Showing 144001 words to 147000 words out of 295847 words
mata tafiya ce a gabanta zata kai mijinta asibiti. Maman su
Aisha ta tausaya mata ta kuma jinjina mata wannan sadaukarwa da ta hanata zama
gidan mutum kamar Alh Musa mai kudi da halin dattako. Bata yi kasa a gwiwa ba bayan
ya dawo daga wurin aiki ta fada masa. Abin yafi taba shi duk da yasan ta koma gidan
tsohon mijinta amma sai da yaji wani iri. Soyayyarta da tausayinta duka a hade.
Nasa salon kaunar shine ya tura mata miliyan biyu da rabi a matsayin gudunmawa.
Mama tayi kuka a ranar yadda Allah ke budawa bawanSa a lokacin da bai taba tsammani
ba. Aurenta da Alh Musa ta yarda silar arzikinta ne da nemawa Hadir waraka.
A Sumaila kuma su Ummi sun isa gida ya fara cika da 'yan biki. Yawanci 'yan uwansu
ne na bangaren Malamijo. Washegari kuma sai ga dangin iyayen amaren mata su ma sun
fara zuwa. Innawuro da matan su Baffa Gide duka sun iso. Ranar ne za'ayi Kamu amare
kowacce dangin uwa na kokarin rufa mata asiri. Shi dai Malamijo tunda ya bada
abinda zai iya ya janye hannuwansa. Duk wannan abu da akeyi Salame bata samu zuwa
ba saboda bata ma da kayan sawa ta shiga taro ga yunwa kamar taci babu ita da
'ya'yanta.
Ranar da yamma Nene ta rufa mayafi ta tafi gidan Salamen. A gaban murhu ta sameta
tana ta uban kauri. Tsaki ta samu zata yi musu danmalele ita da yaranta suci.
Girman kai ya hana ta kwantar da kanta gaban mahaifinta komai lalacewarsa ta nemi
taimako. Taji labarin Mairama tana gidan amma bata gabanta tunda tasan ba ido
gareta ba bata da abinda zata tsinanawa kanta ma. Kauyen da akace ta koma na dangin
babarta ta tabbatar kila wahala kawai take sha daga ita har yaran. 'Yan lokutan da
suke zuwa Sumaila lokacin tana shanawa a jikin Indararo bata ma zuwa gidan don kada
a fara yi mata bani bani. Sai gashi a kasa da shekara guda duniya tayi mata juyin
waina...sama ya koma kasa.
Idanu jazur ta dago tana fyace majina da gefen mataccen zaninta sannan ta kakalo
murmushin dole.
"Nene kece a gidan namu yau?"
Rai a bace Nene Marka tace "nice Salame, cewa nayi bari nazo na gaishe da
hamshakiya matar Alhaji tunda kinfi karfin kowa."
Kamar wata gaula tana fama da cikin da yake neman rinjayarta tace "to ni me nayi"
"Ban sani ba Salame. Mahaifinki ya kwanta ciwo yaci ya cinye har ya warke babu ke
babu inuwarki balle asa rai da mijinki ma zai je. An kai lefen kanenki baki je ba
yanzu don tsabar bakin hali ana biki a matsayinki na babbar 'ya a gidan kin gagara
zuwa kuna gari daya. Anya Salame kin dauko hanya mai bullewa kuwa?"
Da kunya taje gidan nan bayan kowa ya santa a lokacin da take tsaka da jindadi dama
kiris 'yan bakinciki suke jira ayi mata dariya. Jiya Ta Madina tazo har gidan itama
ta kare mata tanadi wai kanwarta ta haihu bata je ba. Yaran da suka gama rainata
suke murna da talaucinta.
"Kin dai ga yanayin da nake ciki dama shi kuke buri shiyasa babu wanda ya damu
dani"
"Kaniyarki, idan zakiyi fitsararki kada kiyi min bazan miki da dadi ba. Idan ban
ganki a wurin bikin nan gobe ba wallahi sai na saba miki. Mutuniyar banza wadda
bata sawa zuciyarta komai ba sai kyashi da hassada. Malamijo ya cuceku wallahi"
Bayan fitarta Salame kuka ta saka. Tana ji tana gani ta zama bolar gida kuma miji
yaki ya saketa ko tasan matsayinta. Tana cikin wannan halin ne kamar daga sama
Halifa yazo. Matashin saurayi dan gatan Alh Salisu. Yaron babu abinda ya nema ya
rasa a wurin mahaifinsa sai dai abu guda. Da matukar wahala babansa yake bashi kudi
idan zai zo Sumaila. Da can yana bashi sai ya zamana Salame tana karanta masa
bukatunta idan zai sake zuwa. A hankali Alh Salisu ya fahimci cewa kudaden da yake
bawa dan nasa aikinta ne ko kunya babu. A yadda yayi matukar tsanar halinta tuni ya
dakile hakan. Taje can ta karata idan Halifa ya soma sana'a yayi mata da nasa
gumin.
Tsabar murna ji tayi kamar an ga watan sallah. Ta rasa inda zata saka kanta don
dadi harda yada habaici wa Maman Danmama danta yazo. Shi dai kunyar irin wannan
abubuwan nata yake yi to amma uwa uwace. Bai wani dade ba da zai tafi ya bata dubu
biyar cikin abinda ya rage masa. Salame duniya tayi dadi ta rasa ina zata kai
farinciki. Dreba ne ya kawo shi kuma yana jiransa ya tafi dashi. Dan cikinta a
wannan hadaddiyar mota harda dreba. Kai inama dai ta kwantar da hankali a gidan Alh
Salisu.
Washegari bayan sunci fara da mai harda hadin salak da kifi sukunbiya ta shirya
'ya'yanta kowa cikin kayan sallarsa na bara kafin Alh Indararo ya banzatar dasu.
Itama wani leshi ta saka cikin irin alkhairin da ta samu albarkacin aikin malamin
tsibbunta wanda ya fita yayi yanzu. Mayafin ma irin mai bakin leshi da ta dade da
dena sakawa ta dauko don na yayin duk sun mutu babu na mora.
Tana tsakiyar yaranta dayake tafiyar kafa ce zata kaita gidan tana murmushin
jindadi. Yau 'yan bakinciki sai dai su mutu. Tana nan kuma har yanzu tana damawa
don tasan da wuya a sami mai dressing irin nata.
Ta kusa gidan bai fi taku kadan ya rage ba ta ji dirin motoci a bayanta sun taho a
guje. Kana ganinsu kasan tafiya ce ta jerentawa wato convey. Motoci ne da suka amsa
sunansu mota masu masifar kyau da daukar ido duka a maimakon nambar mota an rubuta
G. AGALI wato Ghousman Agali kakan Zayyan Muhammad Tureta na wurin uwa.
Guda takwas ne sai kuma helux guda biyu da aka ciko su shakare da buhun hunan kayan
abinci da lemuka na kwali da na roba. Mota cikon ta tara da ta fita daban da sauran
duk da cewa itama tana da kyau sosai Awwab ne a ciki. Shine yayi musu rakiya zuwa
garin Sumaila domin cika umarnin mahaifinsa da hada masoyiyarsa da dangin
mahaifinta. Daga ita har Ummin an kasa samunsu a waya bare a sanar dasu zuwan
bakin.
Sanye yake da wando chinos mai kyau coffee da shirt cream wadda ta dan kama shi.
Idanunsa ya karesu da bakin glass wanda ya kara haska fuskarsa ya kuma boye bacin
ran da yake kwana yake tashi dashi tun komawarsa Katsina. Umarnin Daddy yake son bi
na kauracewa Radhiya har zuwa ayi bikin gidansu sati mai zuwa a gama sannan su sake
tayar da maganarta. Yana ganin wayarta da text wanda bayan kwana biyu babu reply ta
dena yi. A tunaninta ya koma ga Ghazalatu ne ya manta da ita shine take kishi tayi
fushi ta share shi. Matsananciyar kewarta ce ta sanya shi cewa zaiyi musu rakiya
batare da an nema ba. Daddy yasan dalilinsa kuma yana tausaya masa. Lokaci guda har
ya soma rama ga maganganu sunki ci sunki cinyewa a dangi.
Salame dai sakin baki tayi tana mamakin wadannan kyawawan mutane mazansu da matansu
da suke fitowa daga motocin alfarma irin wadannan wurin wa suka zo? Ko sunyi batan
kai ne? Kila bakin Chairman ne ko gidan Hakimi.
***********
Su Alh Ghoumar tun kafin su iso cikin garin Katsina suka sanar da Major suna tafe.
Da suka zo gabadayansu sun kwana a wani hotel ne da safe shi da Alh Sidi da mutum
biyu cikin 'ya'yansu suka je gidan Rtd Major Mustapha. Yayi farinciki da zuwansu ya
sake basu labarin duk yadda ta kasancewa Mairama da su Radhiya. Guda cikin wadanda
aka je dasu wanda shine auta a 'ya'yan Alh Sidi mai suna Ridwan yace zai maka
Maikudi a kotu domin ya ha'incesu ya fada musu karya game da iyalin dan uwansu.
Major baiyi yunkurin bada hakuri ba yace idan sun dawo daga ganinsu din sai su je
Sakkwaton.
"Amma meyasa baku ce a kawo muku su ba kuka taho gabadayanku?" Ya tambayesu da
murmyshi a fuskarsa.
"Domin mu nunawa duniya cewa Mairama, Alheran da Zayyan dangin mahafinsu suna
kaunarsu. Waye zamu samu ya rakamu saboda drebobin namu biyu ne kawai 'yan kasar
nan"
Awwab kamar jira yake dama yazo gaishesu ne da Mami tace sun iso shine yace zaije.
Daddy bashi da niyar hana shi saboda tausayinsa yake ji yana mamakin irin wannan
soyayya mai karfi da ta shigi dan nasa farat daya.
Fitarsu daga gidan ko awa daya ba'ayi ba Mummy Gambo da Hussainar Mami suka zo. Ba
da mutumci suka zo ba su Fauziyya na gaishe su babu wadda ta amsa.
"Ina babar taku?" Hussaina ta tambaya a dakile.
"Hussaina kenan, gani...kai ku bamu wuri" tace dasu Zayyana, suka tashi kuwa suka
yi daki da sauri.
Zama tayi domin su gaisa Mummy ta soma fadan da ya kawota.
"Saboda wata yarinya can bare da babu wata alaka tsakaninku Hassana kike neman bata
mana zumunci? Awwab da bakinsa yace yana son auren Ghazalatu amma tashi daya zance
ya sauya saboda kuna son ku burge wasu"
"To banda ma abinta akwai wani abu da ita yarinyar tafi Ghazalatu ne? Alh Baba da
su Babanmu sunce basu yarda ba ba sai ku hakura ba. Amma ace da kanki kuka je har
gabansa don ya amince a bar danki shafaffe da mai ya yi auren gata mata biyu lokaci
guda"
Daurewa take yi suna ta caba mata maganganu a ganinsu ita ma bata son 'yan uwanta
su rabeta ne.
"Banda naci irin na Ghazalatu nace mata ta hakura da yaron nan taki. Wallahi ba don
tana son shi ba har yanzu bazaki sake ganina a gidan nan ba. Nayi zuwan karshe ne
inji menene ya sanya baki son auren nan?"
"Gambo idan Hussaina bata fahimta ba ta biye miki kun hade min kai nayi zaton ke
zaki fahimta tunda mun zauna tare kin kuma san komai game da iyalin Zayyan. Wallahi
da munsan da batun Ghazalatu Daddy bazai taba zancen wannan hadi ba. Ku duba irin
kunyar dake tattare da ya koma yace musu an fasa auren nan"
"Ke kuma gara a kuntatawa 'yar kanwarki da yaji kunyar cewa 'yan kauye an fasa
auren 'yarsu. Na tabbata 'yar dubu hamsin aka mika musu magana ta mutu har abada"
cewar Hussaina.
"Ki barta tunda Umma tace mu kyalesu mu zuba musu ido daga ita har yaya Mustapha
din. Saboda rashin sanin darajar zumunci kun shirya batawa da kowa..."
"Ke har zaki fada min zumunci Gambo" Mami tace rai a bace su Fauziyya suna jiyota
daga daki kamar yadda Daddy yake jiyota daga falonsa da bai taso ba bayan tafiyar
su Awwab.
"Kinsan me na rasa saboda zumunci? Farincikin 'yata, irin wanda kike nemawa taki
'yar amma saboda zumunci, saboda bin umarnin iyaye, saboda kada nayi sanadin
rushewar ginin da iyayenmu suka fara nasa kafa na take farincikin Zahra"
Daga cikin dakin nasu Fauziyya ta zubawa yayarta ido yayin da Zahran ta fashe da
matsanancin kuka.
Mami kanta hawaye take yi yadda 'yan uwanta suka gagara fahimtarta da mijinta.
Komai suna yi ne domin dabbaka zumuncin amma yanzu saboda fitinar Gambo Ummansu ma
ta soma fushi da ita.
"Ni Hassana banfi kowa cikinku ko cikin dangi ma haka ma 'ya'yana amma nasan cewa
munyi kokari sosai wurin basu tarbiya duk da sun tashi nesa da gida. Zahra tana da
wanda take so amma rana tsaka Alh Baba ya kiramu yace yayi musu mazaje ita da
Fauziyya. Nafi kowa sanin irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Raji amma na
tausasheta nace tayi hakuri ta farantawa kakaninta zaiyi daidai da mune muka
farantawa iyayenmu. Babu wani sabo, shakuwa ko soyayya yaran nan suka amince amma
duk baku gani ba. Kullum kwanan duniya ina tashi da zulumin rayuwar da Zahra zata
yi a gidan mijin da bata so. Ni da ya kamata na tayata neman farinciki nice na dage
kada ta fitar da maganar ko mahaifinta bai sani ba balle 'yan uwanta. Ku har zaku
fada min sanin darajar zumunci?"
Shiru suka yi aka rasa me magana a cikinsu. Basu taba ganin fushin Mami irin wannan
ba. Major yana tsaye basu sani ba yana jin abinda take fada.
"Na gaji da cin kashin da kuke yi min daga ke har Hussaina akan auren Awwab. Babu
wadda ta haifa min dan kuma na fada bazan taba hana shi auren wadda yake so ba.
Idan yace zai iya hada duka su biyun Allah Ya dafa masa."
"Gara ki fadi abinda kike son fada zaki nuna mana kece uwar Awwab"
"Kamar yadda ke uwar Ghazalatu kike wanke kafa kika taho gidana domin taki 'yar ba.
Wai ma me kuke so nayi muku ne? Ince Awwab ya zama silar kunyata mahaifinsa? Har
abada bazan ce ba. Ni na san waye Zayyan a rayuwar Daddy kuma in sha Allahu bazamu
ji kunyar iyalinsa ba."
"Dangin dangiro sun fimu" Gambo tace rai a matukar bace.
"Hussaina, Gambo. Ya isa haka kuzo ku wuce gidajenku"
Major ne yayi maganar idanunsa sun kankance ya fito musu a rikakken sojansa. Basu
iya sake tankawa ba suka fita suka bar Mami Hassana tana zubar da hawaye.
💕[11/2, 7:06 AM] : 35. 💕
Awwab yana tunanin yadda zai shiga gidan ya gabatar musu da bakin ga taron mata tun
daga waje sai Allah Ya taimake shi ya hango Emzee yana tahowa tare da wasu samari
sa'anninsa. Shadda ce a jikinsa light green irin wadda sai ka kula da kyau zaka
gane kalarta saboda rashin turuwa da hular zanna bukar saka mai kyau. Yayi aski da
gyaran fuska dan gemu da gashin bakin da ya fara tarawa an gyare su fuskarsa ta
sake fitowa ga kamannin Zayyan karara. Muhammad Zayyan Tureta kenan yaro matashi da
yake ganiyar kuruciya dan kimanin shekara goma sha takwas.
Kayataccen murmushi yayi da ya hango Awwab ya taho wurinsa da sauri.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Zayyan?" Mammee tace muryarta da jikinta na
rawa.
"Na'am" yace lokacin da ya juya yana fuskantar mutanen. Idanu suka zuba masa suna
mamakin irin wannan kamanni. To ai ko ba'a nemo su ba duk inda suka hado da yaron
nan zasu rantse jininsu ne.
Babu wanda ya sani cikinsu amma yadda ya gansu yawanci dattijai ne masu kuruciyar
basu da yawa yasa ya rissina da zumar gaishesu wannan mata da ta kira sunansa kanwa
ga kakarsa marigayiya Alheran Ghousman ta rungume shi a bainar jama'a tana kuka
tare da ambaton sunansa.
"Zayyan, Zayyannn, Zayyan kuyi hakuri"
Mutanen da suke wurin sai suka fara kallonsu. Emzee ya shiga kici kicin kwace
jikinsa tana kara nanikarsa. Daga gefe Salame matsowa tayi ta kare musu kallo da
kyau. Bata iya ganin fuskar Emzee shiyasa bata san ko waye ba ta kada tawagarta
suka shige gidan.
Awwab ne ya riko hannunsa yana yi mata murmushi yaja shi gefe "nayi ta kokarin
kiran Ummi ko Alheran bana samu. Daga Nijar suke"
"Da gaske?" Emzee yace yana zaro idanu da mamaki. Da sauri ya shige ciki Awwab yace
musu zai je ya sanar da Ummi ne. Duk basu damu ba suka ce zasu jira.
A ciki mata musamman manya ne suke tsokanar Emzee wai ya shigo taron mata.
Hankalinsa baya garesu yana ta wurga ido yana neman Umminsa. Radhiya ya hango ta
fito daga daki da shadda kalar tasa anyi mata doguwar riga mai karamin hannu da bai
kai gwiwar hannunta ba. A Kano akayi musu dinkin Mama ce ta bada. Kamar ba ita ba
tayi kwalliya harda janbaki. Dauri akayi mata irin mai hawa hawan nan dayake
dankwalin da girma babu mai gane yaya gashin yake. Ta sami mayafi dark green kalar
zaren aikin rigar ta yafa ta bayanta iya kafada ya rufe mata hannuwa amma bata hade
shi ta gaba ba. Da gudu gudu ta fito daga dakin tana mita saboda Ummi tace mata
saura ta bata jikinta. Ta yaya za'ace kada ta bata jiki kamar yarinya. Ummin ta
rinka dariya tace ta saba jin suna haka da Innawuro.
"Sai na zata kazama ce"
"Innawuro ai ba sona take ba. Ni da tayi min...."bata iya karasa me zata ce ba ta
fito shine suka hadu da Emzee.
"Ina Ummi?"
"Tana ciki"
"Hamma Awwab yana waje" yace da ita tayi hanyar kofar da sauri.
Shiga yayi ya ganta tamkar ba Ummin da ya sani ba. Sanye take da irin kayansu
dinkin da komai irin na Radhiya. Bata yi kitso ba amma ta tufke gashin ya wuce
kafadarta yana ta kyalli. Mairama tayi matukar kyau babu yadda zaka ce ita ta haife
su. Zamansu a ruga babu yunwa babu kishi sai dai kawai rashin wayewa wanda da
karfin cin tuwo Mama Zainab take cusa musu. Tsallake matan dake zaune a dakin yayi
ya karasa gefenta ya duka ya sanar da ita bakin da suka yi.
Ummi bata san lokacin da taji kwalla ta taru a idanunta ba. Da gaske Major ya nemo
dangin Awwab na Nijar har sun biyosu Sumaila? Da zafin nama ta tashi tunanin me ya
kamata ta farayi domin karramasu ya darsu a ranta.
"Su nawa ne?" Ta tambayi Emzee a yayin da take fita daga dakin.
"Wallahi Ummi motocin da yawa"
Tana fita dakin Yadikko tayi inda suke ta fama da baki ciki harda Innawuro da Nene
Marka. Sanar musu tayi kowacce ta tashi da sauri aka shiga kiran kannenta masu
kuruciya su taho za'a gyara bangaren samari inda babu kowa. Wurin akwai dakuna uku
da baranda mai dan girma. A barandar suke tunanin saukesu idan an share. Hajjo,
Yadikko, Innawuro da Nene Marka kowa ta bazama ana kokarin hada abinda ya dace.
Allah Yasa akwai kofa ta waje da za'a iya shiga wurin ba sai sun shigo cikin
turmutsin 'yan biki ba. Sai da Ummi ta ga komai ya fara daukan saiti tace da Emzee
yaje yace suyi hakuri tana kokarin samun wurin da za'a saukesu ne saboda 'yan biki
gidan a cike yake.
Ya juya zai tafi fadin sakon sai ga Salame da 'ya'yanta ta rasa dakin wa zata je.
Yadikko da Hajjo duka ta leka basa nan. Asabe da Hanne ba saninsu tayi ba kuma ma
dai ta rainasu. Bai kula da ita ba ya rabe abinsa ya wuce. Yarinyar da ta yaye ce
ta shiga jan zaninta tana kuka tare da nuna wasu yaran da suke cin shinkafa
dafaduka.
"Umma umfafa"
"Rufe min baki dalla can za'a zuba muku"
Na biyu a cikinsu shi kuma ya ja hannunta cikin tashin hankalin kuruciya ganin
wadda yaran da suke kallo suke ci ta kusa karewa "Umma zasu wawashe bamu samu ba"
Dagewa tayi ta make bakinsa ya sa kuka kuwa da ta ga an fara kallonta ta rage murya
"dan ubanka rufe min baki maye"
"Ya zaki kira shi maye? Haba kinsan yara sai hakuri ki zaunar dasu mana a zuba musu
abincin"
Ummi Mairama ce tayi maganar saboda zata wuce ta hango Salamen. Wani farinciki taji
a ranta duk da rashin jituwar dake tsakaninsu tana kallon yadda 'yar uwarta ta
chanja. Rashin lokaci saboda shirin biki da kuma hani daga Nene Marka duk da bata
san dalili ba ya hanata zuwa gidanta bayan idonta ya bude. Isowarta taji suna
wannan rigima da yaran.
Batare da ta dago ba, har yanzu tana duke saboda bayanta da ya amsa garin saurin
dukan yaron taji wani uban kamshi mai sanyi da ya mamaye wurin wanda ke fita daga
jikin Ummi tace "barni da shegu basu da aiki sai cin abinci. Gudun kwadayi yau
sukunbiya na saya musuuuuuu" bakin ya makale ta kasa shiru duk da ta kai karshen
kalmar.
Ido ta tsaya gogewa da hannu babu kunya babu tsoron Allah sakamakon gamon da tayi
bayan ta dago. Wata