Showing 141001 words to 144000 words out of 295847 words
dayan ma suna ganin tsayinsa to amma tafiyar basu dauketa ta garaje ba.
Danginsu, jininsu da kaddara ta rabasu. Ya zama wajibi a garesu su yiwa wannan
tafiya shiri na musamman.
**********
Bayan sallar magariba Awwab sunyi da Ghazalatu zai je wurinta. Yana shiryawa suna
waya da Radhiya tana masa shagwaba yana biye mata. Kwankwasa masa kofa akayi tare
da sallama yana makale da wayar a kafada ya budewa Fauziyya kofar.
"Daddy yana kiranka"
Da ka ya amsa ya koma ya gama fesa turare sannan ya yiwa Radhiya sallama da sakon
gaisuwa ga Umminsa.
A dakin Daddy din ya samesu tare da Mami. Yana shiga Daddy yace mata tayi hakuri ta
basu wuri.
"Ba sai kun koreni ba na dade da sanin kuna wareni. To dadin abin ina da 'yan mata
na"
"Zahra da Fauziyya ko? Kinsan dai ko da kudi bazaki saye min Zayyanatu ba" Daddy
yace da murmushin dole saboda kwata kwata baya cikin nutsuwarsa tun jiya. Mami ta
kula kuma ta tambayeshi sau daya yace babu komai sai taja bakinta tayi shiru. Ita
ma din tana da danuwar da take dannewa bata so ta fada masa game da Zahra.
Murmushin ta mayar masa "ka manta jiya baka bata kudin kanwar amarya day ba mun
ganku a rana? Yanzu zanje na sayeta"
Bayan fitarta Daddy ya maida kallonsa ga Awwab da yake zaune a kasa daga gefen wata
duguwar kujera.
"MUHAMMAD"
Dago kai yayi da sauri saboda yadda kiran ya ratsa ko ina a jikinsa. Baya tunanin
idan ba a makaranta ba ko za'a fadawa wani sunansa Daddy yana kiransa da Muhammad
balle da irin wannan yanayi da yake nuni da babu wasa cikin maganar da zasu yi.
"Na'am Daddy"
"Meye tsakaninka da kanwarka Ghazalatu?"
Dama yayi tunanin wannan maganar ce tunda Ghazalatu tace tana tunanin Daddy Haroun
ya sani ko ma yayi zancen da Alh Baba.
"Daddy maganar aure ce"
"Awwab meyasa baka sanar dani ko mahaifiyarka ba?"
Sunkuyar da kansa yayi yana mai takaicin biye mata da yayi tun a lokacin suka boye.
Da an sani a gida zasu iya rokar alfarmar ta gama karatun kafin ayi aure tunda
shine babbar damuwarta. Haka nan dai ya sanar da Daddy dalilin boyewar tasu.
"Rashin sanin kana nemanta ya sanya nayi maka karambani. Zuwanmu Rugar Barkindo na
yiwa kakannin Radhiya alkawarin za ka aureta saboda sharadin da suka gindaya min
kenan na bani ita na dawo da ita cikinku tayi karatu."
Murmushi sosai ya ga Awwab yayi ya sake dukar da kai. Wannan ya tabbatar masa da
zancen Mami da tace tana ganin kamar yana sonta.
"Daddy nagode kuma na karba"
"Yaya zaka yi da kanwarka kuma?"
Babu kwauron baki ya fadawa mahaifinsa cewa dama ya dawo ne domin neman shawararsa
akan yadda ya kamata ya bullowa lamarin.
"Bazan wulakanta Ghazalatu saboda Alheran ba, itama kuma ko ba ni na nemeta da
kaina ba Daddy bazan bari kaji kunyar iyayenta ba"
Hakika tunani da hangen nesa irin na Awwab suna daga cikin dalilin da suka sa Major
yake matukar son yaron. Sai aka samu kyakkyawar shakuwa a tsakaninsu wadda tasa
suke shawartar juna akan abubuwa daban daban. Yaji dadin amsar dan nasa sosai amma
kuma ba abinda nasa iyayen suke so ba ne.
"Ina zaka kai mata biyu a lokaci guda?"
Cikin yanayi na damuwa yace "Daddy nima ban sani ba amma don Allah kada kace na
hakura da kowacce bazan iya ba. Dukkansu ni na kai kaina garesu kuma suka amince
min"
"Muhammad kayi hakuri da Radhiya, su Alh Baba sun ce na bawa iyayenta hakuri
Ghazalatu kadai zaka aura"
A firgici ya dago kai yana mikewa tsaye baki daya "Daddy?"
"Bana son jan zancen nan har Maminku taji. Alhaji yace a bari su gama biki to zan
jira a gama din naji hukuncin da zasu yanke. Na sanar da kai ne saboda idan da
gaske ka fara neman Radhiya ka janye. Bana son ka cigaba da sa mata rai har sai na
gama iya kokarina akan neman amincewarsu ka hada biyun"
Gumi ne sosai ya soma wankewa Awwab fuska. Idan zai iya hakura da Alheran dinsa
tabbas zai iya hakura da aure baki daya. Gurfana yayi a gaban Major kamar mai rokon
gafara.
"Don Allah Daddy kasa baki wallahi zan iya aurensu su duka."
"Tashi kaje dama yace yana nemanka idan ka dawo. Ka yawaita addu'ar zabin Allah"
Jikinsa sam babu kwari haka ya fita kamar mara lafiya. Mami tana kallon fitarsa
Zahra na yi masa magana bai ma san tana yi ba. Jikinta itama sai yayi sanyi. Tabbas
akwai abinda yake faruwa wanda Daddy baya son ta sani. To ko ya gane abinda take
boyewa na Zahra ne? Kai da wahala tace a ranta tana girgiza kai. Zahra bazata taba
fada ba ta sani. Kallon yarinyar tayi a zaune bayan fitar Awwab bai kulata ba tayi
shiru. Zuciyarta ce tayi mata nauyi ta rasa da wa zata yi maganar nan ta saukewa
kanta nauyi. Fitarta kuma ba karamar illa zai iya janyowa zumunci ba. Shirun dai da
ta yi kuma ta roki Zahra da tayi itama shine take ganin kamar zai zame musu
maslaha.
Kafin ya isa gidan Alh Baba missed calls din Ghazalatu sun kai goma. Kiransa take
tun yana wurin Daddy tana masa tuni akan shiru da ta ji. Ransa gabadaya a cunkushe
ya shiga ya gaishe da Mummy kafin ya fito da niyar gaisawa da kakaninsu mata.
"Yayana ka bari sai zaka tafi kaje. Yanzu cinye mana lokacin hira zasuyi"
"Kinfi so dare yayi sosai lokacin na shiga sunyi bacci? Ba dadewa zanyi ba"
"Daddy yace in fada maka kaje wurin Alh Baba shima yana son ganinka. Ni duk za'a
cinye min lokacina"
Murmushi yayi duk don ya nuna mata komai lafiya "My G baki da dama, yanzu su
Alhajin ne masu cinye miki lokaci?"
Tana ta tura baki suka shiga wajen matan Alhajin daga nan ta bishi falonsa. Sun
gaisa yayi masa barka da dawowa shi kuma Alhajin ya bashi karamar robar zamzam da
dabino ya karba da godiya. Ganinsu da yayi da jikar tasa ya faranta masa rai sosai.
A son ransa zuri'arsu suyi ta auren junansu yadda za'a sami hadin kai mai dorewa
har jikoki.
"Dan bamu wuri zanyi magana da yayanki Ghazalatu"
Shikenan za'a sake ci mata lokaci ta ayyana a ranta. Zaman da tayi don ta sami
damar fita dashi ne kada Alh Baba ya dauko doguwar hira a tsakaninsu. Iyakarta
bakin kofa ta makale daga gefe da zummar idan taji hirar zata yi tsayi ta koma tace
ana kiransa. Abinda taji Alh Baba yana cewa ne yasa ta sake matsowa sosai don taji
da kyau.
"Munyi magana da iyayenku jiya. Naji dadi kwarai da kuka hada kai da kanwarka. Kuma
na yanke cewa ayi auren nan da wata uku. Ina fata zaka iya shiryawa kafin nan."
Wani tsalle Ghazalatu ta daka daga inda take. Awwab godiya yayi masa sosai yana
murmushi.
"Sai dai Mustapha ya kawo wani hanzari na cewa ya nema maka auren yarinyar abokinsa
batare da sanin kana neman Ghazalatu ba"
Gabanta taji ya fadi don ta sani babu wadda ake nufi ko da ba'a ambaci suna ba sai
Radhiya yarinyar nan mai kwalkwalin kai.
Kansa a kasa cike da ladabi Awwab yace "hakane Alhaji"
Tsohon ya gyara zamansa yana kallon jikan nasa "tun a jiyan na fada masa sai a basu
hakuri tunda kana da wadda kake so bai kyautu ace sai ka aureta ba. Ni a tsarina ma
Allah Ya gani nafi son ku rinka auren junanku. Ita idan aurenta ya tashi sai yayi
mata duk abinda uba yake yiwa 'yarsa"
Wannan shine son kai. Babu yadda za'ayi Awwab yayi shiru da wannan magana ya karbi
hukuncin Alh Baba batare da ya gabatar masa da nasa uzurin ba.
"Alhaji kayi min izini na auresu su biyu. Ina iya fara auren Ghazalatu sai na
aureta daga baya"
Rai a bace ya soma fada "abinda uban naka ya turoka ka fada min kenan. Wato saboda
jiya nace ban yarda ba shine kai ka shafawa idonka toka zaka yi min rashin kunya?"
"Alhaji kayi hakuri ba haka bane"
"To nace na soke bazaka aureta ba. Banda son dorawa kai wahala ina zaka kai mata
biyu Muhammad? Idan kana son yiwa mahaifinka biyayya ne kaje abinka shima ai
karkashina yake"
Ran Awwab sai kuna yake ya kasa daurewa "Alhaji wallahi ina sonta"
Kallon da Alh Baba ya watsa masa a lokacin kallo ne na tsananin bacin rai.
Ghazalatu da ta gama jin komai hankalinta bai tashi sosai ba sai da taji furucin
Awwab. Kuka ta fashe dashi ga bakinciki ga kishi ta bar wurin a guje. Daga Alhajin
har Awwab sun jiyo muryarta.
"Ka tashi kabi sawun kanwarka ku daidaita. Na gama magana Muhammad bana son sake
jin wata magana"
"Alhaji...."
"Ka tashi ka tafi nace"
Yana fita daga falon waje ya nufa ya shiga mota ya kifa kai akan sitiyari.
"Ya Allah" ya furta a hankali ko ina na jikinsa yana cikin tashin hankali. Bazai
taba iya hakura ko rabuwa da Alheran ba. Ya barta a kira shi da me? Butulu ko
mayaudari? A cikin abinda bai gaza sati biyu ba ya fada matsananciyar soyayyarta
kuma itama ya koya mata sonsa. Akwai kunya da nauyi sosai tsakanin iyayensu wanda
bai cancanci a sanadiyarsa ya kawo wata baraka a tsakani ba kamar yadda baya fatan
kawo baraka ga danginsa. Shi da Ghazalatu sunyi dumu dumu a cikin dangi. Idan baka
dubesu ta nan ba zaka dubesu ta can. Hadi ne tun daga kakanni an cakude da juna.
Dakin mahaifiyarta Mummy Gambo ta wuce kai tsaye tana kuka kamar ranta zai fita.
Babu abinda yake mata yawo a ka sai jin da tayi Awwab da bakinsa yace yana son
wannan yarinyar.
Mummy ta taso ta tarbeta da sauri "me ya sameki?"
"Mummy Yaya ne...Yaya Awwab baya sona"
"Ban gane ba, idan wani shirmen fadanku ne dama kada ki soma gaya min. Kije can ku
sasanta"
"Mummy wata yake so. Yaci amanata wallahi 'yar wannan makauniyar da ta zauna
gidansu yake so"
Nata hankalin sai yafi na Ghazalatu tashi "dena kuka bari na kira Hassana naji daga
bakinta."
Mami tana daki da Zahra wadda take ta kuka tana bata hakuri Mummy ta kira. Shawara
ta yanke gara ta sanar da ita ko Hussaina su tayata bawa Zahra baki.
Sai da ta saita muryarta don ita din ma zuciyarta a karye take "Mummyn yara yanzu
kuwa nake shirin nemanki."
"Kina shirin nemana ki fada min kun yiwa Awwab mata ko" tace cikin gatse.
Mami da bata san wainar da ake toyawa ba tayi dariya "hala yazo ya fada miki. 'Yar
wajen Mairama ce. Kin ganeta ai wadda tazo ta kwana mana biyu matar ....."
Kit taji shiru Mummy ta kashe wayar. Kallon wayar hannunta tayi da mamaki sai kuma
ta soma kiranta missed calls biyar bata dauka. Abin ya dameta ta lallaba Zahra ta
fita ta tafi dakin Daddy.
Mummy Gambo ta cika tayi fam. Ita Mami zata wulakantawa 'ya har tana fada mata
wadda suka zabawa Awwab. Kenan basu aminta da ya auri Ghazalatu ba. A tunaninta
tafi karfin haka a wurin 'yar uwarta ta. Kallon Ghazakatu tayi da take ta kuka tana
rarrashinta ta kira Daddy Haroun a waya don ya fita unguwa. Cewa tayi kawai ya dawo
gida babu lafiya yace to.
Mami tana zuwa dakin Daddy shi kuma ta same shi yana waya da Alh Baba yana ta ban
hakuri. Alh Baba yace ya fadawa Awwab lallai aurensa da Ghazalatu babu fashi. Wurgi
ta ga yayi da wayarsa ta karaso kusa dashi da sauri.
"Daddy lafiya?"
"Ki bari muyi maganar nan bayan bikin su Fauziyya kamar yadda Alh Baba yace"
"Wallahi hankalina ya tashi. Tun jiya ka chanja min gabaki daya. Yanzu Gambo ta
kirani tana cewa munyiwa Awwab mata nace mata eh kawai ta kashe wayar kamar wadda
na yiwa wani abu"
Ran Major tuni ya soma baci kuwa. Yasan Gambo da masifa amma baya son duk abinda
zai sosa ran Mami. Ga dadin haushin akan 'yarta ne ake son kirikiri a gwada son
kai. Meye matsalar ya auri mata biyu da za'a ce dole sai an janye maganar Radhiya.
Radhiya diyar Zayyanunsa.
Sallamar Awwab din suka rinka ji kana jinsa kasan baya cikin nutsuwa. Izinin
shigowa Daddy yayi masa yana zuwa ya zube masa.
"Daddy Alh Baba yace bazan auri Alheran ba. To wallahi idan bai amince ba itama
Ghazalatun na rantse da Allah ko an daura sai na saketa"
"Kai Awwab, kana cikin hankalinka kuwa? Daddy me yake faruwa ne kun kara sakani
cikin duhu"
"Fita ka tafi dakinka" Daddy yace ransa shima a baci. Dakin gabadaya ya juye
walwalar ma'abotansa ta fi kamar an kadata da iska.
Tattaro nutsuwarsa ya daure yayi ya fadawa Mami halin da ake ciki. Boyewar bata da
amfani tunda Gambo ta sani.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yanzu sai Gambo ta ga kamar da gangan nayi"
"Gambo kike ji ko kuwa halin da Awwab zai shiga da yaran nan"
"Daddy ni fa ban ga wata gagarumar matsala a cikin wannan abu ba. Awwab namiji ne
saboda haka zai iya aurensu duka. Ciki mu mun isa muce ga wadda zai zaba ya bar
dayar? Babu wadda mahaifinta baiyi mana halacci ba saboda haka ka kwantar da
hankalinka in sha Allahu komai zai zo da sauki"
A sanyaye yace "Alh Baba yace bazai auri mata biyu ba kuma su Baba sun amince"
Kanta ta dora akan kafadarsa ta kwantar da murya domin kwantar masa da hankali "mu
bi komai a sannu saboda kuskure daya zai iya janyo mana rikici a dangi ko tare da
iyayen Mairama wanda bana fata. Gobe muje mu roki arzikin suyi hakuri su amince ya
auresu su biyun"
Kalamai masu kwantar da hankali ta rinka amfani dasu wurin sanyayawa mijinta rai
suka dauki dogon lokaci suna shawara akan wannan matsala.
Tunda Awwab ya shiga daki bai fito ba sai asuba. Kallo daya Major yayi masa ya san
cewa da wahala idan ya runtsa. Soyayyar Awwab da Alheran daga Allah ce. Ya tabbatar
duk wannan tashin hankalin saboda an hanashi aurenta ne.
**********
Da wuri aka gama komai na sallamar Ummi daga asibiti. Abin da mamaki matuka ta
shafe shekaru kusan goma da makanta yau ita ce take da idanun kallon Radhiya da
Karami. Bayan an bata gilashinta tana kallonsu ta fashe da kuka. Karami bai baro
mahaifinsa da komai ba sai fari da ya dan dara shi wanda ta alakanta shi da
kuruciyarsa sai kuma tsaho da shi Zayyan din yafi dan nasa. Radhiya kuwa tafi dauko
kamanni da ita sai dai ta rasa inda ta samo wannan kirar jiki. Mairama doguwa ce
siririya mai kyaun sura da daukar ido yayin da Radhiya take a murje babu rama amma
baza'a a kirata mai kiba ba. Jikinta a cike yake ko ta ina. Yanayin hancinta sam
baiyi kama da na Umminta ko mahaifinta ba. Idan tayi murmushi sai kaji kamar ka
dauketa saboda yadda fuskar take nuna zallan yarinta idan kumatunta ya lotsa ciki.
Lokacin da suka hada ido da Zainab sai sabon kuka.
"Haka kika koma wata 'yar gayu Zainab dina"
Yaran suna dariya iyayensu suka rungume juna.
"Muje gida kafin ki bar garin nan sai kin zama 'yar gayu kema. Ba biki zakuyi
ba....hmmm Allah Mairama sai nasa idanu sun koma kanki a wurin bikin nan" suka yi
dariya.
A gaban mota Ummi ta zauna Radhiya da Nene Marka suna baya. 'Yan samari kuwa
adaidaita sahu tace su shiga su biyo bayansu.
Sunje gida Ummi ido ya bude ta ga halin da Baba Hadir yake ciki. Tana kuka Zainab
tace mata kada ta jangwalo idanun tayi hakuri haka.
Motsi kadan Radhiya sai ta kalli wayarta babu kiran Awwab. Yadda baiyi bacci ba
jiya yau ma hankalinsa gabadaya ya tashi ne saboda rigimar dake neman kunno kai a
gidansu. Mami da Daddy sunje har gidan Alh Baba akan ya duba lamarin wanda zuwan
nasu ya sake harzuka shi. Mummy da ta sami labari ko kallon arziki ta kasa yiwa
yayarta. Ga Ghazalatu ta kwana kuka kuma tsabar wulakanci ko aurenta ba'ayi ba ace
suna rokon a auro harda wata. Domin su tsayar da abin haka suka yanke shawarar bari
a fara bikin da Ghazalatu. Idan yaso bayan ko da rabin shekara ne Daddy zai sake
yiwa su Alh Baba maganar. Kwanaki biyu suka yi ana wannan tashin tashina.
A Kano kuma Mama ta bude wuta wurin gyara 'yar uwarta Ummi da 'yarta Radhiya. Salon
ta kai Mairama da aka gama gyara kan akayi steaming sai ta sake komawa yarinya
kyaunta ya kuma bayyana. Radhiya ganin Umminta a steamer harda kuka wai ita ya
kamata a yiwa wannan gyaran amma saboda Innawuro bata sonta gashi yanzu tana ji
tana gani babu damar shiga. Mai salon taji sai mita take tana fulatanci tana hausa
ana ta kiran Innuwuro tace mata tazo ta shiga.
"Soya min fatar kai zaki yi ko"
Matar tayi dariya "gyara dai kanwata"
Bisa tsautsayi ta tuge dankwalin Radhiya wai zata yi mata gyara kyauta sai abin
arziki ya bayyana kowa ya gani. Allah Yasa kan ya hade yayi baki sidik gashi ya
soma tofowa. Amma duk da haka ranta ya baci ta tashi ta hade fuska tana kallon
matan da ake yiwa gyara.
"Yasin mace tayi dariya in rangada mata balotelli ta tafi dashi gida"
Kana ganinta kasan ko bata aikata ba to dai zasu ji ba dadi. Mai salon ta koma bata
hakuri sannan tace tazo tayi mata gyaran farcen hannu da kafa da steaming din
fuska. Shikenan ta manta da fushin ta shiga jerin gyara tana ta firirita yau gata a
salon. Kafin su bar wurin tasa mata da yawa dariya.
Washegari ana gobe zasu tafi mai kunshi tazo ta rangada musu baki da ja. Ummi dai
safa ta saka a kafarta tana jin wani iri. Rabonta da ado haka tun Zayyan bai tafi
Liberia ba. Yanzu kam wa zata yiwa. Nene kuwa sai zuga Mama take yi wai a gyare
mata 'yarta ta samo miji dan ubansu.
Radhiya da Emzee suka taru suka rafka mata uwar harara sai da Mama ta hade
kawunansu ta gwara.
"Nenenmu kuke harara"
"Mama wai miji fa take cewa, Ummi ke da aure sai a aljanna ke da babanmu" Emzee
yace da dukkan seriousness.
"Maza iyayen kishi" Mama tace tana tuna lokutan da Ibrahim yake yi mata kunkuni
akan me yasa ta tafi tabar babansa.
Ranar wuni suka yi ana ta gyare gyare saboda tafiyar su Mama da ta matso kusa
sosai. Ibrahim zai koma gidan kakaninsa ya jira dawowarsu. Da safe ta kaisu tasha.
Nene tayi ta yi musu addu'a ita da iyalinta tana fatan Allah Yasa a dace mijinta ya
sami lafiya ya dawo da kafafunsa. Kamar kar su rabu ita da Ummi. Emzee ma dai dokin
budewar idanun Ummi yasa zai bisu Sumaila. Ba don haka ba jira zaiyi sai sun tashi
nan da kwana biyu sannan ya koma.
Sai da suka tashi Mama ta koma gida tare da Ibrahim mai nuna hanya. Suna isa Aisha
'yar wajen Alh Musa ta kirata. Sun gaisa da ita da kanwarta tace mata ga Mamansu su
gaisa. Matar mai mutumci suka gaisa da tambayar juna iyali.
"Antin yara na bugo ne nayi miki godiya irin dawainiyar da kika sha da yaran nan.
Na dawo gidansu biki ya matso babu abinda baki saya kin ajiye ba. Don Allah ina
rokon mu cigaba da zumunci."
"In sha Allahu. Nagode"
"Ina fata kuma zaki zo bikin 'ya'yan naki"
"Ahhh banyi alkawari ba."
Nunawa tayi bata ji dadi ba har tana tambayarta ko don sun rabu da Alh Musa ne.
Mama tayi dariya tace