Showing 57001 words to 60000 words out of 295847 words
debo ruwanta duka zan rinka yi"
Sauran sai suka fara mamakin me take nufi tunda dai haduwa suka yi ana zaginta.
Yadda tayi maganar ne idanu har sun ciko da hawaye yasa Jummai da sauran seniors
din dariya. Kawayen Radhiya ciki ya duri ruwa. Ita kanta a tsorace take. Jummai ta
dafa kafadarta kamar ta saki fitsari don tsoro sai ji tayi tace daga yau kada wani
ya sake ko da aiken daughter dinta ne.
Kowa yayi mamaki harda kawayenta tace Radhiya tana burgeta saboda ko me za'ayi mata
sai ta aikata abinda tayi niya. Idanunta kawai zaka kalla kasan fitina da rigima
suna dawainiya da ita.
Wata kungiya da aka bude a makarantarsu SS wato School Soldiers a nan aka samu
kanta. Da jikinta da zuciyarta take wannan aikin na kare hakkin dalibai. Gashi da
kayan makarantarsu riga da zani ne amma an basu hula irin ta sojoji mai
lankwashewar nan suna sakawa akan hijabansu. Radhiya jin kanta take kamar sojar
gaske. An kamanta gaskiya da amana sannan an gurji seniors masu hana sababbin
dalibai sakat. Idan kaji ana Officer 'Yar soja a makarantar zaka rantse wani babban
soja ne saboda yadda ake shayin shiga tarkonta. Zaman SS shine babban jindadinta a
makarantar.
A haka aka yi karatun cikin ikon Allah tayi nasarar fita da credit bakwai. Emzee
kuma duka taran ya haye. Sai dai ko kadan a yadda ilimin ya tabarbare bazaka hada
makarantar gwamnati dake kauye da wadda take birni ba.
***
Tana jin shigowarsa dakin nata tayi saurin rufe ido kamar mai bacci. Murmushi kawai
yayi yana kada kai. Zainab bazata taba canjawa ba indai tare dashi ne. Shekarun da
suka yi a matsayin ma'aurata bai sa ta canja komai daga yadda ta faro ba. Akan
doguwar kujera irin ta hutawar nan ta dakin ya zauna sannan ya soma yi mata magana.
"Tashi magana zamuyi"
Kin motsawa tayi sai da taji yace bari ya hawo gadon ya tabbatar ko idonta biyu.
Juyowa tayi a hankali tana jin kunyar ya gano karyarta. Bata son yadda take yiwa
Musa amma zuciyarta ta kasa rissina.
"Shawara nazo nema"
"A wurina?" Ta tambaya mamaki yana bayyana a fuskarta.
"Eh, aure nake son karawa sai dai na kasa tsayar da shawara akan na dawo da mamansu
Aisha ko na auro wata daban"
"To ni me kake so nace? Ka auri wadda tafi kwanta maka"
Fuskarsa ta nuna ba haka yaso ba kuma shima bai boye ba yace "zan so kiyi min
rigima irin wadda kowace mace take yiwa mijinta a lokacin da ya tashi yi mata
kishiya"
Cikin yanayin rashin damuwa don har ranta ita bata ga abin rigima ba tace "saboda
me?"
"Saboda nasan cewa ko yaya Zainab ta damu dani kamar yadda na damu da ita. Sai dai
nafi kowa sanin zaman hakuri kike yi a gidan nan. Na tauyeki na hanaki walwala da
jindadin zama da wanda kike so"
An tabo inda yake mata kaikayi sai hawaye sharrr tana gogewa da bayan hannunta.
Musa yana jin kukan har ransa amma yasan ba nasa bane na wani ne "kinyi hakuri
sosai Zainab, naso ace mun haihu don in samu abinda zan cigaba da garkuwa dashi in
ki rabuwa dake amma Allah bai kawo ba. Sai nace zan barki ko don su Aisha. Yanzu
kuma gashi suna shirin aure nan da watanni kadan. Ina ganin kamar bani da sauran
dalilin cigaba da zama sanadin kuncinki"
Kukan Zainab sai ya koma mai sauti. Tana tausayin Musa bisa soyayyar da yake mata.
Tayi iya yinta amma zuciyarta taki amsarsa a matsayin masoyi.
"Kayi hakuri da dukkan bata maka da nake yi, zanyi kokarin gyarawa"
Murmushi yayi mata yana mika mata takardar hannunsa "ni na gyara mana matsalar ina
fata Allah Yasa nayi abinda ya dace. Zainab na sakeki saki daya"
A gigice ta kalle shi hawayenta yana karuwa. Idan ya saketa fa kenan babu sauran
shamaki tsakaninta da Hadir. A gaggauce ta bude takardar sai ta kula guda uku ne a
hade da stapler. Daya takardar saki, daya check na miliyan biyu, dayar kuma
takardar mallakar wani gida ne a Kano da ya saya mata dan madaidaici. Dago kai tayi
sharbe da hawaye harda majina.
Cikin nutsuwarsa yake magana daki-daki "tukwicin kulawar da Aisha da Anisa suka
samu daga gareki ne. Bana son fada amma yabon gwani ya zama dole. A kanki na yarda
ba sojoji bane kadai jaruman kasata harda matansu. Soyayyarki ga baban Ibrahim ita
tafi komai kara miki kima a idanu na. Nayi zaton kudina zai sa ki manta da wanda
yake talaka mai nakasa amma bakiyi ba. Kin so zama da mutumin da bautar kasa ta
nakasa farincikinku domin cikar soyayya. Nagode da lokacinki da kika ara min muka
zauna tare"
Maganganun sunyi mata tsauri sun taba mata zuciya. Tashi yayi zai fita Zainab ta
taho da sauri ta rungume shi tana kuka. Bata taba yi masa haka ba idan ba shi ya
nema ba sai yau.
"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min Abban Aisha. Ka yafe min duk laifukan
da nayi maka a zamanmu tare"
Dago kanta yayi kana ganin damuwa a cikin idanunsa "yanzu dai ki soma hada kayanki
kafin na chanja shawara"
Da hawayen take murmushi "nagode"
"Nima nagode" yace ya sa kai ya fita yana jin a ransa kamar an sauke masa wani kaya
mai nauyi. Ya dade yana tsoron hakkinta kada ya kama shi saboda son zuciyarsa yau
Allah Ya bashi iko ya rabu da ita ba don yana so ba.
Ajiyar zuciya ta saki bayan fitarsa ta mika godiyarta ga Allah sannan cike doki ta
kira Ibrahim.
Labaran tara na NTA ya kunnawa Hadir yana gefe game ya dauke masa hankali a wayar
kiranta ya shigo. Murmushi yayi ya dauka.
"Hello Mama"
Hadir ya juyo ya kalle shi sai kuma ya dauke kai. Ina ma zai iya tambayar lafiyarta
da yayi.
Daga daya bangaren tace "Ibrahim yaya su Umma?"
"Lafiya kalau, ya su Anti Anisa da Baba?"
"Su ma lafiya kalau. Ibrahim nace me kake so gift din graduation ka ki fada min
kamar wata surukar ka ko, na kula ko hira baka son yi dani" tayi karamar dariya.
"Ina naga fuskar" yace a zuci. Ita da bata sakin jiki da kowa bare ayi batun hira.
Daga gaisuwa sai ta fada kogin tunane tunanenta ta bar mutum zuru. Yana mamakin
yadda idan yaje hutu take hira da su Anisa duk da ba wata hirar kirki suke yi ba.
"Ya kayi shiru ne?"
"To kiyi hakuri zan gyara"
"Shikenan, ina babanka?"
Hadir ya kalla suka hada ido. Anya Mama ce kuwa yace a ransa. Bata taba tambayarsa
babansa ba sai su Umma kawai.
Kara kashe shi tayi da wani mamakin ta hanyar cewa ya dora masa wayar a kunne
"saura ka sani a speaker"
Bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba. Wai dama Mama ta iya wasa haka?
Hankalin Hadir gabadaya yana gare shi sai kawai ya dora masa.
Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta da taji sautin numfashinsa. Soyayyar da ta
dade tana dannewa ce ta taso mata. Da suna tare yanzu shekararsu goma sha tara da
aure.
Cikin wani yanayi na shauki da begen da yake nuna soyayya bata tsufa tace "Hadir"
Allah Sarki rayuwa, yaji sunan har tsakiyar kansa amma bazai iya amsa mata ba.
"ASTAGFIRULLAH" tace da sauri ta katse wayar. Shaf ta manta cewa har yanzu tana
karkashin Musa har sai ta gama iddah. Tashi tayi ta bude wardrobe ta dauko
akwatunanta.
Da safe Musa da kansa ya sanar da su Aisha cewa mamansu zata dawo sannan Antinsu
Zainab zata tafi. Sun saba da ita sosai a hannunta suka girma. Tana kuka suna kuka
har airport suka rakata. Motarta Musa yace zai bayar a kawo mata har gida. Tayi ta
masa godiya da kyakkyawar addu'a ta shige jirgi zuwa garinsu tana mai fatan samun
sauyin rayuwa mai dadi.
**********
A firgice Rtd Major Mustapha ya tashi jike da gumi daga mafarkin da yake yawan yi
wanda yake daga masa hankali ya shiga laluben kafar katakonsa. Mafarkin ya tsananta
a gareshi tun bayan da suka sanya ranar komawa kasar haihuwarsu. Korido din da zai
sada shi da kitchen ya nufa don ya sha ruwa ya hango Mami ta barbaza kaya a gabanta
na tsaraba da take ta warewa tana saka sunaye.
Kasa tafiya yayi duk motsinta yake bi da kallo. Wannan kyakkyawar matar kanwarsa
ce, matarsa kuma uwar 'ya'yansa. Hakika a kullum baya gajiya da sanya Hassana cikin
addu'o'insa domin ta cancanci fiye da haka. Tayi hakuri dashi iyakar hakuri
musamman a lokutan da yake ganiyar ciwo har yakan nemi rayuwarta ba a cikin
hayyacinsa ba. Tunanin kawai kan sa tsigar jikinsa tashi. Tabo uku ne a jikin Mami
wanda suka samu a dalilin PTSD dinsa.
Jikinta ya bata yana kallonta haka kawai, ta daga kai suka hada ido. Murmushi suka
yiwa juna ya dawo falon ya zauna.
"Me ya hanaki bacci shabiyu har ta wuce?"
"Aikin nan yaki karewa Daddy. List din mutanen ma kamar bamu yi rabi ba" ta dan
bata rai.
"Ku kuma mata da baku da nutsuwa indai akan tsaraba ne ko"
Tattara kayan ta soma yi gefe sannan ta dube shi "me ya tasheka ne?"
Shirunsa ya fahimtar da ita komai. Kusa dashi taje ta zauna "nan da kwanaki goma in
sha Allah muna gida. Muna kwana biyu an gama gaisawa da 'yan uwa babu inda zamu je
sai wurin Ummin Awwab da Hadir. Lokaci yayi da zaka kore komai daga ranka ka
rungumi kaddara."
"Yes Ma" yace yana murmushi.
Maida masa martanin murmushin tayi ita ma "Tashi muje mu kwanta kasan gobe is a big
day"
Suna kwance tuni Mami tayi bacci amma shi ya kasa sai rarraba dayan biyu yake. Ko
yaya iyalin Zayyan? Allah Yasa suna cikin mafi kyaun yanayi. Sai kuma ya koma
tunanin auren Zahra da Fauziyya da za'ayi nan da wata biyu. Kowaccensu tuni ta hada
degree dinta. Hadi ne na gida zasu auri 'ya'yan 'yan uwa kamar yadda ya kusan
zamewa danginsu al'ada. Har nan aka turo mazan suka daidaita kawunansu. Bai san
lokacin da bacci yayi awon gaba dashi ba.
Washegari kuwa banda shirin tafiyarsu da yaki karewa karfe bakwai na dare suka
tasarma gidan da Mami take aiki. Major sanye yake sa suit sky blue da light grey
din shirt a ciki. Yayi gyaran fuska yayi kyau yana rike da sandarsa da take
taimakawa wurin rage masa rashin jindadin tafiya da kafar katako duk da ya saba
yanzu.
Mami, Zahra, Fauziyya da Zayyana duka abaya ne a jikinsu masu kyau kowacce tayi
nadi da mayafin da ya dace.
Party ne na bankwana iyalin Herr(Mr) da Frau(Mrs) Schmidt suka shiryawa Mami a
matsayinta na shugabar ma'aikatan katon gidan. Sun matukar jindadin zama da ita tun
lokacin da suka basu wuri a gidansu kafin daga baya su kama wani mai dan girma a
waje. Iyalin babu abinda yasa suka likewa Mami kamar tsantsar tarbiyar da yaransu
suke koyi da ita har a makarantunsu. Tarbiya ce irin ta musulunci batare da ta fito
zahiri ta tallata musu addinin ba. A fakaice ta rinka kwadaita musu tana fatan
wataran idan da rabo su karba. Farkon zuwanta sun so hanata zuwa da lullubi ko
karamin hijab. A take tace ta bar aikin. To amma amanar da suke gani daga gareta
yasa da kansu suka sake nemota.
Aikin Mami a gidan yana daga cikin abinda Major bazai taba mantawa a rayuwarsa ba.
Wai shi Mustapha da ya kai matakin Major a soja shine matarsa take aikatau. Abinda
yafi karfi a kasarsu yazo lalura ta cinye komai nasa yafi karfinsa. Bashi da
tamkarta a duk duniya. Ya amince samun kamarta sai wata matar sojan. Jarumar mace
matar jarumin namiji.
Katuwar harabar gidan tasha gyara da fitilu da flowers ko ina yana kyalli ga kayan
abinci a gefe debi wanda kake so.
[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 21. Duk dauriya irin ta Ardo sai da ya matse kwalla
ganin yadda hatta mazan kowanne ido yayi jajir.
Mairama ce ta fara magana cikinsu "ina Awwab dan Ummi? Nasan ya girma yanzu? Anyi
masa aure ne?"
Zahra tace "Mami ashe da gaske dai Ummin Hamma Awwab mu bata sonmu"
Mairama sai dariya ta kufce mata ta daga hannuwa ta tashi tsaye tana cewa "Zahra,
kece ko? Ina Fauziyya da Ibrahim abokin fadan wannan yarinyar?"
Fauziyya da Zahra suka matso suna rike hannuwanta tace "kuji min yara yaushe zan
ganeku da hannu kawai, haka ake yi" ta fada tana rungumesu.
Muryar wata shagwababbiya da hausarta ke fita kamar mai waka saboda yadda yaren
Germany da turanci ya kama mata baki taji tana cewa "Daddy ni kowa baya sona, she
even asked for Hamma that is not here"
Ibrahim kallonta yayi ya tabe baki, yarinya yar shekara sha hudu kamar yadda yaji
Mami ta fada sai ta dage tana zuba tabara Daddynta yana biye mata.
Emzee kuwa murmushi yayi bai ce mata komai ba. A gidan Ardo shine karami bai saba
ganin haka ba shiyasa yadda tayi ya burge shi.
Mairama sai ta sake dariya ta rasa ina zata kai farincikin da yake cikin zuciyarta.
"Such a sweet voice, wace ce wannan?"
Zayyana dadi ya mamayeta ance muryarta da dadi ta tafi da sauri ta ture Fauziyya da
Zahra ta shige jikin Mairama tana cewa cikin tsantsar mamakin wannan 'yar kauyen
"Daddy she speaks English too"
Ibrahim ya kwalo idanu a hankali yace "ji min rainin wayo."
Sai kuma suka tsinkayi Radhiya muryar tayi kicin-kicin da fuska tana kallon Zayyana
"ke yarinya iya bakinki wallahi, Ummina ma 'yar boko ce har secondary ta gama ehe"
"Zaki fara ko?" Mairama tace tana zaunawa har lokacin Zayyana na jikinta ba ta
fahimci dogon zancen Radhiyan ba.
"Ai gara na fada mata gaskiya tun wuri kada ganinki a kauye yasa ayi miki kallon
wata local"
Haba wuri sai ya kaure da dariya harda Major. Sai lokacin Mairama ta gama gane su
waye a wurin kunya ta kamata. Halin Radhiya sai ita.
Zainab tana cewa ta zo Mami ma tana kiranta sai ta rasa wurin wa zata je. Zainab
tace "jeki dai dama ita ce mamanki, ni Zayyan zan dauka nafi kama da maman maza"
Rufe fuska tayi da hannuwanta tana kallonsu a fakaice sai wani blushing take
"wallahi kun sani jin kunya...duk sona kuke yi"
Wata dariyar ta basu Mami ta janyo hannunta ta zauna a kusa da ita "haka kika koma
Alheran din Awwab? Wannan idan na wuni dake cikina sai ya kulle"
"Indai wannan ce baki ga komai ba" cewar Innawuro.
Kowa a cikinsu yana cike da tsananin farinciki. 'Ya'yansu ma ko da basu gama sanin
mahimmancin iyayen nasu a wurin juna ba sun amince wannan haduwa ta faranta ran
iyayensu su ma dole su ji dadi.
"Idan kun gama kukan da dariyar ya kamata a gaisa kuma haka" Ardo yace dasu don ya
dakatar da zubar hawayen matan.
Sai kuma aka soma gaisawa ana tambayar yaya bayan saduwa. Mairama ta fuskanci
bangaren da take jin a nan su Major suke ta saki fuska.
"Daddy ina fata duka kuna lafiya"
"Lafiya kalau Ummin Awwab" yace a sanyaye.
Dan bata rai tayi cikin wasa "abokinmu tun shigowarku banji ko tarinka ba, ai
shikenan."
Dif taji shiru ya rasa wurin babu mai cewa komai cikinsu. Hantar cikinta ta kada a
sanyaye ta rike Zainab "ba dai....Subhanallahi, ba dai shima"
Wani irin kuka Zainab ta saka tana jin ciwon lalurar Hadir har kokon ranta. Jikin
Mairama ya gama saki ta sadakar kila shima babu rai.
Radhiya da Emzee sun gane shine akan kujerar amma su din ma basu iya bata amsa ba.
Major ne ya danyi gyaran murya ya soma maganar da kafin ya kai karshe wurin ya sake
rikicewa.
"Hadir gashi nan muna tare sai dai tsahon shekarun nan da bamu tare ya yi su ne da
paralysis sannan baya iya magana."
Sai da ta dan sami nutsuwa daga wannan tashin hankalin abinda yake ci mata rai
shekara da shekaru ta kasa daurewa cikin karyewa da dashewar murya tace
"uhmmm...uhmm nace babansu Karami. Kuna tare ya rasu ko?"
Major da Hadir da dukkansu da suka san labarin abinda ya sami Zayyan daga bakin shi
kowa gabansa ya fadi. Mairama da ba ganin fuskokinsu take yi ba ta cigaba da
magana.
"Ko baku san ya rasu ba ma?"
"Mun sani Ummin Awwab, muna tare" Major ya amsa da sauri.
Ajiyar zuciya tayi harda guntun murmushi "Alhamdulillahi, da hankalina ba karamin
tashi yake ba da tunanin kila ba'ayi masa sutura kamar kowane Musulmi ba. Nace ko
irin mutuwar nan ce ta su da yawa. Ance ramin kawai ake guda daya. "
Major Mustapha shiru yayi ya rasa me zai fadawa wannan baiwar Allah. Allah ne ya
cece shi a lokacin aka fara kiran sallar Magariba Ardo yace kowa ya tashi. Mazan
waje suka tafi wurin masallacin da yake gefen gidan akwai butoci cike da ruwa.
Ibrahim ya dauko daya ya duka a gaban Hadir zaiyi masa. Emzee yana tsaye a gefe
yana ta kallonsa.
"Za kayi masa?" Ibrahim ya tambaye shi yana murmushi.
Murmushi Emzee yayi ya gyada kai.
"Gashi" Ibrahim ya bashi butar.
Emzee ya karba "ka tsaya ka rinka gani kada nayi ba daidai ba"
Da taimakon Ibrahim din Emzee ya yiwa Hadir alwala. Kukan zuci yake yana murmushin
zahiri. Yau dan Zayyan dinsa ne yake masa alwala.
Bayan sun gama ya kuma cewa shi zai tura shi cikin masallacin. Dadi ya kama Ibrahim
don ba karamin ji da babansa yake ba.
Da suka idar da sallah ma Emzee din ne ya sake turo shi zuwa bakin kofar, Ibrahim
sai ya tsaya daga waje ya kama kujerar suka daga shi sannan aka sauketa a kasa
saboda tudun da yake wurin shigar.
"Sunana Ibrahim Hadir"
Takalminsa yake lalube wannan ya bawa Hadir damar ganin fuskarsa sosai yana
murmushi tamkar an ajiye mahaifinsa a wurin.
"Muhammad Zayyan Tureta"
Wani dagen gira Ibrahim yayi "amma Zeezee naji ana ce maka ko?"
Emzee mai wuyar sabo ya sami kansa da kwashewa da dariya "Zeezee kuma kamar wani
mace, Emzee ne."
Ibrahim sai yaji yana son zolayarsa "ni dai kafi min kama da Zeezee haka zan rinka
kiranka"
"To Surbajo babu damuwa"
Hadir yana jinsu yana dariya a hankali musamman da ya ga Ibrahim yaji dadi yana
cewa zai fadawa Umma kakarsa cewa yazo garin Fulani an saka masa suna irin nasu.
Emzee ya gimtse dariyarsa suka koma gidan.
Major ne karshen komawa ya tsaya amsa wayar Awwab da yake ta mita an tafi ba'a jira
dawowarsa ba.
"Idan kaso ranar da ka dawo a tare dasu zaka kwana babu mai hanaka"
Daga daya bangaren Awwab yana kwance a dakinsa na hotel a Austria washegari goman
dare zai sake wani trip din zuwa Germany ya shafi habarsa.
"Duk dadin ya wuce yanzu. Kun hadu da Ummin?"
"Muna rugarsu a Bauchi"
Tashi yayi zaune da murnarsa "ta tuna ni Daddy?"
"Kai ta fara tambaya"
Wani sanyi yaji a ransa don Allah ne shaida bai taba mantawa dasu ba musamman ita
Mairama mamansa ta biyu. Karshen haduwarsu ranar da duka su ukun suke ta kuka daga
karshe ya gane halin da nasa mahaifin yake ciki. A wurinsa yaji rasuwar babansa
Zayyan mutumin da yake matukar so.
"Daddy Alheran fa?"
"Ita ma baka manta da ita ba?"
Dariya yayi, a shekara goma watanni ne babu tsakaninsu. Babban abinda yafi tunawa
da ita shine fada da kuka. Sauran kuwa sai abinda Ummi ta bashi labari. Da kuma
hotuna da ta nuna masa nasu lokacin suna tare. Tabon inda ta taba yakushinsa yayi
dan siririn layi mai dan duhu daga gefen girarsa ya taba.
"Ban manta ta ba Daddy. Ko za ka bawa Ummin waya?"
"Ka kira ta Mami sai ta hadaku"
**********
Duhun dare ya soma kawo rashin wuta ya sa aka kunna fitilun kwai guda uku aka