Showing 255001 words to 258000 words out of 295847 words

Chapter 86 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

tace "zuwa nayi mu saukewa juna iskokan dake kanmu
Salame saboda na dade da fuskantar cewa kanki yana da matsala"


Wai saboda karfin hali tana kallon kowa a tsaye ta kumburo baki "saboda na daki
'yar gwal shine kuka yo min taron dangi..." waje tayi sai ta tsaya turus gani ashe
harda Malamijo da Nene, ga su Yadikko da Hajjo. A zatonta Mairama ce kadai da
Baffan Rahima da ta gano tare da Alh Indararo shima tana jin ramawa tasa 'yar yazo
yi. Bude baki tayi za ta sake yin magana Malamijo ya kai mata wani wawan marin da
bazaka taba kawowa a ranka dan hannunsa zai iya ba. Hannu ne na tsohon kashi ya
sake bata a kumatun hagu. Wasawasa sai da yayi mata yafi biyar wani tukukin
bakinciki yasa ta kasa kuka.


"Ke mahaukaciyar ina ce Salame? Na fuskanci burinki bakincikinki ya kaini lahira to
amma baki isa ba. Ko Amiru da yake yawon jagaliya bai samin bakincikin da kike
kunsa min ba"


"Duk wannan abin akan Radhiya ne saboda ita kuna kaunar uwarta tunda babanta yana
da kudi ko"


"Rufewa mutane baki mutuniyar banza" cewar Nene tana jin kamar ta maketa.


Jan bakinta tayi ta tsuke kowa a tsakar gidan ita yake yiwa kallon da take fassara
shi da tsana.


Mairama ta dubi iyayen nasu "Malamijo yau gani ga ka ga kuma babbar 'yarka. Ban san
me nayi mata ba tsayin shekarun nan tun farkon aurenmu amma wallahi na gaji. Daga
yau sai yau idan ta kuskura ta sake taba min yara zan dauki matakin da mu duka nan
sai ran kowa in yayi dubu ya baci." Ta mayar da idanu ga Salame "Wai da nake ta
taraki ki sani ba tsoro bane kawai ina yi ne da sa ran wata rana zaki ajiye makaman
yakinki mu zauna lafiya. Amma tunda kince ba haka ba mu zuba nida ke shege ka fasa.
Duk wani zafin rai da kike takama dashi kin kwana da sanin Mairama tana da dubunsa
a ajiye"
"Kinga malama ni dai ba da niya na taba Radhiya ba. Rahima zan daka ta tare wayar
ta sauka a bayanta ko ba haka ba?" Ta tambayi iska tunda babu mai bata amsa jikinta
yana kadawa kada a cigaba da maganar nan allura ta tono garma.


Malamijo zaiyi magana Mairama ta riga shi "assha 'yar uwa, kada kiyi tunanin dukan
Alheran kadai ya kawoni ko daya. Gobe kafin wannan lokacin zaki baiwa ubanta
bayanin dalilin dukan masa 'ya, kuma kada ki manta matar aure ce ban san me zai
faru ba idan mijinta ya ji. Wannan diban albarka da kike yiwa Rahima kadai ya
isheni. Don ta ni kin dade baki yi min rashin mutumci ba. Ranar da duk na gaji na
fyatoki ba ganuwa zakiyi ba"


Dariyar Alh Indararo ce ta katse Mairama "wai ke nan duk masifar akan dukan da
tayiwa Rahima ne dama? To ni tunda na auri Salame ban taba ganin yarinyar nan ta
shigo gidan nan ta fita babu kwalla a idonta ba. Wannan kuma kadan ne cikin
abubuwan da tayi miki"


"Me kake nufi Alhaji? Wai me kika dauki Rahima ne Salame?" Baffan Rahima ya tambaye
shi a zatonsa ta yiwa 'yar tasa abinda yafi wanda ya gani "yanzu ashe alkhairi zai
iya zama sharri, sharrin ma ka rasa wanda zaka yiwa sai dan cikinka. Kudine dubu
dari da 'yan kai Rahima ta kawo tace min a Habuja tayi lalle ta samu. Shine aka
raba kudin ni talatin itama uwar aka ce ta kawo mata talatin sauran kuwa zamu fara
yi mata tanadin aure. Shikenan daga zuwanta ta dawo min gida da fuska a kumbure" ya
kare zuciyarsa a karye saboda shi ba ma'abocin fada bane. Mutum ne mai kyaun hali
da matukar hakuri. Kaddararsa daya bata wuce soyayyar Salame da tayi masa mugun
kamu ba ashe rabon haihuwa ne yasa ya aureta.


Maganganunsa ba karamin shigar Salame tayi ba sai lokacin ta sake kallon ledar da
Rahimar ta yar saboda marukan da ta sha. Kenan Mairama sake bawa Rahima wani kudin
tayi a madadin wanda ta karbe? Wani abu taji yana neman danne mata zuciya sai dai
bata yi nisa ba ta tsinkayi muryar Alh Indararo yana cewa "wanda bashi da kashin
arziki ko a cikin rijiyar kudi zaka tsoma shi bazai taba yi ba. Nan ta dawo da kudi
dubu dari tana yi mana burga wai 'yarta ta fara sana'a. Ci banza ci hofi bana jin
akwai sauransu yanzu ma."


Kallon banza Mairama ta watsa mata saboda da gani babu abin tsinta a jikin Salame
bayan tsiya tsagwaronta. Juyawa tayi da zummar fita daga gidan Alh Indararo ya ga
idan yayi shiru ai wasa ya kare bayan ko rabin tanadin da ya yiwa Salame na
bakinciki bai idar ba. Fada sosai Malamijo da su Nene suke yiwa Salame shi kuwa
yayi saurin tsayar da ita.


"Mairama ince ko kina da masaniyar cewa duk wannan rashin hankalin da Salame take
yi miki tana yi ne saboda son mijinki da take yi"


Cak Mairama ta tsaya ta juyo a hankali ta koma gaban Salame ta rike hannayenta duka
biyu ta soma yi mata fada tamkar 'yar cikinta "da gaske baki da hankali ne Adda? Ta
yaya za'ayi ki bari duniya tasan cewa kina son mijin kanwarki? A lokacin da ake
zaton babansu Karami ya rasu babu kunya kika dubi idanuna ina zaman kunci da zafin
rabuwa kika fada min kinso shi na hakura ban taba daga zancen ba. Adda Salame a
lokacin har tausayinki na ji saboda soyayya bata taba yiwa mutum uzuri sai nake
ganin ba laifinki bane." Hawaye ne mai zafi ya ke fito mata saboda rashin sanin
wace irin mutum yayarta ta zama "idan kika kuskura kika bari su Halifa suka san
wannan abin nayi miki rantsuwa abinda ya rage na kimarki da darajar uwa a zukatansu
sai ya tsiyaye ya bi rariya."


Baki na rawa Salame ta iya hada kalmomin "sharri...sharri ne. Sharri yake min"


Tsawa Malamijo ya daka mata "Ki rufe min baki shashashar banza wadda bata san ciwon
kanta ba...ko kinsan ko sati biyu bamu rufa ba da nasa Halifa ya hadani da babansa
kuma ya tabbatar min dalilinsa na sakinki kenan. Har yaushe zaki cigaba da karar da
rayuwarki akan hangen ta wani"


Mairama gani tayi idan ta cigaba da tsayuwa ba mamaki a kwashi Salame a baro saboda
ji take yau da ita ce ta haifeta sai tayi mata dukan kawo wuka ko za'ayi sa'a kanta
ya dawo daidai.


Abinda Nene Marka take ta gudun fitowarsa Alh Indararo yace "ke kuwa wace irin
zuciya gareki Mairama? Ta so mijinki kin sani baki dauki mataki ba sannan ta
makanta ki tsahon shekaru shima duk taci bulus kenan? To idan ke kin hakura ni
bazan yafe ha'incin da tayi min ba na asirin aurenta ba tare da son raina ba"


Suman tsaye Mairama tayi jikinta yana bari kamar wadda aka kwara wa ruwan sanyi
wani irin kallo take yiwa Salame ita kuwa sai girgiza kai take yi tana hawaye tare
da yarfe hannuwa. Bata taba jin tsoron batawa wani mahaluki rai ba sai yau da take
jin ta tsani kanta saboda sabanin kallon tsana ko fushi sai ta ga kallon tausayi
sosai Mairama take yi mata. Idanu Mairama ta rufe hawaye suka zubo tasa bayan
hannunta share sannan tayi murmushin kafi kuka ciwo. Muryarta tayi mugun sanyi ta
dafa kafadar Salame tace


"A kaina saboda ba kya kaunar ganin murmushi a saman fuskata kika yi shirka Adda?
Shin Adda kina tunanin zaki iya rayuwar da nayi ne har kika zabi neman yadda zaki
mayar da rayuwata taki? Kin taba tsawaita tunani kice Mairama shekararta ashirin da
hudu da aure amma har yau bata taba zaman shekara uku tare da mijinta ba har girma
ya soma zuwa garesu. Ban san kiyayyar da kike yi min ta kai haka ba amma ina
rokonki da ta tsaya a kaina ni kadai kada ki kuma bari ta shafi 'ya'ya. Daga yau
kuma nayi miki alkawarin idan har ba bisa lalura ba ko ke kika nema da kanki bazaki
kara ganin fuskar Mairama ba bare ta sanya miki bacin rai." Tafiya ta soma yi cikin
wani irin kunci mara misaltuwa su Malamijo suka bi bayanta tunda babu wani amfanin
jan magana kuma.


Bacin rai sosai Mairama take ji a wannan lokacin. Ita kam bata taba nufin kowa da
sharri ba amma ga wadda tafi so duk duniya tun kafin tasan kanta tana neman ganin
bayanta. Wanda zai makantaka ko na kwana guda ne ai babban makiyi ne bare wannan
shekaru haka cikin kwanciyar hankali.


Da sauri Salame cikin rashin sanin madafa ta bi bayansu ta sha gaban Mairama. Kuka
ta ga kanwarta tana yi sosai fuskarta tayi ja.


"Me kuma ya rage, raina kike nema?" Mairama tace da kaushin murya. Da sauri Salame
ta girgiza kai "to bani hanya in wuce don ni da kike gani na haufu cikin uwa da uba
bana amai na lashe. Tunda nace kin dena ganin fuskar da kika tsana to kin daina da
gaske ba wasa ba" tace tana rabewa ta gefenta ta fita daga gidan.
A kafa su ka tafi gida babu mai cewa wani uffan kowa da nasa tunani. Sun kusa kofar
gidansu Malamijo ya yanke jiki ya fadi tunani yayi masa yawa saboda ko ba'a fada ba
ya sani cewa shine musabbabin lalacewar duk wani bara gurbi ciki 'ya'yansa kamar
yadda yasan cewa duk wanda ya shiryu a cikinsu daga Allah ne da taimakon Yadikko
matar da bata haifi ko tsinke ba amma taci kashi da fitsarin kusan duka 'ya'yansa.


Allah Yasa Baffan Rahima yana biye dasu saboda son ya ga halin da 'yarsa take ciki
ya tafi da ita gida. Hankalinsu duk ya tashi musamman Mairama da take yiwa yau din
kallon bakar rana ya ciccibe shi ya saba a kafada ya karasa dashi gidan. A kidime
Mairama ta kira Radhiya ta turo musu Lucas tace ai sun kusa gida an duba su.


Da sauri sauri suke shirin saka shi a mota ya farfado yace babu inda zashi.


Hajjo tun tana lallaba shi har ta koma fada "so kake ka cuceni kawai. Cikin
shekarar nan na dana zaman iddah yanzu kuma takaba kake son kakaba min don mugunta
daga dawowata"


Duk da yana jin jiki bai hana shi galla mata harara ba "ina jin har kin gama
lissafin tumunin takaba to ta Allah ba taki ba. Ina nan garau ba mutuwa zanyi ba.
Ke in bakiyi wasa ba fa Hajjo sai na kaiki zan taho daga baya"


Cinya ta buga tana dariyar jindadin ya tashi amma duk da haka bata barshi haka ba
"ashe da rabon ayi suna da kai"


Sam ya manta a waje suke ya kalleta a tsorace yana hadiyar yawu da kyar "wace take
da ciki kuma ni Ali wai ku baku da tausayi ne bazaku barni na huta ba"


Radhiya, Rahima da Mama basu san lokacin da suka sa dariya ba Ummi ta tallewa
Radhiya da Rahima keya tana murmushi suka shige cikin gidan. Manyan daki suka shiga
suna cigaba da tattaunawa Mama da Ummi kuma su ka tafi dakin da aka basu. Radhiya
ma da Rahima daki daya suka shiga nan Rahima tana hawaye ta soma cewa Addarta tayi
hakuri da abinda Ummansu tayi mata. Daure fuska Radhiya tayi tana harararta da wasa


"Rahima bana son kina sake tada wannan maganar. Nasan ko ma meye su Ummi sun gama
daidaitawa a junansu babu ruwanki"


Wani kukan ne ya taho mata ga idonta daya yana zugi kamar zai fado "Adda ni
shikenan Umma bata sona, me nayi mata ta tsaneni?"


Tausayi da kaunar kanwarta ya sake kamata ta zauna a kusa da ita ta rungumeta
haushin Salame yana kara kamata. Allah Yasa kada Rahima taji sauran maganar game da
Gwaggo Salame don tasan it will break her heart fiye da yanzu. A tausashe tace
"Ummi tana sonki kinji kuma bazata sake bari ta dakeki ba"


"Mu ga bayanki" Rahiman tace a kokarinta na nemo nutsuwa ta yafawa kanta a dole.
Radhiya kwanciya tayi Rahima ta dage rigarta wurin yayi wani iri da yanzu ita za'a
sake saukewa wannan bulala bayan wadda ta sauka a fuskarta. Maganin da aka basu
tace za ta shafa mata Radhiyan tace ta bari suyi wanka sai su shafa.


A dakin da su Ummi suke kuwa suna shiga ta haye gado ta kwanta tare da juyawa kofa
baya. Kuka take yi sosai jikinta har wata irin karkarwa yake yi. Abin na Adda
Salame har ya kai haka ashe. Ita kuwa banda auren Zayyan me kuma tayi ta konawa
'yar uwarta rai haka. Mama jikinta duk yayi sanyi a hankali ta zagaya gabanta ta
zauna daga gefe.


"Mairama" tace cikin sigar rarrashi.


Sake juya mata baya tayi muryarta har tana sarkewa tace "ki barni inyi kuka Zainab,
ashe a duniya akwai wanda zai tsaneni har ta kai ga yi min asiri na makance. Ina
nan ina yiwa kaina kallon wadda bata shiga gonar kowa ba ashe na kure yayata
kiyayar tayi tsamari" dago rinannun idanunta tayi suka hada ido tace "Allah kadai
Yasan mutum nawa ne suka tsaneni"


Hawaye Mama ta soma yi itama "mijinki yana sonki Mairama. Ni da Mami muna kaunarki
kamar ciki daya muka fito kuma ga Malamijo da sauran mutanen gidan nan, banda su
Radhiya rabin rai" ta dage mata gira.


Murmushi Ummi tayi kamaninta da Radhiyan suka fito sosai "nagode Zainab Allah Ya
kara mana zumunci. Inama Mami tana nan da nasan bazata gudu ta barni yadda kika yi
ba dazu kawai ina cikin fada na juya neman support na ga wayam"


Mama sai da tayi dariya sannan ta kira mata Mami. Tana dauka bayan sun gaisa take
basu labarin yadda suka yi da Alh Baba wurin shiryasu ita da kannenta.


"Nan ma fa fama muke ina jin shirin ne za'ayi idan an gama hawa saman" cewar Mama.


Ummi cikin kuka take yi musu bayanin abubuwan da suka faru. Su duka ukun kuka suke
yi musamman Mami da tayi nisa tana jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta wanke Salame
irin wankin babban bargon nan. Zumuncin da yake tsakanin su uku abin burgewa ne da
sha'awa domin kowacce da zuciya daya take son sauran.


Bayan sun gama Mama tace "to saura Oga tun dazu wayarki ke haske nasan shine"


Murmushi na musamman Ummi tayi ta mika hannu ta dauko wayar wanda yayi daidai da
sake kiranta da Zayyan yayi. Tana dauka ko sallama bata yi masa ba ya kira sunanta
a kagauce saboda yadda hankalinsa ya tashi. Jin muryarsa kadai ya sake tado mata
abinda Salame tayi sai kawai ta fashe masa da kuka. Yi take yana sauraronta yayin
da Mama ta dauke DK tayi waje don ta basu wuri. Sai da tayi mai isarta tayi shiru
don kanta. Hakuri ya bata tare da kalmomi na kwantar da hankali sannan ya nemi jin
ba'asi.


"Ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allahu jirgin safe zan biyo"


"Sojana" yaji ta yi masa kiran da dole ya amsa.
"Mairama Fillon Zayyan me kuma akayi?"


Kukan yaji ta cigaba da yi "Don Allah ka fada min ni muguwa ce ko naso kaina ne da
yawa da na aureka har ya janyo min kiyayyar Adda Salame?" Ta fada da wata irin
murya abin tausayi.


Kwafa yayi kawai yana jin kamar ya baro garin Sakkwato a lokacin saboda yazo ya
nunawa Salame kurenta.

"Ki bari inzo goben sai na baki amsar da ta dace. A haka babu abinda zaki fahimta"


"To don Allah ka taho da wuri sosai, yau ina jin ko bacci bazan iya ba"


"Saboda kewata ko saboda Salame ikon Allah?"


Dariya ya bata "bani da sauran abinda zance mata na bar maka komai Daadan Alheran"
ta kare cike da kunya.


"Ki cire komai da kowa a ranki ki barni ni kadai yau dinnan bana son tunani ya
dameki. Ina nan tare dake babu wanda zai taba min ke batare da na nuna masa mijinki
yana sonki ba"


Sannu a hankali ya mayar da akalar hirar ta soyayya inda yayi nasarar rabata da duk
wata damuwa.


**********


Hawaye kafewa yayi a idanun Salame tun bayan fitarsu Mairama ta koma ciki tana tafe
kamar kwai ya fashe mata a ciki ta shige dakinta. Mayafi ta dauko ta fito Alh
Indararo yayi wuf ya fito daga falonsa.


"Ina zaki je?"


Bata da wani kuzari bare tayi masa rashin kunya "ka yiwa Allah ka barni inje gidan
Ta Madina"


Baki ya rike saboda tsabar mamaki kamar wata mace "Ta Madina dai mahaifiyarki?"


Kai ta gyada masa kai kace kadangaruwa ce.


"To sai kin dawo yau nasan zata ce tayi gamo. Idan kin fita ki turo min 'ya'yana.
Kuma Yasin kika kuskura isha ta riskeki a waje ko a ina ne har can zani na sabunta
miki kamanni muguwa mai muguwar zuciya"
Bata iya tankawa ba ta fita tayi sa'a kuwa jikin gidansu yaran suka shiga. Gida
tace su koma sannan ta wuce gidan babarta a kafa tafiyar minti sha bakwai ta kaita.
Da sallama ta shiga jama'ar gidan su ka rinka kallonta kamar an ga wata sabuwar
halitta. Babu wanda ta kula ta kunna kai dakin Ta Madina ta sameta zaune akan
tabarma tana gurza goro. Da mamaki ta dago tana kallonta kafin ta soma magana.


"Iko sai Lillahi...Salame ke nake gani ko kuma gizo kike min. Tohhh ni dai ban
kwana dake a raina ba bare ace saka ki nake a zuci har kika fara min gizo"


Daga bakin kofar Salame ta zube saboda ganin uwa mai dadi ta shiga kuka tun daga
kasan zuciyarta. Ta Madina kamar mai kallon film haka ta kare mata kallo ta gama
kukan bata ce komai ba. Sai da ta fuskanci kamar tayi shiru ta tabe baki tace
"alhaki kwikuyo ya biyoki kenan. Ina kyautata zaton wannan hawayen na Rahima ne ko
hakkinta. Ko ma wanne ne a dakin nan nace miki da sannu zaki ganewa idanunki illar
abinda kike matar Alhaji"


Da kyar ta iya cewa "Ta Madina baki kika yi min gashi ya kamani"


"Karya kike" ta nunata da yatsa a harzuke "ke idan nayi miki baki buzunki ma bazai
ganu ba in fada miki."


Kai ta sunkuyar tana ji Ta Madina ta cigaba da fada "wai ni Salame zaki nunawa kina
auren maikudi ban isa dake ba. Nan inda kike zaune lokacin kika tsaya kina fada min
maganganu saboda Rahima tazo ta roki in baki hakuri ki yafe mata ko ma menene tayi
ki dena dukanta. Saboda kinci maiko kin tada kai kika kada baki kika ce mata idan
ta kuma zuwa wurina baki yafe mata nononki da tasha ba. Ni...ni Salame kika yiwa
wannan rashin arziki"


Ta sani ita din mai laifi ce sosai a wurin mahaifiyarta. Idan bata ga ba daidai ba
a dalilin kowa dole ne ta gani a dalilin Ta Madina. Muryarta ta ji tana ta koro
bayani kamar yau akayi.


"Yarinyar nan tayi kuka kamar me tun daga ranar idan tazo daga waje take kwada
sallama na fita mu gaisa. Yau shekara biyu rabona da ita saboda kaninki Sa'adu
rannan yayi fushi ya daukota a ka ya dire min ita yace idan kin isa kizo gabansa ki
tabata. Da yake ta gaji halin kwarai wurin babanta a guje ta fita tana tuna kalmar
rashin yafiya da kika jefa mata...shikenan ta dena zuwa"


Ajiyar zuciya ta saki ta gurfanar da kai "Ta Madina ki yafe min amma yau abinda ke
damuna yafi karfin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login