Showing 33001 words to 36000 words out of 295847 words

Chapter 12 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

da take cikin farinciki sosai ba. Haka dai
take rayuwa daga fada sai masifa sai kuma muguwar hassadar Mairama da tayi sake ta
kama zuciyarta sosai.
Dago labulen dakinta tayi ta fito. A wulakance take kallon kanin nata "ah'a Bature
kai ne dama"


Zamowa yayi daga kan kujerar ya gaisheta. Bai manta zuwansu da sallah ba inda ta
karesu musu tas wai sun haye kujeru abinda ba'a saba ba. Da suka koma gida kowa
yana korafi suna cewa da Adda Mairama ce bazata musu haka ba banda shi don ransa ya
baci. Ya dai ci alwashin idan ba aike ba babu abinda zai sake kaishi gidanta.
Gaisuwar kuwa albarkacin mai aikinta da ya gani ne kada ace basu da hadin kai.
Kusan halinsu daya da Mairama shiyasa Malamijo ya aiko shi don sauran babu mai
yarda yazo.


"Wani abin ne ya faru kazo ko kuwa?"


Shigowar Salisu kenan yaji yadda take yiwa kaninta magana. Shi ya rasa dalilinta na
kin 'yan uwanta yanzu kaf bata son mu'amala ta hadasu. Nashi dangin ma bata raga
musu amma yana daf da magance matsalar nan.


Bature ya gaishe shi ya amsa a mutumce sannan yace ta biyo shi daki. Bakin nan a
gaba ta bi bayansa.


"Me yake damunki ne? Yaro ya taho tun daga Sumaila babu wata tarba me kyau sai me
ya faru? Yanzu ke da 'yan uwanki babu wanda zai zo don sada zumunci wurinki sai da
wani dalili?" Ya jero mata tambayoyin cikin bacin rai.


Juya idanu tayi "ai dai 'yan uwana ne ba na mutum ba"


"Ni kike yiwa magana haka ko Salame?"


Bata saurare shi ba ta fice don sallamar Bature ya koma inda ya fito. Salisu ashe
yana bayanta sai ganinsa tayi ya zauna yana tambayarsa mutanen gida.


"Kawo masa abinci mana Salame" ya umarceta.


Cire baki tayi ta kwalawa Kande kira.


"Ki kyale Kande aiki na ga tana yi. Kuma shi Halifa ba'a kwantar dashi ne? Kusan a
bayan matar nan yake wuni ita bata huta ba shi ba'a barshi ya sake yayi wasa ba"


"Idan ta sauke shi damuna zaiyi. Kuma dai tunda biyanta akeyi meye a ciki?"


"Babu komai kuwa tunda kudinki ne Hajiya"


Magana suke yiwa juna a hasale kowa rai a bace. Bature da bashi da sha'awar kwanar
musu a gida ya katse rigimar ta hanyar fada musu abinda aka turo shi ya fada. A
tare suka juyo kansa. Salisu hankali a tashe Salame kuwa numfashinta taji ya tsaya
na wucin gadi.


"Wane Zayyan din?" Salisu ya tattaro karfin halin tambaya.


"Mijin Adda Mairama."


"Salame kin..." kasa karasa magana yayi ganin ta tafi luuu kamar zata fadi ta saki
kara iya karfinta.


Maimakon Salisu ya tarota sai mamaki ya kama shi har ya kasa motsi. Salame ce fa da
yasan bata kaunar kanwarta. Me zai sa ta shiga wannan yanayi kamar ance mata shi da
kansa ne ya mutu ko mahaifinta.


Bature ma abin ya daure masa kai "Adda cewa nayi mijin Adda Mairama fa ba Malamijo
ba"


Zama kawai tayi dabas akan kujera tana kuka sosai. Shikenan Zayyan ashe bata da
rabon zama dashi. Salisu ya kawar da kai daga gareta.


"Bature yau zaka koma ne?"


"Yanzu ma kuwa in sha Allahu. Gobe za'a tafi gaisuwa"


Zumbur ta mike "ku biyo min, ko kuma dai ka jirani na shirya"


Tsawa Salisu ya daka mata "koma ki zauna. Bature muje"


Bakin gate ya raka Bature ta bashi kudin mota sannan ya koma ciki. Tana nan tana
rusa kuka Kande na bata hakuri. Yana zuwa ya finciko hannunta sai da Kande ta
tsorata. Dakinsa ya kaita ya jefata kan gado iya karfinsa. Fuskarsa a daure babu
wasa ko kadan ya jefa mata tambayar da ta kada mata hanji.


"Tun farkon haduwarmu dama Zayyan kike so?"


Shiru tayi sai faduwar gabanta da ta tsananta.


"Ki bani amsa mana!" Ya sake yi mata tsawa sai da ta firgice.


Wasu sababbin hawayen ta soma yi yaji kamar ya rufeta da duka.


"Kin cuceni, ban dade da aurenki ba zuciyata ta bani cewa ban yiwa kaina adalci
wurin zabar matar aure ba. A tunanina na auro mace mara son zumunci ne kawai da
raina na kasa da ita. Ashe kin wuce haka. Salame mijin kanwarki kike so kuma har
kike kishi da ita alhalin kina gidan naki mijin"


Har yanzu ta kasa magana sai kuka. Shi din ma nasa idon da hawaye saboda bai taba
kawo hakan a matsayin dalilin da yasa take yiwa Mairama haka ba.


"Bazaki je Sakkwato gaisuwa ba" kallonsa tayi da sauri ya sake hade rai "ke daga
yau sai abu yayi tsanani sosai zanyi miki izinin fita kina ji na. Idan kika karya
min doka wallahi, wallahi sai na shayar dake mamaki"


**********


Ranar da aka sallami Mairama a ranar Mal Aminu da Jume su ka amince da a kwashe
kayanta ta koma gidansu Zayyan. Idan iyayenta sun zo sai su tafi da ita gida.


"Ku wuce da ita su Mubaraka sai su zo a kwashe kayan gobe tunda zaman barikin babu
amfani"


Mairama tana jin haka ta ajiye kunyarta a gefe "Kawu ina son zuwa don akwai
abubuwan da nake son hadawa da kaina"


Caraf a kunnen Maikudi "ko ma meye muma din jinin Zayyanu ne. Kije ki huta ni da
kaina zan jagoranci zuwa a debo kayan saboda kada wani abu ya salwanta"


Soye idanu tayi don bazata yarda a hanata zuwa ba. Ta nuna musu akwai makota da
take son yiwa sallama irinsu Christie wadda bata kara gani ba tun lokacin da tace
zata je yi mata girki.


Mal Aminu yace "Ka barta taje Maikudi. Daga nan ma sai mu bincika muji ko akwai
wani abu da zasu bawa iyalin mamatan. Mu bari jikinta ya kara kwari ko nan da kwana
biyu ne"


Ransa baya so saboda ya kula tunda ta dage sai taje akwai dukiya dankare a gidan da
bai taba zuwa ko kofarsa ba.


"Ina mukullin a bani na rike saboda 'yan barka da gaisuwa kada wata ta dafe"


"Maikudi kenan, ko ma wacece ba sai dai muce Allah Ya bada sa'a ba. Sata a gidan
soja, gidan sojan ma a cikin bariki kamar mutum ya tashi da burin karar kwana"
Gwaggo Ladi ta gwaba masa magana.


Bai sake magana ba su ka tafi gida. Jume tasa matan su Badaru gyarawa Mairama dakin
Innar Zayyan. Tana shiga ta tuna ranar sunan Radhiya da hotunan da suka yi da
Zayyan da Awwab a ciki. Idanunta da basa rabo da hawaye suka fara abinda ya zame
musu jiki yanzu.
Jume da kanta tazo tace mata ta shirya ta fito zata yi mata wankan jego. Jariri
kuma Gwaggo Ladi ta dauka tayi masa wanka irin wanda bai samu ba tun ranar
haihuwarsa saboda kasancewarsu a asibiti.


**********


"Ya muke ta bin lungu ne yaro? Nayi zaton a irin unguwannin nan da suke malale da
titi gidan yake"


Rayyanu ya kalli Malamijo ya sake daure zuciyarsa a karo na barkatai ya bashi amsa
akan irin wadannan tambayoyin da yake ta yi masa.


"Gidan iyayenmu ne a nan unguwar. Zayyanu a cikin bariki ya zauna da iyalinsa"


Malamijo sai murmushi "Auhooo ko da naji. Ca nake a nan Mairaman tawa ta zauna ne"


Su hudu ne a ayarin tafiyar banda Rayyanu suka biyo motar haya. Nene Marka,
Malamijo, Hajjo da kuma Salisu. Gidan yanzu Yadikko da Hajjo ne kawai a gidan, ya
saki Dije da Inno yana shirin karo wata. Tun a tashar Kano ana cewa a kawo kudin
mota Malamijo ya shiga tarin karya, daga baya ma sai yayi gaba yana dukan kirji sai
da ya hango Salisu ya biya musu kudin motar su duka sannan ya dawo yana cewa
kwarewa yayi.


"Sai ji nayi wani abu siririt ya wuce min ta makoshi. Kwarewa babu dadi, ammm nawa
ne kudin motar ne?"


Nene tasan dalilin tafiyar tasa sai kawai ta dauke kai. Hajjo ce ta fada an biya
yayi wata barazanar zura hannu a aljihu zai dauko kudin ya bawa shi. Sal da Salisu
yace ya bari duk daga ne.


Iyaye da dangi duk lalacewarsu sunfi ace baka da kowa. Sallamar Malamijo kawai
Mairama taji ta sa kuka sosai. Kuka ne na ganin babban gatan da ya rage mata duk
fadin duniyar nan. Shine bango abin jingina a gareta wanda take sa ran idan tayi
kukan rashin miji zai rarrasheta yace ta barwa Allah komai. Idan tayi kukan rayuwar
marayunta zai yi mata alkawarin matsawar yana numfashi 'ya'yanta bazasu tagayyara
ba.


Jikin Nene Marka ta zube suna kuka tare. Malamijo ya tausayawa Mairama sosai ya
mika hannu ya dauki Radhiya. Zayyan wanda duka gidan an rasa mai kiran sunansa har
Maikudi kuwa saboda tuna musu da marigayi da yake yi matar Badaru ta kwanto daga
bayanta ta mikawa Hajjo.


"Iko sai mai shi, Malamijo dubi yaron nan don Ma'aiki."


Radhiya tana gefensa ya karbi jaririn yana kare masa kallo. Salisu yazo ya karbe
shi shima ya ga kama sosai da mahaifinsa.
"Allah Ya raya mana kai karamin soja

"

Mazan sun koma waje inda ake zuwa yi musu ta'aziyya matan kuma suna daga ciki. Sai
dare ne Mal Aminu ya sanar da Malamijo za'a kwaso kayan Mairama sai su tafi da ita.


"A'a a bar yarinya a gidan mijinta. Idan akwai wata dukiya da bazata iya juyawa ba
ni sai na tafi da ita ba wani abu."


Maikudi yayi saurin cewa "dukiyar marayu zata fi dadi a hannun dangin uba. Saboda
haka gobe zamuje ayi duk yadda za'ayi ne. Gida kuma ba nasu bane na bariki ne.
Tunda ya rasu dole ne su tashi komai dadewa"


A hankali zantukan nasu suka fara neman komawa rigima. Maikudi da Malamijo kowa ya
nuna zalamarsa a fili. Shiyasa kowa cikinsu yake ganin dole ya tsaya akan dukiyar
da basu da tabbacin akwaita.


Shabiyun rana kuwa washegari suka isa kofar gidan da ya kasance na Mairama da
Zayyan kwanaki kadan da suka wuce. Ta kalli gidan Zainab a rufe har yanzu. Tana son
sanin halin da suke ciki da mazansu amma yanzu babu hali sai komai ya daidaita a
nata bangaren. Gidan Christie ma a rufe yake. Bayan ta bude nata gidan sun shiga da
yayyen Zayyan mata da kuma Hajjo sai ga wasu cikin abokan zamansu na kusa. Gaisuwar
mijinta suka yi mata da barkar Zayyan karami. Ta tambayi ina Christie wata ta bata
amsa da cewa ranar da ta haihu Christie tazo tayi mata girki kuma ta farfadawa
makota haihuwar. Ta koma daidai lokacin da Mairama ta suma. A nan take jin duka
sojojin sun rasu ciki kuwa harda mijinta. Bata iya shiga ba ta koma gida bayan ta
sauke musu Radhiya. Shine aka sami wani da ya san gidansu Zayyan aka fada musu. Ita
kuma Christie ta tafi garinsu ta fadi mutuwar har yanzu bata dawo ba.


Duka matan abin tausayi musamman wadanda mazansu suka tafi a bayan su Zayyan. Suna
cike da tsoro da fargabar me zai je ya dawo.


Wasunsu sun saka hannu wurin tattare kayan kitchen da na falon Mairama ana hade
komai wuri guda ana fitarwa. Cikin dakin ta shiga zuciyarta tayi matukar rauni.
Shikenan daga yau duk wasu memories da suka gina da Zayyan a gidan nan cikin wannan
dakin sai dai zu dawo mata a tunani. Kukanta Hajjo ta jiyo ta shiga dakin da sauri.


"Haba Mairama ashe bazaki sakawa zuciyarki salama ba? Ni ko kadan ban so aka ce wai
azo kwasar kaya da wuri kamar ana korarki ba. Su dakata ki sami nutsuwar zuciya sun
ki"


Mairama ta bude wani akwai ta dauko envelop din da Zayyan ya bata hannu na rawa ta
saka a jakar hannunta sannan aka fara hada kayan gidan.


Malamijo yana waje yaki shiga ba don kunya ba sai don bakinciki. Shi kadai a ransa
yake nanata an yaudareshi aka ce masa Zayyan soja ne. To yaji sojan ne amma ba wani
mai mukami bane ashe. Ji dai wannan akurki da ya ajiye masa 'yarsa ya raya a
zuciyarsa. Kuma ashe ma ba nasa bane. To duka kudaden da yake masa alheri dasu a
ina yake samowa? Faduwar gaba yaji da ya tuna indai fa babu wani abin kirki da ya
bari komai na Mairama da 'ya'yan wuyansa zai dawo. Hodijan inji mutanensa, aradun
Allah bazai iya karawa kansa nauyi ba. Yanzu fa yara goma sha bakwai gareshi.
Salame ce kadai a gidan miji tunda dai Zayyan ya rasu. Gata ta tunda tayi aure ta
ari rigar rashin mutumci ta saka.Tsaki yaja sai hankalinsa ya koma ciki inda yake
jiyo muryar Maikudi.


"Kai wannan takadirin yaro da gani zaiyi mugunta. Me kuma yake nema a cikin mata?"


Shiga yayi da Salisu ya sami Maikudi yana fada "ki fito min da duk wani kudi ko
takardun abubuwa masu mahimmanci na Zayyan. Dukiyar magada sai da saka ido. Ba wai
da ka zaki dauke komai ki rike ba"


Salisu ya riko hannunsa "kaga Mal Maikudi duk abin nan ba na rigima bane. Mairama
ba jahila bace da zata ci dukiyar mamaci. Sai dai fa ina so ka sani duk danginku
babu mai gadon Zayyan sai Mairama da 'ya'yanta"


Kamar zai kaiwa Salisu duka ya soma fada "ni nasan ba banza ba kuka taho kwanku da
kwarkwata. Ashe da manufarku. To babu wanda ya isa yayi sama da fadi da dukiyar
magada muddin ina raye"


Mairama dai sai kuka. Malamijo ya zakalkale yana ta zubar musu da daraja a gaban
'yan uwan Zayyan. Idan Maikudi yayi shi za'a ce da sauran kuruciya. Shi kuwa yana
mahaifinta ga jikoki har uku amma har yau bai fasa halinsa ba.


Mal Aminu da kawunsu Zayyan sun shigo sun same su ana ta mayar da magana. Sam Mal
Aminu baiji dadi ba. Ga Mairama sai ajiyar zuciya kawai take yi.


"Daga can ofishin nasu nake an kaini har wurin wani babba cikinsu a nan munyi
magana. A takaice dai muna da yawa da muka rasa 'yan uwa a wurin nan. Amma yace
muyi hakuri ba'a turo komai daga gwamnatin tarayya ba da zasu sallami iyalan
sojojin ko kuma masu rauni"


"Ikon Allah, yanzu ace mutum ya rasa rayuwarsa a bakin aikinku amma babu sallama ga
iyalansa da maraici ya kama su?" Cewar Salisu


"Don ma baka je wurin bane. Mutanen da yawa wallahi. Sun ce kuma sojojin da aka
rasa suna da yawa ba wai na nan bane kadai. Kuma wai gwamnati bata da kudi amma
zasu neme mu idan an sami wani abin"


"Wannan ai zancen banza ne, bata da kudin take kashe mana 'yan uwa? Ni bazan hakura
ba. Wannan magana kuma bazan bari ta mutu a nan ba." Maikudi yace yana tashi tsaye
"idan ma an fada ne don a sa jikina yayi sanyi kada na tsayawa marayun nan wallahi
sai naje" ya zubawa Mal Aminu idanu.


Murmushi yayi kawai yace motar daukan kayan tazo. Kawunsu ne ma ya rinka yi masa
fadan baya son rashin kunya. To amma da yake duka talakawa ne maganarsu bata wani
tasiri a wurinsa.
Abu kamar wasa Mairama da tazo barikin nan a matsayin amarya kasa da shekara biyu
wai har anyi zaman an gama. Mijinta abin kaunarta ya tafi ya barta a hannun wadanda
basu damu da halin da take ciki ba, kawunansu kawai suka sani.


A daren Malamijo yace su shirya da wuri zasu wuce gobe. Mairama ta roke shi
alfarmar zata je gidansu Zainab kafin su tafi. Jume tana zaune tare da Mairama
bayan ta yiwa Zayyan karami wankan yamma tace mata "yanzu Mairama daga yau shikenan
ko? Nasan da wuya ku rinka zuwa tunda kin san ba ni bace na haifi Zayyanu. Ga bakin
kishi yasa ni ban san ta yadda za'ayi na sami dangin mahaifiyarsa ba balle su san
halin da ake ciki ma "


"In sha Allahu zan rinka zuwa Jume. Idan basu zo ba wa zasu nuna a matsayin dangin
uba?"


"To nagode Mairama. Sai kin daura dammarar hakuri da juriya. Yanzu sabuwar rayuwa
ce zata bijiro miki da baki taba zato da tsammani ba." Hawaye ya zubo mata da ta
tuna rasuwar Mal Muhammadu.


Washegari da wuri Mairama ta tafi gidansu Zainab. Allah Ya taimaketa bata mance
hanyar ba. Mahaifiyar Zainab din ta samu wadda ta fada mata kwana hudu da suka wuce
babanta ya kaita Kano gidansu Hadir. Duk da bata san kan garin Kanon sosai ta nemi
tayi mata kwatance amma anyi rashin sa'a ko sunan unguwar bazata iya tunawa ba don
wahala yake mata. Mairama tana kuka tace ta fada mata tazo itama zata koma garinsu.


"Kema mijin naki yaji rauni ne?"


"Rasuwa yayi."


Idanu ta zaro "idan Hadir yaji ban yaya zai ji ba. Allah Ya zama gatanku Mairama"


Sallama tayi mata ta koma gidan domin su karasa shirin tafiya. A daren jiya ta bude
envelop din da Zayyan ya bar mata. Ashe gabadaya sauran kudin gadonsa ne ya bar
mata da takardun gidansa na Kano. Dasu ta fita a jakarta idan ta koma zata fito
dasu ta nunawa iyayen. Dama suna rayuwa ne bayan tafiyar mazan akan albashinsu da
ake bawa matan. Kudi ne da bai wani taka kara ya karya ba. Wasikarta kuwa zuciyarta
ta kasa bata kwarin gwiwar karantawa har lokacin.


**********
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 15. Maikudi ne tsaye a ofishin da aka tura shi cikin
barikin su Zayyan akan maganar kudi ne dai.


"Jiya Babanku yazo akan zancen nan mun fada masa bamu da komai. Ya bada adireshinsa
duk lokacin da kudi yazo zamu nemeku" officer din ya bashi amsa bayan ya gama jero
tambayoyi.


Yana hargaginsa na rashin mutumci yace "Ashe cewa yayi shine babanmu don ya ci
kudin gado. To wallahi karya yake. Babu wata alaka ta jini tsakaninmu"


Wani sojan ne ya shigo yana tambayar wancan me yake faruwa cikin harshen turanci.
Sai da ya sara masa ya bashi amsa da gani ya fishi mukami.


Maikudi yana jin ana bayani duk da bai iya gane duka maganar amma ya dan fahimci me
akeyi ya katse wancan "You understant Zayyan Muhammad Tureta is die? Me.
Biggggggggg broza. Is me faza dinmu daya ai" ya nuna kansa yana murmushi yana so su
fahimci shine babban wan Zayyan.


Mutumin ya hade rai yace a kore shi kuma idan ya kuskura ya sake zuwa ba'a neme shi
ba a kulle shi saboda yana mudu hayaniya. Dayan yana soma fassara masa bai tsaya
jin karshen ba ya fice yana ta Allah Ya isa an kashe masa kani. A hanyarsa ta
komawa ne ya rinka tunanin dole fa akwai abinda Zayyan ya barwa matarsa. Idan ba
haka ba da me suke rayuwa duk tsahon lokacin nan? Yafi karfin ita da kwadayayyen
babanta suyi masa wayau akan hakkinsa.


Yana zuwa dakin da Malamijo yayi masauki ya shiga. A shirye suke suna jiran dawowar
Mairama.


"Dama nazo akan yaran nan ne Radhiya da Zayyan. Nace ko zaka yiwa Mairama magana
idan ta yaye shi zan zo na dawo dasu gabanmu saboda gatansu dai bai wuce wurin
dangin mahaifinsu. Idan kun tafi yanzu kai ma nauyi ne kawai zai kara hawa kanka.
Sannan bazan zuba ido bane tayi aure 'ya'yana su koma agolanci a gidan wani"


Malamijo an tabo inda yake masa kaikayi kuwa. Ina zai kai karin bakuna uku a
gidansa. Gara Mairama yana son abarsa, amma yaran nan da aka ha'ince shi yayi ta
yiwa babansu kallon kitse ashe rogo ne "indai wannan ne babu damuwa. Zanyi magana
da ita kuma dole ta amince don nima bazan so suyi rayuwar agolanci ba azo ana
wulakantasu"


Maikudi ya fita da wani mugun murmushi. Soro ya koma ya zauna jiranta. Ilai kuwa
babu jimawa sai gata tana ta sauri kada a gaji da jiranta. Dukawa ta danyi ta
gaishe shi ya yafito ta da hannu.


"Yaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login