Showing 132001 words to 135000 words out of 295847 words

Chapter 45 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

zaman lafiya dasu.


"A yau zan koma Katsina in sha Allah babban kakanmu ya dawo jiya bamu hadu ba na
taho. Ina komawa zan fadawa Daddy komai don ya fada masa"


"To" yaji tace muryarta tana rawa. Tun ba'aje ko ina ba tasan cewa tana da kishiya.


Zoben da yake karamin yatsansa na farar azurfa mai matukar kyau da harafin A an
rubuta cikin kayataccen rubutu ya cire ya dora mata a tafin hannunta "a hannuna
yana nufin Alheran, da sunanki na saye shi da albashina na farko. Amma yanzu
sunansa Awwab. Don Allah ina rokonki kada ki bawa kowa chance din neman aurenki. I
know naso kaina da yawa amma nayi haka ne don kada wata rigima ta tashi da zata
shafi iyayenmu."


Son zuciya daban, zahirin rayuwa daban. Tana da kaifin tunanin taya shi hango
faruwar abu mara dadi a danginsu idan ya guji 'yar uwarsa ta jini saboda ita. Wani
girma ne na musamman taji ya bakunceta ta kara karfafa zuciyarta. Murmushi tayi
masa bayan ta goge hawayenta duk ta dame idanunta da hijab din da kwalli.


"Kin amince?" Ya sake tambayarta yana kallon kwayar idonta da nasa jajayen idanun
da damuwar tsoron rashin amincewarta ta haddasa.


"Eh"


"Zaki jirani?"


"Eh"


"Babu ke babu Kawu Zakari da sauran sojoji da likitoci fa"


Dariya suka sa a tare ta sake cewa "eh"


"Do you love me?"


Nauyin maganar taji ta dukar da kanta "eh"


"Say it" yace cikin muryar umarni.


Kafada ta noke tana dariya kasa-kasa "ni dai bazan iya ba"
"Zan kira ki fada min a waya"


"Idan Ummi taki bani fa"


"Rufe idonki ki ga wani abu"


Rufewa tayi ya fito da wayar da ya saya mata taji karamar kara ta bude ido daya a
daidai lokacin da ya sake daukarta a hoto.


"Mu gani, nayi kyau?" tace a kagauce tana son ganin yadda hoton yayi.


"Kin bata min hoton da kuka. Da a haka zakiyi sojan abu kadan kuka?"


"Kaine kake sani kukan nan amma ni bana kuka"


"Na soyayya ne so ba damuwa, bazan baki hakuri ba ma" yace yana dariya.


Kallonta yayi ta sanya zoben a yatsan kusa da karamin ta dago masa hannunta tana
tambayarsa ko yayi mata kyau. Ya yaba sosai ya ja mata kunne akan kada ta taba cire
shi wai na alkawari ne. Wayar ya mika mata taki karba wai Ummi zata yi fada.


"Kinsan da ita na fake na taho garin nan da kunya mu koma tare. Muje na kaiwa Ummin
da kaina a baki. Daga nan har na koma aiki sai kunnenki yayi ciwo da wayata"


"Idan baka kira ba ma kuka zanyi"


"Seriously? Kina sona haka"


Bata iya amsa masa da baki ba sai kai da ta daga cikin farinciki mara misaltuwa.


**********


A cikin gidan Alh Baba mahaifin Ghazalatu ya danyi karamin gini mai daki biyu,
toilet biyu da kitchen saboda iyalinsa idan sun zo gari. Ana gobe zasu dawo daga
Umara Gambo da sauran yaran nasu suka iso. Ghazalatu ma komawa tayi ta tayata
gyare-gyare. Ana gobe Awwab zai taho wurin Radhiya cikin dare suna hira da mijinta
ya sako zancen Ghazalatu.


"Ki duba ki gani sa'ar Fauziyya ce gashi suna shirin aure ita sai taron abokai babu
wani tsayayye. Tafiyar nan Alhaji kusan kullum sai yayi min fadan wai mun
sangartasu gashi bai ji wata magana game da aure ba"
Murmushi ya ga matar tasa tayi ya tsaya yana bin ta da kallon mamaki.

"Ko gobe kana iya fadawa Alhaji ya fara shiri anyi masa kwacen mata"


"Ahhh garin yaya labari ya wuceni?" Yace cikin farinciki.


Nan ta labarta masa yadda suka yi da Awwab ranar da ya dawo. Shiru Daddy Haroun
yayi har Mummy ta fara tunanin ko zai ce ita ta hada.


Da sanyin jiki tace "Babu hannuna fa a ciki Daddy, wai ashe shiru suka yi 'yar
banzar yarinyar nan tace sai ta gama makaranta."


"Abinda ban gane ba shin Awwab din Major kike nufi ko wanne?"


Gambo da saurin fushi ta soma harzuka "Awwab nawa garemu? Idan baka so ne sai inji
saboda dan yayata ne kake kinsa ko me"


Ya san halin matarsa da saurin hawa kamar farashi kuma dai daga dawowarsa bai
shirya rigima da ita a wannan daren ba.


"Idan Hassana yayarki ce ni kuma ko ban aureki ba kin san dai kanwata ce. Akwai
maganar da naji game da Awwab din ne shiyasa kika ga haka amma gobe dama munyi da
Major zai zo muyi magana da Alh Baba sai mu fara clearing issue din"


"Wani abu ne ya faru da Awwab din?"


"Kinsa batun matar nan da yaranta da yake ta damuwa dasu iyalin sojan da suka je
Liberia tare?"


"Sosai kuwa, Ghazalatu ma har gidan iyayenta taje ta kwana. Shine tafiyar da nace
maka sunyi da Mami din"


"Yarinyar wajenta Major yayi min magana akan yana son hadasu da Awwab. Gobe zai zo
a gaban su Baba Karami ya gabatar da zancen domin aje ayi magana da iyayensu. Ni da
kaina na fara sanar dashi tun a saudiyya"


Ko a jikin Mummy Gambo wannan bayani "rashin sanin tsakaninsa da Ghazalatu ne ya
janyo amma tunda yanzu sun fada ai shikenan"


"Idan kuma ya riga ya fadawa iyayen yarinyar fa?"


"Sai aje a basu hakuri. Daddy ba wani abu bane ba fa na tada hankali don Allah."

**********
An wayi gari Major yana shirin tafiya gidan Alh Baba inda zai hadu da nasa
mahaifin, baban Mami da ake kira Baban Biyu saboda sune manya a 'ya'yansa don bai
sami haihuwa da wuri ba sai da ya auro mahaifiyarsu. Cikon na hudun nasu suna
Germany ya rasu kuma bisa umarnin Alh Baba jikokinsa biyu daya na wurin mace dayan
kuma na namiji za'a aurawa Zahra da Fauziyya.


Mami ke fada masa tafiyar Awwab din da ya sulale ya gudu Sumaila duk da Major ya
fada masa zasu je gidan Alh Baba da ya dawo daren jiya. Dadi yaji har ransa "kice
ko yau aka bukaci sadaki na mika kawai. Allah Yayi musu albarka. Sun gama min
komai"


Amare Zahra da Fauziyya sun fara gyaran jiki. Wata mata ke yi musu anan cikin
gidan. Da Major zai fita sai Zayyana kadai a falo itama zaman jiransa take yi.
Hajiyar shagwaba ta rinka marairaice masa wai ya bata kudi Ibrahim yace mata anayin
kanwar amarya day jiya da suka yi waya.


Dariya yayi harda kyakyatawa "shi Ibrahim din da kansa ya fada miki haka?"


"Eh Daddy don Allah ka bani kudin yadda za'ayi min nawa invitation card din"


"Kece amaryar?"


"Nice mai gayyata amma kuma bani da outfit da zai dace. Please Daddy"


Hularsa ya cire ya dan sosa gaban kansa. Yanzu idan yace mata ba'ayi da wahala ta
yarda. Ta rinka jero masa tambayoyi kenan shi kuma fitar ce a gabansa.


"Jeki ki fadawa Mami kuyi shawara kafin na dawo"


"Thank you Daddy" ta rungume shi tana murna sannan ta wuce sakin Mami.


Daddy Haroun da Gambo ne karshen zuwa falon na Alh Baba. Sun shigo Major yana
gaisawa da surukansa Bilal wanda zai auri Fauziyya da Fawaz mai auren Zahra. Su
dinma zuwansu kenan yiwa Alhajin barka da dawowa. Suna fita bayan gaishe gaishe
tsakanin su Mummy Gambo da iyayensu ta tashi ta koma bangarensu.


Falon akwai 'yan uwansu maza manya wadanda duka tushensu daya ne banda iyayen nasu
guda uku. Hira suka taba kadan ana tambayar iyalan juna da dan abinda ba'a rasa ba.


"Mustapha" Alh Baba ya kira Major wanda ya tattaro hankalinsa ga uban nasu "Dan
uwanka yayi min zancen akwai yarinya 'yar wajen abokin aikinka da kake son hadawa
aure da Muhammad ko?"


"Eh Alhaji"
"Major nace me zai hana mubi abin a sannu kada a takura yaron nan saboda son kara
kulla zumunci azo a bata shi"

Daddy Haroun yace saboda yana bukatar damar kawo zancen Ghazalatu.


Murmushi Major yayi "in sha Allahu wannan matsalar ina tsammanin ta riga ta kau.
Maganar da nake maka yana hanyar Sumaila zai je wurin yarinyar"


Baba Karami shine mahaifin Major kuma ya fada masa komai kafin ya kawo zancen nan.
Murmushi yayi irin na dattijai "to idan sun hada kansu Alh Baba ina ganin ba sai an
tsaya bata lokaci ba ko yaya kace?"


"Kwarai kuwa, ya kamata ya ajiye iyali hakan ne zai sa ko ina yaje gida zai nufo ba
yawon kasashe ba"


Daddy Haroun sai ya rasa yadda zai bullowa lamarin. Kafin ya fito sai da ya
tabbatar da magana daga wurin Ghazalatu. Shirun ba zai zama alkhairi ba kada aje
ayi hukuncin da zai jawo matsala a gaba.


"Jiya Gambo take fada min Awwab din da Ghazalatu sun daidaita kansu ashe. Ina ganin
me zai hana mu jira ya dawo aji ta bakinsa"


Murmushi sosai Alh Baba yayi yana nuna farincikinsa bisa yadda al'amura suka
kasance. Lallai ba karamin kara hade zumunci za'ayi ba idan akayi wannan auren
saboda iyayensu duka 'yan dangi ne.


"Wannan shine tuwo na mai na" inji Baban Biyu.


"Kai da baka san da wannan din ba kake kokarin nema masa auren wata?"

Baba Karami ya tambayi Major wanda zancen gabadaya yazo masa a bazata.


"Wallahi ban sani ba Baba"


"Tunda abu yazo da haka Mustapha ita waccan yarinya a barta. Ko bai aureta ba daga
ko ina zaka iya tallafawa rayuwarsu. Idan yaso sai ya auri kanwarsa" Baban Biyu
yace yana bin 'yan uwansa da kallo domin neman amincewarsu.


Hankalin Major tashi yayi sosai bai taba zaton da faruwar wannan lamari ba. To
garin yaya shi bai sani ba kuma Mami ma baya tsammanin ta sani.


"Gambo cewa tayi tana so a hadasu ko sun hada kansu ne? Wallahi ni ban taba jin
zancen ba. Babarsu ma bana jin ta sani"


Daddy Haroun sai ya ga tambayar kamar yana nufin kirkira suka yi shi da matarsa sai
yaji ransa ya sosu "ba wani abu ne na jayayya ba Major, tunda da alamu kafi son ya
auri ita waccan yarinya sai ayi haka din."


Sassauta murya Major yayi duk kuwa da cewa nasa ran har yafi na Daddy Haroun baci
"ba zamuyi haka ba, mamaki kawai nake yi nace ban sani ba amma ba wai na karyata
bane."


"Duk da haka ya auri wadda ka zaba masa tun farko ita Ghazalatu ayi maganarta daga
baya idan ta sami wani"


"To iyayen 'ya'ya. Idan kun gama yanke baku hukuncin sai ku saurari nawa. Mustapha,
Haroun, nawa hukuncin shine Muhammad zai auri Ghazalatu. Ita kuma wannan yarinya
tunda bamu riga mun shiga ciki ba Allah Ya bata wani. Bazan so wata baraka ta taso
a cikinku ba saboda wannan dalili. Hakan yayi ko?" Ya juya ga Baban Biyu da Baba
Karami. Duka su biyun sun nuna amincewarsu.


Major bai yi shiru ba duk da haka saboda ance mai daki shi yasan inda yake yi masa
yoyo. Shine yasan Zayyan kuma shi yasan me yasa yake kwadayin hada alakar auratayya
a tsakanin zuri'arsu. Burinsa su dunkule ta yadda ko bayan ransu a gaba zuri'arsu
zata zamo daya. Wannan shine tanadinsa ga Awwab kamar yadda yadda yake da kudirin
hada Ibrahim da Zayyanatu.


"Alhaji ku gafarceni ban tari numfashinku ba. Ina neman alfarmar don Allah a bashi
damar hadasu duka. Yarinyar da nake magana a kai Radhiya ban baro kakaninnta ba sai
da nayi musu alkawarin hadata aure da Awwab"


"MUSTAPHA!!!"


Baba Karami ya daka masa tsawa da kakkausar murya. Duk cikin iyayen nasu ma shine
mara fada amma yadda ya kira sunnan dan nasa ya bashi tsoro.


"Alh Baba ya yanke hukunci, mu mun amince sai kaine da ka haifi Muhammadu kake son
nuna mana iyakarmu? Da can wane dalilin ne yasa kayi musu alkawari batare da kayi
shawara da kowa cikinmu ba?"


"Ku gafarceni Baba in sha Allahu yadda kuka ce hakan za'ayi. Zanje na basu hakuri."


Babu abinda Daddy Haroun bai sani ba game da labarin dan uwan nasa shiyasa yaji
tausayinsa da yace ya riga ya fadawa iyayenta. Ai da kunya ace kuma ya koma yace
musu an fasa "Baba don Allah kuyi hakuri kada maganar nan ta janyo rikici. A bar
Awwab ya auri yarinyar. Ghazalatu kuma ko cikin 'yan uwa sai a sama mata wani"


"Ka bar wannan magana Haroun in sha Allahu Ghazalatu zai aura. Zanje nayi musu
bayani"


Alh Baba ma nasa ran ya soma baci yace "nace na gama magana kuma nan da wata uku
za'ayi auren. Idan ya dawo ka turo min shi. Ku tashi ku tafi kuma kada ku yarda
maganar nan ta kai kunnen iyalanku. Biki ne dasu ku barsu su gama a nutse bana son
kananan maganganu"


Sun fito Major ya rasa abinda yake yi masa dadi. Daddy Haroun yana son farincikin
'yarsa ta wani bangaren yana duba cikin tsakar da dan uwansa zai shiga. Jikin motar
Major suka tsaya drebansa ya taso da sauri Daddy yayi masa alama da ya basu wuri.


"Major ka bani lokaci zanyi magana da su Alhaji. Babu girma ka koma ka cewa mutanen
nan an fasa ko abu makamancin haka"


Murmushi yayi kansa ya kulle yana neman mafita "ka bar maganar, nine nayi abu bisa
rashin sani dama saboda haka zanyi kokarin daidaitawa. Tunda sun hada kansu da
kanwarsa bamubda dalilin cewa wani ya hakura" yayi maganar da tunanin cewa idan da
gaske hasashen Mami akansa da Radhiya gaske ne ita za'a ce ta hakura kenan saboda
ita ba danginsu bace? Kuma da kunya matuka ya kalli idon Daddy yace tasa 'yar ta
hakura.


"Mafi dacewa Major ya auri su biyun. Ka sa min ido zan sake magana dasu."


Shima Major yayi wannan tunanin to amma yanayin aikin Awwab din anya auren mata
biyu lokaci guda zai haifar musu da da mai ido kuwa? Kansa yaji ya soma sara masa
yayi sallama da Daddy Haroun ya shige mota domin tafiya gida.


A hanyar ma dai tunani yake ta yi yana neman mafitar da ta dace. Iyayensu idan ya
koma garesu ma bai san me zai ce dasu ba kamar yadda bai san me zai ce da iyayen
Radhiya ba.


Gajeren tsaki yaja a lokacin da ya dauko waya ya fara laluben nambar Awwab. Gara
dai yaji ta bakinsa kafin yasan me ya kamata yayi kuma.


**********


Ayuba yana zaune gaban Ummi Mairama ya gama yi mata addu'a yana tofawa idanun yace
"Adda Mairama anya ba sihiri bane wannan makantar? Ciwon kan nan da kike ji tun
jiya sai nake ganin kamar addu'armu ce take ci."


"Allah Yasa Ayuba, amma ni kuwa waye ya tsaneni haka da zai yi min asiri?"


Roba biyu ya yiwa tofin ayoyin tsari da neman sauki ya kuma tofa mata a kan
fuskarta sannan ya tashi zai fita.


"Ka turo min yarinyar nan bana jin ko abinci ta baiwa Awwab sai suru....suruuuu"
wani irin haske ne wal ya shiga cikin idonta ga alamun mutum tana gani sai wani
matsanancin ciwon kai kamar an kwada mata guduma. Rike kan tayi da hannuwanta biyu
sosai tana ji kamar zai fadi.
"Ayuba....wayyo Allah kaina Ayuba"


Da sauri ya dawo gabanta ya durkusa sai dai ciwon da take ji yayi tsananin da ya
sumar da ita. Ayuba ya hanzarta fita yana kiran su Yadikko a lokacin Radhiya da
Awwab suke tahowa dakin zai bawa Ummin wayar da ya siyo taki karba suka ga ana
tururuwar shiga dakin ana cewa Mairama ta suma. A guje Radhiya ta shiga ta samu ana
shafawa Umminta ruwa a fuska amma ko motsi bata yi. Kuka ta saka Awwab yace su fito
da ita zai je ya matso da mota kofar gidan. Shima a kidime yake musamman ganin irin
kukan da Alheran dinsa take yi.


Ayuba yana ganin haka yace su kyale masa ita su matsa gefe. Radhiya dai babu inda
zata je sai ma kan Ummin da ta dora akan cinyarta. Da alwalarsa dama ya dauko
littafi mai tsarki ya bude suratul Baqara ya soma karantawa yana yi ya umarci
Radhiya ta rinka shafa mata ruwan tofin nan. Atishawa tayi mai karfi a hankali ta
soma bude idanuwanta wanda suka sauka akan fuskar 'Yar Soja Alheran 'yarta da
Zayyan. Murmushi tayi ta daga hannu ta shafa fuskar Radhiyan wadda bata gane me
yake faruwa ba sai da taji tace.


"Ashe ma na fiki kyau"


Tana kuka tana dariya tace "Ummi kina ganina? Me nake yi yanzu?" Ta murguda bakinta
gefe yayin da Awwab ya dawo ganin me ya hanasu fitowa.


"Hmmm bakin tsiwar kenan ake murguda min"


Wata wawiyar runguma Radhiya ta kai mata tana murna. Kowa a dakin sai san barka.
Ayuba kuwa cewa yake kuyi ta kabbara yau ko waye ya yiwa Adda Mairama asirin nan
Allah Ya dandana masa abinda taji.


"Malam da kanka?" Inji daya daga cikin amaren da za'ayi bikinsu nan da 'yan
kwanaki.


"To na janye...mu godewa Allah da wannan ni'ima da Yayi mana. Da kaina zanje wurin
Malamijo a gona nayi masa albishir"


Dariya suka yi Ummi tana binsu daidai da taimakon murya tana ganesu. Kyakkyawan
matsashin da ta gani a jikin kofa yana murmushi fuskarsa mai cike da annuri ta
yafito da hannu.


"Haka Awwab dina ya koma"


Hannunta ya kama ya rike gam ya kalleta ya kalli Radhiya da nata bakin itama yaki
rufuwa. Wayar Ummin tasu ta dauka cikin hanzari ta kira Emzee ta fada masa wannan
daddadan albishir.


"Ki taimaka ki rufe fuskarki da zani sai na dawo ta ganmu tare" yace yana fita daga
dakinsu zuwa falo ya fadawa Mama Zainab.
"Sorry yaro ni ta fara gani"


"Bata wayar"


Ummi na karba ya soma rokon ta rufe ido ta bar ganin mutane haka sai ya dawo.
Dariya dan nata ya bata. Sun gaisa da Zainab tace zata turo su a yau don bata jin
Karami zai iya bacci.


Awwab ma Mami ya fara kira ya fada mata sannan ya kira Major da yake hanyar komawa
gida daga gidan Alh Baba.


"Ina ka shiga ina ta kira tun dazu?"


Hakuri ya fara bashi sannan ya fada masa abin alkhairin da ya faru "ina isowa na
kiraka nima"


"Na gani ina tare da Alh Baba ne."


Murnar budewar idanun Mairama ta hana shi tambayarsa meye tsakaninsa da Ghazalatu.
Zai jira shi ya dawo din sai suyi magana. Sai dai ciwon kan da take ji wanda da
alamun haske ne yayi mata yawa ya fara addabarta. Awwab yace gara a kaita asibiti
ko akwai abinda zasu bata.


Shi ya kaisu asibitin suka bata magunguna aka koma gida. Hudu har gota Ummi tace
yayi hakuri da tafiyar sai da safe. Abinci aka kai masa tsakar gida wurin Malamijo
sai ga Radhiya ta tazo tace ciwon kan na Ummi ya sake tashi ko bude ido ta kasa.


"Ko dai babban asibiti zaku kaita. Dama can fa tana da lalurar idanun kafin wannan
makantar" cewar Nene Marka.


Rabon ayi komai da Awwab yazo Sumaila a ranar. Nene, Ummi da Radhiya ya dauka suka
nufi Kano domin a samu ta ga babban likitan ido.


**********

Maza ne manya manya majiya karfi masu kirar da kai tsaye zata razana mutum su biyu
aka budewa kofar karfen da mukulli ne kadai zai iya budeta saboda tsananin
karfinta. Mutum hudu suka tarar a ciki kowa da katifarsa a jikin bango. Uku hira
suke a junansu cikin wani yare yayin da cikon na hudun yake zaune ya tankwashe
kafafunsa akan katifar yana tunani.


Dogon mutum wankan tarwada wanda kallo daya zai sa ka gane wahala ce ta kara masa
shekaru ba don ya kai hakan ba a zahiri. Kana iya ganin furfura kadan a cikakken
bakin gashinsa. Dukkan wata cikakkiyar kamala ta mutumin kirki ta tabbata a
fuskarsa. Sai dai zuciyarsa wadda kuncin rayuwa ya yiwa dabaibayi tasa baka ganin
walwalarsa.


Wanda yafi girma cikin mutanen yana zuwa da izgilanci yaje ya take katifar da kafa
daya yana karkada masa yatsa a gaban fuskarsa.


"Tashi nan nake son na rinka kwanciya"


Dayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login