Showing 60001 words to 63000 words out of 295847 words

Chapter 21 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

ajiye
a tsakar gidan. Bishiyar tana kada musu iska daidai gwargwado aka zauna mayar da
zancen yadda kowa yayi rayuwarsa bayan rabuwa. Wannan karon Innawuro ce ta cewa
yaran su tafi gidan Baffa Gide saboda kula da tayi hirar tasu mai taba zuciya ce.


Radhiya tace su taho kowa ya tashi kamar gaske. Suna fita bakin kofar Zayyana tace
da Fauziyya "nan gidan basu da wurin da zamu buya"


"A buya kuma, kunyi gamo ne a hanya?" Radhiya ta tambaya tana waige.


Murmushi Zahra tayi yanzu an girma suna jin kunya. Ibrahim kuwa sai yace "kinga
magana zasuyi mai mahimmanci idan bamu tsaya munji ba wallahi za'ayi ba mu"


Haba Radhiya ta rike tana jinjina kai "Allah ko? To amma zunubin laben wa za'a
rubutawa a cikinmu? Ni dai shekarata goma sha tara da sauran kuruciyata."


Fauziya da Zahra har Ibrahim sai dariya. Emzee da ya saba shi kam bai ga komai ba.
Salati suka ji Inmawuro tayi da karfi tana kuka gabadayansu babu babba babu yaro
suka dawo suka tsaya a siririyar hanyar karasa shiga cikin gidan. Duhu da girman
maganganun suka hana a gano su.
Duk da sun ji yadda iyalin Major da na Hadir suka kare a Kano bai hanasu sake
kokawa iyayensu ba. Jin labarin da Mairama ta bayar a karon farko a rayuwarta ta
fadi yanayin zaman gidan mahaifinta. Tayi haka ba don ta tona masa asiri ba sai don
su Mami su fahimci ainihin yadda al'amura suka kasance mata. Ga wanda bai san
Malamijo ba sai a suna bazaka taba hangowa jikokinsa ma talauci da kuncin rayuwa
ba. Dabbobinsa tarin arziki ne da shi kansa bai san dashi ba. Ko shanu ashirin ya
sayar a yadda suke da girma kosassu zai iya ajiye abincin shekara a gidansa kuma su
wadata da abubuwa da dama da bai taba tunanin ya basu ba.


"Abinda ban fahimta ba Ummin Awwab shin gidan da Zayyan ya gina a Kano me ya faru
dashi?" Major ya tambayeta


Jan numfashi Hadir yayi da karfi sai da suka kalle shi. Rashin damar bawa Mairama
takardun nan kusan shine ya haddasa masa hawan jini. Bai ma san ko Zayyan ya bata
na wurinsa ba. Shi dai burinsa wadda aka bashi ajiya ya sadar da ita ga masu
hakkinta. Takardun suna cikin wani akwatinsa da yake tunanin babu wanda ya taba
bude shi tunda ya koma gida.


A nutse ta warware musu komai da ya wakana tsakaninta da Maikudi. Kunya kuwa ta
kama Badaru kamar ya bace daga wurin saboda abinda yayansa ya aikawa matar kaninsu.


Major rai ya kara baci ba don duhu ba sai an ga jijiyoyin kansa da suka dago.


Mami tace "Wallahi mutumin nan sai munyi da gaske. Ta kowace fuska da zai toshe
miki jindadi sai da yabi. Mu fa aure yace kinyi kuma baki haifi dan cikinki da rai
ba sannan Radhiya tana hannunsa shine muke aikata mata kudin makaranta ta hannunsa"


"Banten uba" Radhiya tace a harzuke tana kumfar baka daga inda suke tsaye. Hanyar
shiga ciki tayi Emzee da Zahra suka rikota.


Idanu sun rufe ta shiga kokawar fuzgewa "ku cikani"


Zainab suka gani a gabansu suna sunkuyar da kai kasa tace duk su dawo su zauna
tunda annobar labe ta kamasu.


"Ban hanaki wannan zagin ba" Mairama tace da Radhiya cikin fada.


"Ai wallahi Ummi sai dai fa kiyi hakuri yau daya dai. Hmmm gaya miki ne banyi ba da
idan munje hutu fa duk inda ya ganni sai ya rankwasheni ko ya makeni. Inata hakuri,
inata hakuri. Wata rana yana rankwashina na tafi a gabansa na dauki Bushira lokacin
tana karama na maka ta da kasa. Shine fa ya dena dukana. Yo ashe harda ke bai kyale
ba"


"Ya isa haka Radhiya kiyi hakuri tunda magana ta fito ba zamu bar masa hakkin
marayu ba" Mami tace da sigar lallashi.
"Uhmhum" kawai ta amsa ba don ta hakura ba.


Badaru ya ari baki ya basu hakuri sannan ya kara da cewa "dole ne na sake neman su
mutanen Nijar din. Bana yi musu zaton wadanda rasuwar Zayyan zata sanya su watsar
da iyalinsa. Allah Yasa su din ma ba wani abin yaje ya fada musu ba. Don ni yanzu
lamarin nasa ya fara bani tsoro kuma."


Sunje sunyi sallar isha sun dawo sai ga yara biyar suka shigo gidan a tare rike da
kwanukan abinci. Biyu yaran babban dan Innawuro ne sauran ukun kuma na mai binsa
mace. Tun a masallaci lokacin Magariba Ardo ya sanar da dan nasa da kuma mijin 'yar
suna da baki ayi abinci na gani na fada.


Farantai da cokula Radhiya ta dauko sai ruwan sanyi da aka aiki Emzee ya siyo a
wani shago daga bakin titi Ibrahim ya bishi.


Anci an sha hira taki karewa Innawuro ta sa Radhiya da Emzee tayata gyaran dakunan
saukar baki. Su Mami da ko baa fada ba da Mairama zasu kwana. Badaru, Major da
Hadir Baffa Gide yazo ya tafi dasu gidansa. Ibrahim da Emzee a dakin Emzee din da
yake daga hanyar waje. Sai 'yan matan su hudu a dakin Innawuro. Dreban da ya kawo
su shima an sama masa masauki.


Da asuba kaji goma aka yanka domin yi musu abincin safe. A gaban Hadir Major ya
fadawa su Baffa da Ardo cewar auren su Zahra ya matsu suna neman izini su tafi da
su Mairama zuwa bayan biki. Radhiya da Zayyan kuma a bar masa su zai nema musu
makaranta su fara jami'a a.


"A yi haka kuwa?" Baffa Gide yace yana kallon Ardo "a son ranmu dai suyi zamansu da
yaran a tare damu har Allah Yasa duka suyi aure."


"Abinda baffanta Gide ya fada gaskiya ne. Ita ga matsalar idanu ga marayunta gara
suna tare damu. Lokaci lokaci idan kun bukaci su zo su kwanan muku biyu sai a turo
su"


Ransa dama ya bashi da wahala kai tsaye su bari ya daukesu. Sai dai kam yaci
alwashin bazai yarda alkawarin da ya daukarwa kansa na cigaba da kula da bayan
Zayyan ya tashi ba.


Sauran labarin da ya kasa bayyanawa jiya na ainihin yadda Zayyan ya rasu ya fada
musu. Baffa Habubakari sai da yayi kuka don tausayi.


Cikin damuwa da fami ga gyambon zuciyarsa yace "Bazan taba iya kallon idanun
matarsa in bata wannan mummunan labari ba. Tana da hakuri amma ina ganin sai ta
tsaneni da iyalina. Yau da nake raye ku ke ganina Allah ne Yayi da sauran kwana na
amma Zayyan shine sila."


Ya nuna Hadir "wannan bawan Allah da lafiya kalau yake wallahi kunji na rantse
zaiyi komai don ganin 'ya'yan Zayyan sun koma karkashin kulawarsa. Sai dai shima
lalura ta same shi ne da ya cigaba da kokarin kare rayuwata kamar yadda dan uwansa
ya fara. Ku taimaka ku barni na kyautatawa bayan Zayyan sannan kuma na saukewa
Hadir nauyin da nasan da yana da lafiya bazai taba bari na dauka ba"


Jikkunansu sunyi sanyi da maganganun Major. Ardo ya kira Innawuro yace "kece uwar
Mairama kakar 'ya'yanta me zaki ce game da batun da bawan Allahn nan yazo dashi?"


Nazari Innawuro ta soma don abun da yake nema ba karami bane. Mairaman da
mahaifinta ya gagara rikewa, dan uwan tsohon mijinta ya tozarta ta yaya zasuyi
saurin amincewa bare. Idan a gaba gori ya taso ko wani abu makamancinsa fa.
Bafillatani duk talaucinsa akwai pride. Basa son zubar da mutumcinsu gaban kowa
saboda babu azo aji dadin takasu.


"To na amince amma Zayyanu kadai zaku dauka. Dalili kuwa kun dai ga irin halin 'Yar
Soja wallahi zama da ita akwai dadi akwai wuya. Mairama kuwa bana son nisa da 'yata
ko kadan."


Hadir ya kafe Major da ido har ya fahimci so yake ya cigaba da rokonsu. Ai kuwa bai
fasa ba yana ta kawo hujjoji.


"Kayi hakuri amma indai ka ga 'Yar soja ta bar garin nan to aure ne ya dauketa"
Innawuro tace don ta kawo karshen muhawarar.


"Na ji na amince" Major ya amsa batare da dogon nazari ba.


Baffa Gide ya kalle shi da mamaki "kada kace min aurenta zakayi."


Mafita daya ya hango ya kuwa yi amfani da ita "a'a , akwai babban dana Awwab shine
nake son aurawa. Dreban jirgin sama ne yana bakin aiki shiyasa bamu zo tare ba."


"Lallai da gaske kake, amma bana so ka cuci yaronka da auren dole don a baka
yarinya. Kasan yanayin zamani"


"Na sani amma ina da yakinin bazai bani kunya ba. Don Allah ku amince. Yanzu ku
bari mu tafi dasu har Sakkwato saboda wancan wan Zayyan din. Sai kuma danginsu na
uwa dake Nijar su ma ina so na hadasu kafin nan da lokacin bikin"


Tsakaninsu da Allah basu da niyar hana shi yaran ko kadan sai dai magana ta gaskiya
sunyi masa haka ne domin kada nan gaba a raina musu. Da mutumcinsu da rufin
asirinsu ya nemi daukar yaran ba wai talauci ko maula ya kaisu ba. Sun kara
jinjinawa Marigayi Zayyan domin wannan abu halinsa na kwarai ne ya kawo haka. Idan
akwai wani abu na bajinta a rayuwar Mairama da Malamijo ya taba yi bai wuce aura
mata dan kwarai irin albarka Zayyan Muhammad Tureta ba.


Innawuro da kanta ta fada musu su hada kaya zasu tafi tare suyi musu kwanaki don
kowa ya sani hirar jiya da wadda aka sake dorawa yau tayi kadan ta cike gurbin
shekarun da suka yi basa tare.
Radhiya sai murna nan da nan ta shiga jibgar kaya. Zainab ta ja ta gefe tace mata
ta debi kamar biyar biyar nata da na Mairama.


"Ni fa na zaci kuna sonmu ne sosai baza ku so muyi kwana kadan ba mu dawo"


Tunda suka farka suke cin dariyar Radhiya ashe abin bai kare ba.


"Mu kuwa muke son ku Radhiya, ko nima 'Yar sojan zan fara fada ne"z


Turo baki tayi "to meyasa kika ce na debi kayan 'yan kadan?"


"Kinga muna zuwa zan sa a kaiku wurin tela ayi muku dinkuna masu kyau. Ko da
wadannan kayan zaki je bikin Zahra da Fauziyya da za'ayi karshen wata mai zuwa?"


Dariya Radhiya tayi kumatunta na dama ya lotsa.


"To gidan wa zamu fara zuwa?"


"Gidana mana"


Mami da take tahowa daga bayansu ta rike baki "sannu maman yara, ashe wayo kike
shirin yi min. To ban yarda ba Katsina zamu wuce"


Zainab ta mairaice "habaaa Mami, mu da zamu zo biki muyi kwanaki. Ki bari a ya da
zango a Kano don Allah"


Mairama suka tambaya ina take son fara zuwa tayi murmushi "duk inda mota ta fara
tsayawa zan sauka ne."


Ta kashe bakin nasu ta barsu da muhawararsu. Wayar Mami aka kira tana dubawa ta ga
Awwab ne. Dariya tayi don jiya yayi ta kira bata sani ba. Tana dagawa a kunnen
Mairama ta manna wayar.


Ko gaisuwa baiyi ba ya fara mita "Kai Mami tun jiya nake kira ki bani Ummi mu gaisa
kinki dauka."


"To Allah Ya huci zuciyarka dan Ummi"


"La ila ha illallahu Ummi kece?" yace yana mai farincikin sake jin muryarta.


"Nice Awwab, yaya aiki?"
"Lafiya kalau, kinga sun taho sun barni ko"


"Kayi hakuri, kana dawowa zaka ganmu in sha Allah"


"Ummi ina Alheran?"


"Tana can wurinsu Zahra tana damunsu da surutu"


Dariya yayi yana imagining yaya ta koma yanzu "ta dena fada ko?"


"Awwab kenan baka manta halin nata ba ashe. Sai kazo zaka ganewa kanka."


"To Ummi don Allah kice Mami ta turo min numbar da zan rinka samunki. Ki gaishe min
da Alheran"


Mami ta bawa wayar ya shiga tambayarta wai yaya girman Alheran yake yanzu don
tsaraba yake son yi musu ita da Umminsa, Anti Zainab da Ibrahim.


"Kai kana fa da wani kanin Zayyan sunansa. Dama mun rabu Ummin taka ta kusa
haihuwa"


Mamaki da jindadi suka baibaye shi nan yayi musu sallama zai fita. Suma aka gama
shiri suka rankaya sai Katsinan Dikko.


**********


Mairama ta rasa wa zata goyi baya tsakanin Mami da Zainab. Gobe su Zainab zasu koma
Kano bayan sun zo sunyi kwanaki uku a Katsina. Gidan kullum cikin hayaniya yake sun
taru sun gama gyara shi an saka komai a muhallinsa.


"Gaskiya Mami wannan fa amfani da girmanki kike yi kina yi min wayo. Ki bar min
'yan matan nan muje suyi sati. Aure fa zasu yi ina ni ina sake cewa su zo su kwanar
min"


"Ai ban hanaki ba, Radhiya ce na hana"


"Ummin Awwab kice wani abu mana"


"Ni ban san yaushe kuka koma haka ba. Ina nan bacci zanyi wadda tayi nasara ta
tasheni. Idan zama ne na zauna. Idan kuma Kano ce tayi kira a hada min kaya"


Dariya ta basu daga baya dai an yanke Zainab zata tafi da 'yan mata kuma mazan ma
ko don Hadir dole su bita. Mairama ce zata rage tare da Mami.


Taron mata ne a kitchen su Zahra na girki Radhiya na koyo.


"Kunsan nima mai aikacin asibiti zan aura a Bauchi zan zauna. Gara na koya kada aji
kunya wata rana"


Emzee da yake shan ruwa sai da ya kware da yaji me take cewa "Adda saurayi gareki
bamu sani ba?"


Daure fuska tayi zai bata kunya a gaban mutane "fata nagari lamiri yaro...meye aibu
don nayi fatan auren likita?"


Ibrahim ya rinka mata wani kallo kafin yasa dariya "na gama harbo jirgin naki. Wato
dai wani ma aikacin asibiti kike so"


"Hhhhhh Adda Kawu Zakari kike so hala? Shi kadai na sani a asibiti"


Yadda tayi da fuska ya karasa fallasata. Suka taru ana tsokanarta, Emzee yace
wannan labari duk rugar Barkindo sai ya tona.


Tun tana da bakin ramawa ta gaji ta watsar ta fita ta koma daki. Zayyana ta samu
tana busar da gashinta da ta wanke da hand dryer. Sai ta dena fushin hankalinta
yayi gaba.


"Shi kuma wannan ya sunansa Zayyana?"


"Hand dryer, kema ki wanke kanki sai na busar miki. Mai kitso zata zo an turota
daga gidan Alh Baba"


Tsit Radhiya tayi kamar ruwa ya cinyeta. Zayyana tayi tayi tace bazata wanke ba
kanta babu datti.


Da su Fauziyya suka shigo Zayyana ta fada musu. Radhiya ta galla mata harara "kinga
ki fita idona, ina ruwanki don naki wankewa ba kaina bane?"


Zayyana ta mike a fusace ta fita "kuma sai na fadaki da Daddy"


"Sannu shasshaka uwar narkewa, shagwabar nan nima na iya. Kuma bazan wanke kan ba"


"Dama masu gashi bakwa son bude kai fa. Shiyasa kullum kina cikin hijabi" inji
Fauziyya.
Zayyana kuwa tana kai karar Radhiya wurin Daddy ashe Mairama ta jiyo yana cewa a
fada mata yace ta wanke shi zai bada kudin kitson. Idan kuma taki wankewa a gida
zai bada kudin salon.


"Daddy fada fa zaka yi mata, kara na kawo"


"Yi hakuri Zayyana ai ko ni bazan taba Alheran ba."


Harda guntun hawayenta tace "kafi sonta akaina"


Ibrahim yana gefensu yace "Daddy ka barni na dan saita yarinyar nan mana."


"Taron dangi zaku yiwa auta. To a kira min Alheran yau sai an wanke kan nan"


Mairama tana ji ta tabo Mami "taimaka ki hana wankin kan nan wallahi idan suka bude
mata kai gidan nan yau ba lafiya"


Mami ta tashi da sauri duk da bata san ko meye matsalar ba. Tana zuwa Zayyana ta
kai rahoton Daddy. Dama su Zahra sun matsu su ga gashinta saboda na Mairama da suke
gani mai tsaho sosai.


Duk sun dauki abin nata wasa suka danneta aka cire dankwalin suna cewa yau sai sun
ga gashin da take boyewa.


**********


Shiri Awwab yake da sauri sauri yau kadai yake da damar fita yayi sayayyar da zaiyi
gobe ya taho Nigeria. Tun dare yake tunanin me zai saya ya kai musu ya rasa. Ba
sabawa yayi da irin wannan abubuwan na mata yayi ba. Dan tunani yayi ya dauki waya
ya kira wadda yasan za ta bashi shawara mai kyau. Ringing biyu ta dauka kamar jira
take dama. A shagwabe ta soma magana tana korafin rashin kiranta da yayi har na
kwana biyu.


"Sorry my G aiki ne"


"Lokacin aiki daban nawa ma daban" Ghazalatu ta sake narke masa.


"Naji nayi laifi shiyasa ma ticket din Abuja na saya don na fara ganinki kafin na
wuce gida"


Ihun da tayi sai da ya cire wayar daga kunnensa yana dariya. Yana matukar son
Ghazalatu. Ita ta nemi su boye soyayyarsu ma sai ta gama degree dinta idan ba haka
ba aure za'ayi mata a gida ta sani. Yanzu wata biyu da yin final exam bautar kasa
take jira. Sun gama tsarinsu idan Awwab ya dawo zasu gabatarwa da iyayensu da
abinda ke tsakaninsu.
Sun taba hira don ta dena fushin tunda taji zai taho washegari.


"G albishirinki"


"Goro kyakkyawa kamar Yayana"


"Su Mami sun je gidan Ummin nan nawa da nake baki labari"


Yadda taji yana murna dole ta taya shi ba don ta damu ba. Yayi ta fada mata ashe
harda kani an yiwa Alheran.


"Na tayaka murna, zan so ganinta gaskiya"


"Ki bini Katsina mana idan na zo"


Dadi taji tayi saurin amincewa. Awwab bai kyaleta ba yace "kune sarakan tsaraba, me
kike ganin zai dace da yarinya about 18 to 19 years"


"Friend kayi mace har kake fada min za kayi mata siyayya?" Tace cikin fushi da
kishi.


"Nope, Alheran nake son sayawa wani abu"


Duk da haka ranta baiyi mata dadi ba amma bata son bata masa rai yanzu sai yace ya
fasa tsayawa a Abujan.


"Ka saya mata takalmi, jaka, turare, kayan kwalliya da jewelleries"


Yaji kayan da yawa to amma so yake ya yi musu abin bajinta "thanks dear" yace da
Ghazalatu kafin ya ajiye wayar.
[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 22. Iyakar karfinta tasa suna jan hijabin nata su ma
suna ja. Mami na isowa tace su dagata amma an makara don Zahra tayi nasarar cire
dankwalin.


Emzee da Ibrahim suna bakin kofa don sun jiyo hayaniya daga dakin. Rasa me bakin
magana akayi harda Mami kuwa. Zainab ce ta kawo Mairama dakin, tunda taji shiru
tasan aikin gama ya gama.


Zayyana ce ta fara dariya gashi ya soma lekowa amma saboda makero baifi a kirga ba
sai wani uban fari fari kamar amosani kamar kora. Kullum tana shafa mai idan tayi
wanka amma yau saboda da mutane a dakin ta hakura ta daure kayanta.
Kowa ta kalla gimtse dariya yake ta harzuka sosai tayi kan Zahra tana ihu "wallahi
sai na rama"


"KE! Samu wuri ki zauna kada naji kinyi fada da kowa."


Kuka ta fashe dashi da karfi "wallahi Ummi kada ki cuceni ki barni na rama."


"Zahra bata dankwalinta kafin na saba muku. Wane irin abu ne haka da girmanku
saboda Allah." Mami ta soma fada.


Jefa mata dankwalin Zahra tayi don yadda take kallonta kamar kura ta ga nama bazata
so hannunsu ya gogi na juna ba.


Jikinsu sai yayi sanyi saboda kukan da take yi ta dauki dankwalinta ta kulle kan
sannan ta mayar da hijabinta. Zainab da Mami na bata hakuri taki kula kowa sai
sautin kuka da take karawa. Mairama tace su kyaleta ba shiru zata yi ba. Kowa ya
fita daga dakin tana zaune tana kukanta dole Mami taje ta fadawa Major.


"A kirawo min ita"


Zahra ta kalli Fauziyya, a, tsorace tace "ba dai ni ba, kece babba kuma ke kika
bude mata kan"


"Zayyana...." Zahra ta soma kira ta bari saboda kyabe fuskar da ta ga tayi ta koma
gefen Major tana cewa


"Daddy kace bazani ba"


"Mazaje waye zai kira min 'yata?" Yace da Ibrahim da Emzee kamar yana rokonsu.


Ibrahim ne ya tashi, Emzee kamar ruwa ya cinye shi. Yana zuwa ya sameta ta gama
hada kayanta a cikin jakar da tazo da ita tana bakin kofa zata fito.


"Dariya ka dawo yi?"


"Daddy ne yake kiranki"


Gani tayi ya tsaya kallonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login