Showing 156001 words to 159000 words out of 295847 words
Biki ne zasu yi na huce haushi anki sakani cikin komai ba sai na kawo ido
na saka musu ba"
"Kece babba fa Hassana, lokaci yana tafiya. Ina ganin ya kamata kiyi yunkuri da
kanki kamar yadda Mairama ta baki shawara. Kunje kuna rigimarku ta mata kun bar min
yaro yana hanging"
"Ya bar kansa dai. Idan yayi sake wani ya nemi Radhiya a Nijar shi ya sani"
Daddy ya mike "to ba dama na baki ba ki saka min yaro a gaba."
"Na nawa kuma" tace tana murmushi.
Washegari da yamma Major, Baba Hadir da Awwab suka tafi gidan gwamnatin Plateau da
yake unguwar Asokoro a Abuja. Kofar gida ya fito da kansa ya tarbesu bayan an bude
kusu gate sun shigo. Da murmushi a saman fuskarsa yace "wannan me Awwab ko?"
Awwab ya rissina kai Excellency ya kamo hannun damansa suka yi musabaha sannan suka
shiga ciki.
"Nayi zaton zaku taho da iyalinku shiyasa muka taho da Arifah da mamanta. Bari na
kirasu ku gaisa"
Waya ya kira sai ga matarsa Haj Rabi da Arifah sun fito. Suna shigowa idanun Arifah
suka sauka akan Awwab mamaki karara ya bayyana akan fuskarta. Sunfi shekara da
haduwa amma ina zata manta shi bayan bata sati biyu bata kira shi a waya ba.
"Captain M.A Mustapha?" Tace tana rike baki.
Excellency ya saki fuska "kin san shi ne?"
Murmushi tayi ta gyada kai tana hango nasara a tattare da soyayyar da take yi masa.
Ace gashi har cikin gidansu kuma da ga mutumin da Dad dinta ya daukesu da matukar
kima a idanunsa.
"Ikon Allah, ashe sun san juna mu sai yanzu Allah Ya nufa"
Arifah dai murna kamar me ta fita taje ta sake kwalliya ta tura wata mai aikin ta
kira mata shi zuwa garden din gidan.
Mai aikin kuwa taje ta isar da sako gashi a gaban mahaifinta dole ya tashi. Shi
gabadaya tunaninsa ya kasa tuna wacece ita.
Takunsa kadai abin kallo ne a lokacin da yake tahowa gareta cikin shiga ta manyan
kaya. Dinkin irin wanda matasa suke yayi ne riga ta dan zarce gwiwa amma hannunta
da kadan ya wuce gwiwar hannu. Yadin yayi masa kyau sosai babu hula a kansa sai
gyaran fuska da yayi batare da sake aski ba.
Tana zaune akan wata kujera karkashin wani abu da akayi da kaba ya bada sassanyar
inuwa ya iso ya tsaya bayan tafiyar wadda tayi masa jagora.
"Zauna mana" Arifah tace tana murmushi.
Kamar bazai zauna ba sai kuma dai ya tuna cewa nan gidansu ne ga kuma irin karamcin
mahaifinta ga nasa iyayen. Tunda ya zauna bata ce komai ba sai aikin kallonsa tana
yaba komai na halittarsa.
"Ya dai?" Ya tambayeta yana hade rai.
"Hmmm Captain baka ganeni ba da gaske?"
Kalmar Captain din kawai tasa ya tuna a ina ya saba jinta "kece mai kirana?"
"Arifah sunana" ta bashi amsa da murmushi "Captain ka wahalar dani ko ince kana kan
wahalar dani sai kuma ga ka a gidanmu abinda ban taba zata ba"
"Allah Yasa dai bazaki sa a kulleni ba a yar da key din"
Dariya tayi "ko daya sai dai ina neman sanin dalilin wannan mugun jan aji da
yakamata ace ni nake yi maka"
Kai tsaye yace mata "na sha fada miki na kusa aure"
"Na dade ina kiranka Captain amma har yau ba'ayi auren ba sai kora da hali da kake
yi min."
Kunyar abubuwan da ya rinka yi mata yaji da kuma rashin dacewarsu "kiyi hakuri
maybe mun fara on the wrong side. Sunana Awwab ke fa?"
"Arifah"
"Arifah ina da wadda nake so sabani ya shiga tsakaninmu. Kiyi hakuri idan hakan ya
bata miki amma iya gaskiyata shine bazan iya hadata da kowa ba"
Ya dade yana fada mata shiyasa bata yi wani mamaki ba "she is lucky amma nima zan
gwada tawa sa'ar idan ka amince"
"Kada muyi haka dake Arifah. Akwai danganta mai girma yanzu tsakaninmu. Mahaifinki
ya taimakawa nawa iyayen kamar yadda naji labarin wadda nake so din itama nata
mahaifin ya taimaki naki. Mu duka wata alaka ce tsakaninmu da bazan so soyayya ta
sake batawa ba kamar yadda tayi min a abaya."
"Wai kana nufin Alheran kake so?"
"Ya akayi kika gane?"
"Saboda ita kadai ce wadda nasan babanta ya yiwa Dad abinda kullum baya gajiya da
bada labarinsa yana binsa da addu'a"
Awwab da ya koma mai wuyar sha'ani sai gashi saboda hirar Alheran ce ya sake yana
yiwa Arifah labarinta. Taji tausayinsu matuka da taji dalilin rabuwarsu.
"Na hakura ba don bazan iya ba sai don Alheran din nan da ban taba gani ba nasan
tafi karfina indai a kan ka ne. Dad dina da naka duka owe their lives to hers. Ina
son Dad dina dole ne in taya shi kyautatawa Alheran da family dinta"
"Nagode sosai Arifah" Awwab yace yana mikewa tsaye.
"Tunda na zama kanwarka Allah Yasa ka dena kin daukar wayata"
Yana tafiya ta jiyo shi yace "daga yanzu da kaina zan rinka kiranki"
Kyakkyawar alaka da aka gina bisa gaskiya da amana ita ce ta cigaba da wanzuwa
tsakanin gidajen mutanen nan guda hudu. Wato gidan gwamna, Major, Baba Hadir da
Mairama matar Tureta.
His Excellency Nasiruddeen ya cika alkawari domin kuwa har cikin gida aka je aka
dauko masa Maikudi yasa aka kulle shi. Idan mutum yana cin kasa ya kiyayi ta shuri.
Radhiya ta mayarda kai sosai a karatunta Nasara tana goya mata baya. Akwai shakuwa
mai karfi tsakaninta da Yousuf yana bata kulawa sosai duk domin sharar fagen
gabatar da soyayyarsa gareta a gaba. Abubuwa da dama na halayenta rashin Awwab ya
sanyata ta barsu sai dai shagwaba kam ko Zayyana albarka. Tazo Nigeria daga Niger
ta zaga dangi sosai lokacin Awwab ya koma aiki.
A lokacin ne kuma akayi bikin Ghazalatu da Nura. Hadadden gift Awwab ya aiko mata
dashi na aure amma bai sami damar zuwa ba saboda training course da ya tafi na
shekara daya a Ukraine zai sami karin mukami idan ya dawo. Habaici da bakaken
maganganu duk da Mami tana bakin kokarinta akan kannen nata sai da suka rinka yaba
mata. Ummansu har tara su tayi ta sanar dasu cewa saboda zumuncinsu kada ya baci
Mairama ta raba 'yarta da Awwab gashi har yanzu ya kasa aure. Hussaina sai cewa
tayi dama can kwadayi ne ya kawosu da suka ga anfi karfinsu sai suka ja baya.
Maganar ta yiwa Mami ciwo amma bahaushe yace wai gani ya kori ji. Idan kuwa hakane
to zata basu mamaki su duka wallahi. Bazata ce musu komai game da tsatson da
Radhiya ta fito ba sai dai ido ya gani anayi.
Duk wannan maganganun anyisu ne ranar Kamun Ghazalatu a Katsina kuma Mama taji
saboda cikinta ya fara nauyi tafi son zama wuri daya shiyasa tana dakin suke yi. Da
daddare suna dakin Mami a gidansu na Katsina daga ita sai Ummi ta tayar da maganar.
"Mairama dan taso muyi magana don Allah"
"Allah Yasa lafiya uwar 'yan hudu"
"Ba amin ba wallahi wannan addu'a sai 'ya'ya"
"Matsoraciya, tunda kika kunso gara kiyi da yawa kawai"
Dariya tayi tana fatan Allah Ya kawowa Ummi miji tayi aure itama.
"Dama magana ce akan Radhiya da Awwab. Ki taimaka mu fitar da Mami kunyar marasa
kunya Mairama. Dazu idan kinji irin kalaman batanci da suke fadawa Mami a gidan da
akayi kamu sai kin kusa kuka."
Shiru Ummi tayi tana nazari. Itama sun yi da ita batare da sun gane ita bace suka
zageta tas akan ta likewa Mami ita da 'ya'yanta. Ai kuwa zata taya Mami nuna musu
kurensu ita ce fa Mairo 'yar kunamar Malamijo.
"Zainab kisha kuruminki kawai ki zuba min ido wannan karon. Ni har za'a nuna min
rashin mutumci ina diyar Ali Gidado? Kawaici ne kawai nake yi domin inganta musu
zumunci amma tunda abin ya zama haka idan kinje gida ki fadawa Baba Hadir suyi
magana da Major. Awwab na dawowa daga Ukraine a daura musu aure da yarinyar nan"
Da karfi Mama ta mike saboda farinciki har sai da cikinta ya amsa amma bata hakura
ba ta rungume Ummi.
"Wani sha'ani sai bikin 'yar mutan Agadas. Kin biyani ko ba soso da sabulu kin
wanke ni da kyau. Su Awwabu za'a shiga sahun manya kice"
Ummi ta dafe kai da kunya "wannan zancen ba dani ba"
"Wai da mu fara gyara amarya tun yanzu in soma aike" ta fada da shakiyanci ai kuwa
tayi nasarar korar Ummi daga dakin tana cewa abu kusan wata goma gaba take wannan
tunani tun yanzu.
**********
"Is it true you be Aboki?" Inyamurin ya tambayi Zayyan da gurbataccen turancinsa
wanda aka fi sani da pidgin english.
"Ni bahaushe ne idan abinda kake nufi kenan" ya amsa masa da turanci cikin calm and
gentle voice dinsa.
Ko a zaman kurkuku Zayyan ya fita daban saboda yadda zuciyarsa take mai kyau Allah
Ya sanya masa kwarjini da haiba a cikin mutanen da yake.
Inyamurin ya daka tsalle yaga dan kasarsu ya rungume shi. Zayyan bai nuna kyama ga
mutumin ba shima ya rike shi. Magana ya koma yi da normal turanci
"Sati na biyu a Wing B cikin wahalar mutanen da muke daki daya dasu. Wani Warden
(gandiroba) ne jiya yace idan sun sake tabani nace ni dan uwan Zayyan ne." Kallon
Zayyan din yayi sosai "kasan me ya bani mamaki?"
"Sai ka fada"
"Ina ambaton sunanka nace kasarmu daya suka watse. Nayi mamaki matuka gaskiya. Who
are you?"
Bai cika son yawan magana ba amma kuma baya son wulakanta mutum ba farko da ya gani
a wurin da yake matsayin dan uwansa na kasa daya. Takaitaccen tarihin rayuwarsa ya
bawa mutumin sai gashi yana hawaye.
"Yanzu kai soja ne kuma kayi wadannan shekarun babu wanda ya taba nemanka?"
"Nawa kundin qaddarar kenan"
"Aboki ni sunana Chibuzor Kalu. Matata ce 'yar kasar nan amma a UK muke da zama. Ta
haihu ne tazo ganin gida da baby, to dama munyi da ita ni zanzo daukarsu. Ni dai
bansan yaya akayi ba aka kamani da kwayoyi a jakata. Ka ganni nan ko taba bana sha
amma anyi mana kudin goro kowa ya ga Igbo man sai yayi masa kallon mai ha'inci. Sun
kulleni ne ana can ana binciken ainihin wanda ake zargin ya saka min kwayoyin a
cikin kayana"
Zayyan ya tausaya masa domin yakan sami labarai akan masu harkar kwayoyi irin
tsananin da suke shiga idan an kama su.
Shi da yake da saurin sabo sai gashi Chibuzor ya zama tamkar wani dansa. Ko ina
tare zaka gansu a cikin prison dinnan har aka gama zaman shari'arsa na tsahon wata
bakwai ana fafatawa aka gano sharri ne kawai aka yi masa. Ranar da zai fita yayi
kuka har ya gode Allah. Bai san haka shakuwa take da tasiri ba sai da zai rabu da
Lt Zayyan Muhammad Tureta.
"Sir please ka bani address dinka, a ina zan sami Maman Alheran?"
Karo na farko tun bayan shigowarsa wannan kangi Zayyan ya sami kansa da zubar
hawaye. Shin yasa rai da zai sake shakar iska freedom ko kuwa? Akwai rabon idanunsa
su sake kallon na Mairama masoyiyarsa da Alheran da kuma abinda Allah Ya azurtasu
dashi? Rungume Chibuzor yayi yana hawaye ya fada masa sunan barrack din da ya
zauna.
"Tell them Lieutenant Zayyan Muhammad Tureta is alive"
💕11/2, 7:11 AM] : 38. 💕
Harabar Nigerian Defence Academy (NDA) ciki da waje cike yake da motoci kala kala
na dunbin jama'ar da suka zo musamman domin taya 'yan uwansu murnar gama karatu da
fita da mukamin second Lieutenant ga mafiya yawansu. Kalilan a ciki irin su Mairama
sun zo ne domin karfafawa 'ya'yansu gwiwa.
Daga Kano Ummi sun taho da Mama, Baba Hadir, Ibrahim da kanwarta Laila da take
tsarar Emzee. Daddy shi kadai ya taho daga Katsina saboda Zayyana ana makarantar
kwana kuma satin Mami daya da tafiya Germany wurin Zahra haihuwa ko yau ko gobe.
Fauziyya nata dan Amin watansa biyu. Ansan bahaushe da karamci da kawaici bisa
ka'ida idan da hali da kuma lafiyar yi Hussaina ko Gambo ya kamata su tafi. Amma
kowacce ta shafewa idonta toka har yau ana nan babu wani chanji. Ummansu tayi fadan
har ta gaji yanzu maganar Hussaina kadai Mummy Gambo take ji. Bikin Nura da
Ghazalatu watanni ya rage don ma an daga saboda korarsa da akayi daga wurin aiki
sai da Daddy Haroun ya shiga ya fita ya sama masa wani. Tun a lokacin Mummy ta soma
shan jinin jikinta game da auren amma tasan ko tasha giyar wake Alh Baba bazai
saurari wata magana akasin wadda suke a kai ba.
Ummi tana tsaka da karatu Mama kuma dama dole ke dauketa daga gefen Baba Hadir. Sau
daya taje China bayan dawowarsu ta saro kaya masu uban yawa. Da suka kusa karewa
sai sako ta bada Ibrahim bashi da isasshen lokaci saboda karatu bare ta barsu tare
ta tafi. Yanzu lafiya ta fara wadata gareshi magana ce dai har yanzu suke ta sa
rai. Sai kuyi dogon zance dashi yanzu ta hanyar rubutu a takarda ko text a waya.
Sai yayi awa guda da Radhiya suna musayar sakonni tace wannan tace wancan duka yana
biye mata. Haka Emzee duk wata hira da uba yana yi da Babansa Hadir ne. Sunfi jin
nauyin Major kasancewar shine babba.
Basu sami ganin Emzee ba yana tare da wadanda zasu yi marching din tare dasu. Sanye
suke da kayan sojoji dalibai koraye kowannensu yana jin kansa wani ne saboda samun
gurbin karatu a NDA sai anyi sa'a. Shima sai yanzu yake jin da baizo ba da ya cuci
kansa. Har tsokanar Radhiya yake yi wai tana missing.
Convey din babban bako na musamman gwamnan jihar Plateau Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu
wanda tun lokacin kamfen jama'ar gari suke kira da Tsohon Soja ta shigo makarantar
jiniya ta karade wurin. Watan shida kenan da rantsar dashi a matsayin sabon gwamna
bayan zaben da aka gabatar a farkon shekara. Motar da yake ciki tare da Arifah sai
da ta kawo shi kusa da inda aka tanada domin zamansa sannan aka bude masa ya fito.
Kwarewa a siyasa da kuma tuna baya shima kayansa da suka dace da tsohon mukaminsa
ya sanya sababbi fil sai ya fito a sojansa don ma dai ya fara ajiye tumbi. Arifah
kuwa wani dankareren lace ta saka yellow da fari anyi mata dinki irin na zamani.
Bata sa dankwali ba sai mayafi fari da ta yafa kashka mai matukar kyau da tsada.
Komai na jikinta kudi ne tayi kyau sosai abinta. Commandant din NDA din wato
shugaban makarantar gabadaya ya taso ya tare shi har mazauninsa. Sai da ya zauna
sannan aka shiga gabatar da events din taron.
Abubuwan da suke yi sun kayatar da Ummi da Mama, Ibrahim kuwa cewa yake ko dai
shima zai taho ne ya kyale BUK. Major da Baba Hadir kowannensu sai ya sami kansa da
tuna lokutan baya da suke training tare da Zayyan a Giginya barrack da irin zaman
da suka yi har rabuwarsu. Suna ta sauraron jawabai daga manyan baki da kuma ganin
abubuwan da sojojin suka tanada domin kawatar da taron Ummi ta kula motsi kadan
Mama sai ta dauko wata danyar goba a jakarta ta gutsira ta mayar.
Suna hada ido Mama ta kawar da kai gefe tana dariya Ummi ta kusa yin ihu don murna.
"Kice Allah abinda nake zargi ne" ta riko hannun Zainab tana binta da kallo ko zata
gane wani sauyi a jikinta.
"Bansan ki da sa ido ba Ummin Awwab" tace mata tana boye dariyarta.
"Harda hanci da baki babu abinda bazan saka miki ba. Taimaka ki fiddani duhu 'yar
uwa. Shin da gaske ne?" Doki da murna sun kamata kai kace kananun yara ne.
Sai da Mama ta rage sautin muryarta ita kuwa ta kawo kunne ta kara mata "ban yi
test ba amma jikina ya bani"
Hannunta Ummi ta damke tana murna sosai "yau Mami zata sha story, ahhh su Zainab an
girma ashe ba'a girma ba"
Dariya tasa daga baya ta shiga nunsta da yatsa "Kinga Mairama ki kiyayeni, wallahi
aure zan miki ko don na rama"
"Aure sai na 'ya'yanku idan sun shirya amma ni kam mijina yana jirana"
Murmushi Mama tayi ta gane wa Ummin take nufi. A hankali hirar ta koma ta Awwab da
Radhiya.
"Kinci amanar soyayya da kika raba min su. Yaushe zata zo hutu ne in samu in hadasu
a gidana. Dama anan aka fara..."
"Dandalin soyayya zaki ce, tunda ga babbar shaida na gani"
"Ya son ranki hajiyata, ai ko sati baiyi ba da fara motsa jikinsa aka..."
Duka Ummi ta kai mata a cinya saboda Ibrahim da ya taso da sauri yayo gaba. Zainab
ba dai barin zance ba. Tun zamansu na baya haka take ta fadi magana ta barsu da
kunya musamman Ummi. Shi kuwa ashe Emzee ya hango a cikin masu wani irin style din
marching abin gwanin sha'awa da burgewa suna wasa da takubba amma na katako anyi
musu fentin tutar Nigeria. Abin ya kayatar kuma Emzee shine yake jagorantar wasan
nasu. Shi yake bada command sauran suna yin yadda yace. Karshen abinda suka yi
shine hada kalar tutar Nigeria wato green white green. Jeruwa suka yi layi biyar
kowannen layi mutum bakwai. Ukun da suke tsakiya a kowanne duka hulunansu farare
sauran biyun na gefen hagu da dama nasu koraye. Sai suka durkusa a kan gwiwa daidai
a haka aka fi ganin ma'anar abinda suka yi. Wurin ya kaure da tafi ga irin kidan
band din sojiji ana yi musu suka tashi suna wani murda takobin hannuwansu a kan
layi suna shirin barin wurin Ibrahim ya daddage yace "MUHAMMAD ZAYYAN TURETAAAAAA"
Mama ta kai masa dundu a baya kuwa "sai kasa yayi mistake ko"
"To nayi shiru"
"Ka daukarwa Radhiya a waya ko kuwa naka idanun kadai ka bawa abinci?"
"Na dauka fa Mama"
Kararar kade kaden baisa mutane sunji kiran da ya yiwa Emzee ba amma tabbas idan ba
karya kunnuwansa suka ji ba His Excellency yaji kalmar Tureta kamar a iska. Bai
sani ba ko yawan tunanin Zayyan da ya fado masa a wurin nan tunda yake ta ganin
sojoji ne ya sa shi jin haka. An kira shi domin yin jawabi ya fara da taya daliban
da suka gama murna kafin ya nusasshesu kalubalen da yake gabansu. Muryarsa ta
karade ko ina saboda spikun da aka saka a wurin gashi harka da masu sanin doka da
oda babu hargagi ko hayaniyar da zata hanaka jin me yake cewa. Cikin harshen
turanci yake jawabinsa.
"Akwai kanina, abokina kuma saviour dina wanda ba don shi ba da bazan kasance tare
daku ba yau. Wannan mutumi ban taba gani ko jin labarin mutumin da aka haife shi
domin ya zama soja ba sai shi. Officer ne wanda ya san ma'anar sadaukarwa kuma ita
ce nake baku shawara da ku runguma hannu bibbiyu. Kunga kowa a cikinmu akwai inda
arzikinsa da abincinsa yake. Kamar yadda kanin nawa yake cewa sojoji ba yinsu akeyi
ba...haifarsu ake domin domin su bada kariya. Saboda haka duk wanda yake tsaye a
cikinku yanzu ina so ya sawa ransa cewa babu kudin da za'a biyaka ya maye gurbin
iyalinka da zaka yi nesa dasu idan bukatar hakan ta taso. Babu wata karramawa da
za'ayi muku ta fanshe hatsarurruka da zaku iya haduwa dasu domin kare rayukan
al'umma. Ku din zababbu ne ku yarda da haka, kuyi aiki da haka ku tsira da mutumci
da kimarku a ko ina cikin duniyar nan. KU RIKE KU SANI CEWA SOJA SHINE JARUMIN DA
IDAN YA GA AN KAWOWA KASARSA HARI SAI YA DAUKI KOWACCE MACE A MATSAYIN MATARSA ,
'YARSA KO