Showing 189001 words to 192000 words out of 295847 words
amarya ta tare Mairama taje kafin
ta wuce Abuja. Yadikko sai ta kasa fada mata an saki Hajjo tunda tasan sun shaku
daga baya. Kuma ma dai tana gudun ta fada ta hanata nata niyar barin gidan. Ita
dinma ba zama take ba tana ta zagayen dangi amma bata leka Salame ba a niyarta sai
ta dawo.
Washegarin tafiyarta amarya ta tare. Malamijo ana ta zumudi yayi aski an gyara ko
ina. Da kullin kazarsa ya shiga dakin amarya da zummar kiranta zuwa turakarsa sai
ya samu bata ciki sai wasu yara dugwi dugwi da yabi ya lissafa su shida cif kwance
wasu akan gadon da shi ya biya aka yi mata kayan daki. Wasu kuma an yi musu
shimfida a kasa. Juyawa yayi zai fita nemanta yaci karo da wani yaro dan kimanin
shekaru sha uku. Bangaje Malamijo yayi ya haye kan doguwar kujerar dakin da babu
kowa a kai ya kwanta.
Abin ya daure masa kai ya tafi dakinsa zai ajiye ledar da hannunsa ya fita neman
ba'asi sai ya sami Hajiyayye zaune akan katifarsa da ya sauya saboda zuwan amarya
ya saka maigida kar ka taka.
"Sannu da zuwa Angona" tace tana make murya.
"Sannunmu dai" ya daure ya amsa kafin kuma ya soma fada "su waye a dakinki?"
"Dakina kuma? Mtsw anya da mutane a dakin kuwa? Ni dai da zan fito ban bar kowa ba
sai yaran namu"
Idanu ya zaro "yaranku ke da wa? Sun kai goma fa inajin"
"Bakwai ne ba yawa. Biyu ne kawai babansu daya. Sauran..."
"Kowa da nasa?" Ya tambaya hankali a tashe.
Murmushi tayi masa tana tasowa gabansa tana rangwada jiki na juyawa.
"Daren yau namu ne ni da kai ka bar batun yara zamuyi maganarsu gobe"
Ledar ta karba ta bude kamshi ya doki hancinta. Kaji ne uku dakwale sun gasu an
yanka musu albasa, kabeji da tumatir. Yawunta ya tsinke bata ankara ba ya tsiyayo
ta gefen baki akan idanun Malamijo. Haka ya tsaya kamar gunki ta kamo hannunsa ta
zaunar dashi jiki na bari zata ci nama. Biyu ta raba naman ta kwashe daya a wata
ledar ta ture gefe.
"Wannan yara sa samu su lamusa da safe. Idan ban basu ba gobe bani da zaman lafiya"
Tashi yayi kawai yana tunanin ko bulala zai samo ya tafka mata. Don yana sonta sai
a ha'ince shi. Ance sakin wawa baifi a ce tana da yara biyu ba. Kuma don jaraba sai
a kawosu su tare a gidan tare. Hannunta da tayi rabon naman tabi ta lashe tas yana
neman abin duka bata sani ba ta tashi itama.
"Cin nama irin wannan yafi dadi idan mutum ya rage kayan jikinsa yadda ana gamawa
sai a fadawa angwanci ko Malamijo nawa na kaina" ta shiga kifta masa idanu.
"Zaki ci kwal ubanki ne" yace a zuci ya kama kofar dakin ya fita.
Wurin ajiyar itace yaje ya sami wata sanda ya dauko wata sanda ya dawo ya jingine
ta a kofar dakin ya kutsa ciki sai ya hadu da wata dattijuwa a zaune da daurin
kirji ta saka ledar naman a tsakanin kafafunta tana ta tauna kashi.
"Ke kuma daga ina" yace yana huci.
"Maigida lafiyarka kuwa?"
Murya dai ta Hajiyayye ce amma wannan ai tafi kama da dattijuwa. Sosai ya shiga
kallonta yau babu foundation fuskar ta nuna da kyau. Da gani a kalla tayi arba'in
da biyar ko ma fin haka. Kayanta da jibge a kasa ya kalla ya kuma kallonta.
"Ke tashi tsaye" ta kuwa mike tana sunne kai wai ita kunya.
"Ya na ganki a bushe kamar ni? Ina abubuwan jikin naki?"
"Au" ta juya ido "kayan da nake ciko dasu kake nufi? Gasu can. Wai naga bacci
zamuyi ne nace bari na cire nasha iska"
"Wai tsaya, kece dai Hajiyayye da muka yi magana yanzun nan kika ce min yaranki
bakwai?
"Kai dai ka damu da son sanin yaran nan naka. To zauna muna ci ina fada maka. Su
goma sha daya ne amma biyu babansu daya nace ma ko..."
"In kin isa Allah shi tsinan. Kin kuwa san ko ni wanene da zaki cuceni haka?
Kalleki fa babu body babu alamar body sai tumulin 'ya'ya. To ki tashi tun muna
shaida juna kije ki tashesu ku bar min gidana"
Bata nuna masa ranta ya baci ba tana cin naman da ya soma kasa tace "ka dai yi
hakuri mu wayi gari sai su koma gidanmu. Idan na tashesu cikin dare yanzun da
wahala suke boye maitarsu. Idan naman kazar bai ishesu ba sai ka ga cikin mutanen
gidan nan ana ciwo ya kama wane. Kaga bazan so ba"
Baki na rawa duka makaman yakin nasa suka bace yace "kina nufin wai...wai...wai ku
din...kina dai nufin"
"Mayu ba. Nayi zaton ma Kawuna ya fada maka tun lokacin da ka tura wakilanka. Kada
ka damu indai zasu ci nama su koshi wallahi babu mai sani a gidan nan. Idan ba haka
ba....toh...don shi babban da na taho dashi ma cewa yake wai ya ga cinyoyinka
kamar..."
A tsorace ya rike cinyoyin nasa ita kuwa ta ci naman nan duka ta cinye. Tun daga
ranar kwanaki shida kenan kullum babban danta wanda ba ma a gidan yake ba zai je
gonar Mamamijo ya debo kaji ko zabi kamar biyar su gyare shi da 'yan uwansa a
tsakar gidan ayi dabge a ci sauran na gani. Malamijo bala'in tsoronsu yake ji ya
kuma kasa fadawa kowa dom yanzu tsorata shi take yi har cikin dare duk da karyar
maita tayi. Ya kara ramewa ya tsotse babu mamora a jikin. Hajiyayye banda nama sai
tatike shi take da karyar maita yana bata kudi. Su Yadikko nasu ido ne babu mai
cewa komai an barshi da sababbin iyalinsa.
**********
Kwana biyu da dawowar Zayyan sun buga soyayya shi da Mairama ko farkon aurensu
albarka. Gaishe su kawai yaran ke zuwa yi babu mai zama a bangaren. Su Radhiya ma
basa kwana sun koma tsakanin gidan Mama da Mami. A haka ance musu wai su barshi ne
ya huta. Yau suke sa ran kiran 'yan uwa a waya a sanar dasu idan ya dawo daga
headquarter. Zasu karasa hada duk abinda ya dace ne domin ya zamana komai anyi shi
officially.
Awwab yaji sauki kuma nan da kwana biyu yake son komawa ya karasa abinda zaiyi ya
dawo kafin hutun ya kare a aura masa Alheran. Raji da Zahra su ma zasu tafi Osun
wurin dangin iyayensa. Daga can su je Katsina sannan su koma Germany.
Arifah da mamanta sunzo jiya yau kuma tace akwai fa zuwansu park ita bata hakura ba
su shirya zata zo su tafi. A gidan kuwa tayi laasar washegari suna yin sallah suka
shirya zasu tafi. Awwab ya dauki Raji a gaban mota sai ,Zayyana da Radhiya a baya.
Ibrahim da Emzee a motar Mama sai su Fauziyya a motar Arifah. Wani sabon park ta
kaisu na dan wane da wane. Ba tsada bace da shigarsa sai dai masu zuwa da irin
abubuwan da ake saidawa kaji pure water guda daya naira ashirin ya sa ba kowa ke
iya zuwa ba. Hakan ya kare shi daga zama matattarar 'yan kwaya kowa ka gani yana
kokarin nuna shi din ya isa.
Wurin ya kawatu da flawoyi kwantacciyar ciyawa da mutum zai iya zama a kai ko babu
shimfidar komai. Ga wani abu kamar korama ruwa yana wucewa da gudu. Akwai manyan
bishiyu masu kara masa ni'ima da daddadar inuwa.
Suna fitowa Emzee da Ibrahim ne suka dauko carpets da za'a shimfida. Raji ya dauko
cooler din da aka zuba robobin ruwa da gwangwanayen lemuka cikin kankara. Zayyana
da Radhiya kwandunan abinci shi kuma Awwab ya nufi wurin masu gasa nama Arifah ta
biyo shi.
"Captain yaushe ne komawar taka?"
"Jibi. Akwai sako ne?"
"Not really.."tace tana dan murmushi. Mayar mata yayi yana jinjina kai.
"Akwai wata a kasa kenan. Haba kanwata kada ki boye min komai"
Radhiya ya gani ta nufosu fuskarta babu walwala. Dama tun a gida ya kula kamar ma
bata son fitowar. Shi kuma dama ce yake gani saboda baya samun chance din zama da
ita suyi hira. Idan ba'a kirata ba to tana wani aiki. Tayi kyau sosai cikin
pakistan da ta saka. Rigar baka da aikin zare pink sai pink din wando mai fadi da
pink din mayafin da ta yafa.
"So cute" ya furta a hankali gabadaya hankalinsa ya koma gareta.
"Muna komawa gida zan bada shawarar ayi ayi bikin nan naku kafin a nemi 'yar mutane
a rasa" Arifah tace tana dariya.
"Da kin kyauta. Yanzu dai zaki fada min me kike son fada ko we talk some other
time? Schatzi akwai kishi yanzu haka sai nayi lallashi"
"Ahhh to bari na gudu kada ta hanani yayanta"
Wurin wasu kujeru da aka baza a karkashin bishiyon Radhiya ta koma ta zauna takaici
ya isheta da kishi.
Awwab na jin me Arifah tace ya gama karbae ledojin naman yace "wanne? Emzee fa
kaninta ne"
A kunyace tace "ba shi ba...how much do you know about Yousuf? Yana kirana kuma dai
nima I like him"
Da farinciki yace "in sha Allahu baki da matsala kanwata. Maybe maganarki yace yana
son muyi"
Amma wannan hadi yayi masa sosai. Tare suka taho inda Radhiya take Arifah ta karbi
ledojin don bata da girman kai shi kuma ya zauna a kujerar dake kallonta.
"Schatzi, kishi?"
Tsuke baki tayi taki yi masa magana ya tashi yaje ya dauko musu maltina guda daya
ya dawo. Bai ce komai ba ya bude ya sha ya tura mata. Sai da ta dan murguda baki
wannan dimple din mai bashi sha'awa ya motsa ta dauka ta sha itama ta tura masa.
Haka suka yi har ta kare.
"Zaki kara?" Ta noke kafada. Haushin nata da biyu ne dama. Ga dariyar da yake yiwa
Arifah ga tafiyarsa jibi duk ya dagula mata lissafi. Tun bai tafi ba ta soma jin
kewarsa. Sati uku yace zaiyi mafi karanci ko yayi wata guda. Duka duka yaushe suka
daidaita yake tunanin sake tafiya ya barta.
Yatsa taji ya kada a kusa da fuskarta ta dago daga tunanin da take yi tana
kallonsa.
"Indai Arifah kike yiwa wannan fushin ki dena zancen Yousuf muke yi. It seems sun
daidaita"
Duk da tana kokarin boyewa ya kula da dadin da hakan yayi mata amma sai ta sake
dinke fuska.
"Me kuma nayi? Kinga tafiya ce a gabana bana son wannan fushin"
Kwallah ya gani ta ciko idon ya sosa mata inda yake kaikaiyi.
"Ya Allah" yace ya soma damuwa "Alheran ba kya son na tafi ne?"
Kifa kanta tayi akan teburin gabanta bayan tace eh.
"Kada ki bari hawayen nan ya fito"
"Me yasa?"
"Zaki sani rarrashin da bai kamata nayi ba with a hug and maybe a..."
Dagowa tayi da sauri "na dena don Allah. Sai ta ga yana kallon fuskarta shine ta
taba idonta taji danshi "kadan ne ya digo Hammana kuma ba ni na fito dashi ba"
Tasowa yayi daga wurin zamansa yana zagayawa gabanta a hankali "ya na iya tunda ya
fito sai na rarrashe ki....come here"
Ba shiri ta mike itama tana ja da bayan "Allah na dena fa...ka tsaya a inda kake"
Bai dakata ba ya cigaba da matsowa "ga wani nan ma yana zuba. Schatzi tana bukatar
rarrashi irin wanda ni kadai zanyi mata ko"
Ga kunya tana ji ga zancen yayi mata girma sauri ta kara ta na neman ina sauran
suke "ba hawaye bane ruwa ne"
Idanunsa har wani ciki suka yi yace "kin fara karya ne? Ina kika ga ruwan?"
"Uhmn, uhmm yawu ne kaga" ta tabo idon ta nuna masa.
Cak ya tsaya ya kwabe fuska "ashe baki dena kazanta ba"
Dariya ta koma yi "zaka taka danyen..."
"Stop Alheran, bana son kazantar nan taki"
Ta kuwa cukule tana jindadin yadda ta dawo ita yake gudu "kalli mana ka gani
danyen...."
"Schatzi!"
"Oui ma Chérie" ta amsa innocently kamar bata san me take yi masa ba.
"Ko ki bari...."
"Ko kayi me?"
"Kada ki kureni ki ga me zanyi din fa" ya gargadeta da hannu yana dawowa kusa da
ita suka soma jerawa suna gangarawa hanyar inda sauran suke.
"To nayi shiru."
"Better. Call me that name again. Dama na gaji da Hamman nan. Su Zayyana su fada
kema ki fada babu bambanci"
"Chérie" tace da wata irin siga mai shiga zuci.
"Meaning?"
"Daidai da Schatzi amma french version"
Tsayawa yayi a gabanta ya hanata cigaba da tafiya "idan na dawo bana son ko sati
muyi ba'a daura aurenmu ba. So tun yanzu ina fada miki zan sanar da su Baba. Idan
kinso ana tambayarki ki sake cewa baki shirya ba"
Dariya ya bata tace masa ko gobe yake so ta shirya.
"Da kin raina kanki kuwa"
Nutsuwa tayi a ladabce tace "Me yasa? Dukana zaka yi?"
Sai da tasa shi dariya "Matsoraciya ina kika baro 'Yar Soja nasan da ita ce cewa
zata yi bismillah "
" 'Yar Sojan lafiya bayan ta kare min ina nan ina son dreba"
Yana juyowa suka hada ido ta gudu duk kiran da yake mata kunya ta hanata tsayawa.
Bata sake bari sun zauna su kadai ba saboda kunyarsa da ta rinka ji. Da ana daukar
hotuna kuwa fafur taki yarda ayi musu su biyu.
**********
Rama 'yar asali ba bogi ba Malamijo ya sake yi gabadaya ya sake karewa sai kasusuwa
sai kayi zaton mayun gidansa sun fara lasarsa ne. Gidan gonarsa yaje za'ayi
lissafin abincin dabbobin da kuma ware wadanda za'a kai Enugu karshen sati.
Yana zuwa babban yaronsa Talle ya soma cewa "Yallabai an fitar da shanun da ka turo
a dauka. Gaskiya kayi dabara da kace a rage wasu saboda nan din ya soma matsarsu
basa walawa sosai"
A take ya soma zufa duk da sanyin gari "wadanne shanu kenan?"
"Wanda ka turo dan wajen amaryarka mai zuwa daukan kaji ya dauka mana. An bashi
ashirin da uku yanzu saboda motocin sunyi kadan zai dawo a cike hamsin din"
Jiri ne kawai ya soma dibar Malamijo saboda tashin hankali jikinsa yana rawa yace
"ni ne zan turo a kwashe shanu? Da can a ina suke ban ce a raba ba sai yau?"
"Ba dai karya yayi min ba yaron nan? Kusan awa guda da tafiyarsa"
Kuka Mamamijo yasa bare da ya soma dubawa a gigice ya fahimci manya manyan bijiman
sa aka kwashe "da su taba shanun nan ba gara su lasheni ba ita da yaranta"
Talle dai lallashi yake yi Malamijo ya kama hanyar gida fakam fakam yana zubar da
hawaye kamar yaro. Daga tarewarta sunci kaji yafi hamsin. Sau biyu ana daukar
tumaki duk yayi shiru don tace masa magana na fita ko ita bata cinyeshi ba yaranta
zasu ci. Dakinta yaranta ne a ciki ita kuma ta tare a dakinsa sauran matan basu da
girki. Sai dai kowacce ta dora abinda ya samu suna kallo ana wadaka da nama kullum.
Babur ya tare ya hau don yayi saurin zuwa gida.
Yana zuwa gidan bata dakinsa ya tafi nata. A can yaji tana waya tana kyakyata
dariya "Talle baka da kyau. Kasan shawararka ta maita tayi sosai. Tsohon banza yana
son ransa da na kada idanu sai kaga yana tsuma. A sayar da shanun nan ko dubu
hamsin hamsin ne tunda kace manya ne kowa ya dau rabonsa"
Wani gululun bakinciki ne ya turnuke shi yadda Hajiyayye tayi masa wasa da hankali.
Yanzu yana fito da maganar nan magauta sai su sami abin dariya. Ta ina zai samu ya
gasa musu gyada a hannu kafin ya damkawa hukuma? Shawara daya ce tazo masa ga bacin
rai ya dauki waya ya kira Mairama.
A lokacin tana ta koyawa Zayyan yadda ake tura sako a waya yana ta mamakin fasaha
da kimiyar nasara sai ga wayar Malamijo. A ladabce ta amsa ga tsoron ko lafiya
saboda shi dai baya kira sai dai a kira shi. Ko gaisuwarta bai amsa ba ya soma
bambami.
"Yanzu Mairama kin kyauta min kenan? Yarinyar nan 'Yar soja ance tazo hutu amma ni
ban ganta ba har yau. Naka naka ne Mairama a rinka zumunci."
"Malamijo kayi hakuri dama satin nan zasu zo da Karami sai wani dalili ya gifta
amma suna tafe wallahi"
"To ni dai idan da hali su taho gobe ko jibi. Idan ma kudin mai ne babu zan biya.
Ina ta shelar akwai jikata a Faransa abokai sunki yarda. Shi kuwa Zayyanu kice ya
taho da kayan sojojinsa idan da bindiga ma ya dauko ko ta katako ce."
Jikinta ne ya bata ba lafiya "Malamijo me ya faru ne?"
Kamar ya fada mata amma zuciyarsa na zargin tana cikin masu murna. Duk wanda yaji
me ya same shi cewa zaiyi Allah Ya kara. Radhiya kuwa yasan ko zata yi dariya sai
ta rama masa su Hajiyayye bazasu tafi haka nan ba. Zayyanu karami kuma ai soja ne
dole ya tsaya masa ko baya so tunda hukuma dai anyita ne domin kare al'umma eheee.
Tana ajiye wayar ta kalli Zayyan da 'yar damuwa a fuskarta "ina jin fa an tabo min
uba, akwai abinda ke damun Malamijo"
Dagowa yayi daga kan cinyarta da yayi matashi "tun baki tabbatar ba kin soma hade
rai"
"Sai naji duk na matsu nima na ganni a Sumailan. Idan wasu ne suka taba shi ba
yarda zanyi ba, ina son tsohona"
"Mairama wai ni wa Alheran ta gado ne? Tawa ce ta fito fili amma kema fa ba jin
magana kike ba"
Dariya tayi sosai kafin suka yanke shawarar tafiya Sumaila jibi su ajiye yaran su
wuce Sakkwato. Daga can kuma suyi Nijar in sun dawo su tsaya a rugar Barkindo kafin
su dawo Abuja.
Zuwansa headquarter dazu an kare komai amma duba da cewa dole ya bukaci lokaci da
iyalinsa shiyasa aka bashi zuwa farkon sabuwar shekara wanda daya ga wata ake son
yin taron karrama shi. Idan an gama zaiyi wata uku yana daukar training da courses
domin ayi updating dinsa tunda Nigeriar da ya dawo ba ita ya bari ba a 1994.
Akan wannan shawarar suka tsaya bayan magariba lokacin su Radhiya sun dawo ya shiga
wurin Baba Hadir. Nan ya sami Awwab zaune a kasa a gabansa yana rokon shi dai yana
dawowa don Allah ayi aurensu da Radhiya kafin ta koma. Ya kara da cewa ya bada
cigiya jiya a cikin estate din block C akwai gida.
A dan littafinsa Baba Hadir ya rubuta masa cewa zai yi magana da ita da kuma su
Daddy.
"Ni dai Baba da ka kyaleta wallahi tsoronta nake kada a maimaita irin na da. Kawai
ka yanke hukunci shikenan"
"Kada ka bada maza mana Awwab ya haka kake tsoron matarka" cewar Zayyan yana
dariya.
Awwab sai ya tashi ya fice yana mai jin kunya. Hadir ne ya rinka masa bayani a
rubuce na abinda ya taba faruwa da kuma bukatar yaron har yanzu.
Sai da Zayyan ya gama karantawa tsaf sai ya bata rai "nifa na baro A B C D din a
Liberia kayi min bayani kawai."
"Zayyan" Hadir yace yana dariya.
"Kaga yara dai naku ne bani da ta cewa akan komai nasu nima dan gayya ne. Fatana
Allah Yasa wannan karon babu wata matsala da za'a samu daga Katsinan"
"Baka ji haushi ba?" Baba Hadir ya rubuta masa.
"Ko kadan dan uwa. Major Mustapha da iyalinsa sunfi karfin haka a wurinmu kaima ka
sani. Ya kula min da iyali sannan ya kula min da kai. Me zan nema kuma? Maganar
yara wannan mukaddari ne idan akwai rabo sai kaga anyi"
"Zayyan" Baba Hadir ya kira sunanshi kawai don jindadin halin abokin nasa.
Dan daure fuska Zayyan yayi "kada ka karar min da suna. Rinka hadawa