Showing 198001 words to 201000 words out of 295847 words

Chapter 67 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

cikin yaran. Yadikko sun tafi asibiti da Atine guda cikin
jariran babu lafiya ko ta kan Malamijo bata bi ba da zasu tafi. Ita yanzu burinta
kawai Atine tayi arba'in yaran su kara kwari itama ta tafi. Shekaru sama da arba'in
tana zaune tamkar sharar gidansa ta kula masa da yara ya bude baki ya fada mata
magana son ransa.


Kannen Mairama da suke zawarci su biyu da sauran kannensu duk sunyi zuru zuru amma
ganinta sai gasu sun fara sakin fuska suna yi musu barka da zuwa.


Hajiyayye ta wani daka musu tsawa saboda tsaurin ido "ba cewa nayi idan yaran nan
sun zo cin abinci kowa ya zauna a daki ba? Ko shi Malamijon bai nanata muku ba
kafin shigowarsu?"


Mayunwatan yaran kananun suka matso suna jira ta zuba musu ta kalli tabarmarta "ku
shiga dakinsa akwai tabarma a bani tawa zan ciyar da yaranmu"
Zayyan da Mairama sun tsaya ne kawai kallon wannan mata mai zubin mahaukata tana ta
bada umarni a gidan. Daurewa tayi ta tambayi wata kanwarta matsayinta a gidan.


"Amaryar Malamijo ce"


"Amarya kuma?" A iya saninta babu sauran wuri a gidan nasu to wa ya saka. Sai gashi
kafin ta tambaya ma ta bata amsa da cewa Hajjo ya saki "Malamijo Hajjo?" Tace kamar
tayi kuka.


Kanenta da suke karatu a Kano gidanta su Laila duka lokacin da suka zo kafin ta
wuce Abuja tasa sun tafi hutu wurin iyayensu mata. Ta san da tuni ta sami labari a
wurinsu.


Babu wanda yayi motsi da Hajiyayye tace su dauke Malamijo daga kan tabarmarta ta
doki cinya tana sababi wai zai farfado ya sameta ne sai ya yiwa bakin nan bayanin
matsayinta.


Abin takaicin ya ishi Zayyan zaiyi magana Ummi ta dakatar dashi ta nuna masa
Radhiya da take bin matar da wani irin kallon raini

"Baki ga suma yayi bane kike zancen a baki tabarma ku ci abinci?"


"Yarinya kada kice zaki yiwa Hajiyayye rashin kunya wallahi sai na farfasa miki
jiki yanzun nan a wuce wurin" babban yace a kule yunwa na cin hanjinsa an tsaya ana
bata musu lokaci. Ko kadan daga uwar har yaran basu da da'a.


Sai da ya gama Radhiya ta tafi gaban kulolin da ta kula suna yiwa kallon mutumci ta
bude da ta ga miya ce nama ya kusan cika ta.


"Wa ya baki izinin taba min abinci? Ke idan Malamijo ya farka zan iya sawa ya
hanaku sake zuwa gidan nan"


Emzee da Ibrahim Radhiya ta nunawa kulolin da hannu tamkar ba da ita ake magana ba
"bros ga fa abinda ya kawomu Sumaila kuzo mu fara aiki"


Tamkar masu jira suka je zasu dauki kulolin nan yaran Hajiyayye suka yi kukan kura
tamkar mayun gaske. Duk abinda suke yi Malamijo ya farfado ya ma dan bude ido da ya
ga abu ya soma kankama ya runtse kayansa ya cigaba da kwanciya. Ummi da Daada wuri
suka samu suka zauna saboda abin kunya ne ace suna da su Emzee su rinka saka baki
suna magana da yara irin na Hajiyayye. Ummi tana da yakinin indai da yaranta a
wurin bata da matsala don ko da Radhiya kadai ta barsu ta ishesu.


Wurin ke neman kacamewa Radhiya ta kira Zayyana ta nuna mata kula daya tace ta
zauna a kai itama ta zauna akan daya ta dora kafa daya kan daya. Tsagerun Hajiyayye
suna son tashinsu amma yadda take kada kafa ga wasu maza a tsaye a gefe wato Emzee
da Ibrahim kowa ya tamke fuska duk sai suka sha jinin jikinsu. Malamijo da yaji
abin baiyi masa ba ya dan kyallo ido daya yace "Zayyan"


Uba da da ne suka amsa a tare. Wai shi Malamijo a tunaninsa ko dai Hajiyayye mayar
gaske ce take son tsorata shi da fatalwar surukinsa zai daure ai ba'a san Fulani da
tsoro ba ya dauke kai kamar bai ganshi ba ya cigaba da cewa Emzee "ina rundunar
sauran sojojin da kace zaku zo tare?"


Ba yaran ba Hajiyayye ma sai da cikinta ya bada sauti "soja kuma"


Emzee ya sake mazewa sai lokacin ta kula da kayan jikinsa ma. Hankalinta yayi
mummunan tashi kuwa a tsorace ta cewa manyan su fita zata san abinyi. Su ma da
sauri suka fita din kada rundunar sojojin su iso. Tana kallo Radhiya ta kira yaran
gidan suka debo kwanaku yau ko biki ake a gidan sai haka. Abincin nan tas ta rabe
musu harda kwakkwafe kular bata bar ko kwayar shinkafa ba.


Zayyan kallonta yayi ya saki murmushi kawai tana kara burge shi. Haka yake kaifi
daya kuma haka yake son 'ya'yansa. Kada su cuci kowa kuma kada su bari a cuce su.
Bayan ta gama ta tura kular wurin wanke wanke ta dawo kusa da Malamijo ta zauna.
Hajiyayye ta rasa me ya kamata ta yi saboda bacin ran da take ciki. Wannan wane
irin mutane ne suka shigo gidan da yake karkashin mulkinta suna neman chaza mata
kai. Kwafa tayi ta bar wurin ta tafi daki zugar yaranta suna biye da ita ana kukan
nama.


Malamijo sai lokacin ya bude ido yana murmushi a hankali yadda babu mai ji sai na
kusa dashi yace "Alakakai gayyar mayu daga nan ma sai gidan tsoho"


Radhiya tace masa "fadi da karfi mana taji Malamijo a haka bazata san kana yi ba"


"Barni da ita a hakan ma kun more min su. Bana so taji ne ta dawo"


"Barka da yamma Malamijo" Zayyan yace bayan yaran sun gama dariyar kalaman
Malamijo.


Jikinsa ne yayi wani mugun sanyi kamar an sare masa gwiwa ya juya ya tabbatar
Zayyan din ne dai yake gani kawai sai ya koma ya kwanta ya rufe idanu.


"Mairama kirawo matar nan tazo ta tsallake ni."


"Tsallakewa kamar wata mayya"


"Yo ba mayyar bace? Aure ne na kaddara na kwasowa kaina. Yanzu don bala'i ko yaya
na kalli bangaren arewa maso gabashin inda kike zaune sai in rinka gane gane"


Ibrahim da Emzee ne suka fara dariya Ummi ta hararesu. Zayyan da ya gane dashi ake
dole ya rike tashi dariyar a gaban suruki.
"Kamar me da me kake gani?" Radhiya ta tambayeshi tana danne dariyarta.


Fuskarsa sai tayi kalar tausayi ya kalli Ummi yana girgiza kai "ina tsoron fada in
saka babarku kuka". Kasa daurewa yayi da ya kyalla ido ya kuma ganin Zayyan a zaune
" 'Yar soja mai kamar mahaifinku matar nan tana son yi min cune. Dadin abin ma dai
tsakanina dashi sai alheri har muka rabu muna mutunta juna"


Dariyar kowa a take ta fito fili Zayyan ya matso ya sake kama hannuwan.Malamijo da
yake shirin sandare masa saboda tsoro "nine dai Zayyan ban mutu ba"


"Minal hubsi wal haba isi....tuf, tuf" ya mike tsaye jiki na tsuma amma a dole
dauriya zaiyi yana tofe tofe "kakana malami ne har ya mutu kuma sunansa naci har
wata fatal..."


Ummi gani tayi abin ya soma yawa baban nata yasa yara suna dariya ta tashi ta riko
hannunsa suka zauna kusa da Zayyan.


"Malamijo Allah Yayi da ransa ashe rufe shi akayi a kurkuku a can kasar da suka je
yaki."


"Ki bari dan Manzo"


"Taba shi kaji wallahi shine"


Ali gadanga Malamijo ikon Allah sai kuka yana shasshafa jikin Zayyan.


"Allah Qadiran Ala Mayyasha'u. Zayyanu kana nan dama?"


Zaman jajantawa akayi ya kira Na'e da bata sanshi ba a wurinta yake jin Yadikko ta
fita. Sun dan taba hira aka tafi yin sallah Mairama ta fada masa Kano zasu wuce a
bar masa yaran. Bai fada mata komai game da Hajiyayye ba sai iya wanda idonta ya
gani. Dan sauran mutumcinsa yaji yana son karewa a idanunta. Idan sun tafi zai
fadawa su Radhiya ko da ja a kasa su fitar masa da ita da yaranta. Kuma a nemo masa
shanunsa kafin jininsa ya karasa hawa.


**********


Kyakyawar matashiya ce irin wadda ake kira black beauty durkushe a gaban Salame
tana sauraron fadan da take yi mata tana share kwalla da kasan hijabinta.


Salame ta zama tamkar wata almajira a yankwane duk ta tsufa fiye da shekarunta
hakora sun soma yin wani layin kore kore daga sama ta kankance idanu tana surfa
mata masifa har wani yawu ne yake kumfa kumfa daga gefen bakin.
"Banza jinin matsiyata. Dangin ubanki kaf basu da farcen susa sai kwala kwalan
idanu kamar mujiya. Yanzu Rahima banda baki daukeni a bakin komai ba in aika miki
cewa bani da lafiya amma kizo min gida hannu na dukan cinya"


Muryarta har ta dashe saboda kuka a tsakar dakin da ko arzikin leda babu ga
kannenta 'ya'yan Alh Indararo sai murguda mata baki suke yi da masu gwalo tace
"Umma wall..."


Hannu ta kai ta mangareta "rufe min baki zaki fara sakin karya yadda ubanki yake
yi. Kina sana'ar yin kunshi amma 'yar kazar nan ko ki dan kullo kudin ki bani domin
saka albarka ya gagara. Kinfi ganewa ki bawa matsiyacin babanki ya ciyar da matarsa
da 'ya'ya ni da na tsugunna na haifeki ko oho"


Maman Danmama ce ta dago yagaggen labulen dakin ta leko "ke kuwa Salame ki bar
yarinyar nan haka mana. Tun shigowarta kin sakata a gaba da bala'i kamar baki san
ciwon haihuwarta ba"


Cike da masifa ta dago "ki dai zuba ruwa a kasa ki sha kawai saboda farinciki. To
dai duk tsiya tafi Danmama da yake karen mota a tasha"

💕[11/2, 7:24 AM 49 💕

🏽Radhiya bata kwanta ba sai da ta gama tsara yadda za ta yi da Hajiyayye gobe. Ba'a
taba mata kaka a kwana lafiya. Yadda ta rabe mata abinci bata sami ko loma daya ba
haka da daren ma dan kadan ta ce Na'e ta zuba musu ita da yaran. Bakinciki yasa
Hajiyayye ta kasa komai saboda sau uku tana kokarin zuwa dakin Malamijo sai ta
tarar da Ibrahim da Emzee a kofar dakin kamar suna gadinsa.


Bayan kowa yaci abincin safe ne Radhiya ta fito tsakar gida tana tambayar waye mai
girki yau. Yadikko ta kama kunnenta ta rike.


"Na fada miki babu mai girki a gidan nan sai amaryar kakanki. Na'e ma da tayi tuwon
dare jiya kawaici tayi miki bata ce komai ba"


Hajiyayyen rabewa tayi a jikin kofar dakinta tana jinsu tayi murmushi. Ashe dai
Yadikko tasan matsayinta. Idan suka yi kuskuren biyewa wannan yarinyar za ta barsu
da jidali ne idan ta tafi don duk wanda ya shiga gonarta sai ya gane kurensa.


"Tunda babu mai girkin dole ni zanyi kenan da kaina. Bari na leka Malamijo ya bada
shanu uku ma sun isa da za'ayi yanka"


"Yanka kuma? Radhiya idan kika zo gidan nan bakya zama kiyi ta mana jaye jaye. Nama
kuma kema kin sani ba'a kawowa gidan nan har kike kiran yanka."


Bata ankara ba sai ga Malamijo ya fito yau dai sanyi ya saka shi saka kayan kirki
ya rufe kasusuwan jikinsa. Daure fuska yayi yana hararar Yadikko.

"Kinji nace bazan bada shanun bane da zaki yanke min hukunci? 'Yar Soja guda nawa
kuke bukata?"
"Uku tace" inji Emzee da suka gama sanin me take da niyar yi.


"Amma shanu uku 'Yar Soja waye zai taya ku aikin naman? Yayi yawa. In baku daya dai
yau kowa yaci"


Murmushin mugunta tayi da Ibrahim yayi mata alama cewa fa Hajiyayye ta leko daga
dakinta tana sauraronsu. Haka take so taji ko wani nata yaji a kai mata rahoto.

"Kada ka damu naman nan ba mune zamu ci ba. Wadanda za'ayiwa yankan kuma danye suke
so"


Idanu Malamijo ya zaro "Hajiyayye zaki yiwa yanka?"


Sai da ta kula kowa ita yake sauraro ta dare kan turmi ta zauna "Bakina dai da zasu
zo. Jiya da na ga yadda gidan nan ya koma shine na kira Sarkin mayun Faransa...can
inda nake karatu. Dayake muna mutumci da 'ya'yansa sai ya daukeni kamar 'yar
cikinsa. To shine nayi masa maganarka na cewa ka auro mayya. Yayi ta mamaki tunda
yasan ni ba mayyar bace. Shine fa yau da sassafe ya kirani wai ya kai maganar can
ofishin majalisar dinkin duniya akan harkar mayu sun ce zasu turo wakilai azo ayi
bincike ke"


Idanun Malamijo tuni suka raina fata ya hau rawar jiki "ni nace kiyi zancena da
wasu ne? Haba Radhiya ashe baki da hankali ban sani ba. Mayun Najeriya basu cinyeni
ba sai na Faransa"


Yadikko tana ji tasan sharrin Radhiya ne amma yadda idanun Malamijo suka kada suka
yi ja sai ta kyale ko banza ta rinka tunawa tana dariya.


Cikinsu Ibrahim ne ya iya daure dariyarsa yace "Turawan mayu inajin kince basa cin
mutane sai mayu 'yan uwansu ko"


"Eh mana, matsalar dai bincike zasu zo yi. Wai ashe daga last year aka haramtawa
duk wanda ba maye ba auren maye saboda gudun rigingimu da suke tasowa." Ta yi kamar
ta rage murya za ta yi rada bayan ta san sarai kowa yana ji "yace zasu kama duka
mayun gidannan ne a tafi dasu. Hukuncin take dokar shine kisa ta hanyar
babbakaraisin din mayun a baiwa oganninsu su ci da bredi"


Tsuuuu zawo ya nemi saukowa daga jikin Hajiyayye cikinta na murdawa tana matse shi
da kyar saboda tsabar kaduwa. Babban yaron da tazo dashi gidan ashe shima yaji ko
takalmi bai saka ba ya fito daga dakin nata a guje Radhiya tana a kamo shi. Dayake
ba niyar kama shi da gaske suka yi ba da gangan suka bari ya gudu. Ragowar yaran
nata ta kalla tace kowa ya tashi tana uban gumi kamar wadda tayi tsere. Muryar
Radhiya taji tana magana da yaren da bata ganewa.


Wayar karya ta gama da French ta juya ta kalli Halifa da yake jindadin wannan drama
yayi ta dariya kamar cikinsa zai kulle "ka rufe kofar nan. Yanzu suka kirani wai
ashe sun ga fitar daya kuma sauran ma sun gama shiri yace idan wani ya sake fita
daga gidannan harda mu za'a ci da bredin"


Hajiyayye da gudu ta saki mayafinta hankalinta gabadaya ya tashi. Ta ma rasa da me
zata ji. Talle da yaki daukar wayarta tun safe taji ya ake ciki game da shannun ko
kuwa wakilan majalisar mayu da za'a turo su kama ta. Acinyeki da bredi wata zuciyar
ta tuna mata. Harda guntun hawaye sai da tayi bata ankara ba kafin ta daure ta fito
inda suke.


"Uhmm nace Malamijo yau me za'a dafa da rana ne? Naga ana ta hira shine baku
kirawoni ba" wai ita nan za ta bagarar kamar bata san me suke yi ba. Daga nan ta
samu ta arce. Ofishin 'yan sanda zata je ta shigar da kara kafin turawan mayun su
iso azo a fitar mata da yaranta.


To shima ba wai yana cikin hayyacinsa bane duk ya gama tsorata ya fara danasanin
kiran Radhiya. Yarinyar nan da ya gama sanin halinta me ya kaishi kiranta da kansa.
Wayarta ce tayi kara a lokacin taken wakar Celine Dion ta film din Titanic wanda ta
sanyawa Awwab. A wurinta wakar bata tsufa sai ma nishadin da take saka ta idan ta
tuna masoyinta.


Idanun Malamijo da na Hajiyayye basu da na biyun kwatance a lokacin. Tsoro ne
karara ya bayyana ita kuwa tana dauka da turance tace masa "Chèri please follow my
lead i'll explain everything later. Say something in German" (ka biyewa duk yadda
kaji nayi, zanyi maka bayani daga baya. Ka yi magana da yaren Jamus)


Yana cikin office dinsu a lokacin ya kirata. Abinda tace kawai ya isa ya saka shi
gane cewa akwai abinda take yi. Alheran dinsa bata ji, sai dai kuma idan ta canja
daga yadda take ta tashi daga yarinyar da ya fara so daga haduwar farko kenan.
Fitinanniyar dai ita ce tashi mai sanya shi nishadi a kowane lokaci.


Speaker ta sanya kowa na ji ya rinka yi mata kalaman soyayyar da yasan cewa ba
fahimta take yi ba ita ma.


"Amaryar Malamijo kin dai ji me yace. Wai ku jeru a daki ke da yaran naki yanzu
zasu shigo. Idan anyi binciken sun ware mayu a cikinku sai su saki sauran"


"Inji uban wa akace mu mayu ne? Garin nan waye bai san gidan iyayena ba? Malamijo
kace wani abu mana" ta fada a raunane hawaye na zuba.


"Ince me? Na auro mayya tayi sanadin da majalisar dinkin duniya ta mayu zata zo
gidana" ya ce gumi na karyo masa. Gidan gabadaya yayi masa zafi dari bisa dari ya
yarda da zancen Radhiya.


Wayar ta dan kara a bakinta "ranka ya dade ko za ka danyi mata hausa ta fahimta.
Mayyar da ta auri kakan nawa ce ta fito" ta kalle su "shine wakilinsu da yake kula
da hausawan mayu"


"Bata wayar" Awwab yace dariya na ciwo shi. Wace mai tsautsayin ce wannan ta shiga
tarkon Alheran?
Ai Hajiyayye na jin haka ta zube a kasa ta fashe da kuka. Tsoro yayi mata yawa
zawon ya fara tsartuwa daga ma'ajiyarsa saboda tsoro. Muryar Awwab dama irin wannan
deep voice din ce mai tahowa daga kirji. Mata da yawa suna fadawa soyayyarsa a
kanta yayin da take razana marasa gaskiya irin Hajiyayye.


"Kayi min rai ranka ya dade aradun Allah karya nake ni ba mayya bace. Mutum ce
kamar kowa kuma indai aurene ko bai sakeni ba ni na saki kaina yanzu zan tafi ba
sai kun zo ba"


Dariya yake neman yi Radhiya tace da sauri "ranka ya dade bari na tayaku binciken
kafin ku iso zan tabbatar da gaskiyarta" kashe wayar tayi ta ga kowa ya fara ja da
baya saboda zawon Hajiyayye. Wari ya isheta amma haka ta daure bata matsa ba.


"Me kike cewa?"


"Nace ba, aurena da Malamijo wallahi duk shiri ne tsakanina da Talle. Rabonmu kawai
muka zo yaga mu tafi amma bani da alaka da mayu. Kuyi hakuri yarana akwai marayu a
ciki. Waye zai kula dasu?"


"Tunda har kun iya kulla cuta ki shirya ko ba'a kamaku an cinye ba zaki shiga
prison. Kurkuku nake nufi" Emzee yace yana cin magani.


Rarrafawa tayi wurin Malamijo wanda hankalinsa ya kwanta da ya gano me Radhiya ta
shirya. Dage hanci yayi ga wari ya dame shi "ki kwashe yaranki kada ki koma min
cikin dakin Hajjo. Daga nan ki tsaya ki kirawo su. Sannan shanuna...."


Tana kuka tuni ta mike tana gyara zani babu kyan gani tace "suna gidan Talle"


"Me kike jira ne baki fita ba sun kusa isowa" Radhiya ta dada tsorata ta. Yaran ta
kira suka fito a gurguje kan kace meye wannan sun fita Malamijo yana daga murya
yana sanar da ita saki uku yayi mata.


Suna fita gidan ya kaure da hayaniya da murna. Malamijo tsananin farinciki yace
"kowa ya shaida wallahi na bawa 'Yar Soja kyautar tunkiya, akwai wata mai ciki ta
zama taki"


"Ahhh nifa gaskiya tayi min kadan" tace tana tura masa baki.


Baiyi fushi ba ya saki fuska "to me kike so Alherin babanta"


"Alheran ne fa ba Alheri ba"


"To ni dai sammakal...me kike so? Kai ku fito kowa yayi shaida zan yiwa babbar jika
ta kyautar bajinta"
"Ni dai kada ka kasa fa"


"Ke! Dube ni nan da kyau Ali Gidado nake. Ciki lafiya baka lafiya. Da kudina a
jikina"


Kowa ya fito harda maijego Atine. Hassana da Usainanta suna bayan Zayyana da Hibbah
da suke jindadin daukar yaran. Radhiya ta dan hadiyi yawu kafin tace "Malamijo za
ka dawo da Hajjo ko?"


"Kamar da kasa yarinya. Ai da shike Allah Ya taimakemu dole mata suke idda kinga
bata gama ba har yanzu da damar kome tsakaninmu"


"To dama so nake tunda ka yarda za ka min abinda nake so su duka matan nan ka hada
da Nene Marka da kai kanka Hajji me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login