Showing 165001 words to 168000 words out of 295847 words
kullum yana
sama kamar tsuntsu har sai yaushe zasu daidaita ta ga ta fara shirin bikinsu.
An gama komai dreban Daddy ya tafi dauko masu fara sauka idan ya kaisu ya dawo
daukar na biyun saboda motar tayi musu kadan kuma babu mai tuka ta Mama. Ibrahim
sai laraba zai dawo shi kuma Emzee nasa zuwan sai kwana biyu kafin suna. Ya gama
mita wai kiran me ake yi musu don za'ayi suna Ummi tace yaushe rabon da su taru
lokaci guda duka. Kuma ma ana gama sunan Rugar Barkindo zasu je da Sumaila kafin
Radhiya ta fara aikinta.
Su uku suka fito daga cikin airport din. Raji, Zahra da kuma Awwab da yake dauke da
Femi. Mutan gida kowa yayi mamaki da murnar ganinsa. Yayi wani irin haske da kyau
saboda kasar Ukraine akwai sanyi sosai. Ga girma da cika ido tamkar Major zamanin
kuruciya. Dukkansu gidan Mama suka shiga ya mikawa Fauziyya Femi ya koma gefen Ummi
da hannuwansa a mike yana jira ta ajiye masa baby Zayyan.
"Naki din, yanzu zaka zo Awwab sai dai in ganka kuma jiya ma munyi waya fa" tace
tana bata rai.
"Ummi kin dena sona ne, a wayar ma fada kike yi min" yace yana dariya.
Sauran ma sai suka soma dariya ana tsokanar Ummi wai Mama tayi mata kwacen da.
"Ga sabo me zanyi da wannan katon nima. Na barwa Mama dama haka take so"
"Ke dai kawai don kinga munfi shiri yanzu shine zaki tashi hankalinki"
Sosai ta rinka zolayar Ummi ta kuwa hana shi baby din ya gama nacinsa ya hakura.
"Abincinku yana gidan Ummi. Zahra mijinki zai ci a can ko a kai masa dakin Awwab?"
Mami ce tayi tambayar tana rike da Jawad da ya hanata zama yace wannan ya nuna
wancan.
"Ni dai na koshi" Awwab yace ya tashi zai tafi daki.
Ummi ta tabe baki "kun gani irin halin nasa, mutum yaki cin abinci kullum koshi
yake kira alhalin baici komai ba"
"Ummi ki rabu dashi yunwa ai ba kanwar uwa bace. Zata koro miki shi anjima"
Daga shi har su Zahran a gajiye suke. Dakinsa wanda aka gyara domin zuwan Raji suka
shiga suyi wanka. Fauziyya ce ta yiwa Femi ya ware suna wasa da Jawad. Mami sai
murmushi wadannan yaran jikokinta ne.
Sai karfe shida da rabi su Radhiya suka iso gidan suma a gajiye sai dai murna da
doki bazasu bari taji da gajiyar jikin nata ba. Ita da Tante Nasara ne da Yousuf.
Suna sauka daga mota tayi gidan Mama da sauri. Irin shigar da ta saba tayi na skirt
mai fadi da riga iya cinya mai dogon hannu madaidaiciya wadda bata kamata ba bare
ta fito da shape din jiki sai rolling din mayafi da tayi. Yousuf yana kallon yadda
take sauri ya girgiza kai. Wani zubin kamar ta girma amma idan abin ya motsa sai
tasa mutum dariyar dole. Yanzu ma saurin da take yi wai kada a gama rigata daukan
baby ne.
Tunawa tayi da jan kunnen da Tante take yi mata akan rashin nutsuwa sai ta tsaya ta
daidaita kanta sannan ta shiga da sallama. Mama tana zaune kasa hakuri tayi ta taso
ta tarbi 'yar tata cike da farinciki.
"Radhiya kece kuwa? Bari dai maman taki tazo naji ko an baro min tawa a can ta kawo
min ta bogi"
"Kai Mama" tace tana murmushi amma duk iya dauriyarta rashin ganin baby din yasa ta
soma bata rai "Mama ina Daada?"
"Wai da gaske haka zaki rinka kiran sa?"
"Oui Maamon" Ta amsa da dariya tana mata salute suka sa dariya tare.
"Yana bayan Mami yanzu ta fita zata dawo am....."
Radhiya har ta kofa tafiyar da bata kai minti guda ba ta kaita gidan Mamin. Tana
iya jiyo muryoyinsu Zayyana ta fada da sauri tana murna. Su duka Mami ce tace su
fita a bar Mama tayi bacci ko ta huta dai.
Kan kace meye wannan sun cika gidan ba babba ba yaro daga kan Zahra har Zayyana.
Murnar ganin juna suke yi sosai. Kowa yayi mamakin Radhiya ta canja sosai ta zama
wata rabin baturiya. Ta dauki Jawad da Femi duka lokaci guda tana juyi dasu.
"To dai ku rage hayaniya kunga mijin Zahra yana ciki kada ku hana shi hutawa" Mami
ta fada tana ficewa da baby a bayanta don bazata yarda suna wannan hayaniyar ta
damka musu dan amana ba. Suje can su karata da nasu 'ya'yan tunda su da kwarinsu.
Zahra ta dora hannu a baki tana kunshe dariya "Hamma Awwab kai Mami, shi yafi kowa
gudun hayaniya yanzu."
Dif Radhiya tayi gabanta na faduwa. Hamma Awwab yana cikin gidan bata sani ba. Da
yaran a hannu ta juya zata fita ta rasa murna ce ko tsoro ko kuma bacin rai na
shareta da yayi. Suna zuwa kofa Femi ya bare baki yana mikawa Zahra hannu.
"Tafi can nima bana yi da kai mai kyuya kawai. Kuma zaka ganni na goya Jawad ne na
bashi chocolate" tace tana mikawa Zayyana shi tunda tafi kusa.
Kukansa da Raji yaji yasa shi bude kofar dakin Awwab kuma a lokacin ne tayi wannan
maganar a kunnuwan Awwab din. Comb ne mai brush mai laushi yake sake kwantar da
sumar kansa duk da yayi aski saisaye amma gashin ya soma fitowa. Dena brushing kan
nasa yayi ya kallo kofar yayi sa'ar ganinta tana hararar Femi da ganin babansa yasa
shi dariya.
Murmushin da baiyi niyya bane ya kwace masa yana kallon yadda take hararar yaro a
gaban iyayensa kuma wai nan fushi ne kawai don yaki binta "Silly girl" ya furta a
hankali idanunsa a kanta har ta fita daga gidan.
Ko da ta isa gidan Tante da Yousuf suna tare da Ummi suna cin abinci. Dukkansu dama
yunwa suke ji tun a hanya. Wurin Ummi taje ta rungumeta tana dariya.
"Umminaaaa"
"Meye haka, tashi ni ki dagani" Ummi tace tana jin kunyar Tante ba don bata murna
ta ganin 'yarta ta ba.
"Alheran rabu da ita kinji. Zuba abinci ki ci"
"Wanka zan fara yi. Ummi yaushe Emzee da Ibrahim zasu zo?"
"Kafin ki fara aikin in sha Allahu. Kiyi wankan sai kuci tare da su Zahra su ma
basu ci ba muna gidan Zainab tun dazu ana hira"
"Ai sai an dawo da komai baya bari na shirya dai."
Dakinta ta wuce akwatunan Fauziyya da Zahra suna gefen inda Ummi ta tura mata nata.
Su ukun a nan zasu kwana. Yousuf a dakin Emzee ita da Nasara a dakin Ummin. A can
gidan Mami kuma Zayyana ce kawai sai Awwab da Raji.
Tana wanka tana tunanin wai Awwab yazo. Yaushe rabon su da haduwa. Gabanta har wani
faduwa yake ta koma shiryawa a hankali. Duk yadda yace yana sonta ko sau daya bai
nemeta a waya ba tunda ta tafi wai shi fushi. Kwafa tayi ita kadai. Ranta taji ya
baci tayi siririn tsaki tana tazar gashinta da ya zarce kafadunta. Dama ita kanta
akwai cika ga santsi shiyasa duk gyaran da take masa bai wuce amfani da shampoo
masu kyau ba sai steaming da Tante take mata a shafe shi da mayuka. Tana daure shi
yake kwanciya a kanta sai tayi rolling dinsa a keya ko tsakiya da ribbon. Ita da
kitso sai sunzo Nigeria ko Nijar.
Doguwar riga ta saka ta wani yadi mai laushi anyi mata free style da dogon hannu.
Karamin mayafi ta yafa bayan ta shafa hoda, kwalli da wani lip gloss light brown.
Sassanyan body spray ta feshi jikinta dashi ta kuma saka turarensa a kayanta.
Kamshinsa bashi da karfi very cool daidai da mata.
Ta bata lokaci sosai sai da tayi sallar magariba da isha ta fito. Fauziyya da Zahra
ta gani da yaransu su Ummi suna gidan Mama har Tante.
"Kunci abincin?"
"Au wai da baki ci ba Radhiya? Shine kika makale a daki" Inji Zahra
Hira suka dasa suna yiwa juna tambayoyin yaushe gamo ta durkusa gaban kwanukan
abincin da aka sauke a tsakar falon ta debi dambun yadda take jin zai isheta da
farfesun a karamin bowl. Kan dinning table ta ajiye komai ta karkata kujerarta
yadda zata ji dadin hira dasu Zayyana ta shigo tana waya da Emzee. Wuri ta samu ta
zauna a kujerar kusa da Radhiya suka ji wannan deep voice din ta Awwab yana
sallama.
Kowa ya amsa sallamar harda Yousuf da ya fito daga daki a lokacin amma Radhiya ta
kasa bude baki kamar wadda ta hadiyi kota. Ko dago kai ma ta kasa yi tana rike da
cokali a hannu tayi kasa da kanta. Zuciyarta na tsananta bugu.
Fuskar Awwab a sake yaje ya mikawa Yousuf hannu suka gaisa tare da fadawa juna
sunayensu. Zama Yousuf yayi a kan daya daga kujerun falon suka gaisa da su Zahra.
Shi kuma Awwab ya tako a nutse zuwa dinning table din da yake kusa da bango daga
bayan kujerar da Yousuf ya zauna.
"Bani wuri" yace da Zayyana yana mata nuni da kujerar da take zaune a kai. Da sauri
ta tashi ta koma wurin su Fauziyya shi kuma ya zauna. Gabadaya ji tayi falon yayi
mata kadan tamkar cikin akurki aka kulleta tare dashi. Bai ce mata komai ba ya
karbi cokalin hannunta ya zuba farfesun akan dambun ya diba yasa a baki sannan ya
mika mata. Sai a lokacin ta dago kanta suka hada ido. Babu wanda zuciya da gangar
jikinsa bai aika masa da sako mai girma a tattare da dan uwansa ba. Sun chanja
sosai shekara kusan uku ba yau ba. Sauke nata idon tayi da sauri ya sake mika mata
spoon din.
Dan cije lebenta tayi tana tuno wani lokaci da abu makamancin haka ya taba faruwa
dasu a Kano da Sumaila. Tana ji a jikinta ma mutanen falon kallonsu suke yi sai
kawai ta dake ta karba. Idan bata basar ba zato zaiyi ta wani damu dashi ne har
yanzu. Diban abincin tayi ta saka a bakinta cike da kunya. Kafin ta mika masa ya
zura hannu ya sake karba ya ci sannan ya bata. Falon kamar anyi ruwa an dauke. Ita
ta kasa kallon gefen da sauran suke shi kuma nasa idanun a kanta suke ba ma kallon
plate din gabansa yake yi sosai ba. Yousuf yana ganin wannan abu yaji wani daci
daci na taso masa dole ya tashi ya koma dakin Emzee. Awwab yayi wani murmushin
gefen baki. Shi kuwa tunani yake wai dama Hamma din da take fada saurayinta ne ko
me? Anya shakuwa zata sa Alheran cin abinci plate daya dashi kuwa? Ko da wasa duk
zamansu bata taba kwatantawa ba.
Sun cinye abincin dama ba wani yawa ne dashi ba Awwab ya janyo flask din "in kara
miki?" Yace yana kallon zoben nan da ya bata har yanzu yana yatsanta
To a gaskiya ba koshi tayi ba ta langabe kai har yanzu taki yarda su hada ido
"kadan"
Zubawa ta ga yana yi fiye da yadda take bukata ta kuma dago kai tana ware masa
idanu "its ok"
Sai da ya zuba wanda yake ji zai ishesu su biyun ya sake mika mata spoon din taci
ta bashi. Da za'a ce mata kyat a guje zata bar wurin saboda kunyar da take ji amma
ita a dole sai ta basar kada ya rainata. Shi kam rabonsa da jin nishadi irin na yau
ya manta. Ya kasa dena kallonta kamar ba Alheran dinsa ba. Tayi masa kyau sosai ga
wata zazzafar soyayyarta tana fizgarsa kamar yadda ya kamu da sonta farkon
haduwarsu. Ba don abinda tayi masa ba da yanzu kila suna da yara kamar nasu Zahra.
Ba komai ya kawo shi gidan Ummi ba a lokacin sai zuwansa wurin Mama suka shigo da
Tante Nasara. Mama da gayya ta dauko zancen Yousuf saboda yaji. Ai kuwa ta tayar
masa da hankali.
"Haj Nasara wato kin mana kwacen 'ya sai munyi da gaske muke ganinta"
Dariya tayi tace "kuma ko na tafi wallahi a bar min yarinya ta sake. Ni da Yousuf
duk mun shagwabata. Idan naji ba daidai ba ke zan fara kamawa"
"Bama zaki ji komai ba. Yaron nan naki akwai nutsuwa Nasara. Naji kamar Radhiya
tace likita ne ko?"
Gaban Awwab sai da yayi wata rawa kamar ance masa anyi auren Radhiya ne. Likita???
Alheran da shegen son likitoci shikenan Ummi ta cuce shi wallahi. Wa ya sani ma ko
sun fara soyayya an barshi a nan akan su Ghazalatu. Bai ko zauna ba ya wuce gidan
Ummin sai yayi sa'ar ganin Yousuf din shine ya tsiri cin abinci tare da ita.
Juice din kankana mai sanyi ta zuba a glass cup bayan sun gama ci ta kurba sau biyu
ta ajiye masa a kusa da hannunsa ta mike abinta ta koma wurinsu Zahra. Daukar cup
din yayi ya shanye ya yi hanyar kofa tare da kiran Zayyana wai zai bata sako.
Wani shu'umin murmushi takeyi na abinda ta gama gani wanda dole ma ta labartawa
'yan uwanta Emzee da Ibrahim amma suna hada ido da ta ga kallon da yayi mata ta
gyara fuskarta.
Radhiya na jin karar rufewar kofar ta tashi da sauri tana dafe kirji.
"Kuturin bala'i...wai... kunji kirjina kuwa? Har wani zazzabi zazzabi ne ya kamani
fa"
Zahra da Fauziyya suka kwashe da dariya harda kyakyatawa. Fauziyya ta karkace kai
tana kallonta a tsaye hannuwa a kirji tace "shegiya Radhiya ashe kina nan baki mutu
ba"
"Lallai ma Adda to wace wannan a gabanki?"
"Nufina Radhiyanmu dai mai balotelli ashe tana nan kin boyeta."
Dariya suke sosai su ukun Zahra tace "Fauziyya auren bakatsine ya koya miki zagi"
Juya idanu tayi tana dariya "Ke Radhiya auren Katsinawa akwai riba wallahi ku dena
gulmar nan haka don naga take taken Hamma wata rana sai yayi hugging dinki a gaban
mutane"
Kunya taji harda dora hannu a ka "haka kika koma maman Jawad?"
"Gaskiya ta fada miki ai, ni da wannan spoon exchange din da aure kuka yi kawai sai
ayi wacce za'ayi ko Fauzi"
"Na shiga uku zasu bata yarinya" Radhiya tace tana dariya sosai.
"Wallahi balotelli na nan ashe kike disguising dinta da wannan hot chick din"
"Kinsan Allah Radhiya ki hana Hamma zaman lafiya...yarinya kill him with love sai
ya dawo yana baki hakurin wannan fushin nasa mara dalili" cewar Fauziyya.
"Ni dai kiyi masa a hankali amma bance a sassauta ba" Zahra ta kawo tata shawarar.
"Ance muku son sa nake yi ne?" Ta basu amsa tana dage gira.
Fauziyya tace "Eh to gaskiya baki ce ba. Na fuskanci shi da Arifah kamar akwai wata
a kasa don yarinyar tayi 100%. Kamar ance zata zo kuwa gobe zanyi kana confirming
meye tsakaninsu"
Nan da nan fuskar Radhiya ta chanja tana jin dan mutumcin da suka fara da Arifan
ta waya yazo karshe. Zahra da Fauziyya sunyi dariya son ransu bayan ta fice zuwa
gidan Mama.
**********
Washegari tsabar gajiya kasa tashi sukayi da wuri gashi sun raba dare suna hira.
Ummi bata sauraresu ba ta shiga kitchen tare da Tante Nasara da ta biyota itama ta
tashi da wurin. Cikinsu Fauziyya ce ta fara tashi taje ta karbi aikin kusan komai
ita ta karasa shi kafin Ummi ta dawo daga yiwa Daadaa wanka don Radhiya ta lakaba
masa daga zuwanta tace ita bata yarda a kira mata sunan baba ba.
Goma saura kowa ya tashi banda Radhiya. Tafi sati bata baccin kirki kullum yawon
tsaraba da kuma kammala shirye shiryen project din ga tafiya a gabanta. Ummi tayi
magana Tante tace a kyaleta ta gaji ne.
Sai shadaya ta tashi babu kowa a dakin. Wanka tayi ta gyara gadon sannan ta shirya
cikin atampa blue da baki riga da zani wrapper. Tayi missing irinsu don bata cika
sakawa ba a France. Ta gama daurinta mai kyau ta tuna ba zama zata yi ba sai kawai
ta tuge shi ta tafi dakin Ummi. A can ta sami bakin mayafi mara nauyi ta yafa ta
sake gyara fuskarta ta fito falo. Nan ma shiru, tana son magana da Yousuf amma
bashi da sim din Nigeria. Ba ya nan yana wurinsu Awwab da Raji duk sun hadu dasu
Daddy da Baba Hadir ana hira a gidan Mami.
Tasan basa wuce gidan Mama shiyasa ta tafi can. Ko neman abinci bata yi ba ta
gaishe da iyayen nasu itama ta zauma zaman hira. Daadaa ta dauka ta shagala da yi
masa wasa sai hamma yake.
"Kawo shi na goya shi bacci yake ji tunda akayi wanka bai koma ba" Ummi ta mika
hannu za ta karbe shi.
"Don Allah goya min Ummi" tace tana ajiye mayafinta a gefe ta duka baya.
Ummi ta gyara tsayuwa "me? Rufa min asiri indai goyon ne ga masu karfi nan ki
dauka"
"Tante" tace tana tura baki.
"Don Allah goya mata mana Mairama"
"Nasan halinta sarai. Dama can ba wani iya raino tayi ba bare yanzu da ta dade babu
wani yaro a inda take. Da dai girki ne sai na sakar mata"
Zahra tace "Ummi ni zan bada labari. Cewa take fa na zunguri Femi don kawai taji
muryarsa"
Dariya suke ta yi mata Tante na tarewa. Mama ma dai sai ta goyi baya "idan bata
koya ba yanzu ba sai yaushe ni da nake fatan kafin shekara ta zagayo mun rike sabon
jika"
"Yauwa Mama" tace tana murmushi ta sake dukawa.
Ummi tace babu ruwanta Mami ce ta goya mata shi aka daure shi sosai don Radhiya kam
bata iya goyo ba. Ana goya mata shi kuwa ta mayar da mayafinta aka bude fuskarsa.
Zama tayi akan kujera ko motsi bata son yi tana tsoron kada goyon ya kwance ya
fadi. Tashi su Fauziyya suka yi zasu je suyi wanka Ummi tace bayan azahar su hadu
duka da yaransu Awwab ya kaisu gidan Daddy Haroun su gaishe su. Bashi da labarin
fitar tace Zayyana ta turo shi don tasan a waya bazaiyi yadda take so ba.
Can ya baro sauran mazan ya shigo falon da sallamar da ta tsinka zuciyar Radhiya.
Dauke kai tayi tana wasa da wayar hannunta ya shigo yana kamshi ya tsaya a bayan
kujerar da take zaune. Na shiga uku tace a ranta tana jin kusancin dake tsakaninsu
yana affecting dinta. Rikicewa tayi sosai amma bata so ta nuna shiyasa taki yarda
ta dago kanta.
"Ummi gani"
"So nake bayan azahar ka hada kan kannenka ku je gidan mamanku Gambo ku gaishe su.
Ga Raji da Yousuf ma duk ku tafi tare"
Shiru yayi amma yasan yanzun nan sai ta fara fada idan yaki amincewa ga mutane a
wurin "to Ummi"
"Radhiya kun gaisa da yayanki ne?" Mama tace saboda dazu ya shigo sauran duka sun
gaishe shi.
"Ina kwana" tace a hankali ko shi da yake bayanta baiji sosai ba. Kin amsawa yayi
tunda dama baiji me tace da kyau ba.
"Nasara muje ki huta ko kin tashi da wuri ga gajiyar tafiya" Ummi tace suka tashi
tare sai Mami da Mama.
Mami ma sai tace zata tafi gida a turo mata Zayyana ta tayata girkin rana. Yana
kallonsu duka suka fice Mama ma ciki tayi abinta dama duk hanyar barinsu tare
nemanta take yi.
Dukuwa yayi da kansa gefen fuskarta taji tsigar jikinta na tashi abinda shi yaji
fiye da haka "kin dena gaisuwa ne?" Taji yace muryarsa na dukan dodon kunnenta.
Muryarta ta sake ragewa tace "na gaisheka fa"
"Sai a sake tunda banji ba"
Humm'umm bai san itama taci ganye bane yanzu ko. Kin magana tayi yana nan tsaye a
bayanta har lokacin har ya soma amsa wayar Arifah tana masa barka da dawowa da
sanar dashi zasu shigo gari da Mamanta kafin suna.
Haushi ya kama Radhiya da ta fahimci da