Showing 3001 words to 6000 words out of 295847 words

Chapter 2 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

Muhammadu ya dawo
ya riski Alheran rai yayi halinsa. Yayi kukan rashinta ba kadan ba. Jume tayi
rantsuwa kwando kwando kan cewa bata ji ko da tari daga dakin Alheran ba. To dayake
abin da tayi ya dameta a rai shine ta dauki Zayyan ta rike. Riko ne dai irin na
matar uba da bata son dan kishiya amma dai duk tsiya tana kulawa dashi. A haka ya
taso gatansa daya mahaifinsa. Maikudi shine babban da namiji a gidan wanda ya
kasance na uku a wurin Jume kuma tashin hankalin gidan gabadaya.
Shekara biyu kenan da rasuwar Mal Muhammadu, Jume da iyalinta suka tattare duk wani
abin arziki suka boye. Dan wanda aka fitar shine aka raba musu tare harda Zayyan.
Sauran Maikudi yaki fito dasu tun ‘yan uwansa suna magana har sun ja bakinsu sun
rufe.

Bashi da kirki ko kadan Jumen ma tsoronsa take ji.
Dakin Jume ya fara shiga daga dawowarsa ya gaisheta. Kamar kullum amsar dai babu
yabo babu fallasa. Haka ya tashi a sabule yana fatan kada ya gamu da Maikudi. Yayi
babbar sa’a kuwa don kwanansa biyu basu hadu ba. A kwana na uku ne Kawunsa Ghoumar
kanin Alheran yazo daga Nijar.

Kafin ya iso gidan ya aika aka kirawo masa Zayyan suka hadu a gidan wani abokin
Mal Muhammadu wanda tare suka sansu a lokacin da suke zuwa fatauci Nijar din.
Zayyan yayi murnar ganinsa sosai saboda ba kasafai yake samun ganin dangin
mahaifiyar tasa ba. A gaban abokin Malam din Ghoumar ya dauko damin kudi ya mikawa
Zayyan.

“Wannan shine kasonka na gadon Alheran. Sai da cutar ajali ta kama Baffanmu ya tuba
ya dawo mana da dukiyar mahaifinmu. A ciki an fitar da kason Alheran shine aka raba
muku kai da Mal Muhammadu bisa doron shari’a”

Kudin Zayyan ya shiga juyawa duk da bai kirga ba ya tabbatar suna da yawa. Ghoumar
yayi murmushi “kasan mahaifinmu yana da rakuma da dabbobi sosai. Sune aka sayar aka
raba naku saboda na sani babu abinda soja zaiyi da rakumi”

Dariya suka yi ya cigaba da yi musu bayanin cewa kason Mal Muhammadu da yake
hannunsa kuma zai kai gidan a lokacin za’a raba shi ne tsakanin Jume da su yaransa
dukkansu. Abokin Mal Muhammadu yace sun zabi bashi nasa a kebence ne saboda sanin
halin Jume da Maikudi. Shawara suka bashi ya tabbatar ya boye domin sun sani wannan
kudi ba karamin gata zai masa ba. A nan hannun aminin mahaifin nasa Mal Aminu ya
bar kudin kafin yayi shawarar me zaiyi dasu. Daga nan suka wuce gidansu tare.

Kamar yadda ya sanar da Zayyan haka Ghoumar ya sake yi musu bayani. Liman aka kira
da wasu malamai biyu suka kasafta kudin tsakanin Jume, ‘ya’yanta shida da Zayyan.
Ana mikawa kowa nasa Maikudi ya tashi yana kumfar baka.

“Yanzu kuke cewa Zayyanu akwai nasa kason a matsayinsa na danta. To kuma banda
tsantsar mugunta me zai sa rabon mahaifinmu a sake kasaftawa dashi?”

Ghoumar ya harare shi “rabon gado ba da ka ake yinsa ba malam. Abu ne da Allah Ya
tsara da kanShi. Zayyan yaci rabon kasancewarsa danta sannan yana da rabo a kason
mahaifinsa”

Rigima ce ta kaure inda Jume da yaranta musamman Maikudi suka dage akan baza’a raba
da Zayyan ba. Da ya ga abin yaci tura yace ya yafe amma Ghoumar da Mal Aminu suka
ce sam sai ya karba.

Tsiya tsiya aka rabu babu dadi. Ghoumar rai a bace yace idan ya kuskura ya basu
wani abu a wancan kudin nasa na shi kadai bai yafe masa ba. Dariya ya bawa Zayyan
ya dai yi masa nasiha da kuma horonsa da rikon zumunci duk da yasan yanayin aikinsa
abin zaiyi wuya.

Suna tafiya kuwa Jume ta kira shi dakinta suna zaune ita da Maikudi sai kumburi
yake shi kadai.

“Zayyanu munyi magana da yayanka tunda kai a bariki kake rayuwa ka bashi kasonka ya
cigaba da juya maka”

Magana ce ta rainin hankali ya gode Allah da wayonsa sarai amma sai ya biye mata
“to Jume amma da na riga na barwa Kawun ne ya yi min kiwon a can Nijar”

Tsuke fuska tayi “kana nufin kai ba kudi aka baka ba?”

“Rakuma ne da dabbobi”

Maikudi ya tashi kamar zai buge shi don zuciyarsa na fada masa karya Zayyan din
yake. Wani kallo mai firgitarwa Zayyan ya watsa masa allurer soja ta motsa. Da
kansa yayi lakwas ya koma ya zauna yana kallon Jume.

“Kina kallo a gabanki yaron nan yake min kallon banza ko Jume?”

Bata kula shi ba ta sake kallon Zayyan fuska babu walwala “abinda za’ayi sai ka
kawo wanda aka baka a gabanmu ya hada ya juya muku din”

A ladabce yace “Gobe da safe in Allah Ya yarda zan je wurin Mal Aminu na karbosu.”

“Shi ka barwa don kana bakinciki da karuwata?” Maikudi yace yana kallonsa shekeke.

Bai tanka shi ba yana sauraron Jume tana fada masa gobe da sassafe yaje ya karbo
kudin ya kawo mata. Daren ranar har bacci ya kwashe shi yana mamakin wannan karfin
hali da iko da aka ki dena nuna masa duk da ya mallaki hankalinsa.

Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke
game da kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano
gidansu Hadir.
[02/11 7:27 AM] My 2nd Mtn: C
Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke
game da kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano
gidansu Hadir.

***********

“Ka koma ka fadawa wadda ta aiko ka na fada na kara ‘yata bazata tafi kwadayi gidan
kowa ba.” Cewar Malamijo yana karkada dan jikinsa duk don ya nuna da gaske fa yake.

Yaron wanda ya kasance kanin Salame da suka hada uwa ya tashi ya bar wurin Salame
na zubar hawaye. Wata tsawa Malamijo ya daka mata ta shi babu shiri jiki na bari.

“Kwalamammiya tashi ki bani wuri. Ku babu mijin babu wata sana’ar kawo dari da
kwabo sai dai aci a cika min shadda da bayan gari. Mtww Kallamu kwoi mugu, ya rinka
rudata sai da na kaiku bokon banza bokon hofi gashi ban ga komai a kasa ba”

Mairama da ke wanki a tsakar gidan ya nuna da bakinsa da yake turawa saitinta “ke
kuma sai bakin hali ba uhm ba uhmm uhmm kinbi kin tsaneni ina mahaifinki. Ko rokona
abu ba kya yi. To duk jarabar mutum dai ba’a sake uba. Nine nan dai uban naki don
ko makaho ya shafaki ya shafani yasan akwai jini. Da namiji kika fito ma sunana zan
maida miki Yasin”

Wankinta ta cigaba tana yi hawaye na diga a cikin bokitin ta jiyo muryar Yadikko
daga dakin girki.

“Ka dai ji kunya Malamijo, kana abu yana damunka shine ka rasa da wadda zaka rinka
wannan magana kamar wata sa’arka sai ‘yar cikinka. Rashin roko tayi min daidai.
Masu yi din banda bakar magana me kake tsinana musu bayan sun gama keta billensu”

Hularsa ya turo gaban goshi a karkace “mutum dai ya shiga taitayinsa dani don ni
dadewa bazata sa na kasa sallamar ‘yan hamayya ba”
Daidai nan Nene kanwarsa da ta kawo musu ziyara daga wani kauyen Gaya inda take
aure ta idar da sallah. Magana take da niyyar yi masa akan yadda yake yi da gidansa
duk da dai ba yau farau ba suka ji an banko kofar gidan.

Ta Madina ce babar Salame ta shigo ko sallama babu “gani nazo da kaina a bani ‘yata
Malamijo ko in nuna maka ba kai kadai aka haifa a watan tijara ba”

Tuni tsakar gidan ta kaure da ‘ya’ya da matansa an fito kallo. Salame jikinta har
bari yake tana kuka.

“Yanzu ke baki ji kunyar shigo min gida ba? Koda shike naji labarin yanzu ma
zawarci kike kina neman mafaka”

Daga murya tayi cikin fada ta nuna shi da yatsa “Ali ba tsoronka nake ji ba. A bani
‘yata biki zamu na ‘ya’yan ‘yar uwata a Kano”

“Bazata ba” yace a takaice.
Fada Innar Salame ta soma yi Nene ta sa baki “Ke Salame wuce ki hado kaya kizo ki
bi mahaifiyarki. Malamijo idan baka bari yaran nan suna rabar dangin iyayensu mata
za’a sami matsala nan gaba”

Wani karkataccen kallo ya bita da shi kafin ya kada baki yace “ke da kika lallabo
cin arziki ina ruwanki da iyalina bayan baki san zafin haihuwar ba?”

Jikinta ne yayi sanyi ta dukar da kai “Malamijo ni???”

Shima sai yaji nasa jikin ya saki don kuwa yana ji da Iyalle ko a cikin dangi “ba
haka nake nufi ba. Ke Salame zo ki bi uwarki kuma sati guda na bada aka dara ban
yafe ba”

Innar Salame tana tsaye tana karkada kafa daya tana jiranta ta fito. Mairama tana
rakube a jikin bango wurin da suke shanya tana jin inama ita ce zata je wurin
dangin tata mahaifiyar. Sai dai ina zata sami wannan damar. Mutanen da suke fulanin
tashi basu nan basu can. Auren ma da Innarta anyi ne kawai saboda sauke bashin da
Malamijo yake bin babanta a lokacin. Hangota Innar Salame tayi sai taji yarinyar ta
bata tausayi.
“Mairama kema ko zaki bimu ne?”

Malamijo yayi wani tsalle sai gashi a gaban Mairama “wannan kuma kinyi tsararo Ta
Madina, babu inda zata je”

Iyalle da kanta tazo taja hannunta ta kaita dakinsu “hada kayanki ki bisu zanyi
maganin abin”

A tsorace Mairama ta hada kayan saboda gudun kada ya hanata tafiya. Basu dade ba a
dakin Yadikko ta kwala musu kira suka tafi dakinta.
“Ni da Nene mun roka muku alfarma ya bari kuyi kwana goma. Idan kunje ku tabbatarwa
da kanku bazaku wuce lokacin da aka dibar muku ba”

Murna a wurin Mairama kai kace bikin na dangin tata mahaifiyar ne. Salame kuwa har
ta gama tsoro bai bata damar sakin jiki ba.

Da zasu tafi kashedi Malamijo ya rinka yanka musu kusan minti goma yana abu daya.
Nene da Yadikko sunyi masa shigar sauri sun kuma hade masa kai ba don haka ba Ta
Madina bata isa ya bata Salame harda karin Mairama ba.

**********

Kano ta Dabo tumbin giwa, birnin na Kano a yau yayi manyan baki daga garin Sumaila
wato Salame da Mairama. Wata unguwa da basu san sunanta ba suka wuce zuga guda ta
‘yan biki daga Sumaila. Yadda Mairama ta saki jiki cikin mutanen sai ta baka mamaki
da tausayi. Tun tasowarsu ita dai bata taba zuwa wani wuri da zata ji dadi da
sa’anninta ba sai makaranta. A can ma ba wani sakin jiki gareta ba saboda tana
ganin kowa yafi karfinsu. Gasu dai da uba mai kudi amma daga kayan makaranta da
akwati baya basu komai. Dan siyayyar nan ta provision sai dai su gani a kwanar
wasu. Shiyasa an rainasu sosai musamman Salame da sunanta ya dace da halinta.
Anyi Kamu a ranar da suka sauka da daddare inda amare aka kunshesu a daki tsakiyar
‘yan mata kawayensu da ‘yan uwa, dangin angwayen su ka zo aka feshesu da turare.

Washegari kuwa lanchin (luncheon) za’ayi a filin wani katon gida mallakar kanin
baban amaren biyu.

Salame ta sami kaya kala biyar sababbi, biyu daga yayar innarta uwar amare sai uku
daga Ta Madinan. Guda ta cire a ciki ta baiwa Mairama tace ta saka kada ta fita
daban tunda su dai ba wasu suturun arziki na shiga taro garesu ba. Mairama sai
murna da godiya ta sanya atampar da akayi mata dinkin riga da zani buba anyiwa
rigar cin baki da irin lace dinnan na adon kaya a wuya da hannaye. Tayi kyau abinta
gwanin sha’awa haka itama Salamen. Motoci bus bus ne aka haya suka rinka kwasarsu
aka kaisu wurin bikin.

Salame tana manne da kanwarta duk da cewa dai tana sakin jiki da ‘yan uwanta suna
hira. Teburinsu su bakwai ne da yake a zagaye yake suna fuskantar juna ana ta
tsokanar wata cikinsu da tayi saurayi daidai kofar shigarsu gidan. Karaf idanun
Salame suka sauka akan Zayyan ya nisa suna magana mai matukar mahimmanci da Hadir.
Daya daga cikin angwayen dan uwa ne ga Hadir din.

Iyayensu maza ciki daya suka fito. Shiyasa da Zayyan ya iso Kano aka sanya shi
cikin abokan ango. Cinikin fili suka gama kafin zuwansu nan a unguwar gandun
albasa. Shi dai Zayyan ya ga wurin babu gidaje sosai amma dillalin yana ta cika
masa baki cewa nan gaba kadan unguwar zata hade harma a rasa filin saidawa. Shima
da yake ba mazauni ba sai ya amince ya biya kudi bisa shawarar Hadir. Zancen gini
kuma a hankali zasu yi tunda har yanzu ko rabin kudin da aka bashi bai taba ba.

Takardun filin ne kwafi biyu da sa hannayensu ya mikawa Hadir daya yace gata nan ya
ajiye masa shi kuma zai aje daya a wurinsa. Sai da suka gama komai duk motsinsa
akan idon Salame sannan su ka koma cikin samari ‘yan uwansu. Ba karamin tafiya yayi
da imanin Salame ba lokaci guda taji sonsa ya game zuciyarta.

Mairama kuwa an sami sake hira tayi hira an kawo abinci kowa plate dinta shake da
jallof din shinkafa da yankan naman sa da aka soya sai salad, tumatir da albasa.
Wayyo dadi jikinta har tsuma yake kuma wai aka kirga su aka sake ajiye musu ledar
tsire ga kuma lemon kwalba. Kar kaso ka ga idanun Mairama hankalinta yayi kwano na
Salame kuma yayi kan Zayyan da bai san da zamanta a wurin ba.

Police band suna wakarsu amma kusan kowa abinci yake ci babu ‘yan rawa. Kwalbar
fanta chapman Mairama ta faki ido ta daga tana kwankwada asalin dadi da sanyi yana
ratsata ta manta da kunyar idanun jama’a. Bata samu ta sauke kwalbar mai 35cl ba
sai da ta shanye shi tas. Daga lokacin da ta soma waige ta tabbatar babu mai
kallonta har zuwa sanda ta ajiye kwalbar Zayyan yana gani. Baki ya rike yana kallon
yadda ko da ta shanye sai da ta sake daga kwalbar ta kwakkwafeta a bakinta. Kasa
cin nasa abincin yayi komai tayi sai yaji ya burge shi shi kadai ya rinka murmushi.
Teburin kusa da nasu Mairama ne duka matan dama su uku ne su ka tashi a tare.
Mairama tana ji suna cewa sallama zasu yiwa amaren su tafi. Tana ganin sun bace
cikin jama’a ta wayance ta tashi da kwalbar lemonta ta ajiye a wurin ta dauki wata
mirinda da ko rabinta ba’a sha ba. Plate din nasu ma basu wani ci sosai ba ga nama
sun bari. Kamar ta dauka shima sai dai ta hakura lemon yafi mahimmaci a gareta.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: D
Banda wanda ta dauka sai da ta dan kurbi na kusa dashi sannan ta juya da sauri da
taji ana kiran sunanta.

Hadir ya tabo Zayyan da yake kyakyata dariya shi kadai da ya hango Mairama tana
zaro idanu. Matan da suka bar teburin ne suka dawo daya ta soma cigiyar lemon da ta
bari. Mairama tayi tsit don kuwa saura kadan ma ta shanye mirindar.

“Kai lafiyarka kuwa?”

Idanu ya lumshe yana kallon kyakkyawar bafulatanar ta tsure karshe ta kuma rungume
kwalbar ta boye cikin lullubinta.

“Mata nayi”

Hadir ya tura kujera baya da sauri “nuna min ita muje mu tsarata wallahi”

Zayyan ya mike da sauri “naki din, kai fa satar budurwa kake yi”

Sauran mazan wurin suka sa dariya shi kuma ya kwashe lemuka uku da ba’a bude ba
yayi gaba.

Salame tana ganin ya nufosu ta tattaro dukkan nutsuwarta tana murmushi don tun dazu
suke hada ido yana murmushi a zatonta ita yake yiwa yayin da hankalinsa kacokan
yana kan Mairama ne.

Sallama yayi musu matan teburin gefen ana ta masifar rashin ganin lemo ya mika musu
biyu sanna ya dubi Mairama da tsoro ya hanata motsi ya mika mata chapman irin wadda
ta fara sha. Dan rausayo kai yayi ya duku wurin kanta.

“Kanwata ga wannan ki kara”

Sai lokacin ta dena jin mitar wadancan matan ta tsuke baki batare da ta juya ba

“rike kayanka bana so”

“Haka ma zaki ce? To ki shirya kuwa don zan tona” yace yana rage murya sosai daidai
kunnenta.

A firgice ta waiga idanunta suka sauka cikin nashi. Ko ma me tayi niyar cewa
makalewa yayi a wuyanta ta sami kanta da manta a ina ma take na ‘yan dakiku.
Lallausan murmushi ya sakar mata wanda ya sake fito da kyaunsa da cikar sa.

“Muje can na fada miki me da me na gani” ya nuna can jikin katanga wurin wata
katuwar bishiyar darbejiya.

Ko dogon nazari bata tsaya yi ba ta bi bayansa kuwa don ta gama tsorata kaddai ace
ya ga lokacin da ta dauke musu lemon. Wani mugun daci ne ya taso ya tokare wuyan
Salame har suka isa bakin bishiyar tana binsu da kallo. Me yake shirin faruwa
tsakanin kanwarta da mutumin da take jin bata taba son wani abu makamancinsa ba a
rayuwarta. Kallon da yake yiwa Mairama kadai ya isheta amsa. Sauran ‘yan mata kuwa
sai shewa itama zasu kwana suna tsokanarta kenan.

Suna isa wurin bishiyar yace “da farko dai sunana Zayyan, ni soja ne”

Idanunta suka yi kwalkwal da hawaye suna barazanar saukowa. Murya na rawa ta fito
da kwalbar da ta boye cikin mayafinta “me yayi zafi ni ‘yasu. Daga shan lemo sai
dauko sojoji. Ni wallahi nayi zaton sun tashi kenan. Don Allah kuyi hakuri kada ka
kamani” tace tana kallon Hadir da ya iso inda suke.

Maganarta dariya ta bashi ya mikawa abokinsa hannu da nufin gabatar dashi a gareta
“Zayyan Tureta…”

Wani kallo ta watsa masa tsoron yayi nasa wuri ta yatsina fuska za ta gwada musu
tsiwarta “ya tureni? To Bismillah dan halak ka fasa. Mutum ya tabani ba hakura
zanyi ba”

Kasa cewa komai suka yi sai dariyar da suke yi mata tana karkada hannuwa. A ranta
tana jin tsoronsu zaratan samari irin haka amma kuma bata so ta basu damar cutar da
ita.

“Kinga ‘yan mata sunansa Zayyan Muhammad Tureta ba tuureta na hankadewa ba, garinsu
ne a Sakkwato”

Kunya taji sosai ta rufe fuska “lahhhhh”

Shima Zayyan sai ya biye mata yace “lahhhhh”

Hadir yana dariya ya basu wuri Zayyan ya kura mata ido “yaya sunanki”

“Mairama” ta amsa da karamar murya.

“Kamar Maryam yake?”

“Haka dai aka saka min a gida ni”

“To fillo ni dai Mairam zan ce. Ina ne gidanku?”

Kallonsa tayi na dan lokaci tana son yin nazari shin kamata zaiyi ko kuwa dai wani
abin ne daban.

“Ba kamani kazo yi ba?”

“Kwantar da hankalinki babu mai sanin kin saci mirinda”

Yadda yayi maganar yana kasha mata ido ya sanya hankalinta ya kwanta itama harda
dariya. Kwatancen gidansu ya nema daga gareta da bayanin kansa sannan yace duk da
karancin lokaci yana son ganawa da mahifinta domin ya nemi aurenta. Kunya sosai ta
lullube Mairama don itama a ‘yar hirar tasu har ya shige zuciyarta. Ta fada masa
gidan da suke yanzu da kuma kwatancen gidansu yace zai zo da daddare su sake
fahimtar juna.

Kusan da gudu-gudu ta koma teburinsu ‘yan matan suka soma zuba mata tambayoyi. Jiki
na rawa ta fada jikin Salame tana dariya.

“Bazaku ji komai ba sai ma gama shawara da Addata”

Wani murmushin yake Salame tayi a ranta tana nadamar tahowarsu da Mairama. Ita kuwa
dadi ya cikata ta fada mata yadda suka yi.

Cikin gatse tace “kice dai wannan tafiyar taki ce”

Bata fahimta ba shiyasa tayi murmushi “gaskiya tawa ce, yace zai tambayi gidan da
muke sai yazo anjima. Ai tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login