Showing 261001 words to 264000 words out of 295847 words
amaren
nasa yace kowacce ta zauna a daki. Gefe ga Innawuro da Nene Marka sai Ta Madina.
Mairama da Mama Zainab suna daki. Can daya barin kuma Alh Indararo ne da Baffan
Rahima.
Kusan tafiyar yaji Zayyan yayi da Salame tana labe a bayan kofa ta kasa karasa
shiga tsakar gidan. Takun da taji daga bayanta da hadadden kamshi mai tafiya da
hankalin duk wanda ya shaka su ne suka sa ta farga ta juya baya. Ai tana hada idanu
dashi kallon da yayi mata sai ji tayi fitsarin da take makalewa yana diga. Zayyan
kuma ya dauke kai kamar bai ganta ba ya taho fuuu shine ta shiga kamar wadda aka
koro.
Babu wanda cikinsa bai yamutsa ba da Zayyan ya shigo duk da cewar da yawansu sun
sanshi amma babu wanda yayi masa wannan sanin ta fuskar sojoji. Escort dinsa na
bayansa sauran suna waje ya nufi gaban Malamijo. Mal Ali Gidado sai ji yayi hantar
cikinsa na kadawa kamar ba surikinsa bane. Yanzu yaron nan idan allurar sojansa ta
tashi ya manta da matsayinsa a gareshi yace zai hada dashi a kulle ai ya shiga uku.
Wani tunani ne ya darsu a zuciyarsa ya kara tsorata wato tunanin ko Mairama ta fada
masa yadda baya ciyar da ita da yaranta sosai lokacin da ta dawo gidan. Dan sakin
fuska yayi ya gaishe shi sannan yace ina Innar Salame.
Ta Madina jiki na rawa taja jiki ta fara yin hanyar kofa za ta gudu Hajjo tace "ga
ta can a bayanka...Ta Madina ana magana"
Idanunta su ka soma kadawa ta dafe kirji "banda abinki Hajjo idan da kara ai
Yadikko zaki nuna matsayin Innarta. Ni dai haihuwar Salame kawai nayi amma komai
nata da tarbiyarta a hannun Yadikko suke. Yau ko wani abu tayi ba daidai ba
tarbiyar Yadikko ce da Malamijo"
Yadikko ta zaro idanu ganin kowa ita yake kallo "daga abin arziki kuma sai kice
nice na haifeta. Irin wannan tunda ya nemi ainihin mahaifiyar nasan cewa akwai
dalili."
Shi dai Malamijo gumi ne ya cika masa tafin hannu ya kalli Salame ta firirice
gabadayanta a ta manne da bango.
Zayyan ya sake daure fuska yana kallonta sannan yace "Malamijo ina son ganinka da
mahaifiyarta muyi magana"
Kan kace kwabo su Hajjo da sauran kowa ya bace sun shige dakunansu. Alh Indararo ma
da Baffan Rahima cewa suka yi zasu jira a soro su ka tafi. Ta Madina ba don taso ba
aka bude musu wani dan daki suka shiga ita da Malamijo. Zayyan zai bi bayansu ya
kalli Salame ya daka mata wata razananniyar tsawa da ta kadawa hatta Mairama da ke
daki ciki "zaki zo ki shige ko sai...."
Bai rufe baki ba ta shige dakin itama ta sami jikin bango ta kuma rabewa sannan
Zayyan ya shigo ya zauna.
"Salame" taji ya ambaci sunanta da wata irin kakkaurar murya. Jinin jikinta ya sake
tsinkewa bakinta kamar ansa kwado ta kasa budewa ta amsa.
Ta Madina kuwa ta kai mata duka "ke dallah bude baki ki amsa kina ji ana kiranki"
"Barta dai so take ta nunawa sojoji iyakarsu" cewar Malamijo a hasale.
Kai ta dago a hankali su ka hada ido da Zayyan sai ji tayi har abada bata fatan
sake kallon wadannan idanuwan masu tsorata mutane su kada masa zuciya da hanta.
Sunkuyar da kanta tayi tana kallon kasa.
Gyara zamansa yayi ya dan rankwafo kansa "naji labarin duka abubuwan da kika yi tun
daga tafiyata zuwa jiya da yamma."
Gumi take yi sosai tsoro iyaka tana ji kuma tayi imanin idan sun nemi tafiya da ita
babu mai hanasu. Yadda ake bada labarin rashin imanin sojoji itama yanzu haka zasu
je su rinka azabtar da ita? Muryar Zayyan ce ta katse mata tunani.
"A jiya da aka fada min abubuwan da kika yi babu abinda yazo raina sama da son
kulleki a dena jin duriyarki har abada...." kallonta yayi na abinda baifi sakan
goma ba ya kula hankalinta yana gareshi kamar yadda yake so "...sai dai kinci
darajar haihuwa Salame. 'Ya'yanki daidai har bakwai idan na rufeki ko kadan banyi
musu adalci ba musamman kananan. Yanzu ina so a gaban mahaifanki ki fada min me
Mairama tayi miki wanda ya janyo faruwar wadannan abubuwa"
Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta ya daga murya "ba dake nake ba?"
Zabura tayi ta sake yin baya "uhmm, uhmmm"
"Kin zama bebeya ne ko me?" Ya sake yi mata tsawa.
"Uhmmm babu komai" tace da kyar iyayenta suna kallonta cike da haushi.
"To ni bari na fada miki me ya hadaku. Shekaru ashirin da hudu da suka wuce nazo
gidan nan tadi wurin kanwarki kika kawo min wasikar tayin soyayya, anyi haka ko
ba'ayi ba?"
"Anyi" tace da sauri.
"A lokacin na amsa miki ko nayi wani abu da zai nuna miki cewa ni Zayyan ina da
fuska biyu ta ha'inci in nemi kanwa in nemi yayarta?"
Girgiza kai ta soma yi a hankali tana tuna yadda ya yayyaga wasikar ya watsar.
"Salame nasan cewa soyayya babu ruwanta da dacewa ko akasin haka. Amma ance wai ana
barin halal ko don kunya. Kanwarki wadda bata da zance sai naki kuma kema a yadda
na fahimta wancan lokacin kina sonta ita ce kike son manemin aurenta. A tunani na
ke mai iya hakuri ce ki bar mata ko da ina sonki balle tun farko ita na nema. A
matsayinki na musulma tun lokacin ya kamata ki karbi kaddara ki rungumi kyautar da
Allah Yayi miki ta Salisu. Ko kinsan cewa Zainab matar Hadir nine na fara nemanta?
Ni na nemi kwatancen gidansu duk da ba wata muguwar soyayya naji ta kamani a
lokacin haduwarmu ba amma kinsan indai saurayi ya nemi gidansu budurwa ko yaya ya
ga abinda yake so ne. Amma abin mamaki ranar da Hadir yaje gidansu da zummar fada
mata ni bazan samu damar cika alkawarin zuwa ba su ka kamu da son juna. Tun daga
wannan ranar har rana irin ta yau ban taba sake yiwa Zainab kallon da ya wuce
kanwata matar dan uwana ba."
Malamijo da Ta Madina sai jinjina kai suke yi yayin da Salame tayi shiru kawai tana
sauraron maganganunsa.
"Ko da kina sona to ba da zuciya daya bane hasali ma nafi danganta abinda kika yi
da hassadar kanwarki. Kun rayu kece 'yar gata saboda kina samun kulawar mahaifiya
ita kuma babu uwa babu dangin uwa. A kullum Mairama ce a kasanki ki bata saura tayi
miki godiya. Lokaci daya kinga abinda kike so shi kuma ya karkata gareta shikenan
kika juya waccan soyayya da kike yi mata zuwa kiyayyar da hassada ta zama
musabbabinta. Kin manta cewa kowane bawa da irin rayuwar da Allah Ya tsara masa.
Wallahi Salame tunda kika ga baki aureni ba ki sani cewa bazaki taba iya rayuwar da
Mairama tayi ba. Duka duka ba don rabon haihuwa ba zaman har na wata nawa muka yi a
karkashin inuwa guda? Mun rabu da kuruciya batare da mun mori komai a
zamantakewarmu ba mun sake haduwa farin gashi na wahala da zuwan shekaru ya zo
gareni. Matata da na bari da kuruciya na dawo ta koma babbar mace. Kinsan yadda
muke ji kasancewar shekarun da ya kamata mu zauna mu fuskanci juna sun kare bama
tare. Duka duka Salame shekara nawa kuma ya rage mana da zamu sake maimaitawa a
doron kasa? Na tafi na bar yarinya ko tafiya bata yi na dawo watanni kadan ga
aurenta. Cikin da bansan meye a ciki ba na dawo na sami katon saurayi yana shirin
zama soja. Salame zaki iya wannan rayuwar da Mairama tayi cikin kunci, kewa da
makanta ga marayu a gabanta???"
Damm taji zuciyarta ta buga sai ga hawaye daga sama yana sintiri akan kumatunta.
Ta Madina ma kuka take yi Malamijo ya sake jin kunyar abinda yayi a baya. Kuncin da
ya baro a baya ne ya tuna shi ma Zayyan din yasa yatsansa ya kore hawayen da ya
taru a gefen idanunsa.
"Labari yazo Zayyan ya mutu amma kika cigaba da nunawa Mairama kiyayya wadda har ta
kaiki ga makanta ta. Abinda nake so ki gane Salame shine ba Mairama kika tsana ba
kuma kiyayyarki ba gareta bane. KIYAYYAR SALAME GA SALAME TAKE. Rayuwarki ce
gabadaya bata yi miki ba saboda kin ginata tun farko da hassada da bakinciki
shiyasa komai baya burgeki sai abinda wani ya samu. Wanin ma wadda kika dauka
kishiyarki baki son ta fiki da komai. Da ace kin kasance mai godiya ga Allah da
karbar kaddara ina me tabbatar miki sai kin kwance zani kin baiwa Mairama kwance.
Dubi irin dimbin arzikin tsohon mijinki yanzu. Ni fa banda kaddara babu wanda yayi
tsammanin dawowata harda ni kaina. Dama kece babba a gidan nan amma da kin karbi
rayuwarki ta farko da duk gidannan sai sunci arzikinki. Kin sake aure kin dauki
karan tsana kin dorawa Rahima saboda ba auren bane a gabanki lokacin. Burinki ace
kin yiwa Mairama zarra kuna zawarci ke kin rigata samun mijin aure saboda kin fita
da komai. Nasan akwai kaddara da rabon haihuwa a kanki amma duk da haka yadda kike
tafiyar da rayuwarki shine ya munanaki a gaban 'yan uwanki."
Mayar da hankalinsa yayi ga Malamijo da Ta Madina "ga iyayenki nan kowa cikinsu
fushi yake da ke. Duk wanda kika raba kin zalince shi musamman 'ya'yanki kin bar
musu abin fada wanda nake fata zancen ya mutu a gidan nan. Ki gyara rayuwarki
wannan shawara nake baki idan kuma kinki ji to na tabbata jikinki yana kaikayi ne
na son a taba lafiyarsa mu kuma zamu taba"
Shiru dakin yayi na wanu dan lokaci kafin Malamijo yayi gyaran murya ya soma magana
"Zayyanu nasan Salame tayi ba daidai ba amma ina tuhumar kaina da zama silar komai.
'Ya'yana ban basu damar girma da iyayensu mata ba bare su samu ingantacciyar
tarbiya. Babu wanda nasan damuwarsa a cikinsu hankalina yana kan dabbobina da yawan
aure aure. Gashi an wayi gari ana ta sako min 'ya'yan bayan dogon jinkirin da suke
samu kafin manema su fito. Nima ban rike Mairama da 'ya'yanta rikon da ya dace uba
ya yiwa 'yarsa da take cikin halin bakincikin mutuwar miji ba ta yaya 'yar uwarta
da ta bari shaidan yayi galaba a kanta zata yi. Ka yafe min do Allah do Annabi"
Kunya ce ta kama Zayyan yace masa dama daga shi har Mairama basu rike shi a rai ba.
"Ke kuma mutuniyar banza tashi zakiyi ki roki kowa gafara musamman Mairama da
Rahima da kika rinka zalinta" cewar Ta Madina.
A sanyaye Salame ta fara cewa su iyayenta su yafe mata zuciyarta tana ta harbawa ta
ma kasa gane wane hali take ciki. Bayan sun ce sun yafe ta koma ga Zayyan shi kuwa
kofa ya nuna mata "kije ki sasanta da kanwarki sannan yanzu zan tura su Rahima su
dawo ki daidaita tsakaninki dasu. Wannan magana bana so su sani kwatakwata burina
kawai ki rungumi 'ya'yanki ki basu tarbiya mai kyau musamman wannan yarinyar da
kika zo min gida da ita sai kin tashi tsaye." Yace yana tuna irin rashin kunyar da
yaji Khadi tana yiwa Rahima watarana a Abuja.
Mikewa yayi zai fita ya dan dawo sai da gabanta ya doka "yauwa zanyi magana da shi
baban Rahima yanzu sai dai ina son yi a gabanki so ki biyoni don ina sauri ne"
"To" tace da azama tana bin bayansa.
Suna zuwa soron su ka same su zaune akan tudun nan kowanne cikinsu ya mike da
sauri. Zayyan hannu ya mika musu suka yi musabaha sannan ya kalli Baffan Rahima
saboda kamanni da suka nuna shine baban nata.
"Ni sunana Zayyan" yace dashi.
"Idris nake" Baffan Rahima yayi masa murmushi.
"Ni kuma Alhaji Indararo aka fi sanina dashi" cewar maigirma miji na Salame.
"Mal Idris alfarma nake nemarwa kaima da iyalina Mairama"
"Haba Yallabai ni kuwa har wace irin alfarma kake tunanin zan iya yi maka?"
Zayyan ya kalli Salame sannan ya kuma kallonsa "Rahima nake so ka bamu idan babu
takura. Dan zaman da mukayi da ita ta shiga ran kowa a gidan musamman ita Umminsu.
Don Allah ka bamu ita kafin nan da Allah Ya kawo mata mijin aure ta sami soyayya da
gatan da ta rasa na mahaifiya"
Baffan Rahima bai san lokacin da murmushi mai hade da dariya suka kwace masa ba
"Yallabai Rahiman tawa ita ce kuke so?"
"Ta cancanci soyayyarmu kuma nayi maka alkawarin zamu riketa kamar 'yar cikinmu"
"To Yallabai za ku rinka kawota in ganta ko?" Yace a raunane harda 'yar kwallarsa.
"Wannan kuma dole ne" Zayyan yace yana dariya.
Mal.Idris ya kamo hannunsa "na baka Rahima amana Yallabai duk da nasan bata baki
nake yi ba sai na fada ba. Nagode nagode sosai"
Juyawa Zayyan yayi ya tambayi Salame "kina da abin fada game da hakan?"
Kada kai tayi a sanyaye. Alh Indararo ya murmusa "sannu da kokari Yallabai nima ina
da yaran wallahi biyar ta haifa min duka mata. Bari na garzaya gidan na turo maka
su sai ka zaba"
Dariya Zayyan ya danne a ransa kuwa yana tunanin ko ganinsa bazasuyi ba. Su ai
'ya'yan so ne basu da matsala. Ra hima kuwa ya fuskanci abinda Mairama keso kenan
amma ta kasa fada masa saboda gudun kada yaki amincewa saboda halin Salame.
"Kina iya tafiya ki turo min matata idan kin shiga" Zayyan yace da Salame.
Ciki ta koma jiki a sanyaye yawancin kowa ya fito sun cigaba da harkokinsu murya
na rawa tace wane daki Mairama take. Da hannu Nene Marka ta nuna mata.
"Dama kiranta yake yi maigidan"
"To ni zanje in fada mata?" Cewar Nene.
"A'a" tace da sauri sannan ta shiga dakin yau harda sallama.
Mama ce ta amsa mata a fili Mairama kuwa a zuci ta amsa ta kawar da kanta gefe.
"Ana kira"
"Wa ake kira?" Mama ta tambayeta.
"Ita" Salame ta amsa tana nuna inda Mairama ta juya mata baya. Murmushi tayi duk da
bata ganin fuskarta amma muryar Salamen tayi laushi a zuci tace kadan ma kika gani.
Dama tayi kwalliyarta tayi kyau ta yafa mayafi a kafada ta fita ko kallon inda
Addarta take bata yi ba.
Tana zuwa soron kamshin da yanzu mijin nata yafi amfani dashi ya doki hancinta ya
mika mata hannu sai da ta waiga baya ta kuma kalli kofa ta girgiza kai.
"Za'a iya shigowa fa"
"Fillo rowa zaki min?"
Murmushi tayi ta taho gareshi ya rungumeta tsam yana jin wata nutsuwa tana ratsa
shi. A kunnenta ya ce "Fillo ashe an sami karuwa? Allah Ya raya mana"
Gabanta ne yace das tsabar tsoro ta dago da sauri "rufa min asiri ni wallahi bani
da komai"
Dungure mata kai yayi "matsoraciya kawai....barkar samun Rahima nake miki"
"Rahima kuma Sojana?"
"Mun gama magana da babanta yanzu ta zama 'yar Zayyan da Fillo"
Mairama bata san lokacin da ta kankame shi tana murna ba. Godiya take ta zuba masa
cikin nutsuwa ya soma mayar da godiyar wani abu daban sai da taji kamar motsin ana
tahowa tayi saurin matsawa gefe yana yi mata dariya.
"Ni yau zan koma amma Abuja zan tafi please ku dawo waahegarin bikin nan bana son
zama babu ku a kusa. Sannan na kashe case dinnan ki bata dama ta gyara kuskurenta"
Dan jimm tayi kafin ta kada kai "shikenan, amma shine ka tsorata mutan gidannan da
dakarunka ko"
"Bukatata zata biya nasan in sha Allahu zata gyara. Da farko tafiya naso yi da ita
amma kinga amfanin shawara Major da Hadir suka kwabeni da hukunci cikin zafin rai.
Tabbas na yarda Salame mai laifi ce sosai wadda bata cancanci a raga mata ba ko
kadan. Amma ta bakin Major yace ku mata idan aka nemi a ci ku da wuta sai ku sake
botsarewa baku ki ayi kan mai uwa da wabi ba. Muna iya hukuntata ta dawo yadda ta
taba zuwa wurin boka yanzu ma ta sake iyaka dai a sake kamata wadda bazata damu ba
indai bukatarta zata biya. Ina ganin mu bata wannan damar idan ta sake baudewa kuma
to zan hadata da masu ladabtar da ita in and out"
Kwalla fal idon Mairama tace "nagode Sojana Allah Ya saka da alkhairi. Amma zaka
jira yaran su dawo ko...idan ka tafi wannan yarinyar damuna zata yi ta hanani
sukuni. Mutum ya girma sai sabuwar sangarta ke shigarta"
Murmushi Zayyan yayi "dole na jira. Ya batun abincin mutanen nan?"
Mairama tace masa an kusa saukewa. Waya ya dauko ya kira Emzee da suke tare da
Awwab da yace su jira ko a gonar Malamijo ne sai ya kirasu. Mairama ce ta karba ta
fada masa inda su Radhiya suke tace su daukosu su dawo gidan.
Zamanta tayi suna ta hira da Zayyan a ciki kuma Salame ta shige tsohon dakinsu da
Mairama zuciyarta sai zafi take ta rasa inda za ta saka ranta taji dadi. Duka fadin
gidannan kowa baya sonta tayi bakinjinin da ita da kanta ta rakitowa kanta.
***********
Mota bata karasawa kofar gidan saboda haka daga can nesa kadan Emzee yace Awwab
yayi parking ya karasa a kafa. Ya shiga suna gaisa da mutane Radhiya da Rahima a
tare suka ji muryarsa. Radhiya ce ta fara fitowa daga dakin da suke da sauri Emzee
yayi kamo hannunta a dan birkice saboda fuskarta da ya gani tayi ja.
"Adda ina da ina ne yake miki ciwo? Kun koma asibitin? Sun baki magani?"
Murmushi tayi "kai Emzee irin wannan tambayoyi"
"Da kyar na wayi gari inata tunanin ko yaya kika kwana. Zo mu tafi tare muke da
Hamma" yace yana kallon Rahima dake tsaye a bayanta ta janyo hijabinta ya rufe mata
fuska.
Mamaki ya kama Radhiya duk da tasan cewa dama zai damu saboda rashin wayarsu jiya.
Yau kuma tun safe take gwada tasa wayar a kashe ashe yana sane. Murmushi tayi
dimple dinta ya shige ciki sosai ta kamo hannun Rahima tana ce masa itama fa akwai
ciwon a jikinta.
Tabe baki yayi "Allah Sarki"
Wata irin fargaba taji a take ta dago kai ta kalle shi sai ta ga yayi gaba abinsa
yana yiwa mutan gidan sallama kamar bai san da zamanta a wurin ba. Idanunta suka
cicciko da kwala tana mamakin wannan abu. Yaki daukar wayarta tun jiya yau kuma ya
ganta ya share. To ko dai yana fushi ne saboda Ummansu ta daki yayarsa ta tambayi
kanta. Babu mai jinta bare ya bata amsa haka ta fito a sabule ta bi bayansu.
Tun kafin ta karaso wurin motar Awwab ya fito ya dora hannu a jikin kofar bangaren
da yake yana kallon yadda Radhiya take tafiya tana dan cije lebenta na kasa. Gashi
wurin da mutane dole ya daure ta karaso.
Gaba Emzee ya tafi zai shiga Awwab ya hade fuska cikin wasa yace "haba inlaw koma
baya ka barni naji ya kwanan iyali"
Murmushi Emzee yayi Radhiya na dariya idanunsu suna cikin na juna Rahima tayi
murmushi ta shiga baya. Ga tsananin mamakinta wata muguwar harara Emzee ya doka
mata yana ganin kawai da gangan tazo masa shiyasa taki fada masa wace babarta.
"Hamma bari kawai zamu taho a kasa ga Halifa can na hango ya fito"
"Wasa nake fa shigo mu tafi kada mu bar Daada da jiranmu"
Ai baya jin yana kaunar zama inuwa daya da Rahima. Ayatul kursiyyu ya shiga
karantawa yana son idan ma wani abu aka yi masa Allah Ya bashi lafiya. Ko da yaji,
wannan soyayya da yake mata daga haduwarsu a ranar ko baccin kirki bai iya yi ba
sai aikin tunaninta.
"Ina biye daku dama