Showing 105001 words to 108000 words out of 295847 words
za kayi mata siyayya?" Tace cikin fushi da
kishi.
"Nope, Alheran nake son sayawa wani abu"
Duk da haka ranta baiyi mata dadi ba amma bata son bata masa rai yanzu sai yace ya
fasa tsayawa a Abujan.
"Ka saya mata takalmi, jaka, turare, kayan kwalliya da jewelleries"
Yaji kayan da yawa to amma so yake ya yi musu abin bajinta "thanks dear" yace da
Ghazalatu kafin ya ajiye wayar.
💕[02/11 7:30 : 22. 💕
Iyakar karfinta tasa suna jan hijabin nata su ma suna ja. Mami na isowa tace su
dagata amma an makara don Zahra tayi nasarar cire dankwalin.
Emzee da Ibrahim suna bakin kofa don sun jiyo hayaniya daga dakin. Rasa me bakin
magana akayi harda Mami kuwa. Zainab ce ta kawo Mairama dakin, tunda taji shiru
tasan aikin gama ya gama.
Zayyana ce ta fara dariya gashi ya soma lekowa amma saboda makero baifi a kirga ba
sai wani uban fari fari kamar amosani kamar kora. Kullum tana shafa mai idan tayi
wanka amma yau saboda da mutane a dakin ta hakura ta daure kayanta.
Kowa ta kalla gimtse dariya yake ta harzuka sosai tayi kan Zahra tana ihu "wallahi
sai na rama"
"KE! Samu wuri ki zauna kada naji kinyi fada da kowa."
Kuka ta fashe dashi da karfi "wallahi Ummi kada ki cuceni ki barni na rama."
"Zahra bata dankwalinta kafin na saba muku. Wane irin abu ne haka da girmanku
saboda Allah." Mami ta soma fada.
Jefa mata dankwalin Zahra tayi don yadda take kallonta kamar kura ta ga nama bazata
so hannunsu ya gogi na juna ba.
Jikinsu sai yayi sanyi saboda kukan da take yi ta dauki dankwalinta ta kulle kan
sannan ta mayar da hijabinta. Zainab da Mami na bata hakuri taki kula kowa sai
sautin kuka da take karawa. Mairama tace su kyaleta ba shiru zata yi ba. Kowa ya
fita daga dakin tana zaune tana kukanta dole Mami taje ta fadawa Major.
"A kirawo min ita"
Zahra ta kalli Fauziyya, a, tsorace tace "ba dai ni ba, kece babba kuma ke kika
bude mata kan"
"Zayyana...." Zahra ta soma kira ta bari saboda kyabe fuskar da ta ga tayi ta koma
gefen Major tana cewa
"Daddy kace bazani ba"
"Mazaje waye zai kira min 'yata?" Yace da Ibrahim da Emzee kamar yana rokonsu.
Ibrahim ne ya tashi, Emzee kamar ruwa ya cinye shi. Yana zuwa ya sameta ta gama
hada kayanta a cikin jakar da tazo da ita tana bakin kofa zata fito.
"Dariya ka dawo yi?"
"Daddy ne yake kiranki"
Gani tayi ya tsaya kallonta yaki tafiya ta zaro masa idanu "in sake bude maka ka
gani da kyau ne?"
Murmushi yayi mata kawai don idan ya sake ya bude baki sai ta saka shi dariyar da
baiyi niyya ba. Sai yanzu ya gane meyasa kan nata yake kullum a daure kamar mai
tallan magani.
Da jakarta a hannu ta shiga su Zahra suka fara kuskus. Daddy ya gani sai ya
shareta "waye ya saka ki kuka?"
Rage tsayi tayi bakin nan a gaba kowa ya ganta yasan an tabota karshe "Daddy na san
komai fa, kaine da kanka ka turo Zayyana su gane min aski na"
Kafin su shigo sai da Mami ta roke shi akan ya taimaka kada yayi dariya. An san
soja da dakiya, amma a cikin iyalansu, iyalan ma na Zayyanunsa mantawa yake ya taba
zama soja. Ya fi fahimtar ya sake tare dasu ya nuna musu shi uba ne a garesu domin
kada a sami wani shamaki tsakaninsu.
"Cewa nayi ace ki wanke kanki fa 'Yar soja uwar sojoji"
Sai da tayi murmushin jindadin kirarin ta sake daurewa "a bani kudin mota in tafi
gida ko kuma a barni na rama"
"Radhiya kiyi hakuri da kaina zanyi punishing dinsu. Amma ki bar zancen ramuwa ko
tafiya gida" Mami tace tana hararar bangaren da su Zahra suke.
Kumbura baki tayi "ni dai wallahi sai dai a zabi daya"
Mairama taji kunyar kada a fara ganin ko harda sakacin tarbiya a halayen Radhiya.
Fada ta soma yi mata tace ta tashi ta koma ciki ta zauna.
"Allah Yasa naji kinyi fada da wani, zaki ga yadda zanyi dake. Ana lallabaki kina
wani botsarewa mutane"
"Laifinsu ne fa ki kyaleta, zo nan kinji Radhiya"
Kin tashi tayi tana kallon Zainab din tace "kema Mama na ga kamar kin danyi dariya
da aka bude kan"
Mairama ta sake fusata Daddy yace duk suyi hakuri laifinsa ne amma tayi hakuri.
"Ku kuma manyan ku daku kuna tsokanarta na kusa bata kambun girma a gidan nan.
Kwanannan zata zama yayar kowa da kowa a cikinku sai na ga wanda zai sake gane mata
askinta" murmushi yayi amma bata ji haushi ba tunda ya yi mata alkawarin zata zama
yayar kowa.
Da yake ba riko gareta ba sai ta saki fuska ta harari wannan ta harari wancan "kun
dai ji me Daddy yace, kuma daga nan ma soja zai kaini abuna. Hahaha idan na dawo
gidan nan za'a ga kawuna"
Zayyana sai tasa hannu ta rike nata kan tana kallonta a tsorace "yanke mana kai
zaki yi?"
"Inaaa yarinya kan Balotelli zanyi muku in huce haushin yau"
Ibrahim ya tuntsire da dariya harda fadowa daga kan kujera. Zainab ta daka masa
duka a baya ko a jikinsa sai dariya yake "zan rike miki su 'yar uwa, ai dai baki
ganni ina dariya ba"
Major ma dariyar yake yadda ta hakikance abinta. Sauran matan babu wadda ta damu da
ball ko 'yan ball balle su fahimci me take nufi da Balotelli din. Hakuri dai yayi
ta bata tana kara jaddada masa burinta na zama soja tunda ta ga yana lallabata.
"Soja mai babban mukami zanyi miki amma ta cikin gida, yanzu dai ku tashi amma idan
kun shiga ciki kada ki kula kowa"
"Daddy gaba fa kenan?" Tace tana ware idanunta ta rike haba.
Su Zainab sai dariya, Major ya dage yana ta bayanin cewa ba gaba yake nufi ba. Kada
ta kula su dai azo ana rigima.
"Au ho...ai na hakura tunda idan na dawo daga soja zan dauki mataki. Baba zanyi
kyau da soja ko?" Tace tana kallon Hadir.
Kai ya gyada mata yana murmushi. Hannunsa taje ta rike tana durkushe a gabansa ita
dai tana son sa sosai, sai da Daddy yace ta bi bayan 'yan uwanta zaiyi magana da
iyayenta ta fita. Da taje dakin daga bakin kofa ta wulla jakarta ciki sai gasu suna
darewa da sauri don ba karamin tsoro ta basu ba. Wata shu'umar dariya tayi wani abu
ma sai an dawo daga makarantar sojoji. Babu wadda ta tanka mata ta shigo ta haye
gado ta kwanta. Wayar Zahra aka kira ashe Awwab ne ya ya tambayeta size din
takalmin Radhiya saboda yasan suna gidan. Kintata kawai tayi ta fada masa saboda
ita dai bazata tambayeta ba a yau dai sannan a gabanta bazata taba mata takalmi ba
don tsoron me zai faru take ji.
A falon Daddy kuwa bayan fitarsu Mairama ta shiga basu hakurin halayyar Radhiya.
Gani take kamar laifinta ne ko sakacin tarbiya ne ya kawo hakan.
"Kowane da da irin halayensa da dabi'u da ake haihuwarsa dashi. Kuma yadda take
dinnan Allah kadai Yasan wace irin tarin baiwa Yayi mata. Ki dena damun kaki
watarana zaki ga kamar ba'ayi ba"
Mami ce da wannan dogon jawabi sauran suna gyada kai. Daddy ya bijoro musu da
zancen da sukayi da su Ardo.
"Hada Awwab da kanwarsa abu ne da na kudurta tun ranar da na dora ido a kanta.
Hadir ya amince ina fata Allah Yasa ku ma ku bani goyon baya"
Gabadaya matan nan uku bakunansu murmushin jindadi suke nunawa. Mami tana maraba da
wannan hadin domin bazata taba kyamar tsatson Mairama da Zayyan ba. Tafi kowa sanin
mahimmancin yin hakan a wurin mijinta. Zai kara sakawa yaji a ransa cewa bai ya da
iyalan Zayyan din ba. Ya so Zayyan tun basu saba ba duk ranar da suka je training
zata kwana yana bata labarin fitinannen basakkwacen nan. Lokaci kalilan ne Radhiya
zata waye tayi zarra cikin sa'anni. Zainab ma taji dadi don burinta su hadu su
baiwa Mairama da 'ya'yanta dukkan farincikin da suka rasa. Allah Ya sani ba don
sa'anni suke da Ibrahim har ta bashi watanni ba itama da zata so hadasu ne.
Farincikin Mairama yafi na kowa. Wadannan mutane masu dimbin karamci a gareta ace
babu kyamar yadda su suka kara wayewa ita da 'ya'yanta suka sake ci baya ta fannin
wayewa da sanin ababen rayuwa amma su nemi hada Radhiya da Awwab, Awwab dinta dai
wanda ya mayar da ita da mijinta iyaye tun farkon haduwarsu. Hawaye ta shiga yi
tana mika godiya garesu.
"Bani da bakin godiya, Zainab kunji wani karamcin kuma?"
"Idan kina haka sai mu ga kamar a wurinka Radhiya da Zayyan ba namu bane Ummin
Awwab"
"Haba Mami kada kice haka mana, farinciki ne kawai yayi min yawa"
Mami ta tambayi Major "yaushe kake tunanin auren?"
"Kuna ganin zamu iya hadawa da na su Zahra? Idan hakan yayi in sha Allahu karshen
sati Alh Baba zai dawo daga Umara sai na fada masa"
To waye ma zaice baiyi na'am da wannan hadi ba. Bakinsu duk yazo daya, abu guda ya
rage a sanar da Alh Baba sai ayi shiri aje a nemi aurenta wurin wadanda ya dace
wato dangin mahaifinta na Sakkwato da kuma marikanta ta bangaren uwa su Ardo
Barkindo.
**********
"Banza jaka bace min da gani ko inyi kwallo dake. Har yau ina tsananin mamakin
yadda akayi na kwaso ki Salame"
Janye tsumman jikinta tayi da ya gama karewa ya tsotse babu wani tudu a jikinta
bayan cikin jikinta na wata shida. Gabadaya ta mokade baka ce Salame bace da
tauraruwarta ta taba haskawa a gidan Salisu. Aure dududu bai wuce shekara takwas ba
amma haihuwarta biyar ga cikin na shida. Da kyar take tafiya yunwa ta yiwa hanjinta
mugun lahani ga yara tun asuba suke kira mata yunwa suna kuka.
Ba ta daddara ba ta sake hada hannuwa a gaban Alh Indararo "Alhaji ko naira hamsin
ce ka bani don Allah, bani da karfin karbo wankau da bazan tambayeka ba"
Kallon kin ma rainani ya jefa mata "sai ki tafi inda kika saba zuwa gidan tsoho aje
a ci abinda ya sauwaka"
Duk magiya da rokonta ta bayan kunnensa tabi sai da ranta ya baci sosai ta tsaya
masa kerere a gaba. Tulun cikinsa kadai ya isa ya tureta dashi ta fadi.
"Ka sakeni in koma gidan ubana ai ba a titi aka daura mana aure ba. Wannan wace
irin rayuwa ce ace matanka tsakaninka dasu bai wuce ka dirka mana ciki ba. Ci da
sha da sutura sai dai mu yiwa kanmu. Ko kunya baka ji duk kudinka. Mune wankau,
surfe da duk wani aikin kaskanci don mu ciyar da kanmu da 'ya 'yanmu"
Marin da ya zabga mata ne yana faman nade hannun malum malum ya gigita ta ta kasa
cigaba da maida martani.
"Ki fita idona Salame, wannan jarababben auren naki kuma yanzu muka fara babu inda
zaki je"
Fuuuu ya fice daga gidan sai dariyar Maman Danmama da ta cika mata kunne. Bata
saurara ba sai da ta fito daga dakinta tazo gaban Salame tana mata dariyar mugunta.
"Mu dai sai dai muce Allah Ya kara karawa. Ki koma wurin bokanki kice masa kwabarki
tayi ruwa. Irin wadannan ranakun tsakaninki da Alhaji su kan sani nishadi da wanke
min zuciya. Anyi walkiya Salame mun ganki tsamo tsamo"
Dan sauran kuzarin nata na fada marin da ta sha ya tafi dashi, shiyasa ta kasa
maidawa Maman Danmama. Ita kuwa batayi shiru ba.
"Ohhh ni 'yasu. Kamar ba'ayi zamanin da kike sa Alhaji ya zage ya zanemu a cikin
gidan nan ba. Kika dawo kika saka shi sakin kowa banda ni wai na zauna nayi raino
kema a gidanku uwargidan babanku aikinta kenan. Ai ance tsafi gaskiyar mai shi.
Kinyi kin gama surkullen tazo ta kare miki"
Wani dukunkunannen hijabi Salame ta saka taki kula Mama ta fita tare da yaranta ta
nufi gida.
A soro suka yi kicibus da Malamijo zai fita. Girma ya kara kama shi sai dai akwai
kyan jiki tunda babu kiba kuma yanzu ya yarda da ci da sha wa kansa mai kyau a
waje. 'Yar fara'ar da ya taho da ita sakamakon faranta masa da amarya tayi kafin ya
fito ce ta bace yana ganinta.
"Allah Yayi dare gari ya waye an kwaso jiki an taho cin banza. To baki isa ba
Salame. Tunda na aurar dake ko dan ihsanin nan na tsakanin da da mahaifi bai taba
giftawa tsakaninmu ba sai ma dai ki karkace ki fada min magana idan kinso. Amma
'yan kwanakin nan kullum ana fada min sai kinzo, kuma ba kya tashi zuwa sai kin
daidaici an gama abinci. Ki kwaso yara rabe-rabe azo aci bati. To na gaji, ki juya
sawunki a likkafa ki koma inda kika fito"
Jikinta har bari yake saboda yunwar dake sasakarta fushi da maidawa mahaifinta
martani ba nata bane yau dinnan idan ba so take daga ita har yaran yunwa ta kar su
ba.
"Ku shige gani nan zuwa" tace tana kadasu ciki.
"Ya ina cewa ku koma kina turasu? Salame, Salame ki kiyayeni." Yace yana nunata da
yatsa.
"Gaisawa kawai zanyi dasu mu tafi"
Tausayinta ya dan ji saboda ya tabbatar yadda ta fige dinnan tabbas kila mijin da
har shi take iya yiwa rashin kunya a kansa ya juya mata baya ne.
"Jeki amma daga yau na sake ganinki zanje na sami Alh Indararon inji ko har ya
cinye sadakinsa ne shiyasa zamu fara raba nauyin. Mairama ma da take ruga ta fiki
abin arziki. Makanta, rashin miji da nisa basu hanata yi min alheri ba."
Kunci taji ya ziyarci zuciyarta saboda ya ambaci kamwarta da ta mayar kishiyarta ta
karfin tsiya. Duk ita ce silar komai tunda dalilinta taje wurin boka aka rabata da
Alh Indararo saboda kawai bata son ta ga tayi gaba ta barta ba wai don ita din
sonsa take yi ba. Da asiri ta rinka cin galaba akansa da matansa komai na tafiya
daidai ta kuma saki jiki tana ta haihuwa don ta tara magada sosai. Cikin jikinta na
da wata biyu bokan nata yace ga garinku. Shikenan duniya tayi mata atishawar 'yan
tsaki. Komai ya lalace wai ita da take mulkin gidan a tsakar gida Alh Indararo ya
kalleta yace yaushe ya aurota. Da bakinsa yake cewa ina Mairama kanwarta. Rai a
bace ta shige ta ce da yaranta su taso su tafi.
"Ki barsu yanzu zan zuba musu abinci Salame" Yadikko tace mata tana kallonta da
tausayawa. Ko bata ce komai ba kana kallonta kasan akwai yunwa daga ita har yaran.
"Tafiya zamuyi, kai ku tashi mana"
"Umma ki bari muci abinci" babbar 'yarta tace idonta cike da kwalla.
"Ko ku tashi ko jikinku ya gaya muku ku duka. Aikin banza kai."
Duk yadda Yadikko taso kin zama tayi saboda kawai an yabi Mairama ta gwammace su
sake kwana da yunwa.
**********
Karfe biyar da rabi Awwab ya sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport da yake
birnin tarayya. Ya saba tafiye tafiyensa babu wasu kaya sai 'yar jaka karama da
yake saka kayan sakawa biyu ko uku ya danganta da kwana nawa zaiyi a garin. Wannan
karon kuwa sai da ya hado da akwati mai kyau na turawa dan madaidaici. Jin kansa
yake wasai babu tarin gajiyar nan saboda a fasinja ya taho ba pilot ba, tun daga
tasowarsu sai minti goma kafin saukar jirgin ya farka.
💕[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 23💕
. Ruwa yaje ya watsawa fuskarsa yayi brush sannan ya dauko wani karamin hankici
kamar tawul iya tafin hannunsa ya goge fuskar. Komawa yayi ya zauna yana jin kansa
yayi wani fresh balle da ya tuna mutanen da zai gani. Kayataccen murmushi yayi shi
kadai wata matashiya da suke zaune tare ta maida masa saboda ya dan fuskanceta ne
yana laluben seat belt dinsa.
"Hi handsome" tace dashi da ingantaccen turancinta.
Sai da ya waiga bayansa ya tabbatar babu kowa sannan ya nuna kansa sai ta gyada
kai.
"Hello" ya maida mata da kyar don baya son mace mara kamun kai. Da ace magana tayi
masa kawai bazai damu ba. Amma idan kaji ana handsome ko beautiful ai kasan kwanan
zancen.
"Kaima bahaushe ne ko?"
Baiyi mamakin da ta gane ba tunda suna zama ya soma waya bai dena ba sai da yaga
jirgin ya fara tafiya.
"Kema haka ko?"
Murmushi tayi, a rayuwarta tana son namiji mai kaurin murya. Ba da karfi ya amsa
mata ba amma amon muryar ya isa ya sanya mata da yawa muradin son kasancewa da mai
ita musamman idan suka hado dashi. Wankan tarwada, dogo, hanci madaidaici da ya
dace da kyakkyawar fuskarsa.
"Na kula baka ci komai ba tun tasowarmu."
Bai wani kare mata kallo ba yace "bana jin yunwa ne"
So take hirar ta tsawaita don tunda ta dora idanu a kansa zuciyarta bata kara samun
sauki ba. Ta kula mutumin kamar yana da ji da kai sai dai kuma bazata bari shan
kamshinsa ya hanata samun abinda take so ba. Dawowarta kenan daga Germany inda taje
hutu wurin yayarta. Mahaifinta tsohon soja ne da ya tsunduma siyasa tun lokacin
mulkin farar hula. Yanzu haka sanata ne da yake wakiltar mazabarsu a jihar Plateau.
"Suna na Arifah"
"Awwab"
Daga haka ya kafa waya a kunne don tuni sun sauka an bada damar kowa ya tashi.
Cikin cabin crew din wata 'yar Nigeria da tasan Awwab tazo suna gaisawa da ya tashi
zai dauki jakarsa.
"Captain yau fa ka yi mana wayo. Kasha bacci ka barmu da aiki"
Sai yanzu Arifah ta ga ya sake sakin fuska harda dariya "ki dauki hutu kema sai mu
koma tare. Yanzu ina da wata guda na mantawa da kowa sai family dina"
'Yar hira suka taba sannan suka yi sallama. Awwab na fita Arifah ta bi bayan matar
da suka gaisa mai suna Chisom ta roketa numbar wayarsa.
"Ki bishi ya baki da kansa, Captain Awwab baya son irin haka don an taba yi masa na
gani"
Marairaicewa tayi tana fada mata yadda take son shi tare da rokon ta taimaka mata.
Kudi ta dauko daga jakarta za ta mika mata Chisom ta bata rai "ba sai kin sayeni
ba, Awwab is a nice man ga number dinsa ki gwada sa'arki"
Arifah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ta rubuce number din da ta karanto mata daga
wayarta ta fita da sauri ko zata sake samunsa sai dai yayi mata nisa bata ma san
ina yayi ba. Bata da damuwa tunda akwai numbar da zata same shi.
Yana fitowa waje hasken rana ya kwale a sama kamar ba shida ke neman yi ba. Jacket
dinsa ya cire ya sakale a hannunsa ya jana jan akwatinsa.
Kamar ance ya kalli hagunsa suka hada ido da Ghazalatu. Taci kwalliya sosai don ta
burge shi ta kuwa yi nasarar sanya shi murmushi. Daga ita sai dreba suka zo
daukarsa kannenta suna makaranta.
"Yayana" tace da ya zagayo wurin motar tana murmushi.
"My G kinyi kyau fa"
"Ba wani nan, kai dai kawai ka dade baka ganni bane"
Gaisawa yayi da dreban ya shiga gaba ita kadai a baya suna ta hira. Ji take kamar
ya dawo bayan motar su zauna tare. Ta rasa gane masa ne ana soyayya amma shi tamkar
wanda ya taso a kauye. Baya irin yadda wayayyu suke yi. Ko gidansu taje hutu haka
zata karaci zamanta hannu wannan bai san ya rike mata ba ko da su kadai suka fita.
Yanzu wata hudu rabon da ya ganta amma simple hug ma su ji dumin juna ya gagara.
Waya ya