Showing 111001 words to 114000 words out of 295847 words

Chapter 38 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

wani langabe kai "yaushe? Ka dade da zuwa ne?"


Wai raina masa wayo zata yi ne? Kowa kallonsu yake yi ana dariya kasa-kasa. Hadir
kansa murmushinsa ya kusa zama dariya da ya gane so take ta nuna bata ganshi ba.


Awwab da bai fahimta ba dama shima anyi masa tambarin wauta idan abin dan farin
nasa ya tashi yace "dazu fa kin farka har muka hada ido."


Tsuke baki ta soma yi. Ya kamata idan ta basar sau daya kawai a wuce wurin amma sai
neman jan zance yake yi.


"Ni din? Bacci fa nayi a kan kujerar nan sai farkawa nayi na ganni a daki su Adda
Zahra sun rikeni sun kaini saboda nauyin baccina, ban san lokacin da ka shigo ba"


Zahra ta soma kifta masa ido akan ya bar zancen haka shi kuma ya dage sai ya ga
abinda ya turewa buzu nadi.


"Lokacin da abin kanki ya zame haka " ya kwatanta da dan jan dankwalin Fauziyya "
har na ga kan...."


Ihu ta saka ta tashi da sauri tana jin kamar taje ta toshe masa baki kada ya karasa
fadin ya ga kanta. Kamar zata yi kuka take kallonsa "idan nace ban ganka ba sai
kawai ka yarda haka ake yi ko Em..." shiru tayi ta shiga waige da ta ga baya wurin
"ina Emzee?" Tayi tambayar tana kallon Ibrahim da dariya tasa ko magana ya kasa.
"Ya fice"


"Ku ga min shegen yaro, shi yace idan na basar kamar ba'ayi ba komai zai wuce."


Gabadaya falon ya sake kaurewa da dariya. Zainab ta tashi ta kama kujerar Hadir
"bari naje na bawa babanku magani, Fauziyya ku kawowa Awwab abinci ko ruwa bai sha
ba tunda ya shigo kun saka min 'ya a gaba"


Gani tayi ya dace su baiwa yaran wuri don ba ta biye musu ana tunzura Radhiya ba.
So take Awwab ya so kanwar tasa da wuri, gara su fara sabawa da juna. Taimakawa
Hadir tayi ya kwanta ta dauko takardun asibitin ta koma kusa dashi tana yi masa
bayanin kowanne don neman shawararsa. Da ido da yanayin chanjin fuska take fahimtar
abubuwa da dama da yake nufi idan tayi masa tambaya.


Sakale tayi tana kallon Awwab yana murmushi "ban san haka kike so ba, to koma ki
sake fitowa. I promise zan tayaki basarwa"


Ita ma sai da abin ya bata dariya ta koma ta zauna tana jiran fitowar Emzee ko ma
ina yaje ya buya. Dama idan ba ganganci ba me zaisa ta karbi shawararsa. Wautar
kanta take gani na biye masa.

Yana jiyo me suke yi a inda ya tsaya ya girgiza kai. Bawa Radhiya shawara wataran
kamar zuba gari ne a rariya. Kana fada yana zuba. Ibrahim da Zayyana suka tashi
suka bi bayan shi zuwa waje. Ibrahim na cewa ta dena binsa ta murguda masa baki
tace ita wurin Emzee zata je ba shi take bi ba.


Ya rage su hudu a falon Awwab ya watsawa su Zahra idanunsa "bazaku bani abincin
bane?"


Da sauri Radhiya ta tashi don yau dai taji kunya fiye da yadda ta saba "bari na
kawo maka"


"No, dawo ki zauna"


Inkiya yake musu su basu wuri sumsum suka tashi suna dariyar dramar Radhiya.


Kai ta sunkuyar karon farko da zata iya tunawa a rayuwarta ta rasa bakin magana
saboda kunyar da ta bawa kanta. Dan gayu kamar wannan kyakkyawa daga ita sai shi a
falo ai dole harshe yayi nauyi tace a zuciyarta.


Nazarinta Awwab yake yi ya dago kansa daga jinginar da yayi da kujera yana mamakin
wannan yarinyar ta gabansa ita ce Alheran dinnan da yake dauka suyi ta yawo a
barrack shekarun baya.


"Alheran" ya ambaci sunanta a hankali taji wani yarr a jikinta saboda yadda muryar
ta ratsata.


"Uhmm"


"Kin dena magana ne kuma?" Ya tsokaneta da ya ga kamar ma a takure take.


Girgiza kai tayi sannan tayi kwafa da guntun tsaki "Wallahi kunya naji, ashe ba
haka ake basarwa ba. Bari Emzee ya dawo zai gamu dani"


"Balotelli zaki yi masa?"


Dago kai tayi da sauri ya dage mata gira yana jin komai nata na burge shi. Ba haka
yayi zaton ganinta ba. Yana ta kissima wata budurwa mai ji da kai da gayu sai ya
hadu da Radhiya wadda kwatancenta sai wanda ya santa. Amma duk da haka yaji tayi
masa a yadda ya sameta cikin kankanin lokaci

💕[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 25💕
Bata tsaya ko ina ba sai daki ta cire hijabin da dankwali ta fada kan gado. Wani
tunani ne ya shigeta haka kawai kada a sake tsautsayi ta dauki dankwalinta ta
daura.


Awwab kamar bai san me yayi ba ya shiga cin abinci hankali kwance yana jin matan
suna kuskus a junansu. To meye ma a ciki daga bata abinci. Da ace sun tashi tare
baya jin akwai abinda zai kasa yi mata sai dai a taka masa birki tunda mace ce.
Allah ne Ya hada jininsa da na iyayenta sai Ya sanya masa matukar kaunarta tun tana
tsumman goyo.


Emzee yaso dauke kai amma ya kasa. Karshe ya dauko wani littafi a kusa dashi ya
bude shi ya kifa akan fuskarsa yana dariyar da ba sauti. Gaskiya yaji kunya kamar
shi aka bawa abincin. Ibrahim ne ya fara tsokanarsa sai kawai ya tashi da plate
dinsa a hannu zai koma daki.


"Dawo ka zauna ka gama cin abincin nan" Awwab yace ko kallonsa baiyi ba.


"Na koshi"


"Kira min Alheran"


Ba musu yaje ya fadi sakon, maimakon amsa sai ta kara dukunkune kanta ta tura a
karkashin filo. Murmushi yayi kawai ya fita ya dawo ya fadawa Awwab taki tashi.


Sai da yaci rabin abincin ya mika masa plate din "ka kai mata nata, sai da safen
ku"


Tashi yayi zai tafi dakin Ibrahim inda aka yi masa masauki Zayyana da ta kasa
hakuri ta fara shagwabe fuska "Hamma ni baka taba yi min irin haka ba, harda bata a
baki"


"Ba kiji ta fada muku cewa a rashinta nake kulaki ba" ya fada da wasa.


Kukan shagwabar da ta saba ta fara "kuma sai na...."


"....fadawa Daddy" Ibrahim ya karashe mata yana kyabe fuska yadda take yi.

Awwab ya kusa kofa don idan ya biye mata karshenta a daren sai ya ga wayar Daddy.
Juye juye ta soma yi Emzee ya dawo daga ajiyewa Radhiya abinci ya ganta.


"Wa kike nema?"


"Kai mana"


"Inyi miki me?"


"Ba Hamma Ibrahim bane yake tsokanata"


"In fada miki sunan Fulatancinsa ki rama?"


Cikin sauri Ibrahim yazo ya tura shi daki yana magiya da yayi shiru. Tun da Radhiya
ta fassara masa ma'anar Surbajo yake gudun sunan kuma dashi Emzee yake samu ya dan
kashe bakin idan ya dame su.


Da yake Mami ta fada musu cewa sammako zasuyi su baro Katsina su ma basu yi sanya
ba wurin tashi da wuri. Zuwan 'yan matan ba karamin dadi ya yiwa Zainab ba. Su
tayata hira ayi ta barkwanci sannan basa bari tayi komai. Zahra da Fauziyya sun
jima da gogewa wurin aikin gida da girki. Saboda Mami taran safe zuwa taran dare
tana gidan aikinta. Su ne suke komai. Shiyasa Zayyana ta shaku dasu sosai wani
zubin bazaka ce yayyenta bane da suka girme mata da yawa.


Kowa ya shirya cikin kayan kirki Radhiya ta bude jakarta kenan bayan ta gama shafa
mai Zainab ta leko tayi kiranta. Dakinta ta bar musu dama. Yanzu kuwa da ta kai
Hadir falo bayan ya gama breakfast sai ta kirata dakinsa. Ledoji uku ne a gabanta
manya ta tura mata daya.


"Ga naki kafin ku tashi daga bacci telan ya kawo"


Radhiya ta bude baki tana kallon kayan da Zainab din take zarowa. Atampa guda uku,
material daya, shadda daya da wasu yadika combination biyu. Kwalkwal tayi ta idanu
zata yi kuka. Duk wannan ita kadai.


"Bana son kuka fa kin sani ko yanzu naje na fada a hanaki yin sojan."
"Mama nagode" tace hawayen yana fitowa. Yarinya ce mai rike abu a rai shiyasa bata
manta alkhairi ko sharri. Da yake dai wasa da shirme sunyi mata yawa a ka shiyasa
sai ka ga kamar bata da damuwar komai.


Banda kaddara da Zayyan yana raye Zainab ta sani da yanzu sun kai wani mataki a
aikinsu. Yadda yake da kwazo da himma tasan 'ya'yansa sai dai wani yaci arzikinsu.
Babban dalilin kiran dama so take ta shirya Radhiya da kanta. Mama Zainab 'yar
kwalliya ce ajin karshe. Idan ka ganta a yanzu da take cikin farincikin kasancewa
da Hadir duk da a zahiri za'a iya cewa nauyi ne shi a gareta amma fes take kullum.
Gogewarta a soyayya duba da tarihin rayuwarta yasa tun jiya ta daukarwa kanta
nauyin sake hada Awwab da Alheran domin su cimma burinsu cikin sauki akan yaran.


Kallo daya zaka yi musu kasan sun dace da juna amma idan ka san kowannensu ta
fannin zamantakewar rayuwa dole ka chanja shawara. Awwab dan boko ne tashin turai.
Yana da ilimi, wayewa da kudi domin kuwa pilots masu aiki da kamfanin KLM suna
cikin mafiya samun kudi cikin tsararrakinsu. Alheran Radhiya kuwa yarinya ce da ta
tashi a rugar fulani a cikin wata karamar hukuma. Wannan kadai ya isa zama
wawakeken bambamci tsakaninsu indai zaman aure zasuyi wanda babu soyayya. Abubuwan
da ya sani ko yake so bata sansu ba bare ta so su. Wayewarsu ba iri daya bace. Tayi
nata karatun daidai gwargwado amma baza'a taba hada shi da nasa ba tunda iyakarta
secondary. Shiyasa indai ana so zaman aurensu yayi karko to a samu soyayya mai
karfi da za ta zama igiyar dauresu.


Wani kaya Zainab ta ciro daga ledar ta mika mata "jeki ki saka wadannan gani nan
zuwa. Ko hoda kada ki shafa sai nazo"


"To Mama" tace ta fita da murnarta taje ta nunawa su Zahra su ka tayata murna.


Yadi ne mai kala biyu. Mara adon light purple ne anyi mata skirt dogo da dankwali.
Rigar kuwa yadinta duka zanen filawoyi ne manya pink da light light purple kamar
skirt din. Tsayinta ya wuce gwiwa da kadan anyi mata dogon hannu mai dan fadi daga
kasansa. Kadan akayi mata shape don kada ta kama jiki ba wani ado a jikinta sai
maballai guda hudu na wuya amma tayi kyau musamman a jikin Radhiya. Wani juyi ta
rinka yi tana jindadi su Zahra na zuga ta har Zainab ta shigo tace suyi sauri wanda
basu ci abinci ba su je su ci nan da awa daya ko kasa da haka su Mami zasu iso.
Duka su ukun su ka fita aka barsu su kadai.


Hoda, kwalli da janbaki pink mara duhu ta shafawa Radhiya a fuska bayan tayi mata
lining da jagira pink mai duhu a leben. Simple make up ne amma fuskarta tayi kyau.
Cikas din kawai kanta ne. Zainab ta daura mata dankwalin da kanta ya danyi tudu
daga keya sannan ta mika mata hijab mai kyau da kananun duwatsu a kasansa pink irin
kayan. Iyakarsa ya sauko kirjinta da kadan. Radhiya harda hajijiya a gaban mudubi.


"Mama nayi kyau ko?"


Murmushi tayi ta yaba sosai da 'yar tasu "kinyi kyau amma don Allah bana son
baragada kinji ko. Wannan hayaniyar da saurin fushi ko fada ki ajiyesu. So nake
naga kina taku daidai yadda babu wanda zai raina min ke"
"Idan nayi sanyi da yawa bazan kai labari ba a makarantar sojoji Mama. Anfi son mu
da dakiya da fada saboda gudun raini"


"Allah nagode Maka. Har yanzu kina jiran zuwa sojan ne bayan miji zan samo miki"



Da murnarta tace "Likita?"


"Idan ba likita bane ba fa?"


"Gaskiya Mama ki barshi kawai. Idan ba likita ba sai dai ko soja irina. Sauran duk
na rainasu, kada ayi auren su rinka kawo karata kullum"


Hannuwa Zainab ta tafa tana dariya, yanzu ta gama cewa ta dena shirme gashi ta hade
fuska tana buga kayanta a ganinta kuma ba laifi bane.


"Jeki kici abinci kada azo ana jiranki"


Kallon kanta ta sake yi yadda tayi kyau abinci zai iya goge mats jambakin ta dawo
tayi zamanta akan gado "bana jin yunwa"


"Ashe kuwa za'a tafi a barki" Zainab tace tana yin gaba.



Ba don taso ba ta tashi itama. Tana saka kafa a falon ta tuna abinda Awwab yayi
mata sai ta juya suka kusa karo da Zainab.


"Wuce muje kici abinci" ta umarceta.


Gani tayi babu alamun Awwab din sai ta saki ranta ta fara gaishe da Hadir da yake
kallon labarai sannan ta tafi gaban dinning table inda kayan tea suke za ta hada
taji Zainab tana tambayar ko Awwab ya shirya.


"Da kyar idan ma ya tashi Mama, shi fa idan yana gida yafi zaman daki yayi bacci
saboda yanayin aikinsa" Zahra ta bata amsa.


Radhiya ta saki murmushi "kice kamar dai mu sojoji ashe nasa aikin shima baya samun
isasshen hutu". Suna mata dariya za ta fara abin nata ta mayar da hankali ga abinda
take yi. Madara da milo ta zuba a cup din nata ta mika hannu za ta dauki sugar
Awwab ya bude kofar dakin ya fito. Wani hadadden kamshi ke tasowa tun kafin ya iso
tsakiyar falon. Yayi kyau cikin wani lallausan yadi ruwan madara. Rabonsa da manyan
kaya ya kwana biyu sai jiya da Daddy ya bashi su guda biyu dinkakku da zai taho. Su
Zainab ya fara gaisarwa sannan ya amsa gaisuwar kannensa da Radhiya da jikinta yayi
sanyi saboda kada a sake irin ta jiya.
Tana tsaye ta kasa karasa abinda take yi balle ta ja kujera ta zauna. Jiya ke mata
yawo a ka yadda ya bata abinci a baki kamar wata baby. Runtse idanu tayi tana son
kawar da tunanin daga zuciyarta taji ya janye kofin daga hannunta.


"Kawo na karasa hadawa naga ba kya sauri"


Sakar masa tayi da sauri ya ture robar sugar din ya kara mata madara da milo ya
fara zuba ruwan zafi.


"Hamma ya isa haka" tace da ta ga ya wuce rabi.


Bai saurareta ba sai da ya cika kofin ya ja kujerar gefenta ya zauna. Kujerar kusa
dashi ya tura mata baya da kafarsa ta zauna tana waigen baya. Babu mai kallonsu
Zainab da Hadir labarai suke gani a tashar Channels. Zahra da Fauziyya suna hirar
angwayensu dake korafin sun makale a Kano. Zayyana kuwa ta tafi dafa indomie.


Wani irin kallo yayi mata sau daya ya dauke kansa, tayi masa kyau sosai har yana
tsoron kada kallon da yake mata ya wuce gona da iri "namu ne mu biyu"


Turo baki tayi "Habaaa Hamma don Allah yunwa nake ji"


"Okay fara sha ki bani" yace yana tura mata kofin.


"Ni a'a, ka shanye na hada wani"


Lumshe idanu yayi yana mata murmushi "wannan zamu sha, jiya dama ance abincin da na
rage miki dawo dashi kikayi. Ko muyi kama-kama da shima baki bari munyi ba"


"Na shiga uku" ta furta a hankali tana cike da kunya ta tura kujerarta baya za ta
tashi ya bata rai.


"Ki dena tashi idan muna magana bana so"


Zama tayi tana ta zumbura masa baki ya sha rabin tea din ya mika mata ta karba ta
bishi da harara.


"Baka saka suga ba ni kuma dashi nake sha" ta mika hannu zata dauko robar ya riga
ta daukewa.


"Da zaki a haka, try it."


Samun kanta tayi da bin umarninsa ta sha tea din shi kuma ya tashi ya koma daki bai
taba doyar da aka soya da kwai ba. Tana nan zaune ya dawo da ledoji masu kyau a
hannunsa da tambarin wani babban kamfani a kasar Germany. Su Zainab ya fara mikawa
ta karba da murmushi ta bude. Turaruka ne na alfarma na mace da na namiji ita da
Babansu Hadir da agogo set shima na mace da namiji.


"Harda dorawa kanka wahala Awwab?"


"Ku sa mana albarka kawai Mama"


"To Allah Ya saka da alkhairi Yasa kafi haka. Allah Ya baku masu yi muku a nan
gaba"


"Amin" kowa ya amsa harda Radhiya.


Leda ta biyu ya mika mata "na Ibrahim da Emzee, suna ina ne ma?"


"Leka ta window wankin mota ake mana"


Komawa yayi dinning table din ya zauna a inda ya tashi Radhiya ta kafe shi da ido.


"Ya?" Yace yana gimtse dariya don ya kula ta fara cika tana jiran nata.


"Ina nawa?"


"Me din?"


Kai tsaye tace "Abin cikin ledar"


"Kina harar tawa zan baki abin cikin leda? Wanda na siyo da sunanki ma zan je in
kaiwa Ummi tayi sadaka dasu"


Kallon shirts da agoguna da Zainab ke fitarwa da sunan Emzee da Ibrahim yasa ta
sake hade rai harda kwalla. Ita da tafi kowa cika baki akan Hamma Awwab amma ita ce
ko tsinke bai bata ba. Abincin ma fushi tayi dashi ta ture. Sai yaji ta dan bashi
tausayi ya gama dariyar abinda yake shirin kulla mata kawai don ya tsokaneta ya
matso da kansa yana mata magana a hankali.


"Kin yarda daga yanzu ko me zamu ci zamu ragewa juna har na koma?" yayi dan
murmushin rigimarsa da Mami a baya "da ko me naci sai na rage miki Mami tayi ta
fada wai ba komai zaki iya ci ba. Ni kuma tana barin wurin sai na tura miki a baki
ko yaya ne ki cinye"


Murmushin da tayi masa jinsa yayi har ransa saboda yadda take lumshe idanu batare
da tayi la'akari da tasirin hakan gareshi ba "to ai kaine baka yi min bayani ba
kawai kasa ni jin kunya jiya."
"Silly girl me akayi na jin kunyar? Kinsan me kike yi min kuwa da?"


Radhiya ta girgiza kai.


Yafito ta yayi da hannu ta sake duku kanta tana shakar daddadan kamshinsa "abin
bakina kike cirewa ki saka a naki idan na hanaki"


Hannuwanta ta saka a gefe da gefen kumatunta ta bude baki da idanu duka a lokaci
daya. Tana ta jiran Hamma Awwab ya dawo gashi ya dawo ya hadata da jin kunyar da
bata taba sanin tana da ita ba. Abin bakinsa fa yace! Yanzu tana tashi kuma zai ce
ta zauna ko yayi maganar yadda kowa sai yaji. Gara kawai tayi kamar bata ji komai
ba ta bawa kanta shawara. Daurewa tayi kamar bata ji nauyin maganar ba tace


"Yanzu dai kasan bazan ci abin baki ba"


"Sure?" Yace yana mata kallon gefen ido.


"Na fa girma"


"If you say so" ya rausaya kansa sai kuma ya tashi tsaye "kinsan me? sai na sa kin
karbi abin bakina kafin na koma Katsina"


"Idan naki fa?"


"Ki tambayeni duk abinda kike so. Amma nima idan nayi winning zan tambayeki"


"Ka shirya bani tsarabata kawai" tace tana dariya ta tashi tayi waje da sauri. Sai
da ta rufe kofar falon ta dafe kirjinta da yake bugu kamar zai ballo. Kofar ta
kalla ta jingina da bango tana girgiza kai

"Abin baki? Hmmuhmm, kai lallai ma Hamma Awwab dinnan idan ba bazan karba ba" kunya
ta ji kamar me amma ta daure sosai tana bashi amsa saboda kada ya gane zancen na
shigarta tana bashi wata ma'anar daban.


Emzee yana kallonta shi ya gama wanke motar Mamansu Zainab har ya fara taya Ibrahim
da yake wankin bus din da zasu tafi Sumaila a ciki. Dauraye hannuwansa yayi Ibrahim
ya bata baya bai hangota ba ya karasa gabanta.


"Ke da wa Adda?"


Dantsen hannunsa ta riko tana dariyar jindadi "Emzee yau na koyi basarwa"


Yasan Addarsa da shirirta "na tayaki murna, wa kika basar?"
"Hamma Awwab mana, wai kasan me yace min kuwa?"


Yatsunsa na nuni ya sanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login