Showing 15001 words to 18000 words out of 295847 words
fuska kada Yadikko tace me suke yi.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: G
*….TUN RAN ZANE*
Hakan take domin kuwa yau ne za’a kai amaren dakunansu. Dakin Yadikko aka tarasu
Malamijo ya shigo zaiyi musu nasiha ta karshe safiyar lahadi.
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan ya juya wurin Yadikko.
"Me ake cewa ne idan za'a kai amarya?"
"Ko addu'a ai ka yi musu"
Hularsa ya turo gaba "abi miji sau da kafa shine shawarata gareku. Banda tsiwa ko
rashin kunya sannan ayi ta hakuri. Duk wadda ta kaso aurenta babu abinda ya
shalleni ah to. Allah bada zaman lafiya ku tashi ku tafi kada ayi dare Mairama tana
da nisa. Birnin Shehu kwai dan karen tafiya daga nan kamar za'a ya da shege"
Wannan magana ma sai da ta taba ran Salame. Babu wanda ya damu da cewa ita ke son
Zayyan har ake wani zancen nisan garin. Haka su ka fito suna ta kuka, kowacce da
abinda take yiwa. Salame kukan rabuwa da masoyi take yi don tasan an riga an cuceta
an rabata da Zayyan. Mairama kuwa kukanta bai wuce na rabuwa da 'yar uwarta da
gidan nasu duk da ba dadinsa suke ji ba, sai kuma fargabar sabuwar rayuwar da zata
fara.
Akori kura biyu ke biye da motocin daukar amaren na kayan dakinsu da aka samu
Malamijo yayi. Gadaje daidai ne da saitin kujeru da kuma kayan kitchen. Gidan
Salame aka fara tsayawa a Kofar na'isa babban gida ne mai bangare uku na Salisu da
'yan uwansa. Yadikko da Hajjo su ne zasu tsaya a nan ayi jere tare da 'yan uwan Ta
Madina. Basuyi mamaki ba ganin har sunyi jeren katon gado a daki daya da kwaba da
madubi masu kyau daidai da zamani wanda Ta Madina da 'yan uwanta suka yi. A falon
ma sunyi mata kujeru manya da suka fi na wajen Malamijo an malale kasan da leda mai
ado da ta dace da labulen da suka yi mata. Kayan da suka zo dasu wani daki guda aka
nuna musu suka jera kujerun da gadon ya dauke su tsaf saboda ba wani yawa garesu
ba.
Kannen Ta Madina suna aiki suna yabawa su Yadikko magana wai kudin Malamijo bai
tsinana musu komai ba. To su din ma basu tanka ba tunda idan anbi ta barawo abi ta
mabi sawu.
Dije da Inno su ne jagora a tafiya kai Mairama nata gidan. Yamma likis suka isa
Allah Yasa ba wata gayya ce ba basu fi su biyar ba. Sanin cewa idan ya kaisu
gidansu Jume sai ta saka shi jin kunya ya nemi alfarmar kanin babansa zai saukesu a
gidan kafin su yi jeren. Nan su ka kwana ana ta tarairayarsu. Mami matar Captain
Mustapha ita ma tayi abinci mai yawa suka je aka yi taro a gidan. Jume ko zuwa bata
yi ba amma 'ya'yanta mata sun je suna ta yada magana wai kalen dangi ya guji nasa
asalin. Haka nan 'yan uwan Mal.Muhammadu sun je da yawansu.
Da safe Hadir ne yaje daukosu aka kaisu gidan da aka bawa Zayyan a bangaren gidajen
da suke cikin barikin. Daki daya ne kato da bandaki a cikinsa sai falo madaidaici
da kitchen karami. Bata zo da komai ba sai iya kayan da Malamijo yayi mata. Anyi
jere lafiya a daren aka kawo amarya dakinta su kuma suka koma Sumaila washegari.
Zaman Zayyan da Mairama abin burgewa ne da sha'awa ga duk wanda ya sansu kuma yake
mu'amala dasu. Babu abinda ya rageta dashi ta fannin soyayya da kyautatawa. Ita ma
a nata bangaren tana binsa sau da kafa da biyayya da tattali. Yanayin gidansu yasa
ta iya girki bashi da matsala ta wannan fannin ma.
Satinsu biyar da aure Zainab ta tare matar Hadir. Mami dadi ya isheta ga hausawa
'yan uwanta a kusa duk da nasu gidajen suna bangare daban. Sunfi girma da kyau. Su
Mairama kuwa layinsu daya da Zainab. Hade kai suka yi suna zaman gaskiya da bawa
juna shawarwari. Mami ce babba amma Zainab duk ta fisu wayewa. Mairama kuwa dama
albarkacin boko ta san wasu abubuwan amma kifin rijiya ce. Idan suna hira abin
dariya, Mairama kana jin hausarta zaka gane bafillatana ce, Zainab sakkwatanci
ziryan ita kuma Mami Hausar Katsina.
Yau juma'a Mairama tana cikin girki kafin dawowar Zayyan taji sallamar Awwab. Kowa
yasan dan gidanta ne na gaban goshi. Zainab har ta gaji da mita ta kama kannensa
Zahra da Fauziyya a matsayin nata.
Kitchen din ya shigo ya sameta tana yanka salad.
"Anti kawo in yanka"
"So ka ke Anti Zainab ta shigo ta soma tsokanarka ko" tace tana murmushi.
"Mami tace in gaisheki kuma zata zo kiyi mata kalba anjima"
"Kaje kace mata nace sai ta shigo sannan ka dawo ka ci abinci"
Fita yayi zai tafi ya ga ta biyo bayansa a guje ta shige bandaki tana kakarin amai.
Awwab ya rasa me zaiyi sai kuka yana mata sannu. Ita ke fama da matsananciyar
tashin zuciya da amai kamar zata fitar da kayan cikinta amma kuma ita ke bashi
hakuri saboda yadda ya gigice mata.
"Awwab ka dena kuka mana" tace cikin rashin kuzari.
Kuka yake sosai "to ki dena aman"
"Na gama muje ka zuba abincin idan kaci sai ka tafi"
Kallonta yayi tana dafa bango tana daga kafa da kyar. Hannunta ya rike har kan
kujera yace "In fadawa Mami ko Anti Zainab?"
Da sauri ta dakatar dashi "a'a kada ka fadawa kowa na ji sauki"
"To kiyi dariya in gani"
Dariya ya bata ya kafeta da ido wai tayi dariya. Motsin mutane suka fara ji daga
waje ya tashi da sauri ya bude kofar. Zayyan ne da wani security soja sun kinkimo
katon kwali ga wasu kwalayen biyu kuma a kasa daga gefe. Yana ganin Awwab yace ya
je ya fadawa Mairama ta koma daki zasu shigo da kaya. Ta ji me yace kafin Awwab din
ya dawo ta koma ciki ta kwanta.
Suna shigo da kayan ya fadawa Zayyan tana amai. Nan fa hankalinsa ya tashi ya bishi
dakin bayan sun gama shigo da kayan.
A kwance take tana jin ya shigo ta tashi zaune.
"Mairam me ya same ki?"
Sai da ta harari Awwab ta bashi amsa "ulcer ta ce ta tashi tun dazu da na sha coke
kirjina ke suya"
"Shine baki taba fada min kina da ulcer ba suk sati nake ajiye miki crate din
minerals? To anyi an gama"
Bata da wata ulcer a iya saninta amma ta ki jinin asibiti. Kitchen din yaje ya zubo
abinci.
"Nasan baki ci ba, tashi"
Wani aman taji ya taho mata daga ganin abincin ta daure "Awwab baici ba ka bashi
zan ci anjima"
"Nima bazan ci ba sai kinci" Awwab din yace yana marairaicewa.
Zayyan ya janyo hannunsa ya zauna a kusa dashi da kyar ya samu ya karba yana ci
yana mata hira.
"Kayi min kwacen mata kirikiri yaron nan"
Mairam ta soma dariya da Awwab ya dage sai ya fada masa me yake nufi. Sai can yamma
ya tafi ya fadawa Maminsa bata da lafiya. Taso zuwa amma tunda Zayyan yana gida sai
ta hakura sai gobe.
Sai dare Zayyan ya bude kwalayen da suka zo dasu. Daya firinji ne madaidaici mai
kofa daya amma da freezer daga sama. Sai kuma TV da bidiyo duka sababbi. Mairama
godiya harda kuka don murna.
Bayan kwana biyu kullum tana fama da amai da jiri ya kaita asibiti aka basu
tabbacin ciki ne da ita. Tamkar ya hadiyeta don farinciki. Gani yake yanzu zai sami
abinda zai kira nasa, jininsa sosai.
**********
Lokaci yana tafiya al'amura suna faruwa garesu. Captain Mustapha ya sami karin
girma zuwa mukamin Major bayan ya dawo daga wani aiki da aka tura shi Warri. Zayyan
da Hadir kuma sun zama Lieutenants.
Cikin Mairama yana da wata shida amma idan ka ganta sai ka rantse bazata kara kwana
ba zata haihu. Su Mami sun gama sadakarwa ‘yan biyu ne a cikin. Bata wani laulayi
sosai sai cin abinci akai akai tayi bulbul ta sake kyau da cikowa. Kwakkwaran motsi
idan tayi Zayyan ya rinka cewa yaya akayi. Zainab ma cikin gareta wata uku amma ita
laulayi yake saka ta don bata iya komai yanzu sai kwanciya duk ta rame abin
tausayi. Mazajensu na fita suke tarewa a gidanta su taimaka mata da aikin gida.
Mami tayi ta kokarin hana Mairama amma bata ji, tafi ganewa motsa jikin dama kuma
haka ake so ga mai juna biyu.
Yau litinin suna tare a gidan Zainab su Awwab suka dawo daga makaranta. Tun da suka
ga gidan a rufe sun san inda Maminsu ta tafi sai suka bita. A falo suke zaune suna
hira yau Zainab din jikinta da kwari ba kamar kwanaki ba.
Kowa yana cin abinci an hadawa yaran a tray karami na silver iyayensu su ma sun
hada tare. Zainab ce ta kula da Awwab gabadaya idanunsa suna kan Mairama. Idan ta
yamutsa fuska sai yayi kamar zaiyi kuka.
“Awwabu ya aka yi ne kake ta kallon mamanka?”
“Anti baki ga cikinta ba kullum yana kato kamar na maman Ebere”
Mami ta tuntsire da dariya “kai kuma baka son cikinta yayi irin na maman Ebere din
ne?”
Ya gyada kai “saboda fashewa zaiyi watarana, haka Ebere tace na mamansu ya fashe a
asibiti.”
Zahra ta kai masa bugu a kafada “Kai Hamma haihuwa zatayi fa mu sami baby” Hamma
shine sunan da Mairama tace su rinka kiransa dashi don da fari Awwab kawai suke
cewa.
Maminsu ya kalla a tsorace “kinji tana rashin kunya Mami, ni dai ba ruwana”
Tsokanarsa Zainab ta shiga yi tana cewa Mairama danta yakware a wautar ‘yan fari.
Da abun ya ishe shi sai ga hawaye Zahra da Fauziyya aka sami na yi. Mairama ta
janyo shi kusa da ita.
“Kyalesu baby zan dauko maka a asibiti idan nawa cikin ya fashe kai kadai zaka
rinka dauka.”
Wata dariya ya saki da ta kara masa kyau da nuna kuruciyarsa yana murna, har da
yiwa su Fauziyya gwalo. A haka rayuwarsu take tafiya komai nasu cikin aminci tamkar
‘yan uwa na jini.
Ranar da nakuda ta kama Mairama Zayyan sun tafi gidan gwamnati shugaban kasa zai
kawo ziyara. Nauyi da kunya ya sanya ta kasa fada masa tun gabanin asuba da ta fara
ciwon har ya fita. Gashi abu yafi karfinta zamani ba na waya ba bare ta nemi
taimako. Allah ne ya kawo mata Awwab tana cikin wannan matsanancin halin ta daure
tace yaje gida ya kira Mami kuma ya tabbata ta taho yanzun nan. Ya kusa shekara
tara a lokacin shiyasa duk da bata fada ba jikinsa ya bashi ba lafiya ba.
A guje ya koma gida sai gasu cikin mintuna kalilan. Tana ganinta tace ya fita ta
shiga daki ta taimaka mata su fito kawai ta fara nishi. Mami ta san babu yadda
zatayi tun da ta hango kai yana neman fitowa a take Allah Ya sako mata karfin
zuciya ta karbi haihuwar santaleliyar yarinyar da Mairama ta haifa.
Tubarakallah yarinyar akwai girma da kiba taci ta koshi tun a ciki ga kyau. Kukan
da ta chanyara ne ya sanar da gidan da yake jikin nasu an sauka. Matar gidan
bayerabiya ce suna kiranta Maman Dolapo ta shigo da sallamarta domin su ma musulmai
ne. Awwab aka tura ya kira Zainab itama tazo suna ta murna aka dora musu ruwan
wanka. Yarinya tana ta wutsil wutsil kakkarfa da ita.
Mami girman yana gareta ita ta yiwa Mairama wanka. Jaririya kuwa Maman Dolapo ta
roki alfarmar a barta tayi mata irin nasu na yarbawa. Babu wanda ya hana saboda
zaman mutumci suke yi da ita. Sun kuwa ga wanka ba irin wanda suka saba ba. Ta
wanke yarinyar nan sosai ga mamakinsu harda manja mai kyau ta dauko daga gidanta ta
shefe jikin yarinyar ta mitstsiketa sosai sannan aka fara wankan da kyau ana fitar
da datti da maikon manjan. Ko da ta gama yarinya kana tabata jikin nan subul ta
kara wani haske kamar jini ya fito. Lallausan kayan sanyi aka sanya mata lokaci na
damuna sannan akace Mairama ta bata nono. Nan fa ake yinta kunyar jama’a ko
karbarta ta kasa. Zainab ta kamata ta maidata daki. Zata rufe mata kofa Awwab yayi
kekam dole ta barshi ya bi bayan mamansa ana musu dariya.
Babu abinda makota basu yiwa Mairama ba. Daki ta shiga tayi kukan rashin dangin uwa
da basu damu da ita ba. Da kanta ta nemi Zayyan akan bata son zuwa gida wanka
saboda ta sani ba wata kulawa da zata samu. Bayan auren nasu sunje sau daya bata ji
dadin gidan ba ko kadan. Wani kallo na kyashi ake watsa mata, Yadikko ce kadai mai
janta a jiki. Malamijo kuwa zubar da girma yayi gaban Zayyan yana fada masa yadda
yake cikin mawuyacin halin kula da iyali. Allah Yasa sunyo musu tsaraba irin ta
Sakkwato amma duk da haka sai da ya bashi kudi. Kurewar lokaci yasa basu tsaya a
gidan Salame ba. Abin da bata sani ba da gangan Zayyan yayi haka don ko kadan baya
kaunar yadda Salamen take yiwa matarsa ita kuma bata gani.
Ba su suka dawo gida ba sai daya saura na dare. Lokacin kowa ya watse hatta Mami ta
tafi saboda yara sun fara bacci. Mairama da jaririyarta ma baccin suke jiki ya gaji
ga wankan da suka sha. Ko ina a gyare tsaf gidan ya bude kofar dakin a hankali don
kada ya tasheta ko fitila bai kunna ba. Kayansa ya cire yaje yayi wanka ya fito
yana komai a nutse don baya son damunta. Duhun dakin yasa garin neman robar mai ya
tunkudu wani abu daga kan madubin ya fado da karfi. Karar ce ta tashi baby din yaji
ana inya inyaa.
Hanyar kofa ya nufa da fari ya ajiye sojancin na wucin gadi, sai yaji muryar
Mairama tana cewa shhhh. Da mugun sauri ya kunna fitila idanunsa a kan gadon.
Kyakkyawan gamo yayi. Masoyiyarsa abar kaunarsa ya gani tare da baby kunshe cikin
shawul fari tas.
Zuciyarsa ce tayi wani irin nauyi ya tako gaban gadon a hankali ya zauna a
gefenta. Murmushi ta sakar masa kafin ta dora masa jaririyar a kan hannuwan da ya
miko mata. Rungumesu yayi tare yana fidda numfashi da sauri. Mairama sai ta soma
hawayen farinciki ta kara shiga jikinsa yana yiwa baby addu’a. Sun dauki lokaci a
haka kafin ya bude fuskarta tana tandar baki.
“Yunwa take ji ko?” ya kalli Mairama
Karbarta tayi ta juya masa baya zata shayar da ita ya hawo gadon ya zagaya gabanta
“kada ki cuceni da kunya”
Ba yadda ta iya yana ta kallonsu cike da sha’awa kamar wani zai ce ba nasa bane.
Bai iya tashi ba har ta gama ya ga babyn tayi bacci ita ma idanu sun fara rufewa.
Kwanciya ya gyara musu ya dauko darduma ya shimfida yana nafilar godiyarsa ga
Allah. Duk gajiyar da ya kwaso ranar babu wani bacci da ya iya yi sai gadinsu har
asuba tayi. A masallaci Major Mustapha da Hadir su ka yi masa barka tare da sauran
abokan aikinsu ana taya shi murna. Papa Dolapo ya tsokane shi wai Allah Yasa dai ba
mai kiriniya bane kamarsa akayi dariya.
Aikinsu bai kare ba zasu koma gidan gwamna. Kafin su tafi Major Mustapha da Hadir
su ka je gidan ganin baby da kuma yi mata addu’a. Zayyan ya dan taba Hadir yana yi
masa magana da ido. Ya san zancen shiyasa ya dubi Major din.
“Sir kaine zaka rada mata suna fa, kayi mata huduba”
Wani iri yaji yadda yaran nan suke matukar girmama shi tamkar yayansu na jini “wane
sunan zan saka mata?”
Shiru Zayyan yayi sai ya koma ciki da sauri wurin Mairama a daki.
“Mairam bamu tsayar da shawarar suna ba ga Major can yana jira”
“Sunanta Alheran” tace tana gyara daurin zaninta.
“Nace sunan Innarmu ta Sumaila zamu fara sakawa”
“Don Allah Sojana sunanta Alheran, idan na sake haihuwa sai a saka sunan Innar”
Muhawara suke yi sosai ya gaji ya karbi nata “baki da wani suna da kike son a saka
mata? Suna biyu nake son a saka”
Sarai ta fahimce shi, a dole yana son bata dama ita ma ta sanyawa yarinyar suna.
Sai dai duk yadda take son saka sunan innarta tana ganin shi yafi dacewa da ya fara
sakawa. Bata yi dogon tunani ba tace “Radhiya”.
Murmushi kawai yayi ya fita ya sanar da Major sunan ‘yarsa Alheran Radhiya Zayyan
Muhammad Tureta. Hadir yace “mutumina wannan sunaye haka”
“ ‘Yar soja ce, ya kamata a komai ta fita daban” ya bashi amsa yana magana a
hankali kada a ji.
Major Mustapha ya gama yi mata huduba sannan yace ya maidata ciki suyi shirin
tafiya bakwai ta kusa.
Kwanaki hudu da haihuwa duk wanda ya kamata ya sami labarin haihuwa daga danginsu
ya sani. Tasha Zayyan yaje ya bada sakon wasika zuwa ga Kawunsa Ghoumar domin a
sanar da sauran dangi abinda aka samu. Sai wasikar ta isa akan gaba suna shirin
zuwa saboda aurensa da yazo da gaggawa basu sami damar halarta ba.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: ***********10
Kyakkyawar kulawa da gyara Mairama take samu daga wurin Nene Marka. Ita da Zainab
da Mami shakuwarsu sai gaba take kara yi. Idan kaga Awwab baya gidan to makaranta
ce ta tsare shi ko dare ya tafi yayi bacci. Amma kullum yana wurin Mairama da
kanwarsa Radhiya. Zahra da Fauziyya suna shan gori yayi ta cewa su Antinsu bata
kawo baby ba har yanzu. Idan ya fadi haka Zahra sai tace ai nata cikin ya kusa
fashewa ne su ma bazasu bari ya taba musu baby ba.
Zayyan ba karamin kewar matarsa yake ba. Ko yaya Nene ta dan bada wuri sai ya faki
ido ya rungumeta yana fada mata yadda yake kewarta da matsuwa ayi arba'in dinnan
kowa ya huta. Jaririyarsu Radhiya ta kara yin bulbul gwanin sha'awa. Idan kayi mata
kallo daya sai ka rasa wa ta debo cikin iyayen. Bafillatanar mahaifiyarta ko sojan
babanta da yake surki tsakanin mutanen Agadas da na Tureta. Yarinya ce mai matukar
shiga rai musamman idan tayi murmushi gefen kumatunta na dama ya lotsa. Awwab har
yatsa yake sakawa a wurin don kawai tayi masa murmushi.
Ranar da su ka cika wata biyu Zayyan ya kwashesu a motar haya sai Sumaila. Mairama
bata taba tunanin zata yi kewar gidansu ba sai yanzu. Sun isa yamma likis 'yan uwa
ana ta tururuwar ganinsu.
Malamijo yana jin isowarsu daga gona ya zari takalmansa ya yo gida. Fadi yake
'yarsa mai auren soja ce ta iso tare da jikarsa. Abin arziki kaza guda ya bayar
irin 'yar sati goman nan aka yanka Yadikko ce da girki tayi musu shinkafa da miya.
Daki aka gyarawa Zayyan ya kwana. Da safe abin mamaki sai ga Salame wai bazata iya
jiran su iso gidanta ba tana kewar Radhiya. Mairama taji dadi balle da ta ga yadda
take haba haba da Radhiyan harda su goyo duk da ana hanata saboda nata cikin ya
fara fitowa.
Zayyan dauke kai yayi saboda shige masa da take yi tana ta so ko magana yayi mata.
Allah sai Ya dauke hankalin Mairama daga garesu bata kula ba.
Kwanansu biyu sannan su ka wuce Balan a karkashin karamar hukumar Gaya inda gidan
Nene yake. Tana da kishiya guda daya mai yara shida. Maigidansu manomi ne babu wani
kudi sai rufin asiri. Irin kyautar da Zayyan yayi mata Mairama kanta tayi mamaki.
Nene Marka harda kuka tana masa godiya.
"Nene mune da godiya, Allah Ya saka da