin zama sai gidansa"


Kirjinta ne ya soma dukan uku uku ta kasa karasa wanke fuskar ya kuma cewa "cire
hannunki in wanke miki"


"Me din?" Tace tare da bude idanun ta da sauri tana matsawa kada yaje ya taba ta.
Ai kuwa kumfar sabulun ta shige duka idanun biyu ta soma ihu tana tsalle sai da su
Fauziyya suka taho garesu da sauri.


"Kinji dadi kin tara min mutane"


"Ka dena min mita ka hure min idona...wayyo yaji"
Su Fauziyya sun kusa karasowa kuma baya son kowa a tare dasu yanzun da yake shirin
daukan duka makaman yakinsa ya nemi daidaitawa da kanwarsa.


"To cire hannun mana"


"Naki wani ne zai shiga"


A daidai nan Fauziyya ta fara zuwa gabanta ya mika mata wani ruwan ta zuba mata ta
wanke fuskar. Da kyar ta bari ta hure mata idanun sunyi jazur dasu kuwa.


Awwab da yake jin hankalinsa ya tashi yace mata ya idon. Harara ta maka masa kamar
ba shine ya janyo mata ba yana wasu maganganu da suke juya mata tunani.


Ana ta yi mata sannu tace su zo su tafi gida an kusa kiran sallah.


"Mal Da'u yace mu tsaya tinkiyar can da ta haihu yanzu ta kasa" Emzee ya sanar da
ita.


Idanun da suka gama yin ja da kumburi ta zaro "ta kasa me?"


"Ta haihu ya kasa cire mahaifar sai shure shure take yi. Yankata zaiyi kawai mu
tafi da ita gida idan mahaifar bata fito ba"


"Gida? Da wa? So kake Malamijo yasa ayi muku farfesu na kuci da burodi da safe?"


Ibrahim da Fauziyya suna dariya ta fada musu Malamijo yace ko kazarsa ce wani abu
ya sameta ita zai kama.


"Hamma kai ya bawa amana kace ka karba" Ibrahim ya tuna masa.


"Ku muje na ajiyeku kawai na nemi wurin kwana a waje da safe zan dawo daukarku.
Naga alama kasawar ma zata yi"


Hankalinta dama a tashe yake ta kyabe fuska yadda Zayyana take yi "bakinka ya sari
danyen...."


Da sauri ya dakatar da ita kafin ta karasa fadin kazantar "ahhhhh don Allah kada ki
karasa. Bazai sara ba in sha Allah"


Ya kama kansa kuwa ta sami kofar ramawa tayi shu'umar dariyar da sai ta tashi
tsokana take yinta "danyen mangwaro fa zan ce ka hanani. Ka ga bishiyarsa can da
nake hawa na tsinko mu rinka dangwala da siga"
Shima harararta yayi na daukar hakkinsa da tayi sannan yace "kwadayi, meye abin
dadi a danyen mangwaro da sugar?"


"Kai dai kawai ka tsorata kayi zaton danyen ka...."


Wannan karon shine fuskarsa kamar zaiyi kuka baya son jin kazantar da ta dage sai
ta fada "habaaa mana Alheran!"


Sai da ta kalli su Fauziyya tace "yanzu danyen kashu din ma ban isa in fada ba?
Shima akwai bishiyarsa daga bayan can"


Hatta Emzee sai da yayi dariya saboda yadda fuskar Awwab tayi.


"Tsokanata kuke yi ko? Nasan me zanyi muku" yace yayi gaba Ghazalatu tayi saurin
tarar dashi.

💕[11/2, 6:45 AM]: 29. 💕

Mota suka nufa cikin sa'a Mal Da'u ya sanar dasu cewa ya fitar da mahaifar tinkiyar
ta tashi. Radhiya sai murna kamar wata mutum. Kafin ta bar gidan ta kudiri niyar
sai anci nama amma bazata so yau da babu hannunta a ciki ba Malamijo ya kare mata
tanadi a bainar jama'a. Kowa wurin zamansa na dazu ya zauna jiki yayi ligib bare ma
Ghazalatu da ta hado da tafiya daga Katsina. Suna isa gida sallar magariba suka
yi.


Abin farinciki wurin Radhiya ashe bayan fitarsu Nene Marka ta iso. Danne tsohuwar
tayi cikin murnar ganinta. Yau tsakar gidan ta san anyi baki kusan kowa anan ya
zauna suna shan iskar Allah suna hirarrakinsu. Ana isha Ghazalatu ko abincin da ake
yi mata tayi bata iya kallo ba tayi bacci ita kadai a dakin Zahra ma taji sauki ta
fito wurin 'yan uwanta.


"Nene muje in nuna miki wani abu" Radhiya tace cikin rada. Dakin da zasu kwana ta
ja ta. Ganin Ghazalatu bacci take yi ta cire dankwalin ta nuna mata kan ta "kinga
abinda Innawuro tayi min" tace kamar zatayi kuka.


"Me zan gani ni Marka, aski akan budurwa saboda Allah"


Caraf a kunnen Ghazalatu. Da dabara ta juyo idonta ya sauka akan Radhiya dariya ta
kusa kwace mata. Ashe ma babu wani dalili da zai sa ta dami kanta akan wannan
namijin. Ji take kamar ta jawo gobe ta ganta a Katsina. Yau din taki karewa tunda
tazo yarinyar take like da Awwab. Bata so ta nuna masa zahirin yadda take kin
mutanen nan saboda yanzu dai a cikinsu take a cikin gidansu ma. Zata jira ko ma
meye sai sun koma inda tafi wayo. Da wayo da dabara sai ta kawo karshen wannan
alakar tun kafin rayuka su fara baci. Tana ji Radhiya tana yiwa Nene bayanin
makeron da tayi da kwarkwata da suka janyo askin.


"Da kansa zai gudu makeron nan kinji 'Yar soja. Gobe da kaina zan shiga kasuwa
akwai wani magani mai kyau idan nayi sa'ar haduwa da matar kanki har sai yafi na da
in sha Allahu"


"Yauwa Nene" ta rungumeta tana murna.


Tuwo taje suka ci da su Zayyana. A dakin da mazan suke ma Emzee ya kai musu nasu ba
kyama ko nuna gayu Awwab yaci nasa. Jakar kayansa ya duba bayan ya gama babu
toothpaste ya manto shi a gidan Mama Zainab. Tun a hanya ya tuna bai damu ba tunda
da niyar komawa gida suka taho. Bazai iya bacci baiyi brush ba. Ya ma tabbatar ko
Emzee ya tambaya za'a bashi amma ransa yafi raya masa ya fita, fitar ma da Alheran
bai gaji da ganinta ba.


"Emzee wane irin toothpaste gareku na manto nawa a Kano"


"Close up ne"


Da murna sabanin rashin jindadi da ya kamata ya nuna yace "kash bana iya amfani
dashi, akwai inda zan iya siyowa nan kusa?"


"Kawo na siyo maka yanzun nan, da wane iri kake amfani?"


Shiru Awwab yayi zancen gaskiya bashi da wani zabi indai yana da kyau yana saya. Da
dai sabulun wanka ne to baya tsallake pears masu mabambantan kamshi da sinadaren
gyaran fata.


"Colgate nake so, amma zani da kaina kwatanta min"


Emzee da wayo ya gano Hamman nasu. Kallonsu yake daga shi har Radhiya ya ga ina
za'a dire wannan abu.


"Ko in kira Adda ta raka ka ta fini sanin wurare. Idan ba'a samu a wani wuri ba
baza'a rasa a wani ba"


Ido ya kafe Emzee dashi yana tunanin ko dai yaron ya fahimci yadda ya damu da ita
ne. Ba ya son bawa kansa kunya a gaban yara ba. To amma meye a ciki don ya damu da
ita ba kanwarsa bace? Yana can yana musu da zuciyarsa Emzee ya fice ya tafi
nemanta. Tana dakin da su Mami zasu kwana sun je ita da Zayyana suna damunsa da
hira. Fauziyya da Zahra suna nasu dakin kowacce tana waya.


"Adda kizo inji Hamma"


"Tayi masa me a daren nan tara saura?" Cewar Mami .


"Nima ban sani ba"
Mairama addu'a take Allah Ya daidaita kansu kada a sami matsala. Zama da Radhiya
idan babu soyayya fa to akwai daru.


"Kai Hajiya yanzu bashi da ikon kiran kanwarsa?" Hajjo tayi maganar tana murmushi
irin na ta fara gano manufar yaron.


"Radhiya tashi kije"


Sai dai tun suna magana Radhiya tayi gaba abinta. Nemanta suka yi suka rasa suka
kwashe da dariya gabadaya.


Ta riga tayi wanka bayan magariba da suka rinka layi ita dasu Zahra kowa jiki yayi
datti. Wata riga ce cotton mara nauyi take bacci da ita sai zani da ta daura da
hijabi a kai. Shima Awwab can dakin da suke a bangaren samarin akwai bandaki wanda
Emzee ya wanke musu shi tas suka yi wanka.


Lokacin da Awwab ya juya bai ga Emzee ba tunanin ina ya tafi ya fara yi sai gashi
ya dawo yace Radhiya tana kofar gida inda ya turata yace ta jira shi. Yana fita shi
da Ibrahim suka kwashe da dariya.


"Zeezee malamin soyayya. Nima na fara ganosu fa" Ibrahim yace yana mika masa hannu
suka tafa.


"Idan ka sami ta ka kuma ka rasa yadda zakayi ka fada mata ka nemeni ka ga aiki da
cikawa"


Daure fuska Ibrahim yayi da wasa "an fada maka na shirya ganganci ne. Idan na samu
ma sai ranar kai amarya zan tura ka daukota"


"Dalili"


"Kada kaje kayi min kwace kana wannan lumshe idanun da shan kamshi tace ta fasa na
fiye surutu"


Emzee sai dariya suka shiga tsokanar juna irin yadda dai matasa sa'o'insu suke yi.


Tun daga ciki ya soma hangota tana tsaye suna magana da wani da sau biyu yana
ganinsa a cikin gidan. Me yiwuwa dai shima kanin Umminta ne. Sallama Awwab yayi
masa suka gaisa ya shige ciki.


"Emzee yace kana kirana kuma wai a waje"


Hannuwansa ya zura a aljihu yana kallonta "aikenki zanyi dama amma na fasa dare
yayi"
"Yo ni ina tsoron dare ne kamar ba soja ba"


Tafiya ya soma yi kawai batare da sanin inda zashi ba ta bishi suna tafe gefe da
gefe.


"Alheran" ya kira sunanta daga can kasan makoshi sai da taji a jikinta.


"Uhmm"


"Bana son ki zama soja"


Bata ga alamun wasa ba a fuskarsa shiyasa taji gabadaya ya karyar mata da gabbai.
Yau sau biyu yana cewa bazata yi soja ba. Na dazu haushi ya bata sosai amma yanzu
da ya fada sai taji tana son sanin dalilinsa na fadin hakan. Me yasa shi da take
tunanin zai taimaka mata ta sami biyan bukata zai rinka neman rabata da abinda ta
girma dashi a ranta. Kafin ta tambaye shi ya cigaba da yi mata bayani.


"Ban taba tunanin zanyi wani karatun da bai shafi zama soja ba. Infact son da nake
yiwa duk wata harka ta military ce tasa na zama pilot. Na rasa abubuwa da yawa
saboda aikin soja. Mahaifina ya dawo gida da kafa daya da lalurar da taso dauke
masa dukkan tunaninsa, Baba Hadir yana zaune a wheelchair babu motsi babu magana"
tsayawa yayi ya juyo sosai yadda zasu fuskanci juna. Ba tsayinsu daya ba amma itama
tana da tsaho daidai gwargwado, duk da haka sai taji kamar ta kankance a gabansa
"na rasa mutum na biyu a rayuwata da na baiwa matsayin uba sannan kike tunanin
Awwab zai iya bari ki zama soja?"


Tambayar ta soki zuciyarta kamar yadda maganganun suka yi tasirin da ya sanya taji
kamar tayi kuka. Babu wani abu daya da zata iya tunawa game da mahaifinta idan ka
cire kamaninsa na hoto. Amma labaran da take ji game dashi ya sa take da burin zama
kamarsa. Tana so nan gaba ko me ta zama idan an tashi ace 'yar Zayyan Muhammad
Tureta ce.


"I may be selfish Alheran amma daga jiya zuwa yau keman kin sani cewa bazan so wani
abu da zai taba min ke ba."


Kallonsa tayi ta ga idanunsa kyam a kanta sai tayi murmushi "me kake so na
karanta?"


"Are you serious? Kin hakura?"


"Ba dole ba kana yi kamar zaka yi min kuka" tace tana dariya. Hamma yafi karfin
komai a wurinta zuciyarta ke sanar da ita.


Da sauri tayi hanyar gida dama ba nisa suka yi ba yabi bayanta yana murmushi har
suka shiga soron. Tsayar da ita yayi ya koma mota ya dauko ledar tsarabarta ya
damka mata.
"Ga naki kayan ledar Allah Yasa komai yayi miki"


Tayi murna sosai ta dauko takalmi daya ta gwada yana haskawa da wayarsa don ta gani
saboda hasken soron bashi da yawan da zata gani da kyau. Guda uku ne takalman biyu
da jakarsu sai turare biyu, dankunne da sarka da tarkacen kayan kwalliyar da bata
san yaya zata yi dasu ba.


Sai da ta gama godiyarta ta karbi wayarsa tace ya buda mata hotuna ta gani. Daya
bayan daya take binsu wani tace yayi kyau wani ta tsokane shi. Da sannu ta iso
wurin hotunansa da uniform dinsa. Nan fa ta rude tana ta yaba yadda kayan suka
burgeta.


Murmushi yayi mata yace "ko dai ta kusa kare miki ne zaki hakura da dreba"


"Sai soja ko likita"


"Time will tell"


"Me kace?"


"Babu komai"


Cigaba da kallon tayi ta budo wani yana tsaye da members na cabin crew dinsa a wata
tafiya da suka yi da ta dace da birthday dinsa. Shi ya ma manta kafin a budewa
fasinja su shiga jirgin suka kawo masa cake da gifts saboda yadda suke jindadin
aiki dashi. Yana sakewa da kowa ayi raha ya wuce. Kasa yin gaba tayi da hoton duk
da yayi kyau sosai amma 'yan matan air hostess din sun wani saka shi a tsakiya.
Tayi gaba a hankali sai da ta gwammace bata yi ba. Wata cikinsu ce take tura masa
cake a baki sauran suna tafi aka dauka. Abinda bata taba ji bane a rayuwarta na
tsananin kishi ya saukar mata a lokacin. Ji tayi ina ma Ghazalatu ce ke bashi akan
wannan mai dan skirt din da tasha kwalliya kamar 'yar tsana.


Gani yayi tayi shiru ya fada mata lokacin da aka yi hoton. Daga murya tayi ba da
niyya ba sai dai bacin ranta a lokacin ya kai makura "ita ma wannan matsayinsu daya
da waccan ne?"


"Waccan?"


Da gatse tace "Matar da zaka aura ba"


"Abokan aikina ne fa"


"To" tace muryarta tana rawa. Duk yada taso boyewa kasawa tayi hawaye kamar famfo
suka shiga sintiri a kumatunta. Karbe wayar yayi ya haske mata fuska tayi saurin
rufewa da tafin hannunta da kasan hijab din tana kara sautin kukan.


"Ya Allah, me nayi miki kuma?"


"Babu komai"


Hankalinsa a tashe yace "amma kike wannan kukan, akwai abinda yake damunki ne?"


"Nima ban sani ba" ta sake bare baki kukan yana karuwa.


Hoton ya kula tana kallo ya dawo da wayar saitin da zata gani sosai. Gabadaya
hotunan ranar birthday din nasa akan idonta yayi marking ya gogesu. Babu kunya
murmushi ya bayyana a saman labbanta.


Dage gira yayi yana mata wani irin kallo "silly girl! Kishi ko? Ko dai ta kare
miki dinne ban sani ba?"


Dinke fuska ta sake yi ta tashi. Yayi ta kiranta haushin kanta da kukan da tayi
yasa taki amsa masa. Samun kansa yayi da sakin murmushi shima yaji dadi ta damu
dashi. Girgiza kai yayi lokaci guda yana kwabar kansa da cewa ya kiyayi wuce gona
da iri akan kanwar tasa. Duk abinda yake yi mata 'yan uwantaka da shakuwa ce

**********
[11/2, 6:45 AM : 30.💕
]🏽

Rtd Major Mustapha tun a hanya suna ta waya da Baffa Habubakari da babban dansa da
ya rako shi wan Zakari. Da kuma wannan soja wanda a yanzu yake rike da mukamin
Captain shima kansa. Rikon amana da cigaban zamani yasa bai taba gazawa a wurin
karbar sakon Major ba.


A harabar Giginya Hotel inda suke sa ran yin masauki suka hadu. Da motoci biyu
hilux cike da sojiji majiya karfi wanda kallo daya zaka yi musu duk wani burbudin
fitsara da rashin kunya su kama gabansu Captain Onomza ya zo wurin.


Ya gaisa dasu Daddy ransa a matukar bace yace a yanzu fa zasu wuce a kamo mutumin.


"Calm down Captain, muyi hakuri zuwa wayewar gari"


"I am sorry Sir, I cannot wait Sir" ce amsar da ya bayar yana 'yar dariya saboda
har yanzu yana girmama Major.


Major ma burinsa ya ga Maikudi a hannu. Tunanin wadanda suka zo dasu yayi ga gajiya
ga kuma firgicin ganin sojojin. To su ma sunyi na'am da a tafin shiyasa babu bata
lokaci suka wuce gidan.


Jume ce tsaye jikin bango domin baiwa kanta kariya kada ta fadi saboda zafin
kalaman Maikudi.


"Kannenka kayi musu tsawa nima kayi min tsawa ina mahaifiyarka?"


"Idan bakya so sai ki bar wannan magana. Abinda ya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login