Showing 147001 words to 150000 words out of 295847 words

Chapter 50 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

take gani kamar kanwarta cikin shiga ta kece raini ta wuce
sa'a. Daga sama har takalmin kafarta sai da ta bisu da ido tana jinjina kyau da
haduwa irin na suturar da mai ita.

"Mairama? Mairama kece ko dai kama ce?"


Sassanyan murmushin nan nata mai kara kawata kyakkyawar fuskarta ta saki "Adda
Salame nice mana"


Tsananin mamaki bai bar Salame ta dakata haka nan ba sai da ta ciro hannu tana yawo
dashi a gaban fuskar Mairama wadda farin gilashinta ya karawa kwarjini.


"Kina ganin me nake da hannuna?" Tace baki na rawa.


Ummi sai ta kama hannun ta rike. Nata yayi laushi sosai saboda gyaran da akayi musu
a salon. Na Salame kuwa sai dai ayi shiru ayi kurum inji dogaran sarki. Kanta da
lamba...a daiyi shirun kawai.


"Adda idanuna sun bude cikin hukuncin ubangiji. Zamuyi magana dai ina da baki" ta
fada tana yin gaba da sauri.


"Banten uba, kai!!!" Salame tace a gigice gabadaya ta kasa gane me take yi. Ko dai
gizo ne tayi mata ba ita din bace a zahiri? A'a Mairama dai kanwarta ita ce da
wannan shigar ta chanja tayi kyau haka kuma wai TANA GANI? Zuciyarta bugu take yi
kawai kamar wadda tayi tsere ga bakinciki da takaici sun taru sunyi mata rubdugu.


Zaninta karamar yarinyar ta sake ja tayi nisa a tunani taji cikin kuka tana cewa
"Umma, umfafa ta kare"


Wata mahaukaciyar mangara ta kaiwa yarinyar wadda take rike da zanin leshin da dama
da kyar ta hade shi a jikinta saboda ciki. Yadda yarinyar tayi gaba ta fadi haka ta
tafi da zanin babarta Salame a hannu. Sai ga Salame matar Alh Indararo a tsaye da
dan sket dinta na ciki ya fita hayyacinsa saboda tsabar jigata da kodewa. Dan lace
din da akayi masa cin baki dashi ya barke yana reto a jikin kafafunta wurin gwiwa
bari daya ne dinkin bai gama fita ba. Kuma gashi na silk mai santsi wani zare zare
nan duk ya fara fita daga inda dinkin lace din ya fita. Bata ma ankara da wuri ba
sai da babbar 'yar tace "Umma ina zaninki?"


Baki ya goge da ashar har ta gama hado shi zata lafta mata ta ga mutane sun zuba
mata ido wasu suna ta dariya. Sai a lokacin ta hango shi a hannun mai kuka.
Kafafunta ta kalla kunya matsananciya da muzanta suka dirar mata. Ga ciki ga dan
lace suna neman kayar da ita haka ta tafi da uban sauri ta finciko zanin ta daura
mutane suna ta dariya. Duk masifarta sai ta rasa abin cewa ta shiga neman wurin
buya saboda kofar gidan babu wani wurin wucewa an cika makil.


Lokacin da Radhiya ta fita Awwab yana tsaye a gefe suna magana da daya daga cikin
mutanen Nijar din amma da yake tun zuwansa hankalinsa gabadaya yana kan kofar yana
fatan fitowarta shiyasa tana leko da kanta ya hangeta. Ajiyar zuciya ya saki da
ganin fuskar da yake matukar so da kauna. Ita kuwa sai waige waige take tana yi
tana komar da kanta saboda mutane.


Alh Sidi ne ya fara ganinta daga inda suke tsaye ya tabo dan uwansa Alh Ghoumar
yana murna "kaga Alheran"


Alh Ghoumar ya juya shima yayi sa'ar ganinta "Allah mai iko, ka ga kamaninta da
tamu Alheran din?"


"Dalilin da yasa na ganeta ma kenan"


Tana wannan leken taji an kamo hannunta an ja ta gaba. Zata yi magana ta ga Emzee
ne. Ita fa bata san da wasu baki ba Hammanta tazo gani. Yana rike da ita bai saketa
ba sai a gabansu. Kanta ne ya nemi juyewa dama ga yara sun yanyame motocin saboda
kyaunsu ga kuma su kansu mutanen da yawa suna ta fitowa daga mota. Kukan Mammee da
ta rungumeta har yafi na dazu domin yadda Radhiya take diban yanayi sosai da
yayarta. Murmushin da Radhiya tayi ya kara karya mata zuciya saboda lotsawar
kumatun sak na yayarta ne.


Emzee yana yi mata bayani su ma suna ta yarensu suna dan hadowa da Hausa saboda
jikokin nasu. Fada musu yayi su dan kara hakuri suka ce babu komai sun san gida ne
na taro gashi ba'a san da zuwansu ba. Radhiya dai yau harda jin kunya yadda mutanen
nan dukkansu suke ta rungumarta matan. Mazan ma ita dai taji wani ya kamo hannunta
babba ne kuwa abokin wasan Zayyan sai dai kafin ta motsa taji wani tattausan hannu
ya janyota baya sannan ya dawo gabanta ya tsaya tsakaninta da mutumin. Babu mai
fahimtar mai Awwab yayi ko dalilinsa sai wanda yasan tsakaninsa sa Radhiya. Abinda
yaji ya ratsa shi kuwa shima sai da yayi nadamar taba hannun nata. Daga inda yake
tsaye yana kallon wannan runguma zuciyarsa ta tsinke da yaga mata sun kare kada a
fara da maza. Kishin da ya yunkuro masa ba kadan bane. Allah ne Ya taimake shi ya
taho da wuri yau da sai anyi abinda zai mutu bai manta ba, wato Alheran dinsa a
jikin wani. Babu ruwansa da alakar dake tsakaninsu tunda ya tabbatar babu
muharraminta ciki idan aka cire kakaninta biyu Alh Ghoumar da Alh Sidi. Sauran duk
wanda ya tabata ya taba masa mata ne.


Ummi da kanta ta rufo mayafi ta leko kiransu. Mutane suna darewa wadannan jama'a
guda wadanda dukkansu kowa ka kalla kasan ya taka wani abu a duniya na arziki
mazansu da matansu suka shige inda aka nuna musu. Tabarmi ne sababbi manya aka
shimfide musu suka zazzauna babu girman kai da jin su din wasu ne. Mammee ta rike
Ummi tana ta sharar hawaye. Rabon da su hadu shekara goma shatara tun ranar sunan
Alheran Radhiya.


Wurin minti goma ana ta matsar kwalla Ummi an fama mata rashin gwarzon namiji
masoyin kwarai Zayyan uban 'ya'yanta.


"Mairama yaya bayan saduwa? Kiyi hakuri. Don Allah ke da 'ya'yan nan kuyi hakuri"
Alh Sidi yace yana duban su duka su ukun.


Salame da kunya ta korota sashen mazan gidan nasu taci karo da wannan abin
al'ajabi. Wurin gabadaya wani irin kamshi yake yi. Sakato tayi tana kallon mutanen.
Maza biyu cikinsu wato su Alh Ghoumar sun dora rawaninsu na al'ada a kawunansu.
Sauran kuwa sai ka rantse wasu larabawa ne. Buzaye ne gaba da baya da kudi ya kara
gyarawa rayuwa suka kara fitowa. Bakinta bai iya neman abin fada ba na nuna mamaki
taji muryar marainiyar wayonta Mairama.


"Don Allah ku dena bamu hakuri ba laifinku bane. Kaddara ce kawai da kuma abinda
Kawun yaran nan yayi mana"


Kallo ta bita dashi suna zaune tsakiyar mutanen da ita da 'ya'yanta. Zuciyarta har
wani girgiza tayi da ta kalli Emzee. Itama sai ya tuna mata da nata tsohon mikin na
son mijin kanwarta. Babban abin da ya daure mata kai shine sanin da tayi Mairama ta
makance suna kauye ita da gayyar yaranta. To tana ina ne ta warke kuma suka yi fes
dasu ba yadda take tsammanin ganinsu ba? Ga wani kyakkyawan saurayi tsaye a gefe ya
tokare kafarsa daya da bango shi kuma ko waye? Tambayoyi take ta yiwa kanta tana
neman amsa ido rufe.


"Matsa a wuce" taji ance daga bayanta. Matsawar tayi kuwa aka fara shigowa da
tray-tray na kayan abinci da abubuwan sha. Duk abinda za'a tanada Innawuro ce ta
kwance gefen zaninta ta bada kudi masu yawa har su Yadikko sai da suka yi mamaki.
Bafillatana tana zaune haka cikinsu ana dariya ashe dukiya ce a jikinta. An dibar
musu cikin abincin bikin sannan aka siyo tsire da balangu mai yawa da lemukan roba
da ruwa masu sanyi.


"Shiga ku gaisa mana 'yan uwan Marigayi ne daga Nijar" Hajjo tayi maganar tana
wucewa ciki ita da su Nene Marka suka gaisa da bakin aka gabatar musu da abinci.
Kamar zata hadiyi zuciya ta juya batare da ta cewa kowa uffan ba ta bar wurin. Su
dinma babu wanda ya kula da ita suna murnar ganin juna.


"Bari mu baku wuri kuci abinci don Allah. An tafi kiran babana sai ku gaisa"


"Ki bar mana yaran idan tashi zaki yi"

Wata mata mai faram faram tace cikin hausar da tafi kama da ta Kanawa. Ilai kuwa
ashe aure ne ya kaita Nijar ita ce amarya cikin matan Alh Sidi amma mutuniyar Kano
ce.


Ummi tana murmushi tace dama wa ya aiketa. Inda Awwab yake tsaye ta kalla "dan Ummi
zo muje kaci abinci"


"Bazai ci cikinmu ba? Tare muka taho shima bako ne" saurayin da suke magana dazu
dashi yace yana dariya.


"Wannan naku ne kada ka damu dani" Radhiya ya kalla ta wani nutsu kamar ba ita ba
"taso ki zuba min".


Ummi na jin haka tayi gaba abinta tana murmushi suka tashi aka basu wuri domin su
samu su sake musamman mazan. Emzee ne kawai bai tashi ba yana aikin amsa musu
tambayoyin da suke yi masa game da rayuwarsu.
Kofar da zata fitar dashi waje Awwab ya bi ba wadda zata sada shi da ainihin tsakar
gidan ba. Radhiya sai tabi bayansa suka fito yayi hanyar inda ya ajiye tasa motar.
Baya ya bude mata babu musu ta zauna shima ya zauna a gaba bangaren dreba kafafunsu
suna waje. Lallen kafarta ya kalla ta saka daya daga cikin takalman da ya kawo mata
tayi matukar kyau.


"Shigar da kafarki ciki"


Zumbura masa baki tayi sannan ta dauke kafafun.


"Me yasa kika dena daukar wayata yau kwana biyu?" Ya tambayeta da wannan deep voice
din tasa.


Shagwabe fuska tayi kafin tace "to ba kaine ka dena kirana ba saboda ka koma
Katsina wurin....wurin"


Fada yaso yi mata na hora shi da tayi ta hana shi jin daddadar muryarta idan tana
shagwaba ko ta hado wani shirmen nata sai ya kasa. Ganinta kawai da yadda tayi masa
kyau ya kawar da komai.


"Wurin wa?"


Harara ta galla masa tana juya idanu ita anyi mata laifi sai dai gabadaya abin da
tayi sauke masa kasala yayi "ai ka fini sanin wa nake nufi. Wurin My G mana ni kuma
ka manta dani"


Bushewa yayi da dariya damuwarsa ta ragu sosai. Babu wani abu da yake tunani sama
da mallakar wannan yarinyar da take gabansa a matsayin matar aurensa.


"Kema G dinki ce ashe"


"A'a wallahi" tace da sauri, hakan ma yana kara bashi dariya har wani kada hannuwa
take yi "taka ce kai dai"


"Yanzu dai kishin dreba kike yi" ya dage mata gira "Allah sarki kanwata ta kare
miki gashi dreban nan bazai barki ba sai kin amsa sunan matarsa"


Tsuke baki tayi tana dariya kunya ta rufe ta. A hankali ta daga kanta suka hada ido
tayi saurin rufe fuskarta da hannuwanta. Yatsun sun sha lalle kamar ya rikosu.


"Schatzi"


"Uhummm"
"I miss you"


"Zaka sa naji kunyarka Hamma"


"Kuma I love you"


Mayafi tasa ta rufe fuskar yanzu tana so ta tashi ta gudu tana gudun kada yace ya
hanata.


Langabe kai yayi yace "Baki bani amsa ba ko daya. Kenan bakiyi missing dina ba kuma
ba kya sona"


Radhiya ba wayo yana fadin haka ta dago da sauri "ba fa kaji nace haka ba"


"Kina son nawa ne? Ba ni kadai nake abuna ba"


"Kai Hamma Allah bance ba" ta fada kamar tayi masa kuka.


Shi kuma ya sami na yi ya cigaba da cewa "do you love me?"


"Eh mana"


Yadda maganar ta fito a bazata haka itama ta fita daga motar harda tuntube ta kutsa
ta cikin mutane tana jin kunya ta barshi da yi mata dariya.


Wayarsa ce tayi ringing sai a lokacin ya kula ashe Mami ta kira shi sau biyar.
Sunyi da ita suna zuwa zai hadata da Ummi tunda sun kasa samuta ya manta shaf. Bai
yi tunanin amsawa ba yana gudun fada ya rufe motar ya koma ta bangaren da bakin
suke don ya bawa Emzee ya kai mata. Ko da ya shiga ma sai yayi sa'a tana wurin dasu
Nene tana basu labarin makantar da tayi da warakarta kwanaki kadan da suka wuce.
Wayar ce ta sake shigowa ya mika mata yana cewa Mami ce.


Karba tayi ta kara a kunne da sallamarta sai dai maimakon muryar Mami sai taji
Fauziyya tana kuka sosai tana cewa "Hamma ka dawo gida ba lafiya"


Ummi na jin haka ta mike tsam ta fita ta kofar waje saboda ko ina na gidan hayaniya
akeyi ta sami gefen wani gida da bishiya a jikin gidansu ta tsaya. Hankalinta a
tashe yake tace "Fauziyya me yake faruwa?"


Gabanta ne ya fadi. Da farko kamar bazata ce komai ba sai da Ummin ta soma yi mata
fadan cewa itama babarsu ce.


"Ummi tun dazu Mami da Zahra suke kuka. Bansan me yake faruwa ba amma har Umma
Hussaina da Mummy sunzo sunyi fada da Mami"
Zantukan Fauziyya sun daure mata kai matuka ta kasa fahimtar me yake faruwa kamar
yadda itama Fauziyyan bata gama ganewa ba. Kwantar mata da hankali tayi tace mata
gobe zasu taho in sha Allahu da Awwab.


Da ta koma su Mammee suka ce zasu tafi Kano su kwana biyu sannan su koma Nijar.
Ummi bata ji dadi ba. Niyarsu matan su kwana a wurinta tun farko amma sun fuskanci
hakan wahalarwa ne gareta saboda yanayin biki da ake yi a gidan babu masaka tsinke.


"Yara muka zo gani dake kuma Alhamdulillah mun gani duka kuna lafiya. Sai dai muna
son muji yaushe ne zaiyi muku daidai mu turo ku taho Niger domin ku hadu da sauran
'yan uwa"


"Ba don bikin da zamuyi a Katsina na yara har biyu ba da tun yanzu zaku tafi dasu"
Ummi tace tana kokarin boye damuwar da ta shiga tun bayan wayarsu da Fauziyya.


"Kema sai kinje Mairama ba yaran kadai ne namu ba" Mammee tace sauran suna dariya.


"In sha Allahu muna gama bikin zan sanar daku Mammee"


Sallamar Malamijo ce ta katse zancen nasu. Bai yarda ya zo wurinsu ba sai da ya
shiga cikin gidan yaje ya chanja kaya. Kayan da zaisa gobe na daurin aure ya sako
saboda motocin da ya gani sun tayar masa da hankali. Ya saka babbar riga yana ta
baza hannuwa. Saboda karfin hali ya sami irin farin abin nan da akan gani malamai
sun ninka sun daure hularsu dashi na ustazai shima haka yayi ya fito ko karya
babbar rigar baiyi ba don ya kara cika ido.


Wurin bakin yaje ganinsu ya sake tayar da hankalinsa yasan lallai ba bakin rainawa
bane.


[11/2, 7:11 AM]🏽
]🏽 : 36.**********💕

Yau falon na Alh Baba ya cika sosai sakamakon yawan wadanda aka zauna dominsu.
Jikokin da abin ya shafa suna cikin gida sai an gama da iyayensu za'a nemesu.


"Wace magana nake ji haka cewa jiya Gambo taje gidan Mustapha da Husaina yau kuma
da Azumi ana rigima?"


Babu wadda ta iya yin ko da tari ne saboda kwarjinin iyayen nasu. Alh Baba ya kara
hade rai yace Mami ta fada masa me ya faru. Kai a kasa ta zayyane masa komai.
Gabadayansu sun nuna fushi akan abinda kannen nata suka yi mata tare da Azumi.


"Naga alama a kokarina na son inganta zumuncin zuri'ata al'amura suna kara
tabarbarewa. A zamaninmu dai mace ko namiji sai dai ace ga wane za'a hadaku aure
kuma ayi auren a zauna lafiya. To amma na kula daku da 'ya'yanku abin ba haka yake
a wurinku ba"
Baba Karami ya kalli su Mummy "Gambo baku kyauta ba ko kadan abinda kuka yiwa
Hassana har gida kuma a gaban 'ya'ya. Ko bata girme ku ba ai ta ci darajar auren
yayanku"


Sun hadu sun yi musu fada akan abinda ya faru sannan Alh Baba yace to tunda abu ya
koma kowa kanta ta sani da 'ya'yanta zai kira yaran ya sake tambayarsu. Duk abinda
suka yanke shikenan.


Kana ganin yadda yake magana kasan akwai bacin rai sosai a tattare dashi

"Zabi ya rage tsakaninku da 'ya'yanku bazan sake saka muku baki ba balle inyi bakin
jini"


"Alhaji kayi hakuri don Allah. Muma kaine ka aurar damu in sha Allahu duk yadda
kace akansu haka za'ayi" Daddy yace sauran 'yan uwansa suka nuna amincewarsu.


Alh Baba sai kuma yaji nauyin yadda duk da yafi kowa sanin cewa son kansa ya nuna
akan komai amma gabadaya yaran da iyayensu kai hatta kannensa kowa ya amince ne
domin biyayya a gareshi. A tunaninsa wannan hadin kara dankon zumunci zaiyi amma
zamani ya chanja. Bai manta ba daren jiya da Baban biyu yake ce masa auren hadi
yanzu a cikin goma daya akan samu ana zaman lafiya. Biyu ayi zaman hakuri sauran
bakwai din kuwa duk mutuwa suke yi wani lokacin ayi rabuwar da zata shafi har
jikoki. Ya bashi shawara cewa idan jikokinsu sun hada kai a junansu a barsu suyi
aure haka kuma masu nema a waje su ma a basu dama.


Haka suka shigo masa Zahra, Ghazalatu da Fauziyya idanunsu a kumbure suna kan kuka
ma. Awwab kuwa kallo daya yayi masa ya dauke kansa. Damuwa da bacin rai sun rufe
kyakkyawar fuskar yaro mai yawan fara'a da wasa da dariya. Anya ya yiwa 'ya'yan
Hassana da Mustapha adalci kuwa? Yara har uku yana neman tauye musu hakki akan
abinda ba addini ba. Don dai kawai Baban Biyu yana da kawaici amma ace jikokinsa
har hudu duka ya nuna shine mai ta cewa akan makomar rayuwarsu kuma nasu kakan ya
nade hannu ya kyale shi.


"Matso nan Fatima" ya yafito Zahra da hannu. A tsorace take ta tashi ta koma kusa
da kafarsa ta zauna. Ya kira Fawaz shima yazo ya zauna daga daya gefen nasa.


"Kana son auren kanwarka?"

Shiru Fawaz yayi na 'yan dakiku kafin ya girgiza kai yace baya so. Haj Azumi tayi
gajeren murmushi. Tun a gida tayi ta nanata masa idan yana son kansa da arziki kada
ya yarda a aura masa yarinyar da bata sonsa. A nasa bangaren shi dai baya kin Zahra
amma kuma ba soyayya bace tsakaninsu shiyasa bai ga amfanin aurenta ba.


Alh Baba ba haka yaso ba amma dole ya karba tunda a gaban iyayensu ake yi.

"Fatima waye shi wanda kike so din?"


Kasa magana tayi ya mayar da tambayar ga Major. Shi din ma bai wani san kan zancen
sosai ba shiyasa Awwab ya fada masa yadda suka yi da ita dazu.
"Yanzu zuri'ata zan hada da kabilu?" Yace cikin wani irin yanayi.


Baba Karami yayi saurin gyara murya "Alhaji kada mu koyawa yaran nan kin 'yan
uwansu musulmi saboda bambancin yare da al'ada. Mun sani cewa babu haramci a
tarayya dasu sai ma kara karfin alakar dake tsakanin musulmi da dan uwansa."


"Haka ne, idan mun tashi daga nan a kira shi a waya yazo da magabatansa idan yana
sonta. Daga yanzu na soke maganar aurenta da Fawaz."


Mami harda hawayen dadi. Lallai mai hakuri shi yake dafa dutse yasha romonsa. Bata
taba tunanin zata sauyi irin wannan game da auren Zahra ba sai gashi ya samu cikin
ruwan sanyi.


"Fauziyya da Bilal fa? Akwai wani korafi makamancin haka tsakaninsu?"


Bilal yaro mai tsananin kunya yace indai bata da wanda take so yana son aurenta.
Fauziyya ma bata bashi kunya ba tace ta amince. Haka ya sanya farinciki a
zukatansu.


"To uban gayya da aurensa ya janyo mana wannan tone-tone. Na baka izini Muhammad ka
nemi amincewar Ghazalatu da waccan yarinyar ayi aurenku rana daya babu wadda zata
jira wata"


Yana dire maganarsa Ghazalatu ta dago jajayen idanunta "Alhaji ina da magana"


"Ina jinki"


"Ni dai na hakura ko wani zaka zaba min zan amince amma banda Yaya Awwab"


Tsawa Daddy Haroun ya daka mata ta fashe da kuka. Tana da kishin da bata jin zata
iya zama da Radhiya da take gani kamar wata kaskantacciyar yarinya. Amma ba wannan
ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login