Showing 228001 words to 231000 words out of 295847 words

Chapter 77 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

yayi
sannan ya karbi award din daga hannun Chief of Army Staff ya mika masa.


Rahima babu inda take kallo sai Emzee da yake tsaye har lokacin a kame babu
gajiyawa taji wata irin azababbiyar soyayyarsa tayi mata kamun in ba kai babu
rayuwa. It was a moment da bazata taba mantawa ba a rayuwarta har abada.


Bayan Zayyan ya zauna ne su Emzee sun koma mazauninsu Chief of army staff din da
kansa ya gabatar da shirin Military Voice yace suna alfahari da wannan yunkuri na
sanar da duniya sadaukarwar da sojoji da iyalansu suke yi. Sannan gashi sun sake
ganin inda yake bukatar a duba domin tallafi ga wadanda suke cikin mawuyacin hali.


Sake yin duhu wurin yayi sai ga Radhiya tana gabatar da shirin sannan aka nuna
bangarori daban daban a ciki wanda ya janyo zubar hawayen mutane da dama a wurin.
Iyayenta da mijinta were so proud haka ma 'yan uwa.


MC KDM sai cewa yayi Radhiya ta fito tace wani abu game da shirin nan nata. Dif
tayi kamar ruwa ya cinyeta ta kasa motsi.. Dif tayi kamar ruwa ya cinyeta ta kasa
motsi.


💕[11/2, 7:24 AM] 👸🏽MAMIN SADIQ 👸🏽: 54.💕

Sake kiranta akayi taji cikinta yayi wata irin murdawa. Ina ita ina yin magana
kuma wai gaban wadannan mutane harda shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da 'yan
majalisu. Kan Awwab taji a daidai kunnenta saboda kamshin turarensa ta gane shine
cikin rada yace.


"Get up baby" taji tsigar jikinta ta tashi.


A sanyaye ta mike ya rike hannunta suna tafiya cikin burgewa ana daukarsu hotuna
sai da ya kaita bakin steps din da zata hau ya tsaya yace mata "go on zan jira
ki".


Har ta haye yana jin taushi da dumin hannunta a cikin tafin hannunsa. Tsayuwa ta
gyara ta kalli iyayenta taji wani kwarin gwiwa ta soma magana a nutse. Ta yabawa
sojoji akan rayuwar da ba kowa yake da zuciyar yinta ba ta kara da rokon a dube su
domin sun cancanci kulawar al'ummar da suke yiwa bauta.
"Soja shi kadai ne yake mayar da kowane dan kasarsa dan uwansa a lokacin tashin
hankali. Kowa zaiyi kokarin ceton nasa amma soja zai tsaya ya kai ceto ga wanda
kila har ya gama taimakon ko kwakkwaran kallo bazai sami damar yi masa ba bare ace
akwai wata alaka. Soja babu ruwansa da bambancin al'ada ko addini. Yare daya yake
fahimta shine SAVE, HELP AND PROTECT EVERYONE." Daada ta kalla tace "Ina rokon
afuwar babban bakonmu domin zan saci kalmominsa long live Nigeria, God bless my
country"


Haka aka rinka tafawa Radhiya sai da tazo step din karshe Awwab ya mika mata hannu
ta rike ya kaita har gaban seat dinta sannan ya koma ya zauna.


Taro ya burge matuka Zayyan ya sami alkhairi fiye da zato da tsammani. Supervisor
din Radhiya tazo ta rungumeta su ma sunji dadi domin kuwa a take wani da minister
of information ya tura musu ya bukaci su cigaba da bata duk wani training da zai
taimaka mata domin su tababbatar da bunkasar wannan shiri.


Sun fito tafiya Arifah tayi gefe ashe mukullin motarta zata karba da tasa dreba ya
kawo mata. Yousuf yazo ya shige ya zauna bayan ya radawa Awwab cewa gida kawai zai
rakata sai ya dawo.


"Kuma an fada maka zan yarda da wannan zancen ne" yace yana dariya.


Yousuf ya rage murya yana dariya shima "ni dai ko yaya sai na tabbatarwa Arifah ni
mijinta ne yau...kada ka rufe min kofa rakiya ce kawai zanyi"


Kusan kowa ya fito ana ta shiga mota. Awwab na kallon Radhiya ta shige motar da
suka zo. Wadda ya tuko ya shiga kai tsaye gidan Daada yabi bayansu Bilal yana
tambayarsa ina zasu je kuma yace "rakiya zanyi na dawo". Daga bakin gate ya cillawa
Bilal key din motar yace shima kada a rufe masa kofa sai ya dawo.


Raji dariya kamar me sun dago angwayen hakurinsu ya kare ne. To su din ma ciki suka
shige kowanne ya kira matarsa.


Tana hawa bene a gajiye taji wayar Awwab saboda kidansa daban ne. Da sauri ta dauka
ga kuma kunyarsa da take ji.


"Kina ina?"


"Yanzu muka shigo gida"


"Yunwa nake ji Schatzi" taji yace harda marairaicewa.


"Ka karasa gida ne?"
"Na biyo matata ta bani"


Saukowa tayi da sauri tana fita suna karo ya riko hannunta ya ja ta gefe sai da ya
gama dube dubensa ya turata wani karamin falo wanda kujeru ne kadai a ciki sai
tutar Nigeria a tsaye. Faduwa gabanta yayi da ya tura kofar da kafarsa ya rinka
taku a hankali zuwa gabanta. Kasa dago kai tayi sai dai ba shiri ta daga din
sakamakon daukan da Awwab yayi mata.


Dagota yayi ta hanyar saka hannuwa daga kasanta yayi sama da ita dole ta saka
hannuwanta ta riko wuyansa domin kada ta fadi. Idanunsu cikin na juna ya soma juyi
da ita yana dariya itama sai da tayi saboda yadda yake yi mata.


"Nice to meet you Mrs Awwab" yace lokacin da ya direta a gabansa.


Kunyar ce ta motsa saboda yadda ya tsareta da idanu ta kasa magana sai ma juyawa da
taso yi ta fita. Hannunta kawai ya janyo ta fado jikinsa ya rungumeta sosai. A tare
suke sauke numfashi da ajiyar zuciya yau burinsu ya cika. Kanta yana kirjinsa ya
saka hannuwa a bayanta ita kuma nata suna ta wurin cikinsa ya soma magana cikin
wani irin salo da shaukin soyayya.


"Alheran don Allah kada mu taba bari fushi ko wata zugar mutane su shiga
tsakaninmu. Nasan ni dake are not perfect but we complete each other. Kece zabin
Awwab tun kin baby har ranar da zai dena numfashi in sha Allah"


Kalamansa sun kara masa matsayi da kima a idanunta. Batare da ta dago kanta ba ta
yi magana don tsokana "har lokacin da aka yi min aski?"


Murmushi yayi "tashinki daga baccin nan da kallon da kika yi min shine lokacin da
Awwab ya fara yiwa Alheran soyayyar da yake fatan ta kare a aure"


Murmushin da tayi ne ya janyo shigewar dimple dinta ciki sosai. Abinda Awwab ya
dade yana jiran damar yi sai ji tayi ya dora lips dinsa a wurin yayi kissing dinta.
Kunya har sai da taji cikinta yana wata irin yamutsewa shi kuwa bai tsaya ba sai
pin din da tayi rolling dashi yabi ya zaresu ya zame mayafin. Kansa ya kai gaban
goshinta yana shafa gashinta da yake kulle cikin ribbon tayi packing dinsa a
tsakiyar kanta ya kuma bata wani kiss din.


Da wata irin murya yace "rufe idanunki"


Ki tayi sai dai suna hada ido ta runtse nata da sauri saboda bata da kuzarin cigaba
da kallon idanunsa. Tana ji yana dan motsi amma bata bude ba taji ya saka hannu ya
zame mata ribbon ya cusa yatsunsa cikin gashinta ya sake matso da ita. Bakinsa ya
hade da nata a nutse ya jefa mata sweet din bakinsa irin wadda suka taba sha a
soron Malamijo. Bata san lokacin da ta bude idanuwanta ba saboda ta gane dandanon
alawar. A haka suka sha ta kusa rabi sannan ya bar mata a bakinta ya sake janyota
jikinsa.


"Ina jindadi idan muna sharing abu...nafi son ko me naci babyna ma taci. I hope
daga yau haka zamu koma yi...it is better than daya ya ragewa daya"


Duk da bakon yanayin da take ji sai da ta tsokane shi "harda abinci ko?"


"Ewww ke fa kazama ce" yana bata fuska da tunanin a tauna abinci daga baki.


Dariya tasa "kaga tuwo zaiyi dadi...."


"Fita, fita ki tafi dirty girl" yace yana nuna mata kofa tare da dora mata
mayafinta a ka.


Turjewa tayi "nama fa?"


"Out" ya kuma cewa yana bata fuska ya dago hannu ya biyota ta kara gaba da sauri.
Tana bude kofar ya janyota ya rungumeta ta baya kansa na kafadarta "babu abinda zai
fito daga bakinki na kyamace shi Schatzi. Idan kin ga dama har kunu musha a haka"


Ita ya bari da bata fuska "shhhh please Hammana dena fada"


"Ko kosai shima zaiyi dadi"


Yatsunta tasa ta toshe kunnuwanta ya sake matseta "juyo kiji last one din"


Kafada ta noke ya juyo da ita da kansa "I love yo baby"


A hankali ta dago kai ta kalle shi idanunta sun kara girma da haske tace "I love
you Chèri" tare da shammatarsa ta fice da sauri.

💕[11/2, 7:24 AM] 55💕
. A bangaren Yousuf da Arifah kwatancen hanya ta rinka yi masa a kunyace har su ka
iso titin da zai sada su da gidan inda daga nan ya gane hanya. Ciki ya shiga tunda
masu gadin sun gane motarta kuma tana ciki. Duk ta daburce saboda auren nasu yazo
da wuri basu gama sabo sosai dashi ba. Ya san da hakan shima shiyasa yake kokarin
dinki duk wata kofa kafin su fara rayuwar auren sosai.


"A love yanzu yaya zaki yi dani?"


Fasa bude kofar tayi ta waigo kadan "me ya faru?"


"Kin taho dani gashi bansan hanyar komawa ba kuma bani da ko cent a jikina da zan
nemi taxi. Ga dare..." yace da wani irin yanayin da zaisa a tausaya masa.


"Kaine fa kace zaka rakoni in karbi motar. Yanzu yaya kake so ayi?"
Kwantar da kansa yayi baya ya jingina da kujerar yana kallonta "Nima ki rakani"


"Yanzu su Mom zasu dawo ace ina naje?"


Bude bangaren shi ta ga zaiyi cikin yanayin ko in kula yace "tunda haka ne muje
kawai na kwana a dakinki kinga gobe sai mu shirya daga nan mu tafi zaifi sauki"


Idanu ta zaro tana kada hannu "wasa kake yi amma"


"Gadon naki karami ne? To ba sai ki kwanta a kasa ba ni ki bani gadon tunda nine
bako"


Dariya ya bata ma yadda yake maganar tace "rufa min asiri...ko za ka kira Yayana
yazo ya daukeka?"


"Ni bazan shiga rayuwar kanwata in hanata samun kulawa daga mijinta ba"


"Hmm Y love rigima kake ji naga alama"


"Ko daya" yace yana kamo hannunta ya rike yana murza yatsun.


"To ka dauki motar ka tafi da ita"


"In bata a hanya gobe ace ba'a ganni ba...naki"


"Bari na nemi dreba ya mayar da kai"


Bata rai yayi "bana so"


"Ya zamuyi to?" Tace tana tura baki don tsoronta daya kada iyayenta su dawo a gansu
sai ace bata da kunya musamman Mom dinta. Bata san yaya akayi ba ya janyota rabin
jikinta a cinyarsa ya rungumeta sosai yana shakar kamshin jikinta mai dadi. Kansa
yana gefen wuyanta sai numfashinsa kawai take ji yace.


"Mhmmm mon amour" yana jin kamar su kwana a haka "...inata baki haske, inata baki
haske kinki ganewa."


Yadda hausar tasa ke fita da abinda yace ne ya sakata dariyar dole "kana ta bani
haske..."


"Eh mana amma baki gane ba....kowane ango yana tare da matarsa ni tawa tana nuna
min halin hausawan Nigeria"
"Ban dau haske bane" tace a hankali tana kokarin zamewa sai gashi tar an hasko wata
torchlight mai mugun haske sosai cikin motar ta barin da yake.


Arifah gabadaya ta gigice don kunya ta fasa guduwa sai ma kara kankame shi da tayi
a kunyace bata son ko waye a tsaye ya ganta a haka. Yusouf kuwa ko a jikinsa sai ma
sauke glass da yayi rabi har lokacin tana cikin jiikinsa. Security din yace da
pidgin english "na Madam i dey find I never see her comot from the car"


Ko kalma daya bai fahimta ba sai ma kullewa da kansa yayi yace "pardon?" Sai kuma
kawai ya dan taba kafadarta


"Ba fa na jin yaren nan ki kore shi kafin nayi masa ido daya na ganin matata"


Yadda yake bata rai ma abin dariya ne. Haka ta daure ta dago kanta kadan "Oga
Sunday I dey come"


"No wahala" mutumin yace tunda ya tabbatar tana nan ya juya abinsa.


Kokarin tashi daga jikinsa ta soma yi "Y love bari na hadaka da driver please"


Sake riketa yayi ta kasa motsawa "ke kuwa ki dau haske mana A love, biyoki nayi fa
don mu taya juna murnar aure"


Duk wasu dabarunsa ta gama ganewa. Ko Radhiya kanwarta ai tasan ta wuce ayi mata
wannan wayon bare ita. Wace murnar aure zata yi a kofar gida. Hannunta ta mika masa
na dama ya riko da nasa ta dan daga hannun sama da kasa tana jinjinawa
"congratulations on your...."


"Rike kayarki tunda baki daukar haske ga abinda nake nufi" yace yana kai mata wani
irin kiss da ya hanata motsawa.


Dirin motocin da suka ji daga waje ne ya tayar musu da hankali su duka ta tashi
daga jikinsa da sauri.

"Yanzu ya zamuyi?"


Tashin hankali karara a fuskarsa yace "nima ban sani ba, ba gidanku bane"


A tsorace take amma dole tayi dariya don ya fita rikicewa. Shiyasa yaso ta dau
haske tun dazu ya samu ya gudu saboda Yousuf mutum ne mai kunya sosai. Ko lokacin
da yaso Radhiya wannan kunyar ita tayi ta cutarsa ya kasa fada da wuri ashe rabon
Arifah Nasiruddeen ne. Saurin kiran Awwab yayi yace yazo ya dauke shi su tafi.


***********
Bayan fitar Radhiya daga falon da sauri ya biyo bayanta amma bai ga alamunta ba. Da
gudu ta shiga cikin gidan tana ji kamar za'a gane me tayi. Awwab zai kirata kenan
don shi bai ki yau ya kwana a gidan ba Yousuf ya kira.


"Ni gaskiya bazan zo ba rakiyar taka tayi kadan ni kuma yanzu na fara" yace masa
yana dariya.


Yousuf ya kalli motocin su Baban Arifa "Kada muyi haka mana Awwab ni da na baka
kanwata ya kamata ka kyautata min"


"Ni ba kanwar na baka ba"


Daga murya Yousuf yayi amma kana ji kasan kawai damuwa ce "kada kasa na dage bikin
nan sai ta gama ècole"


"Daidai kenan, sai ayi bikin da baby dinmu mu shiga gida mu uku ko hudu" bai san me
ya dami Yousuf din ba amma dadin tsokanarsa yake ji yana dariya lokacin da Raji da
Bilal suka fito kowa da murmushi saman fuskokinsu.


"A love kiyi masa magana" Yousuf yace da Arifa kamar yayi kuka.


Tana karbar wayar ta soma magiya don tana iya hango kallon da Mom dinta take sakar
mata bayan ta fito daga mota. Yousuf sai ji yayi wani gumi na neman saukar masa duk
sanyin garin. Tare da Arifah suka matsa wurinsu suna musu barka da dawowa.


"Yousuf ba dai sawa tayi ka kawota ba ka biye mata kai kuma?" Cewar Mom tana musu
kallon daidai.


Awwab na jin muryarta da hannu yayiwa su Raji alama suka shige mota yaja suna
dariya yau sun sami abin tsokanarsa. Rakiyar yau bata yi ba sai dai ko gobe a sake.


Yousuf yace da Mom "na ga ta karbi motar ne ga dare. Su Awwab nake jira zamu tafi
suna hanya"


"To babu damuwa bari na wuce"


Excellency da mutanensa yayi gefe suna magana yana yiwa ango da amarya murmushi
yace su shiga ciki kafin Awwab din ya karaso. A ransa kuwa dariyar yadda Mom sarkin
takura ta ritsa su yake yi. Tunda anyi aure ba shikenan ba, ko don tayi sa'a ba sai
da safe ya dawo mata da 'yarta ba.


A cikin gidan ma kamar yana kan kaya hankalinsa bai kwanta ba saboda hawa da saukar
da Mom ta rinka yi sai da Awwab ya kira shi. Da sauri ya fita daga gidan yana sauke
ajiyar zuciya.
Kai daren ranar kamar yayi ihu saboda yadda su Awwab suka saka shi a gaba da
tsokana. Mami tana jiyo hayaniya daga dakin Awwab inda suke kwana kamar wasu yara.


"Irin haka basarwa ake yi Yousuf" Awwab yace yana mike bayansa akan gado saboda
gajiya.


"Zan rama duk kuyi ku gama. Kuma matsa min na kwanta yau nan nake so."


Ture Awwab yayi tsakiya dariya ta hana shi tabuka komai har Yousuf din ya kwanta a
wurin mutum biyu don da gangan ya bude hannuwa wai baya son takura.


**********


Fauziyya da Zahra sun riga Radhiya shiga daki. Rahima da Zayyana wani dakin suke
kwana a kasa yanzu saboda yayyensu dake saman a dakin Radhiya ga yara biyu.


Yadda take sauke numfashi Zahra ta tambayeta ko gudu tayi ta gyada kai.


"To dai mutum ya girma guje guje ba naki bane amaryarmu" Zahran tace mata.


"Kyaleta fa tayi abinta nan da sati biyu ko da kudi nasan da wuya ta iya daga kafa"


"Me zaisa Adda Fauzi?" Radhiya tace da iyaka gaskiyarta.


Zahra tace "Kyale wannan yayar taki kin santa sarai da tsokana"


Tawul ta dauko za ta cire kayanta ta shiga wanka Fauziyya ta fara yi mata kallon
mara gaskiya saboda a takure take wanda ba halin ta bane.


"Amaryar Hamma kada kice min janbakin nan ya goge...gaskiya ina jin ba mai kyan
kika saya ba. Ni fa shiyasa abu designer bai dameni ba, ance baya fita da wuri sai
an goge shi amma ke lips dinki kamar baki shafa komai ba. Kalli ki gani" ta juya
tana nunawa Zahra da tsokana.


Radhiya ta rasa yadda zata yi sauran abinda basu gane ba ma sun gane don ba karamar
kunya taji ba, shikenan Hammanta ya janyo mata. Turo baki tayi kamar za ta yi musu
kuka "to ba...ba...uhmmm tissue na saka na goge"


Fauziyya ta saki fuska "ohhh irin makeup remover dinnan ko? Please nima bani nagoge
don ni sanyi nake ji bazan iya wanka ba"


"Fauziyya ki kiyayeni ko in kira Ya Bilal yazo ya kwashe mana ke kowa ya huta.
Mutum yana fama da kansa amma baki baya shiru" cewar Zahra amma daga ita har
Fauziyyan dariyar tsokana suke yiwa Radhiya. Yau mai balotelli an dinke mata baki.


Cikin dariya Fauziyya tace "wai ma in tambayeki, makeup remover din baya goge fuska
iyakarsa baki kawai?"


Sai yanzu Radhiya ta fahimci ina suka dosa da wannan tambayar da dariyar. Aka yiwa
wani ma ta rama bare an shiga gonarta. 'Yar dariya tayi tana sunkuyar da kai tace
"sauran yana bakin Hammana shi ya goge min"


Idanu Fauziyya ta zaro Zahra kuwa dariya harda rike ciki. Suna son juna idan an
hado kamar kar a rabu saboda irin wannan dramar.


"Kika bashi ya shanye?" Fauziyya tace fuskarta kadai sai tasa mutum dariya.


Radhiya ta gimtse dariyarta ta zauna kan gado ta dora kafa daya kan daya tana
daukar wayarta. Sunan da ta saka masa Mon Chèri (my sweetheart) ta nemo tana nunawa
Fauziyya "In kira shi ki tabbatar?"


"Zahra ki fadawa su Mama tun wuri kada gobe labari ya wuce goge lipstick a bashi
matarsa"


"Ba tambayata kika yi ba Adda Fauzinmu" tace da shakiyanci.


"Ah to matambayi baya bata gashi nan an dora ki akan hanya yadda zaki gane" cewar
Zahra har lokacin dariya take yi sosai ita da Radhiya. Katse dariyar suka yi a dole
da suka ji ance


"Schatzi" daga cikin wayar hannunta.


Su duka ukun suka kalli wayar harda ita da ta kira bata sani ba kafin suka fice
daga dakin a guje suna dariya sai ka rantse yara ne masu kananun shekaru. Awwab da
yaji shiru sai ya kashe wayar yana tunanin kila bata san ta kira ba saboda dare
yayi.


Da suka koma dakin ma suna kallon juna sai su kwashe da dariya Fauziyya na cewa
dadin abin itama an goge mata nata janbakin yau da tayi kwanan tausayin kanta.


Komai nasu abin sha'awa musamman wannan hadin kan da ya samo asali daga jajircewar
iyayensu.


**********


Washegari wuraren shadaya na safe a can gefe guda na katon falon gidan Zahra ce da
kannen nata Fauziyya da Radhiya Rahima tana yi musu lalle iya yatsun hannu kawai
banda kafa. Su na cikin yi Mami da Mama suka shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login