Showing 171001 words to 174000 words out of 295847 words
sani ba
Murmushi yayi "Ya wuce"
Daidai nan ya wuce wani kanti ta hango katan din lemuka an jere a waje harda na
maltina. Kwadayin ne ya motsa ta dube shi.
"Hammaaaa" muryarta ta doki kunnensa da shagwabarta da take bashi sha'awa yanzu.
"Uhmm"
"Ka saya min maltina don Allah yanzu ka wuce shop din a can" ta nuna da hannu.
"Kinyi dinner ne?"
"Sai anjima"
"Bazan saya ba, na kula ba kya son cin abinci kema"
Sake narke masa tayi sai da ya dage ya iya controlling kansa daga barin janyota
jikinsa.
"Hamma manaaa..."
Bashi da zabin da ya wuce juya kan motar ya barta a mota yaje ya siyo. Katan uku
aka saka masa a booth sai guda hudu masu sanyi a ledar hannunsa. Yana zama ya mika
mata ta balle saman gwangwanin tana sha tana lumshe idanu.
Rabi tasha ta mika masa ya karba sai da ya kalleta ya dora bakinsa a kai ta kawar
da kanta gefe.
"Tell me about your project tunda jira kike na roka"
Sun kusa gida lokacin ta soma yi masa bayani dalla dalla kamar ba Radhiyan da ya
sani ba. Shirmen yana nan amma ta fannin karatun bata wasa. Wannan ita ce Alheran
din da ya fada soyayyarta.
"Impressive. I am proud of you. Amma why mass comm? Meyasa baki zabi wani course
din ba?" Ya tambayeta bayan yayi parking din motar.
Gwangwani na biyu take shirin budewa ya karba ya bude mata. Kafin ta karba ta nuna
masa wannan zoben nasa.
"Ka ga wanda ya zaba min nan. A hannuna sunansa Awwab shi yace yafi son nayi mass
comm"
Duk kalma daya dake fita daga bakinta tana kara hura masa wutar soyayyarta ne.
Bazai sake yarda da wasu dalilai ba da zasu sa yaki aurenta wannan karon. Baya ma
tunanin komawarta school babu igiyoyinsa a kanta. So yake yaje ya kammala abinda
Mama ta katse masa ya dawo ayi komai a gama kafin ya koma aiki.
Kwantar da kansa yayi baya a jikin seat yace "Kin shirya aurensa yanzu"
"A'a"
"Reason?"
"Sai ya dena fushi dani"
Gwangwanin hannunta da ya bude mata ta mika masa "rage min".
Kurba daya yayi ya bata ta dauki ledar ta fita batare da ta sake cewa komai ba.
Yana kallonta har ta shiga gida ya fiddo wayarsa da niyar kiranta ya fallasa mata
duka sirrukan zuciyarsa ya ga kira da bakuwar namba. Yana karawa a kunnensa ya gane
muryar mai maganar mahaifin Arifah ne.
Tambayar farko da ya fara yi masa shine yana son sanin idan shi kadai ne a inda
yake. Idan ba shi kadai bane kuma ya tashi ya kebe akwai maganar da yake so suyi.
Awwab ya tabbatar masa da cewa shi kadai ne sannan yace masa yana bukatar passport
dinsa a daren saboda gobe da sassafe za'a zo a karba. Dakinsa yaje da sauri ya
dauko yanayin muryar Excellency yasa shi jin cewa akwai abinda yake faruwa. Bai
sanar da kowa ina ya tafi ba yaje gidan wanda kamar jiransa suke masu gadin aka
bude masa gate.
Wani falo PA dinsa ya jagorance shi suka je ya same shi tare da bakon da bai sani
ba. Duk da haka ya mika masa hannu suka gaisa bayan ya gaisa da gwamnan. Da turanci
domin kowa ya fahimta ya soma magana.
"Awwab wannan sunansa Chibuzor Kalu"
Murmushi ya sake yiwa mutumin wanda ya dauke a lokacin da yaji Excellency ya fara
fada masa abinda ya kawo Chibuzor garesu.
"Zayyan is alive and in prison"
Mikewa yayi tsaye yaji kansa ya kulle. Gaban Chibuzor yaje ta idanunsa suna nuni da
rauni matuka "is this some kind of a joke?"
[11/2, 7:11 AM]🏽
]🏽 : 41💕
Da ya fito Chibuzor yana tsaye can gefe ya gaji da magana ya koma yana sabunta
tunani da nemarwa kansa mafita. Baiyi zaton haka abin zai zama ba gabadaya ya shiga
cikin tashin hankali saboda tsoron kada ya kasa fitar da Zayyan.
Wancan mutumin ne ya dawo gareshi yace masa akwai mai wannan sunan da ya taba zama
amma yanzu baya nan.
Wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa "a ina zan same shi? Sako nake dashi mai
mahimmanci"
"Kana iya fada min sai na gani sakon yana da amfani ko babu"
Da dukkan murnarsa yace "na hadu da dan uwansa ne a prison...."
"You must be crazy" Sojan ya daka masa tsawar da ta janyo hankalin sauran da suke
gefe. Shi kuwa Chibuzor jikinsa rawa ya soma yi. Tun ba yau ba yaki jinin duk wani
abu da zai hada shi da hukuma. Sauran suka taru a kansa ana ta daga murya ya
gigice. Fada suke yi kawai akan yazo musu da zancen banza. Meye hadinsu da prison
da zai ce ya hadu da dan uwan dayansu. Dadin kayan haushin ma wanda yake magana a
kai baya nan. Basuyi masa uzuri yayi musu bayanin da ya dace ba suka nemi dukansa
ya gudu. A gajiye ya koma hotel din da yayi masauki ya kira matarsa Emma ya fada
mata yadda ta kasance.
"Ka koma gobe ka dage sai sun barka kayi magana da wani mai mukami a ciki. Banda
abinsu waye yake yanke hukunci babu sauraron bayani?"
"Gaskiya bazan iya komawa ba. Akwai matsalolin tsaro a kasar nan. Nayi sa'a da basu
kamani sun rufe ba. Kallon wani mara hankali ina jin suke yi min"
"Yanzu me kake tunanin yi a kai?"
"Ban sani ba" ya fada cike da damuwa.
"Darling, me zai hana kayi amfani da media? Ka tuna nima fa a TV kawata ta ganka a
news lokacin da aka kamaka a airport shine ta fada min"
Ihun murna Chibuzor yayi yana gode mata. Sam baiyi wannan tunanin ba yaje zai jefa
kansa ga wahala.
Karfe goma washegari a gidan talabijin na NTA reshen garin tayi masa. Filin cigiya
da sanarwa ya nema saboda a ganinsa gidan TV musamman na kasa wato NTA zai fi
saurin zama hanyar yada cigiyar. Idan ya gama da nan niyarsa ya nemi gidan rediyo
kuma a nan Sakkwato da Kano. Wata ma'aikaciya ce tayi masa bayanin cewa zai biya
bayan ya fadi na kwana nawa yake so a rinka sanya sakon. Da suka gama da wannan ya
fahimci komai ta bashi form da zai cike abinda yake nema.
"Idan akwai hoton wanda kake nema ko naka idan sun san fuskarka sai ka kawo"
"Babu hoto sai sunaye"
"Rubuta min a nan..." ta saka yatsanta a inda take bukata.
Chibuzor bai rike sunayen duka ba amma ya rubuta abinda ya tuna.
(Ina neman iyalin Lt. Zayyan Muhammad Tureta na Giginya Barrack Sokoto wanda ya
tafi Liberia a 1993. Sunan matarsa Mariyama, yarinyarsa Al.....) duk yadda yaso ya
kasa tuna sunan Radhiya da Zayyan ya fada masa wato Alheran (abokinsa Hadir da
Mustafa da kuma Col. Nasiruddeen Aliyu). Sunan karshe shine wanda yafi zama sosai a
kansa. Matar ya mikawa takardar zata duba domin tsara yadda sanarwar zata kasance
ta karanta bayanin nasa bai wani gamsar da ita ba. Dole sai sunyi masa tambayoyi
kenan yadda zai iya fadar me yake bukata kada ayi asarar kudi.
"Su wadannan baka san sunayen iyayensu ba domin saurin gano su?"
"Akwai matsala ne? Ban sani ba" ya bata amsa yana fatan kada tace bazai yiwu ba.
"Amma ai wannan na rike, Col Nasiruddeen Aliyu.."
Daga bayansa wani ya taho rike da takardu ya dakata da sauri "Col Nasiruddeen Aliyu
dai gwamnan Plateau? Me yayi? Ke akwai sabon news ne?"
"Ka sanshi ne? Nemansa nake" Chibuzor yace shima da sauri.
"Gwamna ne fa, waye bai sanshi ba? Me yake faruwa ne?" Ya tambayi matar.
Hannunsa Chibuzor ya rike "shi gwamnan soja ne? Yaje Liberia tsakanin 1993 da
1994?"
A dan tsorace mutumin ya zame hannunsa "tsohon soja ne yayi retire, amma ban sani
ba ko yaje Liberia"
A gigice Chibuzor ya fito da wayarsa daga aljihu ya rattaba sunan Col. Nasiruddeen
Aliyu a google search. Tashin farko sai ga bayanai sun bayyana game dashi. Inda
yasan ana saurin samun bayani ya fara dubawa wato wikipedia. Karatu yake yana
tsallaken layi kamar wani zai riga shi.
(Tsohon sojan kuma kwararren likita a wancan zamani ya tsunduma cikin siyasa ne
wajajen 1996 inda tauraronsa ya rinka haskawa yayi suna cikin kankanin lokaci.
Mutane suna alakanta wannan nasara tashi da cewa an sanshi a matsayin sojan da ya
kwashi kimanin watanni takwas a hannun 'yan tawayen kasar Liberia kafin Allah Ya
kubutar dashi wani dare da sojoji suka kai sumame a mabuyarsu. Tausayi da
jarumtarsa da aka gani yasa bai taba tsayawa takara ya fadi ba)
Mahaukacin ihu Chibuzor ya saki yana dariya "thank you Jesus" sannan ya kaiwa
mutumin nan wawura ya rungume shi kamkam sai da takardun hannunsa suka fadi. Bai
tsaya bata lokaci ba ya dire mutumin ya fita daga ofishin a guje.
Kai tsaye hotel din ya koma ya tattaro kayansa ya tafi airport. Ba shi ya sami
kansa a kofar gidan gwamnatin dake Jos ba sai yamma. Tunda ya gane wurin shawara
ita ce ya nemi masauki gobe ya dawo. Haka kuwa akayi domin washegari takwas ma a
bakin gate din ta riske shi. Ganin gwamna ba abin wasa bane. Masu gadi suka saka
shi a gaba aka fara masa tambayoyi akan dalilin zuwansa.
"Sako ne zan bawa Col. Nasiruddeen"
Ganin wani mara da'a suke yi masa. Idan ba mara da'a ba ya za'ayi ya kira sunan
gwamna a kofar gidansa kai tsaye irin haka. Shi kuwa dadewa rabonsa da Nigeria da
kuma idan yazo ba yawo yake irin haka ba yasa ya manta abubuwa.
"Nasha wahala ku taimaka min"
"Ka koma ka nemi appoitment dashi ba wai kazo haka kawai gida ba. Idan kowa na iya
ganinsa a gida duka garin nan zasu tare a nan kenan"
"Naji ta yaya ake neman appointment din?"
"Ka je office dinsa ka nema a can. Idan kayi sa'a ka ganshi a wata daya"
Suka kece da dariya. Wannan ko kadan baiyi kama da wanda Gwamnan nasu zai saurara
nan kusa ba saboda ayyuka da suka sha kansa 'yan kwanakin nan. Sannan kuma ai ba
haka nan ake ganinsa ba, akwai matakai da ake bi.
Bai hakura ba yace "yana gida yanzu ko office?"
"Yana office"
"Nagode"
Gefe ya koma abinsa ya tsaya a jikin katangar gidan. Da sauri cikin masu gadin mai
kayan sojoji yazo yace ya bar wurin. Gaba ya kara amma duk inda yayi sai ace ya
matsa wai ba wurin tsayuwa bane. Chibuzor baiyi zuciya ba don biyan bukata yafi
dogon buri. Ainihin titin da ake yin kwanar dama a kansa a shigo titin gidan
gwamnatin yaje ya sami inuwar wani gida da filawoyinsa suka hauro ta saman katanga
ya tsaya. A nan ya wuni ko ruwa bai matsa ya saya ba saboda tsoron kada ya rasa
abinda yake nema.
Gajiya, yunwa da shigowar sanyi wanda baya yiwa mutane da sauki a garin na Jos
sune suka sarke shi amma da yake mutum ne mai juriya da amana bai gajiya ba. Tunawa
kawai yake yi da shekarun Zayyan a prison dinnan yana ji a ransa da yana da hali ko
sakan daya bazai bari ya sake yi ba.
Tara da rabi na dare sai ga jiniyar motocin gwamna sun taho a sukwane. Ko kallon
titin da zai tsallaka baiyi ba ya bi zugar motocin nan a guje yana harin ta
tsakiyar wadda yafi tsammanin ita ce gwamnan ke ciki.
"Zayyan Tureta is alive"
"Zayyan Tureta is alive"
"Lt. Zayyan Tureta"
"Liberia prison"
Wadannan kalmomin ya rinka maimaitawa yana bin motocin yaki sauraron ihun da sojoji
suke yi masa.
His Excellency Nasiruddeen yana bayam mota tsabar gajiya har soma gyangyadi yaji
kalmar TURETA da LIBERIA. Firgigit ya bude idanu ya soma cewa "stop da car" cikin
gaggawa. Dreban sai da ya tsorata amma shi da PA sun kula kamar ba a hayyacinsa
yake ba duk ya rude shiyasa ya danna trafikato zuwa barin dama sauran motocin bayan
suka tsattsaya suma. Yau babu batun jiran a bude masa kofa da kansa ya bude don
sauri ya kusa faduwa saboda babbar rigarsa da ta harde shi. Wurin da sojoji masu
tsaronsa suka danne Chibuzor a kasa ya isa yana yi musu tsawar su daga shi. Kowa
darewa yayi gefe da suka ga ya durkusa ya tayar da Chibuzor zaune. Cikin harshen
turanci yace masa
"Me kace?"
Jikinsa babu kwari sosai ya dago kai yana kallonsa "kaine Col. Nasiruddeen Aliyu?"
"Nine, nine" ya rinka nanatawa yana gyada kai.
Yana jin wata kakkarfar ajiyar zuciya da yaron ya saki don bazai fi sa'an Awwab ba.
"Sir, Lieutenant ZAYYAN MUHAMMAD TURETA..."
"Ina jinka, Tureta nawa kake nufi? Wa ya aikoka? Daga ina kake?" Ya rinka jero
tambayoyin yana jijjiga shi.
"Liberia prison, the Lieutenant is waiting"
Hularsa ya tuge bai sani ba saboda yadda ya tashi tsaye da sauri "Lieutenant Zayyan
fa kace"
"1993 Liberia Peace Keeping Troop"
Zuciyarsa bugawa ta rinka yi da sauri da sauri yana tsoron kada ya gaskata maganar
mutumin ya tashi yaji ashe mafarki yake yi.
"Daga ina kake?"
"Liberia Prison"
"Innalillahibwa inna ilaihi raji'un" yace gumi na karyo masa "Zayyan yana da rai
dama?"
"Yace akwai Hadir ko shima yana da rai?"
Hannuwansa Excellency ya riko ya tayar dashi tsaye "nasan Hadir, nasan Mustapha,
nasan matarsa da 'ya'yansa kowa yana nan"
"Ahghhhh" Chibuzor yace da kyar saboda murdewar da cikinsa yayi ga dukan da ya soma
sha.
Excellency da kansa ya tallabo shi a jikinsa ya ja shi zuwa motarsa jama'arsa suna
kallonsa da mamaki. Wani ne yayi karfin halin cewa
"Your Excellency kawo shi mu saka shi a motarmu"
"Noooo muje kawai" ya amsa yana kankame Chibuzor a jikinsa. Da suka isa daidai
kofar shiga cikin gidan ma da kyar ya bari aka shigar masa dashi ciki. Kansa ya
kulle so yake yaji gamsasshen bayani. Matarsa da Arifah a ranar suka tafi Abuja
daga shi sai ma'aikata. Abinci yasa aka kawo masa yana zaune yana jiran ya gama ci
ya kara yi masa bayani. Shima a nasa bangaren baya jin zai iya yin komai sai ya
sauke wannan nauyin.
"Sunana Chibuzor Kalu"
"Ci abinci tukunna sai muyi magana" ya fada batare da maganar ta kai zuci ba.
"Bazan iya ba..."
Cikakken labari ya samu daga wurin wannan yaro tun daga rabuwar Zayyan dasu Hadir
zuwa yanzu. Sai ga His Excellency the Executive governor of Plateau state yana
zubar da hawaye. Shekaru daidai-daidai har ashirin da biyu rabon Zayyan da
iyalinsa. Kurkukun ce ta fado masa yaji wani kunci yana sauka a ransa. Garin yaya
bai taba tunanin komawa su duba wurare ko za'a same shi ba? To amma a gaban idonsa
aka yi masa harbi guda biyu ya fadi kamar matacce.
Wayarsa ya zaro wadda mutane kakilan suke da layin ga gumi duk ya jika tafin
hannunsa saboda girgiza da yayi ya soma neman sunan Major Mustapha. Bai kai ga
dannawa ba ya kwabi kansa. Bincike ya kamata ya fara yi ya tabbatar ba wai ya tayar
musu da hankali bisa abinda bashi da tabbacinsa ba.
**********
Kwanansu Radhiya biyu da zuwa kuma gobe Tante da Yousuf suke sa ran tafiya Nijar.
Jiya da Ummi tace suje gidan Daddy Haroun kafin lokacin fitar tasu dreban Major ya
kawo rahoton wahalar mai da aka fara tun daren jiya shima bai sami labari da wuri
ba. Yawancin masu ababen hawa kowa yana kan layin mai ko kuma ka daure ka saya
wurin 'yan bumburutu idan kana da hali. Awwab na ji yace idan sun fita sai suyi
full tank a wurin nasu. Raji ya nemi fassarar bayani a wurin Zahra da ta kawo masa
dankadafinsa Femi ta fada masa da turanci. Sai cewa yayi wai yana son yayi
experiencing bin layin mai irin wannan. Shi da kanwarsa a Germany aka haifesu kuma
bai taba katarin samun wannan matsalar ba a duk zuwansa Nigeria.
"Raji ba fa wurin shakatawa bane, nima ban taba bi ba amma nasan labarinsa. Wahala
ce kawai harda fada wani lokacin"
"To ba sai mu kafa tarihi ba" cewar Yousuf da yake jin hausa sosai kasancewar
babansa ba yarensu daya da Nasara ba. Hausar Nijar suke yi mai kamanceceniya da
Sakkwatanci.
"Gaskiya ba dani ba" Awwab ya fada zai gudu daga falon saboda ya ga zasu jajibo
masa wahala baiji ba bai gani ba.
Magana har wurin Daddy saboda Raji ya matsa wai yau daya dai su dana. Ba don yaso
ba aka ce ya tuna bakinsu ne ya karramasu da abinda suke so. Sai da suka yi la'asar
suka bar gidan. Raji yasa Zahra ta hada masa 'yar jaka da irin pillon nan na
matafiya a jirgi na kafada, abin rufa, touch light da 'yan kayan ciye ciye. Awwab
da baya son zuwa sai gashi yana dariyar mugunta. Wai shi nan Raji hango abin yake
kamar wani picnic ko camping. Yousuf ma da nasa shirin suka shige mota Awwab ya bi
bayan dreban da daya motar.
Sa'arsu daya yau tun safe garin dama da hazo da sanyi sanyi ba kamar jiya da suka
iso ba. Amma fa abu tun ana dariya sai gasu sunyi kicin kicin da fuska zukata sun
matso kusa. Layin mai ma ana alfarma. Ga rigimar cin layi da dai sauran abubuwa
marasa dadi da kan biyo bayan zama a layin mai. Layi har dare ko tafiya suka ce
zasu yi yadda wurin ya cushe da wahala su sami hanya ta dadin rai. Haka suka zauna
dare ya gabato sauraye suka ce salamu alaikum sanyin da zai koresu bai kankama ba
gara suma suyi full tank. Dukkansu jikinsu ya fada musu kuwa. Ba su suka koma gida
ba sai hudun dare. Zahra da Ummi ne kadai ido biyu. Take taken Raji na makalewa
Zahra yana ta korafin wahalar da yasha yasa Awwab bin Yousuf bangaren Ummi yana
girgiza kai. Zahra na ta zillewa amma yaki barinta. Awwab na jin yana cewa da a
gida suke wanka yake so ta taimaka masa yayi ya dauki kayan bukatarsa ya fita. Baya
son ganin abinda zai dame shi yazo yana jin kunya shi da kanwarsa su zama surukan
juna. Gara ya basu wuri ko yaya ne ta kula da mijinta. Radhiya ce ta fado masa a
rai lokacin da yake kwanciya a kan bargon da ya jefa a kan kafet din dakin Emzee ya
buga tsaki shi kadai yana ayyana wai ta cuce shi da yanzu shima...kwafa yayi kawai
ya kwanta.
"Kasan babu dadi ko? Ka dawo nan gadon zai ishemu" Yousuf yace da ya jiyo tsakin.
"Its okay mantuwa nayi mai mahimmanci, kaji ina tsaki ko" a rayuwarsa babu abinda
yake masa wahala kamar kwanciya kusa da mutane. Sai yayi ta ganin kamar zai takura
musu kuma shima baya son tasu takurar.
Karamar dariya yaji Yousuf yayi yana cewa "Raji yayi mana wayo. Mun sha wahala tare
wato shi mai mata ya gudu"
"Kai me kake jira" Awwab ya tambayeshi cikin duhun dakin yana fata kada yace abu
guda suke so. Yinin yau kadai Yousuf din ya kwanta masa akwai ilimi amma a wani
kamfani yake aiki ba likita bane. Ko me yasa jiya yaji Mama tace likita?
"Da dai na fara shiri amma na kula kamar bazai yiwu ba." Yanayin maganarsa zaka san
abin baiyi masa dadi ba sai dai a rayuwarsa bai yarda da cusa kai inda ba'a nemansa
ba. Yana son Radhiya kuma kanwa ce gareshi har kullum amma jiya shi kadai yasan me
ya gani suna yi da sunan cin abinci.
"Allah Ya musanya maka da mafi alkhairi"
"Amin, amma meyasa nake ji kamar kasan da wa nake?" Ya kuma yin dariya.
Wayancewa yayi shima yana dariyar
"Ban sani ba fa...kawai fatan alkhairi nake maka"
"Sai ka tayani nema tunda kasan irin wadda nake so"
Abin rufa Awwab yaja ya rufe