Showing 270001 words to 273000 words out of 295847 words
magance toshewar kumburin ya warke gabadaya. Ko idon zai yi lafiya da
wahala ta sake gani sosai dashi. Yatsunsa ya shiga nuna mata yana cewa ta fadi ko
nawa ne. Nan Rahima ta rikice inda bata tantance biyu da uku. Hawaye sosai ta soma
yi da likitan ya soma bayani. Duk yadda Emzee yake kokarin nesanta kansa da ita ba
karamin tausayinta bane hake bin ko ina a jikinsa. Wasu magungunan ya rubuta mata
sannan ya auna karfin idon yace zaiyi mata glass ne su dawo nan da kwana uku.
"Babu yadda za'ayi mu samu gobe da safe saboda tafiya zamuyi a goben" cewar Emzee.
"Zaku iya samu amma sai ka kara kudi. Kayi magana da cashier din idan ka fita"
Nan suka gama komai ya biya kudi cikin wanda Ummi ta bashi. Maimakon su tafi gida
wani babban shago ya wuce da ita ya sa salesgirl din tayata neman frame mai kyau.
Wani round ta zaba ya dace da fuskarta babu dai me yiwa kowa magana ya biya kudin
suka koma asibiti. A mota ya barta yace ya kai musu sannan suka tafi gida.
Zayyan na komawa gida ya sami Mairamansa a kwance Radhiya ta bata tea taki sha wai
bacci kawai take son yi ta rabu da ita.
"Jeki abinki Alheran ajiye min tea din" yace da ita.
Tana fita ya cire rigar khakinsa ya rage singlet da godon wando ya kwanta a kusa da
ita tare da janyota jikinsa.
"Fillo me yake damunki ne kwanakin nan na lura kamar baki da lafiya."
"Stress ne Sojana kuma kaima kasan dole ne tunda kun dauko mana abinda yafi
karfinmu."
Dariya yayi yana shafa kwantaccen gashin kanta da yake nadewa da kansa saboda
laushi. Dinner ce angwaye suka tsara abarsu Baban Arifah yazo ya chanja komai.
Abokansa 'yan siyasa da manyan mutane wasu ba zuwa Jos zasuyi ba shine suke ganin
kawai gara ayi wata a Abujan. Sai kuma bangaren sojoji da suke yiwa Zayyan kallon
wani celebrity suma kowa yana son zuwa bikin 'yarsa. Excellency yace bai ga amfanin
ayi taro gutsi-gutsi ba alhalin mutane daya ne zasu zo. Kuma dama bikin ya rabu
kashi kashi ayi ta tara gajiya da barnar kudi. Hakan da yayi ya kara masa kima a
idanun su Baba Hadir da Daddy domin ya nuna yasan zafin nema ba kamar yadda yake a
wurin 'yan siyasarmu ba ayi sati ana biki ana barin kudi. Shiyasa su Mama kullum
suna tafe ana ta shiri domin suyi taron da zai kayatar ya fitar da mazajensu kunya.
A cikin kunneta Zayyan yace "ni kuwa sai nake ganin kamar na tureki ne Fillo"
Da saurinta ta tashi zaune "rufa min asiri da abin kunya Sojana. Muna bikin 'ya ka
tureni da wane ido zan kalli mutane."
"Kin fiye tsoro kamar ba matar soja ba. Ina ruwanki da mutane. Iyaka ki goya namu
ta goya nasu ba shikenan ba"
"Ni dai ka dena wannan fatan" tace tana sake narke masa.
"Yanzu ma na fara, kinsan irin farincikin da zanyi kuwa idan gaske ne? Hmmm Fillo
kiyi fatan Allah Ya amsa domin ki ganewa idanunki babban matsayin da zaki kara
takawa a zuciyata"
"Kana nufin akwai inda ba ni bace dama?"
"Ko daya, sai dai zan kara mata fadi ne domin a haka kinyi mata yawa" yace yana
kara rungumeta tare da addu'ar cikar burinsa.
A nata bangaren itama hasashen cikin take yi amma kunyar kasancewarsa take. Ina
zata boye kanta ace tayi ciki bayan ta aurar da 'ya. Ga tarin fargabar yadda Zainab
ta haihu.
Sai dare ta iya saukowa Emzee yayi musu bayanin abinda likita yace. Mairama taji
babu dadi sosai. Wata kiyayya ta banza da Salame ta dorawa kanta ta janyo ta
makanta 'yarta da bata yi mata laifin komai ba. Kuka sosai Rahima take yi Zayyan
yace kowa ya fita ya barsu da ita. Daga shi sai ita da Ummi ya rinka yi mata nasiha
akan hakuri da karbar kaddara. A nutse yake janta karshe ya nemi jin me take son
karantawa idan ta gama makaranta tace Nursing take so. Murmushi yayi yana yabawa
zabinta sai dai wani hanzari ba gudu ba shine makarantar da aka sama mata sun ce
sai sunyi mata gwaji kafin ta shiga SS3. Idan bata sami result irin wanda suke
bukata ba sai ta maimaita ajin.
"Daada repeting fa kenan a wayance" tace a sanyaye da guntun hawayenta.
Ummi tayi dariya "kin ganni fa tare muke tafiya da yayyenki Ibrahim da Karami.
Yanzu nan da sati biyu zan koma makaranta ina level 4 suna level 4"
Murmushi tayi kafin tace "Nasan ma sai sunyi min ko don English da Maths"
Kwantar mata da hankali Daada ya cigaba da yi yace ko me ya faru kada ta damu. Ummi
kuma tace za'a daukar mata lesson teacher a gida. Bayan ta koma wurin Radhiya wayar
Malamijo Ummi ta kira ta fada masa.
Fada yayi kamar ya ari baki karshe yace "Mairama kinga hakkinki ko"
Hawaye ta soma yi "Malamijo ka dena fadin haka kaddararmu ce daga ni har Rahiman"
"Ai ko ban fada ba hakan ne. Salame ko kadan bata da hankali. A da bata damu da
Rahima ba yanzu kuma hakkin yarinyar nan bibiyarta yake duk inda ta zauna bata da
zance sai Rahima kamar wata sabon kamu. Tayi ta nunawa mutane kafarta wai ita tayi
mata lalle..."
Dariya ce ta nemi kwacewa Mairama tace "Kayi hakuri ba da niyar bata maka rai na
fada ba"
Albarka ya rinka saka mata yace ba da ita yake fushin ba yana dai jira ya gani ko
wannan dalilin zai sa Salame ta dawo hayyacinta sosai. A yadda ya tsara Na'e da
wasu ne cikin yaran zasu zo Abujan. Yadikko taje Sakkwato ita kuma Hajjo taje
Nijar. Maman 'yan biyu dai banda ita a wannan yawon yaranta kananu ne ga zaman
mota.
**********
Bikin kwana biyu suka halarta a Jos tare da su Tante Nasara da wasu daga Nijar da
suka taho tare. Kudi dai yayi kuka to amma ba abin mamaki bane duba da cewa biki ne
na 'ya daya tilo ga gwamnar jihar tasu.
Gabadaya aka dunguma suka koma Abuja wasu a mota wasu a jirgi. A hanya Ummi ta
rinka amai kamar zata fitar da kayan cikinta don sosai ta galabaita. Mama tana
sannu tana murmushi wanda ya janyo Ummi kai kararta wurin Mami. Hakuri Mami ta bata
tana gargadin Mama da ido saboda birkici musu da Ummin tayi. Zuwa yanzu ta gama
tabbatarwa ciki ne duk da bata je asibiti ba hankalinta duk ya tashi ina za ta kai
abin kunya a cewarta. Da su ka isa gidan Daada su duka ukun suka sauka a nan ana
lallaba patient. 'Ya'yan nasu basu san me yake damunta ba sai hawa suke ana mata
sannu. Sai da ya rage su hudu a dakin da Tante Nasara sannan Mama ta kasa hakuri ta
soma tambayarta.
Doki ne ya isheta tana dariya "Ummin Awwab anya baki harbu ba?"
Ummi ta gama aika mata sakon harara kamar ido zai fado "kin manta bindigeni akayi"
Su duka ukun suka sa dariya ta sake hade rai lokacin da Tante tace "abar zancen
wasa matar Yaya kamar fa ciki ne dake"
"Wannan ya wuce kama Nasara barka da zuwan Daada ne yake sakata amai. Sai dai muce
Allah Ya inganta" cewar Mami.
"Wallahi...wallahi...." ta soma cewa sai kuma kuka sosai tana yi harda sheshsheka
tace "ina zan kai wannan abin kunya don Allah. Ciki kamar wata yarinya?"
Mama ta galla mata harara "Allah Ya bamu hakuri" tana dauko DK da yake kwance akan
gadon "kai taho kaji dan soyayya in yayeka in samo maka kani ko kanwa."
Fuska jajur Ummi take nunata da hannu ga hawaye yaki tsayawa "Ya isheki Zainab
wannan ba abin wasa bane."
"Ni bansan ma me zan ce miki ba. Ki wayi gari bayan shekaru da dama da cikin Zayyan
a jikinki abinda nasan ko a mafarki baki hangowa shine kike kuka? Mairama kyauta
irin wannan ai sai sadaka da kyautata ibada. Uhmm Mami ga kanwarki nan bari na nemi
Emzee ya kaini gida kada ta bata min rai" ta mike za ta fita Tante ta rikota tana
cewa.
"Allah Ya shiryeku kuna abu kamar yara"
Mami ta sauke taguminta da tayi tana kallonsu suna aikin hararar juna "ni tunda
nake ma na taba ganin matan da suka gagara girma kamar wadannan."
Mama tace "baki jinta ne da wani shirme wai kunya...wannan ba shine babbar shaidar
Zayyan ya dawo da soyayyar Mairama ba"
Duk yadda jikin Ummi yake a mace bai hanata jifan Mama da pillow ba itama tana
dariyar "Allah Ya shiryeki Zainab"
"Amin Ya shiryemu mu duka." Ta koma tana kallon Mami "saura ke fa ya kamata mu ga
shaidar cewa har yau kina qalbin Major"
"Allah Ya tsareni da wannan abin kunya" tayi saurin cewa.
Ummi tace "ooooohhh da shine kuke yi min fata saboda rashin tausayi. Ni na manta
yadda ake raino"
"Kin dai san yadda ake samun baby....."
Tante ta hangame baki "Haka kike Zainab?"
"Ta wuce nan Nasara ki kalleta kawai ki dauke kai" cewar Mami.
Tsokanar juna suka cigaba da yi ana cewa Ummi ta tabbatar taje asibiti duk da dai
ko yanzu sun fara kirgin watanni. Babu ruwansu 'ya'ya suna shagalinsu suma suna
nasu.
Washegari duk wasu masu zuwa daga wani garin sun gama isowa. Radhiya dasu Zahra da
wuri suka tafi salon inda Arifah da wata cousin dinta suke jiransu. Gyaran hannu da
kafa aka fara yi musu ga fatar jikinsu tana ta sheki anyi gyara har an gaji. Bayan
sun gama aka zo wankin kai. Radhiya na bude gashinta Arifah ta rike baki ganin
yadda kasansa yayi wani irin ja mai duhu.
"Dye kika saka?"
"Lalle ne" ta bata amsa kafin ta hau bayanin yadda ta kwana hudu tana kwana da
lallen da take shafawa a a gashin kullum. Kimantawa tayi kamar daya bisa ukun
gashin amma daga kasa take saka masa lallen shine yayi wannan kalar. Daga sama zuwa
kafadunta baki yayin da kasan ya bada wata kala mai kyau. Ita da bata saka relaxer
steaming da stretching aka yi mata ranar wuni guda a nan suka kwasheta.
Yau Laraba ranar da ake jira tayi. Karfe takwas mai lalle tazo dama jiya an yiwa
kowa amarya kadai ta rage. Zama na musamman suka yi aka gama ja sannan aka dora
baki. Karfe biyar Mama tayo waya don itama gidanta da baki haka na Mami. Su
Hussaina, Nura da Hany wadda ta soma jin sauki sun taho. Gidan Mami tayi masauki
sauran suna gidan Mummy Gambo.
A jikin katin an riga an rubuta tsarin events ciki harda zuwan baki daga bakwai da
rabi tunda ana Magrib shida da rabi ne zuwa takwas da kwata lokacin da za'a rufe
hall a fara event. Mutanenmu da son biki babu mai son a rufe shi a waje shiyasa duk
mai zuwa shiri yake da gasken gaske.
Wanka Radhiya ta silla tare da dauro alwalar magrib. Bayan ta shafa mai tayi sallah
ta zura kaya don har ita Mama kira take akan idan suka bata lokaci zata saba musu
ne. Riga da skirt ne na wani irin material pink da ya amsa sunansa. Rigar daidai da
jikinta amma wuyan ya rufe mata baya sai daga gaba aka bude. Hannun dogo daga kasa
an bude shi sosai. Shirt din ma sai daga kasan gwiwa aka saka net domin kara masa
fadi. Kafin a fara kwalliya Emzee ya kwankwasa kofar dakin yana kiranta.
Tana lekowa ya saki murmushi "my one and only Sis kinyi kyau"
Itama murmushin tayi "kai Emzee ba ayi kwalliyar ba fa."
"Duk da haka bani da ta biyunki" yace daidai fitowar Rahima ta kada kanta kawai don
yanzu ta saba da halinsa. Dakin Daada ya nufa da Addarsa inda suka sami iyayensu
suna jiransu. Baki yaran su ka saki suna kallon Ummi da Daada sunyi kyau kamar
ranar tasu ce. Ummi lace ne baki a jikinta wanda ya amsa sunansa anyi masa wani
irin adon cin baki da sky blue din zare da stones. Anyi mata kwalliya ta fito sosai
tana haskawa abinka da mai yaron ciki. Mayafinta, takalmi da jaka duka sky blue ne,
ga dankareriyar sarka da abin hannu. Daada kuma shaddarsa ce sky blue din aikin
jikinta simple yet elegant. Yana sanye da hula zannabukar wadda ta dace da kayan.
Ummi rike take da links tana kokarin balle masa a hannun rigar ta kasa. Shigowar
Emzee shine ta bashi ya makala masa.
Daada yace a rufewa Radhiya ido kyauta zai bata. Emzee ne mai wannan aikin sai da
Daada ya bude wata hadaddiyar sarka shigen ta Ummi sannan aka bude mata idon.
Tsabar murna kuka ta saka masa ta fada jikinsa. Emzee sai ya koma gefe yana
daukarsu hoto gashinta ya kwanta a bayanta. Saka mata dankunnen da sarka iyayenta
suka yi tana ta musu addu'a da godiya.Kusan minti goma suna kashe selfie a
tsakaninsu sannan Radhiya ta tafi aka fara zuba mata kwalliya tayi kyau karshe.
Wasu kayan Fauziyya ta daukar mata a wata karamar jaka da kayan gyara kwalliya
saboda idan anyi rabin taron an riga an kama musu daki da zasu chanja kaya a cikin
Sheraton Hotel inda za'ayi event din.
Kowa ya gama shiri ana ta shiga mota masu tafiya da katinsu a hannu tunda card
admit ne. Takwas da minti kadan Awwab ya shigo gidan ya bude wurin da wani irin
kamshi mai ruda tunani da sanya shauki. Three piece tweed suit ce a jikinsa
burgundy color da dark pink necktie da irin hankicin nan da ake leko dashi ta saman
aljihun coat din. Yayi aski da gyaran fuska fuskarsa ta sake fitowa sosai. Yana
shigowa daidai da Zayyana ta riko Radhiya saboda tsinin takalminta suna saukowa a
hankali.
Murmushi ya sakar mata ita ta mayar lokacin da zukatansu ke tsananta bugu ya karasa
step na biyar inda suke tsaya ya mika mata hannu "shall we?"
Kai ta gyada a hankali tana ta murmushi ya riketa suka sauka. Su Zahra na biye dasu
mazansu na waje suka je suka shiga motocin da mazansu ke jiransu. Ankonsu lace ne
cream da head golden kowacce ka kalla kara. Zayyana kai tsaye motar Ibrahim ta wuce
shi da Emzee su ma suit din ce jikinsu grey amma basu saka necktie ba sai maballin
saman da suka bari a bude. Ba shi ba ba Emzee sai ka rasa wanda yafi yin kyau.
Rahima tana biye da ita da dan glass dinta kamar a dauketa a boye Emzee ya kasa
dena kallonta. Ibrahim da baisan dawan garin ba yace bari su dauki mota daya kawai
suka tafi a tasa. Matan na baya suna gaba suna taba hira amma Emzee da Rahima sai
uhm da uhmm.
Bakar Limousine ce ta dauki amare da angwayensu zuwa Sheraton Arifah da Radhiya
suka zama bebayen karfi da yaji. Kayansu babu bambanci ko daya sai sarkarsu yayin
da mazan su ma komai daya ne a jikinsu.
Kofar hall din katuwar poster ce zaune a kasa gefen dama hoton Yousuf da Arifah
wanda suka yi da shadda matan aka saka pin aka danne musu fafaren mayafansu ta
tsakiyar daurin da suka sha. A bangaren hagu kuma Radhiya da Awwab sunyi tsayuwa
iri daya. Matan na zaune akan kujera suna kallon fuskokin mazansu dake tsaye a
gefensu sun dafa hannun kujerar. A tsakiyar hoton an rubuta sunayensu.
Kafin shigarsu iyayen taro suka taho. Kayansu saka iri daya bakin lace na Ummi da
sky blue irin shaddar Daada, Mami Caramel irin shaddar Daddy, Mama light yellow
irin ta Baba Hadir, Tante Brown irin na Alh Moussa sai kuma na Mom light green irin
na Excellency. Idan ka cire iyayen Yousuf sauran hudun zaratan maza ne da suka
dandani me ake kira bautar kasa da jiki da lafiya tare da matansu jarumai wurin
hakuri da juriya. Taku suke ana daukarau hoto a cikin kayataccen hall din har zuwa
mazauninsu. Bayan sun zauna be aka kira angwaye da amare abin gwanin ban sha'awa da
burgewa.
Taro ne na manyan mutane komai cikin nutsuwa da hankali ake gabatar dashi. Bayan an
bude shi da addu'a aka gabatar da takaitaccen tarihin angwayen da amarensu.
Wani abin burgewa shine kiran Emzee da da MC Kdm yayi a matsayin babban abokin
amarya saboda babu wanda yasan Alheran Radhiya Zayyan Tureta sama da shakikinta
Muhammad Zayyan Tureta. Zahra ce ya bada tarihin Awwab sai kuma wani abokin Yousuf
da kawar Arifah 'yar kanin babanta suka bada nasu.
Can cikin taro akwai 'yan gidansu Zayyan da su Hussaina harda Mummy Gambo da
yaranta. Ghazalatu ta shiga wani yanayi na tashin hankali ganin yadda Awwab ya fito
yayi masifar kyau. Kallonsa take bata ko kiftawa saboda yadda take jinsa a ranta.
Ana tsaka da taron ne su ka ji wani dummm sai wanda ya sanya Awwab da Yousuf tashi
lokaci guda kuma hall din yayi duhu sai haske ya koma bakin kofar shigowa. Radhiya
dai taji Awwab ya matse mata hannu kadan sannan a daidai kunnenta yace mata yana
zuwa. Idanu fa sai suka koma bakin kofa bayan kamar minti daya da rabi sai ga
Yousuf da Awwab sun bullo ta katuwar kofar shigowa. Dukkansu sun cire coat dinsu
sai ta cikin mai maballai ta gaba wadda suka dora akan farar shirt din mai dogon
hannu sannan sun cire necktie sun bude maballai biyu na gaban shirts dinsu. Sanye
suke da homburg hats kalar wandunansu an dan turo ta gaba a karkace.
Yousuf ne ya fara magana da mic a hannunsa daga can gefen amaren ta sama aka fara
slide show inda hoton Arifah ya bayyana tana zaune cikin fulawoyi tana murmushi.
Sannu a hankali yake takowa zuwa gareta yana magana cikin harshen turanci duk da
dai faransanci yafi zama sosai a bakinsa.
("Thank you Arifah Nasiruddeen for being a part of life. Thank you for accepting me
to be the man in your life. You are my Queen the most beautiful woman I have ever
seen. To the special you I say I love you")
Ba Arifah ba hatta Mom dinta sai da taji wata kwallar farinciki. Hannunta ya kamo
zuwa tsakiyar filin idanunsu cikin na juna a lokacin da Awwab ya soma taku daidai
zuwa wurin zaman Radhiya.
("Once upon a time an adorable Angel was born") hoton Radhiya ne ya bayyana ranar
sunanta wanda aka daukesu tana hannun Awwab yana murmushi ya dan juyo da fuskarta
yadda zata fito a camera ("You and I were always meant to be. I love you with all
my heart...just so you know, it has always been Alheran Radhiya. The fearless 'Yar
soja, my one and only")
Wannan karon Ummi ce da hawayen ta sunkunyar da kai Daada ya matsa mata hannu yana
cewa suyi kusu addu'ar fatan zaman lafiya.
Awwab ma riko hannun matarsa yayi zuwa tsakiyar filin kusa da Arifah sannan ya yi
mata murmushi shi da Yousuf suka ja baya. Kidan wakar da matasan wurin da dama suka
sani ta Umar M Shareef JININ JIKINA ce ta karade wurin hasken wurin ta koma kan
Awwab, Yousuf, Emzee, Ibrahim, Bilal da Raji duka sun ajiye coats dinsu kowa ya
tsaya a inda ya dace suka fara takun wakar yayin da baitin farko ya cika wurin.
(Da ganinki sai na kamu.. gashi kin zamo jinin jikinaaaa)
Ba tare da kuskuren taku ko tangarda ba domin sun sha wahalar rehearsal da mai
koyar da rawar da suka dauko suke miming wakar suna rawar da ko wadanda suka hau ta
a film din bazasu nuna musu komai ba. Mamaki tukuru.a fuskar Radhiya da Arifah
yayin da jama'a suke kallon